Labarai

WASIYYOYI GUDA GOMA DON KARIYA DAGA ANNOBA





Wallafar


Abdul-Razak Bn Abdul-Muhsin Al-badr


Allah yayi masa gafara da Mahaifansa





Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.


GABATARWA


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, yana amsa roqon wanda ya matsu idan ya roqeshi, kuma yana kai agaji ga wanda ya kirawo shi, kuma yana yaye Cuta, kuma yana yaye Baqin ciki, kuma zukata basa rayuwa sai da Anbatonsa, kuma babu wani Al-amari da zai afku sai da Izininsa, kuma ba'a iya tsira daga abun qi sai da Rahamarsa, kuma ba'a kiyaye wani abu sai da kiyayewarsa, kuma ba'a samun abunda akai guri sai da sawwaqewarsa, kuma ba'a samun rabauta sai da biyayya a gare shi.


Kuma na shaida babu abun bautawa da gaskiya sai Allah, shi kaxai bashi da abokin tarayya, Ubangijin talikai, kuma Ubangijin Mutanen farko da na Qarshe, kuma wanda yake tsaye da Sammai da Qassai.


Kuma Na shaida Cewa Annabi Muhammad Bawansa ne kuma Manzonsa, wanda ya aiko shi da littafi Mai bayani, da kuma tafarki Madaidaici, Allah kayi salati da aminci a gare shi, kuma kayi ga Alayansa da sahabbansa baki xaya


Bayan haka


Waxan nan wasu wasiyyoyi ne Masu anfani zan faxesu sabida abunda ya faru na tsoratar Mutane a waxan nan kwanaki saboda Annoba wacce ake kira (CORONA).


Ina roqon Allah SWT da ya xauke mana ita da baki xayan Musulmai ko a ina suke dukkan Cuta da Bala'i, kuma ya yaye mana tsanani da Cututtuka, kuma ya kiyaye mu baki xayanmu da abunda yake kiyaye bayinsa nagartattu, lallai shi majivincin hakan kuma mai iko akansa


1- Mai ya kamata ace kafin saukar Bala'i?


Daga Usaman Bn Affan -Allah ya yarda dashi- ya ce: na ji Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


"Duk wanda ya ce: da Sunan Allah wanda babu abunda yake cutarwa in an ambaci sunansa a sama ne ko kuma a Qasa, kuma shi mai ji ne Masani" Sau Uku babu abunda zai same shi na Faja'ar Annoba har sai ya wayi gari, kuma duk wanda ya faxeta lkacin da ya wayi gari Sau uku babu abun da zai same shi na Faji'ar Bala'i har sai yayi Maraice


Abu Daud Al-Tayalisi Ya Rawaito shi da waninsa


2- yawaita faxin: "Babu wani Ubangiji Sai kai tsarki ya tabbata a gareka lallai kuma ni nakasance cikin Azzalumai"


Fadin Allah maigirma da Daukaka:


Kuma mai kifi a sã'ad da ya tafi yanã mai hushi, sai ya yi zaton cẽwa ba zã Mu ƙuƙunta masa ba. Sai ya yi kira a cikin duffai cẽwa, "Bãbu abĩn bautãwa fãce Kai. Tsarki ya tabbata a gare Ka. Lalle ne nĩ, na kasance daga azzãlumai."


(Al-anbiya'a: 87,88)


Al-hafiz Ibn Kathir -Allah ya yarda da shi- ya ce: acikin "Tafsirinsa" wajen faxin Allah SWT: "Kuma da haka ne muke tseratar da Muminai"


"Ai idan suka kasance cikin tsanani kuma suka roqe mu suna masu komawa zuwa garemu, musamman idan sukai addu'a da wannan Addu'ar a lokacin faruwar Bala'in


Sannan ya kawo wani hadsi daga Annabi -Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi -ya ce:


"Addu'ar Annabi yunus da yai Addu'a da ita kuma a halin yana cikin Kifi: "Babu Wani ubangiji sai kai tsarki ya tabbata a gareka lallai ni ina cikin waxan da suka zalunci kansu" ba bu wani Mutum da zai yi Addu'a da ita a cikin wani abu face sai Allah ya Amsa Masa"


[Imam Ahmad da Tirmizi ne sukai rawaito shi]


Ibn Kayyim Allah yayi masa rahama yana cewa a cikin "Al-fawa'id)


"saboda ba'a ije tsananin Duniya da kamar wannan Tauhidin, kuma saboda hakan ta kasance Addu'ar kawar da bacin rai da yin Tauhidi, Kuma da Addu'ar Annabi yunus wacce babu wani mai damuwa da zai Addu'a da ita face sai Allah ya yaye masa saboda Tauhidi saboda babu abunda yake jefa Mutum cikin Manyan Vacin Rai sai Shirka, kuma babu Mai ceto shi daga ciki sai tauhidi, domin shi ne Mai tsorata Halitta kuma ma tserar da ita da kuma kareta da Katangeta da agaza mata, kuma dace da Allah ne"


3- Neman tsari daga Wahalarwar Bala'i


Abu Huraira -Allah ya yarda da shi-


"Mazon Allah SAW ya kasance yana neman tsari daga Wahalarwar Bala'i, da faxawa Tavewa, da Mummunar Makoma, da Dariyar abokan gaba"


Daga Abu Huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


"Ka nemi tsari da Allah daga Wahalar Bala'i, da Fadawa tabewa, da Mummunan Rabo, da Kuma Dariyar Makiya"


{Bukhari ne ya rawaito su}


4-Kiyayewa kan Addu'a futa daga Gida


Da hadisin Abu Musa Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


"Idan Mutum ya Futa daga gidan sa sai ya ce: "da sunan Allah, na dogara ga Allah, Babu Dabara babu Karfi sa na Allah" ya ce: za'a ce masa a lokacin Ka shiriya kuma an isar maka kuma an kareka, sai shaixanu su nisance shi, sai wani Shaixani ya ce da shi: ta ya ya zaka iyawa Mutumin da aka shiryar da shi kuma aka isar nasa kuma aka kare shi"?


Abu Daud Ya Rawaito shi


5- Roqon Allah lafiya safiya da Maraice


Daga Abdullahi Bn Umar -Allah ya yarda da shi- ya ce:


Annabi bai kasance ba yana barin wadan nan Addu'o'i lokacin da ya wayi gari ko yayi yammaci: "Allahumma inn as'alukal afiya fid-dunya wal akhira, Allahumma inni as'alukal afwa wal afiya fi dini wa dunyaya wa ahli wa mali, Allahumma astur aurati, wa aamin rau'ati, Allahumma ihfazni min baini yadayya wa min khalfi, wa an yamini, wa an shamali, wa min fauƙi, wa a'uzu bi azamatika an ugtala min tahti"


Ahmad da waninsa suka rawaito shi


6. Yawaita Addu'a


An karbo daga Ibn Umar Allah ya yarda da su,ya ce: Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:


"Duk wanda aka buxewa Qofar Addu'a daga cikinku to za'a buxe masa Qofofin Rahama, kuma ba'a tava tambayar Allah wani abu ba ai abunda ya fi so sama da a roqe shi lafiya"


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


"Lallai Addu'a tana anfani ga abunda ya sauka da ma wanda bai sauka ba, saboda haka ku bayin Allah na horeku da Addu'a"


Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi


7- Nisantar Wuraren da Annobar take ciki


An rawaito daga Abdullahi Bn Amir -Allah ya yarda da su-: "cewa Umar -Allah ya yarda da shi ya futo zuwa Sham yayin da ya kasance a Sarg sai aka sanar da shi cewa Annoba ta faru a Sham, sai Abdulrahman Bn Auf ya bashi labarin cewa Manzon Allah SAW ya ce:


"Idan kuka ji faruwar Annoba a wani gari, to kada ku shige shi, kuma idan ta faru a gari kuna cikinsa, to kada ku futa daga cikinsa"


Da hadisin Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


"Kada a haxa Mara lafiya da Mai Lafiya"


[Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi


8- Aikata Alkhairi da kuma iya yi wajen kyautatawa


An karbo daga Anas Allah ya yarda da su,ya ce: Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:


"Aikin Alkhairi yana kariya daga Mummunar Mutuwa, da Rashin lafiya, da kuma hallaka, kuma Ma'abota Alkairi a Duniya su ne Ma'abotan Alkairi a Lahira"


Hakim ne ya Rawaito shi


Imam Dan Qayyim Allah ya yi masa Rahama ya ce:


"Kuma yana daga cikin Magungunan rashin lafiya aikata Alkairi da kyautatawa da kuma Zikiri da Addu'a da Qanqan da kai, da komawa zuwa ga Allah, da Tuba, saboda waxan nan al'amura suna da Tasiri wajen kau da Illoli, da kuma samun Waraka; Sunfi Magungunan Xabi'a Girma, sai dai gwargwadon shiryawa rai da kuma yadda ta karvesu, da kuma Aqidarta cikin hakan da anfanarwar su"


Zaad Al'Ma'ad


9-Tsayuwar Dare


Da Hadisin Bilal Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


"Na Horeku da tsayuwar dare, saboda ita ce Xabi'ar Mutanen Kirki da suka gabaceku, Kuma cewa tsayuwar Dare tana kusanta Mutum da Allah, Kuma tana hana Zunubai, kuma tana kankare Xunubai, kuma tana korar Shaixanu daga jiki"


Tirmizi da Ahmad sun rawaito shi


10- RUFE QORAI DA RUFE RANDA


An karbo daga Jundubi Dan Abbdullah Allah ya kara yarda a gare shi, ya ce: Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce:


"Ku rufe Randa, Kuma ku daure salka, saboda a shekara akawi wani dare xaya da Allah yake Saukar da Bala'ai a cikinsa duk Kwaryar da ya wuce ta ba'a rufe ba, ko Salka ba tare da xaure bakinta ba to Annobar zata Sauka a cikinta"


Muslim ne ya rawaito shi


Imam Dan Qayyim Allah ya yi masa Rahama ya ce:


"Kuma Wannan yana daga cikin abunda Malaman lafiya da Masanansu basa iya samunsa"


Zaad Al'Ma'ad


A Qarshe ya Wajaba kan kowane Mumini da ya fawwala Al'amarinsa ga Allah SWT yana mai kwaxayin falalarsa, kuma yana fatan kyautarsa, kuma yana mai dogara a gare shi, saboda baki dayan Al'amura a hannun Allah suke, Kuma dole ne subi tsarawarsa, da yadda ya hore su


Kuma yayi Qoqarin karvar abunda ya same shi da haquri da neman Ladan Allah, Saboda Allah SWT yayi Alqawarin lada da rabo mai yawa da duk wanda yayi haquri Saboda ya ce:


"Lallai Kaxai ana cikawa Masu haquri ladansu ba tare da Hisabi ba"


Al-zumar: 10


An rawaito daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- cewa ta tanbayi Annabi SAW game da Annoba, sai ya ce:


"Cewa ita wata Azaba ce da Allah yake saukarwa wanda ya so, saboda haka Allah ya sanya ta Rahama ce ga Muminai, kuma babu Bawan da zai faxa Annoba, ya zauna a garinta yana Mai haquri, yana sane da cewa shi babu abunda zai same shi sai abunda Allah ya rubuta Masa shi, face sai ya kasance yana da kwatankwacin ladan Shahidi"


Buhari ne ya rawaito shi


Kuma ina roqon Allah ya datar damu baki xaya cikin abunda yake so na Ayyuka nagari, da kuma kyawawan Maganganu, saboda shi mai faxar gaskiya, kuma shi yake shiryarwa zuwa Tafarki


Kuma dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai, kuma tsira da Aminci su tabbata ga Annabinmu Muhammad da Alayansa da Sahabbansa ka Amince su



Posts na kwanan nan

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A ...

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA