Labarai




FAHIMTAR ADDINI


(SHINE) TSARI DAGA FITINTINU





WALLAFAR BABBAN MALAMI


DR. SALEH BN FAUZAN BN ABDALLAH AL-FAUZAN





FASSARAR


JUNAIDU ISA IBRAHIM





WANDA YAYI BITA


ISMA’IL GARBA ALIYU





WAKAFINE SABODA ALLAH





BUGU NA HUDU


2010 M /1421 AH





ATARE DASHI AKWAI





TA’ALIKIN


BABBAN MALAMI


SHEIKH ABDUL’AZIZ BN ABDALLAH BN BAZ


AKAN LACCAR








AKWAI TAMBAYOYI DA AKAYIWA BABBAN MALAMIN





SANNAN TATTAUNAWA TARE DA


BABBAN MALAMI


SHEIKH ABDUL’AZIZ BN BAAZ





KAN ABINDA YA SHAFI (FAHIMTAR ADDINI SHINE TSARI DAGA FITINTINU)





DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI





LACCA MAI TAKEN





FAHIMTAR ADDINI (SHINE)  TSARI DAGA FITINTINU


NA BABBAN MALAMI


SHEIKH SALEH BN FAUZAN BN ABDALLAH AL-FAUZAN


     Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijn talikai, tsira da aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad, wanda aka aikoshi rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa, da wanda yayi riko da sunnarsa kuma yayi tafiya akan hanyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan haka:


Lallai Allah – Mai girma da daukaka – Yayi mana baiwa da Musulunci, Allah – Madaukakin sarki - Ya ce: {Yaku wadanda sukayi imani kuyi takawa ga Allah hakikanin takawa, kuma lallai ne kada ku mutu sai alhali ku kuna musulmai. Kuyi riko da igiyar Allah gaba daya, kada ku rarraba, kuma ku tuna da ni’imar da Allah Yayi muku yayin da kuka kasance abokan gaban juna, sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku, saboda haka kuka wayi gari ‘yan uwan juna a sakamakon ni’imarSa, a da kuma kun kasance akan gabar ramin wuta, sai Ya tsamoku daga gareta, kamar haka ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku zaku shiriya. A cikinku a sami wata al’umma wadanda suke kira zuwa ga alheri, kuma suke umarni da kyakkyawa, kuma suna yin hani daga mummuna. Wadannan sune masu rabauta. Kada ku kasance kamar wadanda suka rarrabu, kuma suka sabawa juna bayan hujjoji sunje musu, kuma wadannan suna da azaba mai girma} , Kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka Ya ce: {A yaune Na cika muku Addininku, kuma Na cika muku ni’imaTa, kuma Na yarda da Musulunci ya zama Addini a gareku} , Kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka Ya ce: {Lallai ne Addini a wurin Allah shine Musulunci} . Kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Wanda ya nemi (bin) wani addini baMusulunci ba, to baza’a karba daga gareshi ba, kuma shi a lahira yana daga cikin masu hasara} , Kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Kuyi jihadi a wajen (daukaka addinin) Allah iyakar iyawarku. Shine Ya zabeku, bai kuma sanya wani kunci a cikin Addini. Addinin babanku ne Ibrahim, (Allah) Shine Ya kiraku musulmaituntuni, da kuma cikin wannan (Alkur’ani) don Manzo ya kasance mai shaida a gareku, ku kuma ku kasance masu shaida ga (sauran) mutane. To sai ku tsayar da sallah ku ba da zakka, kuyi riko da (addinin) Allah, Shine Majibincin al’amarinku, to madalla da Majibinci, kuma madalla da mataimaki} .


Lallai ni’imar Musulunci ni’imace wacce babu wani abu da yayi daidai da ita daga wasu ni’imomin daban, duk da ni’imomin Allah masu girma ne, ba’a wulakanta su kuma ba’a kaskantar da su, kai yana wajaba a tinasu kuma a gode musu, sai dai ni’imar Musulunci itace mafi girman ni’imomi, Musuluncin da Allah Ya aiko ManzonSa Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da shi, to aiko wannan Manzon – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ni’imace mai girma; domin cewa shine wanda ya bayyana wannan Musuluncin, kuma yazo da shi, kuma yayi kira zuwa gare shi, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Hakika Allah Yayi baiwa ga muminai, yayin da Ya aiko musu Manzo daga cikinsu wanda yake karanta musu ayoyinSa, kuma yake tsarkakesu, kuma yake koyar da su Littafi da Hikima, koda yake kuma sun kasance kafin (zuwansa) hakika suna cikin bata bayyananne} , sai dai akwai wasu abubuwa masu juyarwa kuma masu bijirowa da suke bijirowa mutum da zasu iya fitar da shi daga wannan Musuluncin – in ya kasance daga ma’abotansa ne – ko su raunana shi a cikin zuciyarsa, ko su hana shi shiga cikinsa, idan ya kasance ba daga ma’abotansa bane.


Akwai wasu fitintinu masu girma da suke bijirowa mutum, to yana wajaba a kansa ya kasance ya sansu, kuma yana kan kiyayesu, kamar yanda yake wajaba a kansa yasan menene mafita daga garesu idan an jarrabeshi da su.


Daga nan ne sahabi mai girma Huzaifa dan Yaman – Allah Ya yarda da shi – ya kasance yana cewa: Mutane sun kasance suna tambayar Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – game da alheri, ni kuma na kasance ina tambayarsa game da sharri, dan tsoron kada na fada cikinsa.


To sanin Musulunci a farko da lura a cikinsa, da sanin hukunce-hukuncensa da rabe-raben abubuwan da ya kunsa al’amarine na wajibi, sannan kuma sanin abinda zai juyar daga gareshi kuma ya tsare tsakanin bawa da shi, ko kuma abinda zai raunana shi a cikin zuciyarsa na aibuka, sai yasan abubuwan anfani kuma yasan abubuwa masu cutarwa, saboda yayi riko da abubuwan anfanin kuma ya nisanci abubuwan cutarwar, idan bai san al’amura masu cutarwa ba da al’amuara masu batarwa ba, watakila zasu iya halakashi alhali shi baya sani, Allah – Madaukaki – Ya umarce mu muyi riko da wannan Addinin har zuwa mutuwa, Madaukakin sarki Ya ce: {Kada ku mutu face sai kuna musulmai} , babu kokwanto cewa wanzuwa akan Musulunci a hannun Allah ne – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, mu bama mallakar wanzuwa a Musulunci har mu mutu, kadai wannan a hannun Allah ne – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, sai dai ma’anar wannan: Cewa mu muyi riko da sabubban da zasu sabbaba wanzuwa akan wannan Musuluncin har zuwa mutuwa: sabubba masu karewa, idan mukayi riko da sabubban to Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – da baiwarSa da kuma falalarSa Zai cika mana ni’imarSa, kuma Zai kashemu akan Musulunci; domin cewa mu mun shinfida sabubba, kuma munyi kokari a cikin tsira, Allah – Madaukaki – Mai hakuri ne kuma Mai baiwa ne, idan yaga kwadayin alheri daga bawanSa da kwadayi a cikinsa, da kuma kin sharri da tsoro daga gareshi, to lallai Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Zai daidaita shi kuma Zai kareshi, Zai tsareshi, kuma Zai kubutar da Addininsa, Zai cika masa alheri.


Amma idan yaga bijirewa daga bawanSa, da rashin kwadayi a cikin alheri, da rashin kin sharri, to lallai Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Zai jibintar masa da abinda ya jibinta, dan ukuba gareshi, da kuma adalcinSa gareshi – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, Madaukakin sarki Ya ce: {Wanda yake sabawa wannan Manzo bayan shiriya ta bayyana a gareshi, yake kuma bin tafarkin da bana muminai ba, zaMu barshi da abinda yadaukarwa kansa, sannan mushigar da shi wutar Jahannama: makoma kuwa ta munana} , sai sababi ya zama daga bawa ne, ya sabawa Manzo, kuma yabi wanin hanyar muminai, sababin daga bangaransa ne, ukubar kuma daga Allah ne – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -: {ZaMu barshi da abinda ya daukarwa kansa, sannan mu shigar da shi wutar Jahannama: makoma ta munana}.


Fitintinu: Jam’in fitina ne, ma’anar fitina: Jarrabawa da kuma ibtila’i; dan gaskiyar imani ko munafunci ya bayyana, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Kuma daga cikin mutane akwai mai cewa ‘munyi imani da Allah’, sannan idan aka cuceshi a kan hanyar Allah, sai yakan dauki fitinar mutane kamar azabar Allah} , baya hakuri a lokacin fitintinu dan ya tabbata akan gaskiya, kawai yana guduwane daga Addininsa yana yiwa masu juyarwa biyayya, yana zatan cewa shi zai tsira da hakan, kawai shi ya fita daga wani sharrine zuwa abinda ya fishi sharri – kamar mai neman tsira ne daga zafin rana ne da wuta – ya sanya fitinar mutane kamar azabar Allah, shin fitinar mutane tayi daidai da azabar Allah ne?! cewa shi idan yabar Addininsa, kuma ya amsawa masu sa fitina kuma ya bisu to ya fita zuwa azabar Allah, da ace shi yayi hakuri akan cutar mutane, kuma yayi hakuri akan cutar bayi, yayi riko da Addininsa, da wannan radadin da yake gamuwa da shi sai ya zama na dan lokaci, yaye bakin ciki a kusa yake, kuma karshe (shine) abin yabo, sai dai cewa shi da akasi baiyi hakuri akan cutar mtane da fitinar mutane ba, kai ya bisu a cikin sabon Allah, kuma ya amsa musu ga abinda suka tambaya na kafircewa Allah, sai ya zama zuwa azabar Allah mai radadi.


Fitina: Itace ibtila’i da jarraba; dan mai gaskiya a cikin imaninsa, mai tabbata akan akidarsa ya bayyana, daga mai kai kawo mai raurawa, wanda farkon guguwa mai faucewa daga fitintinu zata fauceshi.


Amma fahimtar Addini, to Fikihu a luga: Shine fahimta, a shari’a kuma: Shine fahimtar hukunce-hukuncen Allah – Mai girma da daukaka – wadanda sukazo a cikin Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa Allah Ya saukar da wannan alkur’ani, kuma Ya saukar da sunnar Annabi dan shiriya ga mutane, a cikinta akwai shiriya, kuma a cikinta akwai bayanin kowane abu daga abinda bayi suke bukatarsa a al’amuran Addininsu, da abinda zaisa su tsira a duniya da lahira, Allah Ya lamincewa wannan littafin dukkan abinda ‘yan Adam suke bukatarsa, a cikinsa akwai isuwa, kuma a gefansa akwai bayanin Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da sunnar Manzo mai bayyana AlKur’ani, mai fassara AlKur’ani, Madaukakin sarki Ya ce: {Mun saukar maka da Alkur’ani dan ka bayyanawa mutane abinda aka saukar musu} .


Manzo mai bayyanawa ne kuma mai isarwa ne, kuma mai fassara wannan Littafin mai girma ne, littafi da sunnah a cikinsu akwai shiriya daga bata, kuma da bayanin hanyar alheri da hanyar sharri.


Fahimtar Addini: Shine mu hankalta kuma mu fahimta daga Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – hukuncin abinda yake bijiro mana na matsaloli, da abinda ake bijiro mana da shi na fitintinu, har mu nisancesu kuma mu riki hanyar tsira, wannan shine fahimtar Addini.


   Allah – Madaukakin sarki – Yayi umarni da fahimtar Addini, kuma Ya zargi wadanda basa fahimta, tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Ya ce: {Mezai hana wasu jama’a daga kowace kabila (su zauna) don su nemi ilimin addini kuma domin suyi gargadi ga mutanensu idan sun dawomusu, dan su kiyaye dokokin Allah} .


Kuma Ya siffanta munafukai da cewa su basa fahimta, Yana nufin: Basa fahimtar hukunce-hukuncen Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -; domin cewa su basuyi nufin hakan ba, basu ma juya zuwa gareshi ba kuma basu himmatu da shi ba, sai suka zama basa fahimta.


Fitintinu suna da yawa, kuma suna yawaita suna girmama kuma suna sabuntuwa a karshen zamani. Fitintinu masu yawa ne, mutum kuwa yana rayuwa da fitintinu a dukkan rayuwarsa, sai dai akwai mai karantawa da mai yawaitawa, Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Ya bada labarin cewa dukiya da ‘ya’ya fitina ne, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Kadai dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina ne (a gareku), lada mai girma yana wurin Allah} , kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Yaku wadanda sukayi imani kada dukiyoyinku ko ‘ya’yanku su shagaltar daku daga ambatan Allah, wanda ya aikata haka to wadan nan sune masu hasara} .


Dukiyoyi da ‘ya’ya fitina ne, wanda ya fifita son dukiya, da son da, da son gari, da son dangi, da son kasuwanci, da son gidaje akan son Allah da ManzonSa, to ya saurari mafi munin sakamako, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Kace: ‘idan iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan uwanku da matanku da danginku da dukiyoyin da kuka  tara da kasuwaci da kuke tsoron tasgaronsa, da gidajen da kuke sha’awa; idan sun kasance mafiya soyuwa a gareku daga Allah da ManzonSa, da yin jihadi ga hanyarSa, to kuyi jira har sai Allah Yazo da al’amarinSa! Kuma Allah baYa shiryar da mutane fasikai} .


Dukiyoyi da ‘ya’ya fitina ne, mata fitina ce, Madaukakin sarki Ya ce: {Yaku wadanda sukayi imani! Lallai ne daga matanku da ‘ya’yanku akwai wani makiyi a gareku, sai kuyi saunarsa} , kada ku fifita soyayyarsu akan soyayyar Allah da ManzonSa, kada ku fifita biyayyarsu akan biyayyar Allah da ManzonSa, kada ku shagalta da su daga abinda zai kusanto da ku zuwa ga Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, ku kiyaye, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Yaku wadanda sukayi imani! Lallai ne wasu daga matanku da ‘ya’yanku makiyanku ne, sai kuyi hattara da su}, ma’anar ku kiyaye su bai zama: Cewa ku kuyi gaba dasu ba, kuma ku nisance su, ku yanke musuba, a’a, ma’anarsa: Cewa ku kiyayi fitinarsu, ku kiyayi karkata tare da su, idan soyayyarsu tayi karo tare da soyayyar Allah da ManzonSa, kai ku gabatar da soyayar Allah da ManzonSa akan soyayyar dukiya da ‘ya’ya, a wannan lokacin Allah Zai gyara muku dukiyoyi, kuma Zai gyara muku ‘ya’ya, Madaukakin sarki Ya ce: {Yaku wadanda sukayi imani! Lallai ne wasu daga matanku da ‘ya’yanku makiyanku ne, sai kuyi hattara da su, kuma idan kuka yafe kuka kau da kai, kuma kuka gafarta, to lallai Allah Mai gafara ne, Mai jin kai. Dukiyoyinku da ‘ya’yanku fitina dai ne, kuma a wurinn Allah lada mai girma yake. Sai kuji tsoron Allah gwargwadan ikonku} .


Wajibi akan musulmi a wannan matsayar: Yaji tsoron Allah daidai gwargwado, kada ya gabatar da soyayyar matarsa idan tayi karo tare da soyayyar Allah, ko soyayyar dansa, ko soyayyar dukiyarsa; idan hakan yayi karo tare da abinda Allah – Mai girma da daukaka – Yake sonsa, kai ya gabatar da abinda Allah – Mai girma da daukaka – Yake sonsa, da haka ne Zai gyara masa dukiyarsa, kuma Zai gyara masa matarsa, kuma Zai gyara masa ‘ya’yansa.


Alheri da sharri fitina ne, Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma Muna jarrabaku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gareMu ne za’a dawo da ku} , alherin da shine dukiya da girgijen ruwa da bazara da ni’imomi, sharri kuwa a cikinsa akwai ibtila’i da jarrabawa, da fari da yunwa da rashin lafiya, wannan dukkaninsa fitintinu ne da suke bijirowa mutum, Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma Muna jarrabaku da fitinar sharri da ta alheri, kuma gareMu ne za’a dawo da ku}, haka nan da’a da sabo fitina ne, mutum an umarce shi da da’a, kuma an hana shi sabo, biyayya zata bijiro masa, lokacin sallah da ibada zasu zo, kuma lokacin jin dadi da ci da sha da jin dadi (na jima’i) da wanin haka zaizo, to wanne daga cikinsu zai gabatar? Wannan ibtila’i ne da jarrabawa, ibtila’i da jarrabawa daga Allah ne – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -, sashin mtane fitina ne ga sashi, Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma Mun sanya sashinku fitina ga sashi, shin kunayin hakuri ne? Kuma Ubangijinku Ya kasance Mai gani} .


Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - Yana jarrabar mutane sashinsu da sahi, yana jarrabar mumini da kafiri, Yana jarrabar mumini da munafiki, Yana jarrabar bayinSa sashinsu da sashi, Madaukakin sarki Ya ce: {Wancan, da Allah Yaso da Ya ci nasara a kansu (ba tare da yaki ba) kuma amma (Ya wajabta jihadi ne) domin Ya jarraba sashenku da sashe} , kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma Mun sanya sashinku fitina ga sashi, shin kunayin hakuri ne?} .


Mumini da musulmi ana jarrabashi da makiyinsa daga kafirai da munafukai da masu sabo, dan matsayarsa ya bayyana daga garesu da kira zuwa ga Allah, da horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki, da yaki, ko mika wuya da dawwama zuwa hutu, idan ta farkon ta kasance – itace: Kira zuwa ga Allah, da horo da aikin alheri da kuma hani daga abin ki, da yaki – to ya kasance akan alheri, kuma yayi nasara a jarrabawa, idan kuma ya kasance na biyun ne – shine: Mika wuya da dawwama a hutu, da rashin bijirowa mutane alhali su suna kan sharrinsu, da kuma rashin kiransu zuwa ga Allah, da rashin horo da aikin alheri da hani daga abin ki, da rashin yaki a tafarkin Allah, kawai ya mika wuya kuma ya dawwama a cikin hutu – to ya zama asara da rashin nasara a jarrabawa, Madaukakin sarki Ya ce: {Mun sanya sashinku fitina ga sashi} , haka nan yake jarrabar mawadaci da talaka, Madaukakin sarki Ya ce: {Kamar wannan ne Muka fitini sashensu da sashe, domin su ce: ‘Shin wadannan ne Allah Yayi falala a kansu daga tsakaninmu?’ shin, Allah baShi ne Mafi sanin masu godiya (gareShi) ba} .


Kafirai suna wulakanta talakawan musulmai, kuma suna cewa: Shin wadannan ne Allah Yayiwa baiwa a tsakaninmu?! Wadannan wasu mutane ne talakawa, babu komai a hannayensu, ta yaya zasu zama akan shiriya alhali mu kuma akan bata?! Mu mune masu dukiya, mune ma’abota dukiyoyi, mune ma’abota shugabanci ma’abota ra’ayi, kuma ma’abota kullawa da warwarewa, wadannan kuwa talakawa ne miskanai, amma a tare da hakan suke riya cewa su sunfi mu, kuma cewa su sune… {Shin wadan ne wadanda Allah Yayi musu falala daga tsakanimu}, Allah – Madaukakin sarki – Yana cewa: {Shin yanzu baShi ne Mafi sani daga masu godiya ba}, Allah – Mai girma da daukaka – baYa duba zuwa surorinku da dukiyoyinku, kadai Yana duba ne zuwa zukatanku da ayyukanku. Talaka mai godiya, wanda yayi imani da Allah, mai kwadayi a cikin alheri, wannan shine masoyin Allah – Mai girma da daukaka -, amma mai girman kai maiyiwa gaskiya dagawa, wanda aka sawa jiji da kai da dukiyarsa da kuma kansa da alfarmarsa, bai karbi gaskiya ba, to wannan baya daidai da komai a wurin Allah, duk da yana daidai da abu mai girma a gurinsa, to cewa shi baya daidai da komai a wurin Allah, Madaukakin sarki Ya ce: {Shin wadannan ne Allah Yayi musu falala daga tsakaninmu} Yana nufin: Wadannan sun samu shiriya banda mu; su a wannan halin na talauci da fako da bukata, mu mune mafi buwaya daga gare su, kuma mu mune mafiya girma daga gare su, wannan ne a riyawarsu; domin cewa abubuwan kiyastawa a wurinsu sune abubuwan kiyastawa na wadata da dukiya da alfarma, bawai abubuwan kiyastawa na zukata da ayyuka ba, amma abubuwan kiyastawa a wurin Allah – Mai girma da daukaka – sune zukata da ayyuka “Sai dai yana duba zuwa zukatanku da ayyukanku”, Allah – Mai girma da daukaka – Yana bada duniya ga wanda Yake so da wanda baYa so, sai dai cewa shi baYa bada wannan Addinin sai ga wanda Yake so, Madaukakin sarki – Ya ce: {Haka nan Muka fitini sashinsu da sashi dan suce shin wadan nan ne wadanda Allah Yayi falala garesu daga tsakaninmu}.


Haka nan daga mafi girman fitintinu fitinar rarrabuwa da sabani, da bayyanar kungiyoyi da jama’u, wannan yana daga mafi girman fitintinu, wannan wani abune wanda Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya bada labari game da shi, cewa shi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – kamar yanda yake a cikin hadisin Irbad ɗan Sariya – Allah Ya yarda da shi - ya ce: Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yayi mana wa’azi wa’azi isasshe, zukata sukaji tsoro daga gareshi, kuma idanduna suka zubar da hawaye daga gareshi, sai muka ce: Ya Manzon Allah, kamar mai wa’azin mai bankwana, to kayi mana wasicci, ya ce: “ Inayi muku wasicci da tsoron Allah, da ji da bi” ji da bi da da’a, yana nufin: Ga majibinta al’amura musulmai; dan abinda ke cikin hakan daga haduwar kalma, da karfin al’umma, da kwarjinin al’umma a gaban makiyansu, idan sun hadu karkashin jagoranta, kuma karkashin waliccinsu muminai, to cewa hakan yana sanyawa al’umma kwarjini da karfi. “Da ji da bi, koda bawa ne ya shugabance ku”, yana nufin: Kada ku wulakanta majibinta al’amari duk yanda yake, kai ku ji ku bi, muddin dai cewa yana umarni da biyayya ga Allah. “Cewa shi wanda ya rayu daga gareku zaiga sabani mai yawa” wannan labari ne daga gareshi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da afkuwar sabani tsakanin musulmai, kuma shi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – baya furuci daga son rai, to babu makawa abinda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labari da shi sai ya afku ko a gaggauce ko a jinkirce, “Zaiga sabani mai yawa” baice: Zaiga sabani kawai ba, kai ya ce: Mai yawa, sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya shiryar zuwa ga abinda yake tseratarwa daga sharrin wannan sabanin, sai ya ce: “To na horeku da sunnata da sunnar halifofina shiryayyu masu shiryarwa a bayana, kuyi riko da ita kuma ku riketa da turaman hakoranku, na haneku da fararrun al’amura, domin cewa dukkan fararren al’amari bidi’a ne, kuma dukkan bidi’a bata ne”, haka nan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya bada labari daga afkuwar sabani a ra’ayuyyuka da tinanuka, da mazahabobi da jama’u da kungiyoyi, sai dai cewa shi yayi wasicci a hakan da riko da Littafin Allah da sunnarsa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da abinda halifofinsa shiryayyu suke a kansa, to lallai hakan shine lamunin tsira ga wanda yayi aiki da shi, amma wanda hannunsa ya subuce daga sunnar Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da hanyar halifofi shiryayyu, to cewa shi zai bata tare da wadan nan kungiyoyin mabanbanta.


Tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya kasance yana fada a cikin hudubarsa da zancensa: “Lallai cewa” mafificin zance Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya shiriyar (Annnabi) Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafi sharrin al’amura fararrunsu, dukkan bidi’a bata ce, kuma na horeku da jama’a, domin cewa hannun Allah Yana tare da jama’a, wanda ya ware zai ware a cikin wuta”, sai tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bayyana sabubban tsira daga fitintinu sune: Riko da Littafin Allah, da riko da shiriyar Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da kiyayewa daga fararrun al’amura, “Lallai mafi alherin zance Littafin Allah, kuma mafi alherin shiriya shiriyar (Annabi) Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma mafi sharrin al’amura fararrunsu” sannan ya ce: “Na horeku da jama’a”.


Wannan kuma suna daga sabubban tsira, cewa musulmi a lokacin bayyanar sabani da banbanci, da jama’u mabanbanta, yana kasancewa tare da jama’ar musulmai, jama’ar da ta kasance tana tafiya akan zanen Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kuma akan manhajin Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, kada yayi tafiya akan hanyar ma’abota zance, ko ma’abota jayayya, ko ‘yan bidi’a ko da sun anbaci kansu da sunaye masu kayatarwa masu yaudara, sai dai cewa su basa rudar ma’abota imani, ma’abota imani sunayin riko da abinda Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yayi wasicci da shi: “Na horeku da jama’a” jama’ar musulmai, wannan misalin fadinsa ne – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – a cikin hadisin rarrabuwar al’umma, ya ce: “Yahudawa sun rabu kungiya saba’in da daya, Nasara sun rabu kungiya saba’in da biyu, wannan al’ummar zasu rabu kungiya saba’in da uku, dukkansu a cikin wuta (suke) sai daya” Aka ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: “Wanda yake akan abinda nake a kansa a yau da sahabbaina”, wannan misalin fadinsa ne: “Na horeku da jama’a, domin cewa hannun Allah Yana tare da jama’a”, jama’a: Sune wadanda suke akan abinda Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da sahabbansa suke a kansa, koda sun kasance ‘yan kadan ne, sharadin jama’a baya kasancewa su zama da yawa, kai daga sharadinsu su zama akan gaskiya, ko da ‘yan kadan ne, yawa ba dalili ne na gaskiya ba, Madaukakin sarki: {Inda zakayi biyayya ga mafiya yawan wadanda ke cikin kasa zasu batar da kai daga tafarkin Allah, babu abinda suke bi sai zato} .


Muddun dai suna bin zato to cewa su suna batarwa daga tafarkin Allah, koda sun kasance dubun dubata ne, ko dubunnan daruruwa ne, amma wanda yake akan gaskiya to cewa shi shine jama’a, kuma shine kungiya mai tsira abar taimako, kuma shine bangare abin taimako, muddin dai yana kan gaskiya koda ya kasance daya ne ko kuma adadi kadan, sune kungiyar da ta tsira, kuma sune bangare abin taimako, kuma Ahlus Sunnah wal jama’a, kamar yanda Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya ce: “Wata kungiya daga al’ummata bazata gushe ba akan gaskiya suna masu rinjaye, wanda ya tabar da su bazai cutar da su da komai ba, ko wanda ya saba musu, har sai al’amarin Allah – Mai girma da daukaka - ya zo”, sai dai wannan yana bukatuwa zuwa ga hakuri. Kayi riko da abinda Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yake a kansa, kuma kayi riko da abinda jama’a suke a kansa, kungiya wacce ta tsira, Ahlus Sunnah wal jama’a, yana bukatuwa zuwa ga hakuri, musamman ma dai a karshen zamani, domin cewa a karshen zamani mai riko da sunnar Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, wanda ya lazimci jama’ar musulmai, zai gamu da tsanani mai girma, kamar yanda yazo a cikin hadisi (Cewa fitintinu zasu faru a karshen zamani, mai riko da Addininsa zai zama kamar mai riko da garwashin wuta ne, ko akan fagauniyar kaya), yana bukatuwa zuwa hakuri, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Mai riko da sunnata, a lokacin bacin al’ummata, yana da ladan hamsin” (sahabbai) suka ce: Daga cikinmu ko daga cikinsu ya Manzon Allah? Ya ce: “Kai daga cikinku” yana nufin: Daga sahabbai; domin cewa sahabbai sun kasance tare da Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, masu taimaka musu sun kasance da yawa ne, sai dai  mai riko da sunnah a karshen zamani, da lokacin bayyanar fitintinu, bashi da mataimaka, kai mafi yawan mutane kishiyoyinsa ne, suna kunyatashi suna wulakanta shi suna kuskurantar da shi, to yana bukatuwa zuwa hakuri, saboda haka ne wannan ladan mai girma ya tabbata gare shi; saboda tabbatarsa a kan gaskiya a lokacin bayyanar fitintinu da yawan abubuwa masu bijirowa, kuma  Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya siffanta su da: Baki, ya ce: “Aljanna ta tabbata ga baki, (sahabbai) suka ce: Suwaye su ya Manzon Allah? Ya ce: “Wadanda suke gyaruwa idan mutane suka baci”. A cikin wata riwayar: “Suke gyara abinda mutane suka bata”, wannan zai tsinkayar da mu a kan wani al’amari mai girma da zai faru a karshen zamani, to ya wajaba a kanmu mu roki Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – tabbata da mutuwa a kan Musulunci, kuma ya wajaba a kanmu tare da hakan muyi kokari a sanin gaskiya da ma’abotanta, da kuma sanin karya da ma’abotanta; har mu zama tare da gaskiya tare da ma’abotanta, kuma mu kiyaya daga karya da ma’abotanta, hakan kadai yana bukatuwa ne zuwa fahimtar Addini.


Wannan baya yiwuwa daga jahili, kadai yana yiwuwa ne daga wanda Allah Ya azirtashi fahimtar Addini, da basira da ilimi mai anfani, wanda yake banbancewa tsakanin shiriya da bata da shi, da tsakanin bata da shiriya, da kuma tsakanin gaskiya da karya, tsira daga wadannan fitintinun masu girma mai wahala ne, alhali ku kuna gani a yanzu abinda duniya take amayarwa na fitintinu masu girma.


Daga fitintinun: Cewa duniya a yanzu ta kusanci juna, sai ya zama abinda yake faruwa a karshenta yana isa zuwa (daya) karshen nata da sauri, ana cirato abinda yake faruwa na sharri, da fasikanci da kuma sabo – ana ciratowa ta hanyar kafafen sadarwa na zamani a yanzu, har ya shiga cikin kullallun gidaje, kai har yana isa daji a sarari, a cikin gidajen gashi, ta hanyar kafafen sadarwar, suna kallonsa kamar su suna nan a wurin da ya faru a cikinsa. A’a kai zai iya zama ma yafi bayyana daga gurin da sharrin ya faru a cikinsa.


Wannan yana daga ibtila’i da jarrabawa, duniya a yanzu tana amayar da fititinu, fitintinun sha’awowi, ya mamakin yawansu! da fitinun shubuhohi da bace-bace da musun samuwar Allah, ya mamakin yawan hakan! Dukkan wannan yana bijirowa ne zuwa duniya, mafi nisanta da gabashinta da yammacinta, kudancinta da arewacinta, sai dai wanda Allah Yaji kai – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka -. Wannan ana bukatuwa ga mutum zuwa ga basira, yana bukatuwa zuwa riko da kewaye, yana bukatuwa zuwa sanin wadan nan cututtukan masu gangarowa, har ya nisance su, amma mutumin da bashi da basira, bashi da ilimi, bashi da fikihu, watakila zai dauki wannan cewa yana daga daukaka da kuma cigaba. Wasu daga cikinsu suna daukar wannan daga ni’imomi, kuma cewa wadannan hanyoyi ne na wayewa, da hanyoyi na wadata, baya sanin abinda wannan al’amarin ya boye na hadari, da abinda yake dauke da shi na sharri.


Al’amarin mai girma ne sosai, fitintinu a yanzu – kamar yanda kuke ganinsu – ana bijirowa mutane su, ana bijirowa zukata su, kamar yanda Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agre shi – ya ce: “Za’a bijiro da fitintinu akan zukata maimaici- maimaici, duk zuciyar da aka cakuda mata su sai tayi mata gurbi bakin gurbi a cikinta, har ta wayi gari zuciya karkatacciya, bata sanin aikin alheri kuma bata kin abin ki, sai abinda ya dace da son ranta – ko – abinda ya cakuda da son ranta, duk zuciyar da tayi musunsu sai tayi mata farin gurbi, to wannan zuciya ce bazata cutar da ita ba muddin dai sammai da kasa (suna nan)”.


Fitintinu wadannan ana bijiro su a kan zukatan mutane, wace zuciya ce zata musa su? Sai dai zuciyar da zata musa su itace zuciyar masanin fikihu wanda yake neman fahimtar Littafin Allah – Mai girma da daukaka -, wanda yasan hukuncin Allah a cikin wannan al’amuran, amma jahili zasu iya yaudararsa, kuma za iya kawata masa su, yayi izinarsu cigaba ne da kayatarwa, kuma nisanta da su zai yi izina cewa yana daga wauta da koma baya kamar yanda suke cewa.


(Zance na) gaskiya: Shine cewa babu mai tsarewa daga wadan nan fitintinun sai abinda Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka - Ya sanya shi mai tsarewa daga garesu, shine Littafin Allah, da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Wani littafine Muka saukar da shi zuwa gareka dan ka fitar da mutane daga duffan (kafirci) zuwa hasken (Musulunci) da izinin Ubangijinsu zuwa hanyar Mabuwayi Abin godiya} , kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka Ya ce: {Ku bi abinda aka saukar muku daga Ubangijinku kada ku bi wasu masoya koma bayanSa kadan ne abinda kuke wa’azantuwa} , kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka Ya ce: {Lallai wannan alKur’anin yana shiryarwa ga (hanya)mafi mikewa, kuma yana bayar da bushara ga muminai wadanda suke aikata ayyuka na kwarai (cewa) lallai ne suna da wani lada mai girma. Kuma lallai ne wadanda basuyi imani da lahira ba, lallai Mun tanadar musu da wata azaba mai radadi} .


Kuma tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka Ya fada a farkon Surat al-Bakara- wacce itace sura ta biyu a cikin Mushafi madaukaki – Madaukakin sarki Ya ce: Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai {Allah ne Mafi sani da manufarsa da hakan. Wancananka Littafi babu kokwanto a cikinsa, shiriya ne ga masu tsoron Allah. Wadanda suke imani da gaibu kuma suke tsaida sallah kuma suke ciyarwa daga abinda Muka azirtasu. Wadanda suke imani da abinda aka saukar maka da abinda aka saukarwa wadanda ke gabaninka kuma suna sakankancewa da ranar lahira. Wadan nan suna kan shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan sune masu rabauta} , Allah Ya ambata a farkon wannan surar cewa wannan Alkr’anin shiriya ne ga masu tsoron Allah, ga masu tsoron Allah ne a kebance, sannan Ya bayyana su, Ya bayyana suwaye masu tsoron Allah? {Wadanda suke imani da gaibu kuma suke tsaida sallah kuma suke ciyarwa daga abinda Muka azirtasu. Wadanda suke imani da abinda aka saukar maka da abinda aka saukarwa wadanda ke gabaninka kuma suna sakankancewa da ranar lahira} . Sannan Yayi musu hukunci da rabauta da kuma shiriya, {Wadannan suna kan shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadan nan sune masu rabauta}, sannan Ya ambaci sinfi na biyu: Sune kafirai, da sinfi na uku: Sune munafukai.


Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Ya ambata: Cewa mutane a bangaren wannan AlKur’anin sun kasu gida uku:


Kashi na farko: Wadanda sukayi imani da shi a zahiri da badini kuma sune: Masu tsoron Allah, kuma Allah Ya ambaci abinda Ya ambata daga siffofinsu.


Sannan Ya ambaci kashi na biyu: Sune wadanda suka kafirce da wannan littafin a zahiri da badini, sune kafirai, Madaukakin sarki Ya ce: {Lallai wadanda suka kafirta daidai ne a kansu shin kayi musu gargadi ko bakayi musu gargadi ba baza suyi imani ba. Allah Yayi yumki a kan zukatansu da jin su, kuma akwai yana a kan ganinsu, azaba mai girma ta tabbata a garesu} , wadan nan sun kafircewa AlKur’ani a badini da zahiri, sai Allah Yayi yumki akan zukatansu, dan ukuba garesu, sai suka wayi gari basa karbar gaskiya bayan haka.


Kashi na uku: Wadanda sukayi imani da AlKur’ani a zahiri kuma suka kafirce da shi a badini, su ne: Munafukai, Allah Ya ambaci ayoyi goma sha wani abu a cikinsu: Daga fadinSa – Madaukakin sarki -: {Kuma akwai daga mutane wanda yake cewa: Munyi imani da Allah da ranar lahira alhali su ba muminani ba ne. Suna yaudarar Allah da wadanda sukayi imani}…har zuwa fadinSa – Madaukakin sarki -: {Kuma da Allah Ya so da sai Ya tafi da jinsu da gannansu, lallai ne Allah Mai iko ne akan dukkan komai} .


Tabbataccen abu: Cewa Littafin Allah a cikinsa a kwai shiriya da haske, yana bukatuwa daga garemu zuwa ga lura, Madaukakin sarki Ya ce: {Littafi ne Mun saukar da shi zuwa gareka dan su lura da ayoyinsa kuma dan ma’abota hankula su rinka yin tinani} , wanda yake son tsira daga wadan nan fititinun to ya wajaba a kansa ya koma Littafin Allah – Mai girma da daukaka -, wajibi ne ya komawa Littafin Allah, to ta yaya? Shin ya sanya shi a wurinsa? Ya sayi AlKur’ani ya sanya shi a wurinsa!!?


Wajibi ne a kansa ya karanta shi kuma yayi aiki da abinda ke cikinsa, shine tushe na farko ga shiriya da tsira daga sharruka a duniya da lahira, a cikin wannan AlKur’anin mai girma akwai lurarsa da shi, yawaitawa daga karanta shi, yawaitawa daga yin aiki da shi; dan ya zama mai kareka daga wadannan fitintinun da kuma sharruka.


Haka nan sunnar Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -; domin cewa ita tana fassara wannan AlKur’anin, kuma tana bayyana shi, tana bayaninsa, kuma tana nuni a kansa, kamar yanda Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma bayayin magana daga son zuciya. (Shi Alkur’ani) baizamo ba, face wahayi ne da akeyo masa} , Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana cewa: “Lallai ni mai bari ne a cikinku abinda idan kunyi riko da shi bazaku bata ba a bayana: Littafin Allah da sunnata”, wannan lamunin da amintakar daga fitintinu ga wanda yayi riko da su ne kawai.


(Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labari a cikin hadisai: “Lallai cewa za’a samu wasu fitintinu kamar yankewar dare mai duhu, mutum zai wayi gari yana mumini kuma ya maraita yana kafiri, kuma zai maraita yana mumini sai ya wayi gari yana kafiri, zai saida Addininsa da wata haja ta duniya”, zai saida Addininsa da wata haja ta duniya; Yana fifita duniya akan lahira sai yabi a makance tare da duniya: Zai bar sallah, zai hana zakka, zai sabawa Allah da ManzonSa, zai bi Shaidan da mataimakan Shaidan; sai ya saida Addininsa da wata haja ta duniya, muna rokon Allah lafiya daga wadan nan fitintinu masu girma.


Fitintinu suna tsananta, a duk lokacin da zamani ya jinkirta fitintinu za suyi tsanani, har manyan fitintinu masu biyewa juna su zo har zuwa tashin Alkiyama. Mutum yana rayuwa da fitintinu a cikin wannan duniyar, yana rayuwa da su musamman ma mutanen karshen zamani sune mafi yawan rayuwa da fitintinu, kuma fitintinu zasu kasance a zamaninsu mafi yawa; dan kusancin tashin Alkiyama da kuma karewar duniya.


Mutum yana rayuwa da fitintinu har a lokacin mutuwa. Mutum ana fitinarsa har a lokacin mutuwa, zai iyayin kyakkyawar cikawa, kuma zai iyayin mummunar cikawa muna neman tsarin Allah, haka nan ana fitinarsa har a kabari, idan aka ajiyeshi a cikin kabarinsa za’a fitine shi: Mala’iku biyu za suzo masa sai su zaunar da shi, kuma su tambaye shi: Waye Ubangijinka? Menene Addininka? Waye Annabinka? Samun tsira da tabewa suna tsayuwa ne akan amsawa. Idan ya ce: Allah ne Ubangijina, Musulunci Addinina, kuma Annabina Muhammad – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, to cewa wani mai kira zaiyi kira: Cewa bawaNa yayi gaskiya to kuyi masa shinfida irin ta aljanna, kuma ku bude masa kofa zuwa aljanna, sai a bude masa aljanna, kuma kanshinta da dadinta su dinga zo masa, kuma ya dinga kallon masaukansa a cikin aljanna, yana cewa: Ya Ubangiji, Ka tashi alkiyama; har in koma wurin iyalaina da dukiyata, amma idan bai samu ikon amsawa ba to cewa shi zaice: Haa, a lokacin kowace tambaya yana cewa: Haa, bansani ba, naji mutane suna fadin wani abu sai na fadeshi, yana aiki cikin wadatuwa da kuma imani, kawai ya kasance yana dacewa da mutane dan koyi kawai, ko dan kwadayin duniya, manafiki kuwa: Yana bayyanar da imani kuma yana boye kafirci, (zaice) naji mutane suna fadin wani abu sai na fade shi, alhali shi baya sani. Sai wani mai kira yayi kira: Cewa bawaNa yayi karya, kuyi masa shinfida ta wuta kuma ku bude masa kofa zuwa aljanna, sai a kuntata kabarinsa har sai hakarkarinsa sun saba, na farkon kuma sai a yalwata masa kabarinsa iya tsawon ganinsa, kuma yayi duba zuwa ga wurinsa a cikin wuta, kuma zaice: Ya Ubangiji, Kada Ka tashi alkiyama; dan ibtila’i da kuma jarrabawa har a cikin kabari.


Bawa dan Adam abin bijirowa ne ga fitintinu; a cikin rayuwarsa, da lokacin mutuwarsa, da kuma cikin kabarinsa, sai dai kamar yanda Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Ya ce: {Allah Yana tabbatarwa wadanda sukayi imani akan magana tabbatacciya a cikin rayuwar duniya da kuma lahira kuma Yana batar da azzalumai, kuma Yana aikata abinda Yake so} , kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Lallai wadannnan da suka ce, ‘Ubangijinmu, Shine Allah’, sannan suka daidaita, mala’iku na sassauka garesu (a lokacin saukar ajalinsu suna ce musu), ‘Kada kuji tsoro, kuma kada kuyi bakin ciki, kuma kuyi bushara da Aljanna, wadda kun kasance anayi  muku wa’adi da ita. Mune masoyanku a cikin rayuwar duniya da kuma cikin lahira, kuma a cikinta (aljanna) kuna da abinda rayukanku ke sha’awa, kuma kuna da abinda kuke kira (a kawo muku) a cikinta} , kuma Madaukakin sarki Ya ce: {Gidajen aljannar zama, suna shigarsu, su da wadanda suka kyautatu daga iyayensu, da matansu da zuriyarsu. Kuma mala’iku suna shiga zuwa gunsu ta kowace kofa. (Sunace musu) Aminci ya tabbata a gareku saboda hakurin da kukayi, saboda haka madalla da gida na kkarshe (aljanna)} , Yana nufin: Saboda hakurinku a kan Addininku, da kuma tabbatarku akan gaskiya a cikin rayuwar duniya, kun samu wannan girmamawar ne {Aminci ya tabbata a gareku saboda hakurin da kukayi}, basu tabbatar da wannan abun haka kawai ba, kadai sun tabbatar da shi ne dan sakamakon hakuri da kuma tabbata, da imani da Allah da ManzonSa, Madaukakin sarki Ya ce: {Aminci ya tabbata a gareku saboda hakurin da kukayi, saboda haka madalla da gidan karshe (aljanna)}.


Amma kafiri – muna nenman tsarin Allah – sai Allah – alherinSa ya yawaita kuma Ya daukaka – Ya ce game da shi: {Kuma da zaka gani, a lokacin da mala’iku suke karbar rayukan wadanda suka kafirta, suna dukan fuskokinsu da duwawunsu, kuma suna cewa: ‘Ku dandani azabar gobara. Wancan saboda abinda hannayenku suka gabatar ne: Kuma lallai ne Allah bai zama Mai zalunci ga bayinSa ba} , da kuma fadinSa – Madaukakin sarki -: {Kuma da ka gani, a lokacin da azzzalumai suke cikin mayen mutuwa, kuma mala’iku suna masu shinfida hannayensu, (suna ce musu) ‘Ku fito da rayukanku da kanku: A yau ana saka muku da azabar wulakanci saboda abinda kuka kasance kuna fadar wanin gaskiya ga Allah, kuma kun kasance kuna yin girman kai daga ayoyinSa. Hakika kunzo mana daidai, kamar yadda Muka halicceku a farkon lokaci. Kuma kun bar abinda Muka mallaka muku a bayan bayayyakinku, kuma baMu ga masu cetanku a tare daku ba, wadanda kuka riya cewa lallai ne su a cikinku masu tarayya ne. Lallai ne hakika dangantakar dake tsakaninku ta yanke, kuma abinda kuka kasance kuna riwaya ya bace muku} .


Mutum yana rayuwa da fitintinu har zuwa karshen kiftawar idonsa daga rayuwarsa, kai a lokacin sanyashi ma a cikin kabarinsa, al’amarin yana bukatuwa zuwa himmatuwa, fitintinun masu girma ne, tsira a farko tukuna da yin riko ne da Littafin Allah da sunnar ManzonSa, sai dai riko da Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – baya tabbata sai da fahimtar Addinin Allah – Mai girma da daukaka -, fahimtar Addinin Allah baya tabbata haka kawai da tatsuniyoyi, kamar yanda Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma daga cikinsu akwai jahilai, wadanda basu san Littafi ba, sai dai burace-burace, kuma zato kawai sukeyi} .


Ilimi baya samuwa da yawan karatu ko yawan littattafai, ko yawan bita, ilimi baya samuwa da wannan. Kawai ilimi yana samuwa ne ta hanyar neman ilimi ga ma'abota ilimi, da kuma karbar ilimi daga malamai.


Ilimi sai da karba (daga malamai) bawai kawai zuwa yakeyi ba, kamar yanda wasu daga mutane suke zato a yau, sashin mutane a yau suna mallakar littattafai, suna karanta litattafan hadisi, da Jarhi da Ta’adil, da tafsiri, da kaza da kaza, suna riya cewa su da haka ne zasu samu ilimi. A’a wannan wani ilimi ne  wanda ba’a ginashi akan wani tushe ba, ko akan wasu ka’idoji ba; domin cewa shi bai karba daga ma’abota ilimi ba, to babu makawa daga zama a halkokin zikiri da kuma ajujuwan karatu a wurin masana fakihai kuma malamai, kuma babu makawa daga hakuri akan neman ilimi.


              Wanda bai dandani kaskancin neman ilimi ba wani lokaci


                                                      To ya kwankwadi kofin jahilci tsawon rayuwarsa


Babu makawa daga hakuri, ilimi baya samuwa da karatu, kuma baya samuwa haka kawai, kadai yana samuwa ne da karba ga hannayen malamai na gari, fakihai masana, wadanda suke gani da Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.


Babu makawa daga shiga cikin tsarin neman ilimi, kuma babu makawa daga karbar ilimi daga kofofinsa da kuma shiga ta kofofin, kamar yanda Madaukakin sarki Ya ce: {Kuma baya daga cikin aikin da’a kujewa gidaje ta bayansu: sai dai  mai aikin da’a shine wanda yayi takawa. Kuma kujewa gidaje daga kofofinsu} . Ilimi yana da kofofi, kuma yana da madaukansa, yana da masu sanar da shi, to babu makawa – yaku ‘yan uwa – daga shigarku halkokin karantarwa, daidai ne sun kasance a cikin masallatai ne, ko a cikin makarantu, ko a cibiyoyin ilimi, ko a kwalejoji. Muhimmi dai kawai shine ka karbi ilimi daga malamai, muddin dai (malaman) suna nan kuma muddin dai akwai dama.


Amma mu rarrabu kowa ya zauna a daki, yayi laburare yana bita a cikinsa; alhali shi baiyi gini akan tushe ba, kuma bai koyi ka’idojin ilimi ba, to wannan zai tozarta ne, to babu makawa daga neman fahimtar Addinin Allah ta hannayen masana fikihu.


Kamar haka – kamar yanda mukayi nuni – daga sabubban tsira: Lazimtar jama’ar musulmai, da nisanta daga dangantaka zuwa ga kungiyoyi da jama’u wadanda suka saba ga abinda magabatan wannan al’ummar na gari suke a kansa; domin cewa Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yana fada a kungiyar da ta tsira: “Sune wadanda suke akan abinda nake a kansa a yau da sahabbaina”, Allah – Madaukakin sarki – Yana cewa: {Magabata na farko daga Muhajirun da Ansar da wadanda suka bisu da kyautatawa, Allah Ya yarda da su suma sun yarda da Shi, kuma Ya tanadar musu gidajen aljanna; Koramu suna gudana a karkashinsu, suna madawwama a cikinsu har abada. Wancan ne babban rabo mai girma} , wadanda suka bisu da kyautatawa: Sunbi wadanda suka rigaya na farko, kuma Madaukaki Yana cewa: {Wadanda sukazo a bayansu} . Yana nufin: Bayan Muhajirun da Ansar {Wadanda sukazo a bayansu suna cewa ya Ubangijinmu Ka gafarta mana da ‘yan uwanmu wadanda suka rigayemu da imani kuma kada Ka sanya wani gilli a cikin zukatanmu ga wadanda sukayi imani ya Ubangijinmu lallai Kai Mai rangwami ne kuma Mai rahama}.


Amma idan mutum ya ware tare da kungiyoyin da suka saba, kuma ya zama yana zagin sahabbai, ko yana jahilantar da malamai, ko yana jahilantar da shugabanni ko yana maida su masu galadi, to wannan bazai kai ko ina ba sai zuwa ga bata sai dai idan Allah Ya riskar da shi da rahamarSa, ya tuba zuwa ga Allah, ya koma zuwa ga jama’ar musulmai da kungiya wacce ta tsira, a can babu wani abu sai kungiya daya kuma itace mai tsira, Manzon Allah – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya ce a cikin hakkin kungiyoyi saba’in da uku: “Dukkansu ‘yan wuta ne”, kuma kasancewarsu a cikin wuta yana sabawa da sabanin nisantarsu daga gaskiya, daga cikinsu akwai wanda yake kafiri ne, daga cikinsu akwai wanda yake batacce ne, daga cikinsu akwai wanda fasiki ne, muhimmi dai shine cewa kowanne daga cikinsu anyi masa alkawari da wuta sai kungiya daya, suka ce: Waccece ya Manzon Allah? Ya ce: “Wanda yake akan abinda nake a kansa a yau da sahabbaina”, hanyar daya ce kuma jama’ar daya ne, Madaukakin sarki Ya ce: {Lallai wannan tafarkiNa ne madaidaici} , hanya ce daya kawai, Madaukakin sarki Ya ce:: {Lallai wannan tafarkiNane yana madaidaici to kubi shi, kada kubi hanyoyi sai su rarraba ku}, batattun hanyoyi suna da yawa basu da adadi, a yanzu kana ganin kungiyoyi da jama’u masu yawa basu da wani adadi, sai dai jama’a ma’abota sunnah da jama’a to daya ce, tun daga zamanin Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – har zuwa lokacin tashin alkiyama, kamar yanda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Wata kungiya daga al’ummata bazata gushe ba akan gaskiya suna masu rinjaye, wanda ya tabar da su baya cutar da su ko wanda ya saba musu har sai al’amarin Allah yazo” Eh, a can za’asamu wanda zai wulakantar da sha’aninsu, wanda zai jahilantar da su, wanda zai rafkanar da su, wanda zaice: Wadannan wasu mutanene na gari, sai dai basa sanin waki’i ne kawai kuma basu san kaza ba. Dukkan wannan yana wajaba a kan musulmi kada ya juya zuwa gareshi “Sune wanda yake akan irin abinda nake a kansa a yau da sahabbaina”, babu tsira sai da wannan: (shine) Lazimtar jama’ar musulamai.


“Na horeku da jama’a, domin cewa lallai hannun Allah Yana kan jama’a”, Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – a sama da hadisi daya ya kwadaitar da mu akan mu zama tare da jama’a masu riko da tafarkin Annabi – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – da tafarkin sahabbansa, da tafarkin magabatan wannan al’ummar; domin cewa magabatan wannan al’ummar sune mafi sani kuma mafi kusanci zuwa ga gaskiya daga wadanda sukazo a bayansu; saboda haka ne (Annabi) – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – yayi yabo ga zamaninnika uku ko hudu, ya ce: “Mafi alherinku zamanina, sannan wadanda suke binsu, sannan wadanda suke binsu”, maruwaicin hadisin ya ce: Bansani ba bayan zamaninsa shin ya ambaci zamani biyu ne ko uku. Sannan tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa al’amari zai canja bayan wadannan zmaninnikan, kuma lallai cewa al’amari abinda zai faru zai faru a cikinsa, hakika abinda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi  ya bada labari da shi ya afku, bayan karewar lokacin zamaninnika ababen fifitawa abinda ya faru ya faru na fitintinu ya faru a cikin wannan al’ummar, da kuma abubuwan da suka shigo, da kuma mazahabobi mabanbanta, babu wanda ya wanzu akan gaskiya sai jama’ar musulmai wadanda sukayi riko da abinda magabata na gari suke a kansa, da kuma masu da’awar jaddada (Addini) wadanda suke jaddada wannan Addinin ga wannan al’ummar, da wanda ya bisu kuma yayi tafiya akan hanyarsu, wannan yana daga ni’imomin Allah cewa alheri ana samunsa, duk yanda sharri ya yawaita to lallai cewa alheri za’a sameshi; saboda cewa wanda yayi nufinsa ya koma zuwa gare shi, kuma saboda hujjar Allah – Madaukaki – ta tsayu akan halittarSa, a duk lokacin da fitintinu suka yawaita a duk lokacin sharruka suka yawaita, sai dai cewa gaskiya tana nan, godiya ta tabbata ga Allah.


Bama cewa: Lallai al’ummar Musulunci bata nan, kamar yanda wasu marubuta suke fada, ko wasu masu huduba, al’ummar Musulunci tana nan, godiya ta tabbata ga Allah “Wata kungiya bazata gushe ba daga al’ummata a kan gaskiya suna masu rinjaye” sai dai sha’anin (yana kasancewa ne) da komawa zuwa gareta da kuma shiga cikinta.


Muna rokon Allah – Mai girma da daukaka – Ya sanya mu da ku daga wadanda suke sanin gaskiya suke aiki da ita kuma suke riko da ita.


Nugdah ta karshe a cikin mauru’in da ta rage: Itace daga sabubban tsira daga fitintinu – kuma – shine yawan addu’a, musulmi ya yawaita addu’ar cewa Allah Ya kareshi daga fitintinu, hakika (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Ku nemi tsarin Allah daga fitintinu, abinda ya bayyana daga garesu da abinda ya boyu”, kuma (Annabi) tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – ya kasance a cikin tahiyar karshe yana neman tsarin Allah daga abubuwa hudu: Daga azabar Jahannama, da azabar kabari, da fitinar rayuwa da mutuwa, da fitinar Masihul Dajjal”.


To yana wajaba akan musulmi ya yawaita addu’a: Allah Ya kareshi daga sharrin fitintinu, abinda ya bayyana daga garesu da abinda ya boyu, kuma yayiwa Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – naci ya yawaita addu’a, domin cewa Allah – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Makusanci ne Mai amsawa, wanda ya fake gareShi Zai kareshi, wanda ya nemi tsarinSa Zai tsareshi, wanda ya rokeShi za’a amsa masa, Shi – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – Yana sauka kowane dare zuwa saman duniya har sai daya bisa uku na dare na karshe ya wanzu, sai Ya ce: Shin akwai mai tambaya in bashi, shin akwai mai addu’a in amsa masa, shin akwai mai neman gafara in gafarta masa, hakika Ya bude kofarSa – tsarki ya tabbatar maSa Ya daukaka – ga masu tambaya, dare da rana, sai dai wannan kari ne, karin dama ce Allah Yana bada ita ga bayinSa; dan jin kai garesu.


Musulmi ya yawaita rokon Allah – Mai girma da daukaka – a kowane lokaci, musammanma a cikin mafifitan halaye, da lokuta mafifita, halaye mafifita;  kamar sujjada, tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Amma sujjada to ku yawaita addu’a a cikinta, ya cancanta a amsa muku”, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce:  “Mafi kusancin abinda bawa yake kasancewa daga Ubangijinsa alhali shi yana mai sujjada, to ku yawaita addu’a”, ko kamar yanda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce, kuma da a cikin mafifitan lokuta misali: Karshen dare – sulusin dare na karshe – da karshen Sa’a daga ranar Juma’a, da bayan salloli.


Mutum ya yiwa Allah naci kada ya rafkana, kada ya rafkana daga addu’a. Musamman ma dai neman tsira daga fitintinu; domin cewa shi idan ya kubuta daga fitintinu to cewa shi ya kubuta daga dukkan sharri, idan ya kubuta daga fitintinu to Addininsa ya kubuta, idan Addininsa ya kubuta to karshensa ya kubuta.


A kowane hali dai: Fitintinu suna da yawa kuma nau’ika ne, masu kira zuwa fitintinu kuma suna yawaita, suna koyarwa kuma ana koyar da su, kamar yanda tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya ce: “Mutane ne daga fatarmu suna magana da yarukanmu”, masu kira zuwa fitintinu suna magana da yarukanmu, kuma mafi yawancinsu daga fatarmu ne daga larabawa ne, ko daga makusantanmu ne.. To yana wajaba akan mutum ya kiyaye kada ya rudu. Dukkan wanda yayi kira zuwa ga bata ko sabawa al-Qur’ani da sunnah to ka kiyaye shi, koda ya kasance mafi kusancin mutane gareka ne, kuma tsira da amincin Allah su tabbata agare shi ya bada labarin cewa hanyoyin da suka sabawa hanyar Allah akwai wani Shaidani akan kowace hanya da yake kiran mutane zuwa gareta, Shaidanun mutane, da Shaidanun aljanu suna kira zuwa ga bata, Madaukakin sarki Ya ce: {Wadancananka suna kira zuwa ga wuta, Allah Yana kira zuwa ga aljanna} . Shaidan yana kiran jama’arsa dan su zama daga ‘yan wuta, akwai masu kira a can ya wajaba a kanmu mu kiyayesu, kuma mu kiyaye daga shubuhohinsu, yana wajaba a kanmu mu koma zuwa Littafin Allah da sunnar ManzonSa, da kuma ma’abota ilimi; mudinga tambaya kan abinda ya rikice mana (na Addini), Madaukakin sarki Ya ce: {Ku tambayi ma’abota sani in kunkasance bakwa sani} , mu muna rokon Allah a cikin kowace raka’a daga sallarmu lokacin da muke karanta Fatihatul Kitab wacce ita rukuni ce daga rukunan sallah, karantata rukunine daga rukunan sallah, Allah – Madaukakin sarki – Ya ce: {Ka shiryar da mu hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Kayi ni’ima garesu ba wadanda akayi fushi a kansu ba ba kuma batattuba} .


Muna rokonSa Ya shiryar da mu hanya madaidaiciya, kuma Ya nisantar damu hanyar wadanda akayi fushi a kansu, da hanyar ma’abota bata, wadanda akayi fushi akansu: Sune malaman da basa aiki da iliminsu, batattu kuma: Sune wadanda suke aiki bada ilimi ba. Wadanda akayiwa ni’ima kuma: Sune ma’abota ilimi da aiki, sune wadanda Allah Ya fada a cikinsu: {Wanda yabi Allah da wannan Manzo to wadannan suna tare da wadanda Allah Yayi ni’ima garesu sune Annabawa da siddikai da shahidai da salihai kuma madalla da wadannan abokanai} .


Wanda aka datar ga hanyar Allah to abokanan zamansa sun zama wadancan zababbun, wanda ya baude daga hanyar Allah to wadanda akayi fushi a kansu da batattu sun zama abokanan zamansa, muna rokon Allah lafiya.


A nan akwai wata kalma (wacce) jagoran gidan hijira Malik dan Anas – Allah Yayi masa rahama - ya fadeta, kuma ita kalma ce mai girma yana kamata ga musulmi ya lura da ita, kuma yayi nazarinta, Allah Yayi masa rahama ya ce: (Babu abinda zai gyara karshen wannan al’ummar sai abinda ya gyara na farkonta).


Menene abinda ya gyara na farkonta? Shine Littafin Allah da sunnah, da bin Manzo – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, haka nan karshen wannan al’ummar lokacin da sharri da bata da kungiyoyi da jama’u suka yawaita, babu abinda zai gyarata sai abinda ya gyara jama’ar farko, kuma shi yana nan godiya ta tabbata ga Allah, abinda ya gyara jama’ar farko yana nan a hannunmu, shine Littafin Allah, da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, da komawa zuwa ga malamai wadanda suka kebanta da Littafin Allah da sunnar ManzonSa – tsira da amincin Allah su tabbata agare shi – dan su bayyana mana abinda ya rikitar a kanmu.


Ina fadin maganata wannan, kuma ina neman gafarar Allah gareni da ku, kuma ina rokon Allah Ya shiryar da mu da ku hanya madaidaiciya, kuma Ya nisantar da mu da ku hanyar wadanda akayi fushi a kansu da kuma batattu daga ‘yan wuta.


Allah Yayi dadin tsira Yayi aminci ga Annabinmu Muhammad, da alayensa da sahabbansa baki daya.





 



Posts na kwanan nan

FAHIMTAR ADDINI (SHIN ...

FAHIMTAR ADDINI (SHINE) TSARI DAGA FITINTINU 2

FAHIMTAR ADDINI (SHIN ...

FAHIMTAR ADDINI (SHINE) TSARI DAGA FITINTINU 1

ABUBUWAN DA SUKE WARW ...

ABUBUWAN DA SUKE WARWARE MUSULUNCI.

MUJALLADIN HUDUBOBIN ...

MUJALLADIN HUDUBOBIN JUMU’A NA WATAN RAMADAN DA HAUSA