Abubuwa Bakwai Masu
Halakarwa(Yiwa Mace Mumina
Kazafi)
Yiwa Mace Mumina Kazafi: A yanzu za mu yi
bayani akan abu na bakwai kuma na karshe cikin
abubuwa bakwai da Ma'aikin Allah – tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan
da suke halakar da wanda yake ta'amuli dasu ,
wannan abu shine Yiwa Mace Mumina Kazafi.
Kazafi Shine: Jifan mutum da aikata alfasha ta
zina, ko kore juna biyu ko ma Da ba tare da ya
bayar cikakkun shaiduba.
Alokacin da mutum ya jefa kanshi cikin irin
wadannan halayya ta kazafi to lalle ya jefa kansa
cikin halayyar da take halakarwa, domin yin kazafi
ba karamin bala'ibane, alokacin da mutum ai wance
mazinaciyace ko ya yi lalata da ita, ko wannan
ciknnanata bana mijintabane ko danta/'yarta ai bana
mijinta bane to lalle ya tsokano tsuliyar dodo dole ya
kawo cikakkun shaidu na mutane hudu maza
musulmai da zasu bada shaida akan hakan, idan
kuma mai kawo shaiduba ko ya kawo basu cikaba to
kowanne mutum gada cikinsu bulala tamanin (80)
za'a yi masa, kamar yadda bayanai zasu zo nan
gaba kadan.
Wannan shiri da musulunci yake dashi
bakaramin shiri bane domin kare mutunci, masu iya
Magana na cewa mutunci madarane in ya zube bai
kwasuwa, addinin musulunci yana daga cikin
4
manyan manufofinsa kare mutunci, wannan yasa
musulunci ya dauki irin wannan mataki
musammamma 'ya mace, domin alokacin da aka
bata mata suna to gaba daya anbata mata
rayuwarta, shi yasa ayoyin da suka yi Magana akan
kazafi sun anbaci macece basu anbaci namijiba
wannanko ba wai dan hukuncin ya sha daban bane
a'a hukuncin iri dayane ga duk wanda ya yi mace ko
namiji kazafi, kuma bai iya kawo cikakkakun
shaiduba, idan ko ya kawo shaidu da duk abinda
Shara'a ke bukata suka cika to baza'a kira wannan
da sunan kazafiba.
Yiwa mace mumina kazafi bai halattaba kuma
yana cikin abubuwan da suke halakarwa, saboda
haka dadin fira ko kiyayya kada ta dauki mutum ya
yiwa wata/wani kazafi ko yasa a yi.
Ayoyin Da Suka Yi Magana Akan Kazafi: Idan
ka tsaya ka kalli ayoyin zaka gansu kashi ukune
kuma duk suna cikin Suratun Nur.
Kashi Na Farko: Ayata: 4-5, Allah Madaukakin
sarki yana cewa: ''Wadanda suke jifan mata
masu kamunkai (da zina) sannan kuma basu
kawo shaidu huduba to ku yi musu bulala
tamanin (80), kuma kada ku sake karbar
shaidarsu har abada, kuma waddan sune
fasiakai. Saidai kawai wadanda suka tuba
bayan haka kuma suka kyautata to lalle Allah
mai yawan gafarane kuma mai yawan jinkai.''
Anan Allah madaukakin sarki ya bayyana
hukuncin duk mutumin da ya yiwa mace/namiji
kazafi kuma bai iya kawo shaidu huduba sai Allah ya
5
bayyana hukuncin da za'a yi masa. Abu na farko bulala tamanin (80), abu na biyu ba za'a sake karbar shaidarsaba har'abada, abu na uku kuma wannan mutumin fasikine. Sai idan ya tuba, to ananne malamai suke maganar shin inya tuba za'a ci gaba da karbar shaidarsa kuma shikenan shi ba fasiki bane? Amma ko ya tuba sai an yi mishi bulala tamanin. Kashi Na Biyu: Ayoyin da suka yi bayanin maigidan da ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya kawo shaiduba to shi tsinuwa za su yi da matar ta shi, Allah Yana cewa: ''Wadanda kuma suke jifan matansu (da zina) kuma ya kasance basu da shaidu saidai karankansu, to shaidar dayansu (itace) Rantsuwa hudu da Allah lalle shi yana cikin masu gaskiya * (Rantsuwa) ta biyar tsinuwar Allah ta haukanshi in ya kasance cikin makaryata. * Kuma abinda zai hana ayi mata azaba (haddi) shine ta yi Rantsuwa hudu da Allah cewar lalle shi (mijin) yana cikin makaryata *. (Rantsuwa) ta biyar lalle fushin Allah ya tabbata akanta in (mijin nata) ya kasance cikin masu gaskiya'' Surartun Nur, ayata: 6-8.
Anan Allah madaukakin sarki ya yi bayanin idan miji ya yiwa matarshi kazafi kuma bai iya kawo shaidu huduba to 'Li'ani'' za su yi. Amma duk wanda ba miji bane to kodai ya kawo sahaidu mutane hudu maza musulmai ko kuma ayi mishi bulala tamanin, ba maganar shi wanda aka yiwa kazafi wai ya rantse idan ba haka bane, ko kuma shi da ya yi kazafin
6
cewa ya rantse duk babu kodai shaidu ko bulala tamanin. Kashi Na Uku: Ayoyin da suka yi Magana akan kazafin da aka yiwa mata muminai masu kamunkai natsattsu kammalallu to wadannan masu yiwa irin wadannan matan kazafi tsine musu aka yi duniya da lahira. Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Lalle dukkanini wadanda ke jifan mata masu kamun kai gafalallu (daga aikata dukkanin alfasha) wadanda suke muminai to an tsine musu a duniya da kuma lahira, kuma suna da azaba maigirma* Aranar da harsunannu za su bada shaida akansu da hannayansu da kuma kafafuwansu ta sanadiyyar abinda suka kasance suna aikatawa* Awannan ranarce Allah zai cika musu sakamakonsu na gaskiya, kuma zasu sani lalle Allah shi wanda yake mai gaskiya kuma mai bayyanar da abubuwa''. Suratun Nur, ayata: 23-25.
Wannan ya nuna mana shi karankanshi kazafin ya kasu kashi-kashi, kashi na farko shine yiwa gama garin mutane wadanda suke suna da kyawawan halaye da kuma wanda ba'a rasaba, su aka anbaci hukunci yi musu kazafi a kashin farko, sai kuma wanda ya kasance tsakanin miji da mata. Sai wannan kashi na uku, wanda mutum zai ga mace/namiji mai kamun kai mai addini natsattse mumini kawai ya antayo ashar ya watsa mata/mashi ya dinga fadan wasu maganganu wanda da za'a tara mishi arzikin duniya domin ya kawo shaida akan haka ba zai iyaba. Domin wani ya dauka irin halin da
7
yake dashi to kowa haka yake, to kaga bayan ya
kasa kawo wadannan shaidu za'a yi masa hukuncin
kazafi anan duniya sanna kuma ya jira ranar
alkiyama, domin Allah baya bari a taba bayinsa na
kwarai, Ya Allah ka samu daga cikinsu, ka karemu
da sharrin masharranta ka tsaremu ka tsaremana
imanimmu, amin.
Kammalawa: Daga takaitattun bayananan ya
bayyana agaremu yadda musulunci ya dauki mutunci
da daraja da kima ya karewa kowa mutuncinsa
musamman 'ya mace, domin idan ba hakaba sai
kowa ya fadi abinda ya ga dama ko asashi ya fada
yana ganin bai huce aci tararshiba, amma idan
yasan zai sha bulalane to dole ya naba'a yasan me
zai fada, sai yazama yak are mutuncinsa dana
zuriyarsa kamar yadda yak are mutuncin wani dana
ziriyarsa.
Annanne kuma muka zo karshen wannan silsila
wacce take dauke da sharhin wannan hadisi da Abu
Hurairata ya ruwaito daga wurin Ma'aikin Allah na
wadannan abubuwa bakwai masu halakarwa, lalle
ma'aikin Allah ya isar da manzanci kuma tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi, hakika ta'amuli
da wadannan abubuwa tabbas yana halakarwa kuma
wannan kowa ya gani ya tabbatar wannan zai kara
imanine bisa imani. Akaro na gaba zamu kawo
bayanne kuma wadanda zasu haskaka mana
rayuwarmu da addininmu, Allah ya kaimu wannan
lokacin ya hadamu da imani, aimn.