Labarai

 





 





 





 





 





 





 





 





 








TA’ALIKIN BABBAN MALAMI SHEIKH


ABDUL’AZIZ BN ABDALLAH BN BAZ


AKAN LACCAR (FAHIMTAR ADDINI)





Godiya ta tabbata ga Allah Shi kadai, tsira da aminci su tabbata ga wanda babu wani Annabi a bayansa, da alayensa da sahabbansa, da wanda ya shiriya da shiriyarsa.


Bayan haka:


Hakika kunji wannan laccar mai tsada wacce ma’abocin falala babban malami: Saleh bn Fauzan yayita a take mai girma wanda ya cancanci kulawa, shine taken fahimtar Addini, da tafiya akan hanyar magabatan al’umma daga sahabbai da mabiyansu da kyautatawa, da karbar hakan daga ma’abota ilimi da imani daga Ahlus Sunnah wal jama’a.


Hakika ya kyautata kuma ya fa’idantar – Allah Ya ninka sakamakonsa – kuma ya bayyanar da abinda bayaninsa yake kamata a wannan bigiren, dukkan mumini namiji da dukkan mumina mace a cikin wannan duniyar suna cikin mafi tsananin bukatuwa zuwa fahimtar Addini da lura; har  ya san hukuncin Allah a cikin dukkan ayyukan mukallafai, kuma har yayi tafiya akan basira, babu wata hanya zuwa ga hakan sai da fahimtar Addini: Da kulawa da Littafin Allah, da sunnar ManzonSa – tsira da aminci su tabbata agare shi -, kamar yanda wadanda ke gabanmu daga sahabbai da wadanda ke bayansu suka fahimta.


Hanyar azirta da hanyar tsira: Shine hanyar da muminan da suka gabata daga sahabban Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - da mabiyansu da kyautatawa suka shigeta, kamar yanda Allah – Madaukaki – Ya ce: {Kuma lallai wannan ne tafarkina mikakke sai kubi shi, kada kubi wasu hanyoyi daban sais u rabaku daga hanyarSa, wannan ne abinda (Allah) Yake yi muku wasiyya da shi, tsammaninku kuna yin takawa} , to hanyar Allah: Shine ilimi da aiki, shine sanin Littafin Allah da sunnar Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da aiki da su, wannan shine ilimi, kuma wannan shine hanya, wannan shine shiriya, wannan shine Musulunci, wannan shine aikin alheri, wannna shine takawa, saboda haka ne tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka Ya ce a cikin Surat al-Fatiha: {Ka shiryar damu hanya madaidaiciya} , Ubangijinmu Ya sanar da mu mu nemi wannan al’amarin, mu nemi shiriya zuwa hanya madaidaiciya daga gareShi, kuma hanyarSa madaidaiciya: Shine sanin abinda ManzonSa yazo da shi, da kuma aiki da hakan. {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Kayi ni’ima a kansu}, Ya fassara shi da fadinSa: {Hanyar wadanda Kayi ni’ima a kansu}, sune: Ma’abota sanin abinda Allah da ManzonSa suka fadeshi, kuma ma’abota aiki da hakan, sune sahabbai: Sahabban Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sannan wadanda ke bayansu daga masu binsu da kyautatawa, a kan shugabancinsu zamaninnika uku: Zamanin sahabbai, sannan zamanin tabi’ai, sannan masu bin tabi’ai; saboda fadinsa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: “Mafi alherin mutane zamanina, sannan wadanda suke binsu, sannan wadanda suke binsu” karanta hadisin.


Babu wata hanya zuwa sanin wannan al’amarin sai da fahimtar Addini, da kulawa da al-Qur’ani mai girma da sunnah abar tsarkakewa, da karbar hakan daga ma’abota ilimi wadanda suka bi Littafi da sunna suka girmamasu, kuma sukayi tafiya a kansu.


Ilimi (shine): Allah – Mai girma da daukaka – Ya ce, kuma ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya ce, kuma sahabbai sunce, ilimi bai zama: Ra’ayin wane da ra’ayin wane ba, kuma babu makawa daga karbar ilimi daga Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da kuma madauka wannan ilimin sune Ahlus Sunnah wal jama’a, masu tafiya akan hanyar sahabbai da masu binsu da kyautatawa.


Saboda haka ne Madaukakin sarki Ya ce: {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Kayi ni’ima a kansu} , sannan ya bayyana  wasu batattun hanyoyin da kiyayesu yake wajaba, sai ya ce: {Ba wadanda akayi fushi a kansu ba ba kuma batattu ba}, wadanda akayi fushi a kansu: Sune wadanda suka san gaskiya amma suka baude daga gareta; kamar Yahudawa da masu kama da su, batattu kuma: Sune wadanda sukayi tafiya akan jahilci da bata ba tare da ilimi ba; kamar Nasara da wasunsu, wadanda kuma akayiwa ni’ima da muminai na gaskiya, Ahlus Sunnah wal jama’a, kuma kungiyar da ta tsira: Sune wadanda suka san gaskiya kuma sukayi aiki da ita; da dalilanta na shari’a daga Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da aminci su tabbata agare shi -, wadannan sune Ahlus Sunnah wal jama’a, kuma sune ma’abota hanya madaidaiciya, sune wadanda akayi ni’ima agaresu, sune jama’a ababen taimako har zuwa ranar alkiyama, sune abin nufi a cikin fadinSa: {Wanda yabi Allah da Manzo to wadannan suna tare da wadanda Allah Yayi ni’ima garesu sune Annabawa da siddikai da shahidai da salihai kuma madalla da wadan nan abokai} , kuma abin nufi a cikin fadinSa – Madaukaki -: {Lallai mutanen kirki suna cikin ni’ima} , kuma sune abin nufi a cikin fadinSa – Madaukakin sarki -: {Bawai aikin da’a shine ku juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma aikin da’a shine ga wanda yayi imani da Allah da ranar lahira da mala’iku da littattafa da Annabawa, kuma ya bayar da dukiya akan yana sonta, ga dangi da marayu da matalauta da dan hanya da masu rook (bias larura), da ‘yantar da bayi, kuma ya tsayar da sallah, ya bayar da zakka, da masu cika alkawarinsu idan sun kulla alkawarin, da masu hakuri a cikin tsanani da cuta da lokacin yaki, wadannan sune sukayi gaskiya, kuma wadannan sune masu takawa} .


Wajibi akan dukkannin musulmai – maza da mata - shine tafiya akan wannan hanyar, da fahimtar Addini a cikin Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, daga hanyar malaman gaskiya, misalin abinda Malik dan Anas – Allah Yayi masa rahama – limamin gidan hijira a zamaninsa ya fadi wata kalmar da ya fadeta kunjita, kuma ma’abota ilimi suka bishi, sai ma’abota ilimi suka fadeta a bayansa itace: (Babu abinda zai gyara karshen wannan al’ummar sai abinda ya gyara na farkonta), abinda ya gyara na farkonta: Shine rikonsu da Littafin Allah, da sunnar Manzon Allah – tsira da aminci su tabbata agare shi -, da kuma tafiyarsu akan haka, da wasicci da hakan, da taimakekeniya a cikin hakan, wannan shine abinda sukayi tafiya a kansa, kuma shine  abinda Allah Ya gyarasu da shi, kuma babu abinda zai gyara na karshensu sai hakan.


A cikin hadisin Huzaifa – Allah Ya yarda da shi – wanda mai lacca sheikh Saleh yayi nuni zuwa gareshi ya tambayi Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – game da shi, Allah Ya yarda da shi  ya ce: Mutane sun kasance suna tambayarsa game da alheri, ni kuma na kasance ina tambayarsa game da sharri; dan tsoron kar ya riskeni, na ce: Ya Manzon Allah, mu mun kasance a cikin Jahiliyya da sharri, sai Allah Yazo mana da wannan alherin, shin a bayan wannan alherin akwai wani sharrin? Ya ce: “Eh” sai na ce: Shin kuma a bayan wannan sharrin akwai wani alherin? Ya ce: “Eh, kuma a cikinsa akwai kura” na ce: Menene kurar? Ya ce: “Wasu mutanene da suke sunnantuwa ba tare da sunnata ba, kuma suke shiriya ba tare da shiriyata ba zaka sani daga garesu kuma zakayi inkari”, zaka san wasu abubuwa kuma zakayi inkarin wasu abubuwa, sai na ce: Shin bayan wannan sharrin akwai wani alheri? Ya ce: “Eh, wasu masu kira ne akan kofofin Jahannama, wanda ya amsa musu zasu jefashi a cikinta”, na ce: Ya Manzon Allah, ka siffanta mana su, ya ce: “Wasu mutanene daga mu suke, kuma suna magana da yarukanmu”, sune masu kira akan kofofin jahannama, yaruka na larabci, kuma wasu daban suna fassarasu zuwa wasu yarukan daban, na ce: Ya Manzon Allah, me zaka umarceni idan hakan ya riskeni? Ya ce: “Ka lazimci jama’ar musulmai da shugabansu”, jama’ar musulmai: Wadanda sukayi tafiya akan hanyar sahabbai, sune wadanda (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya siffanta su da abinda ya gabata, ya ce: Nace: Idan basu da jama’ar kuma babu shugaba fa? Ya ce: “Ka nisanci wadancan kungiyoyin gaba dayansu, koda zakayi cizo akan tushen bishiya har mutuwa ta riskeka alhali kai kana akan haka” Bukahri da Muslim ne suka ruwaito shi a cikin ingantattun litatttafai biyu. Kuma Amr dan Maimun – babban tabi’i - ya tambayi Abdullahi dan Mas’ud – Allah Ya yarda da shi – game da jama’a, sai Abdullahi ya ce masa: (Jama’a: Abinda ya dace da gaskiya, koda kai kadai ne), idan ka dace da gaskiya koda kai kadaine to kaine jama’a, jama’a: Abinda ya dace da gaskiya koda kai kadai ne, jama’a: Sune masu riko da Littafin Allah da sunnar ManzonSa, kuma suna tafiya akan hanyar magabata na gari; daga sahabban Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da mabiyansu da kyautatwa, sune kungiya abar taimako, kuma sune kungiyar data tsira wacce Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya ce a cikin sha’aninta: “Al’ummata zata rabu kungiya saba’in da uku dukkansu ‘yan wuta ne sai daya” akace: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: “Abinda nake a kansa da sahabbaina”, a cikin wata riwayar daban ya ce: “Sune jama’a”, itace jama’a, kungiyar da ta tsira; domin cewa itace wacce ta hadu akan gaskiya kuma tayi tafiya a kanta, tun daga zamaninsa - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da kuma bayansa, wadannan sune kungiyar da ta tsira, kuma abin nufi a cikin fadinsa – Mai girma da daukaka -: {W annan shine tafarkina mikakke to sai kubishi, kuma kada kubi wasu hanyoyi daban sai su rabaku da hanyarSa} , kuma yazo a cikin hadisi ingantacce daga Ibnu Mas’ud – Allah Ya yarda da shi – ya ce: Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya zana mana wani zane madaidaici, kuma ya ce: “Wannan shine tafarkin Allah”, sannan ya zana wasu zane-zane daga damansa da kuma hagunsa ya ce: “Wadannnan hanyoyi ne, kuma akan kowace hanya daga cikinsu akwai Shaidanin da yake kira zuwa gareta” sannan ya karanta wannan ayar: {Wannan shine tafarkina mikakke to sai kubishi, kuma kada kubi wasu hanyoyi daban}. Kungiyar da ta tsira: Sune Ahlus Sunna wal jama’a, sune kungiya abar taimako, abu daya ne, mazansu da matansu, malumansu da gamagarinsu, sune kungiyar da ta tsira, masu tafiya akan Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; daga aljanu da mutane, daga larabawa da baubayi, daga maza da mata daga dukkanin matakai, sune Ahlus Sunnah wal jama’a, sune kungiyar da ta tsira koda sun banbanta a ilimi da falala, fadin wasu daga magabata: (Sune ma’abota hadisi), da fadin waninsu: (Idan basu zama ma’abota hadisi ba to bansan suwaye su ba?!), da fadin wani daga magabata: (Sune malamai), bawai cewa su wata kungiya daban bace. Malamai sune shugabanninsu, ma’abota hadisi sune shugabanninsu, kuma limamansu, shugabanninsu: Sahabbai. Sahabban Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – sune shugabanni, sannan ma’abota hadisi suna biye musu, fakihan al’umma da malumansu sune shugabanni, sune ababen koyi, sune suke bayyanar da hanya ga mutane. Da fadin sashinsu: (Sune ma’abota hadisi), da fadinsu: (Sune malamai) ma’anarsa bai zama: Sune wata kungiyar daban ba. Sune ma’abota hadisi, kuma sune malamai, kuma sune masu riko da Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da wanda yayi tafiya akan hanyarsu, da wanda ya bisu kuma yayi tafiya akan hanyarsu. Sune kungiyar da ta tsira, sai dai mafi kebantarsu kuma mafificinsu kuma shugabanninsu: Sune limaman hadisi, wadanda suka sanar da mutane alheri, kuma suka shiryar da su gareshi, kuma sukayi musu nuni zuwa gareshi, sahabban Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da mabiyansu daga magabata, sune malamai: Malaman gaskiya wadanda suka san gaskiya kuma sukayi aiki da ita kuma sukayi kira zuwa gareta, sune jagororin kungiyar, sune shugabanninta, sune jagororinta, kuma mabiyansu gamegari suna shiga cikinsu masu binsu ne, daga matansu, da iyayensu, da ‘ya’yansu, da ‘yan uwansu, da ragowar mata ma’abota hanyarsu daga musulmai, koda sun kasance gamagari ne, koda sun kasance ba malamai bane, to sun shiga cikin wannan kungiyar idan sunyi tafiya akan hanyarsu, kuma sun bisu da gaskiya, sun tsaya akan Addinin Allah, amma masu sabawa to su wasu kungiyoyi ne wadanda bazasu kirgu ba, su saba’in da biyu ne, dukkansu zasu koma zuwa kungiya saba’in da biyu tsakanin kafirai da ‘yan bidi’a da batattu, rabe-rabe ne: A cikinsu akwai kafirai, a cikinsu akwai wadanda ba kafiari ba, sai dai cewa su anyi musu alkawari da wuta; saboda cewa su sun baude daga hanya madaidaiciya; domin cewa su sun sabawa gaskiya a cikin abubuwa, daga cikinsu akwai wanda ya fita daga Musulunci, daga cikinsu akwai wanda bai fita ba, sai dai saboda bidi’arsa ya zama akan hadari babba, ko saboda sabonsa ya zama akan hadari babba, hakika tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: “Wanda Yake nufinsa da alheri zai fahimtar da shi Addini” An hadu a kan ingancinsa daga hadisin Mu’awiya – Allah Ya yarda da shi -, daga alamomin alheri kuma cewa Allah Yayi nufin alheri ga bawa, namijine ko mace, balarabene ko baubawa – daga cikin alamomin cewa Allah Yayi nufinsa da alheri: Ya fahimci Addini ta hanyar al-Qur’ani da sunnah, wannan fahimtar Addinin, da kuma ta hanyar ma’abota sanin Littafi da sunnah, ba ta hanyar ‘yan bidi’a da jahilai ba, ta hanyar ma’abota ilimi da Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da aminci su tabbata agare shi -, idan kaga namiji da mace – balarabe ko baubauwa – idan ka ganshi yana neman fahimyar Addini, yana tambaya game da abinda Allah da ManzonSa suka fada, kuma yana kwadayi akan wannan abun yana kokari, to kasan cewa Allah Yayi nufin alheri da shi, kuma daga alamomion alheri, idan kuwa ka ganshi yana mai bijirewa baya kwadayi a cikin Littafin Allah da sunnah, ba mai tafiya ba akan abinda Littafi da sunnah suka kunsheshi ba; to wannan nunine mai girma mabayyani akan cewa Allah baYa nufinsa da alheri. Muna rokon Allah lafiya.


Kuma Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana cewa: “Wanda ya shiga wata hanyar da yake neman wani ilimi a cikinta Allah Zai sawwake wata hanya da ita zuwa aljanna”, kuma yana cewa: “Malamai magada Annabawa ne, Annabawa basu gadar da zinare ko azirfa ba, kadai sun gadar da ilimi ne”, ilimi da Littafin Allah da sunnar ManzonSa, wanda ya rikeshi to yayi riko da rabo mai yawa.


To wajibi akan mai neman ilimi kuma akan kowane musulmi da kowace musulma neman fahimtar Addini, kuma yasan abinda baya yiwuwa ya jahilceshi, daga abinda Allah Ya wajabta a kansa da kuma abinda Ya haramta a kansa.


Allah – Mai girma da daukaka – Yana cewa: {Kuyi riko da igiyar Allah gaba daya kada ku rarraba} , yana nufin: Da Addinin Allah, kuma Madaukaki Yana cewa: {Abinda kukayi sabani a cikinsa daga wani abu to hukuncinsa yana ga Allah} , ba zuwa ga Zaid ko zuwa ga Amr ba {To hukuncinsa yana ga Allah} zuwa ga Littafi da sunnah, kamar yanda yake a cikin wata ayar daban {Idan kukayi jayayya a cikin wani abu to ku maida shi zuwa ga Allah da Manzo idan kun kasance kunyi imani da Allah da ranar lahira hakan shine mafi alheri kuma mafi kyan makoma} .


Yana wajaba komawa zuwa ga al-Qur’ani, zuwa abinda ke cikinsa daga ayoyi masu girma, kamar yanda Allah Ya bayyanashi a cikinsu, kuma a cikinsa akwai shiriya da haske, kuma a cikinsa a kwai nuni akan kowane alheri, kamar yanda tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Lallai wannan al-Qur’anin yana shiryarwa ga (hanya) mafi mikewa} , {Kace shi shiriya ne da waraka ga wadanda sukayi imani} , {Wannan Littafine Mun saukar da shi mai albarkane to sai ku bishi kuma kukiyaye dokokin Allah} , Yasa a koma zuwa gareshi; domin cewa shi  bayyananne ne, da badan cewa a cikinsa akwai ilimi da  shiriya ba da (Allah) tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – bai sa a koma zuwa gareshi ba, a cikinsa akwai shiriya da haske, Madaukakin sarki Ya ce: {Wannan Littafine Mun saukar da shi mai albarkane to sai ku bishi kuma kuyi takawa watakila za’aji kanku}, kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Lallai wannan al-Qur’anin yana shiryarwa ga (hanya) mafi mikewa} ga hanyar da itace mafi daidaituwar hanyoyi kuma mafi shiriyarsu, kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Littafine Mun saukar da shi mai albarka dan suyi tuntuntuni game da ayoyinsa} , musifa itace bijirewa da rafkana da rashin jujjuyawa, inba haka ba fa to a cikin al-Qur’ani a kwai shiriya da haske, a cikin sunnah kuma akwai bayyanar da abinda ya rikitar, sunnah ingantacciya daga Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – akwai bayyanar da abinda ya rikitar, da bayanin abinda zai iya boyuwa, kamar yanda Mai girma da daukaka Ya ce: {Mun saukar maka da Alkur’ani dan ka bayyanawa mutane abinda aka saukar musu} , kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Idan kukaga wadanda suke bin abinda ya rikitar daga gareshi to wadanannan sune wadanda Allah Ya ambata to kukiyaye su”.


Daga alamomin ma’abota alheri da ma’abota gaskiya, bibiyar al-Qur’ani da sunnah, da shiryuwa da al-Qur’ani da sunnah, da kuma yin riko da umarni bayyananne, da yin riko da hakan da kuma tafiya a kansa, da tambayar ma’abota ilimi: Malamai ma’abota sunnah, (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa: “Lallai Allah baYa karbar ilimi karbewa da zai karbeshi daga mutane, sai dai yana karbar ilimi ne da karbar malamai, har idan bai bar wani malami ba sai mutane su riki jahilai shugabanni, sai a tambayesu, sai su bada fatawa ba tare da ilimi ba, sun bata kuma sun batar” , wannan ne karshe, muna rokon Allah lafiya, kamar yanda ya fada a cikin hadisin Huzaifa: Ya ce: “Idan basu da jama’a ko shugaba, to ka nisanci wadancan kungiyoyin gaba dayansu”.


Mai neman ilimi yana neman fahimtar Addini ta hanyar laittafi da sunnah, kuma yana tambayar ma’abota sanin Littafi da sunnah game da abinda ya rikice masa da gaskiya da kuma ikhlasi, da nufi na gari, da tsarkakkiyar niyya; har a shiriyar da shi, har a datar da shi, Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya ce: “Wanda Allah Yake nufinsa da alheri Zai fahimtar da shi Addini”. Wanda ya nemi gaskiya da niyya ta gari Allah Zai datar da shi, Madaukakin sarki Ya ce: {Wadanda sukayi jihadi saboda Mu Zamu shiryar da su hanyoyinMu, kuma lallai Allah Yana tare da masu kyautatawa} , sai dai wanda ya bijire, Allah Zai bijira daga gareshi, Madaukakin sarki Ya ce: {Lokacin da suka karkace sai Allah Ya karkatar da zukatansu} , kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma wanene mafi zalinci daga wanda aka tinatar game da ayoyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abinda hannayensa suka gabatar}  idan ya bijire kuma ya rafkana bai kula ba to yana daga adalcin Allah Ya batar da shi, kuma Ya jibintar masa da abinda ya jibinta; saboda zalincinsa da jahilcinsa da kuma bijirewarsa, amma wanda ya fuskanto ga Allah ya nemi shiriya daga gareShi kuma yayi gaskiya a cikin hakan to Allah Zai shiryar da shi kuma Zai datar da shi. Kayi kokari yakai bawan Allah a cikin kankar da kai gareShi da gaskiya sai Ya datar da kai dacewa, kuma Ya shiryar da kai hanyarSa madaidaiciya, kuma Ya sanar da kai abinda zai amfaneka, kuma Ya kareka sharrin kanka da son ranka, Madaukaki Ya ce: {Ku rokeNi in amsa muku} , kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya ce: {Idan bayiNa suka tambayeka game da Ni to Ni Makusanci ne, iNa amsa addu’ar mai kira idan yayi kira} , kuma a cikin ingantaccen hadisi tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi yana cewa: “Ba wani bawan da zai roki Allah addu’ar da babu zunubi ko yanke zumunci a cikinta sai Allah Ya bashi dayan abu uku: Kodai a gaggauto masa da addu’arsa a duniya, ko kuma ayi masa tanadinta a lahira, ko kuma a juyar masa da sharri kwatankwacin hakan”, a kace: Ya Manzon Allah, sai mu yawaita, ya ce: “Allah ne Mafi yawa”.


Ya kintaci lokutan da suka dace wadanda ake kwadayin amsa addu’a a cikinsu, kamar yanda kukaji a cikin laccar, kamar misalin karshen dare lokacin saukowar Allah, tsakiyar dare na karshe, da karshen sallah kafin sallama, Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana cewa a cikinsa: “Sannan ya zabi abinda yake kayatar da shi a cikin addu’a sai ya roka da shi”, a cikin karshen sallah, a cikin sujjada, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana cewa: “…Amma ruku’u to ku girmama Ubangiji a cikinsa, amma sujjada to kuyi kokari a cikin addu’a, ya cancanta a amsa muku”, yana nufin: Ya cancanta a amsa muku, Muslim ne ya ruwaito shi a cikin ingantaccen (littafinsa), kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana cewa: “Mafi kusancin abinda bawa yake kasancewa daga Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada, to ku yawaita addu’a” Muslim ne ya ruwaito shi kuma.


Ya kamata yin addu’a a cikin sujjada, musamman ma dai a cikin sallar dare, da kuma farilla, ka roki Ubangijinka a cikin farilla da nafila, a cikin sujjadarka, da karshen sallah, ka roki alherin duniya da lahira, kuma mafi muhimmancin abu a binda yake a cikinsa akwai gyaran zuciyarka, da kuma abinda yake a cikinsa akwai shiriyarka, da cikin sallar dare, da karshen dare, in dai zaiyiwu gareka to ka tsawaita sujjada inzai yiwu gareka to ka tsawaita addu’a. Haka nan a karshen yinin Juma’a bayan La’asar, haka nan lokacin huduba ranar Juma’a daga lokacin da liman ya zauna akan minbari har a gama sallah, dukkansu lokutan amsawa ne, tsakanin kiran sallah da iqama ma lokacin amsawa ne. Mumini yayi kintace sannan yayi kwadayi akan cin halal, abincin halal, tufafin halal, ya kintaci kasuwancin halal; domin cewa kasuwancin haram suna daga sabubban hana amsa addu’a, babu wata dabara babu wani karfi sai ga Allah. Ayyukan sabo suna daga sabubban hana amsawa. Bijirewa Allah da rafkana da rashin kulawa suna daga sabubban hana amsawa.


Mumini ya fuskanci Allah yana mai gaskiya mai ikhlasi, yana mai kwadayin gaskiya, Allah Yana sanin kwadayin gaskiya a cikin zuciyarsa da gaskiya a cikin neman gaskiya, kada ya yanke kauna, kai yayi naci a cikin addu’a yayi kokari a cikin addu’a a dukkananin lokuta, ya kintaci lokutan amsawa da gaskiya da kuma kwadayi, ya kiyayi sabubban haramtawa daga ayyukan sabo, da cin haram, da rafkana daga Allah, da yin addu’a da zuciya mai bijirewa rafkananniya, ya fuskanci Allah yana mai gaskiya yana mai kokari, yana mai neman gaskiya, kuma ya abokanci mutanen kirki, yayi abota da mutanen kirki kuma yayi kokari a cikin abokantakarsu, ya kasance tare da su, ya kiyayi abokantaka da mutanen banza, tir da abokan zama, yayi kwadayi akan abokantakar mutanen kirki, ma’abota ilimi da aiki, ma’abota tsoron Allah, ma’abota Addini, yayi kwadayi akan abokantakarsu, da cakuduwa da su, da fa’idantuwa daga garesu.


Muna rokon Allah Ya datar da kowa da kowa ga abinda Ya yarda da shi, kuma Ya azirta mu da ku ilimi mai anfani da aiki na gari da fahimtar Addini, kuma Ya tsaremu gaba daya da musulmai gaba daya daga sharrikan rayukanmu, da munanan ayyukanmu, da kuma fitintinu masu batarwa abinda ya bayyana daga garesu da kuma abinda ya boyu.


Kamar yanda ina rokonSa Ya datar da majibinta al’amuranmu ga dukkanin alheri, Ya taimakesu akan dukkanin alheri, Ya gyara zukatansu da ayyukansu da abokanan ayyukansu, kuma Ya datar da su ga dukkan abinda yake a cikinsa akwai gyaran bayi da garuruwa, kuma Ya taimakesu akan kawar da abinda ya sabawa shari’ar Allah a cikin kasar Allah, kuma Ya datar da jagororin musulmai a kowane guri.


Muna rokon Allah Ya datar da jagororin musulmai a kowane guri ga abinda Zai yardar maSa, kuma Ya taimakesu akan hukunci da shari’arSa da kai kara zuwa gareta, da tsayuwa a kanta, da tilasta talakawa da ita, kamar yanda nake rokonSa – tsarki ya tabbatar maSa – Ya gyara halayen munsulmai a kowane guri, kuma Yayi musu baiwar fahimtar Addini, kuma Ya taimakesu akan biyayyarSa da biyayyar ManzonSa – tsira da aminci su tabbata agare shi -, Ya tsaresu daga bin son rai da Shaidan, lallai cewa Shi Mai yawan ji ne kuma Makusanci ne.


Allah Yayi dadin tsira yayi aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa da mabiyansa da kyautatawa.





TAMBAYOYIN DA AKAYIWA BABBAN MALAMI SHEIKH


ABDUL’AZIZ BN BAAZ BAYAN YAYI TA’ALIKI AKAN


LACCAR (FAHIMTAR ADDINI)





Tambaya 1: Me ake nufi da biyayya ga majibinta al’amari a cikin ayar, shin sune malamai ko kuma shugabanni, ko da sun kasance masu zalintar kawunansu da kuma talakawansu ne?


Amsa 1: Allah – Mai girma da daukaka – Yana cewa: {Yaku wadanda sukayi imani kubi Allah kubi Manzo da majibinta al’amari daga cikinku, idan kukayi jayayya a cikin wani abu to ku maidoshi zuwa ga Allah da ManzonS idan kun kasance kunyi imani da Allah da ranar lahira wancananka shine mafi alheri kuma mafi kyan makoma} . Majibinta al’amari: Sune malamai da sarakuna, sarakunan musulmai da malamansu, sune majibinita al’amari, anayi musu biyayya a cikin biyayya ga Allah idan sunyi umarni da biyayyaa ga Allah kuma abinda yake ba sabon Allah ba.


Malami da sarki anayi musu biyayya; domin da wannan ne halaye zasu daidaita kuma aminci ya tabbata, kuma a zartar da umarni, ayiwa wanda aka zalinta adalci, kuma a tsawatarwa azzalumi, amma idan ba’ayi musu biyayya ba to al’amura zasu baci kuma al’amura zasu lalace, mai karfi zai zalinci mai rauni.


To wajibi shine ayi musu biyayya a cikin biyayya ga Allah a cikin aikin alheri, daidai ne sun kasance sarakuna ne ko malamai; malami zai bayyanar da hukuncin Allah sarki kuma zai zartar da hukuncin Allah, wannan shine daidai a majibinta al’amari, sune masana Allah da shari’arSa, kuma sune sarakunan musulmai, wajibi ne a kansu su zartar da umarnin Allah, kuma wajibine akan talakawa su saurari malamansu akan gaskiya, kuma su saurari sarakunansu a aikin alheri; amma idan sukayi umarni da sabo, daidai ne ya kasance sarki ne ko malami yayi umarni da sabo to baza’ayi masa biyayya ba, idan sarki yace maka: Kasha giya, to kada ka bishi, idan yace maka: Ka sabawa mahaifinka, to kada ka sabawa mahaifinka, idan ya ce: Kaci riba, kada ka ci riba.. haka nan tare da malami idan ya fada maka sabo, kuma masanin shari’a bazai fada maka haka ba, sai dai zai iya zama malami kuma fasiki.


Abin nufi: Malami idan ya umarceka da wani abu na sabon Allah to kada ka bishi a cikin sabon Allah; kadai biyayya a aikin alheri ne, Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana cewa: “Babu biyayya ga wani abin halitta a cikin sabon Mahalicci”, sai dai tawaye ga sugabanni baya halatta koda sunyi sabo, ji da bi yana wajaba a cikin aikin alheri, sai dai kada ka bishi a cikin sabo, lallai kada ka cire wani hannu na biyayya, Annabi – tsira da a mincin Allah su tabbata agare shi – yana cewa: “Ji da bi ya wajaba akan mutum a lokacin farin ciki da abin ki, da a abinda ya so kuma ya ki, muddin dai baiyi umarni da sabon Allah ba, idan akayi umarni da sabon Allah to babu ji kuma babu bi”, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana cewa: “Wanda ya fita daga biyayya kuma ya rabu da jama’a kuma ya mutu to ya mutu irin mutuwar Jahiliyya”, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi yana cewa “Wanda yaga wani abu daga sarkinsa na sabon Allah to yaki abinda yake zuwa (da shi) na sabon Allah, kada ya sake ya cire hannu daga biyayya, domin cewa wanda ya rabu da jama’a to ya mutu irin mutuwar Jahiliyya”, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Duk wanda yazo muku alhali al’amarinku yana hade yana son ya raba jama’arku, kuma ya tsaga sandarku to ku kasheshi, duk yanda yake kuwa”.


Abin nufi: Cewa wajibi shine ji da bi a aikin alheri ga majibinta al’amura daga sarakuna da malamai, da haka ne al’amura zasu tsaru, kuma halaye zasuyi kyau, mutane zasu amintu, kuma ayiwa wanda aka zalinta adalci, a tsawatarwa azzalimi, hanyoyi su amintu, kuma tawaye ga  majibinita al’amura baya halatta da tsaga sanda (rarrabuwa), sai dai idan an samu kafirci a bayyane daga garesu a wajen ‘yan tawayen daga Allah wanda a cikinsa akwai dalili, kuma suna da iko ta hanyar tawayensu zasu iya anfanar da musulmai, kuma su kawar da zalinci, su tsaida daula ta gari. Amma idan sun kasance bazasu iya ba to bai halatta suyi tawaye ba ko da sunga kafirci  a bayyane; domin cewa tawayensu zai cutar da mutane, kuma zai bata al’umma, zai wajabta fitina da kisa ba tare da wani hakki ba, sai dai  idan suna da  iko, kuma suna da karfi akan kawar da wannan azzalimin, wannan shugaban kafiri to su kawar da shi, su dora wani shugaban a bigirensa wanda zai zartar da umarnin Allah, to ya wajaba a kansu suyi hakan idan sun samu kafirci a bayyane a wajensu wanda akwai dalili daga Allah a cikinsa, kuma suna da iko akan samar da gaskiya, da samar da canji na gari da zartar da gaskiya.





Tambaya ta 2: Menene hukuncin sunnanta dokokin da ba na Allah ba?


Amsa ta 2: Idan dokar ta kasance ta dace da shari’a to babu laifi, idan an sunnanta wata doka a hanya, ko a tituna, da wanin hakan daga abubuwan da zasu amfanar da su a gurare, baya sabawa shari’a sai dai zai zartar da al’amura to babu laifi, amma dokokin da suke sabawa shari’a to a’a, idan ya sunnanta wata doka ma’anarta: Cewa babu haddi akan mazinaci, kuma babu haddi akan barawo, kuma babu haddi akan mashayin giya – to wannan batacce ne, wadanannan dokokin batattu ne, kuma idan shugaba ya halatta su to ya kafirta, idan ya ce: Lallai su halal ne, kuma babu laifi da su, wannan zai zama kafirci, wanda ya halatta abin da Allah Ya haramta to ya kafirta.


Tambaya ta 3: Ta yaya za’ayi mu’amala da shi?


Amsa ta 3: Za’ayi mu’amala da shi a aikin alheri, za’a bishi a aikin alheri, ba’a sabo ba har sai Allah Ya kawo canji.


Tambaya ta 4: Ya babban malami kasan abinda ya sauka a farfajiya na fitintinu sai aka samu wasu kungiyoyi misali: Jama’at al-Tablig, da Jama’at al-Ikhwan, da Salafiyya da wasunsu daga kungiyoyi kowace kungiya tana cewa: Lallai ita akan daidai take a cikin bin sunnah. Allah – Ya kiyayeka -, ina tambayarka ka sanar da mu shin wadannene akan daidai daga wadannan kungiyoyin, kuma suwa zamu bi daga cikinsu, kuma ka ambacesu da sunansu? Allah Ya saka maka da mafificin sakamako.


Amsa ta 4: Kaji a cikin lacca da kuma cikin ta’aliki, suwaye kungiyar da za’a bi, kungiyar da ya wajaba a bita, da tafiya akan hanyarta, sune: Ma’abota hanya madaidaciya, sune mabiya Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, sune mabiya Littafi da sunnah wadanda suke kira zuwa Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da aminci su tabbata agare shi -, amma wasu kungiyoyin daban bazamu ji daga garesu ba sai dai idan sun dace da gaskiya, daidai ne sun kasance (Jama’at al-Ikhwan), ko (Jama’t al-Tablig), ko (Ansarul Sunnah), ko wadanda suke cewa: Sune (Salafiyya) ko wasunsu, ko kuma (al-Jama’at al-Islamiyya), ko wata kungiyar da ta ambaci kanta wani abu, ko suka ambaci kansu, koma suka ambci kansu Ahlul Hadis, za’ayi musu biyayya kuma za’a bisu a cikin gaskiya, muddin dai akwai dalilin da suka dace a kansa, abinda kuma ya sabawa dalili za’a mayar musu da shi, za’ace: A’a wannan galadi ne daga gareku, ko kunyi kuskure a wannan, kunyi kuskure yaku ‘yan uwa, kunyi kuskure a cikin wannan al’amarin, muna dacewa akan wannan al’amarin da ya dace da aya mai girma da hadisi madaukaki, ya dace da Ijma’in ma’abota ilimi, ya dace da Ahlus Sunnah wal jama’a, wannan zamu yarda da shi; amma fadinku: Kaza, ko fadinku: Kaza, ko aikinku kaza, to wannan sabanin gaskiya ne, wannan ma’abota ilimine zasu fada musu shi, babu wadanda zasu san hakan sai ma’abota ilimi, sune zasu nunawa kungiyoyin Musulunci: Jama’at al-Tablig, Jama’at al-Ikhwan, Jama’at Ansar al-Sunnah, al-Jama’at a-Salafiyya, kadai malamaine zasu san wannan rabe-raben: Ma’abota sanin al-Qur’ani da sunnah, wadanda suka fahimci Addini ta hanyar littafi da sunnah sune wadanda suke sanin rabe-raben wadannan kungiyoyin, kuma wadannan kungiyoyin a tare da su akwai gaskiya da bata, a tare da su akwai gaskiya, su ba ma’asumai bane, kowane daya ba ma’asumi bane, sai dai gaskiya shine abinda dalili ya tsayu a kansa, abinda dalili ya tsayu a kansa na Littafi da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – daga wadannan kungiyoyin, ko daga Mazahabar Hanbaliyya, ko Shafi’iyya, ko Malikiyya, ko Zahiriyya, ko Hanafiyya ko wasunsu – sune gaskiya, abinda kuma ya sabawa dalili – na Littafi da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana kasancewa kuskure, kuma mai shi idan ya kasance daga ma’abota gaskiya mai ijtihadi kuma mai neman gaskiya zai zama yana da lada idan ya dace, idan ma yayi kuskure zai zama yana da lada.


Amma wadanda suke kira zuwa wanin sunnah, suna kira zuwa wanin Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to wadannan baza’a bisu ba, kuma baza’ayi koyi da suba, kuma baza’a saurara musu ba kuma za’ayi adawa da su, kamar masu kira zuwa Rafidanci (Shi’anci), makiya Ahlus Sunnah wal jama’a makiya sahabbai, suna zagin sahabbai, suna kirkirar karya da shaidar zur dan riyawarsu ga bin Ahlul baiti, to wannan batacce ne; domin cewa Ahlul baiti su daga Ahlus Sunnah wal jama’a suke; (Sayyadina) Aliyu – Allah Ya yarda da shi -, da Hassan da Hussain da Ahlul bait wadanda aka sani da alheri to su daga Ahlus Sunnah ne akan hanyar sahabbai suke, su suna kan jinsin abinda (sayyadina) Abubakar da Umar suke a kansa, wanda ya sabawa Ahlul bait, kuma yake riya cewa su suna sanin gaibu ko cewa su ana bauta musu koma bayan Allah, da kira koma bayan Allah, ko kuma ya kamata a gina masallatai akan kaburburansu ko kubbobi, to wannan galadi ne, wannan batacce ne, baza’ayi koyi da su ba kuma baza’a bisu ba, wadannan ana daukarsu ma’abota bata babu wani kokwanto: Muna rokon Allah lafiya.


Hakanan Almaniyyun wadanda suke kira zuwa ga ra’ayi zuwa ga abinda ya sabawa shari’ar Allah, suna kira zuwa ga soye-soyen rayukansu da barin Littaffi da sunnah, kadai yana bin abinda mutane suke so ne da kuma abinda suke nufinsa, da abinda zai gyara musu duniyarsu, wadannan ya wajaba a yakesu, kada a bisu, kawai ana yin biyayya ne kuma ana bin wanda yayi kira ne zuwa ga Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – kuma ya dace da gaskiya: Ya dace da gaskiya, idan ya kuskure to a’a, za’ace masa: Ka kyautata idan ya kyautata, kuma kayi kuskure idan kayi kuskure, kuma a bishi a daidai kuma ayi masa addu’a da dacewa. Idan yayi kuskure za’ace masa: Kayi kuskure a abu kaza, kuma ka sabawa dalili kaza, wajibine a kanka ka tuba zuwa ga Allah da komawa gaskiya, wanann ma’abota ilime ne zasu fada masa, ma’abota basira, amma gamagari to ya tambayi ma’abota sanin Allah, ma’abota sanin Littafi da sunnah wadanda aka sani wadanda suke bin Littafi da sunnah, basa kira zuwa Ilhadi ko zuwa Shi’anci, ko misalin ma’abota zance (Ilmul kalam) daga Jahamiyya da wasunsu, ko zuwa wanin wannan daga mazahabobi ma’abota karya, kadai ya bi wanda yake kira zuwa Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da dalili, da basira, kuma ya tambayi ma’abota ilimi game da su, wadanda aka sansu da Littafi da sunnah, ya tambayesu: Shin me kuke cewa ne a cikin da’awar wane zuwa kaza, zaice: Kaza, zaice: Kaza; har ya gane, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Ku tambayi ma’abota zikiri in kun kasance bakwa sani} , Allah Yana cewa: {Ku tambayi ma’abota zikiri}, ma’abota sanin Littafin Allah da sunnar ManzonSa sune ma’abota zikiri, amma ‘yan bidi’o’i to su basa daga ma’abota zikiri, masu kira zuwa bidi’a basu ne ma’abota zikiri ba.


Tambaya ta 5: Mu muna cikin wata kasa wacce babu wani malami na Allah a cikinta da za’a karbi ilimi daga gareshi, sai dai muna dogara ne da littattafai da kasussukan Musulunci, hakika kun anbaci: Cewa ilimi ba’a samunsa sai da bita, to me zamuyi alhali mu muna cikin wannan yanayin?


Amsa ta 5: Wajibi ne a kanku ku nemi ilimi a cikin kasussuka masu tsarki daga maluman gaskiya sanannu: A cikin (Nurun alad Darb (Haske akan hanya)) a cikinsa akwai alheri mai yawa, shirin Nurun alad Darb ana yinsa ne tsakanin Magariba da Issha’a daga rediyon Nida’ul Islam (kiran Musulunci), kuma anayinsa karfe tara da rabi na dare daga Iza’atul Qur’anil kareem (Rediyon al-Qur’ani mai girma) a kowane dare, a cikinsa akwai malaman da suke tace gaskiya da dalili, haka nan a cikin kasussuka masu tsafta daga malaman da aka anfana da su; kamar cewa ku kun tambayesu ne. Kuyi kokari a wajen tafiya zuwa guraren da a cikinsu akwai malamai, ku kintaci tsangayun ilimi koda tsakanin wani lokacine da wani daban, magabata sun kasance suna tafiya tafiya mai tsawo kamar haka dan samun ilimi da tabbatar da ilimi, ku shiga cikin tsangayoyi da cibiyoyi masu anfani, ku nemi hakan; har ku anfana. Haka nan mai neman ilimi mai kwadayi yake kasancewa, yana neman kasussuka masu tsafta, yana sauraren kasidu masu tsafta, da tsarftatattun laccoci, ya saurari Nurun alad Darb, yayi tafiya zuwa tsangayun ilimi, koda a wuri mai nisa ne kai koda a masallaci mai nisa ne, zuwa ga malaman sunnah, ya dinga halartar tsangayoyinsu, kuma ya anfana da su, magabata sun kasance suna tafiya daga Yammacin (duniya) zuwa Makka, daga yammaci mai nisa zuwa Makka da Madina, dan neman ilimi, kuma daga Gabashin (duniya) daga Indiya da Fakistan da wanin haka zuwa Makka da Madina, dan neman ilimi, kuma zuwa Syria, to kuyi koyi idan kunyi tafiya zuwa ga wani malamin da kuka sanshi cewa shi yana daga Ahlus Sunnah, ku halacci tsangayoyin ilimi a wurinsa kuma ku anfana. Wannan dukkaninsa yana da kyau, wannan yana daga neman ilimi.


Muna rokon Allah Ya datar da kowa da kowa, kuma Ya azirta mu da ku ilimi mai anfani da aiki na gari.


Allah Ya datar da kowa da kowa, Allah Yayi dadin tsira Yayi aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa.





TATTAUNAWA TARE DA BABBAN MALAMI SHEIKH ABDUL’AZI BN BAAZ


GAME DA (FAHIMTAR ADDINI)


JARIDAR NAN  TA AL-SHARKUL AUSAD (GABAS TA TSAKIYA) CE TA GUDAR DA ITA





Tambaya ta 1: Daga mas’alolin da aka tattauna akwai mas’alar alakar da ke tsakanin shugaba da wanda ake shugabanta da ka’idoji na shari’a ga wadannan alakokin.


Ya Sheikh: A kwai wanda yake ganin cewa aikata sabo da manyan laifuka daga wasu daga shugabanni yana wajabta yi musu tawaye da kokarin canji koda cutarwa ga musulmai a cikin gari zai biyo baya a kansa. Abubuwan da duniyarmu ta Musulunci take fama da shi suna da yawa, to menene ra’ayinku a cikin wannan?


Amsa ta 1: Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai, dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Allah Yayi dadin tsira Yayi aminci ga Manzon Allah, da alayensa da sahabbansa, da wanda ya shiriya da shiriyarsa. Bayan haka:


Hakika Allah – Mai girma da daukaka – Ya ce: {Yaku wadanda sukayi imani ku bi Allah ku bi Manzo da majibinta al’amari daga cikinku, idan kukayi jayayya a cikin wani abu to ku dawo da shi zuwa ga Allah da ManzonS in kun kasance kunyi imani da Allah da ranar Lahira, hakan shine mafi alheri kuma mafi kyan makoma} , wannan ayar nassi ne a cikin wajabcin biyayya ga majibinta al’amari, sune: Sarakuna, da malamai, hakika sunnah ingantacciya tazo daga Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – tana bayyana cewa wannan da’ar lazima ce, kuma ita farilla ce a aikin alheri.


Nassosi daga sunnah suna bayyana ma’ana, kuma suna fa’idantar da  wawaitar ayar cewa abin nufi: Yi musu biyayya a aikin alheri, kuma yana wajaba akan musulmai biyayya ga majibinta al’amura a aikin alheri ba’a sabo ba, idan sukayi umarni da sabo to baza’a bisu a cikin sabo ba, sai dai baya halatta ayi musu tawaye da sabubbansa; saboda fadinsa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – “Ku saurara wanda wani shugaba ya shugabance shi sai ya ganshi yana zuwa da wani abu na sabo to yaki abinda yake zuwa (da shi) na sabon Allah, kada ya cire wani hannu daga biyayya”, da kuma fadinsa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -: “Wanda ya fita daga biyayya kuma ya rabu da jama’a sai ya mutu, to ya mutu irin mutuwar Jahiliyya”, kuma tsira da aminci su tabbata agare shi ya ce: “Ji da bi ya wajaba akan mutum a abinda ya so da abinda yaki, sai dai idan an umarceshi da sabo, idan aka umarce shi da sabo to babu ji babu biyayya”, kuma sahabbai – Allah Ya yarda da su - sun tambaye shi lokacin da aka ambaci cewa za’a samu wasu sarakuna zaku sani (aikin alheri) daga garesu kuma zakuyi inkari – suka ce: To me zaka umarce mu? Ya ce: “Ku basu hakkinsu, kuma ku roki Allah hakkinku”, Ubadah bn Samit – Allah Ya yarda da shi - ya ce: Munyiwa Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – caffa akan ji da biyayya a lokacin farin cikinmu da lokacin bakin cikinmu, da talaucinmu da wadatarmu da babakere a kanmu, kuma kada muyi jayayyar al’amari da ma’abotansa, ya ce: “Sai dai idan kunga kafirci a bayyane, wanda akwai wani dalili gareku a wajen Allah”.


To wannan yana nuni akan cewa baya halatta garesu suyi jayayya da majibinta al’amura, ko yi musu tawaye, sai dai idan sunga kafirci a bayyane a wurinsu wanda akwai wani dalili garesu a wajen Allah; hakan bai zama ba sai dan cewa tawaye ga majibinta al’amura yana sabbaba barna mai yawa da sharri mai girma, sai aminci ya baci, kuma hakkoki su tozarta, kuma tsawatarwa azzalimi bazai sawwaka ba, ko taimakon wanda aka zalinta, kuma hanyoyi su baci bazasu amintu ba, sai a samu barna mai yawa da sharri mai girma akan tawaye ga majibinta al’amura, sai dai idan musulmai sunga kafirci a bayyane wanda suke da wata hujja a wurin Allah a cikinsa, to babu laifi suyiwa wannan shugaban tawaye dan kawar da shi idan suna da iko, amma idan basu da iko to kada suyi tawaye, ko cewa tawayen zai sabbaba sharri mafi yawa to baya halatta suyi tawayen; dan kulawa ga maslahar kowa da kowa.


Ka’ida ta shari’a wacce aka hadu a kanta: (Cewa baya halatta kawar da sharri da sharrin da ya fishi, kai yana wajaba kare sharri da abinda zai gusar da shi ko ya sawwakeshi), amma kare sharri da sharrin da ya fishi yawa to baya halatta da ijma’in musulmai, idan wannan kungiyar ta kasance wacce take son kawar da wannan sarkin wanda ya aikata kafirci a bayyane tana da ikon da zata kawar da shi da ita, kuma ta dora wani shugaban na gari mai hali na gari ba tare da an samu wata barna mai girma akan musulmai da wannan ba, da sharri mafi girma daga wannan sarkin to babu laifi. Amma idan tawayen ya kasance zai jawo barna babba, da bacin aminci, da zalintar mutane, da garkuwa da wanda bai cancanci garkuwa (da shi ba)… zuwa wanin wannan daga zalinci mai girma; to wannan baya halatta, kai wajibine ma ayi hakuri, da ji da biyayya a aikin laheri, da yiwa majibinta al’amura nasiha, da yi musu da’awa ta alheri, da kokari a sawwaka sharri, da karantashi, da yawaita alheri.


Wannan itace hanya madaidaiciya wacce yake wajaba a shigeta; domin cewa a hakan akwai maslahohin masulmai gaba daya; kuma domin cewa a hakan akwai karanta sharri da yawaita alheri; kuma domin cewa a hakan akwai kiyaye aminci da kubutar musulmai daga sharrin da yafi yawa.


Muna rokon Allah dacewa da shiriya ga kowa da kowa.


Tambaya ta 2: Ya babanmu Sheikh: Munsan cewa wannan zancen tushene daga tushen Ahlus Sunnah wal jama’a, sai dai a nan – kaico – daga ‘yan Ahlus Sunnah wal jama’a wanda yake ganin cewa wannan wani tinanine mara kyau, kuma a cikinsa akwai wani abu na rauni, kuma hakika ya karbi wannnan zancen; saboda haka suke kiran samari zuwa gina tsauri a cikin canji?


Amsa ta 2: Wannan galadine daga mai fadarsa, da karancin fahimta; domin cewa su basu fahimci sunnah ba basuma santa ba kamar yanda ya kamata, kawai hamasa ce kawai ta dauke su da kishi dan kawar da munkari akan fadawarsu a cikin abinda yake sabawa shari’a, kamar yanda Kawarijawa da Mu’utazilawa suka fada, son gaskiya ne ya dauke su ko kuma kishin gaskiya, hakan ya daukesu akan fadawarsu cikin karya har suka kafirta musulmai da sabo kamar yanda Kawarijawa suka aikata, ko suka dawwamar da su a cikin wuta sabo da sabo kamar yanda Mu’atalizawa suke aikatawa.


Kawarijawa sun kafirta (mutane) da sabo, kuma sun dawwamar da masu sabo a cikin wuta, Mu’utazilawa kuma sun dace da su a karshe, kuma cewa su ababen dawwamarwa ne a cikinta, sai dai sunce: Lallai su a duniya suna (Manzila bainal manzilataini) wani matsayi tsakanin matsayi biyu, kuma dukkansa bata ne.


Abinda Ahlus Sunnah suke a kansa – shine gaskiya – cewa mai sabo baya kafirta da sabonsa muddin dai bai halattashi ba, idan yayi zina to baya kafirta, idan yayi sata baya kafirta, idan yasha giya baya kafirta, sai dai yana kasancewa mai sabo mai raunin imani fasiki za’a tsayar masa da haddodi, kuma baya kafirta da hakan sai dai idan ya halatta sabon ya ce: Shi halal ne, abinda Kawarijawa suka fada a wannan batacce ne, kuma kafirtawarsu ga mutane ma batacce ne; saboda haka Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  - ya ce a cikin sha’aninsu: Lallai cewa su zasu fice daga Addini irin ficewar kibiya daga abin da aka harba sannnan bazasu dawo ba zuwa gareshi, zasu yaki ma’abota Musulunci zasu bar ma’abota (bautar) gumaka, wannan shine halin Kawarijawa saboda wuce gona da irinsu da jahilcinsu da kuma batansu, dan haka baya dacewa da samari ko wanin samari su kwaikwayi Kawarijawa da Mu’utazilawa, kai yana wajaba suyi tafiya akan mazahabar Ahlus Sunnah wal jama’a akan mahukuntar dalilai na shari’a, sai su tsaya tare da nassosi kamar yanda suka zo, bai halatta suyiwa sarki tawaye ba saboda wani sabo ko wasu laifukan da suka faru daga gareshi, kai wajibi ne a kansu suyi masa nasiha ta hanyar rubutu da kuma baki da baki, ta hanya mai kyau ta hikima, da kuma jayayyar da take itace mafi kyau; har sai sunyi nasara, kuma har sai sharri ya karanta ko ya gushe kuma alheri ya yawaita.


Hakanan nassosi sukazo daga Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Allah – Mai girma da buwaya – Yana cewa: {Saboda rahama ta musamman daga Allah sai ka zamo mai tausasawa garesu, kuma da ka kasance mai kaushin mu’amala mai kekasasshiyar zuciya da sun watse sun barka} .


To wajibi ne akan masu kishin Allah da masu kira zuwa shiriya su lazimci iyakokin shari’a, kuma suyiwa wadanda Allah Ya jibinta musu al’amura nasiha, da zance mai dadi, da hikima, da usulubi mai kyau, har alheri ya yawaita, kuma sharri ya karanta, kuma har masu kira zuwa ga Allah su yawaita, kuma har suyi nishadi a cikin da’awarsu da wacce take itace mafi kyau, bada tsauri ba da kuma tsanani, suyiwa wadanda Allah Ya jibintawa al’amuransu nasiha da mabanbantan hanyoyi mai dadi kubutattu, tare da yi musu addu’a a boye: Cewa Allah Ya shiryar da su kuma Ya datar da su Ya taimake su akan alheri, kuma cewa Allah Ya taimakesu akan barin laifukan da suke aikata su, da kuma tsaida gaskiya.


Haka mumini zai roki Allah yana mai kankar da kai gareShi: Cewa Allah Ya shiryar da majibinta al’amura, kuma Ya taimakesu akan: Barin barna, da tsaida gaskiya da usulubi mai kyau, da kuma abinda yake shine mafi kyau, haka nan tare da ‘yan uwansa masu kishi yayi musu nasiha yayi musu wa’azi ya gargadar da su, har suyi nishadi a cikin da’awa da abinda yake mafi kyau, bada tsauri da tsanani ba, da haka ne alheri zai yawaita, sharri ya karanta, kuma Allah Ya shiryar da majibinta al’amura ga alheri da tabbata a kansa, kuma karshe ya zama abin yabo ga kowa da kowa.


Tambaya ta 3: Da mun kaddara cewa a nan akwai tawaye na shari’a daga wata kungiya daga kungiyoyi, shin wannan zai iya kubutar da kashe mataimakan wannan shugaban da dukkan wanda yake aiki a cikin hukumarsa misali: ‘Yan sanda da jami’an tsaro da wasunsu?


Amsa ta 3: Ya gabata na fada maka: Cewa yiwa sarki tawaye baya halatta sai da sharudda biyu:


Na farkonsu: Samun kafirci baro-baro, wanda suke da wani dalili a wurin Allah.


Sharadi na biyu: Iko akan hanbarar da shugaban hanbararwar da wani sharri mafi girma bazai biyo baya daga gareshi ba, da wanin hakan to baya halatta.


Tambaya ta 4: Wasu daga matasa – Allah Ya kiyayeka – suna zatan cewa kausasawa kafirai – daga wadanda suke zaune a kasashen Musulunci ko daga masu zuwa garesu – hakan yana daga shari’a; saboda haka ne wasu daga ciki suka halatta kashesu da kwace musu (dukiyoyi) idan sunga abinda suke inkari daga garesu.


Amsa ta 4: Kashe kafirin dake zaune a garin Musulunci baya halatta, ko wanda yake zuwa wanda aka amintar wanda kasa ta shigo da shi a cikin aminci, ko kashe masu sabo ko yin ta’addanci a kansu, kai su sukai karar abinda yake faruwa daga garesu na ayyukan munkari ga kotun shari’a, kuma abinda kotunan shari’a suka gani ma ya isa.





Tambaya ta 5: Idan kuma babu kotunan shari’a fa?


Amsa ta 5: Idan babu kotunan sharia’, to sai dai nasiha kawai, nasiha ga majibinta al’amura, da fuskantar da su ga alheri, da taimakekeniya tare da su, har sai sunyi hukunci da shari’ar Allah. Amma idan mai umarnin da mai hanawar yana mika hannunsa yayi kisa ko yayi duka to baya halatta, sai dai yayi taimakekeniya tare da majibinta al’amura da abinda yake shine mafi kyau; har sai sunyi hukunci da shari’ar Allah a cikin bayin Allah, inba haka ba fa to wajibinsa shine nasiha, kuma wajibinsa shine fuskantarwa zuwa ga alheri, kuma wajibinsa shine inkarin abin ki da abinda yake shine mafi kyau, wannan shine wajibinsa, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Kuji tsoron Allah iya iyawarku} ; domin cewa inkarin abin ki da hannu ta hanyar kisa ko duka sharri mafi yawa yana biyo bayansa da kuma barna mai girma ba tare da kokwanto ba, kuma babu kokwanto ga dukkan wanda ya jarraba wadannan al’amuran kuma ya sansu.


Tambaya ta 6: Shin horo da aikin alheri da hani daga abin ki musamman ma canjawa da hannu hakki ne ga kowa da kowa, ko cewa shi hakki ne wanda aka shardantawa shugaba ne ko wanda shugaban ya ayyana shi?


Amsa ta 6: Canjawa ga kowa da kowa ne gwargwadan ikonsa; domin cewa Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana cewa: “Wanda yaga wani abin ki daga cikinku to ya canja shi da hannunsa, idan bazai iya ba to da harshensa, idan bazai iya ba to da zuciyarsa, hakan shine mafi raunin imani”, sai dai canjawa da hannu ba makawa ta zama da ikon da wata barna mai girma da sharri mai yawa bazasu biyo baya ba, to sai ya canja shi da hannu a cikin gidansa: A kan ‘ya’yansa, da matarsa, da ma’aikatan gida, haka nan ma’aikacin gwamnati a hukumarsa wacce yake da alhakin kula da ita, sai ya canja da hannunsa, gwargwadan bayanan da ke gareshi, inba haka ba fa to kada ya canja komai wanda babu alhakin kula da ita gareshi a cikinsa; domin cewa shi idan ya canja da hannunsa a abinda baya shiga karkashin ikonsa to sharri mafi yawa da bala’i mai girma da sharri mai girma zasu biyo baya tsakaninsa da tsakanin mutane, da kuma tsakaninsa da kasar. Sai dai ya wajaba a kansa ya canja da harshe kamar ya ce: (Kai wane kaji tsoron Allah, wannan baya halatta), (wannan haramun ne a kanka), (wannan wajibi ne a kanka), ya bayyana masa da dalilai na shari’a da harshe, amma da hannu sai ya zama bigiren iko, a cikin gidansa, ko ga wanda ke karkashin hannunsa, ko ga wanda akayi masa izini a cikinsa ta hanyar sarki cewa yayi horo da aikin alheri, kamar bangarorin da sarki yake umartarsu kuma yake basu dama, suyi canji gwargwadan yanda aka basu damar da aka basu ta fuskar shari’ar da Allah Ya shara’anta, kada suyi kari a kansa, haka nan sarkin gari ya canja da hannunsa gwargwadan bayanan da ke gareshi.


Tambaya ta 7: Allah Ya kiyayeka a nan akwai wanda yake ganin cewa yana da hakki ayiwa tsariika na gamagari wadanda shugaba yake sanyasu kamar tsarin tafiya akan tituna da kula da iyakoki da fasfot… har zuwa karshe da wasunsu, lura da cewa su ba’a ginasu akan ginshiki na shari’a ba, to me zaku ce – Allah Ya kiyayeku -?


Amsa ta 7: Wannan batacce ne kuma abin ki ne, hakika ya gabata: Cewa tawaye baya halatta ko canjawa da hannu, kai ji da biyayya yana wajaba a cikin wadannan al’amuran wadanda babu wani abin ki a cikinsu, kai shugaba ne ma ya tsarasu dan maslahohin musulmai, to biyayya ga hakan yana wajaba, da ji da bi a cikin hakan; domin cewa wannan yana daga aikin alherin da yake anfanar musulmai, amma abin da yake shi abin ki ne; kamar harajin da shugaba yake ganin halaccinsa to za’a komawa shugaba a cikinsa dan yi masa nasiha da kira zuwa ga Allah, da kuma fuskantar da shi zuwa alheri, bada hannunsa ba ya daki wannan ko ya zubar da jinin wannan ko yayiwa wannan ukuba ba tare da wata hujja ko wani dalili ba, kai babu makawa ya kasance yana da wata hujja daga shugaba da zai dinga tasarrufi da ita gwargwadan umarce-umarcen da ke gare shi, to inba haka bafa to ya isheshi yin nasiha da fuskantarwa, sai dai ga wanda yake a karkashin ikonsa daga ‘ya’ya da mata da makancin hakan daga wadanda yake da iko a kansu.


Tambaya ta 8: Shin Allah – Ya kiyayeka - abinda caffa take hukutawa shine addu’a ga shugaba?


Amsa ta 8: Daga abinda caffa take hukuntawa yin nasiha ga shugaba, daga cikin nasiha: Yi masa addu’a da dacewa, da shiriya da gyaruwar niyya da aiki da gyaruwar abokanan aiki; domin daga cikin sabubban gyaruwar shugaba, da kuma sabubban Allah Yayi masa muwafaka: Ya zama yana da waziri na gaskiya, da zai taimake shi akan alheri, kuma ya tinatar da shi idan ya manta, ya taimakeshi idan ya tina, wadannan suna daga sabubban taufikin Allah ga shugaba.


To wajibi akan talakawa da kuma daidaikun talakawa taimakekeniya tare da shugaba a cikin gyara da kashe sharri da gamawa da shi, da tsaida alheri da daddadan zance, da usulubi mai kyau da fuskantarwa madaidaiciya wacce ake kwadayin alheri a bayanta banda sharri, kuma dukkan aikin da sharri zai biyo bayansa sama da maslaha to baya halatta; domin abin nufi daga shugabanci gaba dayansa shine tabbatar da maslahohi na shari’a, da tunkude barnce-barnace, dukkan aikin da mutum zai aikatashi wanda yake nufin alheri da shi kuma abinda yake mafi sharri zai biyo baya daga abinda yayi nufin kawar da shi da abinda yake abin ki to baya halatta gareshi.


Hakika babban malamin Musulunci Ibnu Taimiyya – Allah Yayi masa rahama - ya bayyanar da wannan ma’anar bayyanarwa cikakkiya a cikin littafin (al-Hisbah) sai a koma masa; saboda fa’ida mai girma.


Tambaya ta 9: Shin wanda yake kin yiwa shugaba addu’a fa - Allah Ya kiyaye ka -?


Amsa ta 9: Wanann yana daga jahilcinsa da rashin basirarsa; domin cewa addu’a ga shugaba yana daga mafi girman kusanci, kuma yana daga mafi girman ayyukan biyayya, kuma yana daga nasiha ga Allah da bayinSa, Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – lokacin da akace da shi: Lallai cewa (kabilar) Daus sunyi sabo alhali su kafirai ne, ya ce: “Ya Allah Ka shiryar da Daus kuma Kazo da su” sai Allah Ya shiryar da su kuma sukazo masa alhali suna musulmai.


Mumini ya dinga yiwa mutane addu’ar alheri, sarki kuwa shine wanda yafi cancanta ayi masa addu’a; domin cewa gyaruwarsa gyaruwar al’umma ce, yi masa addu’a yana daga mafi muhimmancin addu’o’i, kuma daga mafi muhimmancin nasihohi: A datar da shi akan gaskiya, kuma Allah Ya kareshi sharrin kansa, da sharrin munanan abokanan zama, yi masa addu’a da dacewa da shiriya da gyaruwar zuciya da aiki da gyaruwar abokanan aiki yana daga mafi muhimmancin abubuwa masu muhimmanci, kuma yana daga mafifitan ayyukan kusanci, hakika an ruwaito daga Imam Ahmad cewa shi yace: (Da ace ni nasan ina da addu’ar da za’a karbeta da na juyar da ita ga sarki), kuma an ruwaito hakan daga Fudail dan Iyad – Allah Yayi masa rahama -. Allah Shine Mai datarwa.


Allah Yayi dadin tsira Yayi aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya.





 



Posts na kwanan nan

FAHIMTAR ADDINI (SHIN ...

FAHIMTAR ADDINI (SHINE) TSARI DAGA FITINTINU 2

FAHIMTAR ADDINI (SHIN ...

FAHIMTAR ADDINI (SHINE) TSARI DAGA FITINTINU 1

ABUBUWAN DA SUKE WARW ...

ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI.

MUJALLADIN HUDUBOBIN ...

MUJALLADIN HUDUBOBIN JUMU’A NA WATAN RAMADAN DA HAUSA