Labarai




da sunan Allah mai rahama mai jin kai


Dukkan godiya sun tabbata ga Allah, tsira da amincin Allah su tabbata ga manzan Allah, da kuma dukkan wanda suka jibince shi, da iyalan sa da sahabban sa da kuma tabi’ai, da kuma duk wanda yabi tafarkin shiriyar su, bayan haka:


Wadannan wasu jerin rubuce-rubuce ne marasa yawa wadanda zasu haskaka wa musulmai hanya kuma su baiyana musu akidun batattun kungiyoyi dan su guje musu, musamman ma wasu daga cikin su muryoyin su sunyi sama a wadannan kwanakin kuma suna ta yunkuri wajan yada barnar su, hakika mun fara wannan jerin rubuce-rubucen akan kungiyar (shi’a masu limami goma sha biyu), saboda mabiyanta sunfi yawa a yanzu, suna nan a kasar Iran da Iraqi da bangaraen kasashen larabawa...


Kuma mabiyan wannan kungiyar suna yawan cewa mazhabin su baida banbanci da mazhabin ahlussunah, kuma suna cewa ana zaluntar su kuma ana masu karerayi, kuma suna kokarin kare shi’ancin su, da kuma yada littattafai da rubuce-rubuce da yawa dan yada barnan su, da kuma bibiyar littattafan Ahlussunnah da yinkurin yi masu raddi, wanda babu hakan a wajen sauran kungiyoyin.


Yayinda littattafan shi’a suka yawaita a wannan lokaci fiye da lokutan da suka gabata, kuma suke ta yunkurin yada su ta kowace irin hanya a kowani wuri


Hakan sai ya zama wajibi akan mu mu dauko wadannan littattafan muyi musu tsirara mu baiyana abunda ke cikin su na


4


munanan aqidu wadanda suke ta kokarin boye su, kamar yadda wani mai magana ne yace: (daga bakin ku zamu gane addinin ku)!!


Muna rokon Allah madaukaki ya daga tutar sunnah da mabiyan ta, kuma ya kaskantar da karya da bata da kuma mabiyan ta.


Kuma Allah madaukaki shi ne abun nufi da wannan rubutu kuma shi ne mai shiryarwa zuwa ga tafarki madaidaici.


Wanda ya rubuta :


5


❖ Daga cikin aqidar i’yan shi’a masu limamai goma sha biyu: lallai su suna tabbatar da cewa lallai shi’a asalinta yahudanci ne, tushen ta yana komawa ga wani bayahude da ake kira Ibn saba’a alyahudi(bayahude), kuma lallai lallai sayyidina Aliyu dan Abi dalib Allah ya kara masa yadda ya kona su da wuta kuma ya barranta daga gare su.


Duba cikin: littafin (Firaqush shi’a), na Annubakhty, shafi na 22,


Kuma duba cikin littafin (ikhtiyar ma’arifaturrijal) na Addusy, shafi na 107


❖ Kuma sune suke fada suna masu alfahari da suna rafilawa da kuma dalilin da yasa aka sa masu sunan.


Duba cikin littafin (Biharul anwar) na Almajalisy, shafi na 65/97 .


❖ Kuma sune suke fadin cewa: lallai mu Allahn mu ba daya bane da nasu (wato Ahlussunnah), baza mu hadu ba wurin bauta wa Allah daya ba kuma Manzan mu ba daya bane haka nan kuma shugaban mu da na su ba daya bane, domin su Ahlussunnah suna cewa: lallai Ubangijin su shi ne wanda ya kasance annabi Muhammadu ne manzan sa, kuma halifan sa shi ne Abubakar, to mu kuma bamu yadda da wannan Ubangijin ba a matsayin ubangijin mu, kuma bamu yadda da wannan Annabin ba, mu muna cewa ne: lallai wannan ubangijin da halifan Annabin sa shi ne Abubakar to mu ba Ubangijin mu bane, kuma wannan Annabin ba Anabin mu bane.


6


Duba cikin littafin (alanwarun nu’umaniyya), na Ni’imatullahi aljaza’iry, mujalladi na biyu shafi na 278, (2/278).


❖ Kuma sune masu cewa: lallai ba’a ganin Allah ranar alkiyama, kuma shi ba’a siffan ta shi da wani wuri ko kuma wani zamani kuma ba’a nuni gare shi, kuma duk wanda yace lallai shi yana saukowa saman duniya, ko kuma shi yana baiyan ga iyan aljannah kamar wata, ko kuma makamancin haka to kamar ya kafurta ne da shi.


Duba cikin littafin (aqa’idul imamiyya), na Muhammad Rida muzwaffar, shafi na 58.


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah zai ruko kwankwasan mumini ranar alkiyama, shima mumini zai ruko kwankwasan Allah sai ya tuna mai zunuban sa.


Sai aka ce : meye ma’anar zai ruko kwankwasan sa? Yace: sai ya dora hannun sa akan qugun sa (kwankwaso), sai yace: haka kamar yadda dayan mu ke zantawa da dan uwansa akan wani abu da yake faranta masa rai.


Duba cikin littafin (al-usulu assittata asahar) bin diddigi: diya’u addin almahmudy, shafi na 203.


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah yana saukowa zuwa kasa ranar arafah a farkon zawali akan wani rakumi mara lafiya yana zubda miyau kuma yana taba wadanda suke arafa da cinyoyin sa dama da hagu.


Duba cikin littafin (al-usulu assittata asahar) bin diddigi: diya’u addin almahmudy, shafi na 204.


❖ Su ne suke cewa: lallai fuskantar kabari ayi sallah dole ne, koda bai dace da alkibila ba, kamar yadda fuskantar kabari yake a matsayin fuskantar alkibla nanne (fuskar Allah), wato bangaren da Allah ya umarci utane da su fuskanta a wannan halin.


7


Duba cikin littafin (Biharul anar) na Almajlisy, 101/369.


❖ Su ne suke cewa: lallai lafazin (AAH) suna ne daga cikin sunayen Allah mafi kyau, duk wanda yace: (AAH) to hakika ya nemi agaji ne daga Allah.


Duba cikin littafin (Mustadrakul wasa’il), na Nury Addabarsy 2/148.


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah yana kawo ma Hussaini dan Aliyu Allah ya kara musu yadda ziyara, kuma yana musafaha da shi, kuma yana zama tare da shi akan gado.


Duba cikin littafin (Sahifatul Abrar), na Mirza Muhammad Taqy, 2/140.


❖ Su ne suke cewa an canza alkur’ani mai girma kuma wai alkur’ani bai cika ba, kuma wai ingantaccen alkur’ani yana hannun Mhadin su wanda baya nan.


Daga cikin manya-manyan malaman iyan shi’a masu limamai goma sha biyu wanda suka ce an canza alkur’ani akwai:


Aliyu ibn Ibrahim alqummy, Ni’imatullah aljaza’iry, Alfaidh alkashany, Ahmad Addabarsy, Muhammad Baqir Almajlisy, Muhammad bun Annu’man Almulaqqab bi Almufid, Abul hasan Al’amily Adnan Albahrany, Yusuf Albahrany, Annury Addabarsy, Habibullahi Alkhu’iy, Muhammad bn Ya’qub Alkulainy, Muhammad Al’aiyashy, da ma wadan su wanda ba su ba da yawa.


Duba cikin littafin (Asshi’a Al’isna Ashariyya wa tahriful kur’an), na : Muhammad saif, da kuma littafin (Mauqifurrafida Min alkur’an), na : Mamadu Karambiry.


8


❖ Su ne suke cewa: lallai lafazin (Aali Muhammad da kuma Aali Aliyu) an cire su daga cikin alkur’ani.


Duba cikin littafin (Minhajul bara’ah Sharhu Nahjul balagah), na Habibullah Alkhu’iy, 2/216.


❖ Su ne suke cewa: babu wanda ya tattaro alkur’ani kuma yasan ma’anonin sa sai dai malaman su kawai (wato malaman su guda goma sha biyu), kuma wai su sun san ilimin alkur’ani dukkan sa baki saya.


Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/228.


❖ Su ne suke cewa: Alkur’ani ba hujja bane sai an hada shi da maganar malaman su,


Duba cikin littafi (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/169.


❖ Su ne suke cewa: akwai wata surah sunan ta suratul Wilaya, ta fara ne da cewa (Ya ku wadan da sukayi imani kuyi imani da haske guda biyu) wai Saiyidina Usman Dan Affan Allah ya kara masa yadda ne ya cire ta daga alkur’ani, kamar yadda suke riyawa.


Duba cikin littafin (Faslul kidab fi Tahrifi kitabi Rabbil Arbab), na Annury Addabarsy, shafi na 18.


❖ Su ne suke cewa: akwai wani alkur’ani mai suna (mushafu Fatimah) wato ma’ana, sunan shi Alkur’anin Fatimah Allah ya kara mata yadda, kuma wai akwai irin Alkur’anin mu a cikin sa har sau uku.


Duba cikin littafin (Usulul kafy), na Alkulainy, 1/239.


❖ Su ne suke canza fadar Allah madaukaki suna cewa, a cikin ayar da Allah yake cewa: “ ka isar da abun da aka saukar maka daga Ubangijin ka, in kuma baka aikata haka ba to baka isar da sakon Ubangijin ka ba” [ suratul ma’idah ; aya ta 67 ], sai suka ce: “ ka isar da abunda aka saukar maka daga ubangijin ka- gameda Aliyu- in kuma baka baka aikata haka ba to baka isar da sakon Sa ba”, sai suka kara kalmar (gameda Aliyu) da molan kansu!!


9


Wato ma’ana: wai Annabi (S.A.W) ya manta ko kuma ya bar wannan kalmar, wai wata kila yana jin tsoran munafukai ne, kamar yadda ya baiyana haka cikin labarai masu yawa.


Duba cikin littafin (Faslul Kidab fi Tahrifi Kitabi Rabbil Arbab), na Annury Addabarsy, shafi na 182.


❖ Su ne suke cewa: basa inkari ga mai cewa an canza alkur’ani (wannnan abu ne mafi nauyi) amma a wurin iyan shi’a duk wanda ya fadi haka suna mai kallan cewa shi mujtahidi ne, amma kuma duk wanda yake inkarin wilayar sayyidina Aliyyu (nauyi mai sauki), a wurin iyan shi’a shi kafiri ne babu shakka cikin kafurcin sa.


Duba cikin littafin (Al-i’tiqadat), na Ibn Babawaihy Alkummy, shafi na 103.


❖ Su ne suke cewa: sun umurci mabiyan su iyan shi’a da su karanta wannan Alkur’anin dake nan a cikin sallah da kuma yin aiki da hukunce-hukuncen sa har zuwa lokacin da shugaban su zai baiyana, a lokacin za’a dauke wannan alkur’anin daga hannun mutane a tafi da shi zuwa sama sai a kawo Alkur’ani na asali wanda Shugaban muminai Aliyu Bn Abi Dalib ya rubuta , sai ayi ta karanta shi kuma ana aiki da hukunce-hukuncen sa.


Duba cikin littafin (Alanwaru Annu’maniyya), na Ni’matullah Aljaza’iry, 2/363.


❖ Su ne suke cewa: kada ku koya wa matan ku suratu Yusuf, kuma kada ku karanta musu ita, saboda a cikin ta akwai fitintinu, amma ku koya musu Suratun Nur, saboda a cikin ta akwai wa’azozi,


Duba cikin littafin (Alfuru’ mina Alkafy), na Alkulainy 5/516.


10


❖ Su ne suke cewa: lallai duk wanda baiy imani da imamanci ba to imanin sa bai cika ba har sai yayi imani da ita kuma ya kudurce ta.


Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na Muhammad Ridah Muzaffar, shafi na 78.


❖ Su ne suke cewa: imamanci ci gaban annabci ne, kuma dalili ne da ke wajabta aiko da manzanni da turo da Annabawa, kuma shi ne ke wajabta nada shugaba bayan manzo.


Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na Muhammad Rida Muzaffar, shafi na 88.


❖ Su ne suke cewa: ma’anar imamanci wato wani tsari ne na Allah wanda yake nads shugaba n da ya zabe shi da ilimin sa na tun asali game da bayin sa, kamar yadda Allah ke zaban Annabi, kuma yana umurtar Annabi yayi nuni zuwa gare shi kuma yayi umarni da bin shi.


Duba cikin littafin (Aslush shi’a wa Usuluha), na Muhammad Husain Kashifu Algidwa, shafi na 102.


Ai ma shi imamanci asali ne daga cikin asullan addini, imani bai cika sai anyi imani da shi, a wata maganar suna cewa ne: imamanci cigaban annabci ne.


❖ Su ne suke cewa: lallai duk wanda ya musanta imamancin (shugabanci) shugaban muminai Aliyu Dan Abi Dalib da kuma imaman da suka zo a bayan sa to kamar wanda ya musanta annabcin Annabawa ne, kuma lallai duk wanda ya yadda da shugaban muminai Aliyu amma kuma sai bai yadda da daya daga cikin imaman da suka zo a bayan sa ba to kamar wanda ya yadda da dukkan Annabawa ne amma ya ki yadda da annabcin Annabi Muhammad (S.A.W).


❖ Su ne suke cewa : lallai duk wanda ya musanta imamancin daya daga cikin su-wato ma’ana limamai goma sha


11


biyu- to kamar wanda ya yi musun annabcin dukkan Annabawa ne, Allah ya kara aminci a gare su baki daya.


Duba cikin littafin (Minhaju Annajati), na Faidh Alkashany, shafi na 48.


❖ Su ne suke cewa: iyan shi’a Imamiyya sunyi ittifaki akan cewa duk wanda yayi musun imamancin daya daga cikin imamai kuma ya musanta abunda Allah madaukaki ya wajabta a kansa na wajabcin yi musu biyayya to shi kafiri ne kuma batacce, ya cancanci ya dawwama a cikin wuta.


Duba cikin littafin (Haqqul yaqeen Fi Ma’arifati Usuliddeen), na Abdullahi Shibr, 2/189.


❖ Su ne suke cewa: lallai amfani da kalmar Shirka da kuma kafurci suna tabbata ne akan duk wanda bai kudurce imamancin shugaban muminai ba da kuma imamai daga cikin yaran shi, kuma ya fifita wasu akan su, hakan na nuna cewa su iyan wuta ne kuma zasu dawwama a cikin ta.


Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 23/390.


❖ Su ne suke cewa: lallai Annabi (S.A.W) lokacin da aka haife shi ya yi kwanaki ba nonan da za’a shayar da shi, sai Abu Dalib ya dauke shi ya dora shi akan nonon sa, sai Allah ya zuba ruwan nono a cikin nonon Abu Dalib sai ya shayar da Annabi na wasu kwanaki har zuwa lokacin da Abu Dalib ya samu Halimatu Assa’diya sai ya mika shi zuwa gare ta.


Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/448.


❖ Su ne suke cewa: lallai Saiyidina Aliyu Allah ya kara masa yadda yafi Annabi (S.A.W) jarunta, wai asali ma Annabi (S.A.W) bai da jarumtaka.


Duba cikin littafin (Al’anwaru Annu’maniya), na Ni’matullahi Aljaza’iry, 1/17.


12


❖ Su ne suke cewa: Annabi (S.A.W) baya iya bacci har sai ya sumbaci kumatun Fatimah ko kuma ya sumbaci tsakanin nonuwanta (kirjinta).


Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 24/43.


❖ Su ne suke cewa: Annabi baida yara mata, fadima ce kawai yarinyar sa, kuma su Rukaiyya da Ummu kulsum da Zainab su agolansa ne kaai.


Duba cikin littafin (Da’iratul ma’arifil Islamiyyah Asshi’iyyah), 1/27.


❖ Su ne suke cewa: lallai Hasan dan Aliyu Allah ya kara musu yadda shi ne wanda ya tozarta muminai, saboda yayi wa Mu’awiyah Allah ya kara masa yadda mubaya’a.


Duba cikin littafin (Rijalul Kusshy), na Alkusshy. Shafi na 103.


❖ Su ne suke cewa: lallai matar Annabi (S.A.W) zata iya zama kafira kamar matar Annabi Nuhu da Annabi Lud,


Abunda suke nufi da matar Annabi (S.A.W) ita ce uwar muminai Aisha Allah ya kara yadda a gare ta ita da mahaifin ta.


Duba cikin littafin (Hadisul Ifk), na Ja’afar Murtada, shafi na 17.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aisha Allah ya kara mata yadda tayi ridda bayan rasuwar Annabi (S.A.W) kamar yadda Sahabbai da yawa suma sunyi ridda.


Duba cikin littafin (Asshubuhatun tthaqib Fi Bayani Ma’anan Nasib), na Yusuf Albahrany, shafi na 236.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aisha Allah ya kara yadda a gare ta ta tara dinari arba’in na yaudara da sata, ta raba su ga makiya Aliyu Allah ya kara yadda a gare shi!!


13


Duba cikin littafin (Mashariqu Anwarul Yaqin), na Rajab Albarsy, shafi na 86.


❖ Su ne suke cewa: lallai uwar muminai Aisha Alah ya kara yadda a gare ta tayi Zina muna neman tsarin Allah, a cikin fadar Allah madaukaki :” wadannan an barrantar da su daga abun da suke fada”, sai iyan shi’a suka ce: wannan aya tsarkaka ce ga Annabi daga aikata Zina, ba wai ita ba (suna nufin Aisha Allah ya kara yadda a gare ata).


Duba cikin littain (Assiradul Mustaqim), na Zainuddin Annabbady Albayady, 3/165.


❖ Su ne suke cewa: lallai Hafsah ta kafurta lokacin da ta ce: “ waye ya baka wannan labarin” { suratut tahrim :3}, sai Allah yace game da ita da kuma Aisha :” in kun tuba zuwa ga Allah to hakika zukatan ku sun tsarkaka” { suratut Tahrim : 4}, sai sukace ma’ana : zukatanku sun karkata, shi kuma karkata shi ne kafurci, kuma lallai Aisha da Hafsah sun hada kai dan su shayar da Annabi (S.A.W) guba, lokacin da Allah ya bashi labarin abunda suke so su aikata, sai yayi yunkurin kashe su, sai suke ta rantsuwa da Allah akan cewa basu aikata ba, sai Alah ya saukar da fadar sa:” ya ku wadanda suka kafurta baza’ayi muku uzuri ba a yau” { suratut Tahrim : 7},


Duba cikin littafin (Assiradul Mustaqim), na Zainuddin Annabbady Albayady, 3/168.


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah madaukaki yayi magana ne da Manzan Allah (S.A.W) a daren da yaje sama da muryar Aliyu Dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda da kuma yaren sa.


14


Duba cikin lttafin (Kashful Yaqin Fi Fada’ili Ameeril Muminin), na Hasan bn Yusuf bn Almudahhir Alhully, shafi na 229.


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah ya tattauna da Aliyu Dan Abi Dalib Allah ya kara yadda a gare shi a garin Ta’if, kuma mala’ika Jibrilu yana tsakanin su.


Duba cikin littafin (Basa’irud Drajat), na Assaffar, 8/230.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dan Abi Dalib shi ne mai raba aljannah da wuta, zai shigar da iyan aljannah cikin aljannah kuma zai tura iyan wuta zuwa wuta.


Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Assaffar, 8/235.


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah zai shigar da wanda yayi wa Aliyu da’a aljannah koda kuwa ya saba wa Allah madaukaki ne, kuma lallai Allah zaishigar da wanda ya saba wa Aliyu cikin wuta, koda kuwa yayi wa Allah da’a ne.


Duba cikin littafin (Kashful Yaqin Fi Fada’ili Ameeril Muminin), na Hasan bn Yusuf bn Almudahhir Alhully, shafi na 8.


❖ Su ne suke cewa: lalai Aliyu dan Abi Dalib shi ne sirrin Annabawa, kuma lallai Allah madaukaki yace: ya kai Muhammad, na aiko Aliyu tare da Annabawa a sirrance kai kuma na aiko ka tare da shi a baiyyane yana mai karfafa ka.


Duba cikin littafin (Al-asrarul Ulawiyya), na Muhammad Almas’udy, shafi na 181.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu ayah ne ga Annabi Muhammad (S.A.W), kuma lallai Annabi Muhammad yana kira ne zuwa ga yin wilaya ga Aliyu Allah ya kara yadda a gare shi.


Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Muhammad Assaffar, shafi na 91.


❖ Su ne suke cewa: babu wani Annabi Allah zai aiko face sai ya umarce shi da yin wilaya ga sayyidina Aliyu yana so ko baya so.


15


Duba cikin littafin (Al-asrarul Ulawiyya), na Muhammad Almasudy, shafi na 190.


❖ Su ne suke cewa: lallai addini bai cika sai da yin wilaya ga sugaban muminai Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara yadda a gare shi.


Duba cikin littafin (Al’ihtijaj), na Addabarsy, 1/57.


❖ Su ne suke cewa: lallai Manzan Allah (S.A.W) yace: ku saurara lallai mala’ika Jibrilu ya zo wuri na sai yace: ya kai Muhammad, Ubangijin ka yana umurarka da san Aliyu dan Abi Dalib, kuma yana umurtar ka da yi masa wilaya.


Duba cikin littafin (Basa’irud Darajat), na Muhammad Assaffar, shafi na 92.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dan Abi Dalib zai shiga aljannah kafin Annabi Muhammad (S.A.W) ya shiga.


Duba cikin littafin (Ilalu sshara’ii), na Ibn Babawaihy Al-qummy, shafi na 205.


❖ Su ne suke cewa: lalli tsawa tana zuwa ne daga umarnin Mutumin ku,


Sai aka ce ; waye mutumin mu?


Sai sukace: sugaban muminai Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda.


Duba cikin littafin (Al-iktisas), na Al-mufid, shafi na 327.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dn Abi Dalib yana raya matattu kuma yana yaye bakin ciki da damuwa daga wadan da suke cikin bakin ciki da damuwa


Duba cikin littafin (Uyunul Mu’jizat), na Husain Abdulwahhab, shafina 150, da kuma littafin (Halalul Mashakil), da kuma kissar Abdllah Alkhattab ta karya.


❖ Su ne suke cewa: lallai ba wanda zai shiga aljannah sai da izinin Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda.


Duba cikin littafin (Manaqibi Amiril Muminin), na Aliyu bn Almagazily, shafi na 93.


16


❖ Su ne suke cewa: duk wanda saba wa Aliyu to ya kafurta, kuma duk wanda ya fifita wani akan Aliyu to yayi ridda.


Duba cikin litafin (Bisharatul Mustafa Li shi’atil Murtada), 2/79.


❖ Su ne suke cewa: lallai Alah yayi alfahari ga mala’iku da Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kara masa yadda.


Duba cikin littafin (Bisharul Mustafa Li shi’atil Murtada), 1/66.


❖ Su ne suke cewa: lallai Annabawa da Manzanni an aiko su ne dan su tabbatar da wilayar Aliyu dan Abi Dalib ne Allah ya kara masa yadda.


Duba cikin littafin (Alma’alimu Azzulfa), na malamin su Hashim Albahrany, shafi na 303.


❖ Su ne suke cewa: lallai Aliyu dan Abi Dalib yayi nuni da hannun sa zuwa sama , sai wani girgije ya zo shi kuma wai sai yayi sama, sai yazo yayi sallama ga Aliyu dan Abi Dalib, sai yace wa Ammar: zo ka hau wannan dokin tare da ni, kuma kace: “ da sunan Allah ne take tafiya kuma take tsayawa” [ suratu Hud : 41], sai Ammar ya hau kan dokin sai sukayi sama har suka bace daga ganin mu.


Duba cikin littafin (Biharul Anwar) na Almajlisy.


❖ Su ne suke cewa: lallai wani kare ya ciji wasu mutum biyu cikin Sahabbai dan yin ramuwa ga Aliyu dan Abi Dalib, bayan ya fusata da irin fushin larabawa, kuma lallai wani jaki ya shaida cewa lallai Aliyu waliyyin Allah ne kuma shi ne wanda Annabi yayi wasiyya da a bashi jagoranci a bayan sa.


Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 41/247, da kuma 17/306.


17


❖ Su ne suke cewa: fatima da Hassan da Hussaini ma’asumai ne, da kuma yaran Hussaini amma banda yaran Hassan.


Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na Muhammad Rida Muzaffar, shafi na 89, da kuma shafi na 98.


❖ Su ne suke cewa: ba dan Aliyu ba da ba’a halicci Annabi Muhammadu ba, su kuma biyun ba dan Fatima ba da ba’a halicce su ba.


Duba cikin littafin (Al-asrarul Fadimiyya), na Muhammad Almas’udy, shafi na 98.


❖ Su ne suke cewa: lallai Fatima Allah ya kara yadda a gare ta yani yanki ne na Allah mai jujjuya al’amura, amma sai ya baiyana a siffar mace.


Duba cikin littafin (Al-asrarul Fadimiyya), na Muhammad Al-mas’udy, shafi na 355.


❖ Su ne suke cewa: lallai Fatima Allah ya kara yadda a agare ta ta kasance tana yi wa mahaifiyar ta magana tun tana cikin ta ba’a haifeta ba.


Duba cikin littafin (Fatimatuz Zahra’ Minal Mahdi Ilallahdi), na Muhammad Al-qazwiny, shafi na 38.


❖ Su ne suke cewa: lalai imaman iyan shi’a goma sha biyu sunfi Annabawa da Manzannni falala da daraja.


Duba cikin littafin (Al-anwarun Nu’maniyya), na Ni’matullah Aljaza’iry, 3/308.


❖ Su ne suke cewa: lallai imaman iyan shi’a sun san duk abunda ya faru a da da kuma wanda zi faru nan gaba, kuma su babu wani abu da ya boyu a gare su wanda basu san shi


18


ba,kuma su basa mutuwa sai dai in su suka zabi hakan suka damar mutuwa da kan su.


Duba cikin littafin (Usulul Kafy), na Alkulainy, 1/258.260.


❖ Su ne suke cewa: lallai kowane imami yana da wani wuri a ranar lahira na yabo da wata daraja madaukakiya, da kuma halifanci mai karfi wanda dukkan halittun duniya suna kasancewa ne karkashin sa.


Duba cikin littafin (Tahrirul Wasila), na Alkumainy, shafi na 52.


❖ Su ne suke cewa: lallai limamai goma sha biyu suna da wilaya ta halitta, zasu iya halitta komai amma banda Allah mahalicci, kuma wannan wilayar kamar wilayar Allah ce akan halittun sa.


Duba cikin (Misbahul Fuqaha), na Abil Qasim Alku’iy, 5/33.


❖ Su ne suke cewa: lallai mu muna da wasu darajoi a wurin Allah, babu wani mala’ika makusanci da yake da su ko kuma wani Annabi Manzo- wato ma’ana, imamai goma sha biyu- .


Uba cikin littafin (Tahrirul Wasila), na Alkumainy, shafi na 94.


❖ Su ne suke cewa: lallai imamai goma sha biyu in sun zartar da abu to babu abun da ya isa hana wanan abun faruwa, hakanan in sun so faruwar wani abu a lailatul kadari to babu makawa wannan abun sai ya faru da makamancin haka, kuma dukkan wadannan abubuwan babu makawa sai sun tabbata.


Duba cikin littafin (Alburhanul Qadi’), amsoshi ne na tambayoyi game da aqida da shari’ah, na malamin su Muhammad Taqiy Albahjat, shafi na 14.


❖ Su ne suke cewa: lallai wasiyyai (wato ma’ana, imamai goma sha biyu) ana daukar cikin su ne a cikin mahaifa kuma a haife su ta cinya, kuma su najasa bata taba su.


Duba cikin littafin (Madinatul Mu’ajiz), na Hashim Albahrany, 8/22.


19


❖ Su ne suke cewa: lallai Allah da mala’ikun sa da Annabawan sa da Muminai dukkan su suna ziyartar kabarin shugaban muminai Aliyu dan Abi Dalib Allah ya kra yadda a gare shi.


Duba cikin littafin (Alfuru’ minal Kafy), na Alkulainy, 4/580.


❖ Su ne suke cewa: lallai imami kamar Annabi ne shima ya wajaba ya zamo ma’asumi daga dukkan laifi da alfahsha ta baiyane da boye, tun daga yarunta har zuwa mutuwa, da ganganci ko kuma da mantuwa, domin su imamai sune masu tsare shari’ah kuma sune suke tsaye akan al’amuran shari’a, halin su akan haka kamar halin Annabi ne.


Duba cikin littafin (Aqa’idul Imamiyya), na malamin su Ibrahim Azzanjany, 3/179.


❖ Su ne suke cewa: lallai mala’iku an halicce su ne dan su zama masu hidima ga ahlul baity.


Duba cikin littafin (Biharul Anwar), na Almajlisy, 26/335.


❖ Su ne suke cewa: dukkan shabbai sun kafurta, musamman ma Abubakar da Umar da Usman da Khalid bn Alwaleed da Mu’awiya dan Abi Sufyan da Mugira dan Shu’bah, sai da mutum uku ne kawai basu kafurta ba.


Duba cikin littafin (Arraudah mina Alkafy), na Alkulainy, 8/245.


❖ Su ne suke cewa: (aqidar mu (wato aqidar iyan shi’a) a game da barranta: lallai mu mun barranta daga gumaka guda



Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC