Labarai




Tauhidi


Haqqin Allah A Kan Bayinsa


Umar Labxo


Manzu (SAW) ya ce


“Ya Mu’azu, shin ko ka san haqqin Allah a kan bayinsa? Mu’azu ya ce: Allah da Manzonsa


ne mafi sani. Manzo (SAW) ya ce: Haqqinsa shi ne su bauta masa shi kaxai, kada su haxa shi


da kome a wajen bauta. Sa’an nan ya ce: Shin ko ka san haqqinsu a kan Ubangiji? Mu’azu ya


ce: Allah da Manzo ne mafi sani. Ya ce: Kada ya yi musu azaba idan sun kaxaita shi da


bauta.”


(Bukhari da Muslim)


3


بسم الله الرحمن الرحيم


Gabatarwa


Lallai godiya ta tabbata ga Allah, muna gode masa, muna neman taimakonsa, muna neman gafara tasa. Muna


neman tsari da Allah daga sharrin kawunanmu da miyagun ayyukanmu. Wanda Allah ya shirye shi, babu mai vatar


da shi kuma wanda ya vatar babu mai shiriya tasa. Ina shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai,


ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa Muhammad bawansa ne, kuma Ma’aikinsa ne. Tsira da aminci su


tabbata a gare shi, da Alayensa, da Sahabbansa, da waxanda suka bi Sunnarsa har zuwa ranar sakamako.


Bayan haka, babu shakka sanin ilmin Tauhidi shi ne wajibi na farko, kuma mafi muhimmanci a kan bawa


mukallafi, kamar yadda Allah Maxaukaki ya ce, “Saboda haka ka sani cewa babu abin bautawa face Allah.” (Suratu


Mahammad: 19). Sanin cewa babu abin bautawa sai Allah, wanda shi ne sanin Tauhidi, yana gaba da sanin sallah da


zakka da azumi da hajji da dukkan ibadojin Musulunci da shari’o’insa, da dokokinsa da tsare-tsarensa. Domin


Tauhidi shi ne ruhin Musulunci kuma shi ne harsashe wanda ake aza ginin addini a kansa. Ibada, kome kyawunta da


yawanta da ingancinta, idan ba’a xora ta a kan ingantaccen harsashe na Tauhidi ba, to kamar jiki ne ba rai ko kuma


ginin da ba harsashe. Wannan ya sa malamai magabata suke buxe littafansu da bayanin Tauhidi, kamar yadda malam


mai Ahlari ya yi, inda yake cewa a farkon littafinsa, “Auwalu ma yajibu alal mukallafi tas’hihu imanihi,” ma’ana:


“Farkon abinda yake wajaba a kan mukallafi shi ne inganta imaninsa.” Hanya guda ta inganta imani kuwa ita ce sanin


ilmin Tauhidi.


Wannan littafi da nake gabatarwa a yau, wanda kuma na sanya shi ya zama cikamakin Jerin Littafan Shi’a, an


buga shi da farko a shekarar 2005 a matsayin littafi mai zaman kansa. Amma na ga ya dace in sanya shi a cikin


wannan Jerin saboda ya zama qarin bayani ga aqidar Ahalus Sunna wal Jama’a kuma ya zama ciko ga maudu’in


littafin da ya gabace shi a Jerin. Hakan kuma, har yau, zai dace da qa’idar tarbiyya da take cewa idan ka koya wa


mutane cewa kaza ba shi da kyau, to sai ka ba su madadinsa mai kyau, wanda zai maye masa, ya cike gurbinsa.


Tauhidi a bisa tafarkin Sunna da magabatan al’umma na qwarai shi ne madadi mafi alheri ga aqidar Shi’a.


Kuma ina so mai karatu ya sani cewa, a cikin wannan littafi nawa na bi tafarkin malaman Sunna magabata, tun


daga kan Sahabbai da Tabi’ai har zuwa ga limaman mazhabobi, Imam Malik da Shafi’i da Abu Hanifa da Ahmad


binu Hanbal, da wasunsu, na dogaro kacokan a kan Alqur’ani da Sunna wajen shimfixa mas’alolin ilmin Tauhidi.


Ban bi tafarkin Ahalul Kalami ba, ko Mutakallimuna, waxanda suke dogaro a kan Falsafa da Ilmin Manxiqi wajen


tabbatar da mas’alolin Tauhidi. Haka nan, ban bi tafarkin qungiyoyin bidi’a ba, kamar Mu’utazilawa da Jahamawa da


suransu, waxanda suke tawilin sifofin Ubangiji Mabuwayi, ko su kamanta su da sifofin talikai, ko su vata ma’anarsu,


su karkace da ita ga barin yadda Allah ya saukar da ita.


Na zavi in bi wancan tafarki na farko, kuma in kaucewa tafarkai biyu na baya, domin shi ne tafarkin Annabi


(SAW) da muminai: Sahabban Manzon Allah, da Tabi’ansu da Tabi’an Tabi’ai da waxanda suka bi su da


kyautatawa. Allah yana cewa, “Kuma wanda ya savawa Manzo daga bayan shiriya ta bayyana a gare shi, kuma ya bi


wanin hanyar muminai, za mu jivintar masa abinda ya jivinta, kuma mu qone shi da Jahannama. Kuma ta munana ta


zama makoma.” (Suratun Nisa: 115).


Sa’an nan na kawo bayani a kan shirka, a matsayinta na kishiyar Tauhidi, domin da sanin kishiyoyi ne


haqiqanin abubuwa ke bayyana, a san su farin sani. Ga misali, idan kana so mutum ya san launin fari, sani na haqiqa,


to sai ka kawo baqi ka kara kusa da shi, sai ka ga farin ya fito fili tantarwai. Haka nan idan kana so mutum ya san


ma’anar dogo, to sai ka jera dogo da gajere, a sannan sai tsawon dogo ya bayyan.


Wannan ya sa ya zama larura cewa, a wajen darasun Tauhidi to dole kuma a yi darasun shirka domin sanin


Tauhidi ba ya cika sai da fahimtar shirka, kamar yadda imani da Allah ba ya kammala sai an kafirce da waninsa.


Wannan shi ne ma’anar La ilaha illallahu: Babu abin bautawa (da gaskiya) sai Allah. Wannan kalma ta haxa


abubuwa biyu: imani da Allah da kuma kafircewa da waninsa. Ta kore dukkan abin bauta wanin Allah, kuma ta


tabbatar da uluhiyya gare shi, shi kaxai.


Don haka Ubangiji Maxaukaki yake gwama ambaton abubuwan guda biyu a cikin Alqur’ani, kamar inda yake


cewa, “Kuma lalle ne, haqiqa, mun aika a cikin ko wace al’umma da wani manzo (ya ce): Ku bautawa Allah, kuma


ku nisanci xagutu.” (Suratun Nahl: 36). Sai ya gwama ambaton bautar Allah da nesantar xagutu, kamar yadda ya faxi


a wata ayar, “Kuma waxanda suka nisanci shaixannu ga bauta musu, kuma suka mai da al’amari ga Allah, suna da


bushara. To, ka bayar da bushara ga bayina.” (Suratuz Zumar: 17). A nan ma, sai ya gwama bautar aljannu da


komawa ga Allah, wanda yake nufin shirka da Tauhidi.


Saboda haka sanin shirka shi ma wajibi ne a kan Musulmi domin ya kauce mata. Rashin sanin ta ne ya sa da


yawa daga cikin Musulmi suke afkawa cikin ta, kamar yadda Allah Maxaukaki yake cewa, “Kuma mafi yawansu ba


5


su yin imani da Allah face kuma suna masu shirki.” (Suratu Yusuf: 106). Kuma duk mai hankali zai ga haka qarara a


wannan zamani namu, zamanin da ake ALLANTAR DA SHAIHUNNAI, ana bautar GUMAKAN IMAMAI.


A qarshe ina roqon Allah Maxaukaki da ya amfani Musulmi da wannan littafi, da sauran littafan dake cikin


wannan Jeri, ya rubuta min ladansu, kuma ya sanya su gare ni sadaka mai gudanawa a bayan raina. Allah shi ne abin


roqo.


Babi Na Xaya


Tauhidi


Wannan babi zai qunshi bayani a kan ma’anar Tauhidi, muhimmancinsa, falalarsa da kuma wasu daga cikin


fa’idojinsa. Haka nan, zai yi bayani taqaitacce dangane da maqiyan Tauhidi.


Ma’anar Tauhidi


Ma’anar Tauhidi a luga shi ne kaxaitawa. A ilmance, kalamar tana nufin kaxaita Allah Maxaukaki, ko kuma


qudure kaxaitakarsa a zatinsa da sunayensa da sifofinsa da ayyukansa. Watau mutum ya qudure a zuciyarsa cewa,


Allah xaya ne a zatinsa, watau babu wani abin bauta, ko kuma ubangiji, da ya cancanci bauta sai shi, xaya ne a


sunayensa, watau babu wani wanda ke da sunaye irin nasa, ko za’a kira shi takwaransa; xaya ne a cikin sifofinsa,


watau babu wani dake da sifofi irin nasa; kuma xaya ne a ayyukansa, watau babu wani dake iya aiki irin nasa.


Wannan yana nufin tsarkake Ubangiji daga kini, ko sa’a, ko sako, ko mai kama, ko kuma ko wane irin wani


wanda zai yi tarayya da shi a cikin zatinsa, ko allantakarsa, ko sunayensa, ko sifofinsa ko ayyukansa. Allah xaya ne,


shi kaxai yake, makaxaici ne shi ta ko wace fuska: ta zafinsa da haqiqaninsa; ta sunayensa da kyawunsu da tsarkinsu


da xaukakarsu; ta sifofinsa da kyawnsu da tsarkinsu da xaukakarsu da kevantarsu; ta ayyukansa da kyawunsu da


cikarsu da tsarinsu da hikimarsu da ban mamakinsu. Allah xaya yake ta ko wace fuska. Shi ne xaya, mara, guda, tilo.


“Ka ce: Shi ne Allah Makaxaici. Allah wanda ake nufin sa da bukata. Bei haifaa ba, kuma ba’a haife shi ba. Kuma


babu xaya da ya kasance tamka a gare shi.” (Suratul Ikhlasi: 1- 4).


Muhimmancin Tauhidi


Tauhidi shi ne qashin bayan Musulunci kuma shi ne harsashe wanda ake gina shigifar addini a kansa.


Muhimmancinsa yana bayyana daga waxannan abubuwa:


1. An halicci halitta domin kaxaita Allah, kamar yadda yake cewa, “Kuma ban halitta aljannu da mutane ba sai domin


su bauta mini.” (Suratudh Dhariyat: 56). Watau su kaxaita ni da bauta.


7


2. Kira zuwa ga Tauhidi shi ne aikin dukkan annabawa. Allah Maxaukaki ya ce, “Kuma ba mu aiki wani manzo ba a


gabaninka face muna yin wahayi zuwa gare shi, cewa: Lalle ne shi, babu abin bautawa face ni, sai ku bauta mini.”


(Suratul Anbiya: 25). Kuma ya ce, “Kuma lalle ne, haqiqa, mun aika a cikin ko wace al’umma da wani manzo (ya


ce): Ku bautawa Allah, kuma ku nisanci xagutu.” (Suratun Nahl: 36).


Har yau, yana cewa: “Kuma zuwa ga Adawa, (muka aike) xan uwansu Hudu, ya ce: Ya mutanena ku bautawa


Allah; ba ku da wani abin bautawa face shi.” (Suratul A’araf: 65; da Suratu Hud: 50). Kuma ya ce, “Kuma zuwa ga


Samudawa xan uwansu Salihu, ya ce: Ya mutanena, ku bautawa Allah ba ku da wani abin bautawa face shi.”


(Suratul A’araf: 73; da Suratu Hud: 61). Kuma ya ce, “Kuma zuwa Madyana xan uwansu Shu’aibu, ya ce: Ya


mutanena, ku bautawa Allah; ba ku da wani abin bautawa face shi.” (Suratu Hud: 84; da Suratul A’araf: 85).


Waxannan ayoyi guda takwas, da wasu da yawa masu kama da su, suna nuna cewa kira zuwa ga Tauhidi shi ne


aikin dukkan annabawa da manzanni.


3. Tauhidi shi ne na farko; kome yana biyowa bayansa. Wannan ya sa Annabi Muhammad (SAW) ya zauna shekara


goma sha uku a Makka ba ya kome sai kira zuwa ga Tauhidi kawai. Sauran al’amuran Musulunci kaf, wanda ya haxa


da shika- shikansa, da shari‘o’insa, da hukunce-hukuncensa, da kyawawan halayensa, da ladubbansa, waxannan duka


Manzon Allah (SAW) ya koyar da su a shekara goma da ya rayu a Madina. Idan aka duba tsawon lokaci ana iya


ganin cewa Tauhidi, shi kaxai, ya xauki sama da rabi na lokacin da Annabi ya xauka yana iyar da aiken Ubangijinsa.


Kuma Manzo (SAW) ya kasance yana sanar da Sahabbansa cewa idan za su kira mutane zuwa Musuluci, to


Tauhidi ya zama farkon abinda za su yi kira zuwa gare shi. An ruwaito cewa, lokacin da ya aike Mu’azu binu Jabal


(R.A) zuwa qasar Yaman domin ya kira su ga Musulunci, ya yi masa wasiya kamar haka: “Lallai kai za ka samu


wasu mutane ma’abota littafi (Yahudu ko Nasara),to ya zama farkon abinda za ka fara kiran su zuwa gare shi cewa su


kaxaita Allah Maxaukaki. Idan sun karvi wannan, to ka faxa musa cewa Allah ya farlanta a kansu sallah guda biyar a


cikin wuni da dare. Idan suka karva, to ka ba su labari cewa Allah ya farlanta a kansu zakkar dukiyoyinsu wacce za’a


karva daga mawadatansu a maida ga matalautansu.”1


Duka wannan yana nuna muhimmancin Tauhidi.


1 Bukhari da Muslim


Falalar Tauhidi


Tauhidi yana da falala mai yawa wacce take nuna xaukakar darajarsa a Musulunci. Za mu ambata kaxan gada


cikinsu.


1. Tauhidi shiriya ne a duniya kuma aminci ne daga wuta a lahira. Kamar yadda Allah Maxaukaki ya ce, “Waxanda


suka yi imani, kuma ba su gauraya imaninsu da zalunci ba (watau shirka), waxan nan suna da aminci, kuma su ne


shiryayyu.” (Suratul An’am: 82).


2. Tauhidi shi ne qololuwar imani, kamar yadda Manzo (SAW) ya ce, “Imani kashi sittin da shida ne. Mafi


xaukakarsa faxin Babu abin bautawa sai Allah, kuma mafi qarantarsa shi ne gusar da cuta daga hanya.”1


3. Tauhidi sanadin kankare zunubai ne. A cikin hadisi qudusi, Allah mai girma da xaukaka yana cewa, “Ya xan


Adam. Da za ka zo min da gwargwadon cikin qasa na zunubi, amma kuma ba ka haxa kome da ni wajen bauta, da


na zo maka da gwargwadon cikinta na gafara.”2


4. Tauhidi sanadin shiga Aljanna ne, ko ba aiki. Manzon Allah (SAW) ya ce, “Wanda ya mutu ba ya haxa Allah da


kome (wajen bauta), zai shiga Aljanna. Wanda ya mutu yana haxa Allah da wani abu zai shiga wuta.”3 A wani


hadisin, ya ce, “Wanda ya shaida babu abin bautawa sai Allah, shi qaxai ba shi da abokin tarayya, kuma Muhammad


bawansa ne kuma Manzonsa ne. Kuma (ya shaida) cewa Isa bawan Allah ne kuma Manzonsa ne, kuma kalmarsa ce


da ya jefa ta ga Maryamu, kuma ruhu ne daga gare shi. Kuma (ya shaida) cewa Aljanna gaskiya ce, kuma wuta


gaskiya ce, Allah zai shigar da shi Aljanna ko mene ne aikinsa.”4


Fa’idojin Tauhidi


Tauhidi yana da fa’idoji masu yawa ga wanda Allah ya arzuta shi da qudure shi. Daga cikinsu:


1. Tauhidi ‘yanci ne ga mutum, yana ‘yanta shi daga bautar kowa da kome sai Allah, shi kaxai; yana ‘yanta


hankalinsa daga tasirin camfe-camfe da almara da tsoron abinda bai cancnta a tsorace shi ba, kamar aljnnu da


shaixanu da masu ta’ammali da su; yana ‘yanta lamirinsa daga qasqanta da saduda da miqa wuya ga wanin Allah;


kuma yana ‘yanta rayuwarsa daga danniyar Fir’aunawa masu mulkin zalunci, da horewar dujalan malamai masu


1 Muslim.


2 Duba Sunan na Tirmizi.


3 A duba Sahih Muslim.


4 Bukhari da Muslim.


9


vatar da mutane, da bokaye da ‘yan tsibbu masu cin gumin bayi bisa qarya, da duk wasu qananan shaixanu


taqadarai.


2. Tauhidi yana gina mutum kamili, natsatsse, mai gaba gaxi a rayuwa, saboda abin bautarsa guda: Allah, abin


koyinsa guda: Annabi (SAW), abin biyarsa guda: Alqur’arani, burinsa guda: samun yardar Ubangiji. Bai rarraba


kansa tsakanin iyayen giji dabam-daban ba, balle ya ruxe, ko ya rasa alqibla. Kirarinsa a koda yaushe abinda Annabi


Yusuf ya ce, “Ya abokaina biyu na kurkuku! Shin iyayen giji dabam-daban ne mafiya alheri ko kuwa Allah


Makaxaici, mai tarnqwasawa?” (Suratu Yusuf: 39).


3. Tauhidi yana ba da qarfin hali saboda cika ran mai shi da kyakkyawar fata daga Allah, da amin- cewa da shi, da


dogaro a kansa, da yarda da hukuncinsa, da haquri a kan jarrabawarsa, da wadatuwa ga barin waninsa. Sai mutum ya


zama tamakar dutse, a faxa masa a yi rauni, balle idan shi ya faxa!


4. Tauhidi harsashen ‘yan uwantaka ne da daidaito tsakanin mutane da haxin kai. Tauhidi bai barin mutane sashensu


ya xauki sashe a matsayin iyayen giji koma bayan Allah; a qarqashin inuwar Tauhidi mutane duka dai-dai suke,


dukkaninsu bayi ne na Ubangiji guda, babu wanda ke da fifiko a kan xan uwansa sai da tsoron Allah kawai.


Maqiyan Tauhidi


Kalmar La ilaha illallahu shelar tawaye ce ga duk wani xan wasan kwaikwayo mai kambi, ko rawani, ko hular


kwano; da duk wata karagar qarya, da tsarin zalunci ko hanyar makirci. “La” xin nan yatsan kashedi ne a fuskar duk


wani azzalumi, ko jabberi, ko dujali, ko taqadari, wanda yake nufin bautar da bayin Allah, ko danne su, ko wulaqanta


su, ko vatar da su. Wannan ya sa azzalumai da masu girman kai ba su gushe ba suna faxa da masu wannan kalma tun


ran da Muhammadu Manzon Allah ya xaga ta a fuskar Lata da Uzza, da Abu Jahil da Abu Lahabi har ya zuwa yau.


Daga cikin masu gaba da Tauhidi a wannan zamani akwai:


1. Kafirai daga dukkan nau’o’in kafirci da tafarkansa, kamar Mulhidai da Zindiqai da Mushrikai da Yahudu da


Nasara da sauransu.


2. Azzaluman sarakai da masu mulki waxanda suke xauke da sunan Musulunci amma suna qin sa. Da munafukai,


almajiran Yahudu, waxanda suke amsa sunan Musulmi amma suna yi wa Musulunci zagon qasa.


3. Miyagun malamai ‘yan bidi’a, da dujalai waxanda suka xauki addini a matsayin hanyar gina duniya, da gina


gidajensu na gado, da hore mutane domin cin guminsu a bisa zalunci, da vatar da bayin Allah.


Babi Na Biyu


Rabe-raben Tauhidi


Wannan babi zai yi bayanin rabuwar Tauhidi zuwa kashi uku, tare da bayyana waxannan kaso filla-filla. Sa’an


nan zai yi bayani a kan sunayen Allah kyawawa da sifofinsa tsarkaka kuma ya fayyace tafarkin Sunna dangane da


wannan.


Tauhidi ya kasu gida uku: Tauhidin rububiyya, Tauhidin uluhiyya, Tauhidin sunaye da sifofi. Ga bayaninsu


dalla-dalla.


Tauhidin Rububiyya


Tauhidi Rububiyya shi ne mutum ya qudure cewa Allah shi kaxai, shi ne Rabbu. Ma’anar Rabbu a Larabci shi


ne mahalicci kuma mai kulawa da halittar. A Hausa ana fassara wannan kalma da Ubangiji. Rabbu shi ne mai halittar


halittu kuma ya ba su duk abinda suke bukata na ji da gani, qarfi da lafiya, ci da sha, xaukaka da wadata, da sauransu.


Kuma har wa yau, shi ne, idan ya so, yake karve waxan nan abubuwan. Don haka, Rabbu shi ne mai rayawa mai


kashewa, mai xaukakawa mai qaskantawa, mai bayarwa mai hanawa, kamar yadda Allah Maxaukaki yake cewa,


“(Shi ne) Ubangijin sammai da qasa da abinda ke a tsakaninsu, idan kun kasance masu yaqini (za ku gane haka).


Babu abin bautawa face shi. Yana rayawa kuma yana kashewa. (Shi ne) Ubangijin ku, kuma Ubangijin ubanninku na


farko.” (Suratud Dukhan: 7-8).


Kaxaita Allah da rububiyya, watau qudure cewa shi kaxai shi ne ya halicci halittu manya da qanana: sammai da


qasa; rana da wata da taurari; koguna da duwatsu; mutane da aljannu da dabbobi da qwari; tare da qudure cewa shi


kaxai yake da tasarrufi da su, watau shi ke yin yadda ya ga dama da su da ikonsa da qarfinsa. Wannan shi ne


haqiqanin Tauhidin rububiyya. Kuma wannan nau’i na Tauhidi ko mushirikai ba sa ja a kan sa; domin sun san ba


gumakansu ne suka halicci halittu ba, kuma ba su ke sarrafa halittu ba. Wannan ya sa suke iqirari da Tauhidin


rububiyya, kamar yadda Allah ya ba da labarinsu a cikin littafinsa mai girma: “Lalle idan ka tambaye su: wane ne ya


halitta sammai da qasa kuma ya hore rana da wata? Lalle suna cewa: Allah ne. To, yaya ake karkatar da su?” (Suratul


Ankabut: 61). A wata ayar ya ce, “Kuma lalle idan ka tambaye su: Wane ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya


rayar da qasa game da shi a bayan mutuwarta? Lalle suna cewa: Allah ne.” (Suratul Ankabut 63). Har yau, a wata


ayar ya ce, “Kuma lalle idan ka tambeye su: Wane ne ya halitta su? Lalle ne za su ce: Allah ne. To, yaya ake juyarda


su? “ (Suratuz Zukhruf: 87).


11


Daga nan za mu fahimci cewa irin wannan Tauhidi na rububiyya Musulmi da mushirikai sun yi tarayya a kansa.


Har da mushiriakan zamanin Jahiliyya, waxanda aka aike Annabi (SAW) zuwa gare su, ba sa musun sa. Amma


kuma qudure wannan nau’i na Tauhidi shi kaxai bai hana a kira su mushirikai ba. Wannan yana nunawa a fili cewa


qudure nau’i guda na Tauhidi bai isarwa; dole sai an haxa da sauran nau’i biyun: Tauhidin uluhiyya da Tauhidin


sunaye da sifofi.


Tauhidin Uluhiyya


Tauhidin uluhiyya shi ne mutum ya qudure cewa Allah, shi kaxai, shi ne Ilahu. Ma’anar Ilahu a Larabci shi ne


abin bauta, ko kuma wanda ya cancanci a bauta masa. Allah, shi kaxai, shi ya cancanci a bauta masa; shi ne abin


bauta na gaskiya, wanda ake bautawa da cancanta, kuma ba shi da abokin ta rayya a cikin uluhiyyarsa.


Tauhidin uluhiyya ana gina shi a kan Tauhidin rububiyya: watau tunda Allah, shi kaxai, shi ne rabbu wanda ya


halicci halitta kuma yake kulawa da ita, to tabbas shi kaxai shi ya cancanci ya zama ilahu, watau abin bauta na


gaskiya. Wanda ya halicci halitta shi ya kamata halittu su bauta masa; shi ke da haqqin a bauta masa. Idan da halitta


za su bautawa waninsa, to da sun yi zalunci, domin sun xauki haqqinsa sun baiwa wani wanda bai cancance shi ba.


Wannan ya sa ake kiran shirka zalunci kamar yadda Allah Maxaukaki yake cewa, “Kuma a lokacin da Luquman ya


ce wa xansa, alhali kuwa yana yi masa wa’azi: Ya qaramin xana! Kada ka yi shirka game da Allah. Lalle shirki wani


zalunci ne mai girma.” (Suratu Luqman: 13).


Dangane da Tauhidin uluhiyya, Allah yana faxi a cikin littafinsa mai tsarki, “Kuma abin bauta- warku abin


bauta ne guda. Babu wani abin bauta face shi, mai rahama mai jin qai.” (Suratul Baqara: 163). Kuma yana cewa,


“Shi ne Allah wanda babu abin bautawa face shi, mai mulki, mai tsarki, Aminci, mai amintarwa, mai tsarewa,


mabuwayi, mai tilastawa, mai kamun kai. Tsarki ya tabbata a gare shi daga abinda suke yi na shirki da shi.” (Suratul


Hashr: 23). Har yau, yana faxin, “Lalle ni, ni ne Allah. Babu abin bautawa face ni. Sai ka bauta mini kuma ka tsayar


da sallah domin tuna ni.” (Suratu X.H: 14).


Har ila yau, yana cikin Tauhidin uluhiyya kaxaita Allah da haqqin umarni da hani, da halattawa da haramtawa,


da sanya shari’a, da aza doka, da tsara rayuwa. Duka wannan haqqinsa ne a matsayinsa na rabbu. Tunda shi kaxai shi


ya halicci halitta, to, shi kaxai shi yake da haqqin da zai umarce su ko ya hana su; shi ka latta musa ko ya haramta


musu; kuma shi kaxai yake da haqqin ya tsara musu rayuwarsu (domin shi ya ba su rayuwar) kuma su bi tsarinas sau


da qafa.


Haka kuma yana cikin Tauhidin uluhiyya kaxaita Allah da dukkan nau’o’in ibada da launukanta. Ibada tana da


nau’i huxu:


1. Ibadar zuciya, kamar son Allah da tsoronsa da dogaro a gare shi da girmama shi da fatar rahamarsa, da


sauransu.


2. Ibadar harshe, kamar zikiri da yabon Allah da gode masa da tsarkake shi da yi masa kirari da neman gafararsa


(istigfari) da roqon sa (addu’a) da neman tsanantuwa gare shi (tawassuli) da neman tanyonsa (istigasa), da


abinda ya yi kama da haka.


3. Ibadar gavovi, kamar sallah da azumi da xawafi da jihadi.


4. Ibadar dukiya, kamar zakka da sadaka da ciyarwa, da sauransu.


Duka waxannan nau’o’i huxu na ibada haqqin Allah ne shi xaya, bai halasta a fuskantar da wani abu daga cikinsu


zuwa ga waninsu.


Tauhidin Sunaye da Sifofi


Watau sunayen Allah da sifofinsa. Ma’anarsa shi ne mutum ya yi ban gaskiya da dukkan sunayen da Allah


Maxaukaki ya kira kansa da su a cikin Alqur’ani mai girma, ko Annabinsa (SAW) ya kira shi da su a cikin hadisai


ingatattu. Haka nan kuma ya yi ban gaskiya da dukkan sifofin da Allah ya sifanta kansa da su a cikin Alqur’ani mai


girma, ko Annabinsa (SAW) ya sifanta shi da su a cikin hadisai ingatattu. Musulmi zai kaxaita Allah da waxannan


sunaye da sifofi, ya kavance shi da su, ba zai haxa shi tarayya da kowa ba a cikinsu. Haka nan kuma zai yi imani da


su kamar yadda suke, watau kamar yadda Allah ya saukar da su, ko Manzon Allah (SAW) ya bayyana su, ba tare da


ya yi musu tawili ba, ko ya vata ma’anarsu, ko ya kamanta su da sifofin talikai, ko ya ce ga takamaimai yadda suke.


Bari mu ba da misali a nan da wani abu da mutane da yawa suke yin kure a kansa, shi ne baiwa talikai wata sifa


daga cikin sifofin Allah Maxaukaki. Alimul Gaibi, watau Masanin Gaibu, sifa ce daga sifofin Allah waxanda ya


kevanta da su, amma da yawa za ka ji wasu na danganta wannan sifa ga Annabi (SAW), sai su ce Annabi ya san


gaibu! To ka ga wannan shirkar sifa ce; domin sanin gaibu sifa ce ta Allah wacce ba mai tarayya da shi a cikinta,


kamar yadda yake cewa, “Ka ce: Babu wanda ya san gaibi a cikin sammai da qasa face Allah.” (Suratun Naml: 65).


Sunayen Allah


13


Allah Maxaukaki yana da sunaye kyawawa waxanda ya yi umarni a roqe shi da su. “Kuma Allah yana da


sunaye masu kyau, sai ku roqe shi da su.” (Suratul A’araf: 180). Waxannan sunaye suna da yawa ainun; wasu


ambaton su ya zo a cikin Alqur’ani, wasu a cikin hadisai. Misali, faxin Allah mai girma da xaukaka: “Shi ne Allah


wanda babu abin bautawa face shi, Mai mulki (Almalik), Mai tsarki (Alquddus) Aminci (Assalam), Mai amintarwa


(Almu’min), Mai tsarewa (Almuhaimin), Mabuwayi (Ai’aziz), Mai tilastawa (Aljabbar), Mai kamun kai


(Almutakabbir). Tsarki ya takkata a gare shi daga abinda suke yi na shirki da shi. Shi ne Allah Mai halitta (Alkhaliq),


Mai ginawa (Albari’u), Mai surantawa (Almusauwiru). Yana da sunaye masu kyau, abinda ke a cikin sammai da qasa


suna tsarkake shi, kuma shi ne Mabuwayi (Al’aziz), Mai hikima (Alhakim).” (Suratul Hashr: 23-24). Waxannan


sunaye na Allah duka xaya suke; ko wane ana kiran sa da shi, kuma ana roqon sa da shi. “Ka ce: Ku kirayi Allah ko


kuwa ku kirayi Mai rahama (Arrahman). Ko wane kuka kira, to, yana da sunaye mafi kyau.” (Suratul Isra: 110).


Amma dangane da takamaiman adadin sunayen Allah, to babu wanda ya san wannan sai shi, Makaxaici. Akwai


sunayensa kyawawa xari ba xaya, watau tis’in da tara, waxanda suka taho baki xaya a cikin hadisi. Waxannan su


suka fi shahara, amma ba suke nan ba. Sunayen Allah sai shi ya san adadinsu. Akwai waxanda ya saukar a cikin wasu


littafansa waxanda ba mu sani ba, akwai waxanda ya sanar da wasu bayi nasa musamman, akwai kuma waxanda ya


kevanta da sanin su a cikin ilminsa na gaibu bai sanar da su ba ga kowa, kamar yadda wannan hadisi yake nunawa:


Ya kasance daga cikin addu’ar Annabi (SAW) yana cewa, “Ina roqon ka, ya Ubangiji, da dukkan suna wanda yake


naka ne ka kirayi kanka da shi, ko ka saukar da shi a cikin littafanka, ko ka sanar da shi xaya daga cikin halittarka, ko


ka kevanta da shi a cikin ilmin gaibu a wurinka: ka sanya Alqur’ani mai girma ya zama rayuwar zuciyata da hasken


qirjina da yayewar baqin cikina, da tafiyar damuwata da vacin raina.” (Musnad na Imam Ahmad).


Saboda haka, kewayewa da sunayen Allah, watau sanin su dukkaninsu, ya fi qarfin halitta: annabawa da


mala’iku da sauran mutane da aljannu. Abinda yake kan talikai shi ne su yi imani a warware da sunye waxanda


Allah ya sanar da su, waxanda bai sanar da su ba kuwa su yi imani da su a dunqule, kamar yadda suke a sanin Allah


Makaxaici.


Sifofin Allah


Allah mai girma da xaukaka ya sifanta kansa da wasu sifofi da ayyuka a cikin Alqur’ani mai tsarki kuma


Annabinsa (SAW) ya sifanta shi da wasu a cikin hadisai ingatattu. Misalin waxannan sifofi shi ne kamar


kasancewarsa yana zance, yana so, yana qi, yana dariya, ya daidaita a bisa al’arshi, ya zo, yana saukowa zuwa saman


duniya, da sauransu. Wajibi ne a kan ko wane Musulmi ya yi ban gaskiya da wxannan sifofi saboda zuwansu cikin


Alqur’ani da hadisai ingatattu, kuma ya qaxaita Allah da su, kada ya haxa shi tarayya da wani a cikinsu.


Magabatan wannan al’umma, watau Sahabban Annabi (SAW) da Tabi’ansu, suna da qa’ida da suka ajiye, (ko


kuma a ce suka karvo ta daga Annabi, domin ba su yin gaban kansu a sha’anin Tauhidi), ta fahimtar waxannan sifofi.


Qa’idar ita ce a fahimci ma’anarsu kamar yadda take a lugar Larabci, ba tare da yin tawili ba. Misali, idan ake ce


“yadul Lahi,” sai a fassara shi da “hannun Allah,” kada a ce qudurar Allah ko ikonsa. Haka nan idan a ka ce “wa ja’a


rabbuka,” sai a fassara shi: “Kuma Ubangijinka ya zo,” kada a ce ikonsa ya zo. Amma kuma ba’a kamanta sifofin


Allah da sifofin talikai, kuma ba’a cewa ga takamaimansu. Misali, hannun Allah ba’a kamanta shi da hannun


mutane,ko na wata halitta dabam. Haka nan, “Ubangijinka ya zo” ba’a cewa takamaimai ga yadda ya zo, ko kuma ga


yadda zuwansa yake.


Watau ke nan wannan qa’ida ta qunshi abubuwa guda uku:


1. A fahimci sifar kamar yadda take a Larabcinta; kada a yi tawili ko ta’axili. Tawili shi ne kau da ma’ana daga


asalinta zuwa wani abu daban, kamar hannu a ce ma’anarsa iko ko qudura. Ta’axili kuwa shi ne kore ma’ana da vata


ta, ta yadda zai zama babu ta sam.


2. Kada a kamanta sifar da sifofin talikai, domin Allah “Wani abu bai zama kamar tamkarsa ba.” (Suratush Shura:


11). Don haka idan Allah ya ce yana da hannun, to dole ne mu yi imani cewa yana da hannun, domin shi ya faxi.


Cewa ba hannu yake nufi ba, qarfi yake nufi, ko iko ko qudura, wannan karambani ne kawai. Amma kuma dole mu


yi imani cewa hannunsa ba ya kama da hannun ko wace irin halitta; domin mun san babu abinda yake kama da shi.


In da wani zai yi tambaya: To ya hannun yake ke nan? Sai mu ce masa: Allah ne Masani!


3. Kada a ce ga takamaiman sifar yadda take, ko kuma ga haqiqaninta. Domin Allah, shi kaxai, shi ya san


haqiqaninta. Don haka, idan Allah ya ce, “Ubangijinka ya zo.” Sai mu yi imani cewa Allah ya zo; domin shi ya faxi.


Amma dole ne mu yi imani cewa zuwansa ya sha bamban da zuwan ko wane mai zuwa; domin shi Allah Maxaukaki


babu mai kama da shi a cikin zatinsa ko sunayensa ko fifofinsa ko ayyukansa. Kuma ba mu cewa ga takamaimai


yadda ya zo, wannan shi ya barwa kansa sani.


Wannan ita ce qaidar fahimtar sifofin Allah, sai a riqe ta hannu biyu-biyu. Kuma shi ne tafarkin magabata,


Sahabbai da Tabi’ai da Tabi’an Tabi’a,i da imaman mazhabobi guda huxu, kamar yadda za mu gani a nan gaba, in


Allah ya yarda.


15


Misalai daga Alqur’ani


Saboda muhimmancin wannan gava ta Tauhidi, za mu kowo misalai daga Alqur’ani da hadisan Annabi (SAW).


1. Hannun Allah. Ubangiji Makaxaici ya ce, “Lalle waxanda ke yi maka mubaya’a, Allah kawai ne suke yi wa


mubaya’a, hannun Allah na bisa hannayensu.” (Suratul Fathi:10).


2. Hannayen Allah biyu. “(Allah) ya ce: Ya Iblis! Me ya hana ka ka yi sujada ga abinda na halitta da hannayena


biyu?” (Suratu Sad: 75).


3. zuwan Ubangiji. “Kuma Ubangijiinka ya zo, alhali mala’iku suna jere safu-safu.” (Suratul Fajr: 22).


4. Maganar Allah ga wasu manzanni. “Waxannan manzannin mun fifita sashensu a kan sashe: daga cikinsu akwai


wanda Allah ya yi masa magana.” ( Suratul Baqara: 253).


5. Maganar Allah ga Annabi Musa. “Kuma Allah ya yi magana da Musa, magana sosai.” (Suratun Nisa: 164). “Kuma


a lokacin da Musa ya je ga miqatinmu, kuma Ubangijinsa ya yi masa magana.” (Suratul A’araf:143).


6. Daidaitar Ubangiji a bisa al’arshinsa. “Mai rahama ya daidaita a kan Al’arshi.” (X.H.: 5). “Allah shi ne wanda ya


xaukaka sammai ba da ginshiqai ba waxanda kuke ganinsu. Sa’an nan kuma ya daidaita a kan Al’arshi.” (Suratur


Ra’ad: 2).


Misalai daga Sunna


Akwai misalai masu yawa na irin waxannan sifofi a cikin hadisan Annabi (SAW) ingatattu. A nan za mu kawo


kaxan ne kawai.


1. Manzo (SAW) ya ce, “Allah yana dariya zuwa mutane biyu, xayansu zai karhe xayan amma kuma dukkansu za su


shiga aljanna.”1 Daga qarashen hadisin ana fahimta cewa wanda ya yi kisan kafiri ne ya kashe Musulmi sai ya yi


shahada, daga baya shi kuma kafirin ya musulunta sai musuluncinsa ya shafe duk abinda ya aikata kafin ya


musulunta, shi ma Allah ya sa shi a aljanna.


2. Annabi (SAW) ya ce, “Ubangijinmu yana saukowa zuwa sama ta duniya a ko wane dare, lokacin da sulusin dare


na qarshe ya rage. Sai ya ce: Wa zai kira ni in amsa masa? Wa zai roqe in in ba shi? Wa zai nemi gafarata in gafarta


masa?”2


1 Bukhari da Muslim.


2 Shi ma wannan hadisi yana cikin Bukhari da Muslim.


3. Ma’aiki (SAW) ya tambayi wata baiwa: “Ina Allah yake?” Ta ce, “Yana sama.” Sai ya ce, “Ni wane ne?’’ Ta ce,


“Kai Ma’aikin Allah ne. ” Sai ya ce (da ubangijin baiwar): “’Yanta ta; lalle ita mumina ce.”1


Dangane da ma’anar wannan hadisi, Imam Alzahabi yana cewa, “A cikin hadisin baiwa akwai mas’aloli guda


biyu. Ta xaya, halaccin Musulmi ya ce: Ina Allah yake? Ta biyu, faxin wanda aka tambaya: Yana sama. Wanda duk


ya yi musun waxannan mas’aloli, to ya yi wa Annabi (SAW) musu.”


4. Ma’aiki (SAW) ya ce, “Allah zai damqe qasa ranar Alqiyama kuma ya naxe sama da (hannun) damansa. Sa’an


nan ya ce: Ni ne Sarki, ina sarakunan qasa?”2


UbangijiYanaSama:Ya Daidaita a Bisa Al’arshinsa


Ayoyi da hadisai masu yawa sun bayyana cewa Allah Maxaukaki yana sama, kuma ya daidaita a kan


Al’arshinsa. Don haka ya zama wajibi a kan Musulmi da ya qudure wannan kuma kada ya yi tawilin ma’anar


waxannan ayoyi da hadisai. Cewa kuwa Allah yana ko ina, wannan kure ne babba, mai haxari ga aqida, wanda ya


savawa Alqur’ani da Sunna da aqidar Sahabbai da Tabi’ai baki xayansu. Wasu malamai ma, kamar Imam Abu


Hanifa, sun ce kafirci ne.


Allah ya ambata a wurare bakwai a cikin Alqur’ani mai girma cewa ya daidaita a kan Al’arshi. Waxannan


wurare su ne, Suratul A’raf: 54; Suratu Yanus: 3; Suratur Ra’ad: 2; Suratu X.H.: 5; Suratul Fur’qan: 59; Suratus


Sajada: 4; da Suratul Hadid: 4. Kuma ita wannan daidaita xin malaman Sunna magabata sun fassara ta da cewa, “Ya


xaukaka a birbishin” ko kuma “Yana a kan”. Wannan fassara ce Imam Bukhari ya ruwaito a cikin Sahihinsa daga


Abul Aliya da Mujahid, waxanda manyan malaman Tabi’ai ne da suka xauki ilmi daga wajen Sahabbai.


Watau idan a ka ce Allah ya daidaita a kan Al’arshi, ana nufin yana birbishin sa ke nan. Kuma da yake Al’arshi


yana bisa da saman bakwai ne, to sai a ka san cewa tabbas Allah yana sama. Amma takamaimai yaya ya daidaita a


bisa Al’arshin, to wannan yana cikin abinda ya bar wa kansa sani. Saidai a yi imani cewa daidaitarsa Maxaukaki ba ta


kama da daidaitar halitta, domin zatinsa ba ya kama da zatinsu.


Banda waxannan ayoyi da suke bayyana Allah ya daidaita a kan Al’arshinsa, akwai kuma wasu ayoyin


waxanda suke nuna cewa Allah yana sama. Misali, faxin Allah Maxaukaki: “Zuwa gare shi magana mai daxi ke


hawa kuma aiki na qwarai yana xaukaka shi (zuwa gare shi).” (Suratu Faxir: 10). Da faxinsa, “Daga Allah mai


matakala. Mala’iku da Ruhu (Jibrila) suna takawa zuwa gare shi a cikin wani yini wanda gwargwadonsa shekara


1 Duba Muwadda Malik da Sahih Muslim.


2 Sahihul Bukhari.


17



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH