Labarai

Shekaru biyar da suka gabata, na karanta wani labari a mujallar Toronto Star ta ranar 3 ga watan Yuli ta shekarar 1990, wanda aka yi wa suna Islam is not alone in Patriarchal Doctrines (wato Musulunci ba shi kadai ne, hanya wadda a kan bi ta wajen addinai da ke bayar da iko da muhimmanci ga maza kawai ba), wanda Gwynne Dyre ya rubuta. Labarin ya siffanta fusataccen mayar da matanin masu yawa kwarai na mahalarta taron shawarar mata da iko, da aka gudanar a birnin Montreal ta kasar Canada, a kan fadar ra’ayoyin sananniyar matar nan 'yar kasar Masar Dr. Nawal Sa’dawi. Kasawarta na kauce wa magana, ko hali wanda ya kan jefa wasu jama’a cikin laifi, sun hada da bayanai kamar haka: “Jama’ar da suka fi dukan mutane takurawa ga mata, an fara samunsu ne, cikin addinin Yahudanci a cikin Littafin Tsohon Alkawari (Attaura), sa’an nan a addinin


Kirista, kuma sa’an nan a cikin Alkur'ani”; “duk addinai suna bayar da iko da muhimmanci ne, ga maza kawai, zama sakamakon al’ummomi masu bayar da iko da muhimmanci ga maza kawai”; kuma “Mayafin mata ba takamai mai sabon Musulunci ba ne, amma wani tsohon tarihi, al’adu, da ingantattun al’adun kabila daya ce, da take dauke da shi shekaru masu yawa, tare da yawan kiyasi addinai iri daya.” Mahalarta taron ba za su iya jure wa ci gaba da zama ba, yayin da imaninsu ake tunanin cewa ya daidaita da addinin Musulunci. Ta haka, Dr. Sa’dawi ta samu babban alkalamin suka. Ba a karbi ra’ayoyinta ba (a cikin zauren). Bernice Dubois ta Kungiyar Mata ta Duniya (World Movement of Mother's) ta furta cewa: “Amsoshinta suna bayyana wani rashin hazikanci game da imanin wadansu mutane ne.” Alice Shalvi wadda take cikin tsarin sunayen mutane, masu amsa tambayoyi a wagen mahawarar, ta hadaddiyar kungiyar matar Isra’ila (Israel Women Network) cewa ta yi: “Dole ne in ki yarda da (fadar ra’ayoyinta), babu wani batun hazikancin ko imani da lullubi cikin addinin Yahudanci.” Labarin a mujallar ya ce, ko ya ba da gaskiya da cewa, wadanan fusataccen rashin yarda masu yawa kwarai sakamakon karfaffa wani halin yin wani abu musamman ne, a kasashen Turai ta Yamma, (don) a sa wa Musulunci laifi bisa wasu al’adun yi wadanda suke kamar da yawansu wani shashin mallakar tarihin, da al’adun da ingantattun al’adun kabila daya ce ta kasashen Turai ta Yamma. Gwynne Dyer ya rubuta cewa: “Matan Kiristoci da na Yahudawa, ba za su zauna ana yin batu a jinsi daya ba, kamar wadancan mugan Musulmai ba.


Ban yi mamakin ba, cewa mahalarta taron shawarar sun riki wani ra’ayin musun Musulunci, sa’ad da (tattaunawar) ta shafi batuttukar mata. A Turai ta Yamma, an hakikanta cewa, Musulunci shine, ya zama alamar kaskanta mata fiye da dukan sauran addinai. Domin a fahinci yadda tabbatacen wannan ra’ayi yake, ya isa zama hujja issashe, mu ambaci cewa munistan ilimi na kasar Faransa, ya yi umurni kwanan nan, na korar dukan ‘yan-mata dalibai masu sanye da lullubi (mayafi) daga makarantun kasar baki-daya! Wata matashiya daliba Musulma mai sanye da dan kwalin kai an hana hakkinta na neman ilimi a Faransa, yayin da matashiya Kirista 'yar tarikar Katolika mai sanye da cross (gicciye), ko kuma Bayahudiya mai sanye da tagiyar Yahudanci, ba a hana ta ba. Ba za a taba mantawa ba da abin da ya auku ko halin da 'yan-sandan kasar Faransa ke ciki dake hana duk ‘yan mata Musulmai masu sanye da ‘yan kwalayen kai daga shiga manyan makarantunsu, domin neman ilimi. Wannan kan sa a zuciya yawan tunanin wani kuma abin babban kunya irin wannan, na gwamna George Wallace da ya auku a shekarar 1962, da yake tsaye a kofar wata makaranta, yana kokarin toshe mashigin bakaken dalibai, domin hana manufar kebe wata launin fata dabam da wata, a wurin da iri na mutane dabam ake waresu, a wuraren na jama’ar makarantun Alabama. Bambancin dake tsakanin wadannan abubuwan da suka auku guda biyu, shine, bakaken dalibai sun samu halin taimakawar yawancin Amurkawa da ma mutanen duniya baki daya. Shugaba Kennedy na kasar Amurka, a wancan lokacin, ya tura sojoji masu tsaron kasa su yi amfani da karfin tuwo wajen kau da kofar shigar bakaken dalibai. Yayin da a gefe guda kuma, 'yan-mata Musulmi ba su samu taimako daga wani ba. Maganarsu ga alama tanada dan karamin juyayi, ko a ciki da wagen Faransa. Dalilin kuwa shine, rashin hazikancin mai bazuwa sosai da tsoron duk wani abin da yake da alaka da Musulunci a zukatan mutane a daukacin fadin duniya, a yau. Abin da ya fi jan hankalina, ya bani sha’awa fiye da dukan komai, gama da taron shawarar Montreal shine, tambaya guda: Shin, bayanai da Dr.


Sa'dawi ta furta ne, ko kuwa, wata daga cikin masu sukar ta ce, ke dauke da wani


tabbataccen abu? A wani bangare guda kuma, shin, Musulunci, Kiristanci, da Yahudanci


suna da imani ko hazikanci guda ne game da mata? Shin, sun bambanta a ra’ayoyinsu ne?


Shin, Kiristanci da Yahudanci sun kan ba mata kulawa wadda ita ce mafi kyau, fiye da


yanda Musulunci ke yi ne? Mene ne gaskiyar lamarin? Ba abu ne mai sauki ba, a nemo


kuma a samo amsoshin wadannan tambayoyi masu wuya. Farkon wuyar da zai hana


hakan kuwa shine, dole ne mutun (mai bayar da amsar) ya zamo adali mara nuna goyonbaya


ga wani, kuma kada son ransa ya yi tasiri a kansa; a kalla, matsanancin akinsa ya


zama hakan. Wannan shine, abin da Musulunci ya kan koyar. Al-kur’ani ya koya wa


Musulmai fadi gaskiya ko da kuwa wadancan dake kusa da su sosai ba sa sonta. Allah Ya


ce: “Kada ku kusanci dũkiyar maraya face da wadda take ita ce mafi kyau, har ya kai ga


karfinsa. Kuma ku cika mũdu da sikeli da adalci, ba Mu kallafa wa rai face iyawarsa.


Kuma idan kun fadi magana, to, ku yi adalci, kuma ko da ya kasance ma'abũcin zumunta


ne. Kuma da alkawarin Allah ku cika. Wannan ne Ya yi muku wasiyya da shi:


tsammaninku, kuna tunawa) An'am: 152. (Ya ku wadanda suka yi ĩmani! Ku kasance


masu tsayuwa da adalci, masu shaida saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa,


mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance


mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Saboda haka, kada


ku bibiyi son zũciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana ko kuwa kuka


kau da kai, to lalle ne Allah Ya kasance Masani ga abin da kuke aikatawa) Nisa: 135.


Wani dalilin wuyar (tambayoyin) kuma shine, girman fadin fannin na ilimin, da yake dauke da shi, yadda za ka tsai da tunkaransa. Don haka, a cikin 'yan shekarun bara, sai na kashe awowi ina karanta Bible (littafin addinin Kirista), da Kundin fannonin addini, da Kundin Yahudanci, domin nemo amsoshin wadannan tambayoyi. Haka kuma na karanta littafai masu yawa wadanda suka tabo batun matsayin mata na addinai dabam-dabam, wadanda malamai, da masu kokarin yin bayyanai da kare ra’ayoyin addini da masu suka (zargi) suka wallafa. Bayanai (wato labarai ko ra’ayoyi) dake tafe a cikin wadanan babuka masu zuwa, suna yin misali da muhimman ganowar wannan guntun binciken asali (abin da na gano) ne. Ban yi ikirarin cewa, son raina ya yi tasiri a kaina ba da gaske, wannan (aiki) ya gagari yawan iyakacin abin da zan iya dauka. Dukan abin da zan iya fada shine, na yi kokari a ko’ina cikin wannan bincike, in matso da kammalallen Alkur’ani mara aibin, “maganar adalci”. Zan so na bayar da muhimmanci na musamman a wannan gabatarwa cewa, manufata a wannan karatu ba don in ce Yahudanci, ko Kiristanci ba shi da wata daraja, ko wani muhimmanci ba ne (wato mu gane, karatun bata da wata alaka da cin-fuskar Kirista ko Yahudawa, face nuna gaskiya da adalci). A matsayin mu na Musulmi, mun yi imani da tushen kwarai na dukkan addinan biyu. Babu wanda zai iya zama Musulmin ba tare da yin imani da Annabi Musa (A.S.) da kuma Annabi Isa (A.S.) a matsayin Annabawan Allah masu girma ba. Makasudi na kawai shine, in hakikanta cewa Musulunci gaskiya ne, kuma in yabi abin da ba a yi ba na bin umurni na dogon lokaci a kasashen Turai ta Yamma zuwa ga sako na gaskiya na karshe da Allah Ya aiko zuwa ga dukkan halittu. Haka kuma, zan so na bayyana cewa zan fi mayar da hankali na ne, kawai kan “aqida” (wato hanya wadda a kan bi ta wagen addini). Galibi, abin da zan fi mayar da hankalina gare shi, shine, matsayin mata a cikin wadannan addinai guda uku, kamar yadda ya kan bayyana a tushensu na ainihi, ba kamar yadda miliyoyin mabiyansu suka saba yi ba a fadin duniya. Don haka, yawancin dalilan da hujjojin da aka ambata kan zo ne daga Alkur'ani, da Hadisin Manzon Allah (tsira da


amincin Allah su kara tabbata a gareshi), da Littafin Yahudawa, da Littafin Kiristoci, da kuma kalaman wasu daga cikin manyan Qissisan (wato Fada Fadan) coci, wadanda suka yi tasiri da yawa akan mabiyansu, wadanda ra’ayoyinsu sun yi taimako da bayyana ma’ana da siffa Kiristanci (wato suna da matukar tasiri wajen ci gaban addinin Kirista). Wannan sha’ani dake cikin tushoshen kan ruwaito tabbaccen abu da cewa, hazikancin wani addini ta hanyar la'akari da halaye (ra’ayoyi) da dabi'un wasu daga cikin mabiya wannan addini, ta wagen suna kawai, ba dai-dai ba ne, rudu ne, bata ne. Mutane da yawa su na rikita al’adun kabila daya da addini, kuma wadansu da yawa ba su san mene ne abin da littafan addininsu ke fadi ba, kuma wadansu da yawa ba su ma kula ba (wato kan nuna halin ko in kula).


BABI NA 2


Laifin Hauwa'u


Addinan uku sun yarda da tabbataccen abu guda na asali: Allah Ya halicci duk mata da maza, Mahaliccin duniya, da rana da wata da taurari duka. Amma dai, sabani ya kunno kai jim kadan, bayan halittar farkon mutum, Adam, da macen farko, Hauwa'u. Hazikancin ko imani da halittar Adam da Hawa’u na Yahudu da Nasara an bayar da labarinsa daki-daki a Littafin Farawa 2:4 da 3:24. Allah Ya hana dukansu daga cin 'ya'yan itaciyar da aka haramta. Macijin (shaidan) ya lalatad da Hauwa'u ta ci daga gareta, kuma daya bayan daya a cikin wani umurni musamman, Hauwa’u ta laladad da Adam ya ci tare da ita. A lokacin da Allah Ya yi wa Adam tsawa game da abin da ya aikata, sai ya dora dukkan laifin a kan Hauwa'u, inda ya ce: "Macen da Ka ajiye tare da ni a nan, ta bani yanki na 'ya'yan itaciyar, ni kuma na ci;" sakamakon haka, sai Allah Yace da Hauwa'u: "Hakika Zan kara maki yawan radadi da zogi a wajen haihuwa; cikin zafi za ki haifi 'ya'ya. Bukatar ki zata kasance ga mijinki, sannan kuma shi za ya mulke ki." Dangane da Adam kuma sai Yace: "Sakamakon sauraran matar ka da ka yi har ta sanya ka cin abinda aka hana ka ... tsinuwa ta tabbata a kan kasa saboda kai; sai ka wahala sannan za ka ci daga gareta tsawon rayuwar ka...”


Hazikancin Musulunci, ko imani da farkon halitta, ana samunsa ne, a wurare daban-daban a cikin Alkur'ani, kamar haka:


“Kuma ya Adam! Ka zauna kai da matarka a Aljanna sai ku ci daga inda kuka so; kuma kada ku kusanci Wannan itaciya, har ku kasance daga azzalumai." Sai Shaidan ya sanya musu waswasi domin ya bayyana musu abin da aka rufe daga barinsu, daga al'aurarsu, kuma ya ce: "Ubangijinku bai hana ku daga wannan itaciya ba face domin kada ku kasance mala'iku biyu ko kuwa ku kasance daga madawwama.” Kuma ya yi musu rantsuwa; Lalle ne nĩ, a gare ku, hakĩka, daga masu nasĩha ne. Sai ya saukar da su da rũdi. Sa'an nan a lokacin da suka dandani itaciyar, al'aurarsu ta bayyana gare su, kuma


suka shiga suna likawar ganye a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Ubangjinsu Ya kira su: "Shin, Ban hana ku ba daga waccan itaciya, kuma Na ce muku lalle ne Shaidan, a gare ku, makiyi ne bayyananne?" Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kanmu. Kuma idan ba Ka gafarta mana ba, kuma Ka yi mana rahama, hakĩka, Muna kasancewa daga masu hasara”. A'raf: 19 – 23.


Idan aka duba labaran da suka gabata game da farkon halitta da kyau, su kan ruwaito wasu bambance-bambancen fannin ilimi. Sabanin Bible (litaffin addinin Kirista), Alkur'ani ya sanya wa duk Adam da Hauwa’u laifi daidai bisa aikata laifinsu. Ba wani wuri a cikin Alkur’ani da wani zai samu ko da yin dan ambaton cewa wai Hauwa'u ce ta yaudari Adam har ya ci daga itaciyar, ko kuma wai ita ce ta fara ci kafin shi. Hauwa'un cikin Alkur'ani ba mayaudariya ba ce, ko mai jawo hankali namiji ga aikata abin da ya ki ba ce, ko mai halin lalatad da wani ba ce, kuma, bai kamata a ce an dura wa Hauwa'u da laifin zafin ko ciwon haihuwar 'ya'ya ba. Kamar yadda Alkur'ani ya fadi cewa, Allah ba Ya azabtar da wani saboda zunubin wani. Adam da matarsa Hauwa'u sun aikata laifi, amma sun nemi Allah Ya gafarta musu, kuma Allah Ya gafarta musu.


BABI NA 3


Gadon Hauwa'u


Kamannin Hauwa'u a matsayin mayaudariya mai jawo hankalin namiji da aikata sha’anin ma’malar maza da mata, a cikin Bible (littafin addinin Kirista) ya zama sanadin matsanancin tasirin kalmar musun mata mai karfi, a ko’ina cikin hanyar al’adar Yahudu da Kirista. An yi imani da cewa dukan mata sun gaji duk alhakin laifi, da kissar uwarsu ce Hawa’un dake cikin littafin addinin Kirista. Sakamakon haka, dukansu ba amintattu ba ne, a taikace, ba su kamata a yarda da su ba, masu munanan halaye ne, kuma muga ne. An duba fitar jinin al'ada (wato haila), da daukar ciki, da haihuwar 'ya'ya, a matsayin ukuba da ya dace ga jinsin mace, sakamakon alhakin laifin da uwarta, ta asali ta aikata. Domin fahinta ko gane gaskiyar yadda kalmar musun Hauwa'un cikin Bible yake da shi ga magadanta mata, dole ne mu dubi rubuce-rubucen wasu Yahudawa da Kiristoci da suka fi muhummanci na duk lokuta. Bari mu fara da Littafin Tsohon Alkawari, mu ga wasu gajerun rubutu daga abin da ake kira (Adabin Hikima) kamar haka: "Na kwa tarasda wani abu daya da ya fi mutuwa dachi, watau mache wadda azargiya che, zuciyata azargiya che, da kuma; hannuwanta kuma sarka ne; amma wanda ya sami yardar Allah za ya tsere mata; amma za ta kama mai-zunubi. Duba na iske wannan, in ji Mai-Wa'azi, na yi ta auna wani abu a kan wani, ina gwada su, domin in san baichin komi, abin da raina ke nema har yanzu, amma ban samu ba: namiji guda chikin dubu na samu; amma mache guda ban samu ba chikin wadannan duka." Littafin Mai-Wa'azi


7:26 – 28.


A wani bangaren na adabi (litattafan) Yahudawa wadanda aka samu a cikin Bible din, mabiya tarikar Katolika ya zo kamar haka: "Babu muguntar da ke zuwa daga ko'ina, da ta kai muguntar mache. Zunubi ya fara ne daga mache kuma an gode mata, domin kwa dukanmu za mu mutu" Littafin Ecclesiasticus 25:19 – 24.


Wani limamin Yahudawa ya lissafa la'anoni guda tara wadanda aka yi su a kan mata, sakamakon rashin biyayyar Allah da ya auku na Adam da Hauwa’u, kamar haka: “Ya bayar da la'anoni guda tara da mutuwa ga mace: nauyin zubar jinin haila da na budurci; nauyin daukar ciki; nauyin haihuwar 'ya'ya; nauyin renon 'ya'ya; kanta na rufe ne, kamar na wadda ke yin kukan wanda ya mutu; ta kan hurhurje kunnuwanta kamar dauwamammiyar baiwa ko yarinya wadda ke yin bauta wa mai-gidanta; bai kamata a yarda da shaidarta ba; kuma bayan kome da kome ta cancanci a kashe ta- mutuwa"


Har wannan lokacin, Yahudawa maza mabiya tarikar Orthodox (al’adun imani da aikin kwarai) a addu’arsu ta kullum safiya, su kan fadi “Albarka a Hannun Allah take Sarkin duniya da rana da wata da taurari duka, da ba Ka halicce ni mace ba.” Su kuwa mata, a gefe guda, kan yi godiya wa Allah kullum safiya da halittarsu gwargwadon (kamar) yadda Yake so.” An kara samu wani addu'an a litattafan addu’ar Yahudawa masu yawa, kamar haka: “Godiya ta tabbata ga Allah da bai halicce ni mutumin da ba Bayahude ba. Godiya ta tabbatta ga Allah da bai halicce ni mace ba. Godiya ta tabbata ga Allah da bai halicce ni jahili ba.”


Hauwa'un dake cikin Bible ta taka muhimmiyar rawa a Nasaranci fiye da yadda ta taka a Yahudanci. Zunubin da ta aikata yanada matukar muhimmanci a duk bangaskiyar Kirista saboda hazikancin ko bangaskiyar Nasara na dalilin aikowar Annabi Isa (A.S.) a duniya, sakamakon rashin biyayar Hauwa’u ce ga Allah. Ta aikata zunubi kuma ta lalada da Adam har ya biye mata wajen aikata irin zunubin da ta aikata. Sakamakon haka, Allah Ya fitar da su daga Aljanna zuwa Duniya, wadda aka la'anta saboda su. Sun bar zunubinsu ga zuru’oinsu su gada musammam baya mutuwansu wanda Allah bai yafe musu ba, kuma ta haka, duk yan-Adam an haife su cikin zunubi. Domin tsarkake mutane daga “zunubinsu na asali”, Allah Ya sadaukad da Annabi Isa (A.S.), wanda ake dauka a matsayin Dan- Allah, a kan cross (giciye) Don haka, alhakkin kuskuren da Hauwa'u ta tafka, da na mijinta, da na asalin zunubin ‘yan Adam duka, da na mutuwar Dan-Allah duk ana zargin ta da sune. A wani kaulin kuma, mace daya, mai aiki da ra’ayinta ta yi sanadiyyar rashin girmamawar ‘yan Adam duka. To yaya abin yake ga diyanta mata? Su ma masu zunubi ne kamarta, don haka, bai kamata hukuncin da za a yi musu ya sake zani ba da nata. Saurari furucin mai tsanani da wali Paul a cikin Littafin Sabon Alkawari, inda yake cewa: "Bari mache ta koya a kawaiche da biyayya sarai. Amma ban yarda ma mache ta koyas, ko kwa ta sami mulki bisa namiji ba, amma ta kasanche a kawaiche. Gama Adamu aka fara kamantawa, kana Hauwa'u; kuma ba Adamu aka rude ba, amma machen da ta rude ta fadi chikin zunubi." Littafin Timothawus 1 2:11 – 14.


Maganar Wali Tertullian har ba kewaye-kewaye ba ce game da mata, tafi ta wali Paul a cikin lokacin da ya ke zantawa da 'yan'uwansa mata da yafi so sosai a cikin bangaskiya, ya ce: "Ba ku san cewa kowaccen ku Hauwa'u ce ba? Hukuncin Allah da ya hau kan wannan jinsi naku har yanzu babu abin da ya kawar da shi: alhakin laifin tilas yana nan


kuwa. Ku ne shighifar (kofar hanyar) Shedan; ku ne ku ka falasa haramtacciyar itaciya: Ku ne farkon wadanda ku ka kaurace wa doka ta Allah ba da izini ba: Ku ne ita (Hauwa’u) wadda ta jawo hankalinsa (Adam) mutumin da Shedan bai kasance mai karfin zuciya issashe da zai fada masa ba. Kun hallakar da kamannin Allah, mutum, cikin sauki sosai. Sakamakon kaurace wa doka ta Allah ba da izini ba har Dan-Allah ya mutu."


Wali Agustine, amintaccen mutum ne da ya yi imani da wasiyar wadanda su ka riga shi. Ya rubuta wasika zuwa ga wani abokin, inda ya ce: "Mene ne bambanci ko ga matar aure ko ga uwa, ai bata sake zani ba, har yanzu Hauwa'u ce mai halin jawo hankalin namiji ga aikata sha’anin ma’amalar maza da mata da lalle, za mu yi hankali ga kowace mace… ni kam, ban ga wani alfanu da mace ke da shi ga namiji da ya wuce na haihuwar 'ya'ya ba.” Bayan shudewar karnoni, Wali Thomas Aquinas har yau yana daukar mata a matsayin marasa hankula ne inda ya ke cewa: “Bisa la'akari da yadda dabi'ar mutum take, mace mara hankali ce kuma wadda aka haifa cikin kuskure, domin kuwa karfin kwayar haihuwa dake jikin naminji ne kan sanya a haifi cikakken kamanin namiji, yayin da haihuwar mace kan zo ne daga wani nakasa a cikin karfi mai kuzari, ko daga wasu dan rashin lafiyar kayan jikin mutum dake sa ba su iya yin wani abu, ko ma daga wasu abubuwa masu tasiri na waje.”


Daga bisani, Ba'amurken nan mai ra'ayin kawo sauyi (gyare gyare) Martin Luther, shi ma bai ga amfani daga wata mace ba da ya wuce na zuba 'ya'ya barkatai a duniya, ba tare da sauraren illa da kan biyo baya ba. Ya ce: “Idan sun gaji, ko ma sun mutu, hakan babu komai. Bari su mutu lokacin haihuwa, wannan shine dalilin kasancewarsu.”


An sha nanata cewa, mata ba su da wani muhimmancin amfani saboda kasancewar kamannin Hawa’u mai jawo hankalin namiji ga sha’anin ma’amalar maza da mata, mun gode wa labarin da Littafin Farawa ya bayar. Hasali dai, hazikancin ko bangaskiyar Yahudu da Nasara game da mata ya samu gurbata daga imanin da batun cewa, Hauwa'u tana da dabi'ar sabo, da kuma na 'ya'yanta mata. Idan yanzu muka ba da kulawarmu ga abin da Alkur'ani ke fadi dangane da mata, cikin sauri za mu ankara cewa, imani ko hazikancin Musulunci game da mata ya yi matukar bambanta da na Yahudu da Nasara. Bari mu ga abin da Alkur'ani ke fadi:


“Lalle, Musulmi maza da Musulmi mata da muminai maza da muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawali'u mata da masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu hakuri maza da masu hakuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata da masu tsare farjjinsu maza da masu tsare farjjinsu mata da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonsa mata Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma” Ahzab: 35.


“Kuma mummunai maza da mummunai mata sashensu majibincin sashe ne, suna umurni da alheri kuma suna hani daga abin da ba a so, kuma suna tsayar da salla, kuma suna bayar da zakka, kuma suna da’a ga Allah da ManzonSa. Wadannan Allah zai yi musu rahama. Lalle Allah ne Mabuwayi, Mai hikima.”Taubah: 71.


“Sab􀋴oda haka Ubangijinsu Ya karَba musu cَewa, “ Lalle ne Nĩ b 􀋴a zan tozartar da aikin


wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashenku daga sashe. To,


wadanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu, kuma aka cũtar da su a


cikin hanyaTa, kuma suka yi yaki, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidajen Aljanna wadanda koramu ke gudana daga karkashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako”. Al-Imran: 195.


“Wanda ya aikata mummunan aiki to, ba za a saka masa ba face da misalinsa, kuma wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko mace alhali kuwa shĩ mũmini ne, to, wadannan suna shiga Aljanna, ana ciyar da su a cikinta, ba da lissafi ba” Ghafir: 40.


“Wanda ya aikata aiki na kwarai daga namiji ko kuwa mace, alhali yana mũmini, to, hakĩka Muna rayar da shi, rayuwa mai dadi. Kuma haqĩqa Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa” Nahl: 97.


A fili yake cewa, ra'ayin Alkur'ani game da mata bai bambanta fiye da na maza ba. Duk namiji da mace, halittun Allah ne, wadanda babban makasudin zuwansu a duniya shine, bauta wa Ubangijinsu, aikata ayyuka na kwarai, nisantar (wato kauce) wa ayyukan assha, kuma dukansu za a yi musu hisabi dai-dai gwargwado (ta hanya mai dacewa). Alkur'ani, ko kadan bai ambaci mace da cewa shigifar (kofar hanyar) Shedan ce, ko kuwa ta na da dabi’ar yaudara ba. Haka kuma bai taba ambatar namiji da cewa kamannin Allah ne ba; abin da kawai ya nunar shine, dukan maza da mata halittunSa ne shi ke nan. Bisa ga maganar Alkur'ani, rawar da mace zata taka a duniya bai tsaya kawai a kan haihuwar 'ya'ya ba. An bukace ta da aikata ayyuka na kirki kamar yanda ake bukatar wani namiji ya aikata. Alkur'ani bai taba cewa babu mata nagari da suka taba rayuwa ba, Sabanin haka, Alkur'ani ya koya wa dukan muminai, maza da ma mata cewa, su yi koyi da wadancan matan wadanda suka dace kamar Nana Maryam da Matar Fir'auna, kamar haka:


“Kuma Allah Ya buga wani misali domin wadanda suka yi ĩmani; matar Fir'auna, sa'ad da ta ce "Ya Ubangiji! Ka gina mini wani gida a wurinKa a cikin Aljanna. Kuma Ka tsĩrar da ni daga Fir'auna da aikinsa. Kuma Ka tsĩrar da ni daga mutanen nan azzalumai. Da Maryama diyar Imrana wadda ta tsare farjinta, sai Muka hũra a cikinsa daga rũhinMu. Kuma ta gaskata game da ayoyin Ubangijinta da LittattafanSa alhali kuwa ta kasance daga masu tawali'u”. Tahrim: 11 – 13.


BABI NA 4


Kunyatattun Diya Mata


Akan gaskiya, bambancin dake tsakanin ra’ayin Alkur'ani da Bible (littafin addinin


Kirista) game da jinsin mace ya soma ne jim kadan da aka haifi wata mace. Misali, Bible yana bayyana cewa, yawan kwanakin da uwa ke kasancewa cikin rashin tsarkin idan ta haifi mace, yafi tsawo fiye da idan namiji ne, kamar yadda yazo cikin Littafin Leviticus. 12:2 – 5. Bible din mabiya tarikar Katolika kan ambaci a bayyane cewa: “Haihuwar diya mache hasara che.” Ecclesiasticus 22:3. Sabanin wannan abin da aka furta mai gigitarwa, 'ya'ya maza, suna da yabo na musamman, kamar haka: “Mutumen da ya ilmantar da dansa, za a fa kiransa mai-hassada ga makiyinsa.” Ecclesiasticus 30:3.


Wani limamin Yahudawa ya tsanya wani takalifi akan mazan Yahudawa, hayayyafar 'ya'ya, domin a haifar da sabuwar kabilar. A lokaci guda kuma, sun kasa boye irin fifikon da suke nunawa ga 'ya'ya maza, inda yake cewa: “Komai zai tafi dai-dai ga wadanda suka haifi 'ya'ya maza, yayin da sabanin hakan kan tabbata ga wadanda suka haifi diya mata, kowa na farin-ciki da murna da haihuwar da namiji, yayin da kuma kowa ke bakin-ciki da haihuwar diya mace, kuma zaman lafiya kan zo Duniya da zuwan da namiji, idan kuwa diya mace ta zo Duniya, babu abin da ke zuwa.” Ana dubar diya mace a matsayin mai farar kafa (mai mummunar sanadi), kuma mai janyo wa mahaifin ta abin-kunya, kamar haka: “Diyarka fa mai tsaurin-kai che? Ka kula da ita da kyau, domin kada ta misheka abin-dariya a idon makiyanka, abin Magana a gari, abin tsegumi da jin-kunya a wurin jama'a. ” Ecclesiasticus 42:11,


“Ka fa kula sosai da diya mai-tsaurinkai, ko kwa ta lalata dukan wani abu mai-kyau da ta taba. Ka dubi idanunta na rashin-kunya, kada ka yi mamaki idan ta kunyataka.” Ecclesiasticus 26:10 – 11.


Guguwar irin wannan ra’ayi na daukar diya mata a matsayin tushen abin-kunya, ta kai Larabawa, kafin zuwan Musulunci, har suka rika wulakantar da mata tare da kashe su. Alkur'ani ya tabbatad da laifin wannan mugun hali da tsanani, inda ya ke cewa:


(Yana boyewa daga mutane domin mũnin abin da aka yimasa bushara da shi. Shin, zai rike shi a kan wulakanci ko zai turbude shi a cikin turbaya To, abin da suke hukuntawa ya mũnana) Nahl:59.


Abin da za a ambata ne cewa, irin wannan mugun laifi har abada da ba zai taba hanuwa ba (wato a kawo karshesa ba) a kasar Arebiya, ba domin karfin sharuddudin suka masu tsanani da Alkur'ani ya kan suki wannan al’ada da shi ba, kamar yadda yazo a cikin Alkur'ani Surar Nahl: 59, Zukhruf: 17, Takwir: 8 – 9. Kuma, Alkur'ani bai sanya bambanci a tsakanin diya maza da ‘ya’ya mata ba. Sabanin Bible, Alkur'ani ya kan duba haihuwar diya mace da cewa kyauta ce kuma bai wa ce daga Allah, kamar yadda haihuwar namiji take. Alkur'ani ma yana ambaton haihuwar diya mace da farko, kamar haka: (Mulkin sammai da kasa na Allah kawai ne. Yana halitta abin da Yake so. Yana bayar da 'ya'ya mata ga wanda yake so, kuma Yana bayar da diya maza ga wanda Yake so) Shura: 49.


Domin hallaka dukkan alamun laifin kissar diya mace wadda ba ta da laifi, a jama’ar Musulmi, wadda ta fara kasancewa ba ta cikasa yin girma ba, Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya yi wa wadanda aka yiwa bai wa da haihuwar diya mata alkawarin samun babban rabo daga Allah, matukar za su basu kyakkyawar


tarbiyya, kamar yadda yazo cikin Hadisi: “Duk wanda alhakkin tarbiyyantar da diya mace ke wuyansa, kuma ya kan ba su kyakkyawar tarbiyya, za su cece shi daga shiga wutar Jahannama.” Bukhari da Muslim suka ruwaito,” “Duk wanda ya kula da diya mata guda biyu har zuwa balagarsu, ni da shi za mu kasance kamar haka, sai ya hada yatsunsa.” Muslim ya ruwaito.


BABI NA 5


Ilimin Mata


Bambancin dake tsakanin hazakancin ko imani game da mata na Bible da Alkur’ani ba a iyakace shi a kan haihuwar diya mace jaririya ba, ya kan zarce nan. Bari mu gwada ra’ayoyinsu game da wata mace dake kokarin yin koyon addininta. Zuciyar Yahudanci ita ce Attaurah, dokarta. Amma dai, bisa ga maganar littafin Talmud, “An kade (dauke) mata karanta Attaurah.” Wasu daga cikin limaman Yahudawa sun furta cewa, “Gara a kona kalmomin Attaurah a cikin wuta, da a ce an bayar dasu ga mata,” suka kara da cewa, “Duk wanda ya karantar da diyarsa Attaura, kamar ya karantar da ita batsa ne.”


Ra'ayin Wali Paul a cikin Littafin Sabon Alkawari ba mai fasaha ba ne, kamar a jama’ar dukan waliyyai, ga abin da ya ke cewa: “Bari mata su yi shuru chikin ekklesai: Gama ba a yarda musu su yi Magana ba; amma su zama da biyayya, kamar yadda Attaurat kuma ta fadi. Idan kwa su na son su koyi komi, sai su tambayi mazajensu chikin gida: gama abin kumya ne ga mache ta yi Magana chikin ekklesiya.” Littafin Kwarantiyawa 14:34 – 35.


Ta yaya mace za ta samu ilimi ba tare da an bata dammar yin Magana ba? Ta yaya mace za ta girma cikin kwazo da kaifin kwakwalwa (mai wayo) idan aka tilasta mata ci gaba da kasancewa cikin wani halin mika-wuya (yin biyayya)? Ta yaya za ta fadada fahimtarta, matukar mijinta ne kadai hanyarta na samun bayanai, a cikin gida?


Yanzu, domin yin adalci, ya kamata mu tambaya cewa: Shin, matsayin Alkur'ani ya bambanta kuwa? Labari guda mara tsawo da aka bayar a cikin Alkur'ani ya takaita matsayin takaitacce. Khaulah mace ce Musulma wadda mijin ta mai suna Aus ya yi lafazi da wannan bayani a dai dai lokacin fushi, kamar haka: “Ke, a wuri na, kamar bayan mahaifiyata kike.” Irin wannan furuci ne, kafuran Larabawa ke amfani da shi a matsayin sakin macen aure, wanda kan 'yanta miji daga kowane irin sha’ani na ma’amalar miji da matarsa ta aure, amma ba zai bar matar ba ta bar gidan mijin, ko ta sake wani auren. Da jin wadanan kalamai da suka fito daga bakin mijin ta, Khawlah ta kasance a cikin wani yamutsattsen hali. Sai ta tafi sak zuwa wurin Anabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) ta yi roko a yi mata wani abu da halin da take ciki (ta gabatar da kokenta gare shi). Sai Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) a ganinsa ya ce, ta yi hakuri tunda a alama babu wata mafita. Khaulah ta ci gaba da jayayya


da Annabi (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) a wani yin kokarin ya tsirad da ratayayyen aurenta (wadda ba a sake ta ba, kuma ba a aure ta ba). Gaba kadan, sai Alkur'ani ya sa baki (wato ya yi magana) cewa; an karbi hanzarin Khaulah. Firicin Allah mai yanke Sharia’ah ta kawar da wannan al'adar ta rashin adalci sosai. Sai aka saukar da cikakkiyar sura guda wadda aka yi wa suna 'Al-Mujadalah' ko kuma 'Mace mai jayayya' a cikin Alkur'ani bayan wannan aukuwa da ya faru, inda take cewa:


“Lalle Alla Ya ji maganar wadda ke yi maka jayayya game da mijinta, tana kai Kara ga Allah, kuma Allah najin muhawararku. Lalle Allah Mai ji ne, Mai gani.” Mujadalah: 1.


Mace, a hazikancin Alkur'ani, tana da ikon ta yi jayayya, har ma da Annabin (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi) da kansa. Babu wanda ke da iko da ya umurce ta da ta yi shiru. Ba ta karkashin takalifi da zata dauki mijinta a matsayin shi ne kadai madogararta wurin batunta na Addini ko shari'a.


BABI NA 6


Mace Kazamtatta Mara Tsarki


Dokoki da ka’idodin Yahudawa a kan batun mata masu haila lalle, suna da kuntatawa. Littafin Tsohon Alkawari ya kan duba mace mai haila da cewa, kazamtatta ce mara tsarki. Kuma, rashin tsarkinta ya kan “taba” sauran mutane ma. Dukan wanda, ko dukan abin da ta kan taba zai zama mara tsarki har na tsawon kwana guda, kamar haka: “Idan kwa mache tana haila, hailan dake gudu kwa chikin jininta jinni che, sai ta zamna chikin kazamtatta kwana bakwai; dukan wanda ya taba ta za ya kazamtu har yamma ta yi. Kuma dukan abin da ta kwanta a kai chikin kazamtatta za ya kazamtu. Kuma dukan wanda ya taba gadonta za ya wanke tufafinsa, shi yi wanka chikin ruwa, shi kazamtu har yamma ta yi. Kuma kowanene ya taba abin da ta zamna a kansa, za ya wanke tufafinsa, shi yi wanka chikin ruwa, shi kazamtu har yamma ta yi. Idan Kwa bisa gadonta ne, ko Kwa bisa kowane abin da ta zamna a kai, kadan ya taba shi, sai shi kazamtu har yamma ta yi.” Littafin Leviticus. 15:19 – 23.


Saboda “gurbacewar (rashin tsarkin)” halittata, mace mai haila a wani lokaci ta kasance wadda ake “kora” ce, domin kauce wa yiwuwar halin gamuwa da ita ko aiki da ita. An aika ta zuwa ga wani gida na musamman da ake kira “Gidan kazamtattu”, inda za ta zauna iya tsawon kwanakin da take cikin rashin tsarkin. Littafin Yahudawa Talmud ya kan duba mace mai haila da cewa: “mai sa mutuwa” ce, har ma ba tare da halin hada ko taba jiki da ita ba: “Limamin mu na ganin chewa, idan fa mache mai haila ta wuche (maza) guda biyu, idan a farkon hailarta ne, za ta kashe daya daga chikinsu, idan kuwa a karshen hailarta ne, za ta kawo gaba a tsakaninsu.” bPes. 111a.


Bugu da kari, an haramta wa mijin matar dake yin haila shiga wurin ibada Mihrabi (dakin ibadar Yahudawa), idan ta kazamta shi, koda kuwa, da kurar dake fita daga karkashin


kafafunta ne. Ma’aikacin addinin Kirista wadda matarsa, diyarsa, ko mahaifiyarsa ke cikin haila, ba zai iya karanta wa mutane addu'o'i masu albarka a cikin dakin ibada ba. Ba abin mamaki ba ne mata Yahudawa da yawa har yanzu suna dubar jinin haila a matsayin “la’anta”. Addinin Musulunci bai dubar wata mace mai haila tana mallakar wani irin “kazamta mai yaduwa ba”, da ba a taba ta balle a ce “la’ananniya” ce. Ta kan tafiyar da rayuwar ta na kulum cikin kunci guda daya ne: An haramta wa ma’aurata (wato mutum da matarsa) saduwa da juna (tarawar miji da mata) a lokacin da matar ke cikin haila, amma babu laifi su yi kowane irin tabawar jiki kamar wasa, 'yan shafe-shafe a tsakanin su. An haramta wa mace mai haila aiwatar da wasu daga cikin ayyukan ibada, kamar sallolin yau da kullun da azumi, a lokacin da ta ke cikin haila.


BABI NA 7


Bayar da Shaida


Wani kuma muhimmin batu da Alkur'ani da Bible ba su dace ba a kansa, shine, batun bayar da shaidar mata. Gaskiya ne cewa, Alkur'ani ya umurci muminai wadanda ke mu'amala da kudi da cewa, su nemi shaidar mutum biyu maza, ko kuwa namiji daya da mata biyu, kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani Surar Baqarah: 282. Amma dai, gaskiya ne kuma cewa, a wasu wurare Alkur'ani ya kan amince da bayar da shaidar mace dai-dai da yanda ya kan amince da shaidar namiji. A kan gaskiya, shaidar mace kan mayar da shaidar namiji ta banza. Idan mutum yana jifar matarsa da laifin yin jima’i (kuma wadansu shaidau ba su kasance a gare shi ba, face kansa), Alkur'ani ya bukace shi da ya yi muhimmin rantsuwa sau biyar a matsayin shaidar alhakin laifin matar. Idan matar tana yin musun (aikata wannan laifin) sai ta rantse kamar yanda ya rantse (wato sau biyar), ba a dubar ta mai laifi, kuma a cikin kowane hali auren ya mutu, kamar yadda Alkur'ani ya bayyana, Surar Nur: 6 – 11.


A wata fuska kuma, a al'ummar Yahudawa ta farko, an haramta wa mata bayar da shaida. Limaman Yahudawa sun lissafa mata da basu da hurumin bayar da shaida saboda la’anoni guda tara da aka yi a kan dukansu, saboda aukuwar kin bin umurnin Allah da Adam da Hawa’u suka yi, kuma su ka rabu da Aljanna, (duba sashen “Gadon Hauwa'u” domin karin haske). Mata Yahudawa a Isra’ila ta yau, ba a yarda da su bayar da shaida a kotunar da limamin Yahudawa ke jagoransu ba. Limaman sun tabbatar da gaskiyar don me mata ba su iya bayar da shaida a kutonar limamansu ba, ta hanyar karanto Littafin Farawa 18:9 – 16, inda aka ambaci cewa Saratu, matar Annabi Ibrahim (A.S.) ta yi karya. Limaman sun yi amfani da wannan aukuwa a matsayin shaidar cewa mata ba su cancanta su bayar da shaida ba. A nan ya kamata a yi tunanin cewa, wannan labarin da aka ba da labarinsa a cikin Littafin Farawa 18:9 – 16, ya zo a cikin Alkur'ani ba sau daya ba, ba tare da nuna wata yin dan ambaton karya ba da Saratu ta yi, a duba Alkur'ani Surar Hudu: 69-74, Dhariyat: 24-30. A wurin Kiristocin kasashen Turai ta Yamma, da duk tarihin ikilisiya ta cocin Kirista, da shari'ar ta tsakanin mutum da mutum sun hana


mace bayar da shaida sai a karnonin baya-bayan nan suka samu wannan 'yancin. Idan wani miji yana jifar matar aurensa da laifin jima’i (fasikanci ko lalata), abin da ta bayar da shaida a kai ba za karbe shi ba gaba daya, bisa ga maganar Bible. Matar auren da aka jifa da irin wannan laifin, za’a gurfanar da ita a gaban kuliya. A wannan gwadawa, macen auren za ta fuskanci wani sauraren koto mai wuyar fahimta da kaskanci, wanda ake tsammani zai hakikanta alhakin laifinta ko mara laifi, kamar yadda ya zo a cikin Littafin Lissafi. 5:11 – 31. Idan aka iske ta mai laifi ce bayan wannan gurfanarwar, za ta fuskanci hukuncin kisa. Idan aka iske ta ba mai laifi ba, mijinta zai zama mara laifi aikata mugun aiki.


Bayan wannan, idan wani mutum ya auri mace, sa’annan yana jifar ta da cewa bai same ta budurwa ba, ba za a yarda da shaidar da za ta bayar ba. Iyayenta za su gabatar da wata shaidar da zata tabbatar da budurcinta a gaban datibai na birni. Idan kuwa iyayen ba su iya hakikanta da rashin laifin diyarsu ba, sai a jefe ta har ta mutu a kofar gidan ubanta. Idan kuma iyayen sun iya hakikantar da rashin laifinta, za a ci tarar mijin kudi kimanin (Shekel) din azurfa dari kawai ne, kuma ba zai iya saki matar aurensa ba muddar ransa, kamar yadda ya zo:


“Idan kowane mutum ya amre mache, ya shiga wurinta, ya kita kuma, ya yi tseguminta da miyagun sara, ya kwa sa mata mugun suna, yache, Na dauko wannan mache, amma sa'anda na kusa da ita ban iske budurchi gareta ba: Sai uban yarinyan nan da uwatta za su dauki shaidar budurchin yarinyan, su fito da su wurin datibai na birni a wajen kofa: uban yarinyan kuma za ya che ma datiban, Na ba mutumen nan diyata ta zama matatasa, ama ya ki ta; gashi kwa, ya sa mata laifin al'amura na kunya, ya che, ban iske diyarka budurwa ba; ga kwa wadannan abu su ne alamun budurchin diyata. Su kuma sai su bude zanen a gaban datiban gari. Datiban gari kwa su kama mutumen nan su yi masa foro; su chi shi tara shekel na azurfa guda dari, su ba uban yarinyan, da shike ya jawo mugun suna bisa diyar Israila: za ta zama matarsa kuma; ba shi da iko shi saketa muddar ransa. Amma idan zancen nan gaskiya ne, ba a iske shaidar budurchi ga yarinyan ba; daga nan sai su fito da yarinyan a kofar gidan ubanta, mazajen garinta kwa za su jejjefe ta da duwatsu har ta mutu: domin ta aika mugun abu chikin Israila, da ta yi karuwanchi chikin gidan ubanta: hakanan za ka kawasda mugunta daga chikinka.” Littafin Kubawar Shari'a 22:13 – 21.


BABI NA 8


Zina/Kwartanci


A dukan addinan nan uku zina (kwartanci) ana dubarsa wani zunubi ne. Bible (littafin addini Krista) ya kan yanke hukuncin kisa ga duk mazinaci da mazinaciya, hakan ya zo a cikin Littafin Levitucus 20:10. Musulunci ma kan yin hukuncin kisa ga duk mazinaci da


mazinaciya kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani surar Nur: 2. Amma dai, ma’anar Alkur'ani na zina ya sha bambam sosai da ma’anar Bible. Bisa ga maganar Alkur'ani, shine, jibintar wani namiji mai aure ko wata mace wadda take da aure a cikin kwanciya da ita bayan aure. Shi kuwa Bible ya kan duba kwanciyar wata mace wadda take da aure ne, ban da namiji mai aure, a matsayin zina. Duba Littafin Kubawar Shari'a 22:22 da Littafin Misalai 6:20, 7:27.


“Idan an iske mutum ya na kwana da mache wadda ta ke da mijin amre, duka biyunsu za su mutu, shi mutumen da ya kwana da machen, da ita machen kuma: hakanan za ka kawas da mugunta daga chikin Israila.”Littafin Kubawar Shari'a 22:22.


“Namijin da ya yi zina da matar wani mutum, watau wanda ya yi zina da matar makwabchinsa, da shi mazinachi, da ita mazinachiya, hakika za a kasha su.” Littafin Leviticus 20:10.


Bisa ga maganar ma’anar Bible, idan wani namiji mai aure ya kwanta da mace mara aure, wannan ba a dubarsa wani laifi ko kadan. Namiji mai aure da ya kwanta da mace mara aure ba mazinaci ba ne. Kuma mata mara aure da suka kwanta da shi ba mazinata bane. Ana aikata laifin zina ne, kawai idan wani namiji ko mai aure ko mara aure, ya kwanta da mace mai aure. A wannan halin namijin ana dubar sa mazinaci ne, koda bai yi aure ba, kuma macen ana dubar ta mazinaciya ce. A takaice, zina ita ce haramtacciyar saduwa da ya shafi macen dake da aure. Kwanciyar wani namiji mai aure da wata mace mara aure ba wani laifi ba ne a cikin Bible. Mene ne matsayin halin kirki na mutum biyu? Bisa ga maganar Kundin fanonin Yahudawa, an duba matar aure ta zama dukiyar mijinta, kuma zina ya zama wani cin hakkin mijin ne da bai cudanya da mutane ba; matar auren, a matsayin dukiyar mijinta, bata da irin hakki nan a kansa. Wato, idan wani namiji ya aikata zina tare da wata mace mai aure, yana cin dukiyar wani namiji ne, kuma, don haka sai a ladabtar da shi. Har yanzu a kasar Isra'ila, idan wani mutum mai aure ya kwanta da wata mace mara aure, 'ya'yansa da macen nan ana dubar su ba ‘yan halal ba ne. Amma, idan mace mai aure ta kwanta da wani mutum, mai aure ne, ko mara aure ne, 'ya'yanta da mutumin nan ba ‘yan halal ba ne kawai, har ma ana daukar su shegu ne, kuma ba za a yarda da su auri Bayahude ba, ban da sabon tuba (cikin addininYahudanci) da wasu shegu. Wannan haramcin aka bar wa 'ya'yan zuri’o’in mutanen zamunna goma, har sai barnar zina, an dauka cewa ta ragu.


A wata fuska kuma, Alkur'ani bai taba dubar mace ta zama dukiyar namiji ba. Alkur'ani, yana bayyana alakar dake tsakanin ma'aurata da fasahar magana da cewa:


“Kuma akwai daga ayoyinsa, Ya halitta muku matan aure daga kanku domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani).” Rum: 21.


Wannan shine, hazikancin Alkur'ani ko imani gama da aure: kauna, tausayi, da zaman-lafiya ba dukiya ba ne da ninkin ka’ida na kirki ba ne, saboda yana daukar wata jama’a dabam daga wata.


BABI NA 9


Bakanci/Alwashi


Bisa ga maganar Bible, dole mutum namiji ya cika bakanci (wa’adin dake kansa) da mai yiwuya ne ya dauka wa Allah. Kada ya karya alkawarin da ya dauka. A wata fuska kuma, bakancin (wa’adin dake kan) wata mace ba tilas ne ya wajaba gareta ba. Sai mahaifinta ya yarda da shi idan tana zaune a gidansa, ko kuma da yardan mijin ta idan ta yi aure. Idan wani mahaifi ko wani miji bai bayar da goyon bayan bakancin diyarsa ko matarsa ba, dukan kabbarar da ta yi za su zama masu rashin amfani kamar yadda ya zo a cikin Bible:


“Sa'anda mutum ya yi wa'adi ga Ubangiji, ko kwa ya yi rantsuwa, shi yi wa kansa hani, ba za ya warware maganassa ba; sai shi aika duka abin da bakinsa ya furta. Idan kuma mache ce ta yi ma Ubangiji wa'adin komi tana yi ma kanta hani, tana kwa yarinya a gidan ubanta, idan ubanta ya ji wa'adinta, da inda ta yi wa kanta hani, ubanta kwa ya yi shuru da ita: dukan wa'adodinta za su tsaya, dukan abin da ta rantse za ta hana wa kanta za ya tsaya. Amma idan ubanta ya shaida rashin yardansa a ranan da ya ji, kodaya chikin wa'adodinta, ko abin da ta rantse za ta hana wa ranta, ba za ya tsaya ba: Ubangiji kwa za ya yafe mata, domin ubanta ba ya yarda mata ba. Idan kwa ta yi amre, tun wa'adinta yana bisanta, ko kwa garajen bakinta, idan ta yi wa kanta hani; mijinta kwa ya ji, ya yi mata shuru a ranan da ya ji: sai wa'adodinta su tsaya, da hanin da ta hana ma kanta za ya tsaya. Amma idan mijinta ya shaida rashin yardansa chikin ranan da ya ji; sai shi wofintadda wa'adin da ke kanta, da garajen bakinta, idan ta yi ma ranta hani: Uangiji kwa za ya yafe mata.amma wa'adin amraruwa, ko kwa sakakkiya, watau kowane abin da ta yi wa kanta hani, za ya tsaya a kanta. Idan kwa ta yi wa'adi chikin gidan mijinta, ko kwa ta yi wa ranta hani da rantsuwa, mijinta kwa ya ji, ya kwa yi mata shuru,ba ya shaida rashin yardansa ba; sai wa'adodinta duka su tsaya, kowane abin da ta yi wa ranta hani za ya tabbata. Amma idan mijinta ya wofintadda su a ranan da ya ji su; sa'annan dukan abin da bakinta ya furta a kan wa'adodinta, ko a kana bin da tayi wa ranta hani, ba za su tsaya ba; mijinta ya wofintadda su; Ubangiji kwa za ya yafe mata. Kowane wa'adi ken an, da kowace kakarfar rantsuwa maikuntata rai, au mijinta ya tabbatadda shi, au ya wofinta. Amma idan mijinta ya yi mata shuru kawai yau da gobe, da hakanan ya tabbatadda dukan wa'adodinta da dukan hanin da ke bisanta: ya tabbatadda su ken an, yayin da ya yi mata shuru a ranan da ya ji su. Amma idan ya wofintadda su bayan ya ji su; shi za ya dauki alhakkinta.” Littafin Lissafi. 30:2 – 15.


Don me wata kalamar mace bai wajabta gareta ba? Amsar wannan tambaya mara wuya ce: saboda kafin ta yi aure, ita mallakar mahaifinta ce, ko kuma mallakar mijinta ce bayan ta yi aure. Ikon mahaifi da yake da shi a kan diyarsa, ya cika har iyakacin cewa idan ya so yana iya sayar da ita. A cikin rubuce-rubucen limaman Yahudawa an nuna cewa: “Namijin mai yiwuya ne ya sayar da diyarsa, amma macen ba ta iya yin hakan; namijin mai yiwuya ne ya yi alkawarin bayar da diyarsa ga aure, amma macen ba ta iya yin hakan.” Litattafin limaman Yahudawa kan nuna cewa, aure yana yin misali da canja iko


daga uban ne, zuwa mijin: “wata yarda da a aure wani, yana sanya wata mace wadda ake dubar zata zama dukiya mai muhimmanci sosai da zata canja -dukiya wadda lalle, ta isa yabo, ba a kai mata hari, ko hallaka da ta-… Alhali, idan an duba matar zata zama dukiyar wani mutum kuma, ba ta iya yin kabara da mai mallakarta bai yarda da ita ba.


Yana kayatarwa a lura da cewa, wannan koyarwar Bible na batun bakancin mata ya samu galibi, mugun sakamakon wani aiki ko abin da ya auku na musu da cewa mai yiwuya ne ya faru wani lokaci daga baya a kan matan Yahudu da Nasara har zuwa farkon wannan karnin da muke ciki. Wata mace mai aure a duniyar kasashen Turai ta Yamma, bata da matsayin mutum na biye da doka. Babu aikinta da ya kasance yana da amfani na biye da doka. Mijinta yana da hurumin kin ma’amular da yarje jeniya, da ciniki, ko akadin da ta kulla. Mata a kasashen Turai ta Yamma (magada masu yawa na abin wasiyyar Yahudu da Nasara), an hana su, ba su iya kulla wata yarje jeniya saboda kusan wani mutum ne ya mallake su. Mata a kasashen Turai ta Yamma sun sha wahala na kusan shekaru dubu biyu, saboda ra’ayin Bible zuwa ga matsayin mata dangane da ubanninsu da mazajensu.


A Musulunci, bakancin kowane Musulmi, namiji ko ta mace yana wajabta gare shi ne ko gare ta. Babu wani da yake da iko kin ma’amala kabbarar kowa kuma. Rashin cin nasarar cika wata muhimmiyyar rantsuwa (da aka kudurta rantsuya a kanta), wadda wani namiji, ko wata mace ta yi, sai a yi kaffarata kamar yadda aka nuna a cikin Alkur’ani:


“Allah ba Ya kama ku saboda yasassa a cikin rantsuwoyinku, kuma amma Yana kama ku da abin da kuka kudurta rantsuwoyi a kansa. To, kaffararsa ita ce ciyar da miskĩni goma daga matsakaicin abin da kuke ciyar da iyalanku, ko kuwa tufatar da su, ko kuwa 'yantawar wuya. Sa'an nan wanda bai samu ba, sai azumin kwana uku. Wannan ne kaffarar rantsuwoyinku, idan kun rantse. Kuma ku kiyaye rantsuwoyinku. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinsa, tsammaninku kuna godewa”. Ma'idah: 89.


Sahabban Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi), maza da mata, sun kasance suna yin masa mubaya'a baka da baka. Mata da ma maza sun taho wurinsa cikin 'yanci suka yi kabarar rantsuwoyinsu (masa mubaya’a) kamar yadda ya zo a cikin Alkur'ani:


“Ya kai Annabi! Idan mata mũminai suka zo maka suna yi maka mubaya'a a kan ba za su yi shirki da Allah ba ga kome, kuma ba su yin sata kuma ba su yin zina, kuma ba su kashe, ya'yansu, kuma ba su zuwa da karya da suke kirkirawa a tsakanin hannuwansu da kafafunsu kuma ba su saba maka ga wani abu da aka sani na sharĩ'a, to, ka karbi mubaya'arsu, kuma ka nemi Allah Ya gafarta musu. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin-kai”. Mumtahinah: 12.


Wani mutum ba zai iya yin ransuwa ba a maimakon diyarsa, ko matarsa. Ko wani mutum ya ki ma’amala da rantsuwar da mace danginsa ta yi.


BABI NA 10


Dukiyar Matar Aure


Addinan nan uku ra'ayinsu ya zo daya a kan imani tsayayye wanda bai rawa game da muhimmancin aure da rayuwar iyali. Sun kuma yarda da shugabanci mijin kan iyalinsa. Duk da haka, akwai bambance-bambancen kin goyin bayan ayyuka da ake dubarsu mara kyau tsakanin wadannan addinai uku dangane da iyakokin wannan shugabancin. Hanyar al’adar Yahudu da Nasara wadda ba ta yi kama da ta Musulunci ba, kusan tana bayar da shugabancin mijin zuwa ga mai mallakar matarsa.


Hanyar al’adar Yahudawa kan zancen matsayin da miji ke da shi zuwa ga matarsa abin da yake tabbatar da hazikancin cewa yana mallakar ta ne, kamar yadda yake mallakar baiwarsa. Wannan hazikanci ya zama dalilin dake bayan ka’idodi na hali wanda ba na adalci ba ne, saboda ana amfani da shi a wani halin amma ba a wani kuma ba, a cikin dokokin aikata zina, da bayan kwazon mijin don ya ta da bakancin matarsa. Wannan hazikanci shine ke da alhakkin hana wa mace ikon dukiyarta, ko ladan aikinta. Da zarar wata mace Bayahudiya ta yi aure, ta rasa ikon dukiyarta gaba daya, da ladar aikinta zuwa ga mijinta (wato komai nata ya koma hannun mijinta ke ne). Limaman Yahudawa sun furta sosai da cewa hakin mijin kan dukiyar matarsa a matsayin wani halin cewa shine sakamako kai tsaye da na halittar mallakarta da yake da shi: “Tunda mutum ya kai ga mallakar macen, to me zai hana shi mallakar dukiyarta kuma?” kuma “Tunda ya samu mace, shin, me zai sa ba zai samu dukiyarta ba kuma?” Ta haka, aure kan sanya mace mai arziki komawa bata da komai (talaka). Littafin Yahudawa (Talmud) ya kan bayyana halin kudin matar aure kamar haka:


“Ta yaya mache za ta mallaki kowane irin abu? Dukkan abin da ta mallaka ya zama na mijin ta. Da abin da ya mallaka da wanda ta mallaka duk mallakin sa ne… kudaden dake shigo mata ta bangare kasuwanci ko wani abu makamancin haka, da abinda za ta samu a kan hanya, duk sun zama nasa. Kayayyakin kula da gida (ababen masarufi), kai har marmashin burodin dake bisa teburi, duk nasa ne. Shin ta samu ta gayyaci bako gidan ta sannan ta ciyar da shi, idan ta aikata haka, ya zama ta yi wa mijin ta sata…” San. 71a, Git. 62a.


Hakikan al’amarin dai shine, dukiyar wata Bayahudiya na dauke da ma’anar jan hankulan maza wadanda take son su aurenta ne. Iyalin Yahudu za su ba wa diyarsu mace wani rabo daga cikin gadon mahaifinta, don amfani da shi a matsayin sadaki idan aka yi aure. Irin wannan sadakin ne ya sanya diyan Yahudawa mata wani nauyi rashin bukatarsu ga ubaninsu. Mahaifin kan rene diyarsa shakaru da yawa, kuma sa’anan ya yi tanadin aurenta, ta hanyar bayar da sadaki mai kauri. Ta haka, wata diya mace a cikin iyalin Yahudu ta kasance bashi da babu jimlar kayan kudi. Wannan bashi ya kan bayyana abin da ya sa ba a bayyana murna (yin shagali) da haihuwar diya mace a tsohuwar al'ummar


Yahudawa (duba shashin “Kunyatattatun Diya Mata” domin karin bayani). Sadakin ya kasance kyautar aure ce da aka gabatar da ita ga ango a karkashin sharuddar haya na gida. Mijin zai yi kamar mai mallakar sadakin ne, amma, bai iya sayar da shi. Amaryar za ta rasa ikon sadakin a daidai lokacin auren. Kuma, an sa rai ta yi aiki bayan auren, kuma dukan ladan aikinta, za su shiga hannun mijinta ne, sakamakon kudin abincinta, wanda ya kasance takalifinsa ne. Tana iya sake samu dukiyarta kawai ne, ta halaye guda biyu su ne: (1) Ta hanyar kashin aure, ko (2) Mutuwar mijinta. Da ita ce ta fara mutuwa, zai gaje dukiyarta. Idan mijin ya mutu, matar auren ta iya sake samun nata dukiyar kafin aurenta, amma bata da hakkin yin gadon rabo daga cikin dukiyar mallakar mijinta mamaci. Sai a kara da cewa, angon ma ya gabatar da wata kyautar aure ga amaryarsa, amma duk da haka kuma, ya kasance mai wannan kyautar ne muddin suna da aure.


Addinin Kirista, ya bi irin hanyar al’adar Yahudanci sai a kwanan nan. Dukan hukumomin addini da na mazauna kasa daya, a kasashen Kirista dake cikin ikon Rum [Roman (bayan sarki Qostantina)], sun bukaci wani yarjejeniyar dukiya a matsayin wani sharadin shaidar aure. Iyalai su kan mika wa diyansu mata yawaitacen sadakoki kuma, a wani abin da ya tabbata, maza na dan nuna son yin aure da wuri, a yayin da iyalai suna jinkirtad da aurayyan diyansu, sai har daga baya fiye da yadda ya kasance ga al’ada. A karkashin dokar addinin Kirista, wata matar aure ta kasance mai hakkin samun biya sadakinta ne, ga wasu wahaloli da ta sha idan auren ya kasance ya mutu, sai fa idan an kama ta da laifin aikata zina. A irin wannan hali, ta soke hakkinta na sadakin, wadda ya saura a hannun mijinta. A karkashin dokar Kirista, da shari’a ta tsakanin mutum da mutum, mace mai aure a Kiristocin Turai da Amurka ta rasa hakkokin dukiyarta sai har a karshen karni na sha-tara da farkon karni na ashirin. Misali, hakkokin mata a karkashin dokar Turawa, an tattarasu kuma aka bugasu a shekarar 1632. Wadannan hakkoki sun hada da: "Cewa (dukiya) wacce miji ya mallaka tashi ce. Cewa (dukiya) wacce mace ta mallaka ta mijinta ce.” Macen ba wai kawai ta rasa dukiyarta a lokacin auren ba ne, ta ma rasa darajanta na mutum da kansa. Babu wani aikinta da ya kasance yana da amfani na biye da doka. Mijinta na iya kin ma’malar da sayarwa da ta kulla ko kyautar da ta bayar, kasancewar abin dauren da bai da amfani na biye da doka. Mutumin da ta kulla yarjejeniya da shi, an riki shi a matsayin mai laifin sharakawa a wata zamba (wato algus). Dadin dadawa, ba ta iya kai kara, ko a kai kara da sunanta, kuma ba ta iya kai karar mijinta. Wata mace mai aure ta kasance ana kula da ita kamar jaririya ce a idon doka (shari’a). Matar auren ta zama ta mijinta ne kawai, kuma saboda haka ta rasa dukiyarta, da darajarta na mutum da kansa na biye da doka, da sunan danginta,


Tun karni na bakwai ne Musulunci ya bai wa mata masu aure 'yancin kai na mutum da kansa, wane Yahudawa da Kirista na kasashen Turai ta Yamma suka hana su, sai har dan kwanan nan. A Musulunci, amarya da danginta, ba su a karkashin wani takalifi ko ta halin kaka, da su gabatar da wata kyauta ga angon. Yarinya a wani iyalin Musulmi, ba dawainiya (bashe) ba ce. A Musulunci wata mace mai halin girma ce da ba ta bukatar gabatar da kyaututtuka don ta jawo hankulan maza da zasu iya zama mazan aurenta. Angon ne, wanda dole ne ya gabatar da kyautar aure ga amaryar. Wannan kyautar, ana dubar ta dukiyarta ce, kuma ko angon ko dangin amaryar basu da rabo a ciki, ko ikon ta. A wasu al'ummomin Musulmi a yau, kyautar auren ta dolar Amurka dubu dari na lu'u-lu'u ba na al’ada da ake ki ba ne. Amaryar kan rike kyautar aurenta ko da daga baya an


sake ta. Ba a yarda wa mijin ya dauki rabo a cikin dukiyar matarsa ba face abin da ta kan mika masa da yardarta. Alkur'ani ya fito fili karara ya bayyana matsayinsa game da wannan lamari, kamar haka:


“Kuma ku bai wa mata sadakokĩnsu da saukin bayarwa. Sa'an nan idan suka yafe muku wani abu daga gare shi, da dadin rai, to, ku ci shi da jin dadi da saukin hadiya” Nisa: 4.


Dukiyar matar auren da ladar aikinta suna karkashin cikakken ikonta ne, kuma na amfaninta ita kadai, tunda daukar dawainiyar kudin abincinta da na 'ya'yanta alhakin (takalifin) mijinta ne. Ko yaya matar ta kai da arziki, ba a tilasta mata daukar dawainiyar gida ba, sai fa in ita ne da kanta, ta kan bugi kirjin yin hakan da son ranta. Ma'aurata kan gaji junansu. Kuma, a Musulunci, mace mai aure kan rike 'yancin kanta na mutum da kansa na biye da doka, da sunan gidan su. Wani alkali Ba'amurke, ya ambata hakkokin mata Musulmi, cewa: "Wata yarinya Musulma mai yiwuya na iya yin aure sau goma, amma mazan nata da ta aura dabam dabam, ba su iya dauke wa kadaicenta da wasu dabam. Ita Duniyar rana ce da kanta tare da wani suna da doka na mutum da kansa.”


BABI NA 11


Saki


Addinan nan uku suna da banbamcin ra’ayoyi masu isa a fada na kwarai, game da saki. Gaba daya, Addinin Kirista ya kan kin saki kwarai. Littafin Sabon Alkawari ya kan ba da shawarar fadin ra’ayinsa sosai da sosai cewa aure dangantaka ne da bai iya karewa. An ce Annabi Isa (A.S.) ke da takallifin cewa: “Amma dai ina che muku, kowanene ya saki matatasa, im ba domin fasikanchi ba, yana sa ta ta zama mazinachiya: kuma dukan wanda ya amri sakakkiya, zina ya ke yi.” Littafin Matta 5:32. Wannan rashin daidaituwar abin da ya dace shine, rashin nunawa ko karba ba tare da wata shakka ba. A kan ji wani halin kirki cikkake ne, da al'ummomin 'yan-Adam ba su taba samu ba. A lokacin da mutum da matarsa su ka gane gaskiyar cewa, rayuwar aurensu ta gagari gyara, haramta saki ba zai masu kyau ba. Tilasta mugun abokan zamar mutum da matarsa, ci gaba da zama tare, ba da son ransu ba, ba ta da ko karfi, ko dama dama. Ba mamaki ba ne, dukan duniya Kirista an tilasta ta da ba da iznin saki. Yahudanci, a wata fuska, ya kan yarda da aiwatar da saki koda kuwa babu dalili. Littafin Tsohon Alkawari ya kan bai wa mijin ikon sakin matarsa, koda ya ki jininta ne, kamar haka:


“Kadan mutum ya dauki mache ya yi amre da ita, ya kwa zama ba ta da tagomashi a idonsa, domin ya iske wani abin da ba daidai ba a gareta, sai ya rubuta mata takardar saki, shi bata chikin hannunta, shi sallameta daga gidansa. Sa'anda ta fita daga gidansa kuma, in ta so, ta tafi ta zama matar wani mutum. Idan mijin na baya kuma ya ki ta, ya rubuta mata takardar saki, ya bata chikin hannunta, ya sallameta daga gidansa; ko kwa


idan mijin na baya ya mutu, wanda ya dauketa ta zama matatasa; mijin nan nata na fari bashi da iko ya dauketa ta zama matatasa; bayan da ta kazamtu; gama wannan abin kyama ne a wurin Ubangiji: ba kwa za ka sa kasa ta yi zunubi, wanda Ubangiji Allahnka ya ba ka gado ba. ” Littafin Kubawar Shari'a 24:1 – 4.


Ayoyin da suka gabata sun kawo wasu babbar jayayya a tsakanin maluman Yahudawa, saboda sabaninsu a kan fassarar kalmomin “rashin tagomashi” da “kyama” da kuma “ki” wadanda aka ambata a cikin ayoyin da suka gabata. A kan rubuta ra’ayoyinsu dabam dabam a Talmud (littafin Yahudawa) kamar haka:


“Mazhabar Shammai tana ganin cewa, bai kamata mutum ya saki matar sa ba, har sai ya same ta da laifukan da suka shafi zina, yayin da mazhabar Hillel ke ganin cewa, ya samu ya sake ta, koda kuwa ta bata masa wani abinci ne da ta dafa da ba ya so. Liman Akiba kuwa cewa ya yi: Ya samu ya sake ta a lokacin da ya ga wata wadda ta fi ta kyau.” Gittin 90a-b.


Littafin Sabon Alkawari ya kan bin ra'ayin mazhabar Shammai ne, sai dokar Yahudawa ta bi ra’ayin Hillelites da na Liman R. Akiba. Tunda ra'ayin mazhabar Hillelites ce ta rinjaya, ya kasance hanyar dokar al’adar Yahudawa wadda ba ta tsinke ba, a bai wa mijin ‘yancin sakin matarsa, ba tare da ta yi masa wani laifi ba. Shi kuwa Littafin Tsohon Alkawari, ba wai kawai ya bai wa mijin ikon sakin matarsa “mara tagomashi” ba ne, yana dubar sakin wata “mumunar mace” wani takalifi ne, inda yace:


“Mumunar mache na kawo kaskanchi, kallon dukuku, da chiwon zuchiya. Sanyin hanu da runin gwiwa sun tabbata ga mutumen da matarsa ta kasa franta masa rai. Mache che asalin zunubi, sa'annan sabili da ita ne dukanmu za mu mutu. Kada ka bari hujajjen tulu ya zudda ruwa, ko kwa mugunyar mache ta fadi dukan abin da ta ke so. Idan kulawarka bai gamsheta ba, to ka saketa kana ka koreta.” Ecclesiasticus 25:25.


Matar aure da suka tilasta wa mazajennsu da su sakesu an rubuto wadansu kayyadaddun aiyyuka a cikin Talmud (littafin Yahudawa) kamar haka: “Cin abinci a kan hanya, shan abin sha da yawa a kan hanya, shayar da jariri a kan hanya, idan ta aikata kowanne daga cikin wadannan laifuka, Liman Meir ya ce, dole ne, ta rabu da mijin ta.” Git. 89a.


Talmud (littafin Yahudawa) ya sake wajabta sakin bakarariyar mace (wadda ta kai shekaru goma ba tare da ta haihu ba), inda ya ce: “Limamin mu na ganin cewa, idan mutum ya auri mace, kuma ya zauna da ita har shekaru goma ba tare da ta Haifa masa da ba, to ya sake ta.” Yeb 64a.


Matan aure, a gefe guda, ba su iya soma saki a karkshin dokar Yahudanci, Amma dai, matar aure Bayahudiya, tana iya nemar hakki don saki daga wurin mijinta a gaban kotun Yahudawa, da sharadin cewa akwai wani dalili mai karfi da kan kasance. Wani filin ra’ayoyi ‘yan kadan ne, aka yi tanadinsu wa matar auren ta nemi hakkin wani saki. Wannan filin ra’ayoyi su kan hada da: Wani miji dauke da nakasassun jiki, ko cutar fatar jiki, da wani miji da bai iya biya wa matarsa bukata na sha’ain ma’amular maza da mata, da dai sauransu. Kotun kan daure wa matar gindin nemar hakkin wani saki, amma ba zai iya raba (kasha) auren ba. Mijin kawai ne zai iya kashe auren, ta hanyar bai wa matar takardar saki. Kotun na iya masa bulala, da cin sa tara, da sa shi kurkuku, da kuma yi masa azabar kora da bayyana cewa, ba zai taba zama cikin kungiyar mutane cocin Kirista ba, don a tilasta shi ya ba da takardar saki na tilas ga matarsa. Amma dai, idan mijin mai tsaurin kai issashe ne, yana iya kin bayar da sakin matarsa, kuma ya ajiye ta a daure, ya ci



Posts na kwanan nan

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA