Labarai




addinin su da yin musulunci dole, Allah madaukaki yana cewa:


“babu tilastawa a addini hakika shiriya ta bayya daga bata” (suratul bakara ayata 256)


Jihadi domin isar da addinin Allah ga mutane bawai tilasta masu yin addinin ba, saboda fadin Allah madaukaki:


“idan sunyi imani to hakika sun shiryu idan kuma sun juya baya to naka kadai shine isarwa; kuma Allah me ganin bayin sa ne” (suratu al'imran ayata 20)


Dalili kuwa na rashin tilastawa akan shiriya zuwa ga addinin gaskiya da kuma sanin sa kyauta ce na Allah wanda Allah ya kebanta dashi ga wanda yaso cikin bayinsa hakab baya zuwa ta hanyar wajabtawa mutum ko kuwa tilastashi, saboda fadi Allah madaukaki:


“shiriyan su baya kanka sai dai Allah yana shiryar da wanda yaso” (suratul bakara ayata 272)


Baya halatta tilastawa wand aba musulmi ba cikin yahudawa ko kirista shiga musulunci idan kuma hakan ya faru to ba daidai bane, domin daga cikin sharadin shiga musulunci shine ya kasance da zabin mutum ne da kuma son sa bawai da tilastawa da yimai dole. Mutum zai iya cewa to me yasa muke ganin abubuwan masu tayar da hankali na labari akan ta'addanci akan coci a wata kasar da ake yaki, sai muce: labarin zai iya zama gaskiya ko kuma karya, da ace zamu dauka cewa gaskiya ne to masallatai nawa ne aka rusa da yin ta'addanci akan sa a cikin wannan kasa shima?!! Da za'ace akwai kiristoci da aka kashe sai muce musulmai nawa aka kashe suma anan?!! A lokacin da muke magana akan wata kasa wacce take yaki abunda yake a al'adance shine mu rika


magana akan misalin irin wannan abubuwa wanda basu da alaka da musulunci da karantarwan sa, baza'a kira wannan ba da jihadi, dalili kuwa shine dayawa mutane sunyi kaura ko kuma ankashe su kuma wuraren bauta dayawa an rusa su wanda dukkanin wannan abubuwa jihadi yana yaki dasu kuma baya yarda dasu.


Zamu gane banbanci ne tsakanin yaki da jihadi a lokacin da muka kawo wasu daga cikin yakuna wanda akayi su a tarihi daga cikin su akwai:-


• ISKANDAR BABBA: Iskandar babba yana samun girmamawa daga wurin mutanen sa da kasashen duniya baki dayan su a matsayin mutum me tasira a duniya, musamman yakuna masu yawa da akayi domin kara yawan fadin mulkin sa wanda har yakai ga iyakan Imbiradhuriyya na al igrikiyya zuwa indiya.


• JINKIZ KHAN: ya kafa babban Imbiradhuriyya a duniya wacce bayan mutuwar sa takai har zuwa ga sin da gabashin turai kamar kasar porland da makamantan su, kuma yana da mabiya dayawa a kasashe daban daban sannan kuma mutane suna matukar girmama shi a duniya.


• HITLA: ya darkake turai har saida ya hade iyakan Imbiradhuriyyar sa da kasashe da yawa ana turawa.


• IMBIRADHURIYYA NA BIRTANIYA (Imbiradhuriyya wacce ta karade ko ina): mulkin


mallakarta ya karede ko ina a duniya tun daga gabas zuwa yamma shi yasa ake mata kirani da Imbiradhuriyyar da rana yaba bace mata.


• MUSU MULKIN MALLAKA NA FARANSA DA SPAIN DA PORTUGAL DA ITALY DA JAPAN: ya karade duniya gabas zuwa yamma domin fadada shugabancin ta da ikonta.


A takaicen magana: tarayya dukkanin wannan imbiradhuriyya da dukkanin yakunan wacce tayi wanda burinta shine mamayewa arziki da kasashen duniya na daban da kuma fadada karfin fadanta aji da sshugabanci a duniya, kuma tan atarayya har wayau cikin kasancewar sakamakon shine lallata wayewa, da yankawa da bautar da mutane wacce tabar miliyoyi da tabon haka, wannan shine abunda tarihi ya tabbatar mana, Jinkiz khan wanda yana cikin jaruman da ake irgawa a kasarsa ana kalloan sa da jikan sa Hulako cikin garin da ya daidaita a matsayin me laifin yaki, ya daidaita mutane da yada barna a doron kasa da lallatata, hakika Hulako ya lallata gidan hikma da abunda ke cikinta na littattafai da rubuce rubuce na ilimi wanda ba'a iya kimantawa. Akan haka kuma domin sanin banbanci tsakanin yaki da jihadi ya wajaba mu auna tsakanin manufafi na wannan yakuna da sakamakon su da dabi'un su da kuma manufofi na jihadi da sakamon ka sa dabi'un sa! Jihadi wanda ya tsayar da wannan zalumcin ya kuma kiyaye masu addinai musulmai da wand aba musulmai ba.


Gabanin mu kawo wasu daga cikin nassoshi akan jihadi a cikin tsohon alkawari zamu kawo cikin sabon alkawari shima na maganganun Bulu wanda ya wanzar da jihadin da aka ambata cikin tsohon alkawari, kuma da yawa sun yaba akan dukkanin abunda ya aikata cikin wannan yakuna na kashe masu addini na Azli!!


BULUS YANA CEWA CIKIN SAKON SA ZUWA GA IBRANIYAWA (11/30): (30 da imani ne Aswar Ariha ya fadi bayan ya zauna cikin ta na tsawon kwanaki bakwai 31 da imani akayi maraba da zaniyawa ba'a taba hakaba tare da masu laigfi idan aka amshi amsu liken sirri da aminci 32 me kuma nake cewa har wayau domin lokaci bazai isheni ba dana bada labari akan Jada'un da Barak da shamsun da Yaftahu da Dawud da Samuel da annabawa 33 wanda suka samu galaba akan sarakuna da imani sun aikata biyya sun kuma samu alkawura sun rufe bakuna na zaki 34 sun kashe karfin wuta sun tsira daga kaifi takobi sunyi karfi daga rauni sun zama masu tsanani a yaki sun rusha rundunoni na baki)!!


Yanzu zamugani cikin tsohon alkawari abunda ya faru bayan Aswar Ariha ya fadi wanda aka ambata kuma dayawa ke yabon sa cikin sakon Bulus wanda ya gabata!!


SAFAR YUSHA'U (6/16): (16 ya kasanci a karo na bakwai a lokacin da bokaye suka duki kofuka lallai yusha'u yace ma mutane kuyi ihu domin kuma ubangiji ya baku birni. 17 birnin zai kasance da dukkanin abunda ke cikin ga harami ne ga ubangiji. Yayi maraba da zaniyata ne kawai don gaisuwa ita da dukkanin abunda ke cikinta a cikin gida domin ya boye manzannin da aka aiko su. 18


amma ku ku fitar da haramun domin a haramta kuma ku amshi haramun da sanyata a wurin bani isra'il haramun da lalatata. 19 dukkanin zinari da azurfa da kwano na copper da karfe zai kasance me tsarki ga ubangiji kuma zai shiga cikin ma'jiya na ubangiji. 20 sai mutane sukayi ihu suka duki kofuka kuma ya kasance a lokacin da mutane sukaji sautin Buka cewa mutane sunyi ihu ihu me kara sai bango ya fadi daga wurin sa sai mutane suka shiga cikin birni ko wani mutum tare da fuskar sa suka amshi wannan birni. 21 suka haramta dukkanin abunda ke cikinta na namiji da mace yaro da tsoho hatta shanaye da awakai da jakuna da da bakin takobi……24 suka kuma kona birnin da wuta da dukkanin abunda ke cikinta)


Basu tsaya ba kawai akan kisan duk wani abu me rai na maza da mata da yara hatta dabbobi a'a sai da suka kona birnin baki dayan sa da wuta!!!!!!!


SAFAR SAMUEL NA FARKO (15/3): (3 to yanzu ka tafi ka duki sarakuna kuma ka haramta dukkanin abunda suke dashi, kuma kada ka yafe masu, ka kashe namiji da mace, yaro da jariri, shanu da akuwa, rakumi da jaki)


SAFAR HUSHA'U AL ISHAH (13/16): (16 an yima samurata sakamako domin ya sabama allanta, da takobi suka fadi. Suna kashe yaran su da raba masu cikin su).


SAFAR ISHA'A AL ISHAH (13/15): (15 duk wanda ya sumu yana soke shi kuma duk wanda ya samu yana fadar dashi da takobi. 16 yan akuma kashe yaran su


agaban idon su, da kona gidan =je da wulakanta matan su).


SAFAR SAMUEL NA BIYU (4/12): (12 sai dawud ya umurci gilmana sai suka kashe su da yanke hannuwan su da kafafun su da kuma sagaleta akan taguwa na Hibrun)


SAFAR N AKABARUN KWANAKI NA FARKO (20/3): (3 sai dawud ya fitar da mutanen da ke cikinta ya yankasu da zarto da gatari da adda haka dawud ya aikata ga dukkanin mutanen dani Umun)


• Yaki da wuce gona da iri da kuma tsanani a cikin shari'ar musulunci.


• Ruhbaniyyanci a cikin kiristanci:


1. Gauranci yafi aure falala:


2. Rashin yin saki:


3. Yanke kawuna:


• Yakin tsarin bautar da mutane a musulunci.


• Tsarin bauta a cikin littafi me tsarki na yahudawa da kiristoci.


• Yaki da kabilanci a cikin musulunci:


• Halasta jin dadin duniya da kuma kwadaitarwa akan rayata a cikin musulunci.


Allah madaukaki ya aiko Muhammad manzon Allah s.a.w kuma ya saukar masa da shari'a wacce take rahama ga talikai, sai yace:


“kuma bamu aikeka ba face rahama ga talikai” (suratul anbiya'i ayata 107)


Rahama a agresu cikin dukkanin al'amuran su, rahama ga kawunan su da rayukan su wacce ta yanta su daga bautan gumakan da basa amfanar dasu kuma basa cjutar dasu suna bautama bayi irin su sai Allah ya shiryar dasu zuwa ga bautan sa shi kadai da kuma rashin yi masa shirka.


Rahama ga jikin su yadda ya haramta masu abinci da abunsha wanda zayyi sababin halakar dasu, Allah madaukaki yace:


“Kace bani samu, acikin abinda akayo wahayi zuwa gareni, abin haramtawa, akan wani maici wanda yake cin sa face idan ya kasance mushe, ko kuwa jini abin zubarwa, ko kuwa naman alade, to lallai ne shi kazanta ne, ko kuwa fasikanci wanda aka kururuta domin wanin Allah, dashi. Sa’annan wanda lalura ta kama shi, ba mai fita jama’a ba


kuma ba mai ta’addi ba, to lallai Ubangijinka Mai gafara ne , mai jin kai.” (suratul an'am ayata 145)


Kuma rahama ne ga tattalin arzikin su yadda aka haramta masu dukiyan da aka amsa bada hakki ba ko kuma aka tara da algushi da kuma cin dukiyan mutane da barna, Allah madaukaki yana cewa:


“kuma kada kuci dukiyanku a tsakanin ku da barna kuna kaiwa zuwa ga mahukunta domin kuci dukiyan mutane da barna alhali suna sane” (suratul bakara ayata 188)


Ya kuma shar'anta masu tsara abubuwan al'amuran sun a rayuwa sazu gudanu da kuma ginuwa akai kuma yayi daidai da fidira ta mutane wanda babu wuce gona da iri a cikinsa ko kuma sakaci, Allah madaukaki yace:


“ya shar'anta maku cikin addini bunda yayi ma Nuhu wasiyya dashi da abunda mukayi maka wahayi dashi da abunda mukayi wasiyya dashi ga Ibrahim da Musa da Isa; cewa ku tsayar da addini kuma kada ku rarraba a cikin sa; abunda kake kiran mushrikai akai yayi masu girma; Allah yana zaban wanda yaso zuwa gareshi ya kuma shiryar da wanda ya jawo zuwa gare shi” (suratul shura ayata 13)


Allah ya aiko shi da shari'a ta rahama, Allah madaukaki yace:


“saboda rahamar Allah ne ka zama mai tausayi akansu, da ace ka kasance mai tsanani kuma mai fishi da sun tashi daga gefenka, ka zama mai yafiya garesu kuma ka roka musu gafara sannan ka nemi shawararsu, idan ka yunkura don aikata wani abu saika dogara ga Allah, lallai


Allah yana son masu tawakkali.” (suratu al'imran ayata 159)


Ya aiko shi da shari'a me sauki da tausayi, Allah madaukaki yana cewa yana me gori ga mutum da aiko shi zuwa garesu:


“Lallai ne, hakika , manzon daga cikinku yaje muku. Abunda kuka wahala dashi me nauyi ne akansa. Mai kwadayi ne saboda ku. Ga muminai mai tausayi ne, mai jin kai.” (suratul taubah ayata 128)


Ya kasanci cikin siffifin wannan shari'a iatce sauki da rangwame babu tsanani a cikinta da kunci, Allah madaukaki yace:


“Allah baya daura ma rai face abunda da zata iya, tana da ladan abunda ta aikata kuma tana da zunubin abunda ta aikata” (suratul bakara ayata 286)


Kuma manzon Allah s.a.w yana cewa:


“idan na haneku akan wani abu to ku nuisance shi, kuma idan ya umurce ku da wani abu to ku aikata shi gwargwadon iyawan ku” (sahihul buhari)


Aisha matarsa uwar muminai Allah ya kara mata yarda tana cewa:


“ba'a tab aba manzon Allah s.a.w zabi ba akan abu biyu, daya yafi sauki akan dayan, face ya zabi wanda yafi sauki a cikin su matukan be kasance zunubi ba. idan kuma ua kasance zunubi to yafi kowa nisanta daga gareshi” (sahihu muslim)


Allah y aiko shi da shari'a wacce ta yaki dukkanin dangin wuce gona da iri da tsanani cikin nassoshi na shari'a


wanda suke a bayyane wanda suka tsawatar akan sakaci da rashin aikata abunda akayi umurni dashi cikin addini kamar yadda wanda suka gabace mu suka aikata, Allah madaukaki yace:


“kace yaku ma'abota littafi kada ku wuce gona da iri cikin addinin ku wand aba gaskiya ba kuma kada kubi son zuciyoyin mutanen da hakika sun bata tuntuni kuma sun batar da mutane dayawa kuma sun bace akan hanyar madai daiciya” (suratul ma'ida ayata 77)


• Yayi hani akan tsanani da wuce gona da iri cikin addini, manzon Allah s.a.w ya tsawatar akan sa tsawatar wa me tsanani yace: “kashedinku da wuce gona da iri cikin addini, domin kuwa abunda ya halaka wanda suke gabace ku shine wuce gona da iri cikin addini” (Ahmad da Nasa'i da Ibn Majjah ne suka rawaito shi cikin silsilatul sahiha: 2144)


• Kuma yayi hani game da tsanani da wuce gona da iri cikin ibadu, hakika Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda ya rawaito daga gareshi cewa: “wasu mutane uku sun zo gidan matan manzon Allah s.a.w suna tambayan su game da ibadar manzon Allah s.a.w, baya sun fada masu sai suka ce: mu muna ina cikin wannan aiki na manzon Allah s.a.w? wanda an gafarta mashi abunda ya gabata na zunuban sa da abunda zai zo, sai dayan su yace: ni dai daga yau kullam sallah zantayi da daddare har Abadan, sai dayan kuma yace: ni kuma daga yau kullum azumi zantayi bazan hut aba, sai dayan yace: ni zan nisanci mata bazanyi aure ba har Abadan, sai manzon Allah s.a.w yazo yace: “kune kuka ce kaza da kaza ko? Lallai ni wallahi


nafiku tsoron Allah da kiyaye shi, amma ni ina azumi kuma ina hutawa, ina kuma sallah ina barci, ina kuma auran mata, dan haka duk wanda ya kyamaci sunnata to baya tare dani.” (Sahihul buhari)


• Kuma yayi hani game da tsanani da wuce gona da iri cikin mu'amala, hakika manzon Allah s.a.w yace: “lallai addini me sauki ne, kuma babu wanda zai tsananta wannan addini face ya rinjaye shi” (sahihul buhari)


• Kuma yayi hani game da tsanani da wuce gona da iri cikin kira zuwa ga Allah, manzon Allah s.a.w yace: “kuyi bishara kada ku kore mutane kuma ku saukaka kada ku tsananta” (sahihu muslim)


Babu ruhbaniyanci cikin musulunci ko kuma malamin coci kamar yadda yake cikin sauran addinai, kuma hakika Allah ya zargi wannan aiki na mutanen addinan da suka gabata, Allah madaukaki yace:


“Sa’annan muka biyar a bayan su da manzanni mu; kuma muka biyar da Isa dan Maryam, kuma muka bashi Injila kuma muka sanya tausayi da rahama a cikin zukatan wadanda suka bishi, da ruhbananci wanda suka kaga shi bamu rubuta shi ba a kansu, face dai (mun rubuta musu) neman yardan Allah, sa’annan basu tsare shi hakikanin tsarewarsa ba, saboda haka baiwa wadanda


sukayi imani daga cikin su sakamakonsu, kuma masu yawa daga cikin su fasikai ne” (suratul hadid ayata 27)


Kuma manzo Allah ya tsawatar akan haka tsawatarwa ne tsanani yace:


“kada ku tsanantawa kanku sai Allah ya tsananta muku domin kuwa wasu mutane sun tsanantawa kansu sai Allah ya tsananta masu ga kufai can na wuraren ibadun su da gidajen su (rahbaniyyan ci ne wanda suka kirkireta Allah be wajabta masu ba)” (silsilatul sahiha: 3124)


Mu sani cewa Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi be kasance baruhbane ba kuma be shar'anta ma mutanen sa ruhbaniyanci ba, ya umurci Taliban sa ne da su tafi su isar da addinin Allah ga mutane da shiryar dasu zuwa ga addini na ingantacce.


Akwaai nauyi babba akan malamin addinin musulunci dole ne yayi cudanya da mutane yana umurtan su da kyaukyawan aiki da kuma hanasu mummunan aiki ya kuma nuna masu hanya ingantacciya, saboda fadin manzon Allah s.a.w:


“ku isar game dani koda da aya daya ce.” (Sahihul Bukhari)


Sannan kuma ya zama dan kasa nagari abun misali da koyi ga al'ummar sa. manzon Allah s.a.w yace:


“mumini wanda yake cudanya da mutane da kuma yin hakuri abisa cutarwan su, yafi alheri akan muminin da baya cudanya da mutane kuma baya hakuri akan cutarwan su” (buhari ne ya rawaito shi cikin adabul mufrid kuma Albani ya inganta shi cikin sahihul jami'u)


Kuma kada ya zaman masu nauyi yana neman taimakon sun a abunda zaici annabawa sun kasance amincin Allah ya tabbata agaresu suna aiki da hannun su kuma suna kewon dabbobi domin neman abinci dashi da kame kawunan su da kula da iyalan su, hakika ancema manzon Allah s.a.w shin kayi kewon dabbobi? Sai yace:


“eh, akwai wani annabin da beyi kewon dabbobi bane” (sahihul buhari)


Bulus yana cewa cikin sakon farko zuwa ga Kurinsus (7/1): (1 amma ta bangaren al'amura wanda kuka rubuto mun su: abinda yafi shine mutum kada ya taba mace…. 8 sai dai ina cewa ga marasa aure da zaurawa, lallai yafi kyau agare sui dan sun zauna kamar yadda nake) – watan gauro-.


Kuma lallai wannan shine karantarwan bulus da kansa bawai karantarwan shugabammu Isa almasihi bane amnincin Allah ya tabbata agareshi, domin ta sabawa fidira wacce Allah ya halicci mutane akanta hasalima aure sunna ce ta annabawa amincin Allah ya tabbata agaresu Allah madaukaki yace:


“kuma hakika mun aika da manzanni gabanin ka kuma mun sanya masu mataye da zuriya; kuma be kasance ga wani manzo ba daya zo da wata aya face da izinin Allah; ko wani aiki da Allah ya hukunta yana da lokaci sananne” (suratul ra'ad ayata 38)


Shin al'ummar yanxu sun taba nazari akan wannan magana da rashin yin aure da kuma hayaiyafa wanda sakamakon sa shine zai karar da jinsin mutum? Shin Allah yana son mu kare ne ko kuma yanason mu da mu raya kasa na da hayaiyafa? Wannan duka sabanin umurnin Allah ne madaukaki wanda yace:


“kuma shine wanda yasanya ku khalifofi abayan kasa ya kuma daukaka darajan wasu akan wasu a cikin ku domin ya jarabaku cikin abunda ya baku; lallai ubangijin ku me saurin ukuba ne kuma lallai shi me gafara ne me jin kai” (suratul an'am ayata 165)


Duk a lokacin da muke neman mutane da zama gaurantaka da rashin yin aure to fa muna cin karu ne da sha'awar da take tare dasu, sha'awa ce cikin mutum kamar sha'awar cin abinci da shan ruwa, sai dai shari'a ta sanya mashi hanyar biyan sa a shari'ance ta hanyar aure yadda soyayya da tausayi da natsuwar zuciyar ga ma'aurata zai samu da kuma raya kasa, Allah madaukaki yace:


“kuma daga cikin ayoyin shi ya halitta maku mataye daga jikin ku domin ku samu natsuwa zuwa gare su ya kuma sanya soyayya da rahama atsakanin ku; lallai a cikin haka akwai ayoyi ga mutane masu tunani” (suratul rum ayata 21)


Manzon Allah s.a.w ya kasance yanayin umurni dayin aure da kuma kwataidar wa dashi da kuma yin hani akan gaurantaka hani me tsanani yana cewa:


“ku aure mata masu haihuwa wanda kuke son su domin zanyi alfari daku ranan alkiyama” (sahihu Ibn


Hibban, kuma albani ya ingantashi cikin “sahihu Abu Dawud”: 1789)


Ya kuma kwadaitar da samari musamman akan yin aure domin yawan sha'awa da suke da ita da kuma toshe hanyar alfasha, sai yace:


“yaku tarin samari! Duk wanda ya samu dama a cikin ku to yayi aure domin shi yafi rufe gani, da kiyaye farji, wanda kuma bai samu ba sai ya rika yin azumi, domin hakan kariya ce a gareshi” (buhari da muslim ne suka rawaito shi)


Kuma abunda yafi wananan shine ya sanya aure ya zama hanya ya neman kwayawan ayyuka da sadaka, sai yace:


“kuma acikin sduwar dayan ku akwai sadaka”, sai sukace ya manzon Allah! Yanzu wanin mu zai biya sha'awar sa kuma ya samu lada? Sai yace: “yaya kuke gani da ace yaje ya sanyata cikin haramun zai samu zunubi? To haka abun yake idan ya sanyata cikin halal zai samu lada da hakan” (sahihu Muslim)


INJILA NA MATA (5/31): (31 kuma ance: duk wanda ya saki matar sa to ya bata littafin saki. 32 amma kuma ni ina cewa maku: lallai duk wanda ya saki matar sa sai dai idan saboda zina ne zai sanyata yin zina, duk kuma wanda y auri wacce aka saka to yana zina)


Shin al'ummar wannan zamani wayayya sun yarda da rashin halascin yin sadi ko kuma dai mafi yawan kaso na saki


ana samun sa dayawa cikin kasashen da sukaci gaba?!! Shin kiristoci sunci iyabin wannan karantarwan ko kuma sun dauke a matsayin wuce gona da iri ne da tsanantawa?! Abunda yake a bayyane na aiki yana cewa akwai akwai dayawa na auratayya wanda bazai yiwuba suci gaba da zama domin kuwa cikin ci gaba da zaman akwai cucarwa wanda baza'a iya kawar da hakan ba sai da saki, kai mun karanta cikin jaridu yanayin kisan mace ga mijinta kirista a matsayin hanya na rabuwa dashi da rayuwa dashi domin rashin ikon da take dashi na rabuwa dashi!! Amma shi musulunci hakika ya halasta saki domin saukakewa akan mutane a halin rashin iya ci gaban rayuwan aure, sai kowa ya rabu da abokin zaman sa ta hanya ta wayewa kuma ko wanne a cikin su ya auri abunda ya yarda shi na abokin zama agareshi, Allah madaukaki yace:


“ku rikeso da kyautatawa ko kuma ku rabu dasu da kyautatawa” (suratul dalak ayata 2)


Kuma hakika dukkanin kasashen da suka waye ayanzu sunbi shari'ar musulunci akan wannan al'amari kuma sun halasta da dokanta saki kuma sun mayar dashi ya kuma saki a hukumance wanda ya nesanta daga ikon coci wacce take kin aure baki dayan sa.


Lallai yanke kan makiya da kuma gunduwa gunduwa da gawan wanda aka kashe abu ne wanda musulunci ya hana ya kuma tsawatar akan aikata shi, a lokacin da Amru dan Aas, da Shuraihu dan Hasanata dan Ukubata suka aika da sako zuwa ga Abubakar na kan Unaka ta hanyar sham, a


lokacin da ya isa zuwa ga Abubakar sai yayi inkarin haka, sai Ukubata yace masa: ya khalifan manzon Allah muma fa haka suke mana; sai yace: koyi da farisa da rumawa, kada akawo mun kai. Kawai rubutu da sako ya magana ya ishe ni. (Ibn Hajar al askalani ne ya rawaito shi)


Lallai wasu masu gabatar da shiri a cikin kafafen yada labarai na yamma a wannan zamani namu suna jingina wa musulmai al'adar yanke kai, sai dai da masu gabatar da wannan shiri na shashanci zasu koma su karanta tarihi da sun ga sabanin haka shine ingantacce, kawuna nawa aka yanke a cikin garuruwan su hatta cikin shekura nan baya baya kadan da suka wuce. A misali ana samu a jikin bango na coci zanen Milano daga waje na Faris yana rike da kan wani mutum wanda ya yanke a dayan hannun nashi kuma ya rike wuka doguwa, shin mun munga irin wannan ajikin bangon masallatan musulmai?!! Amma abunda ake gani daga wasu musulmai suna yanka wasu mutane a fili da kuma yanke kawunan su wannan ayyuka ne na dai daikon mutane bashi da alaka da shari'a musulunci kuma ya barranta daga shi,


Babban burin wannan aikata wannan aiki shine domin samun wata manufa marakyau na siyasa da kuma bata sunan musulunci da korarn mutane daga gareshi. Wannan mutane ana samun su a matsayin yan ba ruwan mu domin yin fim da na'urar daukan hoton su me tsada kwararriya, suyi fim misali akan yadda aka kashe wanda babu ruwan su babu wani abunda sukayi kuma basu yake su ba. Irin wannan mutane barna suke yadawa a doron kasa da kuma rashin son zaman lafiya. Allah madaukaki yace:


" kuma idan suka juya baya sai su yadu cikin kasa domin yin barna a cikinta kuma su halaka gona da zuriya; kuma bayason barna." (suratul bakara ayata 205)


Wani zai iya cewa: ' to wannan tutar fa wanda wannan mutane ke dagawa wanda ya kunshi rubutu na musulunci a jikin sa, shin wannan baya karfafa da shedar cewa su musulmai ne?. zamu ba da amsa agaresu da cewa: idan mutum yana da mota karama me arha sai ya kawo alama na motar marcedi na makala mata, shin hakan zai sa motar sa ta koma marcedi?' hakika amsar itace A'a. ya kamata ka kwatanta aikin su da kuma karantarwan musulunci zakaga cewa sunyi hannun riga a tsakanin su.


Allah madaukaki yana cewa:


“kuma idan zakuyi ramuwa to ku rama da kwatnkwacin abunda daka maku, kuma da zakuyi hakuri shi yafi alheri ga masu hakuri” (suratun nahali ayata 126)


Musulunci ya yaki tsarin bautan mutane ta ko wani hanya yayi umurni da yanta bawa ya kuma shar'anta yanta su da kuma yin alkawari na lada me yawa ga wanda ya yanta bawansa, ya kuma sanya shi cikin dalilai na shiga aljanna, manzon Allah s.a.w yana cewa:


“duk wanda ya yanta wani bawa Allah zai yanta daga wuta da ko wace daga cikin gabban sa hatta farjin sa” (muslim ne ya rawaito shi)


Sai dai musulunci be haramta tsarin bauta ba saboda kada yaci karo babba da abunda ke faruwa a duniya ya kasance tsari ne na duniya wanda kasashe ke aiki dashi baki dayan su yasancewar sa tsari ne na tattalin arziki da kudi wanda ake dogaru dashi cikin dukkanin al'umma, kuma a kan wannan hanya shugaban mu Isa almasihu be haramta tsarin bauta ba. sai dai musulunci ya hamate dukkanin hanyuka wanda zai kai ga bautar da mutum sai ta hanya daya kacal wacce itace hanyar fursinonin yaki da sharadin shugabanin musulmai ya zartar da zamr dasu bayi, kasancewar musulunci ta takaita hanyoyi na bayi sai hanya daya kawai, sai ya sanya a maimakon sa hanyoyi nay anta bayi ya sanya kaffara dayawa daga zunubai wanda musulmi ke aikatawa kamar misalin:


• KISA A BISA KUSKURE, saboda fadin Allah madaukaki: “duk wanda ya kashe mumini da kuskure to ya yanta bawa mumini da kuma diyya da zai bayar ga iyalan sa sai dai idan sun yafe; idan kuma ya kasance daga cikin mutane ne makiyanku amma mumini to sai a yanta bawa mumini; idan kuma ya kasance cikin mutanen da akwai alkawari tsakanin ku dasu to a biya diyya zuwa ga iyalan sa da kuma yanta bawa mumini” (suratun nisa'i ayata 92)


• KAFFARAR RANTSUWA, saboda fadin Allah madaukaki: “Allah baya kamaku abisa subutan baki na rantsuwan ku sai dai yana kamaku ne a bisa rantsuwar da kukayi shi da tabbaci; kuma kaffarar sa shine ciyar da miskinai goma na tsaka tsakanin abincin da kuke ciyar da iyalan ku ko kuma tufatar dasu ko kuma yanta bawa” (suratul ma'ida ayata 89)


• ZIHARI, saboda fadin Allah madaukaki: “wanda suke zihari akan matansu sa'annan su janye daga abunda suka fadi to su yanta bawa gabanin su kusance su” (suratul mujadala ayata 3)


• YIN JIMA'I A TSAKIYAN RANA DA WATAN RAMADAN, an karbo daga Abi huraira Allah ya kara masa yarda cewa wani mutum ya fadama matar sa cikin Ramadan sai ya tambayi manzon Allah fatawa akan haka, sai yace: “shin kanada bawa?”sai yace: a'a, sai yace: “shin zaka iya azumin wata biyu ajere: “sai yace: a'a, sai yace: “to ka ciyar da miskinai sittin.” (Muslim ne ya rawaito shi)


• YA SANYA SHI KAFFARAN TA'ADI AKAN WANI BAWA, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “duk wanda ya zalumci bawan sa ko kuma ya duke shi to kaffaran sa shine yay anta shi” (muslim ne ya rawaito shi)


Kuma daga cikin abunda zai tabbatar da kwadayin musulunci akan yanta bayi:


1. Yayi umurni da rubuta yarjejeniya, shine kulla yarjejeniya tsakanin bawa da ubangidan sa wanda zai yanta shi akan wani kudi wanda sukayi ittifaki akai atsakanin su, kuma hakika wasu maluman fiqihun78 Allah yayi masu rahama sun wajabta cewa idan bawa ya nemi ubangidan sa rubuta yarjejeniya suna masu kafa hujja da wannan fadin Allah madaukaki cewa: “wanda suke son rubuta yarjejenya cikin abunda kuka mallaka na bayi to ku rubuta masu


78 A wurin imamu Ahamd.


idan kunsan alheri a tare dasu; kuma ku basu cikin dukiyar Allah daya baku” (suratun nur ayata 33)


2. Ya sanya yanta bayi cikin abubuwan da ake basu kudin zakka, shine yanta bawa daga bauta, saboda fadin Allah madaukaki: “lallai zakka ana bayar da itace ga fukara'u da miskinai da masu aikin tattarata, da wanda ake lallashin zuciyar su, da bayi masu fansar kansu, da wanda ya raba fada ya daukan ma kansa biyan kudin, da majahidai fi sabilillah, da matafiyi; wajibi ne daga Allah; kuma Allah masani ne me hikima” (suratul tauba ayata 60)


YAZO CIKIN SAFAR NA TASNIYA (20/10): (10 a lokacin da ya kusanto birni domin yakanta ka kirata zuwa ga yin sulhu, 11 idan sun amsa yin sulhu suka bude maka, to dukkan mutanen da suke nan zasu zama karkashin ikon ka dayi maka bauta. Idan basuyi sulhu dakai sukayi yaki dakai, to kayi masu kawanya. 13 idan ubangiji allanka ya baka birnin a hannun ka to ka kashe dukkan mazajen su da takobi. 14 su kuma matan da yara da dabbobi da dukkan abunda ke cikin birnin ganima agareka, kaci ganimar makiyan ka wanda ubangijinka allanka ya baka. 15 haka zaka aikata da dukkanin birane masu nisa da kai wanda basa cikin biranen wannan mutanen na nan. 16 amma biranen wannan mutane wanda ubangijin ka


allanka ya baka rabonka kada ka rika wani mutum daga ciki, ka haramta su haramtawa).


YAZO CIKIN SAFAR ALKHURUJ (21/7): (7 idan mutum ya siyar da yarinyar sa kamar baiwa, ba'a sakin me yanci kamar yadda bawa yake sakin mutane masu yanci bayan shekara shida na bauta. 8 acikin yanayin cewa shugabanta be burgeta ba wanda ya siye ta kamar abokiya agareshi, ya wajaba yaba mahaifinta damar fansar ta da kudi ya amshe ta daga gareshi).


YAZO CIKIN SAFAR ALKHURUJ (21/5): (5 amma idan bawa yace: inason shugabana da matata da yarana, bazan fita daga me yanci ba, 6 shugabanshi zai gabatar dashi ga allah, ya kuma kusantar dashi zuwa ga kofa ko itace sai ya bugi kunnuna sa da abun duka yayi masa hidima na har Abadan). – wa'ana bauta ta har Abadan-.


YAZO CIKIN SAFAR ALKHURUJ (22/1-3): (ya wajaba akan barawo da ya biya me wanann abunda ya sata, idan kuma bashi da kudi wanda zai isa biya wannan mutumi, to anan za'a siyar da wannan barawo kamar bawa, yabada kudin ga wannan mutumi dayama sata. Yanzu mu karanta abunda injila ya jingina zuwa ga shugabammu almasihu amincin Allah ya tabbata a gareshi.)


Musulunci yayi hurgi da dukkanin abunda yake jawo banbanci tsakanin mutane na shari'a wanda yake furta kabilanci ko kuma aiki dashi ko banbancin launin gfata tsakanin mutane ya kuma sanya banbanci tsakanin su yana ginuwa ne akan tsantsan kusanta da kuma nisantar aiwatar da shari'un Allah, Allah madaukaki yace:


“yaku mutane lallai mun halicce ku daga namiji da mace kuma mukasanya ku kuka zama mutane da kabilu domin ku samu sanayyi; lallai wanda yafi wani acikin ku shine wanda yafi tsoron Allah; lallai Allah masanin ne me bada labari” (suratul hujurat ayata 13)


Kuma manzon Allah s.a.w yace:


“yaku mutane! Lallai ubangijin ku daya ne, kuma babanku daya ne, ku saurara kuji babu falala ga balarabe akan wand aba balarabe ba ko kuma wanda ba balarabe ba akan balarabe, ko kuma fari akan baki, ko baki akan fari sai da tsoron Allah, lallai mafificin ku a gun Allah shine wanda yafi tsoron sa, ku saurara kuji shin na isar? Sai suka ce: eh ka isar ya manzon Allah sai yace: to wanda yaji ya isar zuwa ga wanda bayanan” (silsilatul sahiha)


A LOKACIN DA MUKA SAMU CIKIN LITTAFI ME TSARKI NA YAHUDAWA DA KIRISTOCI ABU MASU ZUWA:


YAZO CIKIN INJILA NA MATA (15/24): (24 sai ya amsa: << ba'a aiko nib a face zuwa ga Kirafa batattu, zuwa ga gidan isra'ila, 25 sai dai mace ta kusa gare shi, kuma tayi mashi sujjada, ta kuma ce: ta taimake ni ya shugabana! 26 sai ya amsa: ba daidai bane a dauki biredin


yara maza a jefama karnuka! 27 sai tace: <<gaskiya ne ya shugabana; sai dai karnuka masu tsaurin ido suna cin yan matan da suka fita daga hannun masu shi! 28 sai yusha'u ya masa: << yake mace, imanin ki yana da girma! Ya kasance maki abunda kike nema!>> sai aka warkar da yaron ta a wannan lokaci).


A cikin wannan nassin akwai raddi a bayyane me karfi kuma ga duk wanda yake ikirarin cewa almasihu yazo ne domin tsarkake duniya da gicciyewa da kuma fansa da makamantan haka, yana cewa maka a fili cewa ba'a aiko ni ba zuwa gare ka kuma bansanka ba!! sai dai an aiko ni ne zuwa ga bani isra'ila su kadai!!


YAZO CIKIN SAFAR NA TASNIYA (23/19): (19 kada ya wajabtama dan uwanka da riba, riban azurfa, ko kuma riban abinci ko riban wani abu cikin abunda da ake riba dasu 20 ga wand aba bani isra'ila bane zaka wajabtawa riba, amma ga kada ka wajabta ga dan uwanka, domin ubangiji allahnka yayi albarka agareka).


Shri'ar musulunc yana umurni ga musulmi daya zama me kyau cikin dukkanin yanajin sun a tufafi da ganin sa da kamshin sa da maganar sa, saboda fadin manzon Allah s.a.w:


“lallai Allah me kyau ne yana son masu kyau” (sahihu muslim)


Kuma Jabir dan Abdullah yace:


(manzon Allah s.a.w yazo mana sai yaga wani mutum buzu buzu gashinsa yayi bakyaun gani sai yace: “shin wannan be samu abunda zai gyara gashin sa bane.” Ya kuma ga wani mutumi shima sanye da tufafi me datti sai yace: “shin wannan bai samu ruwan da zai wanke tufafin shi bane”) (sunan abu dawud kuma albani ya ingantashi)


Kuma abu Ahwas ya rawaito daga babansa yace:


(nazo gun manzon Allah s.a.w cikin riga mara kima79, sai yace: kana da kudi? Sai nace: eh, sai yace: wani irin kudi?80 Sai yace: hakika Allah ya bani rakuma da dabbobi da doki da bawa, sai yace: idan Allah ya baka kudi to aga alamun ni'imar Allah da falalar sa a tattare da kai) (Abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi)


Kuma Jabir dan samurata yace:


(naga manzon Allah s.a.w cikin daren salla81, yana sanye da riga ja, sai na rika kallon sa da wata, wallahi yafi watan nan kyau) (tirmizi ne ya rawaito shi- ingantacce ne)


Kuma Barra'u dan Azib yace:


(manzon Allah s.a.w ya kasance mutum ne matsakaici me fadin kafada82, me yawan gashi83 har zuwa


79 tufafin da be dace da masu kudi ba.


80 Nauyi cikin jinsin kudi.


81 Watan me haske


82 Me fadin kafada


83 Gasgin da yake sauka kafada


kunnen sa, yana da tufafi ja84 bantaba ganin wani abuba a rayuwa me wanda yafi shi kyau) (sahihu muslim)


Kuma Abu Zamil ya rawaito cewa Abdullahi dan Abbas yace:


(a lokacin da kharijawa suka bayyana sai nazo gun Aliyu allah ya kara masa yarda sai yace: ka zo da wannan mutane. Sai ya sanya tufafi me kyau wanda yafi huliyyi na yaman kyau sai Abu zamil yace: Ibn Abbas ya kasance mutum ne me kyau gani – sai dan Abbas yace: sai nazo wurin su sukace mun marhaba da zuwanka ya dan Abbas, wannan rigan fa?! Sai yace: kada ku aibanta mun riga hakika naga manzon Allah s.a.w ya sanya riga wacce tafi irinta kyau) (Abu dawud ne ya rawaito shi kuma shu'aibual arnud yace: isnadin shi me karfi ne)


Kuma shari'a ta dauka kashe dukkanin abunda zai cika rai mutum musulmi cikin dukkanin yanayi ba tare da barna ba da almubazaran ci da girman kai cikin abubuwan da ake bashi lada akai, saboda fadin Allah madaukaki:


“yaku yan Adam ku riki kawarku a ,okacin zuwa ko wani salla kuma kuci kusha kada kuyi barna; lallai shi bayason masu barna” (suratul a'araba ayata 31)


Shiga irin ta musulunci:


Kuma babu wani tufafi cikin shari'ar musulunci da ake kira da suna tufafin musulunci, kamar abunda wasu sufaye da yan shi'a suke sanyawa me launi daban kamar launin kore ko baki ko makamantan su, sai dai akwai siffofi na tufafin shari'ar


84 watan riga ja


musulunci, wanda ya wajaba musulmi ko kuma musulma su takaita akansu, daga cikinsu akwai:


• Ya kasance cikin wannan tufafi babu koyi da wand aba musulmi ba kamar mutum yasa tufafin da buzawa ke sanyawa ko kiristoci ko yahudawa kawai kamar tufafin fadoji da fastoci a misali, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “duk wanda yayi koyi da wasu mutane to shima yana daga cikin su” (Ibn Hibban ne ya rawaito shi -kuma ingantacc ne)


• Ya rufe masa al'auran sa wanda shari'a ya hana bayyanar dashi, kada ya bayyana saboda gajartan sa ko kuma shara-sharansa.


• Ya kasance tufafi ne me tsabta da kyaun gani, hakika manzon Allah s.a.w yaga wani mutum sanye da tufafi me datti sai yace: “shin wannan bashi da ruwan da zai wanke wannan tufafin ne nashi” (sunan abu dawud, silsilatul sahiha: 493)


• Ya kasance tufafi me kamshi wanda baya koran mutane daga kusantan me shi, manzon Allah s.a.w ya hana cin tafarnuwa ko albasa a lokacin zuwa masallaci domin cucarwan dake cikin sa wanda zai samu na gefen sa dashi, saboda fadin sa manzon Allah s.a.w: “duk wanda yaci albasa ko tafarnuwa (wani wurin kuma yace duk wanda yaci albasa da tafarnuwa da lawashi kada ya kusanci masallacin mu. Domin mala'iku suna cutuwa daga abunda yake cucar da dan adam” (sahihu muslim)


• Kada ya zama tufafin na alfahari ne ya kasance bako ne cikin al'umman da yake rayuwa a ciki, idan ya sanya shi mutane zasuyi mamaki domin kyaun sa sai ya karama me shi girman kai da dagawa, ko kuma ya kasance tufafi ne wand abe dace da yayin shi ba a al'adance da kuma kore masa mutuncin sa, sabod afadin manzon Allah s.a.w: “duk wanda ya sanya tufafin alfahari a duniya to Allah zai sanya masa tufafin kaskanci ranar alkiyama” (Ahmad nay a rawaito shi, kuma albani ya inganta shi cikin sahihu abu dawud)


• ya zama babu koyi da maza a cikin sa ga mata, ko kuma koyi da mata ga maza “manzon Allah s.a.w ya tsinema namijin daya sanya tufafin mace ko kuma macen da ta sanya tufafin namiji” (sahihu Ibn Hibban)


Akwai kuma hadisai masu nuni akan muhimmancin musulmi ya rika kula da shigan sa duk wanda yakeson Karin bayani akan haka sai ya koma zuwa ga littattafan tufafi a musulunci, zamu takaita cikin abunda muka ambata a baya cewa shari'ar musulunci ya himmatu matuka da tsaftar musulmi da kuma kyawun ganin sa baya halatta ga musulmi ya kori mutane daga wurin sa domin munin shigan sa da kuma rashin tsabta.


A nan wurin akwai gaba me muhimanci wanda zai iya kawo shubuha game da shari'ar musulunci ga wanda ba musulmai ba a dalilin tufafi musamman a wasu kasashen yamma wanda muke ganin wasu daga cikin musulmai baki ko kuma wasu musulmai sababbin musulunta a wasu kasashe suna sanya tufafi wanda wanda yaganshi zaiyi makakin cewa anya wannan musulmi ne kuwa, kamar ya sanya (mayafi irin wanda muatanen misra suke sakawa musulman su da kristan


su wanda beya sanin cewa shi musulmi ne kawai abunda ya sani shine shi mutumin misra ne) ko kuma ya sanya tufafi sabo ko kuma kayan sojoji kuma shi ba soja bane ko kuma ya kewaye kansa da wani bandeji ba ta hanyar da aka saba gani ba, wanda ya kamata ya sanya irin tufafin da mutane suka sani ne wanda bazai sanya mutane su guje shi ba ko kuma samun shakka akansa ba, hakika manzon Allah s.a.w ya kasance yafi kyauwun mutane a wurin shiga kuma wanda yafi su kamshi kuma duk wanda ya ganshi yanajin natsuwa da kwanciyan hankali.


Sai dai ya wajaba nu banbance tsakanin kayan da akasan wasu mutanen ne ke sanyawa da kuma kayan da wasu bangare ne ke sanyawa ko kuwa wasu bangare na mazhaba domin addini kamar misali abunda sufaye da shi'a keyi, amma kayan makaranta ko jami'u da kungiyoyi na kasa da kasa data cikin gida kaya domin a gane su wanda bawai an ginashi bane akan wani turba na mazhaba ko bangaranci a'a kawai domin a rika gane wannan ma'aikatan ne dashi ko kuma dalibai.


Allah madaukaki yace:


“kace masu wanene ya haramta ado na Allah wanda ya fitar da ita domin bayin sa da dadadan abubuwa na arziki; kace anyi su ne domin wanda sukayi imani cikin rayuwan duniya kuma nasu ne su kadai a ranan alkiyama; Kaman haka ne muke bayyana ayoyi ga mutane masu sani” (suratul a'araf ayata 32)


Shari'ar musulunci ta halasta jin dadi da more dukkanin dayan ci da sha, sai abunda da dalili ya nassanta akan haramcin sa, Allah madaukaki yace:


“an haramta maku mushe da jini da naman alade da abunda aka yanka domin wanin Allah da kuma wanda aka shaketa ta mutu da wanda aka duka ko harba da dutse ta mutu da wacce ta fado daga tsauni ta mutu da wacce yar uwarta ta tunkura da kaho ta mutu da wanda dabban farauta ya kashe sai wanda kuka yanka da abunda aka yanka akan gunki (shima an haramta) kuma kada kuyi rabo da kibau na caca; wannan fasikanci ne.” (suratul ma'ida ayata 3)


Allah madaukaki yana cewa:


“suna tambayan ka game da giya da caca; kace suna da zunubi me girma da dan amfani ga mutane; kuma zunubin su yafi amfanin su girma; kuma suna tambayan ka me zasu ciyar kace masu abunda ya samu ya sawwaka ya ragu; kaman haka ne Allah yake bayyana maku ayoyin sa koda zakuyi tunani” (suratul bakara ayata 219)


Ya kuma sharada rashin yin barna, Allah madaukaki yace:


“kuma kuci kusha kada kuyi barna; lallai shi bayason mabarnata” (suratul a'araf ayata 31)


Ya kuma bayyana hanya ingantacciya na ci da sha wanda suka kunshi lafiya da izinin Allah ga jiki daga cutuka, manzon Allah s.a.w yana cewa:


“mutum be taba cika tunbi na sharri ba kamar ciki, ya ishi dan adam yaci wasu yan loma na abinci wanda zai karfafa kashin bayan sa dashi, idan ya kasance babu


makawa to: ya raba daya biya uku na cikin sa yaci abinci, daya bisa uku na ruwa, daya bisa uku kuma nayin nunfashi” (Tirmizi ne ya rawaito shi – kuma ingantacce ne – cikin “al irawa'I”: 1983)


Rayuwa a shari'ar musulunci bawai kamar yadda wasu ke tsammanin ta bane cewa babu wasa acikin ta wanda yake halal, Hanzalata yana cewa:


“Abubakar ya hadu dani sai yace: ya kake ya Hanzalata? Sai nace: hanzalata yayi munafunci! Sai yace: subhanallah! Me kake cewa:? Sai nace: idan muna gun manzon Allah s.a.w yana tunatar damu akan wuta da aljanna sai kaga kamar muna ganin su da idanun mu, amma idan muka bar wurin manzon Allah s.a.w sai mu shagalta da matan mu da yara sai mu manta dayawa!. Sai Abubakar yace: wallahi nima ina fama da irin wannan abu. Sai suka tafi zuwa ga manzon allah s.a.w muka shiga wurin shi sai nace: Hanzalata yayi munafunci ya manzon Allah! Sai manzon Allah s.a.w yace: “me yayi haka”sai nace: ya manzon Allah! Idan muna wurin ka kana tunatar damu akan wuta da akjanna sai kaga kamar muna ganin su da idanun mu, amma da zaran mun bar wurin ka sai mu shagalta da matan mu da yara da kayan wasa sai mu manta dayawa! Sai manzon Allah s.a.w yace: “ina rantsuwa da wanda raina ke hannun sa! da zaku dawwama akan halin da kuke a wurina a ciki da kuma zikiri da mala'iku sun gaisa daku akan gadajen ku da


hanyoyin ku, sai dai ya Hanzalat! Lokaci bayan lokaci ya maimata haka har sau uku.”85


Sai manzon Allah s.aw ya bayyana cikin wannann hadisi cewa wasa halal ne da kuma hutar da kai anason yin shi domin mutum ya samu nishadi da lafiyanta, kuma ya bayyana wa sahabban sa ladubba na wasa da zaulaya a lokacin da suka tamabaye shi sukace: ya manzon Allah kana mana wasa! Sai yace: “eh inayi amma bana fadi sai face gaskiya”86


Kamar yadda wasa yana kasancewa da magana haka kuma yake kasancewa da aiki, Anas dan Malik Allah ya kara masa yarda yace:


“Wani mutum cikin mutanen kauye me suna Zahir, ya kasance yana kawo ma manzon Allah kyauta na kayan kyauye, sai manzon Allah s.a.w ya shiryashi idan zai tafi. Sai manzon Allah s.a.w yace: “lallai Zahid shine dan kyauyen mu mukuma yan birnin sa, sai manzon Allah s.a.w yaje masa wata rana yana siyar da kayan sa sai ya kamashi daga bayan sa baya ganin sa, sai yace: wanene wannan? Sakeni! Sai ya juya yaga manzon Allah s.a.w sai yaci gaba da hada bayansa da kirjin manzon Allah. Sai manzon Allah s.a.w yace: “wazai siya wannan bawan?”sai Zahid yace: ya manzon Allah ai arha zanyi bazanyi kudi ba, sai manzon Allah s.a.w yace: “amma dai zakayi kudi


85 Sahihu muslim mujalladi na 4 shafi na 2104 lambar hadisi na 2750


86 Sunan tirmizi mujalladi na 4 shafi na 357 lambar hadisi na 1990


agun Allah! Ko kuma yace: kai me tsada ne agun Allah”87.”


Yana da ladubba acikin shari'ar musulunci daga cikin su akwai:


▪ ya kasance babu cutarwa cikin wasan ga musulmi ko kuma muzguna masa aciki, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “baya halatta ga musulmi ya tsorata musulmi”88


▪ Kada wasan ya fita daga cikin abota, yayi karya domin ya sanya mutane daria, saboda fadin manzon Allah s.a.w: “bani ya tabbata ga wanda yake bada labari sai yayi karya domin yasa mutane dariya! Bani ya tabbata a gareshi bani ya tabbata a gareshi!”89


Kamar yadda shari'ar musulunci ta halasta wasa da sharadin ya kasance halal kamar jifan kibiya ko kwari da baka da tseren doki, manzon Allah s.a.w yace: “dukkanin wani wasan da musulmi zayyi bashi da kyau sai dai jifa mashi ko koyon tseren doki ko kuma wasan sa da matar shi” (Tirmzi ne ya rawaito shi kuma albani ya igantashi), kuma dukkanin abunda yake gida jika da kuma kare lafiya na nau'ukan motsa jiki kamar nunkaya da gasa da kokawa, manzon Allah s.a.w yayi kokawa da wani mutum wanda


87 Sahihu ibn hibban ,ujalladi na 13, shafi na 106, lambar hadisi na 5790 – kuma ingantacce ne.


88Musnad imamu Ahmad, mujalladi na 5, shafi na 362, lambar hadisi na 23114 – kuma ingantacce ne


89 Sunan abu dawud, mujalladi na 4, shafi na 297, lambar hadisi 4990 – hadisi ne hasan.


ake kira – Rakanata- sai manzon Allah s.a.w ya kayar dashi kuma ya kasance me karfi sai yace: a sanya akuya da akuya sai manzon Allah ya kayar dashi sai yace: mu sake sai ya kayar dashi har sau uku sai mutumin yace: me zance ma iyalai na? karkace ya cinye akuya daya dayan kuma ta fado to dayan kuma me zance masu, sai manzon Allah s.a.w yace: “bazamu hada maka shan kayi ba da kuma cin tara dauki akuyoyin ka”albani ne ya rawaito shi- kuma hasan ne.


1. Ukubar yanke hannu cikin littafi me tsarki.


2. Ukubar zina cikin littafi me tsarki.


3. Ukubar kisa cikin littafi me tsarki


4. Yancin yin addini cikin littafi me tsarki (yin ridda)


5. Shari'ar kishi cikin littafi me tsarki (li'ani – yin rantuwa tsakanin ma'aurata domin barranta dga tuhumar yin zina)


Mafiya yawan kasashen turawa suna tashi ta hanyar sanarwan su domin bata suna ga addinin musulunci ta hanyar tallata haddoji wanda ake zartarwa a musulunci da cewa hakan be dace da ci gaban zamani ba wanda duniya ke ciki yanzu da makamantan haka na manufar su na kare mutane game da wannan addini na Allah wanda da mutane zasu kalleshi ba tare da kabilanci ba ko kuma hukuncin da akayi mashi abaya ba da sunsan cewa lallai addini ne na gaskiya wanda ya wajaba abishi sai dai tsoro sautin gaskiya ya isa ga mutane dukda cewa sai fay a isan ko mutum yaki ko yaso domin tabbatar da alkawarin Allah da yake cewa: “suna son kashe hasken Allah da bakunan su sai dai Allah yaki hakan sai ya cika hasken sa koda kuwa kafirai sunki hakan” (suratul taubah ayata 32)


Zartar da haddoji cikin musulunci zartar da shari'ar Allah ne bawai daga wurin musulmai bane kuma mun gani cikin babukan da suka wuce cewa rahama ce ga mutum da al'umma baki daya kuma zamu gani cikin shafuka na littafi me tsarki na tsohon alkawari da sabon zartar da haddoji abunda suke aibantawa a wurin musulmai hasalima yafi tsanani ma, sai dai kafafen yada labaran turawa wanda suke makirci da kuma aiki da gabban su wurin ganin sun batama shari'ar musulunci suna wanda hakan baya karamai komai face yaduwa kasancewar sa sauti ne na gaskiya wanda baza'a iya


kashe shi ba, kuma Allah yayi gaskiya: “kuma shine wanda ya aiko da manzon sa da shiriya da addinin gaskiya domin ya rinjayar dashi akan dukkanin addinai koda kuwa mushrikai sunki hakan”suratul taubah ayata 33.


SHIN TSOHON ALKAWARI LITTAFI NE ME TSARKI NA KIRISTOCI DA YAHUDAWA?!


Gabanin mu kutsa cikin koro wani hukunce hukunce (haddoji) daga shari'ar kiristoci da yahudawa, munason sanin idan tsohon alkawari littafi ne me tsarki a gun kiristoci da yahudawa ko a'a", karkashin tattaunawa ta da wasu daga cikin kiristoc na samu suna bayya cewa littafi me tsarki tsoho da sabon alkawarin duk Kalmar Allah ne na asali sauran kuma an cancanza wanda zabai bace ba ko kuma canzuwa, bayan karanta mashi wasu nassoshi daga cikin tsohon alkawari sai yayi gaggawan dawowa da janyewa yana cewa zaka iya tambayan malamin addini akan wannan nassoshi ni ba bayahude bane, kai al'amarin yakan kaisu cikin wasu lokuta na barranta daga tsohon alkawari baki daya yana cewa dukkan wannan ya kasance ne gabanin zuwan almasihu amma bayan yazo sai komai ya canza, kuma tabbas tafsirin sa ba'a sallama masa a hankalce ko ta fuskan rawaitowa. Dukkanin kirista bazai iya zama kirista ba sai dai idan yayi imani da littafi me tsarki tsoho da sabon alkawari baki daya, wannan abu a bayyane yake agun dukkan kirista, akan haka idan wani kirista beyi imani ba da tsohon alkawari ba dayin imani kawai da sabon alkawari to ya zama arne da addinin kiristanci! Duk wanda yake son tabbatarwa akan haka zai iya tambayan malamun su yaji dakan sa abunda zasu ce mashi!


Hakika an ambata cikin injila na mata (5/17) cewa Isa yace: “kada kuyi tsamanin cewa nazo ne domin na toye


Namus ko kuma kuma annabawa. Banzo domin toyewa ba sai don cikawa. Lallai gaskiya ce nake fada maku: har zuwa karshen duniya babu wani harafi da zai gushe ko kuma wata kalma daya cikin Namus har yazama duka. Duk wanda ya toye daya daga cikin wasiyyoyi kanana kuma mutane suka sani a hakan, za'a kirashi makaskanci cikin sama.”


Zamu kawo wasu daga cikin nassoshin haddoji wanda suka zo cikin littafi me tsarki:-


Safar altasniya (25/11): (11 idan mutum biyu sukayi fada da juna, da mutum da dan uwan sa, sai matar daya daga ckin su tazo kwatan mijinta a hannun wanda ya duke shi, sai hannun ta ya zarce ya kama al'auran shi, 12 ku yanke hannun ta, kuma kada idonka yaji tausayi).


SAFAR AL LAWIYYIN (21/9): (9 idan wata diya tayi datti na aikata zina to hakika ya bata mahaifinta da datti. Da wuta za'a konata!!!!!!!!).


SAFAR AL TASNIYA (22/20): (20 sai dai idan wannan al'amari ya kasance ingantacce kuma ba'a samu kazanta ba ga budurwa, 21 za'a fitar da budurwa zuwa ga


kofar mahaifinta mazajen birnin su jefe ta da duwatsu har sai ta mutu domin ta aikata mummunan abu cikin bani isra'ila da zinan da tayi cikin gidan mahaifinta sai a cije sharri daga tsakiyan ka).


SAFAR AL TASNIYA (22/22): (22 idan aka samu wani akan matan wani za'a kashe duka su biyun mutumin da matan).


SAFAR AL TASNIYA (22/23): (23 idan mace ta kasance budurwa wani ya nemi auren ta sai mutum ya same ta a cikin birni ya kwanta da ita, 24 to ku fito dasu zuwa ga kofar wannan birni sai ku jefe su da duwatsu har sai sun mutu).


AN AMBATA CIKIN INJILA NA MATA (5/27) CEWA ISA YACE: (27 hakika kunji cewa ancema tsofaffi: kada kayi zina. Amma ni inace maku: lallai duk wanda ya kalli matar wani domin sha'awa, hakika yayi zina da ita cikin zuciyar sa. idan ya kasance idonka na dama ya sanyaka hakan to ka cire shi ka huragar dashi domin hakan yafi maka alheri da wani gabbanka ya halaka kuma kar ya jefa jikin ka duka a cikin jahannama. Idan ya kasance hannun ka ne na dama yayi aikin to ka yanke shi ka hurgar dashi, hakan yafi zama maka alheri daya halaka daya daga cikin gabban ka ya kuma jefaka cikin jahannama.)


SAFAR AL LAWIYYIN (20/10): (10 idan wani yayi zina da mace, idan yayi zina da mace yar uwa, to za'a kashe shi da ita. 11 idan mutum ya kwanta da matar babanshi, hakika ya bayyana al'auran bababnshi. Za'a kashe su. Jinin su yana kansu. 12 idan mutum ya kwanta da yar uwar sa, za'a kashe su, hakika sun aikata alfasha.


Kuma jinin su yana kansu. 13 idan mutum ya kwanta dana miji kwanciya irin na mace, hakika sun aikata datti. Za'a kashe su. Kuma jinin su yana kansu. 14 kuma idan mutum ya hada yarinya da mamanta wannan sabo ne. da wuta za'a kona shi dasu, domin kada sabo ya kasance a tsakanin ku. 15 idan kuma mutum ya kwanta da dabba, za'a kashe shi da dabbar….).


Haka dai al Ishah yaci gaba da Ambato ukubar mutuwa ga macen da ta kwanta da dabba ko kuma namiji wand ayaga al'auran yar uwansa tare da wata mata ko kuma yaga al'aurar kanwar mahaifiyar sa ko kanwar mahaifi ko ya kwanta da matan kawun sa ko bdan uwansa!! Mutum zai iya cewa ashe almasihu be share wannan ukubar ba na zina wacce take jifa har sai an mutu ya mayar da ita laifi wacce bata a ukuba? Shin baya fad aba cikin injila na yuhana (8/7): (7 duk wanda yakasance a cikin ku bashi da budurwa to ya jefata da dutse) sai muyi bada amsa agareshi da cewa: hakika maluman Lahuta cikin kiristoci sunyi ittifakin cewa wanann labari bata inganta ba an karata ne cikin injila a cikin karni na goma na miladiyya90, akan haka ne baya halatta dogaro akai.


Ka kara akan haka da maganganun shugaban mu almasihu da kansa waccce take kore sabawa Namus ko kuma shari'ar Musa, injila na mata (5/17): (17 kada kuyi tsammanin nazo ne domin toye Namus ko kuma annabawa, banzo ba domin toyewa ba sai dan cikawa. 18


90 Bart D. Ehrman ‘‘Misquoting Jesus in the Bible’’ LECTURE minute 33:00. /see also ،Bart D. Ehrman "Jesus and the Adulteress،" ‘‘New Testament Studies’’ ،xxxiv (1988) pp. 24-44./ See also ،Bruce Metzger ،A Textual Commentary on the Greek New Testament (Stuttgart ،1971) ،pages 219-221.


lallai ina fada maku gaskiya: har zuwa karshen duniya babu wani harafi daya da zai gushe ko kuma kalma daya cikin Namus har ya zama duka).


Watan ta wani ma'anar da taban da ace shugaban mu almasihu yana tare damu ayau daya jefe duk matan da tayi zina kamar yadda shari'ar Musa ya fada.


BULUS YANA CEWA CIKIN SAKON SA ZUWA GA IBRANIYAWA (28/10): “duk wanda ya sabama Namus na Musa to a gaban shedu biyu ko uku zai mutu babu taisayi..”


SAFAR AL KHURUJ (21/12): (12 wanda ya duki mutum ya mutu za’a kashe shi….14 idan mutum ya zalumci dan uwan sa domin ya kashe shi da yaudara to a wurin mayanka na za’a kashe shi. 15 wanda ya duki babanshi ko mahaifiyarshi za’a kashe shi. 16 wanda ya saci mutum ya siyar dashi ko kuma aka same shi a hannun shi za’a kashe shi. 17 wanda ya zagi babanshi ko maman shi za’a kashe shi.. 22 idan mutum yayi fada ya bige mace me ciki sai yaron cikinta ya fado amma bata samu wata cutarwa ba, za’aci shi tara zai biya ta hannun alkali 23 idan kuma ta cutu za'a bata rai da rai, 24 ido da ido, hakori da hakori, hannu da hannu, kafa da kafa, 25 kuna da kuna, kwankwa tsawa da kwankwa tsawa).


SAFAR AL KHURUJ (21/18): (18 kada kabar boka ta rayu. 19 duk wanda ya kwanda da dabba akashe shi. 20


wanda yayi yanka ga wani ba ubangiji bas hi kadai zai halaka).


SAFAR AL TAKWIN (9/6): (6 wanda ya zubar da jinin mutum da mutum za'a zubar da jinin shi).


SAFAR AL ADAD: (35/31): (31 kada ku amshi fansa na kudi akan mutumin da yayi kisa me zunubin mutuwa, za'a kashe shi ne… 33 kada ku lalata kasar da kuke cikinta, domin jini yana lallata kasa, kuma akan kasa ba'a kankare zunubi domin jinin da aka zubar a cikinta sai da jinin wanda ya zubar dashi).


SAFAR ALKHURUJ (32/26): (26 musa ya tsaya a kofar wurin sa, sai yace: “duk wani na Allah yazo nan”sai suka hadu awurin sa baki daya yaran Lawi. 27 sai yace masu: “haka ubangiji allan bani isra'ila yace: kowa yasa wukan sa akan cinyan sa kuje ku dawo daga kofa zuwa kofa a muhalla, kowa ya kashe dan uwan sa kowa ya kashe abokin sa kowa ya kashe dan na kusa dashi.” 28 sai yaran Lawi suka aikata yadda musa ya umurce su. Aka kashe kusan mutum dubu uku a wannan rana).


SAFAR AL TASNIYA (21/18): (18 idan mutum yana da yaro marajin magana takadari bayajin maganar mahaifin shi da mahaifiyar sa, kuma suna ladabta shi amma baya ji. 19 mahaifin shi zai rike shi da mahaifiyar shi sai su zo dashi zuwa ga shugaban birnin su zuwa ga kofar wurin sa, 20 sai su ce mashi: wannan yaro namu takadari marajin maganan mu, kuma shi me barna ne da maye. 21 sai mutanen ganin dukan su sujefe shi da dutse har sai yam utu).


INJILA NA LUKA (19/27) ana jinginawa ga shugaba almasihu cewa yace: (27 amma makiyana wannan sune wanda basa so na mallake su ku zo dasu zuwa nan ku yanka su a gabana").


SAFAR AL TASNIYA (13/12): (12 idan kaji labari a cikin daya daga garuruwan ka wanda ubangijin ka allanka ya baka domin ka zauna a cikinta, 13 wasu mutanen yaran Lu'aim sun fita daga tsakiyar ka suka kara mutanen garin su suna ce masu: muje mu bautawa wani allan wanda basu sanshi ba. 14 ka bincika ka tabbar da yin tambaya dakyau idan al'amarin gaskiya ya tabbata, wani mjutum ya aikata haka a tsakiyar ka, 15 ku kashe mutanen wannan birni da takobi. 16 ka tara dukkan kayan ta a tsakiyan filinta, ka kona su da wutan garin kuma dukkan kayan ta baki dayan sun a ubangiji ne allanka, zai ka kasance kwafai ba'a ginata ba bayan ka).


SAFAR AL TASNIYA (7/1): (1 duk lokacin da ubangijin ka allanka yazo dakai cikin kasar da kake ciki domin ka mallaketa, aka kori mutane dayawa a gabanka…. 2 ubangijin allanka ya koro su gabanka, ka duke su, lallai kana haramta su. Kada ya yanka masu alkawari, kuma kada ka tausaya masu. 3 kuma kada ka aure su… sai dai haka zaka aikata dasu: da rusa mayankan su ka sassare wuraren bautan su, ya yayyanka rigunan yakin su, ka kona gumakan su da wuta).


SAFAR EZIKEL (9/4): (4 sai ubangiji yace mashi: “ka tekara tsakiyan birni, Ka sanya zane akan fuskan mutanen masu nadama da hucewa.” 5 sai wannan suka fadi acikin kunne na: “ku tsallaka cikin birni a bayan sa ku duka. Kada ku tausaya kuma kada kuyi yafiya. 6 tsoho da matashi mara lafiya da mace da yaro, ku kashe su domin halaka. Kuma kada ku kusanci mutumin da akwai zane akan sa, ka fara daga makdisi”sai suka fara da maza tsofafi wanda suke bakin gida. 7 sai yace masu: “sun lallata gidan da datti, sun cika wuraren bautan da gawa. Ku fito”sai suka fito cikin birnin).


SAFAR AL ADAD (5/11): (11 sai ubangiji yace ma Musa: “kayima bani isra'ila wasiyya kace masu: idan matar mutum tayi sabo ta ha'ince shi 13 dayin zina da wani mutum na daban, kuma al'amarin ya buya ga mijinta, kuma babu wani dalili akan su kuma ba'a kama su ba suna yin zinan 14 idan mujinta yayi kishi ya dawo daga rakiyan matar sa kuma ta kasance najasa, ko kuma yayi kishi akan matar shi duk da cewa me tsarki ce 15 to mutumin yazo yakai matan zuwa ga boka, kuma yazo da garin masara na yawan ifata goma (kamar lita biyu da rabi). Kada ya zuba mashi mai, kuma kada ya zuba mashi madara, saboda gabatarwa ne na kishi, gabatarwa na tunatarwa yana tunatar da zunubi. 16 sai bokan ya sanya matar ta tsuguna agaban ubangiji, 17 sai ya amshi ruwa me


tsarki a cikin kwarya na tire sai ya tsinci wasu tsakuwa na kasar gidan ya sanya cikin ruwan 18 ya bude kan matan, ya sanya a hannun ta gabatarwa na tunatarwa wanda shine gabatarwa na kishi, sai boka ya dauki ruwan la'ana da hannun sa me daci 19 yasa matan ta rantse da cewa: idan wani mutum daban be kwanta dake ba, kuma baki ha'inci mijinki ba, to ki barranta daga ruwan la'anta me daci wannan 20 amma idan kin ha'inci mijin ki kika kwanta da wani mutum wanda bashi ba 21 ubangiji ya sanya tsinuwar mutanen ki akanki, zai barranta daga gareki a lokacin da ubangiji ya sanya cinyan ki rube kuma cikinki ya kunbura. 22 kuwa wannan ruwa na la'ana ya shiga cikin hanjin ki domin yasa cikinki ya kunbura, da cinyarki ya rube.” Sai matan tace: Amin. Amin 23 sa'annan wannan boka ya rubuta wannan tsinuwa ajikin bango ya share shi da ruwa me daci; 24 ya shayar da matan wannan ruwan tsinuwa me daci sai ruwan rantsuwa ya shigeta domin ya sanya mata radadi. 25 sa'annan boka ya rike hannun matan ta gabatar da kishi, ya rinjayar da ita agaban ubangiji, sa'annan ya kaita zuwa wurin yanka. 26 kuma ya dibo gwargwadon kamdan hannun sa dayayi mata ya kona shi akan mayanka, bayan haka sai y aba matan ruwan tasha. 27 idan matar tayi zunubi ta ha'inci mijinta, to alokacin da take shan ruwna tana jawo tsinuwa ya sanya mata radadi sai ya kunbura mata ciki ya kuma rubar mata da cinya, sai matar ta zama tsinanniya a tsakiyan mutanen ta. 28 amma idan ta kasance barrantacciya me tsarki zata barranta tayi ciki).


A karshe inason fadi cewa dukkanin abunda muka Ambato cikin littafi me tsarki, domin manufan warware kulli da dimuwan wannan wanda suke zargin musulunci da shari'ar musulunci da abubuwa masu yaw aba tare da wani fuskan gaskiya ba kuma ba tare da dubi ba a farko ciki abunda littafi su me tsarki ya fadi. Lallai shari'ar musulunci ita kadai ce a fadin duniya cikin shari'u wacce take yaki da dukkanin abunda yake kawo kabilanci da banbanci a tsakanin mutane da cin dunkiyoyin su da satan su da daidaita su da ta'adi akan mutuncin su da abunda suka mallaka.


A lokacin da muka karanta cikin littafi me tsarki cikin safar al TASNIYA (23/19): (19 kada ka wajabta ma dan uwanka riba, riban azurfa, ko kuma riban abinci, ko kuma riban duk abunda ake sa masa riba 20 kawia ga bako ne zaka wajabtama riba, amma dan uwanka kada ka wajabta masa riba, domin ubangijin ka allanka yayi maka albarka).


A CIKIN SAFAR ALKHURUJ (3/22): (22 ko wace mata ta nemi daga makwabciyar ta da kuma bakuwar gidan ta kayan azurfa da kayan zinari da tufafi kuma tasanya shi akan yaranku maza da mata. Sais u sanya misrawa).


A CIKIN SAFAR ZAKARIYYA (14/1): (1 wata ran ace ga ubangijin ka zaizo sai ya raba rabonka a tsakiyan ka. Kuma dukkanin mutane su hadu dominn yin yaki, sai ka amshi birnin, sai ka rusa gidaje,ka wukanta mata, ka fitar da rabin birni zuwa ga fursinonin yaki).


To ina kafafen yada labarai na turawa suke wanda suke tuhumar shari'ar musulunci dare da rana da karya, daga ina zasu warware abunda muka karanta yanzu ya take hakkokin mutane a fili!! Sai dai sanin su a ciki cewa addini ne na gaskiya da kuma makircin su akan sa shi yasanya su suke jifansa da wannnan sharri domin su kori mutane daga gareshi musamman ma bayan sunga karbuwar da yake samu yadda ake shiga musulunci. Sai dai kash sun zama kamar me sanya hannun sa a gaban rana domin yak are hasken sa a duniya, Allah madaukaki yace:


“a lokacin da littafi daga wurin Allah yazo masu me gasgatawa ga abunda yake a gaba gare su kuma sun kasance gabanin haka suna tambaya game da wanda suka kafurta; a lokacin da abunda suka sani yazo masu sai suka kafurta dashi; tsinuwar Allah ta tabbata akan kafirai (89) tir da abunda suka siya da kawunan su dasu kafurce da abunda Allah ya saukar saboda hassadan Allah ya saukar da falalar sa akan wanda yaso cikin bayin sa; sai suka dawo da fushi akan fushi; kuma kafirai sunada azaba ta wulakanci (90) idan akace masu kubi abunda Allah ya saukar masu sai suce munyi imani da abunda aka saukar mana kuma suna kafurta da duk abunda bashi ba kuma shi gaskiya ne me gasgatawa ga abunda ke tare dasu; kace to dan me yasa kuke kashe annabawan Allah a baya idan kun kasance muminai (91) kuma hakika Musa yazo maku da hujjoji sa'annan kuma kuka riki dan maraki a bayan sa kuma kuna azzalumai (92)” (Suratul bakara 89-92)


Ina fadi da yakini cewa babu abunda zai ceci al'ummar duniya cikin halin da suke cikin na dimuwar da ya same su cikin dukkanin bangarori na halaye da zamantakewa da



Posts na kwanan nan

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A ...

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA