Tabbatar da Kasancewar Allah tare da Halittunsa
da cewa Hakan ba ya Kore Xaukakarsa a kan Al’arshinsa
A cikin faxin Manzon Allah (SAW), “Mafificin imani shi ne ka san cewa, Allah yana
tare da kai inda duk kake.” (Hadisi ne kyakkyawa). Da faxinsa, “Idan xayanku yana sallah, to
kada ya tofa kaki a nahiyar fuskarsa, ko a damansa; domin lalle Allah yana nahiyar fuskarsa.
Amma ya tofa a hagunsa, ko a qarqashin sawunsa.” (Bukhari da Muslim).
Da faxin Manzo (SAW), “Ya Allah! Ubangijin sammai bakwai da qasa, Ubangijin
Al’arshi mai girma. Ya Ubangijinmu, Ubangijin dukan kome, mai tsaga qwaya da iri (su tsiro),
mai saukar da Attaura da Linjila da Qur’ani. Ina neman tsarinka daga sharrin kaina da sharrin
dukan wata dabba da kake riqe da makwankwaxarta. Kai ne na farko, babu wani abu gabaninka,
kuma kai ne na qarshe, babu wani abu a bayanka. Kai ne na sarari, babu wani abu birbishinka
kuma kai ne na voye, babu wani abu koma bayanka. Ka biya mini bashi, kuma ka wadatar da ni
daga talauci.” (Muslim ya ruwaito shi).
Da faxinsa (SAW) lokacin da Sahabbai suka xaga murya da zikiri: “Ya ku mutane! Ku
sauqaqa wa kawunanku; lalle ku ba kurma kuke kira ba, ko wanda ba ya nan. Amma kuna kiran
mai ji ne, mai gani, makusanci. Lalle wanda kuke kira ya fi kusanci izuwa xayanku daga wuyan
abin hawansa.” (Bukhari da Muslim).
Tabbatar da Ganin Muminai ga
Ubangijinsu Ranar Qiyama
A cikin faxin Manzon Allah (SAW), “Lalle ku da sannu za ku ga Ubangijinku, kamar
yadda kuke ganin wata a daren sha huxu. Ba za ku yi turereniya ba wajen ganinsa. Idan kun
samu iko kada sallah ta gagare ku kafin hudowar rana da kafin faxuwarta, to ku aikata.” (Bukhari
da Muslim).
Matsayin Ahalus Sunna dangane da Hadisan
da suke Bayanin Sifofin Ubangiji
Akwai hadisai da yawa irin waxanda muka ambata, waxanda a cikinsu Manzon Allah
(SAW) yake bad a labari dangane da Ubangijinsa. Tawagar masu tsira, Ahalus Sunna wal
Jama’a, suna ban gaskiya das u, ba tare da karkatar da ma’anarsu ko vata ma’anar ba, kuma ba
17
tare da takamaimai ko misaltawa ba. Domin su, Ahalus Sunnah, tsakatsakiya ne a cikin
qungiyoyin al’umma, kamar yadda al’ummar take tsakatsakiya a tsakanin sauran al’ummai.
Matsayin Ahalus Sunna wal Jama’a
a tsakanin qungiyoyin Al’umma
Ahalus Sunna tsakatsakiya ne a babin sifofin Ubangiji Maxaukaki tsakanin Jahamawa
masu vata ma’anar sifofin da Mushabbiha masu kamanta su da sifofin bayi.
Haka nan, su tsakatsakiya ne a babin ayyukan Allah tsakanin Jabarawa da Qadarawa da
wasunsu. A babin sunayen imani da addini kuwa, su tsakatsakiya ne tsakanin Haruriyya da
Mu’utazilawa da Murji’a da Jahamawa. Kamar yadda a dangane da Sahabban Annabi (SAW)
suke tsakatsakiya tsakanin Rafilawa da Khawarijawa.
Wajabcin imani da Daidaito da Kasantuwa
tare da Bayi da Bayanin cewa Babu kore Juna tsakanin Biyun
Babu shakka abinda muka ambata na imani da Allah ya haxa da yin imani da abinda
Ubangiji ya ba da labari da shi a cikin Littafinsa, kuma ya zo ta hanyar tawaturi daga Manzonsa,
kuma magabatan al’umma suka haxu a kai, cewa Allah Maxaukaki yana birbishin sammansa, a
kan Al’arshinsa, yana mai xaukaka a bisa halittunsa.
Da cewa shi Ubangiji Maxaukaki yana tare da bayinsa inda duk suke, yana sane da
abinda suke aikatawa, kamar yadda Allah ya game bayanin haka a cikin faxinsa, “Shi ne wanda
ya halitta sammai da qasa a cikin wasu kwanuka shida, sa’an nan ya daidaitu a kan Al’arshi,
yana sanin abinda ke shiga cikin qasa da abinda ke fita daga gare ta, da abinda ke sauka daga
sama da abinda ke shiga cikinta, kuma shi yana tare da ku, duk inda kuka kasance. Kuma Allah
mai gani ne ga abinda kuke aikatawa.” (Suratul Hadid: 4).
Kuma faxinsa, “shi yana tare da ku” ba yana nufin yana gauraye da halitta ba ne; domin
ba’a fahimtar haka daga Lugga. Saboda ga wata, wanda shi aya ne daga cikin ayoyin Allah kuma
yana cikin mafi qanqantar halittun Allah, yana sama kuma yana tare da matafiyi da wanin
matafiyi inda duk yake.
Shi Ubangiji Maxaukaki yana kan Al’arshinsa, yana kallon bayinsa, yana mai cikakken
iko da su, yana mai tsinkaye a kansu… da wanin wannan na ma’anonin Rububiyyarsa.
Kuma dukan wannan zance da Allah ya ambata, cewa yana kan Al’arshi kuma yana tare
da mu, gaskiya ne a bisa haqiqaninsa, ba ya bukatar wata karkatar da ma’ana, sai dai ana
18
tsarkake shi daga tsammace-tsammacen qarya, kamar a yi zaton cewa faxar “yana cikin sama”
ma’anarsa saman ta yi masa inuwa, ko tana xauke da shi. Wannan qarya ne a bisa ijma’in
malamai masu imani. Domin Allah kursiyyunsa ya wadaci sammai da qasa (to ya za’a ce sama ta
yi masa inuwa ko tana xauke da shi?), kuma shi yana riqe da sammai da qasa don kada su gushe,
kuma yana riqe da sama don kada ta faxi a kan qasa sai da izininsa, kuma yana daga cikin
ayoyinsa sama da qasa su tsayu da umarninsa.
Wajabcin Imani da Kusancin Allah
ga Halittarsa da cewa Hakan ba ya
Kore Xaukakarsa da Birbishintakarsa
Har yau, imani da Allah ya haxa da yin imani cewa shi makusanci ne, mai amsawar kira,
kamar yadda Allah Maxaukaki ya game tsakanin biyun a cikin faxinsa, “Kuma idan bayina suka
tambaye ka daga gare ni, to, lalle ni Makusanci ne. Ina karva kiran mai kira idan ya kira ni.”
(Suratul Baqara: 186). Da faxin Manzo (SAW), “Wanda kuke kira ya fi kusa da xayanku daga
wuyan abin hawansa.”
Abinda aka ambata a cikin Alqur’ani da Sunna na kusancinsa da kasancewarsa tare da
bayinsa, ba ya kore xaukakarsa da birbishintakarsa. Domin shi, mai girma da xaukaka, wani abu
bai zama kamar tamkarsa ba. Shi maxaukaki ne a cikin kusancinsa, makusanci ne a cikin
xaukakarsa.
Wajabcin Imani da cewa Alqur’ani
Zancen Allah ne a Haqiqa
Yana daga cikin imani da Allah da Littafansa, yin imani da cewa Alquar’ani zancen
Allah, abin saukarwa ne, ba halittacce ba ne. Daga gare shi ya faru, kuma gare shi zai koma.
Kuma Allah ya yi furuci da shi a haqiqa, kuma cewa wannan Alqur’anin da ya saukar ga
Muhammad (SAW) maganar Allah ne a haqiqa, ba maganar waninsa ba.
Bai halatta a saki magana da cewa, Alqur’ani hikayar maganar Allah ne, ko bayani ne na
maganar. Idan mutane suka karanta shi, ko suka rubuta shi a takardu, wannan ba ya fitar da shi
daga kasancewa zancen Allah Maxaukaki na haqiqa. Domin magana ana danganta ta ga wanda
ya faxe ta da farko, ba wanda ya isar da ita, ko ya iyar da ita ba.
Alqur’ani zancen Allah ne, haruffansa da ma’anoninsa, ba haruffan ne kawai maganar
Allah ba banda ma’ana, kuma ba ma’anar kawai ba ce banda haruffan.
19
Wajabcin Imani da Ganin Muminai
ga Ubangijinsu Ranar Alqiyama
Har yau, abinda muka ambata na imani da Allah da Littafansa da Mala’ikunsa da
Manzanninsa ya haxa da yin imani da cewa Muminai za su ga Allah a Ranar Qiyama, quru-quru
da idanunsu, kamar yadda suke ganin rana tantarwai idan babu girgije da ya kare ta, kuma kamar
yadda suke ganin wata a daren sha huxu, ba sa turereniya a wajen ganinsa.
Za su gan shi, tsarki ya tabbatar masa, a filin tashin qiyama, sa’an nan kuma su gan shi
bayan shiga Aljanna gwargwadon yadda ya so su gan shi, Maxaukaki.
Wajabcin Imani da Ranar Lahira
da Abinda ke Cikinta
Yana daga cikin imani da Ranar Lahira, ban gaskiya da duk abinda Annabi (SAW) ya ba
da labari da shi na abinda zai faru bayan mutuwa. Don haka, Ahalus Sunna suna imani da fitinar
kabari, da azabarsa da ni’imarsa.
Dangane da fitinar kabari, ana jarrabar mutane a cikin kaburburansu. Sai a ce da mutum:
Wane ne Ubangijinka? Mene ne addininka? Wane ne Annabinka?
Sai Allah ya tabbatar da waxanda suka yi imani da magana tabbatacciya a cikin rayuwar
duniya da cikin Lahira. Mumini sai ya ce: Allah ne Ubangijina, Musulunci ne addinina,
Muhammadu ne Annabina.
Shi kuwa mai shakku sai ya ce: Ha! Ha! Ban sani ba. Na ji mutane na faxin wani abu, ni
ma sai na faxa. Sai a doke shi da guduma ta baqin qarfe, sai ya yi qara wacce ko wace halitta za
ta ji ta in banda mutum. Da mutum zai ji ta, da sai ya mutu saboda tsananinta.
Sa’an nan bayan wannan jarrabawar, sai ni’ima ko azaba har ranar tashin Qiyama,
lokacin da za’a komo da rayuka zuwa ga jikkunansu.
Sa’an nan, sai Alqiyama da Allah ya ba da labarinta a cikin Littafinsa, da bisa harshen
Manzonsa, kuma Musulmi suka haxu a kanta, ta tashi. Mutane su tashi daga qaburburansu zuwa
ga Ubangijin talukai suna tsirara, ba kaciya, ba takalma, Rana ta matso dab da su, gumi ya kama
su har wuya.
Sa’an nan sai a kafa sikeli wanda za’a auna aikin bayi da shi. “To, waxanda sikelinsu ya
yi nauyi, to, waxan nan su ne masu babban rabo. Kuma waxanda sikelinsu ya yi sauqi, to, waxan
20
nan ne waxanda suka yi hasarar rayukansu suna madauwama a cikin Jahannama.” (Suratul
Muminun: 102-103).
Kuma a watsa littafai, watau takardun ayyuka. Wani ya kama takardarsa da hannun dama,
wani da hannun hagu ko ta bayan bayansa, kamar yadda Allah Maxaukaki yake faxi, “Kuma
kowane mutum mun lazimta masa abin rikodinsa a cikin wuyansa, kuma mu fitar masa a Ranar
Qiyama da littafi wanda zai haxu da shi buxaxxe. Ka karanta littafinka. Ranka ya isa ya zama
mai hisabi a kanka a yau.” (Suratul Isra: 13-14).
Sai Allah ya yi hisabi ga talukai. Ya kevanta da bawansa mumini, ya tabbatar masa da
zunubansa, kamar yadda aka sifanta a cikin Alqur’ani da Sunna. Kafirai kuwa, ba’a yi musu
hisabi irin hisabin wanda ake auna kyawawan ayyukansa da munana, domin su ba su da
kyawawan ayyuka. Sai dai za’a qididdige ayyukansu, a lasafce su, sai a tsayar da su a kansu, a
tabbatar musu da su.
Tafkin Annabi (SAW)
da Wurin da Yake da Sifofinsa
A cikin filin Qiyama akwai Tafkin Annabi (SAW). Ruwansa ya fi nono fari, kuma ya fi
zuma zaqi. Qoqunan shansa kamar adadin taurarin sama. Tsawonsa tafiyar wata, haka nan
faxinsa tafiyar wata. Wanda ya sha shi sau xaya, ba zai ji qishi ba har abada.
Siraxi: Ma’anarsa da Yadda
ake Wucewa a Kansa
Siraxi ana kafa shi a kan Jahannama. Shi ne gada wacce take tsakanin Aljanna da wuta.
Mutane za su wuce ta kansa gwargwadon ayyukansu: wasu kamar qiftawar ido, wasu kamar
walqiya, wasu kamar kaxawar iska, wasu kamar tafiyar ingarman doki, wasu kamar tafiyar
raqumi, wasu kamar a guje, wasu kamar a tafe, wasu kamar da jan gindi. Wasu kuma za’a fauce
su, a jefa cikin Jahannama; domin a kan gadar akwai qugiyoyi waxanda suke fauce mutane
saboda ayyukansu.
21
Kadarko tsakanin Aljanna da Wuta
Wanda ya wuce a kan siraxi, zai shiga Aljanna. Bayan wuce Siraxi, sai mutane su tsaya a
kan wani kadarko tsakanin Aljanna da wuta. Sai a yi ramuwa tsakanin waxanda suka cuci.1
Bayan an tsaftace su, an tsarkake su, sai a yi musu izini su shiga Aljanna.
Farkon wanda zai buxe qofar Aljanna shi ne Muhammad Manzon Allah (SAW), kuma
farkon al’ummar da za ta shiga ita ce al’ummarsa.
Cetuka na Annabi (SAW)
Manzon Allah (SAW) yana da ceto guda uku Ranar Alqiyama:
Ceto na farko, zai ceci mutane da aljanu da suke filin tashin Qiyama baki xaya, don Allah
ya yi hukunci tsakaninsu, bayan dukan Annabawa sun ja da baya: Adamu da Nuhu da Ibrahimu
da Musa da Isa xan Maryamu. Har a zo kan Annabi Muhammad (SAW), sai ya yi ceto.
Ceto na biyu, shi ne ya ceci ‘yan Aljanna don su shiga Aljanna. Waxan nan ceto guda
biyu na Annabi (SAW) ne shi kaxai a keve.
Sai ceto na uku wanda zai ceci waxanda suka cancanci shiga wuta, a shigar da su
Aljanna. Wannan ceto Annabi Muhammad (SAW) yana yin sa, kuma sauran Annabawa da
Siddiqai da wasunsu, su ma suna yi. Sai su ceci waxanda suka cancanci shiga wuta, kada su
shige ta. Kuma su ceci waxanda suka riga suka shiga wuta, a fito da su a sa su cikin Aljanna.
Fitarwar Allah ga wasu masu Savo daga Wuta
da Rahamarsa ba da Ceton Kowa ba
Allah zai fitar da wasu mutane daga wuta ba da ceton kowa ba; amma don falalarsa da
rahamarsa kawai. Sa’an nan sai a samu ragowar wuri a cikin Aljanna, waxanda suka shige ta
daga mutanen duniya ba su cika ta ba. Sai Allah ya halitta mata wasu mutane, su shige ta.
Abubuwan da Gidan Lahira ya qunsa na hisabi da iqabi da Aljanna da wuta, da
bayaninsu filla-filla duka an ambace su, ta hanya mai gamsarwa mai warkarwa, a cikin Littafan
da aka saukar daga sama, da ilmin da aka gada daga Annabawa, da ilmin da aka gada daga
Annabinmu Muhammad (SAW). Wanda yake bukatar bayaninsu, zai same su a inda suke.2
1 Babu mai shiga Aljanna da hakkin wani a wuyansa. Sai bayan mai hakki ya rama, an tsarkake kowa daga hakkin
dan uwansa, sa’an nan sai su shiga Aljanna suna tsarkakakku, tsaftatattu daga dukan hakki.
2 Wannan wani kalubale ne ga Musulmi a cikin hikima cewa su nemi ilmin Tauhidi da Akida.
22
Imani da Qaddara da Darajojin Qaddara
Tawagar masu tsira ta Ahalus Sunna wal Jama’a suna ban gaskiya da qaddara: alherinta
da sharrinta. Kuma imani da qaddara hawa biyu ne, kuma ko wane hawa yana qunsar abubuwa
biyu.
Hawa na farko shi ne imani da cewa Allah Maxaukaki masani ne da halittu, kuma cewa
su suna aikata aiki gwargwadon saninsa na tun azal wanda yake sifantuwa da shi tun azal, kuma
har abada. Ya san dukan halayensu na xa’a da na savo, da arzikinsu da ajalinsu. Sa’an nan kuma
Allah ya rubuta qaddarorin halittu a Lauhul Mahafuz.
Farkon abinda Allah ya halitta shi ne alqalami. Sai ya ce da shi: Rubuta! Sai ya ce: Me
zan rubuta? Sai ya ce: Rubuta abinda zai kasance har zuwa Ranar Qiyama.
Saboda haka, abinda duk ya samu mutum, da ma ba zai tava kauce masa ba. Kuma
abinda duk ya kauce wa mutum, da ma ba zai tava samun sa ba. Alqaluma sun bushe, kuma an
ninke takardu, kamar yadda Allah Maxaukaki yake faxi, “Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah
yana sanin abinda yake cikin sama da qasa? Lalle ne wancan yana cikin Littafi, lalle wancan ga
Allah mai sauqi ne.” (Suratul Hajji: 70). Kuma yana faxin, “Wata masifa ba za ta auku ba a cikin
qasa ko a cikin rayukanku face tana a cikin littafi a gabanin mu halitta ta. Lalle wannan, ga
Allah, mai sauqi ne. (Suratul Hadid: 22).
Wannan qaddarawa, wacce take biye da ilmin Allah Maxaukaki, tana kasancewa a
wurare a dunqule da a fayyace. Allah ya rubuta abinda yake so a cikin Lauhul Mahafuz. Kuma
lokacin da ya halicci jikin xan tayi (a cikin uwarsa), kafin ya busa masa rai, sai ya aiko Mala’ika
ya umarce shi da kalmomi huxu: Sai a ce masa: Rubuta arziqinsa da ajalinsa da aikinsa da mara
rabo ne shi ko mai rabo, da abubuwan da suka yi kama da haka.
Irin wannan qaddarawar, a da qungiyar Qadariyya masu tsananin ra’ayi sun kasance suna
musun ta. Amma a yau, masu musun ta kaxan ne.1
Hawa na biyu na qaddara shi ne nufin Allah mai zarcewa da qudurarsa mai gamewa.
Wajibi a nan shi ne imani da cewa, abinda Allah ya so shi zai kasance, kuma abinda bai so ba ba
zai kasance ba. Kuma cewa, duk abinda yake cikin sammai da qasa na motsi da shuru, ba sa
kasancewa sai da nufin Allah Maxaukaki. Duk abinda ba ya nufi, ba ya kasancewa a cikin
mulkinsa. Kuma shi, tsarki ya tabbatar masa, mai iko ne a bisa dukan kome na samammun
abubuwa da rasassu. Babu wani abin halitta a cikin sama ko a qasa, face Allah ne mahaliccinsa.
Ba mahalicci sai shi, kuma babu Ubangiji sai shi.
1“A da, da a yau” da ya ambata yana nufin a zamanin Shaihul Islami Ibnu Tamiyya. Mu a zamaninmu, ba karba ko
musu ne matsala ba, SANI shi ne matsala. Sai ka san abu sa’an nan za ka karbe shi ko ka yi musun sa. Muna da
sauran aiki!
23
Amma tare da haka, Allah ya umarci bayi da su yi masa xa’a, su yi xa’a ga Manzanninsa.
Kuma ya hane su ga barin savo.
Kuma shi, mai girma da xaukaki, yana son masu taqawa da masu kyautatawa da masu
adalci. Kuma yana yarda da waxanda suka yi imani, suka yi ayyuka na qwarai. Ba ya son kafirai,
kuma ba ya yarda da mutane fasiqai. Ba ya umarni da alfasha, ba ya yarje wa bayinsa kafirci,
kuma ba ya son fasadi.
Bayi masu aikata ayyukansu ne a haqiqa, kuma Allah shi ne mahaliccin ayukan nasu.
Bawa shi ne mumini, shi ne kafiri,1 shi ne mai biyyaya, shi ne mai fajirci, shi ne mai
sallah, shi ne mai azumi.
Bayi suna da iko a kan ayyukansu, suna da nufi. Amma Allah shi ne mahaliccin su da
ikonsu da nufinsu, kamar yadda Maxaukaki yake cewa, “Ga wanda ya so, daga cikinku, ya
shiriya. Kuma ba za ku so ba, sai idan Allah Ubangijin halitta ya yarda.” (Suratut Takwir: 28-
29).
Wannan hawa na qaddara, kafatanin qungiyar Qadariyya, waxanda Annabi (SAW) ya
kira su Majusawan wannan al’umma, suna qaryatawa da shi. Wasu masu tabbatar da qaddara
kuma suna wuce gona da iri, har ta kai su suvale bawa daga iko da zavi da yake da su. Kuma su
fitar da hikimomi da maslahohi daga ayyukan Allah da hukunce-hukuncensa.
Haqiqanin Imani da kuma
Hukuncin mai Aikata Babban Zunubi
Yana daga cikin aqidar Ahalus Sunna cewa, addini da imani sun tattare magana da aiki:
maganar zuciya da harshe, da aikin zuciya da harshe da gavvai. Kuma cewa imani yana qaruwa
da aiki, yana raguwa da savo.
Amma duk da haka, ba sa kafirta Musulmi saboda aikata savo da manyan zunubai, kamar
yadda Khawarijawa suke yi. ‘Yan uwartakar imani tana tabbata tare da aikata savo, kamar yadda
Allah Maxaukaki yake cewa, “To wanda aka yi rangwamen wani abu gare shi daga xan uwansa,
to, a bi da alheri,” (Suratul Baqara: 178). Da faxinsa, “Kuma idan jama’a biyu ta muminai suka
yi yaqi, to, ku yi sulhu a tsakaninsu. Sai idan xayansu ta yi zalunci a kan gudar, to, sai ku yaqi
wadda ke yin zalunci har ta koma ga umarnin Allah. To, idan ta koma, sai ku yi sulhu a
1 Watau shi ne mumini idan ya yi imani, ba’a cewa Allah ne ya imanantar da shi duk da cewa Allah ne mahaliccin
imaninsa, kuma da mufinsa ya yi imanin. Shi ne kafiri idan ya yi kafirci, ba’a cewa Allah ne ya kafirtar da shi duk da
cewa Allah ne mahaliccin kafircinsa, kuma da nufinsa ya kafirta. Watau imaninsa da kafircinsa aikinsa ne, saboda
zabinsa ne, ikonsa ne, kuma Allah zai yi masa sakamako a kai, duk da cewa imanin da kafircin halittar Allah ne
kuma nufinsa ne.
24
tsakaninsu da adalci, kuma ku daidaita. Lalle Allah na son masu daidaitawa. Muminai ‘yan uwan
juna kawai ne, saboda haka ku yi sulhu a tsakanin ‘yan uwanku biyu.” (Suratul Hujurat: 9-10).
Ba sa suvale fasiqi Musulmi daga Musuluncinsa baki xaya. Ba sa yi masa hukunci da
dauwama a cikin wuta, kamar yadda Mu’utazilawa suke qudurewa.
Amma su a wajensu, fasiqi yana shiga cikin sunan imani, kamar yadda Allah Maxaukaki
ya ce, “Sa’an na idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutane maqiya a gare ku, kuma
shi mumini ne, sai ‘yantarwar wuya mumina.” (Suratun Nisa: 93).
Kuma tana yiwuwa ya zama bai shiga cikin sunan imani ba kai tsaye, kamar cikin faxin
Allah Maxaukaki, “Abin sani kawai, muminai su ne waxanda suke idan an ambaci Allah,
zukatansu su firgita, kuma idan an karanta ayoyinsa a kansu, su qara musu wani imani.” (Suratul
Anfal: 2). Ko faxin Annabi (SAW), “Mai zina ba ya zina a lokacin da yake zina alhalin yana
mumini, haka nan ba ya sata a lokacin da yake satar alhalin yana mumini, haka nan ba ya shan
giya a lokacin da yake shan ta alhali yana mumini, haka nan ba ya xaukar wani abu mai qima
daga dukiyar ganima wanda zai sa mutane su dube shi a lokacin da yake xaukar alhali yana
mumini.”
Don haka, a nan sai mu ce: Shi mumini ne mai tauyayyen imani, ko kuma, mumini ne
saboda imaninsa kuma fasiqi ne saboda kaba’irarsa. Saboda haka, ba za’a ba shi sunan imani kai
tsaye ba, ba kuma za’a savule masa sunan kai tsaye ba.
Abinda ya Wajaba dangane da Sahabbai
da Bayanin Falalarsu
Yana daga cikin aqidar Ahalus Sunna wal Jama’a, kuvutar zukatansu da harasansu ga
Sahabban Manzon Allah (SAW),1 kamar yadda Allah Maxaukaki ya sifanta su a cikin faxinsa,
“Kuma waxanda suka zo daga bayansu,2 suna cewa: Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara a gare mu,
kuma ga ‘yan uwanmu, waxanda suka riga mu yin imani, kada ka sanya wani qulli a cikin
zukatanmu ga waxanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle kai ne mai tausayi, mai jin qai.”
(Suratul Hashri: 10).
Kuma saboda xa’a ga Ma’aiki (SAW) a cikin faxinsa, “Kada ku zagi Sahabbaina! Na
rantse da wanda raina ke hannunsa, da xayanku zai ciyar da kwatankwacin (dutsen) uhudu na
zinare, da ba zai kai (ladan) mudu guda ba na xayansu, ko rabin mudu.”
Ahalus Sunna suna karvar abinda ya zo a cikin Alqur’ani da Sunna da ijma’in malamai
na falalar Sahabbai da martabobinsu. Suna fifita waxanda suka ciyar da dukiya daga cikinsu
1 Kubutar zukatansu da harasansu, watau ba sa kin su da zukatansu, ba sa zagin su da harasansu.
2 Watau daga bayan Sahabbai, sauran Musulmi duka ke nan.
25
kuma suka yi yaqi kafin Cin Makka, wanda shi ne Sulhin Hudaibiyya, a kan waxanda suka ciyar
da dukiya suka yi yaqi a bayansa. Kamar yadda suke gabatar da Muhajiruna a kan Ansarawa.
Haka nan, suna yin imani da cewa, Allah ya faxa wa Sahabbai da suka halarci Yaqin
Badar, alhali su xari uku ne da goma sha wani abu, “Ku aikata abinda kuka ga dama, lalle na
gafarta muku!” Kamar yadda suke imani da cewa, ba xaya da zai shiga wuta daga Sahabban da
suka yi mubaya’a ga Annabi (SAW) a qarqashin itaciya, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya
ba da labari da haka. Maimakon haka, duka Allah ya yarda da su, su ma sun yarda da shi. Kuma
su fiye da dubu da xari huxu ne.
Ahalus Sunna suna shaida da Aljanna ga waxanda Annabi (SAW) ya yi musu shaida,
kamar Sahabbai goma (Asharatul Mubassharuna bil Janna), da Thabitu xan Qaisu xan Shammas,
da sauran Sahabbai waxanda Annabi ya yi wa shaida. Kuma suna ban gaskiya da abinda ya zo ta
hanyar tawaturi daga Sarkin Musulmi Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara masa yarda, da waninsa,
cewa mafifita a cikin wannan al’umma, bayan Annabinta, su ne Abubakar, sa’an nan Umar,
sa’an nan na uku Usmanu, sa’an nan na huxu Ali, Allah ya qara musu yarda baki xaya, kamar
yadda Hadisai suka nuna, kuma Sahabbai suka yi tarayya a kan gabatar da Usmanu a bisa Ali a
wajen mubaya’a.
Tare da cewa wasu Ahalus Sunna, bayan sun yi ittifaqi a kan fifita Abubakar da Umar,
sun yi savani dangane da Usmanu da Ali: waye ya fi a cikinsu? Sashe suka fifita Usmanu, suka
sa Ali na huxu, wani sashe suka fifita Ali, wani sashen kuma suka tsaya, ba su fifita kowa ba a
cikin biyun.
Amma daga bisani al’amarin Ahalus Sunna ya tabbata a kan gabatar da Usmanu, sa’an
nan Ali. Koda yake wannan mas’ala, mas’alar fifiko tsakanin Usmanu da Ali, ba ta cikin
al’amuran aqida waxanda ake xaukar wanda ya sava cikinsu a matsayin vatacce a wajen mafi
yawan malaman Sunna.
Sai dai abinda ake xaukar mai savani a cikinsa vatacce shi ne mas’alar Khilafa kanta.
Domin Ahalus Sunna sun yi ban gaskiya da cewa Khalifa bayan Manzon Allah (SAW) shi ne
Abubakr, sa’an nan Umar, sa’an nan Usmanu, sa’an nan Ali. Wanda ya yi suka dangane da
Khalifancin xaya daga cikin waxan nan, to, jakin gidansu ya fi shi shiriya.
Matsayin Ahalul Baiti
a Wajen Ahalus Sunna wal Jama’a
Ahalus Sunna suna qaunar iyalin gidan Annabi (SAW), Ahalul Baiti, suna jivintar su,
suna kiyaye wasiyyar Manzon Allah (SAW) dangane da su, inda yake faxi a Ranar Gadir Khum,
“Ina gam muku da Allah dangane da iyalin gidana.”
26
Da faxin Manzon Allah (SAW) ga baffansa Abbas a lokacin da ya yi masa koken cewa
wani sashe na Quraishawa suna mugusta ma’amala ga Banu Hashim, ya ce, “Na rantse da wanda
raina yake hannunsa, ba za su yi imani ba har sai sun so ku saboda kusancina.”
Da faxinsa, “Lalle Allah ya zavi Kinanatu daga ‘ya’yan Isma’il, kuma ya zavi
Quraishawa daga Kinanatu, kuma ya zavi Banu Hashim daga Quraishawa, kuma ya zave ni daga
Banu Hashim.”
Ahalus Sunna suna jivintar matan Manzon Allah (SAW), Uwayen Muminai, suna imani
da cewa su matansa ne a Aljanna. Musamman Khadija, uwar mafi yawan ‘ya’yansa kuma farkon
wacce ta yi imani da shi, ta taimake shi a bisa al’amarinsa, kuma ta zama tana da matsayi babba
a wajensa.
Da Siddiqa xiyar Siddiqu, Allah ya qara mata yarda, wacce Annabi (SAW) ya ce
dangane da ita, “Fifikon A’isha a kan sauran mata kamar fifikon Tharid1 ne a kan sauran abinci.”
Kuvutar Ahalus Sunna wal Jama’a
daga Abinda ‘Yan Bidi’a Suke Faxi
dangane da Sahabbai da Ahalul Baiti
Ahalus Sunna suna barranta daga tafarkin Rafilawa (‘yan Shi’a) waxanda suke qin
Sahabbai, suna zagin su, da kuma tafarkin Nasibawa waxanda suke cutata wa Ahalul Baiti ta
hanyar magana ko a aikace.
Suna kamewa ga barin abinda ya faru na savani tsakanin Sahabbai. Suna imani da cewa,
abubuwan da ake ruwaitowa na kurakuransu wasu a ciki qarya ne, wasu kuma an yi qari da ragi
a cikinsu, an sauya haqiqaninsu. Abinda yake gaskiya kuma, Sahabban suna da uzuri karvavve a
cikinsa: imma dai sun yi ijtihadi ne suka dace da dai-dai, wa imma sun yi ijtihadi suka yi kure.
Tare da haka, Ahalus Sunna ba sa qudure cewa Sahabbai ma’asumai ne ga barin manyan
zunubai da qananansu. Amma suna xauka cewa, zunubai na iya faruwa daga gare su. Sai dai
suna da ayyuka da suka gabatar da falala waxanda suke wajabta yafe zunubansu idan sun aikata
zunuban. Kuma ana gafarta musu zunubai da ba’a gafarta wa na bayansu, saboda suna da
kyawawan ayyuka masu shafe zunubai irin waxanda na bayansu ba su da su.
Sa’an nan ya tabbata daga Manzon Allah (SAW) cewa su ne mafifitan tsara, kuma
mudun xayansu, idan ya yi sadaka da shi, ya fi zinare kwatankwacin dutsen Uhudu na waxanda
suka zo daga bayansu.
1 Tharid wani nau’in abinci ne wanda ba bu kamar sa a kasar Larabawa.
27
Har yau, idan xayansu ya aikata zunubi, to tana yiwuwa ya tuba, ko ya aikata kyawawan
ayyuka waxanda suka shafe zunubin, ko ya zama an gafarta masa saboda falalar rigayensa ga
shiga Musulunci, ko saboda ceton Annabi (SAW) gare shi, domin babu shakka Sahabbai su suka
fi cancanta da cetonsa. Ko kuma tana yiwuwa ya zama an jarrabe shi da wani bala’i a duniya
wanda aka kankare masa zunubin a dalilinsa.
Idan ya zama haka dangane da zunuban da aka tabbatar da faruwarsu, to ina da al’amuran
da suka yi ijtihadi a cikinsu: idan sun yi dai-dai a ba su lada biyu, idan kuma sun yi kure a ba su
lada xaya, kuren kuma an yafe?
Sa’an nan kuma har yau, abinda ake wa wasu daga cikinsu inkari a kan aikata shi, idan
aka gwada shi da falalarsu da kyawawan ayyukansu, sai a ga qanqane ne ainun. Domin imaninsu
da Allah da Manzonsa, da jihadinsu don xaukaka addini, da hijirarsu, da taimakonsu ga addini,
da ilmi mai amfani da suka yaxa, da aiki mai kyau da suka gabatar, duka waxan nan suna dushe
duk wani qaramin zunubi da zai iya faruwa daga vangarensu.
Wanda ya dubi rayuwar Sahabbai da idon ilmi da basira, ya dubi abinda Allah ya yi musu
baiwa da shi na falala, zai sani a yaqini cewa su ne mafifitan halitta bayan Annabawa. Ba’a yi
kamarsu ba, kuma ba za’a yi ba. Kuma sune zavavvu daga cikin wannan al’umma wacce ita ce
mafificiya a cikin al’ummai, kuma mafi girma a wajen Allah.
Matsayin Ahalus Sunna wal Jama’a
dangane da Karamomin Waliyyai
Yana cikin aqidar Ahalus Sunna gaskatawa da karamomin waliyyai, da abinda Allah
yake gudanarwa a bisa hannayensu na al’amuran da suka sava al’ada. Kuma wannan yana
haxawa da nau’i-nau’i na ilmai da fahimta mai zurfi, da nau’i-nau’i na baiwa da tasiri, kamar
abubuwan da aka ruwaito daga al’umman farko a cikin Suratul Kahafi, da sauran su. Haka nan,
an ruwaito irin waxan nan al’amura daga magabatan wannan al’umma, kamar Sahabbai da
Tabi’ai da sauran malaman al’umma. Kuma irn waxan nan karamomi suna nan a cikin wannan
al’umma har zuwa ranar Alqiyama.
Sifofin Ahalus Sunna wal Jama’a
Yana cikin tafarkin Ahalus Sunna wal Jama’a bin gurabun Manzon Allah (SAW) a voye
da sarari, da bin tafarkin masu rigaye na farko na Muhajiruna da Ansar, da bin wasiyyar Manzon
Allah (SAW) inda yake cewa, “Na umarce ku da bin Sunnata da Sunnar Khalifofi shiryatattu,
masu shiryarwa a bayana. Ku yi riqo da ita, kuma ku ciza a kanta da fiqoqinku. Sa’an nan ina
gargaxin ku ga barin qagaggun abubuwa; domin dukan bidi’a vata ce.”
28
Ahalus Sunna suna qudure cewa, mafi gaskiyar zance shi ne maganar Allah, kuma mafi
alherin shiriya ita ce shiriyar Muhammad (SAW). Don haka suke fifita maganar Allah a kan ta
mutane, suna gabatar da shiriyar Annabi (SAW) a kan shiriyar kowa.
Wannan dalili ne ya sa ake kiran su Ahalul Kitabi was Sunna, kuma aka kira su Ahalul
Jama’a; saboda Jama’a ita ce haxin kai, kishiyar rarrabuwa. Ijma’i kuwa shi ne tushe na uku
wanda a kansa ake dogaro a fagen ilmi da addini.
Ahalus Sunna suna auna dukan abinda mutane suke kai na maganganu da ayyuka, na
voye da na sarari, waxanda suka shafi addini, da waxan nan tushe guda uku: Alqur’ani da Sunna
da Ijma’i. Kuma ijma’in da suke izna da shi, shi ne abinda magabata na gari suka kasance a kai,
domin a bayansu savani ya yi yawa, kuma ya yaxu a cikin al’umma.
Mas’aloli Masu Gamewa
Sa’an nan kuma tare da waxan nan tushe uku, Ahalus Sunna suna yin umarni da
kyakkyawan aiki, suna hani ga barin mummuna, kamar yadda Shari’a ta wajabta.
Suna qudure wajabcin tsayar da Hajji da Jihadi da Sallar Jumma’a da Sallolin Idi a
qarqashin Sarakunan Musulunci, na-kirki ne ko fajirai.1 Kuma suna kiyaye sallah a cikin jama’a.
Suna bauta wa Allah da yi wa al’umma nasiha, suna masu quduri da faxin Annabi
(SAW), “Mumini ga (xan uwansa) mumini kamar gini ne mai qarfi, sashensa yana qarfafar
sashe.” Da faxinsa, “Misalin muminai a soyayyarsu da tausayinsu da tausasawarsu ga juna,
kamar misalin jiki guda ne, idan wata gava ta yi rashin lafiya, sai sauran jikin ya amsa da zazzavi
da rashin barci.”
Ahalus Sunna suna umarni da yin haquri yayin jarraba da musiba, da yin godiya yayin
sauqi da yalwa, da yarda da qaddara mai xaci.
Haka nan, suna kira zuwa ga kyawawan halaye da ayyuka na-qwarai. Suna quduri da
faxin Annabi (SAW), “Mafi cikar muminai ga imani, shi ne mafi kyawunsu ga halaye.” Suna
umarni da ka sada wanda ya yanke zumuncinka, ka ba wanda ya hana maka, ka yi rangwame ga
wanda ya zalunce ka. Suna umarni da bin iyaye, da sada zumunci, da kyawun maqwaftaka, da
kyautata wa marayu da miskinai da ‘yan tafarki, da tausasa wa bawa. Suna hani ga barin alfahari
da girman kai, da zalunci, da danniya ga bayin Allah ba bisa haqqi ba. Suna umarni da
maxaukakan halaye,2 suna hani ga barin qananansu.1
1 Ahalus Sunna ba su yarda da tawaye ga masu mulki ba, amma suna bin su a cikin abinda ya yi dai-dai, su yi musu
nasiha a kan abinda ya saba haka. Don haka, idan sarki fajiri ya yi umarni da aiki mai kyau, kamar jihadi ko sallah,
sai ayi masa biyayya. Idan kuwa ya yi umarni da aiki mara kyawu, sai a yi masa nasiha, kuma ba za’a bi shi a kai ba.
2 Kamar jarunta da izza da kishi da kunya da tawali’u da kyauta da son naka (‘yan uwa) da fifita wani a kan kai.
29
Duk abinda suke faxi ko suke aikatawa, na waxan nan abubuwa da wasunsu, to suna yin
haka ne a cikin bin Alqur’ani da Sunna. Tafarkinsu shi ne Musulunci wanda Allah ya aiko
Mahammad (SAW) da shi. Kuma yayin da Annabi (SAW) ya ba da labari cewa al’ummarsa za ta
kasu gida saba’in da uku, duka suna wuta sai xaya kawai ita ce Jama’a. A wani hadisin kuma ya
ce, “Su ne waxanda suke kan abinda nake kai a yau, ni da Sahabbaina.” To sai masu riqo da
Musulunci tsintsa, wanda babu gauraye, suka zama su ne Ahalus Sunna wal Jama’a.
A cikinsu akwai Siddiqai da Shahidai da Salihai. A cikinsu akwai Malaman Shiriya,
Fitillun Zamani, da Ma’abota darajoji da falala. A cikinsu akwai Abdalu da Shuwagabannin
Addini, waxanda Musulmi suka yi ijma’i a kan shiriyarsu. Su ne tawaga masu rinjaye, waxanda
Annabi (SAW) ya ce dangane da su, “Wata tawaga daga cikin al’ummata ba za su gushe ba a
kan gaskiya suna masu rinjaye, wanda ya sava musu ko ya basar da su ba zai cuce su da kome
ba, har Alqiyama ta tashi.”
Muna roqon Allah ya sanya mu a cikinsu, kuma kada ya karkatar da zukatanmu bayan ya
shiryar da mu, kuma ya ba mu rahama daga gare shi. Lalle shi ne mai baiwa. Allah ne Masani.
Allah ya yi daxin tsira ga Annabi Muhammad, da Alayensa da Sahabbansa, tare da
aminci mai yawa.
Rufewa
Taron Dangi a kan Ahalus Sunna
Xan uwa mai karatu, wannan ita ce aqidar Ahalus Sunna, kamar yadda xaya daga
manyan malaman Sunna, Shaihul Islami Ibnu Taimiyya, ya shimfixa ta a cikin wannan
taqaitaccen littafi mai yawan fa’ida.
Wannan ita ce aqidar Sunna a cikin kyawunta da garai-garai xinta da tsakatsakiyarta.
Kamar yadda ake iya gani an tsamo ta daga zunzurutun ayoyin Alqur’ani da Hadisan Annabi, ba
wata fassara, ba wani tawili ko qarin bayani, don mutum ya karve ta kamar yadda Allah ya
saukar da ita, kuma kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya isar da it ga al’umma.
Aqida ce tatacciya, mai sauqi, tsakatsakiya, madaidaiciya a tafarki, ba ta zarqale ba a
dama ko a hagu, amma ta daidaita a tsakiya (Siraxal Mustaqima). Aqida ce wacce ta yi nesa da
guluwwi da qaqale. Ba mai zargin ta da tsauri sai jahili ko mai son zuciya.
Amma duk da sauqin wannan aqida da dogaronta kacokan a kan Alqur’ani da Sunna da
daidaitonta da tsakatsakiyarta, a yau wannan aqida an yi mata ca. Kafirai da Jahilai da ‘yan
bidi’a sun yi gamayya wajen sukan wannan aqida da kiran ta da sunaye dabam-daban don
qoqarin vata ta, da nesanta mutane da ita. Wani lokaci su kira ta Wahhabiyya, wani yayi su ce
1 Kamar tsoro da karanta da ragwanta da karaya da ganin kyashi da hassada da rowa da kwadayi da roko.
30
Takfiriyya, wani jiqon su ce ta masu tsaurin ra’ayi ce. To duka wannan babu mamaki, kuma
babu damuwa, domin wannan aqidar ita ce Musulunci; don haka duk mai qin Musulunci dole ya
qi ta.
Ya isa abin alfahari da godiyar Allah ga masu bin wannan aqida a ce kafiran duniya da
dangogin masu yin bidi’a da jahilai ‘yan takarda, waxanda suke zaton iya Turanci shi ne ilmi, su
haxu a kan gaba da ita da yaqar ta da qoqarin bushe haskenta.
Babu shakka wasu daga cikin masu da’awar bin wannan aqida suna yin tsanani, suna
nuna tsauri, suna wuce gona da iri a ayyukansu da maganganunsu. Amma duka wannan ba laifin
aqidar ba ne; laifin masu bin ta da jahilci ne, kuma iqirari da samuwar irin waxan nan mutane da
yarda da kurakuransu riqo ne da wannan aqida wacce take kira zuwa ga adalci da gaskiya.
Saboda haka, dole ne mu xamfari irin waxan nan mutane, mu matso da su, mu kira su ta
hanyar da aqidar ta koya mana, watau hamyar lalama da ruwan sanyi. Da haka ne za mu tantance
tsakanin jahili mai kyawun niyya da munafuki mai shigege, wanda ya ari sunan aqidar don ya
vata ta.
Muna roqon Allah Maxaukaki, da Sunayensa Kyawawa da Sifofinsa Tsarkaka
Maxaukaka, ya raya mu a kan wannan aqida, ya kashe mu a kanta, ya tashe mu gobe Qiyama a
tare da masu bin ta.
Tsarki ya tabbatar maka, ya Ubangiji, tare da godiya a gare ka. Ina shaidawa babu abin
baitawa da gaskiya sai kai. Ina neman gafararka, ina tuba zuwa gare ka.