1
Jerin Littafan Shi’a Na 11
Aqidar Ahalus Sunna
Umar Labxo
2
بسم الله الرحمن الرحيم
Gabatarwa
Godiya ta tabbata ga Allah Maxaukakin Sarki. Tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad
(SAW) da Alayensa da Sahabbansa da waxanda suka bi tafarkinsu har zuwa Ranar Sakamako.
Bayan haka, yana daga cikin qa’idojin koyarwa da tarbiyya idan aka hana wa mutane abu
mummuna sai a musanya musu da wani kyakkyawa wanda zai maye makwafin na farkon kuma
ya cike gurbinsa. Bin wannan qa’ida ne ya sa, bayan bayanin vacin tafarkin Shi’anci da
muguscin aqidun ‘yan Shi’a a cikin littafai goma da suka gabata a wannan jeri, mu ka ga ya
zama wajaba mu kawo bayanin tafarkin Sunna da Aqidar Ahalus Sunna wacce ita ce aqidar
Annabi (SAW) da Sahabbansa, da Tabi’ai da waxanda suka bi tafarkinsu har ya zuwa yau.
Wannan littafi fassara ce ta littafin Al’aqidatul Wasixiyya na Shaihul Islami Ibnu
Taimiyya, Allah ya jiqan sa. Littafin ya tattare aqidar Ahalus Sunna a sauqaqe, tare da dogaro
kacokan wajen tabbatar da ita a kan Alqur’ani da Hadisai ingantattu a bisa fahimtar magabata
na-gari.
Rubuta aqidar Ahalus Sunna a sauqaqe tare da dogaro da Alqur’ani da Sunna a bisa
fahimtar magabatan al’umma, kamar yadda Ibnu Taimiyya ya yi a cikin wannan littafin, abu ne
da xaruruwan malaman Sunna suka yi tun daga qarni na biyu bayan Hijira har ya zuwa yau.
Wani malami na zamanin nan mai suna Abdussalam binu Barjis Aali Abdilkarim ya tattara
tarihin irin waxan nan littafai xari uku da talati da huxu (334) da manyan malaman Sunna suka
rubuta tun daga shekarar 167 B.H. har zuwa 1400 B.H., a cikin littafinsa mai suna Tarikhu
Tadwinil Aqidatis Salafiyya, wanda ya buga a shekara ta 1430/2009.
Littafan aqida yawanci suna qunsar qudure-qudure da Ahalus Sunna suke qudurewa a
matsayin imani, kamar qudure cewa imani ya haxa magana da aiki, da cewa ana sifanta Allah da
abinda ya sifanta kansa da shi ko Manzonsa ya sifanta shi da shi, da cewa Alqur’ani zancen
Allah ne ba halittacce ba ne, da cewa Allah shi ne Mahaliccin kome, da cewa abinda Allah ya so
shi yake kasancewa kuma abinda bai so ba ba zai kasance ba, da cewa Allah mai iko ne akan
dukkan kome, da cewa Ahalus Sunna ba sa kafirta mai sallah don ya aikata zunubi, da cewa suna
imani da ceto ga masu zunubai, da sauran su. Irin waxan nan abubuwa su ne tattare a cikin
littafin da muke gabatarwa a nan.
Wani abu da irin waxan nan littafai suke sifantuwa da shi, wanda kuma littafin da muke
fassarawa shi ma ya sifantu da shi, shi ne dogaro kacokan da ayoyin Alqur’ani da hadisan
Annabi ingantattu, kamar yadda muka ambata a baya kaxan, saboda al’amuran aqida babu ra’ayi
ko ijtihadi a cikin su. Don haka mai karatu zai ga ruwan ayoyi a cikin wannan littafi, a yawancin
lokuta ma babu wata fassara ko qarin bayani. Kamar yadda mai karatu zai lura da cewa,
3
yawancin hadisan da aka ambata a cikin littafin hadisan Sahihaini ne, watau Bukhari da Muslim,
waxanda su ne qololuwar inganci.
Wannan shi ne abinda yake gaskata abinda muka gabatar da ambaton sa a baya cewa,
wannan aqida ita ce aqidar Annabi (SAW) da Sahabbansa; domin an tsamota ne kai tsaye daga
Alqur’ani da Sunna, kuma gwargwadon fahimtar Sahabbai da Tabi’ai da waxanda suka bi su da
kyautatawa har zuwa ranarmu ta yau.
Kuma cewa wannan fahimta ita ce fahimtar Sahabbai da Tabi’ai ba wai faxi ne kawai da
baki ba, a’a haka abin yake. Idan mutum ya duba Kitabut Tauhid a cikin Sahihul Bukhari haka
zai gani. Haka nan, idan ya duba babin Tauhidi ko aqida a cikin littafan Hadisi duka: Muslim da
Abu Dawud da Tirmizi da Nasa’i da Ibnu Majah da Muwaxxa, da sauransu, haka zai gani.
Kuma wannan ita ce aqidar limaman Mazhabobi: Imam Malik da Shafi’i da Abu Hanifa
da Ahmad binu Hambal da mabiyansu. Ba’a samu kauce wa wannan aqida ba sai a wajen ‘yan
baya, a lokacin da ilmin Falsafa ya yaxu a tsakanin Musulmi kuma suka tasirantu da shi. A
wannan lokaci ne qungiyoyin bidi’a, kamar Mu’utazilawa, suka fara dogaro da hankali,
maimakon nassi, wajen fahimtar al’amuran aqida. Kuma ko ba’a faxi ba, hankali wanda a
xabi’arsa taqaitacce ne, ba zai wadatar ba a cikin al’amuran aqida da imani.
Wannan ya sa dukkan maluma na gari suka zargi Ilmul Kalami, watau ilmin da yake
dogaro da hankali wajen warware mas’alolin Tauhidi da aqida. Kuma suka xaura himma wajen
rubuta irin waxan nan littafai na aqida waxanda muke gabatar da xaya daga cikin mafi
kyawunsu: Al’aqidatul Wasixiyya.
Mun yi fassara mai sauqi, da nufin ganar da kafatanin makaranta, kamar yadda muka
saba a cikin ayyukanmu, tare da kiyayewa da saqon da littafin yake isarwa, babu daxi, babu ragi.
A wajen fassara ayoyin Alqur’ani, mun dogara da Tarjamar Ma’anonin Alqur’ani Mai Girma
zuwa ga Harshen Hausa na Shaihu Abubakar Mahamud Gumi, ba mu fita daga cikinsa ba sai a
‘yan wurare kaxan. Dangane da hadisai kuwa, rashin tsayayyar fassara ga littafan Hadisai ta
tilasta mana dogaro da kai wajen fassara su, tare da qoqarin bayyana ma’anarsu da kiyayewa da
manufarsu.
Muna roqon Allah Maxaukaki ya xora mu a bisa doron sawaba, ya sa ihilasi da tsarkin
niyya a cikin ayyukanmu da maganganunmu, ya nesanta mu da riya da son-a-sani. Allah ya
amfane mu da abinda muka rubuta, ya sa ya zama guzurin zuwa kabari. Allahumma Amin.
4
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinqai
Aqidar Tawagar Masu Tsira
Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya aiki Manzonsa da shiriya da addinin gaskiya domin
ya rinjayar da shi a kan addinai dukansu. Kuma Allah ya isa ya zama mai shaida.
Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai, ba shi da abokin tarayya,
don tabbatarwa ga tauhidinsa. Kuma ina shaidawa cewa, Muhammad bawansa ne, kuma
Manzonsa ne. Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, da Alayensa da Sahabbansa, tare da
sallamawa mai tarin yawa.
Bayan haka, wannan ita ce aqidar tawagar masu tsira, taimakakku har zuwa tsayuwar
alqiyama: Ahalus Sunna wal Jama’a. Shi ne imani da Allah da mala’ikunsa da littafansa da
Manzanninsa da tashi bayan mutuwa. Da imani da qaddara, alherinta da sharrinta.
Yana daga imani da Allah, imani da abinda ya sifanta kansa da shi a cikin littafinsa, da
abinda Manzonsa ya sifanta shi da shi, ba tare da karkatarwa ba ko vata ma’ana, haka nan ba tare
da takamaimai ko kamantawa ba. Amma suna imani da cewa, shi Allah Maxaukaki “Wani abu
bai zama kamar tamkarsa ba, kuma shi ne mai ji, mai gani.” (Suratush Shura: 11).
Don haka ba sa kore masa abinda ya sifanta kansa da shi, kuma ba sa karkatar da zance
ga barin mahallinsa. Ba sa ilhadi a cikin sunayen Allah da ayoyinsa. Ba sa takamaimaitar da
sifofinsa kuma ba sa kamanta su da sifofin halittunsa. Domin shi, tsarki ya tabbatar masa, ba shi
da takwara, ko sako, ko kini, kuma ba’a kwatanta shi da halittunsa, tsarki ya tabbatar masa, ya
xaukaka. Babu shakka shi, Maxaukaki, shi ne ya fi sanin kansa, ya fi sanin waninsa. Shi ne mafi
gaskiyar zance kuma mafi kyawun magana daga halittarsa.
Sa’an nan kuma, Manzanninsa masu gaskiya ne, ababen gaskatawa, savanin waxanda
suke faxi masa abinda ba su sani ba. Don haka ya ce, “Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka,
Ubangijin rinjaye, daga barin abinda suke siffantawa. Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.” (Suratus Saffat: 180-182). Sai Ubangiji ya
tsarkake kansa ga barin abinda masu savawa Manzanni suke sifanta shi da shi, kuma ya yi
sallama ga Manzanni saboda kuvutar abinda suka faxi daga tawaya da aibu.
Shi, tsarki ya tabbatar masa, ya haxa tsakanin korewa da tabbatarwa a cikin abinda ya
ambaci kansa kuma ya sifanta kansa da shi. Saboda haka, babu karkacewa ga Ahalus Sunna wal
Jama’a ga barin abinda Manzanni suka zo da shi. Domin shi ne tafarki madaidaici, tafarkin
waxanda Allah ya yi ni’ima a gare su na Annabawa da Siddiqai da Shahidai da Salihan bayi.
5
Babi Na Xaya
Sunayen Allah da Sifofinsa a cikin Alqur’ani
Gamewa tsakanin Korewa da Tabbatarwa
a cikin Sifanta Allah Maxaukaki
Daga cikin wannan akwai abinda Allah ya sifanta kansa da shi a cikin Suratul Ikhlas,
wacce take dai-dai da sulusin Alqur’ani, inda yake cewa, “Ka ce: Shi ne Allah Makaxaici, Allah
wanda ake nufin sa da bukata. Bai Haifa ba, kuma ba’a haife shi ba. Kuma babu xaya da ya
kasance tamka a gare shi.”
Haka nan abinda ya sifanta kansa da shi a cikin mafi girman aya a Littafinsa, inda yake
cewa, “Allah babu wani ubangiji face shi, Rayayye, mai tsayuwa da kome, gyangyaxi ba ya
kama shi, kuma barci ba ya kama shi, shi ne da abinda yake cikin sammai da abinda yake cikin
qasa. Wane ne wanda yake yin ceto a wurinsa, face da izininsa? Yana sanin abinda yake a gaba
gare su da abinda yake a bayansu. Kuma ba su kewayewa da kome daga ilminsa, face da abinda
ya so. Kursiyyunsa ya yalwaci sammai da qasa. Kuma tsare su ba ya nauyayar sa. Kuma shi ne
maxaukaki, mai girma.” (Suratul Baqara: 255).
Gamewa tsakanin Xaukakarsa da Kusancinsa
da Azaliyyarsa da Abadiyyarsa1
A cikin faxin Allah, tsarki ya tabbatar masa, “Shi ne na farko, na qarshe, Bayyananne,
Voyayye, kuma shi ne Masani ga dukan kome.” (Suratul Hadid: 3). Da faxinsa Maxaukaki,
“Kuma ka dogara a kan Rayayye wanda ba ya mutuwa.” (Suratul Furqan: 58). Da faxinsa,
“Kuma shi ne Masani, mai hikima.” (Suratut Tahrim: 2). “Kuma shi ne mai hikima, mai
labartawa.” (Suratu Saba: 1).
Kewayewar Ilminsa da Dukan Halittarsa
“Ya san abinda yake shiga a cikin qasa da abinda yake fita daga gare ta, da abinda yake
sauka daga sama da abinda yake hawa a cikinta.” (Suratu Saba: 2). “Kuma a wurinsa mabuxan
gaibi suke, babu wanda yake sanin su face shi, kuma yana sanin abinda ke a cikin tudu da ruwa,
kuma wani ganye ba ya faxuwa, face ya san shi, kuma babu wata qwaya a cikin duffan qasa,
1 Azaliyyarsa: rashin farko, watau na tun fil azal. Abadiyyarsa: rashin karshe, watau na har abada.
6
kuma babu xanye, kuma babu qeqasasshe, face yana a cikin wani littafi mai bayyanawa.”
(Suratul An’am: 59).
Kuma da faxinsa, “Kuma wata mace ba ta yin ciki, kuma ba ta haihuwa, face da saninsa.”
(Suratu Faxir: 11 da Suratu Fussilat: 47). Da faxinsa, “Domin ku san lalle Allah mai iko ne a kan
dukan kome, kuma lalle Allah, haqiqa ya kewaye ga dukan kome da sani.” (Suratux Xalaq: 12).
Da faxinsa, “Lalle Allah shi ne mai arzutawa, mai ikon yi, mai cikakken qarfi. (Suratuz Zariyat:
58).
Tabbatar da Ji da Gani ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah, “Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba, kuma shi ne mai ji, mai
gani.” (Suratush Shura: 11). Da faxinsa, “Lalle ne, Allah madalla da abinda yake yi muku wa’azi
da shi. Lalle ne Allah ya kasance mai ji ne, mai gani.” (Suratun Nisa: 58).
Tabbatar da So da Nufi ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah, “Kuma don me, a lokacin da ka shiga gonarka, ka ce: Abinda Allah
ya so (shi ke tabbata) babu wani qarfi face gami da Allah.” (Suratul Kahaf: 39). Da faxinsa,
“Kuma da Allah ya so, da ba za su yaqi juna ba, kuma amma Allah yana aikata abinda yake
nufi.” (Suratul Baqara: 253).
Da faxinsa, “An halatta muku dabbobin jin daxi, face abinda ake karantawa a kanku, ba
kuna masu halattar da farauta ba alhali kuwa kuna masu harama. Lalle ne, Allah yana hukunta
abinda yake nufi.” (Suratul Ma’ida: 1). Da faxinsa, “Domin haka wanda Allah ya yi nufin ya
shiryar da shi sai ya buxa qirjinsa domin Musulunci, kuma wanda ya yi nufin ya vatar da shi, sai
ya sanya qirjinsa mai qunci matsattse, kamar dai yana takawa1 ne cikin sama.” (Suratul An’am:
125).
1 Mai takawa zuwa sama kirjinsa kunci yake yi, saboda iskar numfashi tana raguwa gare shi, kamar yadda ilmin
Kimiyya ya tabbatar.
7
Tabbatar da Soyayyar Allah da Qaunarsa
ga Muminai masu Taqawa Gwargwadon
yadda ya Dace da Girmansa
A cikin faxin Allah, “Kuma ku kyautata; lalle ne, Allah yana son masu kyautatawa.”
(Suratul Baqara: 195). “Kuma ku daidaita.1 Lalle Allah na son masu daidaitawa.” (Suratul
Hujurat: 9). “To, matuqar sun tsaya sosai gare ku, sai ku tsayu sosai gare su. Lalle ne Allah yana
son masu taqawa.” (Suratut Tauba: 7). “Lalle ne, Allah yana son masu tuba, kuma yana son
masu tsarkakewa.” (Suratul Baqara: 222).
Da faxinsa, “Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to, ku bi ni, Allah ya so ku.”
(Suratu Aali Imrana: 31). Da faxinsa, “Lalle Allah yana son waxanda ke yin yaqi domin
xaukaka kalmarsa, a cikin safu kamar su gini ne mai xamfarar juna.” (Suratus Saff: 4). Da
faxinsa, “Kuma shi ne mai gafara, mai bayyana soyayya.” (Suratul Buruj: 14).
Tabbatar da sifantuwarsa, Maxaukaki,
da Rahama da Gafara
A cikin faxin Allah, “Da sunan Allah, mai rahama, mai jin qai.” (Suratul Fatiha: 1). Da
faxinsa, “Ya Ubangijinmu! Ka yalwaci dukan kome da rahama da ilmi.” (Suratu Gafir: 7). Da
faxinsa, “Kuma (Allah) ya kasance mai jin qai ga muminai.” (Suratul Ahzab: 43). Da faxinsa,
“Kuma rahamata, ta yalwaci dukan kome.” (Suratul A’araf: 156). Da faxinsa, “Ubangijinku ya
wajabta rahama ga kansa.” (Suratul An’am: 54). Da faxinsa, “Kuma shi ne mai gafara, mai jin
qai.” (Suratu Yunus: 107 da Suratul Ahqaf: 8). Da faxinsa, “Sai dai Allah ne mafificin masu
tsari, kuma shi ne mafi rahamar masu rahama.” (Suratu Yusuf: 64).
Bayanin Yardar Allah da Fushinsa da Qiyayyarsa
da cewa Shi mai Sifantuwa ne da haka
A cikin faxin Allah Maxaukaki, “Allah ya yarda da su, kuma sun yarda da shi.” (Suratul
Ma’ida: 119 da Suratut Tauba: 100 da Suratul Mujadala: 22 da Suratul Bayyina: 8). Da faxinsa,
“Kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci, to, sakamakonsa Jahannama, yana
madauwami a cikinta, kuma Allah ya yi fushi a kansa, kuma ya la’ane shi.” (Suratun Nisa: 93).
Da faxinsa, “Wannan domin, lalle su, sun bi abinda ya fusatar da Allah, kuma sun qi yardarsa.”
1 Daidaitawa a nan yana nufin sulhuntawa tsakanin masu sabani.
8
(Suratu Muhammad: 28). “Saboda haka a lokacin da suka husatar da mu, muka yi musu azabar
ramuwa.” (Suratuz Zukhruf: 55).
Da faxinsa, “Kuma amma Allah ya qi zaburarsu, sai ya nauyayar da zamansu.” (Suratut
Tauba: 46). Da faxinsa, “Ya girmama ga zama abin qyama a wurin Allah, ku faxi abinda ba ku
aikatawa.” (Suratus Saff: 3).
Bayanin Zuwan Allah domin
Rabe Hukunci tsakanin Bayinsa,
Gwargwadon yadda ya dace da Girmansa
A cikin faxin Allah, “Shin, suna jiran, face dai Allah ya je musu a cikin wasu inuwoyi na
girgije, da mala’iku, kuma an hukunta al’amarin?.” (Suratul Baqara: 210). Da faxinsa, “Shin,
suna jiran (wani abu), face dai mala’iku su je musu, ko kuwa Ubangijinka ya je, ko kuwa sashen
ayoyin Ubangijinka ya je.” (Suratul An’am: 158). Da faxinsa, “A’aha! Idan aka niqa qasa
niqewa sosai, kuma Ubangijinka ya zo, alhali mala’iku na jere, safu-safu.” (Suratul Fajr: 21-22).
Da faxinsa, “Kuma a ranar da sama take tsatssagewa tare da gizagizai, kuma a saukar da
mala’iku, saukarwa.” (Suratul Furqan: 25).
Tabbatar da Fuska ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah, “Kuma fuskar Ubangijinka, mai girman jalala da karimci, shi ne
yake wanzuwa.” (Suratur Rahman: 27). “Ko wane abu mai halaka ne face fuskarsa.” (Suratul
Qasas: 88).
Tabbatar da Hannaye Biyu ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah mai girma da xaukaka, “(Allah) ya ce: Ya Iblis! Me ya hana ka, ka yi
sujada ga abinda na halitta da hannayena biyu?” (Suratu S.: 75). “Kuma Yahudu suka ce:
Hannun Allah abin yi wa ququmi ne. An sanya hannuwansu a cikin ququmi! Kuma an la’ane su
saboda abinda suka faxa. A’a, hannuwansa biyu shimfixaxxu ne, yana ciyarwa yadda yake so.”
(Suratul Ma’ida: 64).
9
Tabbatar da Idanu Biyu Ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah, “Sai ka yi haquri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kana
idanunmu.” (Suratux Xur: 48). “Kuma muka xauke Nuhu a kan (jirgi) na alluna da qusoshi.
Tana gudana, a cikin kiyayewarmu, domin sakamako ga wanda aka yi wa kafirci.” (Suratul
Qamar: 13-14). “Kuma na jefa wani so daga gare ni a kanka. Kuma domin a riqe ka da kyau a
kan ganina.” (Suratu X.H.: 39).
Tabbatar da Ji da Gani ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah, “Lalle Allah ya ji maganar wadda ke yi maka jayayya game da
mijinta, tana kai qara ga Allah, kuma Allah na jin muhawararku. Lalle Allah mai ji ne, mai
gani.” (Suratul Mujadala: 1). Da faxinsa, “Lalle ne, haqiqa, Allah ya ji maganar waxanda suka
ce: Lalle ne, Allah faqiri ne, mu ne wadatattu.” (Suratu Aali Imrana: 181). Da faxinsa, “Ko suna
zaton lalle mu, ba mu jin asirinsu da ganawarsu? Na’am! Kuma Manzanninmu na tare da su suna
rubutawa.” (Suratuz Zukhruf: 80). “Kada ku ji tsoro. Lalle ni, ina tare da ku, ina ji, kuma ina
gani.” (Suratu X.H.: 46). “Ashe, bai sani ba cewa Allah yana gani.” (Suratul Alaq: 14). “Wanda
yake ganin ka a lokacin da kake tashi tsaye. Da jujjuyawarka a cikin masu yin sujada. Lalle shi,
shi ne mai ji, Masani.” (Suratush Shu’ara: 218-220). “Kuma ka ce: Ku yi aiki, sa’an nan Allah
zai ga aikinku, da Manzonsa da Muminai.” (Suratut Tauba: 105).
Tabbatar da Hila da Kaidi ga Allah Maxaukaki
Gwargwadon yadda ya dace da shi
A cikin faxin Allah, “Kuma (Allah) shi ne mai tsananin hila.” (Suratur Ra’ad: 13). Da
faxinsa, “Kuma (kafirai) suka yi makirci, Allah kuma ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma
Allah ne mafi alherin masu saka wa makirci.” (Suratu Aali Imrana: 54). Da faxinsa, “Kuma suka
qullamakirci, kuma muka qulla sakamakon makirci, alhali su ba su sani ba.” (Suratun Namli:
50). Da faxinsa, “Lalle ne su, suna qulla kaidi na sosai, kuma ni, ina mayar da kaidi (gare su)
kamar yadda suke qulla kaidi.” (Suratux Xariq: 15-16).
Sifanta Allah da Rangwame da Gafara
da Rahama da Buwaya da Iko
A cikin faxin Allah, “Idan kun bayyana alheri, ko kuwa kuka voye shi, ko kuwa kuka
yafe laifi daga cuta, to, lalle ne Allah ya kasance mai yafewa, mai ikon yi.” (Suratun Nisa: 149).
“Kuma su yafe, kuma su kau da kai. Shin, ba ku son Allah ya gafarta muku, alhali Allah mai
10
gafara ne, mai jin qai.” (Suratun Nur: 22). Da faxinsa, “Alhali kuwa rinjaye ga Allah yake kuma
da Manzonsa, kuma da muminai.” (Suratul Munafiqun: 8). Da faxinsa dangane da Iblis: “(Iblis)
ya ce: To, ina rantsuwa da buwayarka, lalle ina vatar da su gaba xaya.” (Suratu S.: 82).
Tabbatar da Suna ga Allah da Kore Kama da Shi
A cikin faxin Allah, “Sunan Ubangijinka, mai girman jalala da karimci, ya tsarkaka.”
(Suratur Rahman: 78). Da faxinsa, “Sai ka bauta masa, kuma ka yi haquri ga bautarsa. Shin ka
san wani takwara gare shi?” (Suratu Maryam: 65). “Kuma babu xaya da ya kasance tamka gare
shi.” (Suratul Ikhlas: 4). Da faxinsa, “Saboda haka kada ku sanya wa Allah wasu kishiyoyi,
alhali kuwa kuna sani.” (Suratul Baqara: 22). “Kuma akwai daga mutane wanda yake riqon
kinaye, baicin Allah, suna son su, kamar son Allah.” (Suratul Baqara: 165).
Kore Abokin Tarayya ga barin Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah, “Kuma ka ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda bai riqi xa ba, kuma
abokin tarayya bai kasance a gare shi ba a cikin mulkinsa, kuma wani masoyi saboda wulakanci
bai kasance a gare shi ba. Kuma ka girmama shi, girmamawa.” (Suratul Isra: 111). “Abinda yake
a cikin sammai da wanda yake a cikin qasa suna tasbihi ga Allah. Gare shi mulki yake, kuma
gare shi godiya take. Kuma shi, a kan kome, mai ikon yi ne.” (Suratut Tagabun: 1).
Da faxinsa, “Albarka ta tabbata ga wanda ya saukar da (Littafi) mai rarrabewa a kan
Bawansa, domin ya kasance mai gargaxi ga halitta.” (Suratul Furqan: 1). “Wanda yake da
mulkin sammai da qasa, kuma bai riqi abin haihuwa ba, kuma abokin tarayya bai kasance a gare
shi ba a cikin mulkinsa, kuma ya halitta dukan kowane abu, sa’an nan ya qaddara shi
qaddarawa.” (Suratul Furqan: 2).
Da faxinsa, “Allah bai riqi wani abin haihuwa ba, kuma babu wani abin bautawa tare da
shi. Idan haka ne, (akwai abin bautawa tare da shi), lalle ne, da kowane abin bautawar ya tafi da
abinda ya halitta, kuma lalle ne, da waxansu sun rinjaya a kan waxansu. Tsarki ya tabbata ga
Allah, daga abinda suke siffantawa. Masanin voye da bayyane. Sa’an nan ya xaukaka daga barin
abinda suke yi na shirka.” (Suratul Muminun: 91-92).
Da faxinsa, “Sa’an nan kada ku bayar da waxansu misalai ga Allah. Lalle ne Allah yana
sani, kuma ku, ba ku sani ba.” (Suratun Nahal: 74). Da faxinsa, “Ka ce: Abin sani kawai,
Ubangijina ya hana abubuwan alfasha: abinda ya bayyana daga gare su da abinda ya voyu, da
zunubi da rarraba jama’a, ba da wani hakki ba, kuma da ku yi shirki da Allah ga abinda bai
saukar da wani dalili ba gare shi, kuma da ku faxi abinda ba ku sani ba, ga Allah.” (Suratul
A’araf: 33).
11
Tabbatar da Daidaitar Allah a kan Al’arshinsa
A cikin faxin Allah Maxaukaki, “Mai rahama, ya daidaita a kan Al’arshi.” (Suratu X.H.:
5) a wurare bakwai a cikin Alqur’ani. A cikin Suratul A’arafi ya ce, “Lalle ne Ubangijinku Allah
ne, wanda ya halitta sammai da qasa a cikin kwanaki shida, sa’an nan kuma ya daidaita a kan
Al’arshi.” (Suratul A’arafi: 54). Kuma ya ce a cikin Suratu Yunus (AS): “Lalle Allah ne
Ubangijinku wanda ya halicci sammai da qasa a cikin kwana shida, sa’an nan kuma ya daidaita a
kan Al’arshi.” (Suratu Yunus: 3).
A cikin Suratur Ra’ad kuma ya ce, “Allah shi ne wanda ya xaukaka sammai, ba da
ginshiqai ba waxanda kuke ganin su. Sa’an nan ya daidaita a kan Al’arshi.” (Suratur Ra’ad: 2).
Kuma a cikin Suratu X.H. ya ce, “Mai rahama ya daidaita a kan Al’arshi.” (Suratu X.H.: 5).
Haka nan a cikin Suratul Furqan ya ce, “Sa’an nan ya daidaita a kan Al’arshi, mai rahama.”
(Suratul Furqan: 59). Kuma a cikin Suratus Sajada ya ce, “Allah ne wanda ya halitta sammai da
qasa da abinda yake a tsakaninsu a cikin kwanuka shida, sa’n nan ya daidaita a kan Al’arshi.”
(Suratus Sajada: 4). Kuma ya ce a cikin Suratul Hadid: “Shi ne wanda ya halitta sammai da qasa
a cikin wasu kwanuka shida, sa’an nan ya daidaita a kan Al’arshi.” (Suratul Hadid: 4).
Tabbatar da Xaukakar Allah a bisa Halittunsa
A cikin faxin Allah, “A lokacin da Ubangiji ya ce: Ya Isa! Lalle ni mai karvar ranka ne,
kuma mai xaukake ka ne zuwa gare ni.” (Suratu Aali Imrana: 55). Da faxinsa, “Allah ya
xaukake shi zuwa gare shi.” (Suratun Nisa: 158). “Zuwa gare shi magana mai daxi ke hawa,
kuma aiki na qwarai yana xaukar sa.” (Suratu Faxir: 10).
Da faxinsa, “Kuma Fir’auna ya ce: Ya Hamana! Ka gina mini bene, xammanina za ni isa
ga qofofi. Qofofin sammai, domin in yi ninqaya zuwa ga abin bautawar Musa. Kuma lalle ni,
haqiqa, ina zaton sa maqaryaci.” (Suratu Gafir: 36-37). Da faxinsa, “Shin ko kun amince cewa
wanda ke cikin sama, ba zai iya shafe qasa tare da ku ba, sai ga ta tana mai girgiza? Ko kun
amince cewa wanda ke cikin sama ba zai iya sako muku iskar guguwa ba? To, za ku san yadda
(aqibar) gargaxina take.” (Suratul Mulk: 16-17).
Tabbatar da Kasancewar Allah Tare da Halittarsu
A cikin faxin Allah Maxaukaki, “Shi ne wanda ya halitta sammai da qasa a cikin wasu
kwanuka shida, sa’an nan ya daidaitu a kan Al’arshi, yana sanin abinda ke shiga cikin qasa da
abinda ke fita daga gare ta, da abinda ke sauka daga sama da abinda ke hawa cikinta, kuma shi
12
yana tare da ku, duk inda kuka kasance. Kuma Allah mai gani ne ga abinda kuke aikatawa.”
(Suratul Hadid: 4).
Da faxinsa, “Wata ganawa ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah shi ne na huxu
xinta, kuma babu ta mutum biyar face shi ne na shida xinta, kuma babu abinda ya kasa wannan
kuma babu abinda yake mafi yawa face shi yana tare da su duk inda suka kasance, sa’an nan ya
ba su labari game da abinda suka aikata a Ranar Qiyama. Lalle Allah masani ne ga dukan kome.”
(Suratul Mujadala: 7).
Da faxinsa, “Kada ka yi baqin ciki, lalle ne Allah yana tare da mu.” (Suratut Tauba: 40).
Da faxinsa, “(Allah) ya ce: Kada ku ji tsoro. Lalle ni, ina tare da ku, ina ji, kuma ina gani.”
(Suratu X.H.: 46). Da faxinsa, “Lalle Allah yana tare da waxanda suka yi taqawa da waxanda
suke su masu kyautatawa ne.” (Suratun Nahal: 128). Da faxinsa, “Kuma ku yi haquri. Lalle ne
Allah yana tare da masu haquri.” (Suratul Anfal: 46). Da faxinsa, “Da yawa qungiya kaxan ta
rinjayi wata qungiya mai yawa da izinin Allah, kuma Allah yana tare da masu haquri.” (Suratul
Baqara: 249).
Tabbatar da Magana ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah mai girma da xaukaka, “Kuma wane ne mafi gaskiya daga Allah ga
labari?” (Suratun Nisa: 87). Da faxinsa, “Wane ne mafi gaskiya daga Allah ga magana?”
(Suratun Nisa: 122). Da faxinsa, “Kuma lokacin da Allah ya ce: Ya Isa xan Maryama!” (Suratul
Ma’iada: 116). Da faxinsa, “Kuma kalmar Ubangijinka ta cika, tana gaskiya da adalci.” (Suratul
An’am: 115).
Da faxinsa, “Kuma Allah ya yi magana da Musa, magana sosai.” (Suratun Nisa: 164). Da
faxinsa, “Daga cikinsu akwai wanda Allah ya yi masa magana.” (Suratul Baqara: 253). Da
faxinsa, “Kuma a lokacin da Musa ya je ga miqatinmu, kuma Ubangijinsa ya yi masa magana.”
(Suratul A’araf: 143). Da faxinsa, “Kuma muka kira shi daga gefen dutse na dama, kuma muka
kusanta shi yana abokin ganawa.” (Suratu Maryam: 52). Da faxinsa, “Kuma a lokacin da
Ubangijinka ya kirayi Musa: Ka je wa mutanen nan azzalumai.” (Suratush Shu’ara: 10).
Da faxinsa, “Kuma Ubangijinsu ya kira su: Shin, ban hana ku ba daga waccan itaciya?”
(Suratul A’araf: 22). Da faxinsa, “Kuma ranar da ya kira su, sa’an nan ya ce: Mene ne kuka
karva wa Manzanni?” (Suratul Qasas: 65). Da faxinsa, “Idan wani daga mushirikai ya nemi
maqwabtakarka, to, ka ba shi maqwabtakar har ya ji maganar Allah.” (Suratut Tauba: 6). Da
faxinsa, “Alhali kuwa, haqiqa, wata qungiya daga gare su sun kasance suna jin maganar Allah,
sa’an nan kuma su karkatar da ita daga bayan sun gane ta, alhali su, suna sane.” (Suratul Baqara:
75). Da faxinsa, “Suna son su musanya maganar Allah ne. Ka ce: Ba za ku bi mu ba. Kamar
wannan ne Allah ya ce, a gabanin haka.” (Suratul Fathi: 15).
13
Da faxinsa Maxaukaki, “Ka karanta abinda aka yi wahayi zuwa gare ka, na littafin
Ubangijinka. Babu mai musanyawa ga kalmominsa.” (Suratul Kahaf: 27). Da faxinsa, “Lalle ne
wannan Alqur’ani yana gaya wa Bani Isra’ila mafi yawan abinda su suke sava wa junansu a
ciki.” (Suratun Namli: 76).
Tabbatar da Saukar da Alqur’ani
daga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Allah mai girma da xaukaka, “Kuma wannan Littafi ne, mun saukar da shi,
mai albarka ne.” (Suratul An’am: 92 da 155). Da faxinsa, Da mun saukar da wannan Alqur’ani a
kan dutse, da lalle ka ga dutsen yana mai tawali’u, mai tsattsagewa saboda tsoron Allah.”
(Suratul Hashri: 21).
Da faxinsa, “Kuma idan muka musanya wata aya a matsayin wata aya, kuma Allah ne
mafi sani ga abinda yake saukarwa, sai su ce: Abin sani kawai, kai maqirqiri ne. A’a, mafi
yawansu ba sa sani. Ka ce: Ruhul Qudusi ne ya saukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya,
domin ya tabbatar da waxanda suka yi imani, kuma (domin) shiriya da bushara ga Musulmi.
Kuma lalle ne, haqiqa, muna sanin (cewa) lalle ne su, suna cewa: Abin sani kawai, wani mutum
ne yake karantar da shi. Harshen wanda suke karkatar da maganar zuwa gare shi, Ba’ajame ne,
kuma wannan (Alqur’ani) harshe ne Balarabe bayyananne.” (Suratun Nahali: 101-103).
Tabbatar da Ganin Muminai
ga Ubangijinsu Ranar Alqiyama
A cikin faxin Allah Maxaukaki, “Wasu fuskoki, a ranar nan, masu annuri ne. Zuwa ga
Ubangijinsu masu kallo ne.” (Suratul Qiyama: 22-23). “A kan Karagu, suna ta kallo.” (Suratul
Muxaffifin: 23). Da faxinsa, “Waxanda suka kyautata yi, suna da abu mai kyawu1 kuma da
qari.” (Suratu Yunus: 26). Da faxinsa, “Suna da abinda suke so a cikinta, kuma tare da mu akwai
qarin2 ni’ima.” (Suratu Q.: 35).
Irin bayanan da muka gabatar a sama suna da yawa a cikin Alqur’ani. Wanda ya yi
darasun Alqur’ani, tare da tunani, yana mai neman shiriya daga gare shi, tafarkin gaskiya zai
bayyana gare shi.
1 Hadisi ya fassara abu mai kyau da Aljanna, kari kuma shi ne ganin Ubangiji a cikin Aljannar.
2 Karin ni’ima shi ne ganin Ubangiji a cikin Aljanna.
14
Babi Na Biyu
Sunayen Allah da Sifofinsa a cikin
Hadisan Annabi (SAW)
Sa’an nan kuma sai Sunnar Manzon Allah (SAW), domin ita Sunna tana fassara
Alqur’ani kuma tana bayyana shi, kamar yadda take fayyace shi, tana shiryarwa zuwa gare shi.
Dukan sifofin da Manzo (SAW) ya sifanta Ubangijinsa, mai girma da xaukaka, da su a
cikin hadisai ingantattu waxanda masana suka yi na’am da su, ya wajaba a yi imani da su, kamar
Alqur’ani ba bambanci.
Daga cikinsu akwai:
Tabbatar Saukar Ubangiji zuwa Saman Duniya
Gwargwadon yadda ya Dace da Girmansa
A cikin faxin Manzon Allah (SAW), “Ubangijinmu yana sauka zuwa saman duniya a
kowane dare, a sulusin daren na qarshe. Sai ya ce: Wa zai roqe ni, in amsa masa? Wa zai
tambaye ni, in ba shi? Wa zai nemi gafarata, in gafarta masa?” (Bukhari da Muslim).
Tabbatar da cewa Allah yana Murna,
yana Dariya, yana Mamaki
A cikin faxin Manzon Allah (SAW), “Allah ya fi tsananin farin ciki da tuban bawansa
mumini mai tuba, daga xayanku da abin hawansa.”1 (Bukhari da Muslim). Da faxinsa, “Allah
yana dariya zuwa ga mutane biyu, waxanda xayansu yake kashe xaya, kuma duka su shiga
Aljanna.”2 (Bukhari da Muslim).
Da faxinsa, “Ubangijinmu yana mamaki da xebe qaunar bayinsa, alhali alherinsa yana
kusa. Yana duban ku, kuna cikin qunci, kuna xebe qauna, sai ya yi ta dariya, yana sane da cewa
buxinku yana kusa.” (Hadisi ne kyakkyawa).
1 Wannan dogon hadisi ne ya takaice shi. Hadisin yana buga misali da mutumin da abin hawansa dauke da
guzurinsa ya bata a daji. Ya fitar da rai da samunsa, kuma ya kusa mutuwa saboda kishirwa, sai ga abin hawan ya
gan shi. Allah ya fi murna da tuban bawansa daga murnar mai abin hawan nan da abin hawansa.
2 Dayan kafiri ne zai kashe Musulmi sai ya zama ya yi shahada. Sai daga baya shi kuma mai kisan ya musulunta, sai
shi ma ya shiga Aljanna.
15
Tabbatar da Qafa da Sawu
ga Allah Maxaukaki1
A cikin faxin Manzon Allah (SAW), “Jahannama ba za ta gushe ba, ana jefa (mutane) a
cikinta, tana cewa: Akwai qari? Har sai Ubangijin buwaya ya sanya qafarsa a cikinta (a wata
ruwayar, ya sanya sawunsa), sai sashenta ya motse zuwa sashe, sai ta ce: Ya isa! Ya isa!”
(Bukhari da Muslim).
Tabbatar da Kira da Sauti da Zance
ga Allah Maxaukaki
A cikin faxin Manzon Allah (SAW), “(Ubangiji) Maxaukaki yana cewa: Ya Adamu! Sai
y ace: Amsawarka! Amsawarka! Sai ya kira shi da sauti: Allah yana umarnin ka, ka fitar da wata
tawaga daga zuri’arka zuwa wuta.” (Bukhari da Muslim). Da faxinsa, :Babu xaya daga cikinku
face Ubangijinsa zai yi Magana das hi, babu mai tafinta tsakaninsu.”
Tabbatar da Xaukakar Allah
a bisa Halittarsa
da Daidaitarsa a bisa Al’arshinsa
A cikin faxin Manzon Allah (SAW) a cikin ruqiyya ga mara lafiya, “Ubangijinmu Allah
wanda yake cikin sama, sunanka ya tsarkaka. Umarninka yana cikin sama da qasa. Kamar yadda
rahamarka take cikin sama, ka sanya rahamarka cikin qasa. Ka gafarta mana kurakuranmu da
zunubanmu, kai ne Ubangijin muminai. Ka saukar da wata rahama daga rahamarka, da wata
waraka daga warakarka a kan wannan mara lafiya. Sai (mara lafiyar) ya warke.” (Hadisi ne
kyakkyawa. Abu Dawud da waninsa suka ruwaito shi).
Da faxin Manzo (SAW), “Ba za ku amince mini ba, alhali ni amintaccen wanda ke cikin
sama ne.” (Hadisi ne ingantacce). Da faxinsa, “Kuma Al’arshin yana kan ruwa, kuma Allah yana
kan Al’arshin, kuma yana sane da halin da kuke ciki.” (Hadisi ne kyakkyawa. Abu Dawud da
waninsa suka ruwaito shi). Da tambayarsa ga wata Baiwa, “Ina Allah yake? Ta ce: Cikin Sama.
Ya ce: Ni wane ne? Ta ce: Kai Manzon Allah ne. Sai ya ce (da ubangijin Baiwar): Enta ta; domin
hqiqa ita mumina ce.” (Muslim ya ruwaito shi).
1 Allah yana da kafa da sawu, saboda Annabi ya tabbatar da haka. Saboda haka, sai a yi imani da cewa yana da su.
Ba’a tawili ko a karkatar da ma’anarsu, amma kuma ba’a cewa takamaimai ga yadda suke. Sai dai ana imani cewa,
sun saba da na bayi; saboda Ubangiji halittu ba sa kama da shi.
16