Labarai
dubu hamsin ne.” (Suratul Ma’arij: 3-4). Da faixinsa, “Shin ko kun amince cewa wanda ke cikin sama, ba zai iya


shafe qasa tare da ku ba sai ga ta tana mai girgiza. Ko kun amince cewa wanda ke cikin sama ba zai iya sako muku


iskar guguwa ba? To za ku san yadda (aqibar) gargaxina take.” (Suratul Mulk: 16-17).


Har yau, akwai hadisai ingatattu waxanda suke bayyana cewa Allah yana sama, kuma ya daidaita a kan


Al’arshinsa. Kamar faxin Manzon Allah (SAW): “Shin ba za ku amince mini ba alhali ni ne amintaccen wanda yake


cikin sama? Labarin sama yana zuwa mini safe da yammaci.”1 Da faxinsa, “Lokacin da Allah ya qare halitta sai ya


rubuta a cikin littafinsa, littafin yana nan a wurinsa a kan Al’arshi: lalle rahamata ta rinjayi fushina.”2


A dalilin waxannan ayoyin da hadisai ne ya wajaba Musulmi ya qudure cewa Allah yana sama, amma ba tare


da qudure takamaimai yadda yake a sama xin ba, kuma ya qudure cewa Allah ya daidaita a bisa Al’arshiinsa,


daidaita wacce ta dace da xaukakarsa, wacce mu ba mu san haqiqaninta ko takamaimanta ba.


Maganganun Malamai


Qudure cewa Allah yana sama, kuma ya daidaita a kan Al’arshi daidaito wanda ya dace da shi, ita ce aqidar


magabatan al’umma: Sahabbai da Tabi’ai da Tabi’an Tabi’ai da limaman mazhabobi huxu da kuma sauran malamai


na Sunna. Babu xaya da ya yi savani a kan wannan.3 A nan, za mu kawo misalai na maganganun malamai dangane


da haka.


Maganar Imam Abu Hanifa


Imam Abu Hanifa ya ce, “Wanda ya ce: Ban sani ba, shin Ubangijina a sama yake ko a qasa, to kaqiqa ya


kafirta; domin Allah Maxaukaki yana cewa: “Mai rahama ya daidaita a kan Al’arshi.” Kuma Al’arshinsa a kan saman


bakwai yake. Idan kuma mutum ya ce: Yana kan Al’arshi amma ban sani ba Al’arshin a sama yake ko a qasa? To shi


ma kafiri ne; domin ya musa cewa yana sama. Kuma wanda ya musa cewa yana sama to lallai ya kafirta.”4


1 A duba Bukhari da Muslim.


2 Bukhari da Muslim sun fitar das hi.


3 Duba Minhajul Muslim na Abubakar Aljaza’iri, shafi na 21.


4 Duba Kitabul Arshi na Imam Alzahabi, shafi na 70-71.


Maganar Imam Malik


Imam Malik ya ce, “Allah yana sama kuma ilminsa yana ko ina.”1


Har yau, an tambaye shi dangane da faxin Allah Maxaukaki, “Mai rahama ya daidaita a kan Al’arshi.” Sai ya


ce, “Daidaito dai sananne ne, takamaimai (yaya ya daidaita) kuwa, wannan ba’a sani ba. Kuma imani da shi wajibi


ne.”


Watau yana nufin daidaito kowa ya san ma’anarsa. Amma idan a ka dangana shi ga Allah to babu wanda zai san


takamaimai ya ya daidaita; domin Allah shi kaxai ya san kansa a haqiqa.


Maganar Imam Shafi’i


Shi ma Imam Shafi’i an ruwaito yana cewa, “Lallai Allah Maxaukaki yana kan Al’arshinsa, a cikin


samaniyarsa. Yana kusantowa ga bayinsa yadda ya so. Kuma lallai Allah yana saukowa zuwa saman duniya yadda ya


so.”2


Maganar Imam Ahmad


An tambayi Ahmad binu Hanbal dangane da faxin Ubangiji Maxaukaki: “Shi ne wanda ya halitta sammai da


qasa a cikin wasu kwanuka shida, sa’an nan ya daidaitu a kan Al’arshi, yana sanin abinda ke shiga cikin qasa da


abinda ke fita daga gare ta, da abinda ke sauka daga sama da abinda ke hawa cikinta, kuma shi yana tare da ku, duk


inda kuka kasance. Kuma Allah mai gani ne ga abinda kuke aikatawa.” (Suratul Hadid: 4). Aka ce: Mene ne ake nufi


da: “kuma shi yana tare da ku”?


Da kuma faxinsa Maxaukaki, “Ashe, ba ka ga cewa lalle Allah yana sane da abinda yake a cikin sammai da


abinda ke cikin qasa ba? Wata ganawa ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah shi ne na huxu xinta, kuma babu


ta mutum biyar face shi ne na shida xinta, kuma babu abinda yake mafi yawa face shi yana tare da su duk inda suka


kasance, sa’an nan ya ba su labari game da abinda suka aikata a Ranar Qiyama. Lalle Allah Masani ne ga dukan


kome.” (Suratul Mujadala: 7). Suka ce: Me ake nufi da: “wata ganawa ta mutum uku ba za ta kasance ba face Allah


shi ne na huxu xinta”?


1 Kitabul Arshi na Imam Alzahabi, shafi na 71.


2 Kitabul Arshi, shafi na 89.


19


Sai Imam Ahmad ya ce, “Ilminsa ya kewaye da kome. Kuma Ubangijinmu yana kan A’arshi ba da takamaimai ba, ba


da sifantawa ba.”1


Maganar Shaihu Abdulqadir Jilani


Shaihu Abdulqadir ya ce, “Ya kamata a danganta sifar daidato (ga Allah) ba tare da tawili ba, kuma cewa


daidaitar zati ne (a haqiqa) a kan Al’arshi.”2


Maganar Ibnu Taimiya


Shaihul Islam Ibnu Taimiya ya ce, “Wanda duk ya ce Allah yana ko ina da zatinsa, to wannan ya savawa


Alqur’ani da Sunna da ijma’in magabatan al’umma da malamanta, tare kuma da savawa xabi’a wacce Allah ya


halicci bayinsa a kanta, da hankali bayyananne.”3


Maganar Mujaddadi Xanfodiyo


Shaihu Usmanu Xanfodiyo ya ce, “Babu aibu a ce Allah yana sama, domin da yawa hadisai sun yi nuni zuwa ga


haka, haka nan zahirin ayoyi. Sai dai aqida na vaci idan a ka qudure hakan ba tare da tsarkake Allah ga barin yin


kama da halitta ba, da kuma tabbatar da rashin sanin takamaimai.”4


Maganar Abu Zaid mai Risala


Abu Muhammad Abdullahi binu Abi Zaid Alqairawani, mai mashahurin littafin Fiqihun nan da ake cewa


Risala, ya rubuta littafi musamman domin bayanin aqidar Imam Malik. A cikinsa yana cewa, “Kuma shi (Ubangiji)


yana kan Al’arshinsa mai girma da zatinsa, kuma yana a ko ina da ilminsa.”5


1 A duba Kitabul Arshi na Zahabi, shafi na 97.


2 A duba littafin Alguniyya li Dalibi Darikil Haqqi na Shaihu Abdul Kadir Jilani, shafi na 55.


3 Duba Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiyya, mujalladi na 5 shafi na 230.


4 Duba Aljami’ul Hawi li Ghalibi ma fi Kutubis Shaihi Usman binu Foduye na Usman Almasini, shafi na 131.


5 A duba Aqidatul Imam Malik na Ibnu Abi Zaid Alqairawani, shafi na 28.


Maganar Shaihu Abubakar Gumi


Shaihu Abubakar Mahmud Gumi, da yake fassara faxin Ubangij,i “Mai rahama ya daidaita a kan Al’arshi.”


(Suratu X.H.: 5), ya yi qarin bayani kamar haka: “Allah ya daidaitu a kan Al’arshi daidaita wadda ta dace da shi.”1


Da waxannan maganganun malamai za mu tabbatar cewa aqida ingantacciya shi ne a qudure cewa Allah yana


sama, ya daidaita a kan Al’arshi daidaita wacce ta dace da girman zatinsa. Kuma wannan daidaita tasa ba ta yi kama


da daidaitar bayi ba, kamar yadda ba’a iya sanin takamaimai ya yake a saman, ko kuma ya ya daidaita. Domin Allah


bai yi bayanin takamaimai xin ba, kuma Annabinsa (SAW) bai yi bayaninta ba. Don haka ba’a iya sanin ta, kuma


babu laifi ga rashin sani xin.


Amma cewa Allah yana ko ina, to wannan vatacciyar aqida ce. Kai, tana ma kaiwa ga kafirci, kamar yadda


Imam Abu Hanifa da waninsa suka faxi.


1 A duba Alqur’ani Mai Girma da kuma Tarjaman Ma’anoninsa zuwa Harshen Hausa na Abubakar Mahmud Gumi, shafi na 467.


21


Babi na Uku


Shirka


A cikin wannan babi, za mu yi bayani a kan ma’anar shirka da asalinta. Haka kuma, za mu yi magana a kan haxarin


shirka da illolinta.


Ma’anar Shirka


Shirka, a Luga, ma’anarta tarayya ko haxaka.


A ilmance, ko a shar’ance, shirka tana nufin mutum ya haxa Ubangiji Maxaukaki da wani abokin tarayya a


cikin abinda yake haqqi ne na Allah da ya kevanta da shi, shi kaxai, kamar ya riqi wani abin bauta tare da Allah, ko


kuma koma bayan Allah, da zai riqa bauta masa, ko ya yi masa biyayya, ko ya nemi taimako daga gare shi, ko ya


kevance shi da soyayya, tsoro, fata, ko girmamawa, da sauran irin waxannan abubuwa waxanda babu wanda ya


cancanta a kevance shi da su sai Allah Maxaukaki, shi kaxai.


Abin bauta wanin Allah yana iya zama gunki ne da aka sassaqa daga itace ko aka gina da dutse; ko mutum, mai


rai ko matacce, kamar wani azzalumin sarki ko wani dujalin malami mai vatar da mutane; ko shaixani ko aljani


wanda ake iya gani a cikin wata siffa daga siffofi; ko dabba, kamar saniya da biri da sauransu; ko wata fikira ko wani


abin voye, kamar tsarin mulki na masu dimokraxiyya. Haka nan, son zuciyar mutum, idan ya sanya shi sama da


umarnin Allah da haninsa, yana iya zama abin bautarsa, kamar yadda Allah Maxaukaki yake cewa, “Shin, ka ga


wanda ya riqi Ubangijinsa son zuciyarsa? Shin to, kai ne ke kasancewa mai tsaro a kansa?” (Suratul Furqan: 43).


Asalin Shirka


Zurfafawa wajen qaunar bayin Allah na gari, kamr annabawa da waliyai, da wuce iyaka wajen girmama su da


kambama su shi ne ya zama asalin shirka a duniya.


A cikin Alqur’ani mai tsarki, Allah Maxaukaki ya ba mu labarin gumaka na farko da aka bautawa a duniya.


Ubangiji mai girma da xaukaka ya ce, “Kuma suka ce, faufau, kada ku bar gumakanku, kuma faufau, kada ku bar


Wadda kuma kada ku bar Suwa, kuma kada ku bar Yagusa da Ya’uqa da Nasra.” (Suratu Nuh: 23). Dangane da


bayanin ma’anar wannan aya, an ruwaito daga Sahabbai da yawa, cikinsu har da Abdullahi binu Abbas (R.A), cewa


waxannan sunaye biyar da aka ambata a cikin ayar, watau Wadda da Suwa da Yagusa da Ya’uqa da Nasra, a asali


sunayen wasu bayin Allah ne salihai daga mutanen Annabi Nuhu (AS). Lokacin da suka mutu sai Shaixan ya


qawatawa mutanensu da su riqa yin ibada a wurin da aka bunne su. Bayan waxannan sun shuxe kuma sai ya


qawatawa ‘ya’yansu da jikokinsu waxanda suka zo a bayansu da su gina mutum-mutumi ga ko wannensu, domin su


riqa tuna su da shi. Ya raya musu cewa yin haka zai sanya su riqa tunawa da su sosai, kuma su yi koyi da ayyukansu


kyawawa. Sa’an nan bayan waxannan kuma sun shuxe, sai ya umarci waxanda suka zo a bayansu da su bauta musu


koma bayan Allah. Ya raya musu cewa dama iyayensu da kakanninsu bauta musu suke yi. Wannan shi ne asalin


shirka.


Dangane da bayanin ma’anar wannan aya da muka kawo, Imam Bukhari ya ruwaito a cikin littafnsa da ake


cewa Sahihul Bukhari, daga Abdullahi binu Abbas (RA) ya ce, “Waxannan (sunaye) biyar sunayen wasu mazaje ne


salihai daga mutanen Nuhu. Yayin da suka mutu Shaixan ya yi wahayi ga mutanensu da su kafa gumaka a wuraren


da suka kasance suna zama, kuma su kira su da sunayensu. Sai suka aikata haka. Amma ba’a bauta musu ba sai


bayan da waxannan mutanen suka qare, kuma ilmi ya yi qaranci, sai aka bauta musu.”


Haka nan, Imam Suyuxi, ya ambata a cikin littafinsa mai suna Addurrul Manthur cewa, Abdu binu Humaidin


ya ruwaito daga Abu Muxahhir, ya ce: Wata rana mutane na zaune a wurin Abu Ja’afar Albaqir sai suka yi labarin


Yazid binu Muhallab, sai Abu Ja’afar ya ce, “Haqiqa wannan an kashe shi a qasar da aka fara bautawa wanin


Allah.” Sa’an nan sai ya ambaci Wadda, ya ce, “Wadda ya kasance mutum ne Musulmi, kuma mai farin jini a wajen


mutanensa. Lokacin da ya mutu sai suka yi cincirindo a kabarinsa, a can qasar Babila, suka yi matuqar juyayi. Da


Ibilis ya ga juyayinsu sai ya je musu a shigar mutane, ya ce da su: Na ga juyayinku bisa wannan (mamaci naku), ko


kuna so in suranta muku irin surarsa, ku ajiye ta a wurin taruwarku, ku riqa tuna shi da ita? Sai suka ce: E. Sai ya


suranta musu mai kama da shi, suka ajiye shi a wurin taruwarsu, suka yi ta tuna (Wadda) da ita wannan sura. Lokacin


da (Ibilis) ya ga halin da suke ciki na tuna wannan bawan Allah, sai ya ce da su: Ko kuna son in ginawa ko wane


xayanku mutum-mutumi mai kama da shi (Wadda) ku ajiye shi a gidajenku ku riqa tuna shi da shi? Sai suka ce: E.


Sai ya ginawa ko wane mutanen gida mutum-mutumi mai kama da shi. Su kuwa suka mai da hankali, suka yi ta tuna


shi. ‘Ya’yansu suka tashi suna ganin yadda suke girmama waxannan gumaka. Zamani ya shuxe, kuma batun cewa


ana tuna wani ne da wannan gunki ya wuce, har daga bisani suka riqe shi abin bautawa koma bayan Allah. Sai


Wadda ya zama farkon abinda aka bautawa koma bayan Allah a bayan qasa, watau gunkin da suka sa wa suna


Wadda.”


23


Waxannan ingantattun ruwayoyi guda biyu, musamman ta cikin Sahihul Bukhari, littafin da al’ummar Musulmi


suka haxu a kan cewa bayan Alqur’ani babu wani littafi da ya fi shi inganci, suna tabbatar da cewa wuce makaxi da


rawa wajen girmama waliyai da tsarkake su, da kuma zurfafawa a cikin son su da yabon su da kambama su,


waxannan al’amura su ne asalin abinda ya jefa mutane a shirka, ba’a wannan al’umma ba kawai, a’a har ma da


al’umman farko.1


Haxarin Shirka


Shirka tana da matuqar haxari ga mutum a duniyarsa da lahirarsa. Kai, a haqiqa ma, babu abinda ya fi shirka


haxari ga xan Adam, tunda tana gada masa rashin rabo da asara ta har abada. Haxarin shirka yana bayyana a cikin


waxannan abubuwa:


1. Shirka ita ce mafi girman zalunci, kamar yadda Allah ya bayyana da faxinsa, “Lalle Shirka wani zalunci ne mai


girma.” (Suratu Luqman: 13). Abinda ya sa ta zama haka, saboda ita zalunci ne ga Allah Maxaukaki. Wanda duk ya


bautawa wanin Allah, da ko wace irin nau’in ibada, to ya xauki haqqin Allah, wanda shi qaxai ya cancanta da shi, ya


bayar da shi ga wani wanda bai cancance shi ba. Sai ya zama ya zalunci Allah mai girma da xaukaka ta hanyar hana


masa haqqinsa. Kuma babu shakka cewa, mafi girman zalunci ba abinda ya dace da shi sai mafi girman uquba:


dauwama a wuta.


2. Allah ba ya gafartawa mai shirka, idan ya mutu bai tuba ba. Ubangiji ya ce, “Lalle ne Allah ba ya gafarta a yi


shirki da shi, kuma yana gafarta abinda yake bayan wannan ga wanda yake so.” (Suratun Nisa: 48).


3. Allah ya haramta aljanna a kan mai shirka kuma shi zai dauwama har abada a cikin wuta. Allah ya ce, “Lalle ne


shi, wanda ya yi shirki da Allah, to lalle ne, Allah ya haramta masa Aljanna. Kuma babu mataimaka ga azzalumai.”


(Suratul Ma’ida: 72).


4. Shirka tana rusa aikin bawa, kome kyawun aikainsa da yawansa ba zai amfane shi ba a lahira. Allah Mabuwayi ya


ce, “Kuma an yi wahayi zuwa gare ka (ya Muhammad) da kuma zuwa ga waxanda suke gabaninka (na annabawa):


Lalle idan ka yi shirki, haqiqa, aikinka zai vaci, kuma lalle za ka kasance daga masu hasara.” (Suratuz Zumar: 65).


A wata ayar kuma, Ubangiji yana fadi, bayan ya lisafa manya annabawa da manzonni, aiki har da Ibrahim Ishaq,


ya’aqub, Nuhu, Dawuda, Sulaiman, Ayyuba Yusuf Isa, Iiyas, Isma’ial, Aliyasa’u Yunus, Luxdu, bayan yaa lasafa


1 Duba littafinmu Matsayin Sufanci da Darika a Musulunci.


waxannan duka sai yace, “Kuma da sun yi shirki da haqiqa, abinda suka kasance suna aikatawa ya lalce”. (An’ami:


83-88). Babu shakka wannan yana nuna manamunin shirka da hadarinta.


5. Wani haxari kuma da ya shafi rayhwar duniya shi ne cewa ruco shirka jininsa halal ne. Allah makaxaici ya ce, to,


ku yaqi mushdrikai inda duk kuka same su, kuma ku kama su, kuma ku tsare su, kuma ku zaune musu sukkan


madakata”. (Suratut Taba: 5).


Illolin Shirka


Shirka tana da illoli masu yawa rayuwar al’ummai da xaixekun mutane. Ga wasu daga cikinsu.


1. Shirka qasqanci ne da wuwaqkanci ga bil Adama. Allah maxaukaki ya halici mutane ya girmama su, ya xaukaka


su, ya fifita su, akan yawancin halittarsa. Yace, “Kuma lalle ne mun girmama yan Adam, kuma muka dauke su a


cikin qasa da teku, kuma muka arzuta su daga abubuwa masu daxai, kuma muka fifita su akan masu yawa daga


waxanda muka halitta, fifitawa”. (Isra’: 70) saboda haka ba yan wannan girmamawa xa daukakawa da fifitawa, idan


xan Adam ya bautawa wata halitta wacce ba ta kai ya shi ba, kuma dabbobic ko duwatsu ko itace, to lalle wannan ba


qaramar wulaqantawa ba ce ga kansa. Dan Adam shi ne shugaban halitta a bayyan qasa, kuma shi aka horewa kome,


don haka bai kamata ya bautawa kowa ba sai Allah da ya halicce shi.


2. Shirka mafakar camfe-canfe ce da almarori. Mai shirka yana qudure cewa akwai wani mai iko ban da Allah. Yana


girmama, kuma yana tsoron abubuwa kamar gumaka, aljanu da sharidanu mamata da dodanni ya zama yana qarvar


duk wata baukaura da soko-burutsu camfe-camfe da almarori tsibbu da surklle, kuma yana gaskata maganganun


bokaye, yau duba, masu bugun qasa da miyagun malamai.


3. Shirka tana kawo tsoro da damuwa masu hana zuciya nashaxi: Domin mutumin da yake qarvar camfe-camfe da


almanri kuma yana gaskata qaryace-qaryacen maqaryata, to zuciyarsa za ta ciki da tsoro na ba gaira basabab saboda


ya dogara da iyayen gijin qarya wadanda ba sa iya amfanar sansu ko su ijewa kansu sharri, balle su yiwa wani. Allah


maxaukaki yana cewa, “zamu jefa tsoro a cikin zukatan waxanda suka kafirta, saboda shirkin da suke yi da Allah


game da abinda bai saukar da wani dalili ba game da shi”. (Suratu Ali Imraha: 151).


4. Shirka tana hana shagata da aiki na gari. Domin tana koyawa masu yin ta su sogara ga cefon masu ceto, da girman


masu girma da alfarmar masu alfarma. Sai ka ji suna cewa da wani bawa, annabi ko waliyi ko shaihi, ya tuna da su


ranar shiga jirginsa!


25


Ko kuma wai suna cikin aljihunsa. Allah manzon (SAW) yana faxawa xiyarsa, “Ya ke Faxina xiyar Muhammad, ki


tambaye ni cikin dukiyata abinda kike so, ban amfana miki kome ga barin Allah.”1


5. Shirka tana raba kan al’umma. Shirka bantawa iyayen giji dabam-daban ne, da son su, da jin tsoron su, da


girmamam su. Sai ya zama zukakan al’umma sun rarraba, kowa zuciyarsa na tare da abin bautarsa. Wannan kuwa shi


ne babban dalilin rarrabuwar kawuna, domin haxuwa akan aqida guda shi ne haxin kai na gaskiya, ba haxa baki ba


na munafinci. Don haka Allah mabuwayi yake yi mana wannan gargaxi: “Kuma kada ku kasance daga mushirika


watau waxanda suka rarraba addininsu kuma suka kasance qungiya-qungiya, kowace qungiya tana mai farin cikin da


abinda ke a gare ta”. (Suratur Rum: 31-32)


1 A duba Sahihul Bukhari.


Babi Na Huxu


Rabe-Raben Shirka


A cikin wannan babi, za mu yi bayani a kan rabe-raben shirka zuwa shirka voyayya da bayyananna, da kuma shirka


babba da qarama. Sa’an nan za mu kawo bayani filla-filla dangane da rabe-raben shirka qarama, tare da ambaton


hujjoji masu qarfi daga Littafin Allah da Sunnar Manzon Allah (SAW).


Shirka Babba da Shirka Qarama


Shirka ta kasu gida biyu: shirka babba da shirka qarama. Shirka babba, ko kuma Alshirkul Akbar, ita ce wacce


Allah ba ya gafarta ta, kuma mai yin ta ba ya shiga aljanna har abada, sai fa idan ya tuba tuba ingantacce. Ubangiji


mai girma da xaukaka yana cewa, “Lallai ne Allah ba ya gafarta a yi shirka gami da shi, kuma amma yana gafarta


abinda yake bayan wannan ga wanda yake so, kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, lalle ne, ya qirqiri zunubi mai


girma.” (Suratun Nisa’i: 48). A wata ayar kuma ya ce, “Lalle ne Allah ba ya gafarta a yi shirka da shi, kuma yana


gafarta abinda yake bayan wannan ga wanda yake so. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ya vace vata mai


nisa.” (Suratun Nisa’i: 116).


Shirka qarama kuwa, wacce ake kira Alshirkul Asgar, tana daga cikin manyan zunubai, watau kaba’ira,


waxanda duk mai yin su, kuma ya nace a kan aikata su, to ana jiye masa tsoron ya mutu kafiri, idan ba Allah ne ya yi


masa gyaxar dogo ba, ya riske shi da rahama tasa, ya arzuta shi da tuba kafin zuwan ajalinsa. Za mu zo da qarin


bayani dangane da shirka qarama a nan gaba kaxan, in Allah ya yarda.


Shirka Bayyananna da Shirka Voyayya


Shirka babba ta kasu zuwa shirka bayyananna, Alshirkul Jaliyyu, da shirka voyayya, Alshirkul Khafiyyu.


Shirka babba bayyananna ita ce bauta wa wani abu dabam tare da Allah Maxaukaki. Shi wannan abin bautawar da


aka haxa da Allah ya zama tauraro ne kamar wata da rana, ko wani sandararren abu ne kamar gunki na itace da


duwatsu, ko kuwa wata dabba ce kamar saniya da maciji, ko kuwa mutum ne kamar waxanda suka bauta wa Fir’auna


da Buda da Shaihunnai da sauransu, ko waxanda suka bauta wa Annabi Isa xan Maryamu (AS), ko kuwa wata halitta


ce da ba’a iya gani kamar aljannu da shaixanu da mala’iku, duka wannan xaya ne. Ko wanne daga waxan nan aka


bauta wa, an aikata shirka babba bayyananna.


27


Ita kuwa shirka babba voyayya ta haxa da girmama qaburbura da kusheyi, da roqon mamata, da neman


taimakonsu, da bixar biyan bukata daga gare su, kamar warkar da cuta, ko yaye qunci, ko rinjaye bisa abokan gaba,


da sauran irin waxan nan abubuwa waxanda babu mai iko a kansu sai Allah Maxaukaki, shi kaxai.


Har ila yau, shirka babba bayyananna ta qunshi riqar wanin Allah a matsayin mai ba da doka, ko mai ba da


shari’a, kamar misali a baiwa wani mutum ko wasu gungun mutane haqqin sanya shari’a da kafa dokoki waxanda


suka savawa dokokin Allah da hukuncinsa, kamar yadda abin yake a cikin tsarin Dimokraxiyya wanda muke


aiwatarwa a yau – Dimokraxiyya shu’uma, azzaluma, jahila, wacce take buxewa shuwagabanni marasa amana kafar


satar dukiyar jama’a, su bar su ba ko qarfanfana!


Wanda duk ya baiwa wani mutum, ko wasu gungun mutane, haqqin kafa masa doka ko sanya masa shari’a


wacce ta sava da shari’ar Allah, to haqiqa ya riqi wannan mutum, ko mutane, a matsayin ababen bauta. Wannan ya


sa Alqur’ani ya kira Yahudu da Kirista da sunan mushirikai, ya ce sun riqi malamansu da shugabanninsu a matsayin


iyayengiji ababen bauta saboda sun bi son zukatansu, sun karvi tsarin da suka shimfixa musu.


A cikin Suratut Tauba, Allah yana cewa, “Sun riqi malamansu (watau Yahudawa) da Ruhubanansu (watau


Kirista) ubangiji baicin Allah, kuma sun riqi Masihu xan Maryama (haka). Kuma ba’a umarce su ba face su bauta wa


Ubangiji guda. Babu abin bautawa face shi. Tsarkinsa ya tabbata daga barin abinda suke yin shirka da shi.” (Suratut


Tauba: 31). Wannan aya Annabi (SAW) ya fassara ta ga Adiyyu binu Hatin Axxa’i (RA) wanda a zamanin jahiliyya


Kirista ne kuma ya musulunta. Lokacin da ya zo wurin Annabi (SAW) ya karanta masa wannan aya sai ya ce: Ya


Ma’aikin Allah, ai ba bauta musu suke yi ba. Sai Annabi (SAW) ya ce, “Ai lallai. Haqiqa su sun haramta musu halal


kuma sun halatta musu haram amma suka yi musu biyayya. To wannan it ace bautar da suka yi musu.” (Ahmad da


Tirmizi).


Wannan aya da kuma hadisin Annabi (SAW) wanda ya fassara ta suna tabbatar da cewa, wanda duk ya yi


biyayya ga wanin Allah a cikin abinda ya savawa shari’ar Allah, ko abinda Allah bai yi izini da shi ba, to haqiqa


wannan ya riqe shi abin bauta kuma ya yi shirka da shi, ko da bai kira shi da sunan ubangiji ba. Don haka a wata ayar


yake cewa, “Kada ku ci daga abinda ba’a ambaci sunan Allah ba a kansa (yayin yankansa). Kuma lalle ne shi


fasiqanci ne. Kuma lalle ne, shaixanu, haqiqa, suna yin ishara zuwa ga masoyansu, domin su yi jayayya da ku. Kuma


idan kuka yi musu xa’a lalle ne ku, haqiqa, masu shirka ne.” (Suratul An’am: 121). Wannan yana nuna cewa, yin


xa’a ga Shaixan da baraden Shaixan, cikin abinda ya savawa Allah, shirka ne.


Nau’o’in Shirka Qarama


Shirka qarama, kamar yadda muka ambata a baya, tana cikin jerin kaba’ira, koda yake ta fi sauran manyan


zunubai girma. A qarqashin shirka qarama akwai abubuwa guda goma:


1. Rantsuwa da wanin Allah, kamar mutum ya rantse da Annabi (SAW) ko da xakin Ka’aba, ko da aradu, da


sauransu. Manzo (SAW) ya ce, “Wanda ya rantse da wanin Allah haqiqa ya kafirta, ko (a wata ruwayar ya ce) ya yi


shirka.”1


Abdullahi binu Mas’ud ya ce, “In rantse da Allah a kan qarya ya fi soyuwa a gare ni da in rantse da wanin Allah


a kan gaskiya.” Wannan magana ta wannan babban Sahabi tana nuna girman haxarin rantsuwa da wanin Allah, tunda


har ya gwammace ya rantse da Allah a kan qarya da ya rantse da waninsa koda gaskiya yake yi. Dalili saboda qarya


kaba’ira ce, rantsuwa da wanin Allah kuwa shirka ce. Shirka kuwa ta fi kaba’ira haxari nesa ba kusa ba!


2. Xaura guru da kambu da rataya zare a wuya. An ruwaito daga Imran binu Husain (RA) ya ce: Annabi (SAW) ya ga


kambu a damtsen wani mutum, sai ya ce, “Mene ne wannan?” Sai mutumin ya ce: Maganin (cutar) wahina ne. Sai


Annabi (SAW) ya ce, “Cire shi, haqiqa babu abinda zai qara maka sai cuta. Kuma da za ka mutu da shi a jikinka, da


ba za ka rabauta ba har abada.”2


Haka nan an ruwaito cewa Sahabin Annabi (SAW), Huzaifa binul Yaman (RA), ya shiga ya duba wani mara


lafiya sai ya ga wani xan zare rataye a wuyansa, wai yana maganin zazzavi da shi. Sai ya tsinke zaren ya jefar, sa’an


nan ya karanta wannan aya: “Kuma mafi yawansu ba su yin imani da Allah face kuma suna masu shirka.” (Suratu


Yusuf: 106).


3. Rataya Laya. Ahmad binu Hanbal ya ruwaito daga Uquba binu Amir (RA) cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce,


“Wanda ya rataya laya kada Allah ya cika masa.” A wata ruwayar kuma ya ce, “Wanda ya rataya laya haqiqa ya yi


shirka.”


4. Tofi. Shi tofi ya kasu gida biyu. Akwai tofi na shirka shi ne wanda ake yi da sunan wanin Allah, ko kuma da wani


harshe ba harshen Larabci ba wanda kuma ba’a san ma’anarsa ba. Wannan shi ake cewa surkulle. Kuma akwai tofi na


Sunna wanda ake yi da sunayen Allah, ko sifofinsa, ko da ayoyin Qur’ani.


1 Tirmizi ya ruwaito shi kuma y ace hadisi ne mai kyau.


2 Ahmad da Ibnu Maja ne suka ruwaito shi.


29


An karvo ruwaya daga Aufu binu Malik (RA) ya ce: Mun kasance muna yin tofi a (zamanin) jahiliyya. Sai


muka ce da Annabi (SAW): Ya kake gani dangane da haka? Sai ya ce, “Ku bijiro min da abinda kuke tofawa (in


jiya). Babu laifi ga tofi matuqar ba shirka ba ne.”1


5. Tsafi ko sihiri. Shi tsafi nau’i ne na rufa-ido da ba-duhu, kuma ya qunshi rantse-rantse da surkulle da qulle-qulle


da tofin shirka. Tsafi ya zama shirka saboda a cikinsa akwai neman taimako da wanin Allah, kamar ibilisai da aljannu


da rauhanai da taurari da sauransu.


Sihiri yana daga cikin manyan zunubai waxanda suke tavar da mai aikata su. Ubangiji Maxaukaki yana cewa,


“Kuma masihirci ba ya cin nasara duk inda ya je.” (Suratu X.H.: 69). A wata ayar kuma ya ce, “Abinda kuka zo da


shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai vata shi. Haqiqa Allah ba ya vata aikin mavarnata.” (Suratu Yunus: 81).


Bukhari ya ruwaito daga Bujalah binu Abduh (RA) ya ce, “Umar binul Khaxxabi ya rubuto mana (umarni)


cewa, mu kashe dukkan matsafi da matsafiya. Sai muka kashe wasu matsafa guda uku.” Kuma kamar yadda tsafi


yake haramun haka nan zuwa wajen matsafi da gaskata shi. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Mutane uku ba su shiga


aljanna: mai dimantar giya, da mai gaskata tsafi, da mai yanke zumunci.”2


6. Ba da labari da taurari. Wannan wani launi ne na tsafi kuma masu yin sa suna riya cewa suna sanin abinda zai faru


nan gaba ta hanyar ilmin taurari. Annabi (SAW) ya ce, “Wanda ya xarshi wani yanki na taurari haqiqa ya xarshi


wani yanki na tsafi.” (Abu Dawud). Amma fa wannan bai haxa da ilmin Falaki ba wanda ya qunshi darasun taurari


da gurabunsu da girman jikinsu (faxi da tsawo) da hanyoyinsu da nisan tsakaninsu da juna. Wannan ilmi ne na


kimiyya mai zaman kansa wanda aka gina shi a kan darasu da tsokaci da lura ta yau da kullum.


7. Bokanci da duba. Boka shi ne mutumin da yake da’awar sanin abinda yake qunshe a cikin gaibu daga abubuwan


da za su faru a nan gaba, ko kuma abubuwan da suke voye cikin zukatan mutane. Shi kuwa duba ya haxa da bokanci


da bugun qasa da duban taurari, da sauransu. Muslim ya ruwaito a cikin Sahihinsa cewa, Manzon Allah (SAW) ya ce,


“Wanda ya je ga xan duba ya tambaye shi wani abu, kuma ya gaskata shi (a kan abinda ya faxi), to ba’a karvar


sallarsa ta kwana arba’in.” Haka kuma Abu Dawud ya ruwaito cewa, Ma’aikin Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya je


wurin boka kuma ya gaskata shi a kan abinda yake faxi, to haqiqa ya kafirta da abinda aka saukarwa Muhammad


(SAW).”


8. Cin alwashi ga wanin Allah, kamar mutum ya yi alwashi ga qaburbura, ko mutanen dake bunne a cikinsu, ko wani


shaihi ko waliyyi, mai rai ko mamaci. Yadda ake cin alwashi shi ne mutum ya ce: Idan bukatata kaza ta biya, to zan


1 Muslim ya fitar da shi.


2 Ahmad da Ibnu Hibban suka ruwaito shi.


yi aikin ibada kaza, ko zan bayar da sadakar kaza. Misali mara lafiya ya ce: Idan na warke zan yi azumi kaza, ko


mace mai ciki ta ce idan ta haihu lafiya za ta sadaukar da kaza.


Cin alwashi ibada ne; don haka yin sa ga wanin Allah ya zama shirka, saboda ibada ba ya halatta a gabatar da


ita sai ga Allah Maxaukaki, shi kaxai. Ubangiji mai girma da xaukaka ya ce, “Kuma abinda kuka ciyar daga ciyarwa,


ko kuka cika alwashi daga wani bakance, to, lalle ne, Allah yana sanin sa. Kuma azzalumai ba su da wasu


mataimaka.” (Suratul Baqara: 270). Malaman Tafsiri sun ambata cewa, azzalumai da aka ambata a cikin ayar abinda


ake nufi da su masu shirka, saboda Allah yana faxi a cikin wata ayar, “Lalle shirka wani zalunci ne mai girma.”


(Suratu Luqman: 13). Wanda duk ya yi alwashi ga wanin Allah, to haqiqa ya yi shirka da Allah, kuma ya zama


azzalumi.


9. Yanka ga wanin Allah, kamar a ce za’a warkar da wata cuta amma sai an zubar da jinin dabba mai kama kaza, ko


kaza mai launi iri kaza, da sauran irin waxan nan abubuwa. Yana daga cikin wannan kuma yanke kawunan mutane


ko wasu gavovin jikinsu da nufin cimma wata biyan bukata.


Allah ya haramta cin duk abinda aka ambaci sunan wanin Allah a yayin yankansa, da abinda aka yanka a kan


dandamalin gumaka (Suratul Ma’ida: 3), ko a kan wni dutse ko a gindin wata itaciya, da sauransu. Kuma ya yi


umarni dukkan yanka ya zama an yi dominsa, da sunansa. Allah Maxaukaki ya ce, “Saboda haka, ka yi sallah domin


Ubangijinka, kuma ka soke (baiko, watau sukar raqumi wanda shi ne a matsayin yankansa).” (Suratul Kausar: 2).


Kuma ya ce, “Ka ce: Lalle ne sallata, da baikona, da rayuwata da mutuwata na Allah ne Ubangijin talikai. Babu


abokin tarayya a gare shi. Kuma da wancan aka umarce ni, kuma ni ne farkon masu sallamawa.” (Suratul An’am:


161-162).


An karvo ruwaya daga Ali binu Abi Xalib (RA) ya ce: Annabi (SAW) ya yi mini zance da kalmomi huxu. Ya


ce, “Allah ya la’anci wanda ya yi yanka ga wanin Allah. Allah ya la’anci wanda ya voye mai laifi. Allah ya la’anci


wanda ya sauya alamar qasa.” (Muslim). Ya voye mai laifi, watau ya rufa masa asiri, ko ya taimake shi ta ko wace


hanya. Ya sauya alamar qasa, watau ya gusar da alamar kan iyaka don ya shigo da haqqin wani cikin mulkinsa.


10. Camfi. Shi ma camfi nau’i ne na shirka. Idan mutum ya yi wani abu, ko ya bar yin wani abu, saboda camfi to


haqiqa ya yi shirka; saboda bai kyautata dogaro ga Allah ba. Imam Ahmad ya ruwaito cewa, Manzon Allah (SAW)


ya ce, “Wanda camfi ya hana shi (aikata) wata bukata tasa, to haqiqa ya yi shirka.” Sai aka tambayi Annabi (SAW):


To mene ne kaffarar yin haka? Sai ya ce, “Kaffararsa (shi ne) mutum ya ce: Ya Ubangiji babu alheri sai alherinka,


kuma babu camfi sai qaddararka, kuma babu abin bautawa waninka.”


31


Amma wannan bai haxa da abinda Bahaushe yake cewa “Ina ji a jikina” ba ko “Jikina yana ba ni.” Idan mutum


ya ji xar-xar a kan wani abu da ya yi niyyar aikatawa, kamar misalai zai yi tafiya sai ya riqa jin kamar zai yi hatsari a


wannan tafiyar, to wannan ba ya shafar imanin mutum matuqar dai bai hana shi abinda ya yi nufin yi ba. Wannan


yana daga cikin raunin xan Adam, kuma tawakkali shi ne maganinsa.


Abu Dawud da Tirmizi sun ruwaito daga Abdullahi binu Abbas (RA) cewa, Annabi (SAW) ya ce, “Camfi


shirka ne, camfi shirka ne. Kuma babu wani daga cikinmu face…sai dai Allah yana tafiyar da wannan da tawakkali.”


Ma’anar faxinsa “babu wani daga cinmu face…” watau babu wani daga cikinmu ‘yan Adam face ya ji xar-xar a wani


lokaci na rayuwarsa. To sai dai maganin wannan ga Musulmi, kamar yadda hadisin ya bayyana, shi ne tawakkali.


Idan mutum ya rabu da wannan abu da yake ji a jikinsa, ya dogara ga Allah, sai Allah ya fitar da shi daga zuciyarsa.


“Kuma wanda ya dogara ga Allah, to, Allah ne ma’ishinsa.” (Suratux Xalaq: 3).


Kishiyar camfi shi ne fata na gari, kamar mutum ya sa rai da gamuwa da wani alheri saboda wata magana mai


daxi da ya ji, ko wani abu mai kyau da ya gani. Misali mutum yana bukatar riga sai ya ji an kira wani sunansa


Mairiga, ko yana bukatar kuxi sai ya ji an kira Malam Maikuxi, sai ya yi fatan samun riga ko kuxi, wannan babu


laifi. Hasali ma Annabi (SAW) ya kasance yana son irin haka. Bambancinsu da camfi shi ne, fata na gari yana sa


kyakkyawan fata daga Allah da kyautata zato da shi. Camfi kuwa yana kai mutum ga muzanta zato ga Allah da


tsoron wani abu da bai da tasiri, ba gaira ba dalili.


Waxan nan su ne abubuwan da suke qarqashin shirka qarama, mun kawo su filla-filla saboda girman haxarinsu,


da kuma matuqar yaxuwarsu a tsakanin mutane, da illarsu ga imanin Musulmi. Imani shi ne tushen kome a


Musulunci, saboda haka duk abinda zai tava shi, to dole ne a fahimce shi da kyau kuma a kauce masa. Allah ya tsare


mana imaninmu, amin.


Babi Na Biyar


Shirkokin Zamani da Zindiqanci


A cikin wannan babi, za mu tavo batun wasu nau’o’in shirka waxanda suka shigo mana sakamakon dangantakarmu


da kafirai Turawan mulkin mallaka. Waxan nan shirkoki an shigo da su cikin rayuwarmu a lokacin da muke


qarqashin danniya da mulkin zalunci na Turawa, kuma a bayan samun ‘yancin kanmu, rabuwa da su ya yi mana


wuya. Hakan kuwa ya faru saboda nacewa a kan ci gaba da aiki da su da almajiran Turawa suke yi, watau ‘yan Boko,


waxanda jahiltar addininsu da tarihinsu ya sa suke zaton aiki da al’adun Turawa wata larura ce, ko burgewa.


Shirkokin Dimokraxiyya


A qarqashin tsarin Dimokraxiyya akwai nau’o’i na shirka waxanda Musulmi suke quduri da su, ko suke


aikatawa, a bisa rashin sani. Za mu karkasa su domin sauqin fahimta kamar haka:


1. Shirka a tushen Dimokraxiyya. An gina tsarin Dimokraxiyya a kan tushe na shirka wanda yake cewa jama’ar qasa


su ne masu mulki da iko (soverienty) kuma mahukunta da shugabannin siyasa suna mulki ne a madadinsu.


Wannan quduri ya zama shirka saboda, a tsarin Musulunci, Allah shi kaxai shi ne mai mulki. Ubangiji


Maxaukaki yana cewa, “Ka ce: Ya Allah Mamallakin mulki, kana bayar da mulki ga wanda kake so.” (Suratu Aali


Imrana: 26). A wata ayar yana cewa, “Ya halitta ku daga rai guda, sa’an nan ya sanya ma’aurata daga gare shi. Kuma


ya saukar muku daga dabbobin gida nau’i takwas, yana halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bayan halitta,


a cikin duffai uku. Wannan shi ne Allah Ubangijinku. Mulki a gare shi yake. To, yaya ake karkatar da ku?” (Suratuz


Zumar: 6). Har yau, a wata ayar yana cewa, “Yana shigar da dare a cikin rana, kuma yana shigar da rana a cikin dare.


Kuma ya hore rana da wata kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Wannan shi ne Allah, Ubangijinku,


gare shi mulki yake, kuma waxanda kuke kira, waninsa, ba su mallakar ko fatar gurtsun dabino.” (Suratu Faxir: 13).


Saboda haka, a tsarin Musulunci, duk mai yin mulki a madadin Allah yake yi, shi ya sa ya zama wajibi mulkin


ya zama gwargwadon umarninsa da haninsa. Idan aka qudure cewa mutane su ne mamallaka (soverien), to an samu


masu mulki biyu ke nan: Allah da mutane. Wannan kuma shi ne ainihin shirka. Allah maxaukaki yana cewa, “Kuma


ka ce: Godiya ta tabbata ga Allah wanda bai riqi xa ba, kuma abokin tarayya bai kasance a gare shi ba a cikin


mulkinsa.” (Suratul Isra: 111).


33


Amma Dimokraxiyya da ma’anar mulkin wakilci da tuntuvar juna, to wannan babu illa a cikinsa, matuqar an


guje wa qudure-qudure da muka ambata a sama. Wannan ma yana iya zuwa qarqashin tsarin Shura, wanda


Musulunci yake koyar da shi.


2.Tsarin Mulki. Amincewa da cewa kundin tsarin mulki yana gaba da dukkan shari’o’in qasa da dokokinta, kuma duk


dokar da ta sava masa shafaffiya ce, shi ma wannan shirka ce domin, da farko, yana aza tsarin mulki sama da


Alqur’ani mai girma, na biyu kuma yana baiwa mutanen da suka rubuta tsarin mulkin haqqin shar’antawa bayin


Allah wata shari’a wacce ta savawa shari’ar Allah domin su bi. Babu wani mai haqqin shar’antawa bayi shari’a


su bi sai Mahaliccin bayi, shi kaxai. Wanda duk ya baiwa wani wannan haqqin, to ya yi shirka da shi.


Amma babu laifi mutane, Musulmi da waxanda ba Musulmi ba, su haxu a kan wasu sharuxxa da yarjejeniyoyi,


rubutattu ko ba rubutattu ba, waxanda za su rayu a kansu, kamar yadda ya faru tsakanin Manzon Allah (SAW) da


al’umman Yahudawa da wasunsu a farkon hijirar Annabi (SAW) zuwa Madina. Amma kada Musulmi ya yarda cewa


waxan nan sharuxxa da yarjejeniyoyi suna sama da dukkan shari’a da doka. Wannan shi ne haxarin da ya wajaba


Musulmi ya gujewa.


3.Zandaqa. Na kawo zandaqa a qarqashin shirkokin zamani saboda mu a ‘yan shekarun nan ne zandaqar ta shigo


mana. Amma a haqiqa zandaqa ta daxe a duniyar Musulmi, ana yaqar al’umma da ita qarqashin sunaye badamdaban.


Daga cikin waxan nan sunaye akwai sunan Sufanci wanda mu ma da shi ne ta shigo mana.


Zandaqa tana xaukar salo da yawa, amma mafi haxari wanda kuma shi ne muke fama da shi a nan qasar, shi ne


ALLANTAR da wasu mutane waxanda ake zaton bayin Allah ne na qwarai. Sai a ba su sifofin Ubangiji, ko ma a


kira su da sunan ALLAH, kamar yadda muke ji a bakin wasu vatattu masu fakewa da son Annabi (SAW) da son


waliyyai, daga qarshe sai su xaura yaqi da Allah da Manzonsa da muminai.


Waxan nan mutane a kwanan nan al’amarinsu ya yi qarfi, inda har suke fitowa suna furta kalmomin ridda a fili,


kamar yadda wani vatacce da ake kira Abdul Inyas ya yi a Kano.1


Ilhadi aqida ce da maqiyan Musulunci suke qoqarin yaxa ta a tsakanin Musulmi ta hanyoyi dabam-daban, tare


da amfani da dukiya da maqaman duniya, da sauransu. A kwanan nan mun samu labara cewa, banda amfani da


xariqun Sufaye wajen yaxa wannan aqida, ana kuma jan samari da ‘yan mata masu qarancin sani da tarbiyya, zuwa


1 Duba littafi na 6 a Jerin Littafan Sufanci mai taken Tushen Tabargaza a Tafarkin Sufanci.


ga qudure wannan aqida. Gungun matasa da suka sako a gaba su ne masu shirya fina-finan Hausa, waxanda ake


amfani da jahilcinsu da rashin tarbiyyar iyayensu, ana sanya su cikin aqidar Bautar Shaixan wacce suke kira da


Turanci: ILLUMINATI.


Wajibi ne mutane su ilmantu, su faxaku, su waye, domin kaucewa irin wannan makirci da maqiyanmu suke


kitsa mana don raba mu da addininmu. Kuma wajibi ne a yi wa matasa kan-da-garki, domin yawanci su ake nufi da


wannan makircin.


Allah ya isar mana.


Tsarki ya tabbatar maka, ya Ubangiji, tare da godiya a gare ka. Ina shaidawa babu abin baitawa da gaskiya sai


kai. Ina neman gafararka, ina tuba zuwa gare ka.Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC