Abubuwa Bakwai Masu
Halakarwa(Juya Baya A Lokacin
Yaki)
Ja-Da-Baya Lokacin Gumurzu: A yanzu za mu
yi bayani akan abu na shida cikin abubuwa bakwai
da Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi- ya lissafa cikin abubuwan da suke halakar
da wanda yake ta'amuli dasu , wannan abu shine
Juya Baya A Lokacin Yaki.
Jihadi wani al'amarine da musulunci ya
shar'antashi ya kuma tsarashi kamar yadda ya tsara
rayuwar bil'adama ta duniya da kuma ta lahira.
Ayoyi na Alkur'ani mai girma da ingantattun Hadisai
Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi- duk sun zayyana yadda jihadi yake hanan
kuma malamai sun zayyana yadda yaki yake domin
habbaka addinin Allah, kuma kamar sauran al'amura
sai mutum ya yi kamar yadda aka shar'anta sannan
zai sami ladanshi. Yaki domin habbaka addinin Allah
shine kololuwar musulunci, kamar yadda Ma'aikin
Allah – tsira da amincin Allah su tabbata a gareshiya
bayyana a Hadisin Mu'az.
Kuma kamar yadda Allah madaukakin Sarki ya
bayyana a cikin Alkur'ani mai girma cewa: ''An
wajabta muku yaki alhalin bakwasansa''
Bakara, ayata: 216.
4
A wannan dogon hadisi da muke bayani a
kanshi, Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi- ya lissafa juyawa da nufin
guduwa yana daga cikin abubuwa masu halakarwa
domin kamar wannan juyawar da mayaki ya yi yana
nufin a murkushe musulunci kenan.
Amma juyawar da zata laifi sai idan yawan
musulmai daidaine dana kafirai, ko kuma su
wadanda ba musulmanba sun ninka musulmai ribinyi
biyu, amma idan yawan wadanda ba musulmai ya
ninka yawan musulmai sama da sau biyu to
awannan lokaci babu laifi idan musulmi ya juya da
baya kamar yadda aya Suratul Anfal ta yi nuni:
''Ayanzu Allah Ya sawwaka muku, kuma ya
bayyanar da cewa a cikinku akwai masu rauni,
idan an sami mutane dari daga cikinku masu
hakuri zasu rinjayi mutane dari biyu (daga
cikinsu), in kuma an sami mutane dubu daga
cikinku zasu rinjayi dubu biyu (daga cikinsu)
da izinin Allah, Allah Yana tare da masu hakuri.
Ayata: 66.
Ma'aikin Allah – tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi- yana cewa ''Kada ku yi fatan
haduwa da abokan gaba, ku roki Allah zaman lafiya,
idan kuma har kuka hadu da su to ku tabbata, ku
sani aljannah tana karkashin inuwar takobi''.
Ya Allah muna rokonka ka zaunar da mu lafiya,
kuma ka dawowa da musulunci izzarsa da kimarsa
da darajassa.
Kammalawa: wannan ya nuna yadda musulunci
bai yarda da juyawa da bayaba a lokacin da aka yi
5
futo-na-fito, kuma mu sani annan ba wai ana
bayanine akan abinda ya shafi hukunce-hukuncen
yaki bane (Jihadi) wannan wurinsa daban malamai
sun fayyace shi da yadda ya karkasu da matsayin ko
wanne kaso daga cikinsu, amma anan an yi
bayanine akan abinda ya shafi tserewane afagen
fama. Ya Allah ka tsaremu ka tsare mana
rayukammu da imanimmu. Amin
Rbutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu