Labarai




SIFFAR SALLAR ANNABI – TSIRA DA AMINCIJ ALLAH


SU TABBATA AGARE SHI -


Na shehin Malami


AbdulAziz ɗan Abdullah ɗan Baaz


Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin ƙai


Dukkanin godiya ta tabbata ga Allah Shi kaɗai, tsira


da aminci su tabbata ga bawanSa kuma manzonSa


Annabimmu Muhammad da alayansa da sahabbansa.


Bayan haka:


Waɗannan wasu taƙaitattun bayanai ne a cikin siffar


sallar Annabi, ina son in gabatar da su ga dukkanin


musulmi da musulma, domin duk wanda ya gani yayi


ƙoƙarin koyi da shi a cikin hakan, saboda faɗinsa: (Ku yi


sallah kamar yadda kuka ga ina yin sallah) 1 Bukhari ne


ya rawaito shi. Ga bayanin hakan ga mai karatu:


1 Bukhari, babin kiran sallah (605), Darimi, al-Sallah: (1253).


3





Kyautata alwala


1. Zai kyautata alwala, shi ne yayi alwala kamar


yadda Allah Ya umarce shi, don yin aiki da faɗinSa -


tsarki ya tabbatar maSa Ya ɗaukaka -:





 {Ya ku waɗanda suka yi imani, idan kun tashi za ku


yi sallah, to, ku wanke fuskokinku da hannayenku zuwa


gwiwoyi, kuma ku shafi kawunanku, kuma (ku wanke)


ƙafafunku zuwa idon sawu}2 Zuwa ƙarshen ayar.


Da faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi _ (Ba’a karɓar sallah ba tare da tsarki ba)3 .


Fuskantar Alƙibla


2- Wanda zaiyi sallah zai fuskanci alƙibla, ita ce


kuma Ka’abah, duk ta inda yake da dukkanin jikinsa


yana nufin yin sallar da zaiyita da zuciyarsa ta farilla ko


nafila, ba zai furta niyya da harshensa ba, domin ba a


shar’anta furta niyya ba, yin hakan bidi’a  ne, saboda


Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -


bai furta niyya ba haka nan sahabbansa - Allah Ya


 


2  Suratul Ma'idah, aya ta: 6.


3  Muslim, Tsarki (224), Tirmizi, Tsarki (1), Ibnu Majah, Tsarki da sunnoninsa (272),


Ahmad (2/73).


yarda da su -, sai ya sanya suturar da zai yi sallah ga


reta idan ya kasance liman ne ko shi kaɗai yake sallah.


Fuskantar alƙibla sharaɗi ne a sallah, saidai a wasu


mas’alolin da aka togance kuma sanannu da a ka yi


bayaninsu a littattafan malamai.


Kabbarar harama, da ɗaga hannaye biyu a lokacin


kabbarar, da kuma ɗora hannayen biyu akan ƙirji.


3. Yana yin kabbarar harama yana cewa: Allahu


Akbar, yana mai kallon inda zai yi sujjada da


idanuwansa zuwa bigiren sujjadarsa.


4. Yana daga hannuwansa daura da kafaɗunsa ko


daidai da kunnuwansa.


5. Ya sanya hannuwansa a ƙirjinsa, na dama akan


tafin na hagu, da wuyan hannu da damtse, saboda


tabbatuwar hakan daga Annabi - tsira da amincin Allah


su tabbata a gare shi -.


Addu'ar buɗe Salla


6. An sunnanta, (mai sallah) ya karanta Addu’ar


buɗe sallah, ita ce: Ya Allah Ka nisantar da tsakanina da


kurakuraina kamar yadda Ka nisantar da gabas da


yamma, Ya Ubangiji Ka tsaftace ni daga kurakuraina


kamar yadda ake tsaftace farin tufa daga datti, ya Allah


5


Ka wankeni daga kurakuraina da ruwa da ƙanƙara da


sanyi.


Idan (mai sallah) ya ga dama maimakon wannan sai


ya karanta:


Tsarki ya tabbata a gareKa ya Allah haɗi da gode


maKa,


(4). 4


 kuma sunanKa ya girmama kuma ƙarfinKa ya


ɗaukaka, kuma babu abin bautawa da gaskiya sai Kai


Idan ya yi (wata addu’ar) da ba waɗannan ba cikin


addu’oin buɗe sallah tabbatattu daga Annabi to babu


wani laifi, abinda yafi yayi wannan wani lokacin kuma


yayi waccan wani lokacin daban, domin hakan yafi


kaiwa ƙoli wurin biyayya, sannan sai ya ce:


Ina neman tsari daga sheɗan jefaffe.


Da sunan Allah Mai rahama Mai jin ƙai, sai ya


karanta Fatiha, saboda faɗinSa: (Babu sallah ga wanda


bai karanta Fatihatul Kitab ba)5 . Sai ya ce: Amin, bayan


(ya karanta ta) a bayyane a cikin sallar da ake karatu a


bayya ne,  kuma a sirrance idan sallar a ɓoye ake yinta,


sannan ya karanta abinda ya sawwaƙa na AlKur’ani.


4 Al-Bukhari, Kiran sallah (711), Muslim Masallatai da wuraran sallah (598), Nasa’i


buɗe sallah (895), Abu Dawud Sallah (781), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnantu


fiha (805), Ahmad (2/231), al-Darimi (Sallah1244).


5 Bukhari Kiran sallah (723), Muslim (394), Tirmizi Sallah (247), Nasa’i Buɗe sallah


(911), Abu Dawud Sallah (822), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnantu fiha (837),


Ahmad (5/316), al-Darimi (1242).


6


Abinda ya fi ya karanta bayan Fatiha a sallar Azahar


da La’asar da Issha cikin tsakatsakin Mufassal, a Asuba


cikin dogayan Mufassal, a Magariba kuma wani lokacin


cikin dogayan Mufassal, wani lokacin kuma cikin


gajerun Mufassal, don yin aiki da hadisan da suka zo da


hakan .


Ruku’i da tasowa daga ruku’in da kuma


abinda ya ƙunsa


7. Zai yi ruku’i yana mai yin kabbara kuma yana


ɗaga hannayansa zuwa daidai kafaɗunsa ko


kunnuwansa, yana mai sanya kansa daidai da gadon


bayansa, yana ɗora hannayansa akan gwiwowinsa,


yana mai wara yatsunsa, ya kuma nutsu a ruku’insa


yana mai cewa:


Tsarki ya tabbata ga Ubangijina Mai girma.  


Abinda yafi shine ya maimaita faɗin sau uku ko


sama da haka, kuma an so ya ce tare da hakan: (Tsarki


ya tabbata a gareKa ya Allah Ubangiji tare da gode


maKa, ya Ubangiji Ka gafarta min6 .


8. Yana ɗago kansa daga ruku’i yana mai ɗaga


hannayansa zuwa kafaɗunsa ko daura da kunnuwansa,


6 Bukhari Tafsirul Kur’an (4683), Muslim Sallah (484), Nasa’i Taɗbik (1122), Abu


Dawud (877), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (889).


7


yana mai cewa: (Allah Ya ji mai gode masa (7) -7 Idan ya


kasance liman ko shi kaɗi ne sai ya ce a lokacin da yake


tasowa: (Rabbana Walakal Hamdu, Hamdan Kasiran


Ɗayyiban Mubarakan Fihi, Mil’as Samawati, Wa Mil


al’ard, Wa Mil’a Ma Baina huma, Wa Mil’a Ma Shi’ata


Min Shai’in Ba’adu) 8 . Amma idan ya kasance mamu ne


to a lokacin ɗagowa daga ruku'u sai ya ce:


Rabbana walakal Hamd”. Zuwa ƙarshen abinda ya


gabata, idan kuma kowannan su ya ƙara, wato liman


da mamu da mai sallah shi kaɗai" (Ahlus Thana’i wal


majd, a haƙƙun ma ƙalal abdu, wakulluna laka abdu.


Allahumma La mani’a lima aaɗaita wala mu’uɗiya lima


mana’a ta, wala yanfa’u zal jadd mikal jadd (9)"9 Yin


hakan yana da kyau, saboda tabbatuwar hakan daga


gare shi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -,


kuma an so kowannen su ya ɗora hannuwansa a


ƙirjinsa kamar yadda yayi a tsaye kafin yayi ruku’i,


saboda tabbatuwar abinda yake nuni akan hakan daga


Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -


cikin Hadisin Wa’il ɗan Hujri da Sahl ɗan Sa’ad - Allah


Ya yarda da su -.


7 Bukhari, Azan (657), Muslim al-Sallah (411), Tirmizi al-Sallah (361), Nasa’i Imamah


(832), Abu Dawud Sallah (601), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (1238),


Malik Annida’u Lissalah (306), Darimi al-Sallah (1256).


8 Muslim, Salatul Musafirin wa ƙasriha (771), Tirmizi al-Da’awat (3423), Abu Dawud


al-Sallah (760), Ahmad (1/103).


9 Muslim Sallah (477), Nasa’i Taɗbiƙ (1068), Abu Dawud Sallah (847), Ahmad (3/87),


Darimi Sallah (1313).


8


Sujjada da ɗagowa daga gareta da abinda ya


ƙunshi hakan


9. Yana yin sujjada tare da kabbara, yana sanya


gwiwowinsa kafin hannayansa, idan haka ya sawwaƙa


a gare shi, idan kuma yayi masa wahala sai ya fara


gabatar da hannayansa kafin gwiwowinsa, yana mai


fuskantar da yatsun kafafuwansa da hannayansa zuwa


alƙibla, yana mai haɗe yatsun hannuwansa yana miƙar


da su, kuma sujjudar ta kasance akan gaɓɓai bakwai:


Fuska tare da hanci, da hannuwa da gwiwowi, da cikin


yatsun ƙafafuwa, kuma ya ce:


Subhana Rabbiyal Aalah.   ) ( �ﻋﻷا �ر نﺎﺤ�ﺳ)


An sunnanta ya faɗi hakan sau uku ko sama da haka


, kuma an so ya faɗa tare da hakan: (Subhana


Kallahumma wabi hamdiKa, Allahumma ghfirli 10 . Ya


yawaita addu’a saboda faɗin Annabi - tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi -: (Amma a ruku’i to ku


girmama Ubangiji a cikinsa, Amma a Sujjada to ku yi


ƙoƙarin addu’a domin ya cancanci a amsa muku) 11 Ya


kuma roƙi Ubangijinsa na alhairan duniya da lahira,


hakan a sallar farilla ne ko sallar nafila, ya buɗa


damatsansa daga ɓarin jikinsa, cikinsa kuma daga


10 Bukhari, Azan (761), Muslim, Sallah (484), Nasa’i Taɗbiƙ (1122), Abu Dawud,


Sallah (877), Ibnu Majah Iƙamatus Salah Was Sunanu fiha (889), Ahmad (6/43).


11 Muslim (479), Nasa’i Taɗbiƙ (1120), Abu Dawud Sallah (876), Ahmad (1/219),


Darimi Assalah (1325).


9


cinyoyinsa, ya kuma raba cinyoyinsa da ƙwaurinsa, ya


ɗaga hannayansa daga barin ƙasa, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare - shi: (Ku


daidaita a sujjada, kada ɗayanku ya shinfiɗa hannuwa


irin shinfiɗawar kare) 12


Zama tsakanin sujjadu biyu da kaifiyyarsa


10. Yana ɗago kansa tare da kabbara, ya kuma


shinfiɗa diddigensa na hagu sai ya zauna a kansa, ya


kuma kafe ƙafarsa ta dama, ya ɗora hannayansa akan


cinyoyinsa da gwiwowinsa sai ya ce: (Ya Allah Ka


gafarta mini Ka ji ƙaina Ka shiryar da ni Ka azurtani Ka


tsare ni Ka agaza mini 13 Ya kuma natsu a wannan


zaman.


11. Yana yin sujjada ta biyu tare da kabbara, ya


kuma yi hakan kamar yadda yayi a sujjada ta farko.


12- Yana ɗago kansa tare da kabbara, sai ya zauna


zama ƙanƙani kamar yadda ya zauna tsakanin sujjada


biyu, ana kiransa da zaman hutu, wannan zaman


mustahabbi ne, idan ya bari babu wani laifi akansa,


babu wani zikiri ko wata addu’a a cikinsa, sannan ya


yunƙura ya tashi tsaye zuwa raka’a ta biyu yana mai


dogara akan gwiwowinsa idan hakan ya yiwu a gare


12 Bukhari Azan (788), Muslim Salah (493), Ahmad (3/192).


13 Tirmizi sallah (284), Abu Dawud Sallah (850), Ibnu Majah Iƙamatus Salah


Wassunnatu fiha (898).


10


shi, idan kuma yayi masa wahala ya dogara akan ƙasa,


sannan ya karanta Fatiha da abinda ya sawwaƙa a gare


shi na AlKur’ani bayan Fatihar, sannan ya yi kamar


yadda ya yi a raka’a ta farko.


Zama domin yin Tahiya a zama na biyu da


kaifiyyarsa


13. Idan sallar ta kasance mai raka’a biyu ce kamar


sallar Asuba da Juma’a da Idi biyu, to sai ya zauna


bayan ya ɗago kansa daga sujjada ta biyu yana mai


kafa ƙafarsa ta dama yana kuma shinfiɗa ƙafarsa ta


hagu, yana ɗora hannun sa na dama akan cinyarsa ta


dama, yana naɗe yatsunsu baki ɗaya sai manuniya, sai


ya yi nuni da ita akan Tauhidi, idan ya naɗe ƙaramin


yatsansa da wanda yake biye da shi na dama ya kuma


lanƙwasa babban yatsa da na tsakiya ya yi nuni da


manuniya (kaɗai) hakan ma ya yi kyau, saboda


tabbatuwar duka siffofin biyu daga Manzon Allah -


tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, abinda ya


fi shi ne ya yi wannan a wani lokaci kuma ya yi wancan,


sai ya dora hannun sa na hagu akan cinyarsa ta hagu


da gwiwarsa, sannan sai ya yi Tahiya a wannan zaman,


ita ce kuma: (Dukkanin gaisuwa kyawawa sun tabbata


ga Allah, da salloli da kyawawan (maganganu), aminci


ya tabbata a gareka ya kai wannan Annabi da rahamar


Allah da albarkarSa, aminci ya tabbata a garemu da


kuma bayin Allah salihai, ina shaidawa babu abin


11


bautawa da cancanta sai Allah kuma ina shaidawa


(Annabi) Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne.  


Sannan sai ya ce:


Ya Allah Ka yi salati ga (Annabi) Muhammad da


iyalan Muhammad kamar yadda Ka yi salati ga (annabi)


Ibrahim da iyalan Ibrahim, lalle Kai abin godewa ne


kuma mai girma. Ya Allah ka yi albarka ga (annabi)


Muhammad da iyalan Muhammad kamar yadda ka yi


albarka ga (annabi) Ibrahim da iyalan Ibrahim lalle Kai


abin godewa ne kuma Mai girma. 14 Kuma ya nemi


tsarin Allah akan abubuwa huɗu, sai ya ce: Ya Ubangiji


ina neman tsarinKa daga azabar Jahannama da azabar


ƙabari da fitinar rayuwa da ta mutuwa da fitinar


Masihul Dajjal (Jujal) 15 Sannan ya yi addu’a da abinda


ya ga dama na alhairan duniya da lahira, idan kuma ya


yi addu’a ga iyayansa ko wasu daga cikin musulmai


duka babu laifi, daidai ne hakan a sallar farilla ne ko


nafila, saboda gamewar faɗin Annabi - tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi - a cikin Hadisin ɗan Mas’ud


a lokacin daya koyar da shi Tahiya, sannan ya zaɓi


addu’ar da tafi ƙayatar da shi sai yayi addu'a da ita. A


wani lafazin kuma, sannan ya zaɓi abinda yake so ya


14 ( )Bukhari, Kiran sallah (797), Muslim Salah (402), Tirmizi Nikah (1105), Nasa’i


Sahwu (1298), Abu Dawud Sallah (968), Ibnu Majah, Iƙamatus Salah Wassunnantu fiha


(889), Ahmad (1/428), Darimi (1340).


15Bukhari Jana’iza (1311), Muslim Masajid wa mawadi’us Salah (588), Tirmizi


Da’awar (3604), Nasa’i Isti’aza (5513), Abu Dawud Salah (983), Ibnu Majah Iƙamatus


Salah Wassunnatu fiha (909), Ahmad (2/454), Darimi Salah (1344).


12


roƙa, wannan ya game duk abinda bawa yake so na


duniya da lahira, sannan yayi sallama a damar sa da


kuma hagunsa, ya ce: Assalamu alaikum wa


rahmatullah.  


Zama domin yin Tahiya a sallah mai raka’a biyu ko


huɗu da kaifiyyarsa


Idan sallar ta kasance mai raka’a uku ce, kamar


Magariba ko mai raka’a huɗu ce kamar Azahar da


La’asar da Issha, sai ya yi Tahiyar da aka ambata a


baya, tare da yin salati ga Annabi - tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi -, sannan sai ya yunƙura ya


tashi tsaye yana mai dogara a kan gwiwowinsa yana


ɗaga hannayansa daidai kafaɗunsa ko daidai


kunnuwansa yana cewa: Allahu Akbar, yana mai ɗora


hannayansa akan ƙirjinsa kamar yadda ya gabata, sai


ya karanta Fatiha kaɗai, idan ya karanta a raka’a ta uku


da ta huɗu a Azahar ƙari akan Fatihar a wasu lokutan


to babu laifi, saboda tabbatuwar abinda yake nuni


akan hakan daga annabi - tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi - cikin Hadisin Abu Sa’idu, sannan sai


ya yi Tahiya bayan raka’a ta uku a magariba, da kuma


bayan raka’a ta huɗu a Azahar da La’asar da isha


kamar yadda ya gabata a hakan a sallah mai raka’a


biyu, sannan ya yi sallama a damansa da kuma


hagunsa, ya kuma nemi gafarar Allah sau uku, sannan


ya ce: (Ya Allah Kai ne aminci, daga gareKa aminci yake


13


alherinKa ya yawaita ya Ma’abocin girma da karamci) 16


Kafin ya juya ya fuskanci mutane idan ya kasance liman


ne, sannan ya ce: (Babu abin bautawa da gaskiya sai


Allah Shi kaɗai Yake, ba Shi da abokin tarayya, kuma


Shi Mai iko ne akan dukkan komai. Ya Allah babu mai


hana abinda Ka bayar kuma babu mai bayar da abinda


Ka hana, wadatar mai wadata bata anfani a wurinKa,


babu ƙarfi kuma babu wata dabara sai da taimakon


Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, ba ma


bautawa kowa sai Shi, ni’ima ta sa ce da falala, da yabo


mai kyau, babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, muna


masu tsarkake addini gare Shi, ko da kafirai sun ƙi 17 , Sai


ya yi tasbihi: Subhanallah, talatin da uku, ya gode maSa


kwatankwacin


 hakan,


 yayi


 maSa


kabbara


kwatankwacin hakan a cikon na ɗarin sai yace: Babu


abin bautawa da gaskiya sai Allah ba Shi da bokin


tarayya, mulki naSa ne, kuma godiya taSa ce, kuma Shi


Mai iko ne akan dukkan komai.


Kuma ya karanta Ayatul Kursiyy, da Kulhuwa da


Falaƙi da Nas a bayan kowacce sallah, kuma an so a


maimaita waɗannan surorin uku, sau uku bayan sallar


Asuba da Magariba, saboda Hadisan da suka zo akan


16Muslim Masallatai da wuraran sallah(591), Tirmizi Sallah(300), Abu Dawud (1512),


Ibnu Majah Iƙamatus Salah Wassunnatu fiha (928), Ahmad (5/280), Darimi Sallah


(1348).


17 Bukhari, Kiran Sallah (808), Muslim, Msallatai da wuraran sallah(593), Nasa’i


Rafkannuwa (1341), Abu Dawud Sallah (1505), Ahmad (4/250), Darimi Sallah (1349).


14


haka daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi -.


Dukkanin waɗannan zikiran sunna ne ba wajibi ba


ne.


Kuma an shar’anta ga kowanne musulmi da


musulma yin sallah (nafila) kafin sallar Azahar raka’a


huɗu bayanta kuma raka’a biyu, da raka'a biyu bayan


Magariba, da raka'a biyu bayan sallar Issha, da raka'a


biyu kafin sallar Asuba, idan aka haɗa ya kama raka’a


goma sha biyu. Waɗannan raka’o'in ana kiransu da


Rawatib, domin Annabi - tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi - ya kasance yana kiyaye su a halin


zaman gida. Amma a halin tafiya ya kasance ba ya


yinsu saidai na kafin Asuba da Wuturi, domin tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi ya kasance yana


kiyaye su a halin zaman gida da kuma tafiya.


farilla18


 Abinda yafi a sallaci waɗannan nafilfilin da Wuturi a


gida, idan yayi su a masallaci babu wani laifi, saboda


faɗin Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare


shi -: “Mafificin sallar mutum a gidansa saidai (sallar)


Kiyaye waɗannan raka’oin yana cikin sabubban


shiga aljanna, saboda faɗin Annabi - tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi -: (Wanda ya yi sallah raka’a


18Bukhari, Ladubba (5762), Muslim, Salatul musafirin wa ƙasruha (781), Tirmizi


Sallah (450), Nasa’i tsayuwar dare da nafilar rana (1599), Abu Dawud Sallah (1447),


Ahmad (5/186), Malik, Kiran Sallah (293), Darimi Sallah (1366).


15


goma sha biyu a yini da dare domin neman lada, Allah


Zai gina masa gida a aljanna)19 . Muslim ne ya ruwaito


shi a Sahihinsa, idan ya yi raka’a huɗu kafin La’asar, da


raka’a biyu kafin Magariba, da raka’a biyu kafin Issha


to ya yi kyau, domin abinda yake nuni akan hakan ya


inganta daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata


a gare shi -.


Allah Shi ne Majiɓincin datarwa. Tsira da amincin


Allah su tabbata ga Annabimmu Muhammad ɗan


Abdullah da alayansa da sahabbansa da mabiyansa da


kyautatawa har zuwa ranar sakamako.


 19Muslim Salatul musafirin wa ƙasruha (728), Tirmizi Sallah (415), Nasa’i Kiyamul


Lail wa Taɗawwu’un Nahar (1801), Abu Dawud Sallah (1250), Ibnu Majah, Iƙamatus


Salah Wassunnatu fiha (1141), Ahmad (6/327).


16





Teburin bayani


Kyautata alwala ............................................................... 4


Fuskantar Alƙibla ............................................................. 4


Kabbarar harama, da ɗaga hannaye biyu a lokacin


kabbarar, da kuma ɗora hannayen biyu akan ƙirji. ........ 5


Addu'ar buɗe Salla .......................................................... 5


Ruku’i da tasowa daga ruku’in da kuma abinda ya


ƙunsa ............................................................................... 7


Sujjada da ɗagowa daga gareta da abinda ya ƙunshi


hakan .............................................................................. 9


Zama tsakanin sujjadu biyu da kaifiyyarsa.................... 10


Zama domin yin Tahiya a zama na biyu da kaifiyyarsa . 11


Zama domin yin Tahiya a sallah mai raka’a biyu ko


huɗu da kaifiyyarsa ....................................................... 13



 



Posts na kwanan nan

SIFFAR SALLAR ANNABI ...

SIFFAR SALLAR ANNABI – TSIRA DA AMINCIJ ALLAH

FAHIMTAR ADDINI (SHIN ...

FAHIMTAR ADDINI (SHINE) TSARI DAGA FITINTINU 2

FAHIMTAR ADDINI (SHIN ...

FAHIMTAR ADDINI (SHINE) TSARI DAGA FITINTINU 1

ABUBUWAN DA SUKE WARW ...

ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI.