Labarai

1


Jerin Littafan Shi’a Na 3


Aqidar


Taqiyya


a wajen


‘Yan Shi’a


Umar Labxo


2


بسم الله الرحمن الرحيم


Ma’anar Taqiyya ita ce bayyana savanin abinda yake zuci, watau


mutum ya faxi savanin abinda ya qudure a zuciyarsa, ko ya aikata wani aiki


tare da nuna cewa ya yarda da aikin amma a zuciyarsa yana ganin aikin ba


dai-dai ba ne, ko bai dace ba, ko kuma haramun ne. Zai yi haka da niyyar


jawo hankalin wasu, ko yaudarar su, da nuna musu kansa ba a haqiqanin


yadda yake ba.


Ayatullahi Khumaini ya bayyana ma’anar taqiyya a wajen ‘yan Shi’a,


kamar haka: “Taqiyya ma’anarta ita ce mutum ya faxi magana wacce ta


savawa ainihin abinda yake akwai, ko ya aikata wani aiki wanda yake sava


wa mizanin Shari’a.”1


Manufar Taqiyya ita ce jawo hankalin mutane da samun yardarsu da


soyayyarsu ta hanyar voye abinda aka san ba sa so, ko ba zai karvu ba a


wajensu. Khumaini yana faxi dangane da haka, “An shar’anta Taqiyya


domin yin kara ga mutane da jawo soyayyarsu da qaunarsu.”2 A wani wurin


kuma ya ce, “Abin nufi da kara shi ne ya zama manufar ita ce haxa kai da


xayantaka ta hanyar jawo soyayyar masu sava mana da samun qaunarsu.”3


Masu sava mana, a maganar tasa, su ne duk waxada ba ‘yan Shi’a ba.


‘Yan Shi’a sun san aqidunsu ba za su tava karvuwa ba ga Musulmi,


saboda savawarsu ga Alqur’ani da Sunnah da hankali lafiyayye. Don haka


suke voye su, su xauki salon yaudara da munafurci, wanda suke kira kara,


don yaxa su da tallata su a tsakanin jama’a. Haka nan, suna xaukar son


1 Duba Kashful Asrai na Ayatullahi Khumaini, bugun Teheran, 1363, shafi na 147.


2 Duba littafinsa, Arrasa’il, bugun Qum-Iran, mujalladi na 2, shafi na 175.


3 Arrasa’il, mujalladi na 2, shafi na 174.


3


iyalin gidan Annabi(SAW), Ahalul Baiti, a watsayin wani mayafi da suke


lullve wannan munafurci nasu da shi.


Taqiyya tana da muhimmanci sosai, da matsayi mai girma, da falala


mai yawa a cikin tafarkin Shi’anci. Dangane da wannan, babban


malaminsu, Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, ya ruwaito daga Imaminsu


na biyar Abu Ja’afar, wai ya ce: “Taqiyya tana daga addinina da addinin


iyayena. Kuma babu imani ga wanda bai da taqiyya.”1


Babu shakka dangana wannan riwaya ga Abu Ja’afar, Allah ya yi


masa rahama, qarya ce tsagwaronta; saboda Abu Ja’afar da iyayensa ba su


san munafurci ko yaudara ba.


‘Yan Shi’a suna amfani da Taqiyya a matsayin wani mayafi da suke


lulluve bidi’arsu da miyagun aqidojinsu da shi. Suna da hanyoyi masu yawa


na yin haka. Da farko dai, idan bai zama dole ba, xan Shi’a ya kan so ya


voye haqiqanin cewa shi xan Shi’a ne, musamman inda ya san mutane suna


da wayewa game da qungiyar. Idan kuma asirinsa ya tonu, aka san cewa shi


xan Shi’a ne, to sai ya yi qoqarin nuna cewa ba wani abu ne Shi’a ba face


qaunar iyalin gidan Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, da goyon bayan su


da jivintar su.


Koda yake ‘yan Shi’a suna qudure matuqar gaba da qiyayya ga


Sahabban Annabi, waxanda suke xaukar su a matsayin kafirai da suka yi


ridda, amma suna voye wannan qiyayya da quduri nasu, ba sa bayyana su ga


mutane. Sau da yawa ma su kan yi musun hakan, kuma su kan nuna cewa


qin Sahabbai wani mummnan abu ne wanda bai kamata a zarge su da shi ba.


Amma littafansu da maganganunsu suna tabbatar da haka.


1 Duba Usulul Kafi na Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, bugun Darul Murtadi, Bairut, Lebanon, 1426,


mujalladi na 2, shafi na 219.


4


Haka nan, ‘yan Shi’a suna yin taqiyya dangane da Alqur’ani mai


girma, inda suke nuna cewa su ma suna ban gaskiya da shi kamar sauran


Musulmi, duk da yake suna qudure cewa wai Sahabbai sun yi sauye-sauye a


cikinsa. Ga aqidar Shi’a, Alqur’ani an yi qari da ragi a cikinsa, saboda haka


ba dukkaninsa suka yarda da shi ba. Amma suna voye wannan quduri nasu,


su nuna cewa sun yarda da Alqur’ani dukkaninsa.


Wani salon Taqiyya kuma da ‘yan Shi’a suke nunawa shi ne makirci a


cikin alaqar su da mutane. Za ka ga xan Shi’a yana yin kirki, yana habahaba


da mutane, kuma yana taimakon su, amma duk yana yin haka ne domin


jawo hankalinsu da shigar da su tafarkin Shi’anci. A wani yayi, su kan


gabatar da taimako da agaji ga marasa lafiya, ko mabukata, da sunan


taimakon ‘yan uwa Musulmi, amma duka Taqiyya ce. Manufarsu a koda


yaushe ita ce jawo hankalin mutane waxanda ba su san haqiqanin tafarkinsu


ba.


Fagagen Taqiyya


Taqiyya a wajen ‘yan Shi’a tana shiga dukkanin fagage na addini da


rayuwa. Suna yin Taqiyya a cikin ma’amala, kamar yadda muka gabatar,


kuma suna yin ta a cikin ibadoji da harkoki na yau-da-kullum.


Taqiyya a Cikin Sallah


‘Yan Shi’a suna yin Taqiyya a cikin sallah, kuma wannan yana ba su


dama su yi sallah tare da Ahalus Sunnah domin su yaudare su. Koda yake


suna xaukar Ahalus Sunnah a matsayin kafirai, saboda ba su yi imani da


Imamai ba kuma ba su barranta daga Sahabbai ba, amma yana halatta a gare


5


su su bi su sallah, kuma sallar ta inganta ba sai sun rama ta ba, matuqar dai


da niyyar Taqiyya suka yi ta.


Babban malaminsu, Ayatullahi Ruhullahi Khumaini, yana faxi


dangane da kama hannu a sallah kamar haka: “Xora xayan hannaye a bisa


xayan, kamar yadda masu sava mana suke yi , yana vata sallah idan an yi


hakan da gan-gan. Amma babu laifi idan aka yi shi a bisa ga Taqiyya.”1


Masu sava mana, yana nufin Ahalus Sunnah.2


Magajin Khumaini, watau jagoran qasar Iran a yau, Ayatullahi Ali


Khamna’i, da aka tambaye shi, ya ce: “Sallah na inganta a bayansu (Ahalus


Sunnah) idan ya zama an yi ta saboda kara gare su.”3 Kara, a maganarsa,


tana nufin yaudara.


Har yau, an tambayi wani babban malamin nasu mai suna Ayatullahil


Uzma Abul Qasim Alkhu’i: Shin sallah na inganta a bayan limami Ahalus


Sunna? Sai ya ce, “Tana inganta idan an yi ta bisa Taqiyya.”4


Shi kuwa Ayatullahi Muhammad Rida Musawi Kalbayakani cewa ya


yi, “Babu laifi a yi sallah a bayansu tare da larura, amma idan ba larura to


za’a rama sallar idan an samu ikon yin haka.”5


Mai karatu zai lura cewa sharaxin sallar xan Shi’a a bayan Ahalus


Sunna shi ne Taqiyya ko larura. Idan larura ta sa shi, to zai rama idan ya


samu iko. Amma idan ya yi bisa Taqiyya ne to sallar ta inganta, kuma ba sai


ya rama ba. A wani qaulin ma cewa aka yi zai samu lada, kamar yadda ya zo


a wata ruwayar daga malaminsu, Kalbayakani, ya ce: “Sallah na inganta a


bayan Ahalus Sunna a yayin Taqiyya, kuma ladan hakan yana da yawa.”6


1 A duba Taharirul Wasila na Khumaini, mujalladi na 1, shafi na 186.


2 Duba littafinmu Matsayin Musulmi a Wajen ‘Yan Shi’a.


3 A duba Ajwibatul Istifta’at na Ali Khamna’i, bugun Darul Haqqi, Bairut, shafi na 178.


4 Duba Masa’ilun Wa Rudud na Khu’i, bugun Qum, mujalladi na 1, shafi na 26.


5 Duba littafinsa, Irshadus Sa’il, bugun Maktabatul Faqih, Kuwait, shafi na 39.


6 Duba Majma’ul Masa’il na Kalbayakani, bugun Maktabatul Irfan, Kuwait, mujalladi na 1, shafi na 194.


6


Taqiyya a cikin Azumi da Hajji


Kamar yadda ya halasta ga xan Shi’a ya yi Taqiyya a sallah, haka nan


ya halasta gare shi ya yi Taqiyya a cikin azumi da hajji domin yaudarar


Ahalus Sunnah.


Babban malamin Shi’a na wannan zamani, wanda ‘yan Shi’ar Nijeriya


suke yin koyi da shi, Ayatullahi Khumaini, yana cewa: “A sani abinda ake


fa’idanta daga ruwayoyi shi ne ingancin aikin da aka gina a kan Taqiyya,


sawa’un an yi Taqiyyar ne saboda savanin dake tsakaninmu da su (Ahalus


Sunna) a hukunci, kamar shafa a kan huffi da buxa baki da zarar gudan rana


ya faxi, ko kuwa saboda savanin tabbatar faruwar wani abu, kamar kamawar


wata, misali tsayuwar Arafa a ranar takwas ga wata saboda su a wajensu tara


ne.”1


Abinda Khumaini yake faxi a nan shi ne, ruwayoyi daga Imaman


Shi’a suna tabbatar da cewa duk aikin da aka gina shi a kan Taqiyya ya


inganta. Sai ya ba da misali da cewa, idan xan Shi’a ya yi shafa a kan huffi


don ya yaudari Ahalus Sunna, ko ya gaggauta buxa baki, to aikinsa ya


inganta duk da cewa su a wajensu waxan nan abubuwa biyu ba sa inganta.


Kamar yadda aka sani, ‘yan Shi’a ba sa shafa a kan huffi (wanda


Sunna ce ta Annabi (SAW) amma su ba su yarda da ita ba) kamar yadda ba


sa gaggauta buxa baki (wanda shi ma Sunna ce da suke musun ta) sai dai su


jinkirta sai taurari sun fito.2 Haka nan, idan xan Shi’a bai ga wata ba yana


iya kama azumi tare da Ahalus Sunna a kan Taqiyya kuma azumin nasa ya


yi, kamar yadda yake iya tsayuwar Arafa ranar takwas ga watan Zul Hijja (a


lissafinsa) idan Ahalus Sunna suka ce tara ne, kuma hajjinsa ya yi.


1 A duba littafin Arrasa’il na Khumaini, bugun Qum, 1385 B.H., mujalladi na 2, shafi na 196.


2 Duba littafinmu, Bacin Tafarkin ‘Yan Shi’a, babin Fikihun ‘Yan Shi’a.


7


Duba ka gani, ya xan uwa mai karatu, wannan abin mamaki na ‘yan


Shi’a. Su ba abinda ya dame su! Ko ina ta faxi sha ne a wajensu. Su dai su


voye gaskiyar lamarinsu; kada a gane su. Wannan addini na ‘yan Shi’a da


arha yake! Anya Allah ake nufi da wannan addinin?!


Taqiyya a Jana’iza da Sallar Gawa


‘Yan Shi’a suna yaudarar Ahalus Sunna wajen halartar jana’izar


mamatansu da yi musu sallah, amma ba addu’a suke yi musu ba; la’anar su


suke yi. Wannan shi ne abinda manyan malamansu, kai har ma da Imamansu


(a faxinsu) suke koya musu.


Wani malami daga cikin magabatansu mai suna Muhammad binu


Muhammad binu Nu’uman wanda suke wa laqabi da Almufid, yana cewa:


“Ba ya halasta ga wani daga cikin masu imani ya wanki mai sava wa


gaskiya dangane da wilaya. Kuma kada ya yi masa sallah sai dai idan larura


ta tilasta masa yin haka bisa ga Taqiyya. To sai ya wanke shi irin wankin


masu sava mana, kuma kada ya ba shi wasiqa.1 Sa’an nan idan ya yi masa


sallah, to sai ya la’ance shi, kada ya yi masa addu’a a cikinta.”2


Malaman Shi’a sun karvo ruwaya daga Imaminsu na shida, Abu


Abdillah Ja’afar Sadiq (Allah ya rahamshe shi kuma ya isar masa qarerayin


da aka laqa masa) cewa wai, “Wata rana Hussaini binu Ali (Imami na uku ke


nan a wajen ‘yan Shi’a, Allah ya qara masa yarda) ya fita zuwa jana’izar


wani munafuki da ya mutu, sai ya gamu da wani almajirinsa. Ya tambayi


almajirin: Ina za ka, wane? Sai ya ce: Ina guje wa jana’izar wan nan


munafukin ne; kada in yi masa sallah. Sai Hussaini ya ce masa: Zo mu je ka


1 ‘Yan Shi’a suna danka wasika a hannun mamatansu, su bunne su da ita. Wani kaset da suka nuna yadda


suke jana’iza a nan Nijeriya ya tabbatar da haka. Nemi kaset din don ka gane wa idanunka.


2 Duba littafin Almuqni’ah na Binu Nu’uman Almufid, bugun Mu’asasatun Nashril Islami, Qum-Iran, shafi


na 85.


8


tsaya a damana, duk abinda ka ji na faxi ka faxa. Lokacin da liman ya yi


kabbara a kan (mamacin) sai Hussaini ya ce: Allahu Akbar! Ya Allah, ka


la’anci wane bawanka la’ana dubu, haxaxxiya ba rababbiya ba. Ya Allah, ka


wulaqanta bawan nan naka a cikin bayi, ka shigar da shi zafin wutarka, ka


xanxana masa tsananin azabarka, domin ya kasance yana jivintar


maqiyanka, yana gaba da masoyanka, yana qin iyalin gidan Annabinka.”1


Jivintar maqiyan Allah, a wajen ‘yan Shi’a, shi ne soyayya ga


Sahabbai, gaba da masoyan Allah kuma qin Ahalul Baiti. Waxan nan su ne


sifofin Ahalus Sunna da malaman Shi’a suke laqa musu bisa qarya da


zalunci. Ahalus Sunna suna son, kuma suna jivintar, Sahabbai da Ahalul


Baiti dukkaninsu, Allah ya qara yarda a gare baki xaya.


Har yau, Alhurrul Amili ya ruwaito a cikin littafinsa, Wasa’ilus Shi’a,


daga Abu Abdillahi wai y ace, “Idan (mamacin) mai musun gaskiya ne sai


ka ce: Ya Allah, ka cika cikinsa da wuta, ka cika qabarinsa da wuta, ka aiko


masa da macizai da kunami!”2


Ya xan uwa mai karatu, dubi wannan qiyayya da qeta da mugun nufi


dake cike da zukatan ‘yan Shi’a, kuma suna dangana shi bisa qarya ga


zavavvun bayin Allah, shiyagabannin Ahalul Baitti. Muna roqon Allah ya


shirye su, ya shiryatar da mu baki xaya.


Shin Gaskiya Ne ‘Yan Shi’a Suna Son Ahalul Baiti?


Babban makamin Taqiyya da ‘yan Shi’a suke amfani da shi, shi ne


son iyalin gidan Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, da jivintar su, da goyon


bayan su. Amma wannan da’awa tasu, maganganunsu da rubuce-rubucensu


1 Wannan ruwaya Aldusi ya fitar da ita a cikin littafinsa, Tahzibul Ahakami, mujalladi na 3, shafi na 197; da


Ibnu Babawaihi Alqummi a cikin Man La Yahaduruhul Faqih, mujalladi na 1, shafi na 105; da Alhurrul Amili


a cikin Wasa’ilus Shi’a, mujalladi na 2, shafi na 771.


2 Duba Wasa’ilus Shi’a na Muhammad binul Hassan Alhurrul Amili, mujalladi na 2, shafi na 771.


9


suna qaryata ta. Za mu kawo misalai na irin waxan nan maganganu nasu


waxanda muka tsamo daga cikin littafan manyan malamansu.


Tavargazarsu Ga Annabi(SAW)


Da farko dai ‘yan Shi’a sun yi wa Annabi(SAW) cin fuska ta hanyar


zargin iyalinsa, watau Innar Muminai A’isha(RA), da zina, da nacewarsu a


kan wannan zargi duk da kuvutarwa, da barrantarwa, da wankewa da


Alqur’ani ya yi mata daga wannan zargin. Sa’an nan, suka zargi manyan


Sahabbansa, kuma surukansa, da liwaxi, watau Umar binul Khaxxabi uban


matarsa Hafsa da Usmanu binu Affan mijin xiyansa biyu, Ruqayya da


Ummu Kulthum. Babu shakka a cikin wannan zargi ga waxanda suke kusa


da Annabi, yake son su, kuma ya yarda da su, akwai cin fuska ga


Manzo(SAW) da keta irili da suka mummuna.


Amma ‘yan Shi’a ba su tsaya a nan ba. A’a sun fito fili sun faxi wasu


munanan maganganu da suke nuna suka ga Annabi(SAW) kai tsaye. Ba za


mu kawo misalai masu yawa ba saboda muninsu, amma za mu ba da misali


xaya rak saboda mai karatu ya gani da idanunsa irin abinda ‘yan Shi’a suke


faxi a haqqin Annabinmu Muhammad(SAW), kuma ya san cewa da’awar


son Ahalul Baiti Taqiyya ce kawai suke yi. Ibnu Taimiya ya hakaito faxinsu


cewa, “A ranar lahira za’a qona al’aurar Annabi (SAW), saboda ya auri


A’isha.”1 Wal iyazu billahi!!


Wannan xanyar magana, wacce take nuna kafircin mai faxin ta, ‘yan


Shi’a na wannan zamani suna maimaita ta, kamar yadda ya zo a littafin


Kashful Asrari wa Tabri’atil A’immatil Axhari na Sayyid Hussain


Almusawi. Ya rubuta cewa, xaya daga manyan malaman Shi’a na wannan


zamani, mai suna Sayyid Ali Garawi, ya ce: “Lallai Annabi (SAW) babu


makawa sai al’aurarsa ta shiga wuta saboda ya auri wasu mata mushirikai.”2


Yana nufin Aisha da Hafsa, Allah ya qara musu yarda.


1 Duba Majmu’ul Fatawa na Ibnu Taimiya, bugun Saudi Arabiya, mujalladi na 28, shafi na 262.


2 Duba Kashful Asrari na Musawi, bugun Darul Iman, Iskandariyya, 2002, shafi na 21-22.


10


Wannan magana ba ta bukatar wani dogon sharhi. Babu shakka cewa,


wanda duk yake qudure cewa SILIN GASHI XAYA na Annabi(SAW) zai


shiga wuta, to wannan KAFIRI ne.


Banda wannan, manyan malaman Shi’a suna zargin Annabi(SAW) da


cewa ya gaza isar da aike. Ayatullahi Khumaini yana faxi a cikin littafinsa


Kashful Asrari kamar haka, “A bayyane take cewa da Annabi ya isar da


saqo dangane da lamarin Imama gwargwadon yadda Allah ya umarce shi,


kuma ya yi qoqarin da ya kamata dangane da lamarin, da dukkan wannan


savani bai taso ba a qasashen Musulmi, kuma da ba’a samu qiyayya da


yaqoqa ba, kuma da ba’a samu savani ba a tushen addini da ressansa.”1


Sai mai hankali ya dubi wannan magana da abinda ta qunsa:


Khumaini yana nufin Annabi(SAW) bai isar da aike ba kamar yadda Allah


ya umarce shi, kuma shi ne sanadin gaba da qiyayya da yaqoqa tsakanin


al’umma. Watau ke nan Annabi(SAW) BA RAHAMA BA NE SHI GA


TALIKAI, kamar yadda Allah ya sifanta shi a cikn Alqur’ani, tunda ya zama


sanadin yaqoqa da qiyayya da gaba a tsakanin al’umma. Wal iyazu billahi!!


Har yau, wani malamin Shi’a na wannan zamanin, mai suna Jabir


Agani, yana faxi dangane da Annabinmu(SAW) kamar haka: “Amincin


Allah ya tabbata a gare ka, ya Ma’aikin Allah, amma ka yi kuskure, kuskure


mai girma(!!) a yayin da ka fita daga duniya ba tare da ka yi wasiya ga kowa


ba (dangane da al’amarin Imama). Kai za ka xauki alhakin hayaniyar da


al’umma ta afka a ciki, da fitintinun da take fama da su. Don me ba ka yi


wasiya ba, ya Ma’aikin Allah?!”2


Sai mu duba wannan magana da kyau, ya ‘yan uwa Musulmi. Akwai


kafircin da ya wuce mutum ya ce: ANNABI(SAW) YA YI KUSKURE,


KUMA BAI ISAR DA AIKEN ALLAH BA? Wal iyazu billah!!


Wannan ita ce maganar masu da’awar cewa suna son iyalin gidan


Annabi(SAW), watau Ahalul Baiti, kuma suna jivintar su, suna goyon bayan


su!! A bayyane take cewa wannan da’awa Taqiyya ce kawai.


1 Duba Kashful Asrari na Khumaini, shafi na 50.


2 A duba Shafin Gizo mai adireshi kamar haka: http://www.youtube.com/watch?v=l 8s KGuwa 4o.


11


Tavargazarsu Ga Ali(RA)


A cikin qoqarinsu na vata sunan shugabannin Musulunci da siffanta


su da siffar marasa mutunci, malaman Shi’a suna dangana maganganu masu


yawa ga Sarkin Musulmi Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara masa yarda, irin


maganganun da ba mai furta su sai wanda ya kai matuqa a rashin mutunci.


Babban malaminsu mai suna Muhammad Baqir Almajalisi ya ruwaito cewa:


Wata mace ta miqe a cikin masallaci, alhalin Sayyidina Ali yana yin


huxuba, sai ta ce, “Ya kai makashin masoya!” Wai sai Sayyidina Ali ya


dube ta, ya ce: “Ya ke mara kunya, ya ballagaza. Ya wacce ba ta haila kamar


yadda mata ke haila. Ya wacce a kan abin naninta akwai wani abu da ya


burtso, yana reto.”1 “ABINNANI,” wannan fassarata ce, amma shi mai


ruwayar ya yi amfani da wata kalmar Larabci da take nufin FARJI, wacce


idan da za mu fassara ta zuwa Hausa to da sai dai mu koma ga tsohuwar


Hausa ta Maguzawa mu nemo kalmar.


Saboda Allah, ya xan uwa mai karatu, tana yiwuwa Ali binu Abi


Xalib, Allah ya qara masa yarda, ya furta waxannan kalmomi, alhali yana


kan mimbari yana huxuba a masallaci? Kuma idan ya yi nufin ladabtar da


wannan matar ne, ko mayar mata da martani, babu wasu kalmomin da suka


fi dacewa da matsayinsa na Sahabi, kuma qanin Annabi(SAW), wanda ya


taso aka raine shi a gidan Annabta? Babu shakka wannan qoqarin vata sunan


Ali ne, da ma sauran Ahalul Baiti, da ‘yan Shi’a suke yi, kuma a lokaci guda


suna fakewa (suna yin Taqiyya) da cewa wai su masu qaunar su ne.


Har yau, akwai wani labari da ‘yan Shi’a suke bayarwa cewa, wai


wata rana wata mace ta yi wa wani mutum qazafi, sai ta xauki ruwan qwai


farin, ta zuba shi a tsakanin qafafunta, ta ce wai ya yi lalata da ita, kuma


wannan maniyyinsa ne. Wai sai Ali binu Abi Xalib(RA) ya tashi, ya duba


tsakanin qafafunta, ya ce qarya take yi, wannan ba maniyyi ba ne!!2


Mai karatu, sai ka duba wannan magana da idanun basira. Ta qaqa Ali


zai duba tsakanin qafafun mace muharrama don kawai ya tabbatar da qarya


ko gaskiyarta?! Shin duka garin ba wata mace wacce za’a sa ta yi wannan


1 Duba Biharul Anwari na Muhammad Baqir Almajalisi, bugun Ihiya’ut Turathi, Bairut, 1403, mujalladi na


41, shafi na 293.


2 Duba Biharul Anwari na Majalisi, mujalladi na 4, shafi na 303.


12


aikin? Shin wannan ba qoqarin zubar da mutuncin Sarkin Musulmi Ali ba


ne?


Tavargazarsu Ga Nana Faxima(RA)


Malaman Shi’a sun siffanta Nana Faxima, Allah ya qara mata yarda,


da siffofi waxanda suke nuna matuqar suka da zubar da girma. A nan ma, za


mu taqaita saboda munin waxannan siffofin. A dangane da gadonta da


suka ce wai Khalifa Abubakar Siddiq ya hana ta, kuma wai Umar ya xaure


masa gindi a kan haka, suna ruwaito yadda ita Faxima xin ta kai gwauro ta


kai mari don neman gadon nata. Suka ce, “Faxima(AS) ta iske Abubakar da


Umar a masallaci, ta yi musu maganar gadonta na gonar Fadak, inda ta yi


faxa da su, ta yi kururuwa, mutane suka taru, kuma ta kama wuyan Umar ta


jawo shi zuwa gare ta.”1


Mai karatu ya dubi yadda wannan ruwaya ta siffanta Faxima: matar


aure, Musulma, ta iske mazaje, abokan ubanta (kuma surukansa), a bainar


jama’a, ta yi faxa da su a kan gona, har ta ci kwalar xayansu!! Shin idan ma


wannan gadon ya dame ta, ba ta da miji, ko wani xan uwa, da zai karvo mata


haqqinta? Ai ba Faxima ba, wacce take Balarabiya, Baquraishiya,


Bahashima, kuma ‘yar Manzon Allah(SAW), ko wata ‘yar Fulani


Bakanuwa, ba za ta aikata wannan rashin mutuncin ba. Amma abin mamaki


shi ne, ‘yan Shi’a sun yarda da wannan ruwaya, kuma suna kattaba ta a cikin


littafansu!!


Irin waxan nan maganganu na vatanci da ‘yan Shi’a suke dangana wa


Ahalul Baiti suna da yawa ainun a cikin littafansu. A nan, mun kawo xan


misali ne kawai don mu tabbatar wa da mai karatu cewa da’awar qaunar


iyalin gidan Manzon Allah(SAW) da Shi’awa suke yi munafurci ne kawai da


yaudara da Taqiyya!!


1 Duba Kitab Salim binu Qais na Salim binu Qais Alhilali, bugun Mu’assasatul Bi’itha, Bairut, ba tarihi, shafi


na 253.


13



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA