Labarai

Da sunan Allah mai rahama mai jinkai. ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA.





3


﴿الٓمٓٓ ١ ذََٰٓٓلِكَ ٱٓٓلۡكِتََٰ بٓ لٓٓاَ رَٓيۡبََۛ فِٓيهِِۛ هدٗى لٓ لۡ متَّقِينَٓ ٢ ٱٓٓلَّذِينَٓ يٓٓ ؤۡمِ نونَٓ


بِٓٱلۡغَيۡبِٓ وَٓٓي قِي مونَ ٱٓٓلصَّلَوَٰةَٓ وَٓٓمِمَّا رَٓزَقۡنََٰ همۡ يٓ نفِ قونَٓ ٣ وَٓٓٓٱلَّذِينَٓ نٓٓزِلَٓ


ي ؤۡمِ نونَ بِٓمَآ أٓ


نزِلَ مِٓن قَٓبۡلِكَ وَٓبِٓ


إِلَيۡكَ وَٓمَآ أٓ ٱلۡأٓخِرَةِٓ همۡ يٓ وقِ نونَٓٓ ٤ وْٓٓلََٰٓئِٓ


أ كَ عَٓلىََٰ هدٗى مِنٓ


وْلََٰٓئِكَ ه مٓٓ


رَّ بِهِمۡ وَۡۖٓأ ٱلۡ مفۡلِ حونَٓٓٓ ٥ ﴾ ]ٓٓالبقرة:ٓ 1 - 5 ]


{ALIF, LAM, MIM


Wannan littafi ne da babu wani kokwnto a cikinsa, shiriya ne ga masu takawa. Su ne wadanda suke yin imani da gaibu, kuma suke tsayar da sallah, kuma suke ciyarwa daga abinda muka azurta su da shi. Da kuma wadanda suke yin imani da abinda aka saukar maka, da kuma abinda aka saukar a gabaninka, dan gane da lahira kuma masu sakankancewa ne. Wadannan suna kan shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo} [Bakara, aya ta: 1-5] ﴿ٱ للّٓ لٓٓآَ إِٓلََٰهَ إِٓلاَّ هوَ ٱٓٓلۡحَ يٓ ٱٓٓلۡقَ يو مٓ خ ذه ۡ


لاَ تَٓأ سۥِٓٓنَةٞ وَٓلاَ نَٓوۡمٞ لَّٓ هٓ مۥَٓٓا فٓيِٓ


ٱلسَّمََٰوََٰتِٓ وَٓٓمَا فٓيِ رٓٓۡ ضٓ


َ


ٱلأۡ مَٓٓن ذَٓا ٱٓٓلَّذِيٓ يَٓٓشۡفَ ع عِٓندَه إٓۥِٓٓٓلاَّ بِٓإِذۡنِهِٓ يۦَٓٓٓعۡلَ م مَٓٓا بَٓيۡنَٓ


يۡدِيهِمۡ وَٓمَا خَٓلۡفَ همۡ وَۡۖٓلاَ يٓ


َ


أ حيِ طونَٓ بٓٓشَِيۡءٖ مِنۡ عِٓلۡمِهِٓ إٓۦِٓٓٓلاَّ بِٓمَا شَٓآءَ وَٓسِعَ كرۡسِ ي هٓ


ٱلسَّمََٰوََٰتِٓ وَٓٓٓ رۡضَٓۡۖ


َ


ٱلأۡ وَٓٓلاَ يَٓ  و ده حۥِٓٓفۡ ظ همَا وَٓ هوَ ٱٓٓلۡعَلِ يٓ ٱٓٓلۡعَظِي مٓ ٢٥٥ ﴾ ]ٓٓالبقرةٓ:ٓ 255 ]


4


{Allah shi ne wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, rayayye ne kuma wanda ya tsayu da kansa ne, gyangyadi ba ya kama shi balle barci, shi ke da duk abinda yake a sammai da kassai, babu wanda zai yi ceto a wurinsa sai da izininsa, ya san abinda yake gabansu da kuma bayansu, (su) bayi ba sa sanin wani abu na iliminsa sai abinda ya ga dama su sani, Kursiyunsa ya yalwaci sammai da kassai, kuma ba ya yi masa nauyi kiyaye su, shi madaukaki ne maigirma.} [Ayatul Kursiy, Bakara aya ta:255.] ﴿ءَامَنَ ٱٓٓلرَّ سو لٓ نٓٓزِلَٓٓ


بِمَآ أٓ إِلَيۡهِ مِٓن رَّٓ بِهِٓ وۦَٓٓٓٱلۡ مؤۡمِ نو نٓ كلٌّ ءَٓامَنَ بِٓٓٱلَّلِّٓٓ


وَمَلََٰٓئِكَتِهِٓ وۦَٓٓ ك تبِهِٓ وۦَٓٓ ر سلِهِٓ حۦَٓٓدٖ مِن ر سلِهِٓ


َ


لاَ نفَ رِ ق بَٓيۡنَ أٓ وۦَٓٓٓقَال واْ سَٓمِعۡنَآ


طَعۡنَا غفۡرَانَكَ رَٓبَّنَا وَٓإِلَيۡكَٓٓ


َ


وَأ ٱلٓۡمَصِي رٓ 􀎋 لٓٓاَ يٓ كَل ف ٱٓٓ للّٓ نَٓٓٓفۡسًا إِٓلاَّ وسۡعَهَا لَٓهَا مَٓآ


كَسَبَتۡ وَٓعَلَيۡهَا مَٓا ٱٓٓكۡتَسَبَتٓۡ نَٓٓا رَٓبَّنَا وَٓلآَ


ۡ


خۡطَأ


َ


وۡ أٓ


َ


رَبَّنَا لٓاَ تٓ ؤَاخِذۡنَآ إِٓن نٓسَِّينَآ أٓ


تَحمِۡلۡ عَٓلَيۡنَآ إِٓصۡرٗا كَٓمَا حَٓمَلۡتَ هٓ عۥَٓٓلىَ ٱٓٓلَّذِينَٓ مِٓٓن قَٓبۡلِنَا رَٓبَّنَٓا وَٓٓلاَ تح مِلۡنَا مَٓا لٓٓآَ


طَاقَةَ لَٓنَا بِٓهِ وۡۖۦَٓٓٓٓٱعۡ فٓ عَٓٓنَّا وَٓٓٱغۡفِرۡٓ لَٓٓنَا وَٓٓٱرۡحَمۡنَآٓ نٓٓتَ مَٓوۡلَىَٰنَا فَٓٓ


َ


أ ٱن صرۡنَآ عَٓٓلىَ ٱٓٓلۡقَوۡمِٓٓٓ


ٱلۡكََٰفِرِينَٓ ٢٨٥ ﴾ ]ٓٓالبقرة:ٓ 285 - 286 ]ٓ


{Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a


5


tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take "


Allah ba ya dorawa rai sai abinda za ta iya, tana da (ladan) abin da ta aikata, kuma tana da (ukubar laifin) da ta aikata. Ya Ubangijinmu kada ka kamamu idan muka manta ko kuskure. Ya Ubangijinmu kada ka dora mana nauyi kamar yadda ka dora shi ga wadanda suka zo kafin mu. Ya Ubangijinmu kuma kada ka dora mana abinda ba za mu iya ba, ka yi mana afuwa ka gafarta mana, kai ne majibintin al'amuran mu, ka taimaka mana akan mutanan da suke kafirai.} [Bakara, aya ta: 285- 286] ﴿حمٓٓ ١ تَٓٓنزِي ل ٱٓٓلۡكِتََٰبِٓ مِٓٓنَ ٱٓٓلَّلِّٓ ٱٓٓلۡعَزِٓيزِٓ ٱٓٓلۡعَلِيمِٓ ٢ غَٓٓافِرِ ٱٓٓلذَّنۢبِٓ وَٓٓقَابِلِٓ


ٱلتَّوۡبِٓ شَٓٓدِيدِ ٱٓٓلۡعِقَابِٓ ذِٓٓي ٱٓٓلطَّوۡلِٓ لآَ إِٓلََٰهَ إِٓلاَّ هوَ إِۡۖٓلَيۡهِ ٱٓٓلۡمَصِي رٓ ٣ ﴾ ]ٓٓغافر:ٓ 1 - 3 ]ٓ


{HA MIM


Saukar da littafi daga Allah mabuwayi, Masani. Mai gafarta zunubi kuma mai karbar tuba, mai tsananin ukuba ma'abocin ni'ima, babu abin bautawa da cancanta sai shi, gare shi makoma take} [Ghafir, aya ta: 1-3]


6


﴿ هوَ ٱٓٓ للّٓ ٱٓٓلَّذِي لٓٓآَ إِٓلََٰهَ إِٓلاَّ هوَ عََٰۡۖٓلِ م ٱٓٓلۡغَيۡبِٓ وَٓٓٓٱلشَّهََٰدَةِٓ هوَ ٱٓٓلرَّحۡمََٰ نٓٓ


ٱلرَّحِي مٓ ٢٢ هوَ ٱٓٓ للّٓ ٱٓٓلَّذِي لٓٓآَ إِٓلََٰهَ إِٓٓلاَّ هوَ ٱٓٓلۡمَلِ كٓ ٱٓٓلۡ ق دو سٓ ٱٓٓلسَّلََٰ مٓ ٱٓٓلۡ مؤۡمِ نٓٓ


ٱلۡ مهَيۡمِ نٓ ٱٓٓلۡعَزِي زٓ ٱٓٓلۡجَبَّا رٓ ٱٓٓلۡ متَكَب رٓ سبۡحََٰنَ ٱٓٓلَّلِّٓ عَٓمَّا يٓ شۡرِ كونَٓ ٢٣ هوَ ٱٓٓ للّٓ ٱٓٓلۡخََٰلِ قٓٓ


ٱلۡبَارِ ئٓ ٱٓٓلۡ مصَ وِ رٓ لَۡٓٓۖ ه سٓٓۡمَآ ءٓ


َ


ٱلأۡ ٱٓٓلۡح سۡنَ يٓ يٓٓ سَ بِ ح لَٓ هٓ مۥَٓٓا فٓيِ ٱٓٓلسَّمََٰوََٰتِٓ وَٓٓٓ رۡضِ َ


ٱلأۡ وَٓٓ هوَٓ


ٱلۡعَزِي زٓ ٱٓٓلۡحَكِي مٓ ٢٤ ﴾ ]ٓٓالحشر:ٓٓ 22 - 24 ]ٓ


{Shi ne Allah ,wanda babu wani abin bautawa face Shi, Masanin boye da sarari, shi ne mai yawan rahama mai yawan jinkai.


Shi ne Allah wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, shi ne Sarki, Mai tsarki mai aminci, mai amintarwa, mai kula da komai, mabuwayi, mai karfin iko akan komai, mai ji-da-isa, tsarki ya tabbata ga Allah daga barin abinda suke ra shi da shi. Shi ne Allah mahalicci, mai kagar halitta mai surantawa, yana da sunaye mafiya kyau, duk abinda yake sammai da kasa suna masa tasbihi, shi ne mabuwayi mai hikima} [Suratul Hashr, aya ta: 22-24] ﴿ق لۡ هوَ ٱٓٓ للّٓ حَٓٓ دٓ


َ


أ ١ ﴾ٓٓ ]ٓٓالإخلاص: 1 ]


{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."} ﴿ عو ذ بِٓرَ بِٓٓ


َ


ق لۡ أٓ ٱلۡفَلَقِٓ ١ ﴾ٓٓ ]ٓٓالفلق:ٓٓ 1 ]ٓ


7


{Ka ce "ina neman tsari daga Ubangijin safiya."} ﴿ عو ذ بِٓرَ بِٓٓ


َ


ق لۡ أٓ ٱلنَّاسِٓ ١ ﴾ٓ ]ٓٓالناسٓ:ٓ 1 ]ٓ


{Ka ce "ina neman tsari daga Ubangijin mutane."}


cikakkakkiyar surar ake karantawa, kafa uku (3).


» أعوذ بٓكلمات آٓللّ آلتامات مٓن شٓر مٓا خٓلق «


"Ina neman tsari daga kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta. "


Sau uku (3).


بسِْمِٓ آٓللِّٓ آٓلَّذِي لٓٓآَ يَٓٓ ض رٓ مَٓٓعَٓ آٓسْمِهِٓ شَٓٓيْ ءٓ فٓٓيِ رْٓٓضِٓ «


ْ


الأ وَٓٓلآَ فٓٓيِ آٓلسَّمَاءِٓ وَٓٓ هوَٓٓٓ


» السَّمِي عٓ آٓلْعَلِي مٓ


"Da sunan Allah, wanda babu wani abu mai cutarwa da sunansa a sama ko a kasa . Kuma shi ne Mai ji Masani"


Sau uku (3).


» رضيت بٓاللّ رٓبًّا وٓبالإسلام دٓينًا وٓبمحمد صٓلي آللّ عٓليه وٓسلم نٓبيًّا «


"Na yarda da Allah Ubangiji, da Musulunci addini, kuma Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi annabi."


8


Sau uku (3).


أصبحنا وٓأصبح آلملك لٓلّ وٓالحمد لٓلّ لٓا إٓله إٓلا آللّ وٓحدة لٓا شٓريكٓ «


له. لٓٓه آلملك وٓله آلحمد وٓهو عٓلى كٓل شٓيء قٓدير. رٓٓب أٓسألك خٓير مٓا فٓي هٓذآ


اليوم وٓخير مٓا بٓعده. وٓٓأعوذ بٓك مٓن شٓر مٓا فٓي هٓذا آليوم وٓمن شٓر مٓا بٓعده.ٓ


ر بِ أٓعوذ بٓك مٓن آلكسل وٓالهرم وٓسوء آلكِبَر. وٓٓأعوذ بٓك مٓن عٓذاب آلنارٓ


» وعذاب آلقبر


"Mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari na Allah ne , godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya tasa ce, kuma shi mai iko ne akan komai. Ya Ubangiji ina rokonka alherin wannan yini da alherin dake bayansa, ina kuma neman tsarinka daga sharrin wannan yini da sharrin dake bayan sa. Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga kasala da tsufa, da mummunan girma, ina neman tsarinka daga azabar wuta da kuma azabar kabari."


Da yamma kuma sai ya ce: Mun kai yammaci, kuma mulki ya kai yammaci na Allah ne. sai kuma ya ce:


» أمسينا وٓأمسي آلملك لٓلّ «


9


"Ya Ubangiji ina rokonka alherin wannan daren.... zuwa karshe, maimakon: Mun wayi gari ya wayi gari. Da kuma (wannan yini)."


» اللهم بٓك أٓصبحنا وٓبك أٓمسينا وٓبك نٓحيا وٓبك نٓموت وٓاليك آلنشورٓ «


"Ya Allah gareka muka wayi gari, kuma gareka muka yi yammaci, kuma gareka muke rayuwa kuma gareka muke mutuwa, kuma gareka Makoma take."


» اللهم بٓك أٓمسينا وٓبك أٓصبحنا وٓبك نٓموت وٓبك نٓحيا وٓإليك آلمصير «


"Da yamma kuma sai ya ce: Ya Ubangiji gareka muke yammaci , kuma gareka muka wayi gari, kuma gareka muke mutuwa, kuma gareka muke komawa."


اللهم مٓا أٓصبح بٓي مٓن نٓعمة أٓو بٓأحد مٓن خٓلقك فٓمنك وٓحدك لٓآ «


» شريك لٓك فٓلك آلحمد وٓلك آلشكر


"Ya Ubangiji duk abinda ya wayi gari a gareni na ni'ima ko ga wani cikin halittarka to daga gareka ne, kai kadai, baka da abokin tarayya, yabo naka ne kuma godiya taka ce."


Da yamma kuma sai ya ce:


» ما أٓٓمسي بٓٓي «


10


"Abinda ya yi yammaci a gare ni."


اللهم إٓني أٓصبحت فٓي نٓعمة وٓعافية وٓستر. فٓٓأتم نٓعمتك عٓل ى وٓعافيتكٓٓ «


» وسترك فٓي آلدنيا وٓالآخرةٓ


"Ya Ubangiji na wayi gari cikin ni'ima da lafiya da rufin asiri, ka cika ni'imarka a gareni da lafiyarka da rufin asirinka duniya da lahira."


Sau uku (3).


Da yamma kuma sai ya ce:


اللهم إٓٓني أٓٓمسيت « … »


"Ya Ubangiji ni na kai maraice: zuwa karshe."


اللهم إٓني أٓعوذ بٓك مٓن آلهم وٓالحزنٓ. وٓٓأعوذ بٓك مٓن آلعجز وٓالكسل.ٓٓ «


» وأعوذ بٓك مٓن آلجبن وٓالبخل. وٓٓأعوذ بٓك مٓن غٓلبة آلديْنِ وٓمن قٓهْر آلرجال


"Ya Ubangiji ni ina neman tsarinka daga damuwa da bakin ciki, ina neman tsarinka daga gajiyawa da kuma kasala, ina kuma neman tsarinka daga tsoro da rowa, ina kuma neman tsarinka daga rinjayar bashi da kada mutane su fi karfi na."


11


اللهم إٓني أٓسألك آلعافية فٓي آلدنيا وٓالآخرةٓ. آٓللهم إٓني أٓسألك آلعفوٓ «


والعافية فٓي دٓيني وٓدنياي وٓأهلي وٓمالي. آٓللهم آستر عٓوراتي وٓآمن رٓوعاتي. آٓللهمٓ


احفظني مِٓن بٓين يٓديَّ وٓمِن خٓلفي وٓعن يٓميني وٓعن شٓمالي وٓمن فٓوقي. وٓٓأعوذٓ


بعظمت غتال مٓن تٓحتي


» ك أٓن أٓ


"Ya Ubangiji ni ina rokonka yafiya anan duniya da kuma lahira, Ya Ubangiji ni ina rokonka afuwa da yafiya a addinina da duniyata da iyalina da kuma dukiyata, Ya Ubangiji ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona. Ya Ubangiji ka tsare ni ta gabana da ta bayana, ta damata da ta haguna da kuma ta samana, ina kuma neman tsari da buwayarka kada a halakani ta kasa ta."


اللهم أٓنت رٓبي لٓا إٓله إٓلا أٓنت. خٓٓلقتني وٓأنا عٓبدك. وٓٓأنا عٓلى عٓهدكٓ «


ووعدك مٓا آستطعت. أٓٓعوذ بٓك مٓن شٓر مٓا صٓنعت. أٓٓبوء لٓك بٓنعمتك عٓلى.ٓٓ


» وأبوء بٓذنبي. فٓٓاغفر لٓي. فٓٓإنه لٓا يٓغفر آلذنوب إٓلا أٓنت


"Ya Allah ! kai ne Ubangiji na, babu abin bautawa da cancanta sai kai, kai ka halicceni ni bawanka ne, ni kuma ina kan al'kawarinka gwargwadon iko, ina neman tsarinka daga sharrin abinda na aikata, ina tabbatar da ni'imarka a gare ni, ina tabbatarda zunubi


12


na, ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai kai."


اللهم فٓاطر آلسماوات وٓالأرض. عٓٓالم آلغيب وٓالشهادة. رٓٓبَّ كٓل شٓيءٓ «


ومَلِيكه. أٓٓشهد أٓن لٓا إٓله إٓلا أٓنت. أٓٓعوذ بٓك مٓن شٓر نٓفسي وٓمن شٓرٓ


» الشيطان وٓشركه وٓأن أٓقترف عٓلى نٓفسي سٓوءاً أٓو أٓ جرَّه إٓلي مٓسلم


"Ya Ubangiji ! mahaliccin sammai da kasa, masanin boye da sarari, Ubangijin komai kuma mamallakinsa, ina shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai kai, ina neman tsarinka daga sharrin kaina da kuma sharrin shaidan da abin shirkarsa, da kuma kada in aikatawa kaina mummunan abu ko in kai shi ga wani Musulmi."


شه دك وٓأشهد حٓملة عٓرشك وٓملائكتك وٓأنبياءكٓٓ «


اللهم إٓني أٓصبحت أٓ


» وجميع خٓلقك بٓأنك أٓنت آللّ لٓا إٓله إٓلا أٓنت وٓأن مٓحمدًا عٓبدك وٓرسولك


"Ya Ubangiji ni na wayi gari ina shaida maka ina kuma shaidawa (Mala'iku) masu dauke da al'arshinka da Mala'ikunka da Annabawanka da dukkanin halittunka da cewar kai ne : Allah wanda babu abin bautawa da cancanta sai kai, kuma lalle (Annabi) Muhammad bawanka ne kuma Manzonka ne."


Da yamma kuma:


13


اللهم إٓٓني أٓمسيت « … »


"Ya Ubangiji ! ni na kai maraice: zuwa karshe," (sau hudu) (4).


لا إٓٓله إٓٓلآ آٓللّ وٓٓحده لٓٓآ شٓٓريك لٓٓه. لٓٓهٓ آٓلملك وٓٓله آٓلحمد. وٓٓهو عٓٓلى كٓٓلٓٓ «


» شيء قٓٓدير


"Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma shi maiiko ne akan komai."


Sau dari (100), da safe da kuma yamma.


» حسبي آٓللّ لٓٓا إٓٓله إٓٓلا هٓٓو عٓليه تٓٓوكلت وٓٓهو رٓٓب آٓلعرشٓآٓلعظيم «


"Allah ya isar mini, babu abin bautawa da cancanta sai shi, a gare shi na dogara, kuma shi ne Ubamgijin Al arshi mai girma."


Sau bakwai (7).


» حسبي آللّوٓكفيٓ. سٓٓمع آللّ لٓمن دٓعاء لٓٓيسوٓراء آللّ مٓرمىٓ «


"Allah ya isar min, kuma ya wadatar, Allah ya ji duk wanda ya roke shi, babu mafaka in ba wurin Allah ba."


14


» سبحان آللّ وٓبحمده «


"Tsarki ya tabbata ga Allah hadi da gode masa."


Sau dari (100), da safe ko da yamma, ko kuma dukkan su.


» أستغفر آللّوٓأتوب إٓليه «


"Ina neman gafarar Allah ina tuba zuwa gare shi."


Sau dari (100).


Wannan shi ne gwargwadon abin da ya sawwaka da aka rubuta, ina rokon Allah madaukakin sarki ya anfanar da shi.


Wanda ya rubuta shi ne: Muhammad dan Salih Al usaimin, 20/1/1418 (Bayan Hijira).



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA