Labarai
Babi na farko


Lallai dayawa daga cikin ayyukan mutane suna aikata su


ne karkashin inuwar shari'a na musulunci karkashin


hukunce hukunce masu zuwa a dunkule saboda hukuncin


aikin ya bayyana a garemu tsakanin halasci ko kuma


haramci:


1- Farilla: wannan shine kololuwa wurin martaba na


ayyukan bayi, shine duk wani abu da Allah ya nema aikata shi


wanda yake dole da wani dalili kai tsaye wanda babu shubuha a


cikin sa, kamar umurni da yin salla da azumi da karatun


alkur'ani, hukuncin sa shine lazumtar aikata haka da kuma


zuwa da abunda aka bukata daga bawa na wannan ayyuka tare


da samun lada akan aikatashi ko kuma zunubi akan wanda yaki


aikatashi.


2- Mustahabbi: shine dukkanin abunda Allah yayi umurni


dashi ba akan fuskar dole ba, ana bayar da lada ga wanda ya


aikata shi sannan kuma babu zunubi ga wanda be aikatashi ba,


kamar misalign asiwaki kafin fara salla.


3- Halal: shine dukkanin abunda babu lada akan aikatashi


ko kuma zunubi akan barin shi, kamar tafiya da hawan mota da


makamantan su na dukkanin abunda aka yarda da aikatashi


cikin ayyuka na al'ada na rayuwan mutum na yau da kullum.


4- Makaruhi: shine dukkanin abunda Allah ya hana hana


aikatashi ba akan dole ba, ana bada lada ga wanda yabar


aikatashi domin biyayya ga Allah kuma babu zunubi ga wanda


ya aikata shi, sai dai anason ya nesanta daga gareshi da kuma


abunda ya kunsa sai dai baza'a rubuta zunubi bag a wanda ya


aikata shi, sai dai yawan maimatashi da dogewa akan shi zai iya


sa mutum ke tare iyakokin Allah da kuma fadawa zuwa ga


abunda Allah mabuwayi da daukaka ya hana aikatawa, dalilin


da yasa baza'a rubuta zunubi ba ga mutumin daya aikata


5


makaruhi dukda cewa aiki ne wanda aka kyamace shi saboda


zai iya yayi ne domin biyan wanin lalura me girma da yanayi


na rayuwan mutum wanda zai sanya shi aikata wannan aiki da


yake makaruhi, misali ubangiji madaukaki yana kin saki amma


be haramta shi ba akan bayin sa domin fadada masu al'amuran


su idan akwai laluran aikata hakan.


5- Haramun: shine dukkanin wani aiki da Allah ya hana


aikatashi a fuskar wajibi da wani dalili kai tsaye wanda babu


wani shubuha a cikin sa, ana bayar da zunubi ga wanda ya


aikata shi sannan kuma akwai lada ga wanda yabar aikata shi


domin biyayya ga Allah, Kaman haramcin shan giya.


Banbanci tsakanin halal da haramun:


Lallai sanin halal da kuma banbanta shi daga haram shine


ginshiki na musulunci da kuma dalili akan imani, yana hade ne


da ayyukan zuciya kamar yadda kuma yake hade da ayyukan


gabbai, hukuncin asali na aikata abubuwa shine halal babu


haramun sai ga abunda dalili yazo ingantacce kuma a bayyane


akan haramcin sa, haramtawa da halastawa hakki ne na Allah


madaukaki, kasancewar sa shine mahalicci da reno da


saukakewa da bada ni'ima yana halastawa bayin sa abunda yake


so ya kuma haramta musu abunda yake so, sai dai saboda


rahamar Allah madaukaki da falalar daga gareshi ya sanya halal


da haram domin dalilai wanda ake iya hankalta wanda yake


komawa ga maslahar mutum, akan wannan Allah madaukaki be


halasta wani abu ba face me dadi kuma be haramta komai ba


sai datti.


Canzawar aiki daga wannan gida na hukunci zuwa wani


gida:


1. canzawar aiki daga halal ya koma gidan haramci ko


kuma akasin haka:


6


aiki na halal zai iya canzawa zuwa haramun idan aka samu


dalilai wanda zasu say a canza maimakon aiki ya zama me


kyau wanda rai ke sonsa zuwa aikin mummuna wanda yake


cutar da jiki, misali akan haka shine hukuncin sharia na yawo


akan hanya shine halal, sai dai zai iya canzawa zuwa haramun


idan wani shugaba na musulunci na wani kasa ya karrara


haramcin yawo daga karfe goma na dare misali akan wasu


tutuka ko kuma cikin wasu bira ne saboda wasu dalilai na tsaro


wanda zai iya kaiwa ga rasa ran mutum.


Aiki na haramun zai iya canzawa zuwa halal idan


aka samu dalilai wanda zai sanyashi haka na lalura domin


kiyaye rai daga halaka, kamar shan giya, shan giya hukuncin sa


haramun ne sai zai iya zama halal idan mutum ya bata hanya


acikin sahara ya kusan mutuwa saboda kishi kuma bai samu


ruwa ba sai giya, a wannan yanayi zai sha giyan nan


gwargwadon yadda zai kiyaye ran sa daga halaka amma kuma


bazai wuce wannan kima ba.


2. Aiki ya canza daga wajabci zuwa haramci ko kuma


akasin haka:


Aikin zai iya canzawa daga wajabci zuwa haramci, kuma aikin


na haramun zai iya canzawa zuwa na wajibi, saboda dalilai


wanda zai kawo hakan kamar yadda mukayi bayani a baya,


misali salla wajibi ne sai dai aikata salla zai iya zama haramun


idan mutum yayi salla a cikin gidansa a tsakiyar girgizan kasa


me tsanani wanda yana da tabbacin fa zai halaka idan dai be


fita daga wannan gidan ba da sauri!! Ko kuma ta'addanci ga


mutum na yanke masa kafa hakan haramun ne sai dai uziri na


rashin lafiya zai iya a yankewa mutum kafar sa domin ceton


rayuwan daga halaka to anan wurin yanke kafan wannan mara


lafiya ya zama wajibi akan likita domin masa magani idan


kuma be aikata hakan ba yana da laifi kuma Allah zai azabtar


dashi akan rashin yanke wannan kafa ta mara lafiya.


7


3. Canzawan aiki daga makaruhi zuwa zuwa mustahabbi,


da kuma canzawan aiki daga mustahabbi ko kuma sunna suwa


haramci:


Aiki na makaruhi zai iya canzawa zuwa mustahabbi ko kuma


wajabci, misali saki aiki ne wanda yake makaruhi a shari'a


Allah madaukaki yana kyamansa sai dai a wani lokutan rashin


sakin matan zai iya kaiwa zuwa ga haramun wanda babu wani


hanya da zai gusar da hakan sai sakinta, kamar idan mace ta


kasance me karancin kamun kai kuma ya kasa gyarata anan


wurin abunda yafi shine ya saketa, anan wurin aiki makaruhi ya


zama mustahabbi.


Aiki mustahabbi zai iya komawa haramun, misali yin asuwaki


aiki ne wanda yake mustahabbi amma zai iya zama makaruhiko


kuma haramun idan hakoran mutum suna ciwo zasu fita ya


kuma san cewa idan fa yayi asuwaki zasu fita, a cikin wannan


hali yin asuwaki yaci karo da ka'ida ta shari'a cikin musulunci


wacce tace (babu cuta kuma babu cutarwa).


A takaice:


A takaice da dunkule maganar da sharhin sa ya gabata


shine muslunci ba addini bane makaho wanda baya gani


kuma bay alula da uzirin mutane da ikon sun a rayuwa nay


au da kullum, lallai makanci ya hakika yana cikin idanun


makiyan sa ne wanda suke son yada shubuhohi da


kararyaki akan musulunci domin su rufe hasken Allah


kuma Allah sai ya cika hasken sa koda kuwa kafirai basaso.


Me yuwa ne yakai me karatu me karamci


kasan cewa musulunci ba addini ne ban a zalumci addini ne


na adalci, shi kuma adalci suna cikin sunayen Allah


kyawawa, saboda haka haramci da halastawa a cikin


musulunci sun ginu ne akan adalci ba akan makanta ba, shi


8


kuma zalumci baki dayan sa haramun ne a cikin shari'ar


musulunci.


9


Babi na biyu


A cikin hasken nassoshi na alkur'ani me girma Allah


madaukaki yayi umurni da kyautatawa ga mata da kuma


karramata da rayuwa da ita me dadi hatta bayan karewan


soyayya ta zuciya, Allah madaukaki yace: " kuyi zama dasu me


kyau da dadi, idan kun kyamaci su to wata kila fa kuna


kyamatan abu sai Allah yasa masa alheri me yawa"


(suratun nisa'i ayata 19)


Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " kada mumini ya


kyamaci mumina idan ya kyamaci wani dabi'a daga gareta zai


yarda da wasu". Muslim ne ya rawaito shi.


Allah madaukaki yayi bayanin hakkokin mata akan mijinta


kamar yadda mijin shima yake da hakkoki akanta, sai Allah


madaukaki yace: " suma sunada kwatankwacin abunda yake


kansu na kyautatawa"


(suratul bakara ayata 228)


Wasiyyar manzon Allah s.a.w ta kasance gabanin rasuwar sa da


kula da dama da karrama su da kuma rashin zalumtar su da


danne masu hakkokin su, manzon Allah s.a.w yace: " ina maku


wasiyya na alheri game da mata" muslim ne ya rawaito shi.


Ya kuma kara cewa s.a.w: " wanda yafi muminai cikan imani


shine wanda yafisu kyawawan dabi'u kuma zababbun ku sune


wanda suka kasance zababbu ga iyalan su" tirmizi da ibn


hibban ne suka rawaito shi, tirmizi yace hadisi ne hasan sahih


kuma yana cikin littafin sahihul jami'u lambar hadisi na: 1230.


10


An karbo hadisi kuma daga Aisha Allah ya kara mata yarda


tace: manzon Allah s.a.w yace: " mafi alherin ku shine wanda


ya zama mafi alheri ga iyalan sa kuma ni nafiku zama mafi


alheri ga iyalai na". Ibn hibban ne ya rawaito shi cikin littafin


san a sahihi da tirmizi hadisi na 3314 cikin littafin sahihul


jami'u.


Ya kuma yi umurni da hakuri akan kura kuran su da kuma


raunin hankalinta da kuma kawar dakai daga kaskancinta yana


me bayyana dabi'ar mace wanda Allah madaukaki ya halicce ta


akai, sai manzon Allah s.a.w yace: " lallai mace fa an halicce ta


ne daga kashin hakarkari, bazata taba mike maka ba, idan


zakaji dadi da ita kaji dadi da ita a haka a karkacenta, idan


kuma kace zata mikar da ita zaka karya ta ne kawai, karyata


shine sakinta". Muslim ne ya rawaito shi.


Ya kuma kara fadi har wayau cewa: " ina maku wasiyya na


alheri ga mata saboda an halicce su ne daga kashin hakarkari


kuma mafi karkacewar kashin hakar kari shine na sama, idan


kace zaka mikar dashi zaka karya shi idan kuma ka kyale shi


hakan zaici gaba da zama a karkatanshi, sabo da haka ina maku


wasiyya na alheri akansu". Buhari ne ya rawaito shi.


Maznon Allah s.a.w shine abun koyin musulmai wanda Allah


ya wajabta masu bin sunnar sa, Allah madaukaki yace: " hakika


kunada koyi na kwarai daga manzon Allah ga wanda yake


kwadayin samun rahamar Allah da rana ta karshe ya kuma


ambaci Allah dayawa".


(Suratul ahazab ayata 21)


11


Shine abun kuyi na kololuwa da kuwa dabi'a masu daraja Allah


ya aiko shi da addini mikakke kuma ubangijin sa ya


tarbiyyantar dashi ya kuma kyautata tarbiyyan sai ya kasance


abun kuyi wurin kyawawan dabi'u da halaye na gari, Allah


madaukaki yace: " lallai kana kan dabi'u masu girma".


(Suratul kalam ayata 4)


Yayi aiki da kyawawan dabi'un sa a aikace akan abubuwan da


suka faru ya sanyata kuma suka zama milali na gani, cikin fadin


sa s.a.w: " an aiko ni ne domin na cika kyawawun halaye".


Malik ya kawo shi cikin muwadda da kuma buhari cikin adabul


mufrad kuma yana cikin littafin sahihah lambar hadisi na (45).


Matar sa Aisha tana fadi game dashi wacce tasan bubuwan shi


mu'amala saba da sahabban sa: " dabi'un sa ya kasance alkur'ani


ne". ahmad ne ya rawaito shi cikin sahihul jami'a(4811), watan


yana bin umurnin da yayi yana kuma barin dukkanin abunda da


ya hana babu wata dabi'a ta kwarai wanda alkur'ani ya


kwataidar akanta face manzon Allah s.a.w ya kasance wanda


yafi kowa riko da ita, kuma babu wata dabi'a mara kyau wanda


alkur'ani ya hana face manzon Allah s.a.w ya kasance wanda


yafi kowa tsananin nisantar sa.


Hakika duk wanda yake bibiyan tarihin sa da lura cikin hadisan


sa masu daraja zai gani a bayyane cewa manzon Allah s.a.w ya


hana hakan kuma ya tsawatar akan haka matuka, matar sa


Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa game dashi: "


manzon Allah s.a.w be taba dukan komai ba da hannun sa ko


mace ko wani bawan sa me masa hidima sai dai yayi jihadi


12


fisabilillah. Kuma ba'a taba masa wani laifi ba ya rama sai dai


idan an keta hurumin Allah shine yake ramako domin Allah


madaukaki mabuwayi" msulim ne ya rawaito hadisin [ ma'anar


hadisin shine ba'a taba cutar dashi bay ace zai dau fansa ko


kuma ramuwa ba sai dai idan an keta iyakokin Allah sai ya


taimaki hakan ya kuma ladabta wanda ya keta su].


Kai hatta makiyan sa wanda suke kokarin bata da'awar sa da


kuma katange mutane daga gareta basu taba tabbatar da wani


abu akan haka ba wanda yake sabama abunda muka ambata.


Bari muka abunda wanda yafi kusanci dashi cikin mutane ya


kuma lazimce shi sosai wanda babu shakka dadewa da lazimtar


mutum zai bayyana maka halayen sa baki daya, hadimin sa


Anas dan malik yana cewa game dashi wanda yayi masa


hidima na tsawon shekaru goma:


" na yima manzon Allah s.a.w hidima na tsawon shekaru goma


amma be taba cemun ba kul ko sau daya, kuma be taba cemun


ba game da wani abu dana aikata me yasa ka aikata ko kuma


abunda ban aikata ba yacemun me yasa baka aikata shi ba?


Manzon Allah s.a.w ya kasance yafi kowa kyawawun dabi'u


cikin mutane" muslim da tirmizi ne suka rawaito shi.


13


Babi na uku


Lallai inda ake samu dalilai a musulunci shine cikin nassosi na


littafin Allah madaukaki da sunnar manzon sa in gantacce me


daraja amincin Allah ya tabbata a gareshi da sahabban sa da


iyalan sa, daga cikin wannan abubuwa biyun ne zamu kafa


hujja dasu wanda a karkashin su ne zai bayyanar mana


hukuncin dukar mace a cikin musulunci shin hakan wajibi ne


ko kuma mustahabbi ko halal ko makaruhi ne ko kuma


haramun daga cikin hadisin da Iyas dan Abdullahi ya rawaito


inda yace: manzon Allah s.a.w yace: " kada ku rika dukan


bayin Allah mata, sai umar yazo wurin manzon Allah s.a.w


yace masa: mata suna bijirewa mazajen su, sai yayi ramgwame


akan dukan su sai gidan manzon Allah s.a.w ya cika da mata


suna kawo koken mazajen su, sai manzon Allah s.a.w yace: "


hakika gidan Muhammad fay a cikia da mata suna kokawa akan


mazajen su to wa'innan basu basa cikin zababbun su". Abu


dawud da ibn majjah da darimi ne suka rawaito shi, albani yace


hadisi ne ingantacce.


A karkashin sharhin wannan hadisin me dajara zai abubuwa


Kaman haka zasu bayyanan mana:


Lallai hadisin nan na manzon Allah me girma be fade shi ba a


lokaci gudu kuma a zamani daya, ya fadeshi ne s.a.w cikin


zamani guda uku mabanbanta:


Zamani na farko: manzon Allah s.a.w yace a cikinta " kada ku


rika dukan bayin Allah mata" wannan shine karshen zamani na


farko da wuri na farko.


A bisa da haka duk wanda yaji wannan maganar daga manzon


Allah s.a.w zai sani cewa lallai hukuncin dukan mata a


muslunci haramun saboda manzon Allah s.a.w ya hana kuma


14


duk wanda ya aikata hakan ya sabama Allah kuma za'a hukunta


shi saboda ya sabama wannan umurni na manzon Allah s.a.w.


Zamani na biyu: zuwan Umar dan kaddab Allah ya kara masa


yarda a lokacin da ya sabawa lokacin farko wanda manzon


Allah s.a.w yace acikin sa: " kada ku rika dukan bayin Allah


mata" domin kawo kuka akan mata da cewar sa: mata suna


bijirewa mazajen su. Watan ma'ana basa bin umurnin su kuma


suna kausasa masu da magana kuma sun galabe mazajen su,


anan ne manzon Allajh s.a.w yayi rangwame da dukan mata


saboda amfani da yayi da ra'anin sa na fiqhun zamani da lalura


na rayuwa wanda rayuwa bazayyiwu ba sai dashi, sai dai kuma


yaye yanayin wannan duka yake? Wannan shine abunda


zamuyi magana akan sa nan bada jimawa ba.


Zamani na uku: bayan izinin manzon Allah s.a.w ga, mazaje


da kudan matan su wanda suke saba masu da bijirewa akan


mazajen su, sai mata dayawa sukazo gun manzon Allah s.a.


yana kokawa akan mazajen su, sai manzon Allah s.a.w yace: "


hakika gidan Muhammadu ya cika da mata suna kokawa akan


mazajen su lallai wannan mazajen basa cikin zababbun cikin


ku"


Wannan shine zamani na karshe wanda hukuncin haramcin


dukan mata ya bayyana a cikin musulunci wanda hakan


makaruhi ne da kuma haramun idan mijin ya ketare iyakokin


Allah -wanda zamuyi bayanin haka nan bada jimawa ba- shin


za'a fahimta cikin wannan nassin hadisin cewa manzon Allah


s.a.w ya kwadaita akan dukan mata? Ko kuma yayi shagube ne


ga dukkanin me dukan matar sa? Lallai cikin maganar sa s.a.w


akwai rashin mugunta da kuma kore alheri ga mutumin dake


dukan matar sa?!!!


Hakika sahabbai Allah ya kara masu yarda sun fahimci isharar


wannan maganar ta manzon Allah s.a.w kuma sun gane cewa


lallai duk wanda yake dukan matar sa bazai taba samn yardan


15


da kyautatawa ba daga manzon Allah s.a.w, babu shakka kuma


cewa duk abunda manzon Allah s.a.w be yarda dashi ba to yana


cikin hukuncin makaruhanci me tsanani wanda hakan zai iya


kaiwa zuwa ga haramun.


Hasali ma a lokacin da mijin Fadima ditar kais ya saketa wasu


mutum biyu sun zo sun nemi aurenta wanda sune mu'awiya dan


abu sufyan da Abu jahmin da usama dan zaid Allah ya kara


masu yarda, a lokacin ne manzon Allah s.a.w yace mata: " shi


mu'awiya mutum ne talaka, shi kuma abu jahmin mutum ne me


yawan dukan mata amma shi usama dan zaid" sai ta fada da


hannun cewa: usama! Usama!". Muslim ne ya rawaito shi.


Hakika mun gani yadda yake cewa asali da hukuncin farko


akan dukan mata haramun ne sa'annan ya canza ya zama halal


saboda wasu dalili da magani na musamman wanda suka sanya


hakan daga nan kuma ya canza zuwa makaruhanci babba, sai


dai yaushe ne dukan mace yake zama haramun? Dukan mace


yana zama haramun ne idan ya kasance najin ciwo maimakon


wanda zai ladabtar kawai ba tare da jin ciwo ba lallai dukkanin


ta'adi cikin musulunci haramun ne idan ya kasance zalumci ne


ko kuma muganta, Allah madaukaki yace cikin littafin sa me


hikima yana tsawatarwa gane da dukkanin nau'in zalumci: "


duk wanda yayi zalumci daga cikin ku zamu dandana masa


azaba me girma"


(suratul furkan ayata 19)


16


Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa: " kuji tsoron zalumci


domin kuwa zalumci duhu ne ranar alkiyama" muslim ne ya


rawaito shi.


An kuma karbo hadisi daga Anas Allah ya kara masa yarda


yace: manzon Allah s.a.w yace: " kuji tsoron addu'ar wanda aka


zalumta koda kuma kafiri ne saboda addu'ar sa bashi da wani


shamaki tsakanin sa da Allah". Ahmad ne ya rawaito shi kuma


albani ya inganta shi.


Musulunci ya haramta cutarwa koya yake da dukkanin surorin


sa da nau'ukan sa shin na magana saboda fadin Allah


madaukaki cewa: " lalllai wanda suke jifan mata muminai


kamammu wanda babu ruwan su an tsine masu duniya da lahira


kuma suna da azaba me girma".


(Suratun nur ayata 23)


Ko kuma cutarwa na jiki da kuda da makamantan sa sai idan ya


kasance a bisa hakki ne, saboda fadin Allah madaukaki cewa: "


wanda suke cutar da muminai maza da mat aba tare da wani


laifi ba to haki sun daukan ma kansu nauyi da zunubi


bayyananne"


(suratul ahazab ayata 58)


Wannan haramcin ya shafi kowa cikin mutane maza da mata


kanana da manya musulmi da kafiri, an karbo hadisi daga abi


huraira Allah ya kara masa yarda daga manzon Allah s.a.w


yace: " musulumi shine wanda mutane suka kubuta daga


sharrin harshen sa da hannun sa mumini kuma shine wanda


mutane suka amince masa akan dukiyar su da jinin su".


Sanunan al nisa'i, sheikh albani yace hadisi ne hasan sahih.


Duk wanda yace musulunci yana ta'addanci ko kuma mugunta


ko dukan mace to hakika yayi kage ga addinin Allah karya me


girma.


17


Alkalanci ta musulunci yana daukan al'amarin dukan mace da


cutar da ita daga wurin mijinta da matukar muuhimmanci


sannan kuma beyi kasa a gwewa ba wurin hukunta ladabtarwa


ga miji akan me ta'adi da zalumci da mugunta ba akanta kuma


yana dabbaka shi a aikace da hukunci na shari'a a duk lokacin


da aka kawo kara akan haka, misali wannan kararraki masu


zuwa:


1- Sharidar riyad ta yada akan shafinta na intanet a kwanan


wata 12/12/2012 labari kamar haka:


Kotun koli akan laifuffuka na yankin jihar katif cikin kasar


saudiyya tayi hukunci akan miji akan ta'addancin da yayi ma


matar sa na duka da cewa za'ayi masa bulala 30 a idon mutane


saboda haka ya zama izina ga masu ta'addanci akan matar su,


sannan kuma tayi masa hukunci har wayau da zai karantar a


daya daga cikin makaruntu na gaba da sakandire a fannin


mu'amala tare da matan aure da kuma al'amarin iyali, sannan


kuma zai gabatar da jarabawa na rubutu wanda zai sanya shi a


cikin fayel din wannan shari'a.


Akan irin wannan matsala dukkanin kotuna cikin garuruwan


musulmai baki daya suna hukunta miji wanda yayi ta'addanci


ga matar sa da duka, ta dayan bangaren kuma matan da suke


tsoratar da mazajen su da nuna su da makami ko kuma niyyar


cutar dasu da makirci ga mazajen su ana masu hukuncin bulala


ba dayawa ba daganan kuma akaisu wurin yan sanda domin


wannan aiki nasu da sukayi ma mazajen su idan mijin ya


barranta daga wannan tuhumar.


18


Abunda muke so a cikin wannan hukunci shine lallai musulmi


me hankali wanda yake bin karantarwan musulunci baya yarda


da zalumtar mace ko kuma yi mata ta'addanci, kamar yadda


addinin mu ya be karantar damu ba ko kuma umurtan mu da


hakan sai dai ya haramta mana hakan ya kuma sanya hakan


cikin ayyukan zalumci na haramun, hasali ma ya umurce mu ne


da hakuri da yafiya da kawar dakai da kuma sakayya akan laifi


da kyakyawan aiki, dukda cewa musulunci be sanya dukan


mace ya zama halal ba ya dai sanya shi ya zama a wasu lokutan


kadai ya kamata ayi hakan idan ya rayuwan ma'aurata bazai


gyaru ba sai dashikuma ya kayyade hakan da sharudda wanda


zai sanya hakan ya zama yayi karanci sosai domin tabbatar da


burin daya wanda shine kiyaye gida da kuma ladubban jama'a


cikin al'umma baki daya.


19


Babi na hudu


Mutum zai iya cewa shin baya fi dacewa ba da namiji ya rika


yima matar sa wa'azi idan ta bijire maimakon dukanta, sai muce


mas aba haka bane wannan shine hukuncin Allah madaukaki


me buwaya wanda yace cikin littafin sa me hikima:


" Wanda kuma kuke tsoron bijirewar su kuyi masa wa'azi a


farko sannan ku kaurace masu a wurin kwana sannan kuma ku


duke su, idan kuma sunyi maku biyayya to kada kirkizo wani


hanyar cutarwa a gare su, lallai Allah ya kasance madaukaki ne


me girma".


(Suratun nisa'i ayata 34)


Manzon Allah s.a.w kuma yace cikin hajjin san a bankwana:


" ku saurara kuji ina maku wasiyya na alheri game da mata


domin lallai suna rayuwa ne akarkashin ku amma baku mallaki


komai ba da ya wuce haka game dasu, sai dai idan sunzo da


alfasha bayyananne, idan suka aikata haka to ku kaurace masu


a wurin kwana sannan kuma idan basu shiryu ba sai ku duke su


duka bana jin rauni ba, idan kuma sukayi maku biyayya to kada


ku kirkiro wata hanyar zalumci akan su. Ku saurara kuji lallai


kuna da hakki akan matan ku haka suma suna da hakki akan


ku" tirmizi ne ya rawaito shi, albani yace hadisi ne hasan.


Haka zamu rika ganin yadda Allah madaukaki me hikima yake


bayyana mana cikin hikimar sa masani ga harkokin bayin sa da


manzon sa me daraja hanya domin magance matsalolin mace


wanda ta bijire a hankali har zuwa matakai uku:


1. Mataki na farko:


20


Ya nuna ma miji hanyar wa'azi da nasiha a matsayin mafita na


farko domin gyara macen da ta bijire kafen kaurace mata a


wurin kwana wannan matakan wajibi ne binsu a jere a wurin


mafiya yawan malaman fiqihu, ya wajaba akan namiji ya


kusanci zuciyar matar sa da maganganu masu dadi da kuma


jiyar da ita abunda zai lallashi zuciyar ta ya kuma nuna mata


muhimmancin ta a wurinshi da cewa lallai yanasonta da alheri


yana mata nasiha ya kuma aiwatar da ikon sa akan mata nasiha


da wa'azi wurin ganin cewa ya gyara halinta, musani cewa fa


wa'azi baya zuwa daga busashiyar zuciya ko kuma da usulubi


mara kausasawasai dai yana samuwa ne da magana me dadi da


kuma mu'amala kamar siyan kauta ga mace har ta amshi


maganar mijinta da zuciya daya kuma cikin yarda,hakika ya


wajaba akan mace me kwakwalwa da dabi'u kyawawa data


wa'aztu daga maganar mijinta tana kallon makomar gidanta da


yaranta, amma idan mace ta kasance me taurin kai me


mummunan hali to nasiha baya amfanar da ita ko kuma wa'azi


ko fadakarwa sai mijin ya aikata abunda zai iya cikin haka sai


ya tafi zuwa mataki na biyu cikin jerin kamar yadda Allah


madaukaki ya umurce mu dashi wanda shine kaurace mata a


wurin kwana.


2. Mataki na biyu:


Miji ya bi hanyar kwarace wa a wurin kwana watan ya juya


mata baya kuma kada ya kusanceta har na tsawon kwana uku


amma kuma kada ya wuce kwanaki uku saboda fadin manzon


Allah s.a.w cewa: " baya halatta ga musulmi daya kaurace ma


dan uwansa sama da kwana uku". Muwadda da buhari da


buslim duk sun rawaito shi.


Domin ya tsawatar mata akan aikinta wannan shine mataki na


biyu kuma damace ga matan domin ta gyara cikin wannan


lokaci na tsawon kwanaki uku, idan ta gyara halinta to ya


wajaba a gareshi dana yanke wannan kaura nashi ya yafe masa


21


da nasiha idan kuma taci gaba dayin girman kai da dagawa ya


zama wannan kauracewan da yayi mata be amfanar da komai


ba sai na tafi zuwa mataki na uku.


3. Mataki na uku:


Idan miji yayi kokarin gayra wannan mata nashi ta hanyar


nasiha da wa'azi da kyawawan magana da kauta duka amma


babu amfani sannan ya kaurace mata a wurin kwana amma


duka shiru ya kuma bayyana mata rashin yardanshi da aikinta


shima be samu nasaraba, to anan wurin an yardan ma miji daya


ladabtar da matan da duka wanda banajin ciwo ba ko kuma yi


mata wani lahani, hakika malamai inyi ittifaki akan wajabcin


bin wannan matakai a jere wurin warware matsalar mace wanda


ta bijire wanda sune wa'azi a matakin farko sai kaurace mata


sannan idan bata gyara ba sai duka, Ada'u yace nace ma ibn


Abbas menene duka mara cutar wa? Sai yace mun shine duka


da asiwaki da makamantan su!! Hasanul basari yace: ma'ana


duka bame tasiri ba. Dan Allah dai ya kai makaranci me daraja


shin duka da asuwaki yakai ace masa duka na mugunta da


rashin tausayi abunda bai wuce tsayin pensir ban a rubutu?


Idan dai kana daukan duka da pensir a matsayin duka na


mugunta da rashin tausayi to kazoo mugani baki dayan mu


dakai sau nawa muke gani a cikin gidajen talabijin na holanda


da sauransu suna sawwara mana labarin miji wanda yayi fishi


da matar sa ko kuma tsakanin sa da abokin sa ko kuma wata


mata ko shugaban kamfani da ma'aikacin sa wanda muke gani a


cikin labarin wannan mutumi zai daura yatsantsa manuni akan


kirjin sa yana masa kashedi ko kuma sanya pensir a kirjin sa


wani loakci ma har abun yakai ga mari, hakan na faruwa cikin


dayawa daga cikin finafinai idan miji yayi fushi da matar sa


hakan na kaiwa ga mari me karfi a fuskanta sa'annan ya bar


wurin, amma wannan dukkunin sa turawa basa daukan sa a


matsayin mugunta kawai yanayi ne yakai mijin nan da marin


matar sa, kuma kaga suna daukan wannan mutumi a matsayin


22


mutum wayayye, duk da cewa mari a fuska haramun ne a


musulunci sai dai suna fada ne da musulunci suna fadin karya


akansa cewa yana koyar da rashin tausayi.


Duk da cewa musulunci yaba namiji damar amfanin da ikon sa


na ganin ya gyara wannan mata cikin matakin farko dana biyu


sannan na uku lallai musulunce yaba wannan matar hakki na


neman saki tun kafin akwai ga wannan mataki abunda yake kira


da suna khul'i idan ta iatce ta nemi hakan daganan kuma sai ta


yanke ma kanta hukunci inane zata gaba: wannan shine abunda


zamuyi magana akansa nan gaba da yardan Allah madaukaki.


Masani fa cewa nasiha da kauracewa sannan duka bashi bane


hanyar warware matsaloli nay au da kullum ba tsakanin


ma'aurata, wannan hanya ce ta warware manyan matsaloli a


tsakanin su, misali da ace miji zai cema matar sa ki girka mana


shinkafa yau da kifi sai ta manta ta girka shinkafa da kaza shin


wannan ayar zai tabbata akanta da yayi mata nasiha sannan ya


kaurace mata sai kuma duka?!!!!


Amsar itace a'a, wannan al'amura ne kanana wanda ya wajaba a


rika yafiya akai ba tare da ladabtarwa ba, amma kuma idan


matan ta kasance bata da halaye na gari me girman kai sannan


mijin ya fara ganin ta fara ayyuka na bijirewa da girman kai da


saba masa!! Mu anan muna magana ne akan mace wanda ta


bijire wacce take bukatan nasiha da shiryarwa da magani akan


matsalolinta kamar mara lafiya ne wanda yake bukatan magani,


muyi kaddar cewa wannan mata wanda ta bijire mijin yayi


nasihar da kauracen wa da duka na tsawon lokaci taki gayruwa


shin sakinta shine yafi ko kuma duka wanda bana cutarwa


ba?!!!! Idan duka ya kasance harara gefe shi kuma saki


makanta to lallai me harar gefe yafi makaho kuma da za'a bar


wannan mata akan halinta zata tarwatsa iyalan nan da al'umma


baki daki!!


23


Babi na biyar


Tun gabanin kungiyar kare hakkin dan adam ta duniya ta gara


yaki da mugunta tsakanin ma'aurata da yara hakika musulunci


ya rigata da hakan yadda yayi yaki dashi ya kuma haramta shi


da tanadar wa me aikata hakan da ukuba nan duniya dana lahira


bawai haramta hakan ya tsaya bane akan aikin kawai a'a hatta


magana wanda ya shafi hakan yana cikin wannan haramci


wanda hakan yafi zama kamala akan dokokiwanda suke yin


ukuba na duniya kawai tun gabanin shekaru 1400 da suka wuce


manzon Allah s.a.w yace: " musulmi shine wanda musulmi ya


kubuta daga sharrin harshen sa da hannun sa, mumini kuma


shine wanda mutane suka aminta masa akan jinin su da dukiyan


su" Ahmad da tirmizi ne suka rawaito hadisin, albani kuma ya


ingantashi.


Ya kuma kara cewa har wayau: " ba mumini bane me yawan


suka ko kuma tsinuwa ko alfasha ko kuma mara kama kai".


Buhari ne ya rawaito shi cikin adabul kadi da tirmizi kuma


albani ya inganta shi.


Me tambaya zai iya tambaya cewa ta yaya musunci ya hana


mugunta amma kuma ya halatta miji ya duki matar sa?!!


Game da amsan wannan tambaya ya kamata muyi bayani a


farko banbanci tsakanin abunda duka yake nufi a cikin rayuwan


mu ta yau da ma'anarta a cikin shari'ar musulunci, a cikin


rayuwan mu tayau idan mutum yaji cewa mutum ya duki matar


sa abunda zai zo a tunanin sa shine wannan aiki na rashin


tausayi ne da mugunta da zalumci na wannan miji wanda yakai


sa da dukan matar sa sannan yanayin wannan mata da mijinta


ya zalumta da duka shine ya jijji mata ciwuka dukkanin jikinta


da karaya, wannan shine ma'anar duka a rayuwan mu ta yau


24


wanda muka samo shi dilimin mu da rayuwan mu da cewa


shine misalign daya duki matar sa, amma idan nace maka na


duki karar rawan kowa shin zata fahimci cewa tana ta'addanci


ga wannan kofa?!! Sannan idan nace maka zan duke misali shin


zaka fahimci cewa zan maka ta'adi ne irin haka?!! Kenan


Kalmar duka tana cancanzawa gwargwadon yadda akayi


amfani da ita a harshen wannan mutane da kuma dabi'ar


wannan mutumi dukkanin wannan zai zo cikin tunanin mu akan


ma'anar duka, saboda haka ma'anar duka a musulunci yasha


banban gabaki daya da ma'anar sa cikin rayuwan mu nay au


wanda hakan haramun ne kuma ta'addanci ne a cikin musulunci


sosai, wannan ma'anonin bazasu taba haduwa ba har Abadan


idan munason yin adalci saboda haka ya wajaba muce babu


dukan mata ga miji acikin musulunci kuma ba'a yardan masa da


wulakantata ba ko kuma muzguna mata ko yi mata magana da


kalamai marasa dadi, ma'anar duka a musulunci yana nufin


duka dan kadan kamar misalign dukan karar rawa wanda ake


nufin isharantar da matan dashi da cewa lallai tanayin kuskure


cikin hakkin mijinta sannan kuma mijin yanada hakki na


gyarata da daidaita ta, kuma hakika musulunci ya gindayawa


miji matakai na warware matsalolin mace wanda ta bijire


wanda matakai ne da suke gabanin duka ya sanya duka shine


shine mataki na karshi ga duk macen da bata gyaru ba har zuwa


wannan mataki, kuma musulunci ya zo da tsawatar wa da


hukunce hukunce na shari'a ga mijin da ya wuce gona da iri


yadda zai zama me sabo me ketare iyakokin Allah madaukaki


wanda ya cancanci a azabtar dashi duniya da lahira wannan


matakai kuwa sune:


Dokokin ladabtar wa da duka:


1- Bi mataki bayan mataki wurin warware matsala ta


hanyar yin kokarin sa wurin matakai na farko dana biyu wanda


suke gabanin duka da yin wa'azi da fadakarwa sa'annan kaurace


mata a wurin kwana.


25


2- Dukan ya kasance da asiwaki ko kuma makamancin


haka wanda dan kara ne da be wuce tsayin pensir din rubutu ba


da fadin sa.


3- Nisantar fuska wurin duka ko kuma gabban da ake ji


dasu, saboda musulunci ya hana dukan fuskar na miji ne ko


mace ko kuma dabbobi, saboda fuska tana da daraja sannan


kuma taba shi yana cutar da ganin mutum kamar yadda aka


haramta dukan gabbai wanda ake ji dasu na jiki kuma an


tsananta akan hakan, wannan sune iyakokin Allah duk kuma


wanda ya ketare su to yayi zunubi.


4- Wurin dukan kada ya zama a idon mutane cikin ko wani


hali, baya halatta miji ya duki matar sa a gababan mutane


musamman yaransa, saboda hakan akwai wulakanta matar


acikin sa a karon farko sannan kuma jawo lallacewar tarbiyyan


yaran, wani irin tarbiyya ce wannan uba keyi da dukan


mahaifiyar su a gaban su ko kuma a kunnan su?!!!


5- Kada dukan ya zama me cutarwa wanda zayyi mata


tabo a jiki ko kuma karaya ko ciwo, duk mijin daya jima matar


sa ciwo ko tabo ko karaya yayi zunubi kuma wannan miji mugu


ne me bushashen zuciya wanda bayason gyaruwan matar kawai


hukuntata yake sonyi sannan kuma ya jawo kiyayya sannan


kuma shari'ar musulunci me adalci ta wajaba a tuhume shi da


kuma hukunta shi akan haka.


26


Babi na shida


Lallai maganar dukan mace ba matsala ce wacce ta shafi wani


lokaci ba ko zama daya kawai ba cikin al'umma guda daya, a'a


wannan matsalatra kwaita cikin dukkanin al'ummomi na


dukkanin zamani baka daya, kuma duk wanda yakeson sani


darajar mace cikin al'ummonin da ana samun littattafai dayawa


wanda sukayi magana akan hakan, game da darajar mace kuma


cikin al'ummar girka da rumawa da china da hindiya na da


can… zuwa dai karshen su, sannan kuma akan haka yaya


addinin yahudanci da kiristanci suka mu'amalaci al'amarin


dukan mace wacce ta zama matsala wanda aka saba kuma tana


yaduwa cikin al'umma tsofaffi har zuwa al'ummar shugaban mu


almasihi, shin shugaban mu almasihi amincin Allah ya tabbata


a gareshi yayi magana akan haramcin dukan mace koda sau


daya?!!! Kuma shin akwai nassoshi cikin littattafai masu tsarki


ltsohon alkawari ne ko kuma sabon alkawari wanda ya haramta


ko kuma kyamatan dukan mace?!! Bayan bincika zai bayyanan


maka cewa babu wani abu wanda yake nuna haka.


Idan kirista ya duki matarsa shin yayi sabo sannan za'a hukunta


ta fuskan addini wanda hakan itace ukubansa wanda nassi yazo


dashi cikin littafi me tsarki? Hakika bayi sabo ba saboda babu


wani nassi wanda yake nuna hakan cikin littafi masu tsarki shin


tsohon alkawari ne ko kuma sabon alkawari!!


Kamar kuma yadda babu wani hukunci ta bangaren doka na


ukuba akan mijin daya duki matar sa sai dai idan alamar


ta'addanci ya bayyana a jikin matar kamar karaya ko kuma


kunburi ko ciwo, amma idan babu wani alama wanda ya


bayyana a jikinta to tayaya za'a tabbatar da dukan nan nashi


dayayi mata!!! Ma'ana idan yayi mata duka wanda babu ciwo


ko karaya acikin sa baza'a mai wani ukuba baa nan duniya ko


kuma cikin dokakin su!!!


27


Mu duba mugani cikin yahudanci da buzanci shin akwai wani


nassi wanda yake haramta dukan mace?!!!


Hakika babu wani nassi na addini cikin ko wani addini wanda


yake haramta dukan mace sai cikin musulunci kadai!!!!!! Kafin


ko bayan dukan mace ya tashi daga hukuncin haramci ne zuwa


makaruhanci dukda haka dai musulunci shi kadai ne wani


addini wanda ya nassanta akan kyamar dukan mace!! Amma


sauran addinan babu furta ba kai tsaye haramci ko kuma


kyaman haka a wurin su.


Kamar yadda babu wani addini wanda ya shinfida dokoki ya


iayaka wurin dukan mace sai musulunci kawai, watan ma'ana


idan miji kirista ya kasa mallakan zuciyar say a duki matan sa,


to menene tsari ko kuma iyaka wanda baya halatta ya ketare


su? Shin kiristanci ya nassa akan dokoki da iyaka ga miji na


dukan matan sa kamar ace kada ya duki fuskanta ko kuma yayi


mata rauni wanda zai bar mata tabo ajiki… da sauarn su?


Hakika babu hakan.


Duk me lura da rayuwan mu nay au wanda muke ciki sai ga


akwai wasu adadi na kiyasi game da dukan mata wanda mazan


kiristoci sukeyi ko kuma yahudawa ko kuma sauran su wand


aba musulmai ba, kaje ka bincika cikin hukunce hukunce da


kararraki a gaban yan sanda ko kuma kotu a amerika da


kasashen turawa zakaga adadi wanda aka kiyasta na dukan


mata wanda mazaje marasa tausayi suke yima matan su da


yaran su!!!


Hatta a cikin al'ummar jihiliyya gabanin zuwan musulunci zaka


samu cewa larabawa suna zane matan su irin bulalan da sukeyi


ma bayin su kuma hakan ya zama sananne ko al'ada wanda ba


haramun bane ko kuma akwai hukunci akan haka na wani


shari'a ko kuma wani doka, a lokacin da aka aiko Muhammad


s.a.w ya hana wannan aiki hanawa me tsanani sai yace: " shin


dayan ku zai duki matar sa da dara da gangan kamar yadda


yake dukan zane bawan sa sa'annan kuma ya kwanta da ita a


cikin daren", buhari da muslim ne suka rawaito shi amma


28


lafazin na buhari ne, a cikin wannanhadisi manzon Allah yana


raddi game dukan matar sa cd rana sannan kuma da daddare


yana neman ya kwanta da ita!! Watan ma'ana taya zaka zama


mugu me baki hali da ita da rana amma kana son ta manta


hakan da daddare ka lallashe ta!!.


Sau dayawa abunda mutanen addinin kiristanci suna sawwara


mana shine shugabammu almasihi amincin Allah ya tabbata


agareshi shine mutumi na farko wanda ya fara karewa mace


hakkokinta kuma shine wanda ya bata hakkokinta wanda babu


wani addinin da suka bata irin sa, kuma littafi me tsarki ya mata


adalci sannan ya kuma daga darajarta!!! Sai dai kuma shin


wannan maganar yana daidai da aikin mu na yanzu?!!!


Kowa ya sani cewa littafi me tsarki ya haramtawa mace shiga


cikin tsarin shugaban cin coci wanda shine shugaban masu


tsarki ko kuma meyin yankan me tsarki, shin wannan mace


karama ce ko budurwa ko tsohuwa, al'amarin bashi da alaka da


shekaru ko kuma jinsin mata, babu wani littafi cikin littattafai


amsu tsarki na tsohon alkawari ko kuma sabon alkawari wanda


yayi ishara da shigan mace cikin tsarin shugabancin coci, bare


kuma a bata daman a zama cikin malaman addini, mace asali


ma ba'a mata izinin magana ba a cikin coci ko kuma karantan


wani abu cikin coci kuma ba'a bata izinin neman wani matsayi


ban a manyan malaman coci kawai matsayin da aka yardan


mata da nema shine mataimakan malamai wanda matsayi ne


nayin hidima ga malamai!!!!! Hakika littafi me tsarki ya


gabatar mana da nau'oka na malaman su dukkanin su mazaje ne


29


shin manyan malaman ne na farko kamar Nuhu da Ayyub da


Ibrahim da Ishaq da yakub, ko kuma kuma malaman haruniyya


ne ko kuma malaman malikus sadik, ko kuma malaman


manzanni da khalifofin su na kasa kasa, dukkanin su mazaje ne,


sannan da ace za'a ba mace matsayin malanta da shugabarmu


Maryam akaba itace tafi cancanta da wannan matsayi sai dai


karkashin karantarwan addinin kiristanci an haramta ma mace


haka!!!!!


Bari mu kawo wasu daga cikin nassoshi cikin littattafai


masu tsarki domin muga matsayin mace a cikinta da


darajar ta:


1. Mace ana azabtar da ita da laifin namji:


Safar na Irmiya (23:34): " annabi ko kuma wani mahaluki ko


mutanen da yake cewa: wahayin Allah, za'a azabtar dashi da


iyalin sa"


2. Kona mace mazinaciya da wuta:


Safar al lawiyyin (9:21): " idan wani mahaluki ya tayi sabo na


zina to hakika tayi datti a kona ta da wuta"


3. Yanke hannun mace da wasu dalila wanda hankali


baya dauka:


Safar al tasniya (11:25): " idan mutane biyu sukayi fada da


juna mutum da dan uwan sa sai matar daya daga cikin su tazo


wurin domin ta kwaci mijinta sai hannunta yayi tazar ce ta


kama al'aurar sa, za'a yanke mata hannu kuma za'a tsire idanun


ta".


4. Macen da aka saketa da ita da tsohuwa mara aure


da mazinaciya duka daya ne:


Safar al lawiyyin (9:21): " duk wani mutum me girma …..,


wannan yana auren mace ce tsarki. Ita kuma mace tsohuwa


30


mara aure ko wanda aka saka ko me daddi ko mazinaciya to


kada ya aure daya daga cikin su, sai dai ya aure masu tsarki


daga mutanen sa, sannan kuma kada ya bata shukar sa a


tsakanin kafafuwar sa saboda ni ne ubangiji me tsarki".


5. Bautar macen da aka saka ga mijinta:


Sakon bulus zuwa ga mutanen afsis (5:22): "yaku mata kuyi


bauta ga mazajenku kamar ubangiji, saboda namiji shine


shugaban mace kamar yadda masihi shine shugaban coci kuma


shine me tsarkakejiki. Sai dai kamar yadda coci take bauta ga


masihi, haka mata zasu rika bautan mazan su cikin komai"


6. Wajabtawa mace yin shiru cikin coci:


Sakon bulus na farko zuwa ga mutanen kurunsus (14:34): "


matan ku su rika yin shiru a cikin coci, saboda ba'ayi mata izini


ba da magana kawai bauta zasuyi kamar yadda namus yace. Sai


dai idan suna son sanin wanin abu to su tambayi mazajen su a


gida, saboda abun kyama ne ga mace tayi magana cikin coci".


7. Mata sanadi ce ta bata:


Sakon bulus na farko zuwa ga timosayis (11:2): " mata su


koyi shiru cikin bauta. Sai dai ba'ayima mace izini ba da neman


ilima ko kuma ta shugabanci namiji, ta zauna shiru kawai,


saboda adam aka fara halitta sannan sai hauwa. Kuma adam


beyi laifi ba mace ce tayi laifi sai ta'addanci ya auku. Sai dai


wannan zunubi nata zata tsakaka daga garesu da haihuwan yara


matukar sun tabbata cikin imani da so da girmamawa tare da


hankalta"


8. Shugabantan namiji ga mace:


Sakon badris na farko (3:1): " gare ku yaku mata ku zama


masu bauta ga mazajen ku… taka adon ku ya zama irin adon


wace, na bude gari da sanya zinari da tufafi, sai dai mutumin


zuciya na biye wurin tabbatar da farna, adon rai da bankwana


31


na tsanake, wanda sune kafafuwan allah masu yawan


nauyi.haka mata suka asance ada can masu tsarki da tawakkali


ga allah suna gyara jikin su suna bauta ga mazajen su, kamar


yadda saratu tayima Ibrahim biyayya tana me kiransa da


"shugabana".


Safarul takwin (3:16): " sai mace tace: ina wahala dayawa


wurin daukan maka ciki da Haifa maka yara kuma ga kafafunka


nake biyayya"


9. Jifar mace mazinaciya har sai ta mutu:


Safar al tasniya (22:13): " idan mutum ya aure mace lokacin


da yayi amfani da ita sai yaji ya kita, ya kuma jingina mata


dalilan magana, sannan yayi ishara da cewa sunanta mayafi, sai


yace: wannan matar na rike ta kuma nayi zunubi da ita ban


sameta da budurci ba, sai uba da uwa su dauki yarinyar su su


fitar mata da alamar budurci zuwa ga malaman garin zuwa ga


kofa,… sai malaman wannan gari su dauki wannan mutum su


ladabtar dashi suci tarar sa na azurfa dari,… sai dai idan


wannan al'amari ya kasance ingantacce ba'a sami budurci ba


ajikin yarin yan. Sai a fitar da ita zuwa kofar gidan babanta


mazajen wannan gari su jefe ta da duwasu har sai ta mutu".


Safar al tasniya (22:22): " idan aka samu wani mutum kwance


da wata mace matar wani, to a kashe su biyun: namijin daya


kwanta da matar, sai a cire sharri daga isr'il".


Safar al tasniya (22:23): " idan mace budurwa ta wani ya nemi


aurenta sai wani mutum ya sameta na daban ya kwanta a ita a


cikin gari, to ku fita dasu zuwa kofar wannan gari ku jefe su da


dutse har sai sun mutu".


10. Mace tana kasa da namiji a daraja:


Sakon bulus na farko zuwa ga mutanen kurnunsus (11:3): "


inason ku sani cewa shugaban ko wani namiji shine masihi,


shugaban mace kuma shine namiji, shugaban masihi kuma


32


shine Allah. Ko wani mutum da yake salla ko ya zama annabi


to akan sa akwai abu wnada wulakanta kansa, amma duk mace


da take salla ko annabta kanta abude to ta wulakanta kanta


saboda da ita da wanda aka aske abu daya ne. idan mace ta


zama bata rufe kanta to a rake mata gashin kanta, idan kuma ya


kasance abun kyama ga mace a rage mata gashi ko kuma aski


to ta rufe shi. Baya halatta namiji ya rufe kansa saboda


kasancewar sa surar allah da kokarin sa. Ita kuma mace kokarin


namiji ce, saboda namiji ba daga mace yake ba ita macen ce


take daga namiji. Kuma saboda na miji ba'a halicce sa ba domin


mace, ita macece aka halitta domin namiji. Saboda haka ya


wajaba ga mace ya zama akwai shugabanci akanta saboda da


mala'ika."


11. karantar da mata littafin diskoliyya (littafe ne wanda ya


kunshi karantar da ubangiji da manzanni):


Babi na biyu cikin littafin diskoliyya me maudu'in (ya


wajaba akan mata su bautawa mazajensu kuma su rika


tafiya ka hikima) yana cewa: " mace tayi ma mijinta bauta


domin shine shugabanta,… kiri tsoron mijin ki ke mace,


kuma ki rikajin kunyar sa da neman yardan sa shi kadai


bayan Allah, kamar misalign abunda mukace, ki hutashe


dashi wurin maki hidima domin ya jawo zuwa gareki,….


Idan kina son ki kasance mumina wanda Allah ya yarda da


ita kada ku rika kwalli domin samarin mazaje su yarda,


kuma kada ki rika sha'awar riga mara nauyi masu nauyi


wanda basu dace da kowa ba sai mazinata domin wanda


suke son ki kasance a haka su rika binki. Idan kun kasance


bakwa aikata wannan ayyukan masu muni saboda zunubai


to ki rika kwalliya ke kadai domin addini saboda da haka


ne zaki tsagu ga wanda zai ganki yayi sha'awarki, to me


yasa bazaku kiyaye ba domin kada ku fada cikin zunubi,


kuma kada kusa wani yafada cikin shakka ko kuma kishi


domin ki, idan kinyi kuskure na daurewanki akan wannan


33


aiki to lallai zaki fadi, domin kina gina sababi ne na halakar


da ran wannan mutumi. Sannan idan kayi kuskure ga wani


akan wannan aiki lokaci daya shi kuma zai kasance sababi


na kayi kuskure ga mutane dayawa, ke kuma kina cikin


karanci kwadayi, kamar yadda littafi me tsarki yake cewa:


(idan munafika ya fada cikin sharrukan mutane dayawa to


lallai yana sani da kuma yawowa masa radadi da kunya),


duk wacce take aikata haka zata halaka da zunubi sannan


kuma zata farauto zuciyar maza ba tare da kayan farauta


ba, ku karanci abunda littafi me tsarki yake cewa game da


wanda yake kirkira akan wannan mutane kamar haka


cikin fadin sa: ( kanakin mace me zunubi sama da mutuwa,


wannan dinnan da ta zama abun farautan jahilai), ya kuma


kara fada a wani wuri na daban: ( misalign tsutsan da yake


cin katako, haka mace me zunubi take halaka mijinta) ya


kuma kara fada cewa: ( abunda yafi shine zama a lungun


saman gida sama da zama tare da mace me datti mara


kama kai). Kada kuyi koyi da irin wannan mata, yaku


matan misihi idan kuna son ku kasance muminai to lallai


ku himmatu da mijinki domin samun yardan sa shi kadai.


Kada kawata fuskar ki da Allah ya halicceta, babu abunda


yake rage kwalliya, soboda dukkan abunda Allah ya halicce


sa yana da kyau sosai, baya bukatar kwalliya, duk abunda


ya karo akan kyau to lallai yana canza ni'imar mahalicci.


Idan kina tafiya ya kasance kina kallon kasa bayan kin rufe


jikinki baki daya, ka nisanci dukkanin wani aboki wanda


be cancanci kasance wa abayi ba tare da mazaje, da yawa


abokan fasikanci ne, kada mace mumina ta rika cudanya


da maza. Sannan kuma idan zata rufe fuskarta ta rufeshi


da tsoron kallon maza samari… abunda ya wajaba agareki


idan kin kasanc emumina shine ki guji dukkanin nau'i na


kari, da kuma kallon idanu dayawa… (lallai zama a daji


yafi alheri da zama da mace me dogon harshe mara


tarbiyya)".


34


Babi na bakwai


Makiya musulunci dayawa sunyi kokarin yada wasu shubuhohi


game da musulunci daga cikin su akwai maganar dukan mace


suna amfani da almakashin su na sirihi wanda suka saba yadda


suke hakaito wa daga cikin ayoyin alkur'ani me girma da


hadisan manzon Allah s.a.w dukkanin maganar da shubaha zai


ina hawa kansa tare da tabbatar da abunda zai tabbatar da


wannan shubuhar nasu, kamar duka a cikin musulunci misali


sais u ambaci tsurar maganar kawai ba tare da Ambato maganar


da yake gaban sa ba ko bayan sa suna kokarin kawo shibuhohi


na karya akan musulunci da dabarar su mummuna wacce tayi


nisa gabaki daya da gaskiya da maudu'i, baza su kawo maudu'in


ba baki dayan sa sais u yanke sa wanda za'a masa mummunan


fahimfa, musa yin wannan aiki suna kirkiran karya ga


musulunci da ikirarin wayewar su da warkewan su wurin


mu'amala da mace da matan sun a gida, sai dai a hakika sun


rufe idon su akan wasu gaskiya da hakika masu zuwa:


Na farko: lallai musulunci shine addini daya tilo wanda yayi


bayani akan alaka ta rahama da soyayya tsakanin ma'aurata,


kuma shine addina daya tilo wanda yah aka ta'addanci da cuta


na magana ne ko kuma aiki, Allah madaukaki yana cewa: "


kuma daga cikin ayoyin say a halitta maku mata daga kawunan


ku domin ku samu natsuwa zuwa gare su ya kuma sanya


soyayya da rahama atsakanin ku"


(suratul rum ayata 21)


Amma fa musani cewa wannan soyayyar da rahama bata zuwa


sai bayan daurin aure ingantacce wanda ya halatta a shari'a.


Na biyu: lallai musulunci shine addini daya tilo wanda ya


magance duka da wulakantar da mace da kuma kallonta da idon


35


nakasa tun shekaru dubu daya da dari hudu da suka wuce a


baya ya kuma irga hakan daga cikin ayyukan nakasu ga maza.


Da ace zamu bincike na keke da keke cikin littattafai masu


tsarki na kiristoci tsohon alkawari ne ko kuma sabon alkawari


bazamu samu ishara ba akan haka na kusa ko kuma ta nesa


wanda yake haramta dukan mace.


Na uku: lallai musulunci ya kwadaitar da yin mu'ama na


karamci ga mata cikin dukkanin ayoyin alkur'ani da hadisai


masu daraja wanda suke magana akan alaka tsakanin ma'aurata,


Allah madaukaki yace: " suma sunada irin abunda kuke dashi


akansu a wurin na kyautatawa"


(Suratul bakara ayata 228)


Na hudu: lallai musulunci ya sanya mu'ama ta mutane ta jin kai


musamman tsakanin ma'aurata daga cikin ayyukan da suke


jawo lada da sakamako, manzon Allah s.a.w yace: " babu wata


ciyarwa da za'ayi ana neman yardan Allah da ita face Allah ya


baka lada akanta hatta loman da zaka sanya a bakin matar ka"


buhari da muslim ne suka rawaito shi.


Na biyar: lallai musulunci ya halalta dukar mace a wasu lokuta


bawai ka'ida bace sannan kuma gindaya wasu sharudda ga miji


wanda zai farayin su kafin duka wanda shine mafita na karshe


sannan kuma dukan ya kasance kare barna ne babba, saboda


kasancewar mata ba'a yanayi daya suke cikin dukkanin zamani


da al'umomin da iyalai. Abunda zai iya daidai da wannan


al'umma ba dole bane yayi daidai ga wasun su kila ma su ya


cutar dasu ne, sannan abunda zayyi daidai na mu'amala da wani


mace bazai zama yayi daidai ga waccen macen ba cikin wani


al'umma ta daban ko kuma cikin zamani na daban duk yadda


kayi kokarin sanya shi ya dace da ita kuwa, hakan yana cikin


gamayyar muslumci da karade dukkanin al'amura.


36


Na shida: lallai zahirin mugunta na zamanta kewar iyali ya


yandu cikin garuwan mutane da kasashe wanda sukaci gaba da


wanda basuci gaba ba cikin wannan zamani namu, maza nawa


ne na kiristoci turawa suke yin ta'addanci a fili ga matan su a


gaban mutane a filin jirgi ko wurin cin abici ko wani wurin


taruwa na daban kai hatta akan tituna manya a gaban wurin


wucewar mutane ana samu hakan bawai a asirce akeyin su ba


a'a takai ga har a gidajen yada labarai wanda ake gani da wanda


akeji duk suna kawo wannan labari.


Kuma mata nawa ne na kiristoci cikin turawa cikin Amerika da


kanada da austreliya wanda suka ware bangare nay an sanda


domin fuskantar aikin ta'addanci akan mata na duka gada


mazajen su, sannan wannan shari'ar bazata yiwu ba sai ansamu


alamomi na fili kamar yadda mukayi bayani a abaya kamar


karaya ko kuma kunburan kasan ido ko tabo a fuska saboda da


wannan duka, duk wanda ya bincika cikin hasashe na gwamnati


na bangaren yan sanda cikin amerika da kasashen turawa da


austireliya hakan zai bayyanan masa.


Abunda yake bayyana yaduwan mugunta na iyalai cikin


kasashen yamma wanda suke ikiraren wayewa da ci gaba na


hakkin dan adam bana arziki ba abubuwa ne Kaman haka:


1. Yaduwar kungiyoyi na hukuma da wanda bana hukuma


ba cikin kasashen turawa wanda suke kurmushe matsalar


ta'addanci ga mata da muguntan iyalai wanda sashin shari'a ta


kasa magance masu hakan na zalumcin mazaje akan matan su.


2. Wannan sanarwan da ake nanatawa akoda yaushe cikin


kafafen yada labarai wanda ake gani da naji wanda suke


kwadaitar da isar da hukuma cikin gaggawa game da duk wani


labari na ta'addancin daya daga cikin ma'aura ta ga abokin


zaman sa.Posts na kwanan nan

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A ...

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA