NI MUSULMI NE
IMANI DA ALLAH
Ni Musulmi ne…….
∙Na yi imani da Allah shi kaxai, ba shi
da abokin tarayya, babu wani ubangiji
bayan shi, bai haifa ba, ba a haife shi
ba, sam ba shi da kwatankwaci.
∙Mahaliccin sammai da qassai, kuma
mamallakinsu, masanin abin da ya
vuya da abin da yake a bayyane, rayayyen
da ba ya mutuwa, tsayayyen da
ba ya barci.
∙Yana da sunaye kyawawa da sifofi
maxaukaka, a cikinsu akwai sunaye
casa'in da tara, wanda ya kiyaye su ya
٦
-6-
NI MUSULMI NE
kuma roqi Allah da su ya shiga
aljanna.
∙A cikinsu akwai sifofin kaxaita Allah,
shi mai girma da xaukaka shi ne "alwaahidu"
al-ahadu" "al-fardu' (ma'ana
shi xaya ne tilo), shi ne ake nufi da
buqata, mamallakin kowa da komai
kuma mai mulki.
∙Da sifofin xaukaka; ka ga shi ne mai
yawan hikima, qwararre, mai shiryatarwa,
kuma shi ne gaskiya, na farko
da na qarshe, na bayyane da na voye,
wanda zai gaje komai kuma wanzajje,
mawadaci kuma mai tsarki, mahalarci
makusanci, mai hukunci mai adalci,
-7-
٧
NI MUSULMI NE
hasken sammai da qassai, ma'abocin
xaukaka da karamci.
∙Da sifofin girma; shi ne mabuwayi mai
xaukaka da girma, mai sa a yi dole,
mai tsananin qarfi, wanda ya rinjayi
kowa, mai iko kuma mai qaddarawa,
mai taimako maxaukakin da babu
irinsa.
∙Da sifofin iko; shi ne masani mai ji
mai gani, rayayye.
٨
-8-
NI MUSULMI NE
mai riqewa mai shimfixawa, mai
dankwafarwa mai xaukakawa, mai
buwayarwa mai qasqantarwa, mai
bayarwa mai hanawa, mai amfanarwa
mai cutarwa, mai rayarwa mai
matarwa, mai qaddamarwa mai
jinkirtarwa.
∙Da sifofin da suke nuna halittunsa; shi
mahalicci ne mai yin abu ba da misali
ba, mai surantawa mai samar da
komai, gwani wajen qirqirar halitta ba
tare da ya ga ta wani ba, mai dawo da
abu mai tashin komai, mai tattara
komai mai yawan baiwa da yawan
buxi, mai yawan azurtawa mai wadatarwa,
wanda ya san qididdigar komai,
shi ne wanda ya mamaye komai, mai
-9-
٩
NI MUSULMI NE
kiyayewa mai lura da komai, mahaliccin
sammai da qassai.
∙Da sifofin rahama; shi ne mai rahama
mai jin qai, mai tausayi mai baiwa, mai
son bayi mai kyautatawa, mai kuma
yawan gafara da afuwa mai amsar
tuba, mai aminci da bayar da kariya
da tsaro, mai tausayi, wanda ake gode
masa, mai karamci da ni'imtarwa, mai
baiwa mai taimako, mai amsar addu'a
mai yalwa mai haquri mai shiryatarwa,
mai yawan haquri mai yawan
tausasawa, majivincin al'amurra, mai
ceto mai taimako, mai karvar tuba.
∙Ya yi wa xan adam ni'imomin da ba
su da iyaka, babu wata ni'ima da bawa
yake ciki face daga Allah shi kaxai
take, shi ne wanda ya halicce shi ya
kuma raya shi, ya kuma sanya masa ji
١٠
-10-
NI MUSULMI NE
da gani, ya karrama shi ya kuma kyautata
masa.
∙Saboda haka ne ya zama wajibi akan
bawa ya kaxaita Allah shi kaxai wajen
bauta –wadda ita ce aikata abin da aka
bayar da umurni da nesantar abin da
aka hana-, domin babu wani da ya
cancanci ibada sai Allah.
∙Haka ma lallai Allah ya san dukkan
halayen da bawa yake ciki, shin na
xa'a ne ko na savo, dole ne bawa ya
cika zuci-yarsa da ganin kwarjinin
Allah mai tsarki da xaukaka, da ganin
girmansa da sonsa, ya kuma ji kunyar
sava masa, ya nesanci haka saboda
Allah yana ganinsa, ya kuma san abin
da yake yi na savo.
∙Ya yi farin ciki da kyawawan ayyukan
-11-
١١
NI MUSULMI NE
da zasu kusanta shi da yardar mahaliccinsa
mai girma da xaukaka, ya kuma
ci gaba da aikata su har ya sami
matsayin "al-ihsan"; saboda imani yana
qaruwa da qaruwar xa'a, yana kuma
raguwa da aikata savo.
∙Ka da ya miqa ragamarsa ga sha'awa
ko son zuciya ko bidi'a, ya miqa ragamarsa
ne kawai ga Allah shi kaxai,
yana mai bin umurnin Annabi (sallallahu
alaihi wa sallam), ka da manufarsa
ta aiki ta zamo neman karikitan
duniya, a maimakon haka ya nemi
ladan Allah ne kawai da su.
∙Haka ma lallai Allah mai rahama ne
ga mutum sama da rahamar da uwa
take yi wa xanta, kuma rahamarsa ta
yalwaci dukkan komai, don haka
wajibi ne a kan bawa ya roqe shi, ya
١٢
-12-
NI MUSULMI NE
kuma qasqantar da kansa a gabansa
wajen neman buqatunsa na duniya da
na lahira, ka da ya roqi kowa.
∙Saboda babu wata fa'ida a roqon wani
ba Allah ba, babu wanda ke mallakan
cikakken iko ban da Allah, babu wanda
yake jin abin da ke faruwa a sirri da
wajen ganawa in ba Allah ba, babu
wanda ke mallakar qaddara wani abu
in ba Allah ba, don haka babu mai
ikon amsa addu'arsa in ba Allah ba.
∙Saboda haka bai halatta ga musulmi
ya roqi qabari ba, ko ya roqi na cikin
qabarin, ko wane ne aka rufe a cikin
qabarin kuwa, saboda ba ya jinsa, ta
ma yaya
zai amsa masa ko ya amfane shi?
Lallai Allah shi kaxai shi ne mai amfa-
13-
١٣
NI MUSULMI NE
narwa, mai kuma cutarwa, saboda
haka bai halatta musulmi ya gina masallaci
akan qabari ba, domin Annabi
(sallallahu alaihi wa sallam) ya hana
yin haka.
∙Saboda haka wajibi ne akan bawa ya
yi duba zuwa ga rauninsa da kuma
qarfin Allah mabuwayin sarki, ya
kuma sake duba talaucinsa da wadatar
Allah maxaukakin sarki, ya kuma
duba jahilcinsa da sanin Allah maxaukakin
sarki, ya kuma yin duba zuwa ga
qasqancinsa da girman Allah maxaukakin
sarki.
∙Ya kuma san cewa lallai girma da
buwaya suna ga Allah ne da manzonsa
da muminai.
∙Domin haka ya wajaba ya zama cikin
١٤
-14-
NI MUSULMI NE
waxannan muminan, waxanda ba sa
dogara da kowa sai Allah, ba sa neman
taimakon kowa sai Allah, ba sa neman
tsari daga kowa sai Allah, ba sa neman
ceton kowa sai Allah, ba sa tsoron
kowa sai Allah, ba sa fatan komai daga
wurin kowa sai Allah, ba sa roqon
kowa sai Allah, ba sa yanka saboda
kowa sai Allah, ba sa bakance saboda
kowa sai Allah, ba sa ranstuwa da
kowa sai Allah, ba sa xaura layu da
tsumburkai, ba sa gasgata bokaye da
masu tsubbu da taurari da matsafa, ba
kuma sa zuwa wajensu.
∙Su ba sa shu'umanci, suna kuma takatsantsan
da kura-kuren harsunansu
kan ka da su ja su zuwa wuta. Ba sa
cewa: "Abin da Allah ya so da abin da
wane ya so" ko "ba domin Allah da kai
-15-
١٥
NI MUSULMI NE
ba" ko "na dogara da Allah da kai",
a'a su ne masu cewa: "Na dogara ga
Allah shi kaxai" ko " abin da Alah ya
so sannan wane ya so"; saboda waxancan
kalmomi suna daidaita tsakanin
Allah da bayinsa, suna kuma cikin
qaramin shirka.
∙Kamar yadda ya wajaba mu yi imani
da Allah, haka ma ya wajaba mu
kafirce wa xagutai.
∙Babban xagutu shi ne shaixan, da
kuma duk wanda aka bauta masa ba
Allah ba da yardarsa.
∙A cikin waxanan xagutan akwai
wanda duk ya sanya wata doka da ta
haramta abin da Allah ya halatta, ko
ta halatta abin da Allah ya haramta.
∙Haka ma xagutu ne duk wanda ya yi
١٦
-16-
NI MUSULMI NE
kira zuwa ga aikata haka, ko ya
umurci mutane da shi, ko ya yi hukunci
da shi, saboda ya qetare iyakar
halitta na ya ji ya kuma bi.
∙Allah shi kaxai shi ne ya halicci
mutane, ya kuma san mene ne zai
gyara su, don haka babu wani wanda
ya isa ya sanya masu doka in ba shi ba.
-17-
١٧
NI MUSULMI NE
(2) IMANI DA MALA'IKU
∙Na yi imani da mala'ikun da Allah ya
halicce su daga haske, ya kuma sanya
musu fukafukai, wasu bibbiyu wasu
uku-uku wasu kuma hurhuxu. Su
kuma ba sa cin abinci, ba sa shan ruwa,
ba sa barci, ba sa kuma auratayya, ya
umurce su da wasu ayyuka suna kuma
aikatawa.
∙Mala'iku dawwama suke yi cikin aikin
xa'a ba sa gajiya, ba sa kuma savon
Allah, suna jin tsoron ubangijinsu da
yake sama da su, a cikinsu akwai
wanda yake sujada tun ranar da Allah
ya halicci sammai da qassai har zuwa
ranar alqiyama, idan kuma ya xaga
kansa sai ya ce: mun ambaci tsarkinka
ya Allah, ba mu bauta maka da bautar
١٨
-18-
NI MUSULMI NE
da ta dace da kai ba.
∙Su bayin Allah ne, ba kuma mata ba
ne, ba kuma mataimakansa ba ne,
suna ceton muminai da izinin Allah a
ranar alqiyama.
∙A cikinsu akwai masu kiyayewa: su ne
waxanda suke bai wa bayi kariya ga
barin abubuwan qi.
∙A cikinsu akwai masu girma kuma
marubuta: su ne waxanda suke rubuta
ayyukan bayi na alhairi da na sharri
(masu kyau da munana)
∙A cikinsu kuma akwai masu tasbihi:
su ne waxanda suke tasbihi dare da
rana ba sa gajiya har zuwa ranar
alqiyama.
∙A cikinsu akwai masu shawagi: su ne
-19-
١٩
NI MUSULMI NE
waxanda suke halartar majalisun
zikiri da na karatun Alqur'ani da
majalisu na ilimi.
∙A cikinsu akwai waxanda suke xaukan
al'arshin mai rahama: su takwas ne, su
manyan halittu ne daga cikin halittun
Allah, tsuntsu zai iya tashi daga gefen
kunnen xaya daga cikinsu ya yi tafiyar
shekaru xari biyar kafin ya isa zuwa
wuyarsa.
∙A cikinsu akwai mala'ikan mutuwa:
shi ne mai amsar rayukan bayi da
izinin Allah, yana da mataimaka.
∙A cikinsu akwai Israfilu: wanda zai
busa qaho dukkan halittu su mutu
kafin tashin alqiyama, sannan ya sake
٢٠
-20-
NI MUSULMI NE
busawa nan take ka gansu a tsaye suna
duban juna suna sauraro.
∙A cikinsu akwai Mika'ilu: shi ne wanda
aka wakkala masa ruwan sama.
∙A cikinsu akwai Ridwan: shi ne mai
tsaron aljanna, yana da mataimaka
waxanda duka suke kai-komo wajen
jin daxi da walwalar muminai a
aljanna.
∙A cikinsu akwai Maliku: shi ne mai
tsaron wuta, yana da mataimaka –
shugabanninsu su goma sha tara neakwai
gudumomin qarfe tare da su,
suna yi ma kafirai azaba da su ne a
cikin wuta,- Allah ya kiyaye mu-.
-21-
٢١
NI MUSULMI NE
∙Babban mala'iku shi ne Jibrilu:
wanda aka wakkala masa wahayi zuwa
ga annbawa da manzanni.
∙Tabbas Annabi (sallallahu alaihi wa
sallam) ya ganshi a sifarsa da Allah ya
halicce shi, ya toshe sasanni saboda
girmansa, yana fukakai xari shida, shi
ne wanda ya kifar da alqaryar Annabi
Luxu da gefen fuffukensa, ya xaga ta
sama ya juya ta ya kuma kifar da ita,
ya sanya samanta ya koma qasa (juyin
waina).
∙Akwai kuma adadi masu yawa
waxanda ba waxannan ba, -babu
wanda ya san iyakan rundunar
ubangijinka in ba shi ba.
٢٢
-22-
NI MUSULMI NE
[ المدثر: ٣١ ] ﴾ μ´ ³ ² ± ° ¯﴿
∙ Mala'iku suna son muminai waxanda
Allah yake sonsu, suna masu addu'a,
suna kuma neman masu gafara.
∙Mala'iku duk da qarfinsu suna zuwa
yaqi tare da muminai.
-23-
٢٣
NI MUSULMI NE
(3) IMANI DA
LITATTAFAI
∙Na yi imani da litattafan Allah
waxanda ya saukar zuwa ga manzanninsa,
kuma lallai duka –a asalin
yadda aka saukar da su- maganar
Allah ne da ya yi masu wahayi domin
su isar da shari'arsa da addininsa,
manyan waxannan litattafai su ne:
∙Alqur'ani mai girma da aka saukar
wa manzonmu Muhammadu (sallallahu
alaihi wa sallam).
∙Injila da aka saukar wa Annabi Isah
(alaihis-salam).
∙At-taura da aka saukar wa Annabi
Musa (alaihis-salam).
∙Zabura da aka saukar wa Annabi
٢٤
-24-
NI MUSULMI NE
Dauda (alaihis-salam).
∙Da kuma shafukan da aka saukar wa
Annabi Ibrahim (alaihis-salam)
∙A cikinsu akwai waxanda aka caccanja
su kafin saukar da Alqur'ani.
∙Kuma lallai Alqur'ani mai girma ya
mamaye dukkan waxannan litattafan,
shi ne alqali akan dokokinsu da
hukunce-hukuncensu, wanda kuma
daga saukansa ya share duk wani
hukunci na su da ya sava masa.
∙Kuma lallai Allah ba zai karvi aiki da
komai ba a ranar alqiyama sai aiki da
Alqur'ani, ba zai karvi aiki da litattafan
da suka gabata ba bayan saukar
Alqur'ani ga Annabi Muhammadu
(sallallahu alaihi wa sallam).
∙Tabbas Alqur'ani magana ne na Allah
-25-
٢٥
NI MUSULMI NE
mai gajiyarwa, yana da tsarki, varna
ba ta zuwa masa ta ko'ina, duk wanda
ya yi magana da shi ya yi gaskiya, duk
wanda ya yi hukunci da shi ya yi
adalci, duk wanda ya yi aiki da shi to
kuwa lallai an shiryatar da shi zuwa ga
kyakkyawar hanya, duk wanda ya yi
riqo da shi ya sami babban rabo kuma
ya tsira, wanda kuma ya juya masa
baya ya tsinci kansa cikin halakakku.
∙Ma'abota Alqur'ani su ne jama'ar
Allah kevavvun Allah, fiyayyen
mutane shi ne wanda ya koyi karanta
Alqur'ani da aiki da shi ya kuma koyar
da shi, domin zai zo ranar alqiyama ya
yi ceto ga waxanda suka karanta shi
suka kuma kiyaye shi sannan suka yi
aiki da shi, yana mai neman aljanna ga
iyalansa.
٢٦
-26-
NI MUSULMI NE
∙Alqur'ani yana tsarkake zukata ga
barin abin da ke gurvata su na
abubuwa masu rikitarwa da
sha'awaice-sha'awaice, yana kuma
kusanta su zuwa ga mahaliccinsu mai
girma da xaukaka, yana kuma
kwaxaitar da su zuwa ga yin aikin da
zasu sami rabo da dawwamammiyar
ni'ima.
∙Cikin ladubban karanta Alqur'ani
akwai:
Tsarki da alola.
Fuskantar alqibla.
Zama cikin ladabi da natsuwa.
Rashin gaggawa wajen karanta
shi.
Tsoron Allah da qasqantar da
-27-
٢٧
NI MUSULMI NE
kai.
Bayyanar da baqin ciki akan
zunubai da wuce gona da iri.
Kuka saboda tsoron Allah da
ganin girman maganarsa.
Rashin xaga murya wajen
karanta shi saboda ka da ya
daburta masu sallah.
Lura da tadabburi wajen karanta
shi.
Halarto da zuciya.
Tunani cikin ayoyin Allah.
Kuma mu tabbatar da cewa
tsayar da hukunce-hukuncen
wannan littafin tsakanin mutane
shi ne babban dalilin samun
xaukaka da nasara akan abokan
٢٨
-28-
NI MUSULMI NE
gaba a bayan qasa.
Ya xan uwa musulmi ka yi gaggawa
zuwa ga ubangijinka, ka riqe wannan
littafi gam, ka yi fatar ka da wani ya
riga ka zuwa wajen Allah, Allah yana
farin ciki da komowarka zuwa gare shi
fiye da farin cikin da iyalai suke yi
idan wanda ba ya nan a cikinsu ya
komo.
-29-
٢٩
NI MUSULMI NE
(4) IMANI DA
MANZANNI.
∙Na yi imani da manzannin Allah, lallai
Allah ya zavi manzanni daga cikin
mutane, ya yi masu wahayin
shari'arsa, ya kuma umurce su da su
isar zuwa ga mutane, kuma duk wanda
ya bi su zai shiga aljanna, wanda kuma
ya sava masu zai shiga wuta.
∙Sannan ya qarfafi gwiwarsu da mu'ujuzozi
waxanda suka bayyanar da
gaskiyarsu, domin su yi amfani da su
ga duk wani wanda ya qaryata su, su
kuma zama hujja ne a gare su.
∙Kuma tabbas farkon manzanni shi ne
Annabi Nuhu (alaihis-salam), cikamakonsu
kuma shi ne Annabi Muhammadu
(sallallahu alaihi wa sallam).
٣٠
-30-
NI MUSULMI NE
∙Kuma mutane ne su, suna cin abinci.
Suna sha, suna kuma auratayya, suna
rashin lafiya, suna mutuwa, kuma su
ne fiyayyun halittun Allah, an katange
su ga barin yin savo.
∙Manzannin Allah suna da yawa, a
cikinsu akwai waxanda Allah ya
ambace su a cikin Alqur'ani, waxanda
su ne: Annabi Muhammadu (sallallahu
alaihi wa sallam) da Ibrahim Khalilurrahman
da Musa Kalimul-lah da Isah
Kalmar Allah da Nuhu (alaihimussalam)
waxanda su ne "ulul-azmi"
daga cikin manzani (tsira da aminci su
tabbata a gare su). Akwai kuma
Isma'il da Ishaq da Ya'akub da
Haruna da Ayuba da Yunusa da
Sulaiman da Dauda da Yahya da
Zakariyya da Hudu da Salihu da
-31-
٣١
NI MUSULMI NE
Yusuf da Shu'aibu da Ilyasu da Luxu
da Zulkifli da Idris da sauransu masu
yawa, a cikinsu akwai waxanda Allah
ya bayar da labarinsu a cikin
Alqur'ani, akwai kuma waxanda bai
bayar da labaransu ba.
∙Farkon abin da manzanni suka yi kira
akai shi ne kaxaita Allah, kuma mafi
girman abin da suka hana shi ne haxa
Allah da wani a wajen bauta, dukkansu
sun zo da musulunci ne da kira
zuwa ga kaxaita Allah, duk kuwa da
cewa shari'o'insu da hanyoyin yin
bautarsu ga Allah mai girma da
xaukaka ya xan canja saboda canjin
zamunnansu da garuruwansu.
∙Kuma lallai manzanni sun yi bishara
da zuwan Annabi Muhammadu
(sallallahu alaihi wa sallam), sun kuma
٣٢
-32-
NI MUSULMI NE
umurci mabiyansu da su yi imani da
shi (sallallahu alaihi wa sallam) idan
an aiko shi suna nan.
∙Bambancin dake tsakanin manzo da
annabi shi ne: shi manzo an aiko shi ne
da sabuwar shari'a, an kuma umurce
shi da ya isar da ita zuwa ga mutane.
Shi kuwa annabi an aiko shi ne domin
ya tabbatar da shari'ar manzannin da
suka gabace shi.
∙Na yi imani da cewa fiyayyen
manzanni a wurin Allah shi ne Muhammadu
(sallallahu alaihi wa sallam),
shi xin xaya ne daga cikin 'ya'yan
Isma'il xan Ibrahim (alaihimas-salam),
Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki
xaya, da annabcinsa Allah ya cika
annabta, da manzancinsa ne kuma
Allah ya cika saqwanni.
-33-
٣٣
NI MUSULMI NE
∙Ya qarfafe shi da mu'ujuzozi, ya
kuma fifita shi akan dukkan manzanninsa
kamar yadda ya fifita saqonsa
akan dukkan saqwanni, ya kuma
xaukaka shari'arsa akan dukka
shari'o'i, littafinsa ma –Alqur'ani- ya
fifita shi akan dukkan litattafai, al'ummarsa
ma –musulmai- ya fifita su akan
saura al'ummatai.
∙Ubangijinsa ya ba shi abin da bai
baiwa wani annabi kafinsa ba, a cikin
abubuwan da ya ba shi akwai:
1) Alwasilat: ita ce babban matsayi
a cikin aljanna, Allah ya tanadi
wannan matsayi ne domin
Annabi (sallallahu alaihi wa
sallam)
2) Alkausar: wani kogi ne a cikin
٣٤
-34-
NI MUSULMI NE
aljanna, yana gudana ne ta
qarqashin al'arshi.
3) Alhaudhu: shi ne tafkin ruwan da
babu wanda zai sha shi a ranar
alqiya sai musulmi.
ranar da mutane zasu sha matsanancin
qishin ruwa, gumi ya mamaye
jikkunansu tun daga gwiwowinsu har
zuwa cikkunansu da kafaxunsu, kowa
gwargwadon abin da ya aikata,
musulmai zasu sha wannan ruwan ne
da kofunan da Annabi (sallallahu
alaihi wa sallam) zai ba su da hannayensa
masu girma da albarka, bayan
haka ba zasu qara jin qishirwa ba har
abada.
4) Ceto: wannan shi ne matsayin da
ake cewa da shi "maqamul-
35-
٣٥
NI MUSULMI NE
mahmud" a ranar alqiyama;
lallai manzon Allah (sallallahu
alaihi wa sallam) zai yi ceto a
wurin Allah, har ya fitar da
musulmai masu laifi daga wuta,
ta yadda babu wani da yake faxin
"La'ilaha illallahu Muhammad
ur-rasulullahi" da zai yi saura a
cikinta, mai savo ba zai dawwama
cikin wuta ba, za a fitar da shi
bayan an tsarkake shi daga
savonsa.
∙Duk wanda ya yi imani da dukkan
annabawa amma bai yi imani da
Annabi Muhammadu (sallallahu alaihi
wa sallam) ba, to kuwa lallai ba zai
tava fita daga wuta ba.
5) Kuma lallai Allah ya taimake shi,
ya kuma taimaki rundunarsa da
٣٦
-36-
NI MUSULMI NE
mabiyansa har zuwa ranar
alqiyama, ta hanyar saka tsoro da
razana a zukatan maqiyansu na
tsawon tafiyar wata, ba a kuma
bayar da haka ga wani annabi
kafinsa ba (sallallahu alaihi wa
sallam).
6) An sanya qasa a gare shi da
sauran musulmai ta zamo wajen
sujada, kuma mai tsarki, wannan
ma ba a bai wa annabawan da
suka gabace shi ba.
7) Allah ya aike shi zuwa ga mutane
da aljannu baki xaya, sa'ilin da
ya aiki kowane Annabi zuwa ga
jama'arsa kaxai.
8) Kuma lallai shi ne farkon wanda
qabarinsa zai tsage ya fito, farkon
-37-
٣٧
NI MUSULMI NE
mai ceto, kuma farkon wanda zai
qwanqwasa qofar aljanna, sai
Ridwan –mai tsaron
aljanna- ya ce: wane ne? sai ya ce:
Muhammadu ne, sai Ridwan ya ce: kai
kaxai aka umurce ni da na buve wa, ka
da kuma in buxe wa wani kafinka.
A cikin mu'ujuzozinsa (sallallahu
alaihi wa sallam) akwai:
Tsagewar wata.
Ya mayar wa Qatadatu idonsa da
aka cire masa a ranar Uhdu,
wannan idon kuma ya zamo ya fi
lafiya akan xayan.
Ya mayar da maqyangyamar
Ibnul-Hakam lokacin da aka
karya ta a ranar Badar.
٣٨
-38-
NI MUSULMI NE
Ya nemi bishiya da ta yi shaida,
kuma ta shaida da "shahadataini"
har sau uku a gaban wani
kafiri, ya kuma musulunta.
Kukan kututturen bishiya wanda
manzon Allah (sallallahu alaihi
wa sallam) yake huxuba a kansa
lokacin da ya bar shi, bai kuma yi
shiru ba sai da (sallallahu alaihi
wa sallam)ya xaura hannayensa a
kanshi.
Haka ma yawaitar abinci a
hannunsa (sallallahu alaihi wa
sallam) har mutane sama da
tamanin suka ci gwargwadon
tafuka biyu na abinci suka kuma
qoshi.
Haka ma yawaitan ruwa a ranar
-39-
٣٩
NI MUSULMI NE
Hudaibiyya, lokacin da ruwa ya
qare wa runduna ba su da sama
da kimanin kofi xaya, sai Annabi
(sallallahu alaihi wa sallam) ya
sanya hannunsa, nan take sai
ruwa ya ci gaba da vuvvugowa
daga yatsunsa masu albarka
(sallallahu alaihi wa sallam),
mutane suka sha suka kuma yi
alola, kuma adadinsu ya kai
kimanin mutum dubu xaya da
xari huxu.
Haka ma an yi tafiya da shi zuwa
"Masjidu- al-aqsa", sannan an yi
"Mi'iraji" da shi zuwa maxaukakan
sammai har zuwa magaryar
tuqewa.
A cikin mu'ujuzozinsa (sallallahu
alaihi wa sallam) akwai labarai
٤٠
-40-
NI MUSULMI NE
na al'ummatan da suka gabata da
na annabawansu,
tabbas shi "ummiyyi' ne, ba ya karatu
balle rubutu. Haka ma bayar da
labarin abin da zai faru nan gaba na
buxe Parisa da Rum, da kuma kekketa
mulkin Kisra da ya keta saqon manzon
Allah (sallallahu alaihi wa sallam), da
ma wasunsu na mu'ujuzozi masu
yawa.
Mafi girman mu'ujuzarsa shi ne
Alqur'ani mai girma, shi ne kuma
dawwamammen mu'ujiza har zuwa
ranar sakamako.
Sannan Allah ya xaukaka ambatonsa
(sallallahu alaihi wa sallam)
ta yadda mai girma da xaukaka
ya gwama sunansa da sunansa, ya
-41-
٤١
NI MUSULMI NE
kuma sa kalmar shahada
"La'ilaha illallahu Muhammad
ur-rasulullah" ta zamo farkon
abin da bawa zai shiga musulunci
da ita, kuma qarshen abin da ya
kamata bawa ya bar duniya da
ita, duk wanda maganarsa ta
qarshe ta zama "La'ilaha
illallahu" to kuwa ya shiga aljanna.
Game da Annabinmu (sallallahu
alaihi wa sallam) ya zama
wajibinmu ne ka da mu gabatar
da maganar kowa a cikin halittu
akan maganarsa, ko ra'ayin
kowane mai bi akan umurninsa,
idan wasu mutane sun riga ka yin
hijira zuwa gare shi (sallallahu
alaihi wa sallam), to kai ma ka yi
hijira zuwa ga sunnarsa a cikin
٤٢
-42-
NI MUSULMI NE
dukkan al'amurranka, ka da ka
bi kowa in ba shi ba.
Mu haxa kai gaba xaya akan
umurninsa, mu yi masa biyayya
.[ ﴿! " # $ % &' ﴾ [النساء: ٨٠
(sallallahu alaihi wa sallam), saboda
duk wanda ya yi wa manzo biyayya to
kuwa lallai ya bi Allah.
Ka da mu kira shi ba da manzon
Allah (sallallahu alaihi wa sallam)
ba, ka da mu ce da shi
"Muhammadu" kawai.
Mu ladabtu da ladubbansa, mu yi
koyi da shi a dukkan halayensa
(sallallahu alaihi wa sallam) a
wurin barcinsa ne ko warin cin
abincinsa da tafiyarsa da sallarsa
da azuminsa da sadakarsa da
-43-
٤٣
NI MUSULMI NE
jahadinsa (sallallahu alaihi wa
sallam).
Mu so shi fiye da yadda muke son
kanmu da 'ya'yanmu da iyayenmu
da ma mutane baki xaya.
∙Kuma dole ne mu so duk wanda yake
son manzon Allah (sallallahu alaihi wa
sallam), yake kuma koyi da shi. Mu
kuma qi mai qin manzon Allah
(sallallahu alaihi wa sallam), yake
kuma qin lizimtar shari'arsa.
∙Ya zama wajibi akan musulmi ya so
muminai, ya kuma taimake su, ya yi
kama da su, ya kuma damu da
al'amurransu, ya taimake su wajen
aikin alhairi, ya riqe su a matsayin
abokai.
∙Wajibi ne a gare shi ya qi kafirai da
٤٤
-44-
NI MUSULMI NE
kafircinsu, ka da ya yi masu biyayya,
ka da ya haxa kai da su wajen cin
mutuncin musulmai, ka da ya taimake
su akan varnarsu, ka da ya yi tarayya
da su a bukukuwansu, kuma haramun
ne ya zalunce su, dole ne ya yi masu
adalci.
∙Wajibi ne mu so iyayen muminai,
matan Annabi (sallallahu alaihi wa
sallam), mu kuma so sahabbansa
(sallallahu alaihi wa sallam); saboda su
ne fiyayyun mutane bayan annabawa.
∙Haka ma ya wajaba mu rayar da
sunnarsa (sallallahu alaihi wa sallam),
mu kuma bayyanar da shari'arsa, mu
kuma isar da kiransa zuwa ga mutane
baki xaya, sannan mu yi haquri akan
abin da zamu gamu da shi na cutarwa
game da hakan, hakan dole ne.
-45-
٤٥
NI MUSULMI NE
∙Saboda lallai sunnar Allah za ta ci
gaba da gudana akan halittunsa,
saboda babu wani annabi daga cikin
annabawa ko waliyyi da ya yi kira
zuwa gaskiya face an qi shi kuma an
cutar da shi.
∙ya kai musulmi, ka faxaka, ka da ka
yarda cutarwar da kafirai suke maka
ta kawar da kai ga barin addininka,
domin an cutar da manzon Allah
(sallallahu alaihi wa sallam) lokacin da
yake cikin sahabbansa marasa yawa,
an kuma cutar da sahabbansa sun yi
haquri.
∙Ka da wai danganta ka da rashin
hankali da rashin tunani da ci baya su
sa himmarka ta yi rauni, ko su ce: an
٤٦
-46-
NI MUSULMI NE
yi maka wankin qwaqwalwa. Kyakkyawar
koyi da manzon Allah ya wajaba
a gare ka, domin dai tabbas wasu sun
ce da shi: mawaqi wasu kuma sun ce:
mahaukaci.
∙Ka da ka damu idan an ce maka: mai
tsattsaurar ra'ayi ko vatacce. Wannan
shi ne halin kafirai tare da muminai:
.[ المطففين: ٣٢ ] ﴾Ü Û Ú Ù Ø ×﴿
(idan sun gansu sai su ce: lallai
waxannan tabbas vatattu ne) [32,
mutaffifina]
∙Shin bai ishe ka ba idan aka ce
mutane sun kasu kashi biyu kai ka
zamanto a cikin kashin da Annabi
(sallallahu alaihi wa sallam) yake?!
-47-
٤٧
NI MUSULMI NE
o n m l k j i h< ﴿∙
.[ الفرقان: ٢٧ ] ﴾ q p
Ka qyale su har zuwa ranar da
azzalumi zai ciji yatsarsa yana mai
cewa: kaico na, ina ma na bi hanya
tare da manzon Allah.
∙Ka da ka ruxe idan sun ce maka xan
ta'adda, ko asharari, wannan qarerayi
ne na azzalumai a kan muminai duniya
da lahira, domin lokacin da mika'ilu
suka kora su akan fuskokinsu zuwa
jahannama, suka yi ta duba cikin suka
ce:
.[ ﴿! " # $ % & ' ) ( *﴾ [ ص: ٦٢
mene ne ya sa ba mu ganin mutanen
da muka qirga su cikin ashararai?
٤٨
-48-
NI MUSULMI NE
∙A nan ne muminai zasu kira su
(waxanda suka kira su da ashararai)
daga babban matsayi a cikin Firdausi,
su ce:
.[ ﴿& ' ) ( * + ,﴾ [الأعراف: ٤٤
(Lallai kan mu mun sami abin da
ubangijinmu ya yi mana alqawari
gaskiya ne) [44, al-a'arafi]
-49-
٤٩
NI MUSULMI NE
(5) IMANI DA RANAR
LAHIRA
∙Na yi imani da ranar lahira, ita ce
ranar da duniya za ta qare (gidan
aiki), ranar lahira kuma ta fara (gidan
sakamako), masu biyayya a saka masu
da aljanna, masu savo kuma a saka
masu da wuta.
∙A ranar alqiyama ne ake sanya
mizani, a kuma baiwa kowane bawa
littafinsa, duk wanda ya amshi
littafinsa da hannun damansa to kuwa
lallai yana tare da Annabi (sallallahu
alaihi wa sallam) a aljanna, wanda
kuma duk ya amshi littafinsa da
hannun hagunsa to kuwa lallai yana
tare da Fir'auna (Allah ya la'ace shi) a
cikin wuta.
٥٠
-50-
NI MUSULMI NE
∙Ana kafa siraxi, duk wanda ya qetare
shi ya shiga aljanna, wanda kuma
tsininsa ya fizgo shi saboda mugun
aikinsa zai faxa wuta.
∙Ranar alqiyama tana da alamu
manya da qanana.
∙A cikin qananan alamun akwai:
tozarta amana da yawan kashe-kashe,
ka ga fasiqai sun xauki jan ragamar
al'umma da qarfi, sannan wawaye su
riqa magana akan al'amurran
al'umma masu muhimmanci.
∙A cikin manyan alamun akwai:
bayyanar Mahdi da tsayuwan Halifanci
na gaskiya akan tsari irin na
Annabi kafin tashin alqiyama da
fitowar Dujal.
∙Da saukowar Annabi Isah (alaihis-
51-
٥١
NI MUSULMI NE
salam) domin ya jagoranci musulmai
ya kuma yaqi kafirai,
ya kuma karya kuros, ya kashe alade,
ba zai yarda da komai ba sai
musulunci.
∙Babu wani gida -a birni ko a qauyeda
zai saura face Allah ya shigar da
wanan addinin ko dai girman mai
girma ko da qasqancin qasqantacce.
∙Da fitowar Yajuju da Majuju, haka
ma fitowar dabbar da za ta yi magana
da mutane, da hudowar rana daga
mafaxarta da xauke Alqur'ani da
makamantan haka.
∙Duk wanda ya aikata wani aiki na
alhairi ko sharri ko da gwargwadon
qwayar zarra ne zai gani a ranar
alqiyama a cikin littafinsa.
٥٢
-52-
NI MUSULMI NE
∙Ku yi gaggawa zuwa ga aikata
ayyukan xa'a tun lokacin rubuta su bai
qare da mutuwar bawa ba, a kuma
lokacin da babu wanda ya sani sai
Allah.
∙Iyalinsa su yi masa wanka, su kuma
yi masa likkafani, su yi masa sallah su
binne shi, mala'iku biyu su zo masa
"Munkar" da "Nakir" su zaunar da
shi su tambaye shi: wane ne ubangijinka?
Mene ne addininka? Wane ne
annabinka?
∙Idan ya amsa da cewa: Allah shi ne
ubangijina, kuma Musulunci shi ne
addinina, Muhammadu (sallallahu
alaihi wa sallam) shi ne annabina
kuma manzona – Allah ya katartar da
shi zuwa ga haka- za a buxe masa taga
cikin qabarinsa har ya zuwa aljanna,
-53-
٥٣
NI MUSULMI NE
ya hango mazauninsa a can, da
benensa da mulkinsa, ya kama farin
ciki, a kuma yalwata masa qabarinsa
iya ganinsa.
∙Idan kuma yana cikin kafirai ne, to
ba zai iya amsawa da komai ba, amsa a
wannan lokacin ba wai wayau da
kaifin qwaqwalwa ke kawo ta ba.
Sai dai Allah yana tabbatar da
ma'abota imani a wannan lokaci;
saboda abubuwan da suka gabatar na
kyawawan ayyuka da kaxaita Allah, da
bayar da farillai da jahadi da biyayya
da umurni da aikin alhairi da hana
munanan ayyuka da sadaka da
karatun Alqur'ani da azumi a lokacin
garji da tsayuwar darare masu tsawo
da sanyi.
٥٤
-54-
NI MUSULMI NE
∙Amma idan ya zamo kafiri ne shi, to
lallai qabarinsa zai quntata har kafaxunsa
su shige cikin jikinsa, qabarin na
sa ya zamo rami ne daga cikin ramukan
wuta saboda mum-munar aikinsa.
∙Ya xan uwa musulmi, ka yi qoqari,
yanzu lokaci ne na aiki ba hisabi, gobe
kuma ranar hisabi ne babu aiki.
∙A wannan rana ce musulmai masu
biyayya -su kaxai- zasu shiga aljanna,
saboda Allah ba zai karvi komai ba a
ranar alqiyama sai musulunci.
∙A cikin aljanna akwai ni'imar da
kunne bai tava ji ba, ido bai tava gani
ba, kuma ba ta tava xarsanuwa a cikin
zuciyar wani mutum ba. Kuma
ni'imarta za ta dawwama har abada ba
yankewa, mutanen cikinta ba zasu
-55-
٥٥
NI MUSULMI NE
mutu ba, mafi girmar ni'ima ita ce
duba zuwa ga zatin Ubangijin talikai.
∙Masu savo da fajirai da kafirai zasu
shiga wuta, a cikin wuta akwai azaba
mai tsanani, wadda Allah ya tanadar
wa kafirai, manyan duwatsu kafaffu
ma ba zasu iya jurewa ba, a can ne za a
yi ta azabtar da su babu qaqqautawa.
∙A can ne mabiya xagutai zasu yi
addu'ar a ruvanya azaba
ga shugabannin da suka vatar da su,
sai Allah ya bayar da umurnin a
ruvanya azaba a gare su baki xaya.
∙Ya xan uwana musulmi ka dawwama
akan gaskiya, ka da yawan waxanda
suka sava ya ruxe ka, saboda idan har
ka bi mafi yawan waxanda suke a
bayan qasa zasu vatar da kai ga barin
٥٦
-56-
NI MUSULMI NE
hanyar Allah, kai dai ka ci gaba ta
tafiya tare da masu zuwa wajen Allah.
∙Domin dai tabbas samun wasu
jama'a masu riqo da gaskiya a cikin
al'ummar Annabi Muhammadu
(sallallahu alaihi wa sallam) abu ne
wanda ba zai gushe ba, wanda ya sava
masu ko ya bayar da su ba zai rage su
da komai ba har zuwa tashin alqiyama.
∙Shin ina dubara ta riskar waxannan
darajoji da tsira, da kuma nesantar
waxancan azabu? Ina dubara ta cin
ma waxancan magabata makusanta da
kuma nesantar waxancan masu juya
baya kuma halakakku? Lallai babu
wata hanya sai tuba ta gaskiya da za ta
gyara abin da ya wuce, da kuma aiki
na gari da zai gyara abin da ya yi
saura na rayuwa, da kuma kyakk-
57-
٥٧
NI MUSULMI NE
yawar xammara wajen tsayawa daidai
akan hanya babu karkata.
∙Ka zamo kana tare da mutane da
jikinka, ka siya ka siyar ka yi aure, ka
raya duniya da abin da Allah ya
halatta maka.
∙Ka da ka xamfara komai na duniya
da zuciyarka, ka tafi da zuciyarka
zuwa in da ya kamata ta kasance, can
qarqashin al'arshin mai rahama, ka yi
sujada da zuciyarka, sujadar da babu
xagowa har zuwa ranar tashin
alqiyama.
٥٨
-58-
NI MUSULMI NE
(6) IMANI DA QADDARA
∙Shi ne mu yi imani da cewa lallai
Allah ya san duk abin da yake a cikin
wannan duniya, haka ma duk abin da
ya kasance da wanda zai kasance a
gaba har zuwa ranar alqiyama, kai
daidai da sanin halin qwayar zarra bai
kuvuce masa ba.
Kuma lallai tabbas ya san ayyukan
bayi da arzikinsu da lokutan ajalinsu,
kuma su wane ne 'yan aljanna a
cikinsu, su kuma wane ne 'yan wuta
tun kafin ya halicce su.
∙Kuma lallai Allah ya rubuta waxannan
qaddarorin a cikin "Lauhulmahfuz"
tun kafin ya halicci sammai
da qassai da shekaru dubu hamsin,
kuma wannan "Lauhul-mahfuz" xin
-59-
٥٩
NI MUSULMI NE
babu wanda ke leqa shi, shin shi
mala'ika ne makusanci ko kuwa
annabi mursali.
∙Kai har jinjiri a cikin mahaifiyarsa
Allah zai umurci mala'iku da su
rubuta shi a matsayin namiji ko
tamace, su kuma rubuta arzikinsa da
aikinsa da ajalinsa da makomarsa
(zuwa aljanna ko wuta), su kuma
rubuta abubuwan da zasu faru da shi
na alhairi ko na sharri.
∙Sannan a daren "Lailatul-qadri"
abubuwan da aka qaddara zasu faru a
shekara su sauka daga "Lauhulmahfuz",
na ajalin mutane ne da
arzikinsu da wanda zai yi aikin hajji a
cikin wannan shekarar da dai makamantan
haka, a dai qaddara duk abin da
zai faru a cikinta a wannan daren.
٦٠
-60-
NI MUSULMI NE
∙Sannan abubuwan da aka qaddara su
faru kullum a lokutansu a kuma kan
abubuwan da aka qaddara masu haka,
Allah ya xaukaka wasu mutane, ya
kuma qasqantar da wasu.
∙Mun yi imani da cewa duk abin da
Allah ya so shi ne zai faru, abin da ya
so ya faru, abin da bai
so ba ba zai faru ba, babu wanda ya isa
ya rinjayi Allah, kuma lallai shi ne ke
juya zukata, yana shiryatar da wanda
yake so da falalarsa da rahamarsa, ya
kuma vatar da wanda ya so da
adalcinsa da hikimarsa, shi xin ya san
wanda ya cancanci shiriya kamar
yadda ya san wanda ya cancanci vata.
∙Shi Allah ba a tambayarsa akan
abubuwan da yake aikatawa, mutane
-61-
٦١
NI MUSULMI NE
ne kawai ake tambayarsu.
∙Kuma lallai mun yi imanin cewa
Allah shi ne ya halicci dukkan komai,
babu daidai da qwayar zarra a
wannan duniya face Allah shi ne ya
halicce ta, ya kuma halicci motsinta da
shirunta.
∙Kuma lallai ya halicci bayi da ayyukansu,
shi kuma ya halicci iko da qudura
ga bayi domin su zavi ayyukansu
da kansu.
∙Kuma lallai Allah maxaukakin sarki
ya umurci halittunsa su yi masa biyayya,
ya kuma yi masu alqawarin aljannarsa,
ya kuma hana su aikata savo, ya
kuma yi wa masu savo gargaxi da
wutarsa, bai wajabta masu wani aiki
ba sai abin da zasu iya, daga nan sai
٦٢
-62-
NI MUSULMI NE
suka kasu kashi biyu: Muminai da
Kafirai, su suka so haka suka kuma
zava, duk hakan Allah ne ya halitta
masu ikon yin hakan a cikinsu.
∙Kuma lallai lada da azaba suna zuwa
ne gwargwadon yadda mutum yake
wajen bin shari'a, ba wai akan sanin
da ya yi masu tun asali ba, duk wani
wanda ya yi aiki ko da gwargwadon
qwayar zarra ne na alhairi zai sami
lada, haka ma wanda ya yi wani aiki
ko da gwargwadon qwayar zarra ne na
sharri za a yi masa uquba akan haka.
∙Kuma lallai abin lura shi ne qarshen
ayyuka, kuma kowane bawa an sawwaqe
masa abin da aka
halitta dominsa na jin daxi a aljanna
ko shan wahala a cikin wuta.
-63-
٦٣
NI MUSULMI NE
∙Saboda haka ne ya zama dole bawa
ya ji tsoron mummunar makoma, ya
dage wajen roqon Allah, yana mai
nuna talaucinsa zuwa gare shi kan ya
shiryatar da shi zuwa ga hanya madaidaiciya,
ya kuma dawwama wajen
neman taimakonsa a kan yin masa
xa'a, ya kuma ci gaba da neman tsarin
kar ya sava masa; saboda bawa ba shi
da wani iko akan duka waxannan
halaye in ba da qaddarawar Allah ba.
∙Kuma tabbas muminai sun yarda da
qaddarar Allah da ikonsa na alhairi da
sharri a cikin abubuwa masu xaci da
masu daxi, kuma suna da yaqinin cewa
babu wani da ya isa ya amfane su sai
idan Allah ne ya qaddara, kamar
yadda babu wanda zai cutar da su sai
da abin da Allah ya rubuta.
٦٤
-64-
NI MUSULMI NE
∙Babu yadda za a yi bawa ya sami
garxin imani sai idan ya san cewa: duk
abin da ya same shi dama ba zai tava
kuskure masa ba, abin da kuma ya
kuskure masa ba zai tava samunsa ba.
∙A qarshe: ina gode wa Allah, ina
kuma roqonsa kan ya shigar da ni
aljanna, ni da sauran musulmai, ya
kuma kare ni ga barin wuta, ni da
sauran musulmai, amin.
ALLAH KA YI SALATI GA ANNABI
MUHAMMADU DA ALAYENSA DA
SAHABBANSA KA KUMA YI TSIRA A GARE SU.
QARSHEN ADDU'ARMU SHI NE: (GODIYA TA
TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI).