5. Manzon Allah s.a.w yana bayyana soyayyar sa ga
iyalan sa:
Ya kasance manzon Allah s.a.w baya samun nauyi a zuciya
wurin bayyana soyayyar sa ga iyalan sa hasalima ya dauki
hakan cikin kyawawan dabi'u da kuma kyautata zaman takewa
da tarayya, kuma musamman ma kasancewar an aiko shi cikin
al'ummar jahilai wanda basa ganin mace da wani kima, Aisha
Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ banyi kishi ba akan matan manzon Allah s.a.w sai akan
Khadija kawai kuma ban risketa ta mutu gabanin manzon
Allah s.a.w ya aure ni. Sai tace: manzon Allah s.a.w ya
kasance idan ya yanka akuya sai yace: ko aika ta zuwa ga
kawayen Khadija. Sai tace: sai wata rana kishinta ya
kamani sai nace: Khadija kuma?!! Sai manzon Allah s.a.w
yace: “ lallai ni an azurtani da soyayyanta ” muslim ne ya
rawaito shi.
An kuma karbo daga Aisha Allah ya kara mata yarda tace:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance idan aka abmaci kahdija sai
ya yabeta ya kuma kyautata yabon nata sai tace: sai wata rana
kishin hakan ya kama ni sai nace ya naga kana yawan
anbatonta ne bayan Allah ya canza maka ita da wacce tafita
alheri! Sai yace: “ Allah be canzamun da wacce tafita alheri
ba: hakika tayi imani dani a lokacin da mutane suka
kafurta dani kuma ta gasgatani a lokacin da mutane suka
karyata ni, kuma ta yalwatani da dukiyar ta a lokacin da
mutane suka hanani nasu, kuma Allah ya azurtani da yaro
daga dagare a lokacin daya hanani yara daga sauran mata
” Ahmad ne ya rawaito shi, kuma shu'aibu al arnu'ut yace:
wannan hadisi ne ingantacce kuma silsilan sa ingantacce ne
cikin littafin mutabi'at.
6. Manzon Allah s.a.w yana tsabta domin kyautata
zama na auratayya:
Karantarwan musulunci yana nuni akan cewa Allah madaukaki
me kyau ne kuma yana son kwalliya kuma me karamci ne da
kyauta kuma yana son masu karamci da kyauta, me tsabta ne
kuma yana son masu tsabta kamar yadda manzon Allah s.a.w
ya bada labari kuma wannan umurni ne ga musulmi ya kasance
cikin yanayi me kyau da shiga me kyau tare da mutane
musamman ga iyalin sa, saboda haka ne manzon Allah s.a.w
yayi umurni da himmatuwa da wannan bangare kuma ya
jaddada hakan:
“ idan dayanku ya kusanci iyalin sa kuma yana so ya koma
to yayi alwalla ” Muslim ne ya rawaito shi.
Ya kuma kara fadi har wayau: “ wannan shi yafi tsabta da
tsari da kuma tsarki ” abu dawud ne ya rawaito shi kuma
albani ya inganta shi.
7. Manzon Allah yana musayar soyayya da iyalin sa:
Lallai soyayya ta hakika ita cw wadda take lizimtar mutum
cikin dukkanin halinsa baya canzawa cikin wani lokaci kuma
wannan shine halin manzon Allah s.a.w tare da iyalin sa yadda
Aisha Allah ya kara mata yarda take cewa:
“ na ksance ina wanka tare da manzon Allah s.a.w cikin
kwarya daya, dukkanin mu muna da janaba. Ya kasance
yana umurtata dana daura zani daga kirjina zuwa gwewata
sai yayi wasa dani na debe sha'awa ina cikin al'ada. Kuma
ya kasance yana fitomun da kansa ya mikomun yana cikin
ittikafi na wanke masa ina cikin al'ada ta ” buhari ne ya
rawaito shi.
8. Manzon Allah s.a.w baya yada sirrin iyalan sa:
Lallai alaka ta aure da abunda ke cikin ta sirri ne cikin sirrori
wanda musulunci ya tsananta akan kiyaye su da kuma rashin
yada su musamman ma irin wanda babu kunya a cikin jin su
kuma tana tafiyar da mutuncin mutum, manzon Allah s.a.w
yana cewa:
“ lallai daga cikin mafiya sharrin mutane a wurin Allah
ranan alkiyama shine mutumin da yake kwanciya da matar
sa sai yazo ya yada sirrin ta ” muslim ne ya rawaito shi.
9. Manzon Allah s.a.w yana magana ta soyayya da ban
mamaki ga matan sa:
Hakika manzon Allah s.a.w ya kasance me saukin hali ne me
kyauwun siffa ne yana jiyar da iyalan sa magana wacce take
nuna soyayya da tausayi kuma yana kiran ko wanne daga cikin
su da abunda yake so na sunaye ya kasance yana kiran Aisha
Allah ya kara mata yarda da suna:
“ yake iyar fara ” kuma ya kaiwa matuka wurin tausasa masu
magana na soyayya ya wani lokaci kuma ya kankanta sunan su
domin ya bayyana masu abunda zuciyar sa yake masu suna
dashi na soyayya sai yace “ yake iyar Aisha… ” Muslim ne ya
rawaito shi.
10. Manzon Allah s.a.w yana kusantar iyalan sa hatta a
lokacin uziri na shari'a:
Hatta a lokacin uziri na shari'a ga iyalan say a kasance yana
zama dasu kuma yaci abinci tare dasu da shan ruwa da kuma
wasa dasu na debe sha'awa ba tare dayin jima'i dasu ba domin
ya kosar da raunin zuciyar su kuma ya bayyana hukunce
hukunce na shari'a cikin irin wannan matsaloli, da kuma abunda
ya halatta ga miji tare iyalin sa da kuma abunda zayyi daidai da
halinta da yanayin ta, wanda yake sabanin karantarwa da kuma
shari'a na littafi me tsarki na kiristoci wacce take mace me
al'ada a matsayin najasa kuma tana umurtan miji da nisantar
matanshi a halin uziri na shari'a (ka duba cikin littafin safar
allaween 15:19), Aisha uwar muminai Allah ya kara mata yarda
tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yana wasa da ita na debe
kewa a cikin rigan ciki na mutum ina cikin al'ada, sai dai
kuma shi yafi ku mallakar kansa cikin halin da kame kansa
” baihaqi ne ya rawaito shi.
11. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana kiyaye yanayi
na damuwar iyalan sa:
Bukatar mace ga namiji da kuma bukatar maniji ga mace abune
na fidira kuma dawwamamme bawai abu bane na dan lokaci
kamar sauran halittu na daban wanda suke da wani lokata
wanda suke aure a cikin sa sai kuma a rabu kowa ya tafi
harkokin sa, kada na miji ya kaurace masu alokacin uzirin su na
shari'a ya kwana tare dasu kuma yaji dadi dasu suma suji dadi
dashi banda yin jima'a, Aisha Allah ya kara mata yarda tana
cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yan asallar dare ni kuma
ina gefen sa kuma ina cikin al'ada na lulluba da mayafi
wanda akayishi daga sufi shima ya lullaba da gefen wannan
mayafi “ muslim ne ya rawaito shi.
12. Manzon Allah s.aw ya kasance yana debe kewa tare
da iyalan sa:
Lallai dukkanin ayyukan sa baki dayan su karantarwa ne ga
al'ummar sa da kuma bayanin hukunce hukunce na fiqihu
wanda acikin su mutanen sa zasu iya aiwatar da rayuwan su na
addini, was an da yakeyi da iyan san a debe kewa a lokacin
al'adar su da bacci tare dasu yana nuni ne ga hakan a shari'an ce
na bayanin tsarkin jikin mace da kuma tsarkin wurinta da
halaccin bacci tare da ita cikin bargo daya da sauran sun a
hukunce hukunce wanda za'a ciro daga cikin wannan aiki nasa,
Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance yana kishin gida akan
kirjina ina al'ada ya karanta alkur'ani ” Muslim ne ya
rawaito shi.
13. Manzon Allah s.a.w yana wanka da iyalin sa:
Lallai manzon Allah s.a.w ya kasance me kwadayin shigar da
farin ciki ga zuciyar iyalan sa cikin dukkanin yanayi hatta a
bayan gama jima'I wanda mafiya yawan lokuta mutum yana
kasancewa ne a cikin su karancin nishadi na jikin sa da kuma
rashin karfi na jiki da sanyi manzon Allah s.a.w ya kasance yan
awanka tare da iyalin sa kuma harda wasa da zaulaya a lokacin
wankan, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ na kasance ina wanka ni da manzon Allah s.a.w cikin
kwarya daya, muna rigangeniya wani lokaci na rigashi
wani lokaci ya rigani ta fuskan wasa, har yace a cikin wasa:
ki ragemun ruwan. Nima nace: ka ragemun ruwan ” nisa'i
ne ya rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
14. Manzon Allah s.a.w yana sunbatar iyalin sa:
Debe kewa lamuni ne ga ci gaban rayuwan ma'aurata bayan
gam da katar din Allah kuma da biyan dukkanin abunda yake
fado mata ta hanyar wasa yan kadan da kuma magana yar
kadan zaka samu soyayyar iyalin ka kuma zaka kashe mata
kishin ruwan ta na damuwa kuma ka zama dalili na tabbatan
kwanciyar hankalin su hakika manzon Allah s.a.w ya kasance
yana lura da wannan bangare dan karami baya mantawa dashi,
Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa: “ manzon Allah
yazo zai sunbace ni sai nace masa ina azumi fa sai yacemun
ai nima ina azumin sai ya sun bace ni. Nisa'i da Ahmad da
Ibn kuzaima ne suka rawaito shi kuma hadisi ne ingantacce.
• Manzon Allah s.a.w tare da iyalan sa ta
bangaren dan adamtaka:
• Manzon Allah s.a.w mutum ne kamar sauran mutane an
bashi falala ne akan mutane da annabta ya kuma samu daukaka
ne akan su da isar da sako kuma an aiko shi zuwa garesu domin
ya fitar dasu daga bautan bayi zuwa bautan Ubangijin bayi
kuma ya sanar dasu shari'ar Allah wannan falala ce ta Allah
wanda yake ba wanda yaso cikin bayin sa saboda fadin sa
madaukaki:
“ kace masu ni ba komai bane face mutum irin ku anyi
mani wahayi cewa Allahn ku shi daya ne duk wanda yake
kwadayin haduwa da ubangijin sa sai ya aikata ayyuka na
kwarai kuma kada ya hada Allah dawani cikin ibadar sa ”
suratul kahafi ayata 110.
• Bashi da wani siffa na allantaka besan gaibu ba kuma
baya amfanar wa baya kuma cutarwa kuma baya juya komai
cikin duniyan nan, Allah madaukaki yana cewa akan sa:
“ kace masu bana mallakawa kaina amfani ko kuma
cutarwa sai abunda Allah yaso kuma da ace nasan gaibu da
ban yawaita aikata alheri kuma da wani mummunan abu
be same nib a nib a komai bane face me gargadi da bishara
ga mutane muminai ” suratul a'araf ayata 188.
• Duk da falalar sa da daukakan sa da kuma matsayin sa
da darajar daya samu da sakon annabta yana kin a wuce gona
da iri akan yabon sa ko kuma a kaishi matsayi wanda ba
matsayin bawa ba ga Allah wanda Allah ya zaban masa shi
domin girmamashi da ita, manzon Allah s.a.w yana cewa:
“ kada ku rika kurantani kamar yadda kiristoci suka
koranta dan maryan, lallai ni bawa ne, dan haka kuce:
bawan Allah kuma manzon sa ” buhari ne ya rawaito shi.
• Siffofin sa na mutum ne dukanin abunda ke gudana akan
mutane ya gudana masa masu bijirowa, shi bame dawwama
bane cikin wannan duniya, Allah madaukaki yace akan sa:
“ Muhammadu be kasance ba face manzo wanda manzanni
sun gabata gabanin sa yanzu shin idan yam utu ko kuma
aka kashe shi zaku juya akan duga duganku ne? duk
wanda ya juya akan duga dugan sa to bazai cutar da Allah
ba da komai kuma da sannu Allah zai sakama masu godiya
” suratu al'imran ayata 144.
• Abunda yake samun su na cuta da rashin lafiya shima
yana samun sa yana rashin lafiya da cuta kuma yana neman
magani, Abdullahi dan mas'ud yana cewa:
“ na shiga wurin manzon Allah s.a.w yana zazzabi sai nace:
ya manzon Allah kana zazzabi ne me zafi? Sai yace: “ eh
mana ina zazzabi kamar yadda wanin ku yake yi ” sai nace:
hakan kana da lada biyu kenan? Sai yace: eh kwarai haka
ne, babu wani musulmi wanda wata cuta zata same shi na
kaya ne zuwa saman ta face Allah ya kankare masa
zunuban sa dashi kamar yadda bishaya take kankare
ganyen ta ” buhari ne ya rawaito shi.
Abin nufi cikin wannan hadisi wanda ya gabata cikin fadin sa
cewa: hakan kanada lada biyu kenan? Ma'anar hakan zai fito
fili ne cikin hadisi me girma wanda Sa'ad dan Abi waqqas
Allah ya kara masa yarda yace: “ nace ya manzon Allah
wanene yafi mutane girman bala'i sai yace “ annabawa sai
wanda suke biye masu a wurin imani haka har zuwa kasa
ana rajabtan mutum ne gwargwaon addinin sa idan
addinin sa ya kasance tsantsa to bala'in sa zaifi tsanani idan
kuma akwai tauni a cikin addinin sa za'a jarabe sa ne
gwargwadon addinin sa kamar yadda bala'i yake wanke
bawa har sai ya barshi yana tafiya a kasa bashi da zunubi
ko daya ” “ hadisi ne ingantacce Tirmizi ne ya rawato shi.
• Yana so kuma yana ki, Umar dan kaddab yana cewa
wani mutum yazo wurin manzon Allah s.a.w sai yace:
“ bani da abunda zan baka amma ka dan nemo bashi har
na samu abunda zan baka ” sai Umar dan kaddab yace: ya
manzon Allah baka mahaifi na da mahaifiyata fansa
agareka Allah be daura maka wannan b aka bashi abunda
kake dashi idan baka da komai kada ka daurama kanka sai
yace: sai manzon Allah s.a.w yaki maganar, sai Umar yace:
idan yayi fushi kuma ana gane hakan daga fuskar sa sai
wani mutum ya mike cikin mutanen madina yace: na bada
mahaifin ada mahaifiyana fansa a gareka ya manzon Allah
ka bayar kada kaji tsoron takaitawa domin wani me mulki
sai yace: sai manzon Allah s.a.w yayi murmushi yace: “ da
wannan ne aka umurce ni ” dabari ne ya rawaito hadisin cikin
littafin tahazib da kuma Barraz cikin littafin san a sanadi.
• Yana murna kuma yana bakin ciki, a lokacin da yaron sa
Ibrahim ya rasu sai manzon Allah yayi kuka sai me ta'aziyya
yace masa:
“ kodai Abubakr ko Umar lallai kaine mafi cancantan
wanda Allah ya girmama hakkin sa sai manzon Allah s.aw
yace: “ lallai idanu sunayin hawaye kuma zuciya tana bakin
ciki amma bazamu fadi abunda zai fusata Ubangijin mu ba
badan yayi alkawari na gaskiya ba da kuma lokaci na taro
kuma lallai karshe yana bin na farko ne da mun samu akan
ya Ibrahim mafificin abunda muka samu kuma lallai muna
bakin ciki dakai ” Ibn majjah ne ya rawaito shi kuma albani ya
ingantashi.
• Yana dariya kuma yana kuka, Usama dan zaid yace wani
yaro na daya daga cikin yaran manzon Allah s.a.w mata ya
rasu, sai ta aika masa domin yazo mata, sai ya aiko mata:
“ lallai ga abun ya Allah ya amsa nashi ne kuma abunda ya
bayar nashi ne kuma dukkan komai a wurin sa yana
kasancewa ne zuwa wani lokaci sananne kiyi hakuri kuma
jure ” .
Sai ta aiko masa tayi masa rantsuwa sai manzon Allah s.a.w
ya tashi sai na mike nima nabishi da mu'azu dan jabal da
ubayyu dan ka'ab da ubadata dan samit a lokacin da muka
shiga sai manzon Allah s.a.w ya dauki yaron ransa yana
jijjiga da motsi a cikin zuciyar sa sai yace: ran ya fita sai
manzon Allah s.a.w yayi kuka sai ubada dan samit yace
masa: menene wannan ya manzon Allah? Sai yace: “
rahama ce wanda Allah ya sanya cikin zukatan dan adam
kuma lallai Allah yanayin rahama ne ga bayin sa musu jin
tausayi ” buhari da muslim ne suka rawaito shi da kuma Ibn
majjah kuma lafazin nashi ne.
• Yana farin ciki kuma yana jin radadi , a lokacin da jafar
yazo gun manzon Allah s.a.w daga kasan habasha, sai idanun
manzon Allah suka gashi sai yace: “ bansan da zuwan jafar
ba shin dashi ne zanyi farin ciki ko kuma da bude garin
khaibara? ” hakan sai yayi daidai da bude garin khaibara.
Silsilatul sahiha.
• Yana rafkana kuma yana mantuwa, hakika yayi
mantuwa cikin sallar sa kuma aka tunatar dashi, Abdullahi dan
Umar yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w yayi mana sallah cikin daya daga
sallar azahar ko kuma la'asar raka'a biyu sai zul yadaini
yace: ya manzon Allah ka manta ne ko kuma an rage
raka'ar sallar ne? sai yace: “ banyi mantuwa ba kuma ba'a
rage raka'ar sallar ba ” . Sai yace: ai raka'a biyu kayi, sai
ya juyo ya kalli mutane yace: “ shin abunda zul yadaini ya
fada haka ne? ” sai suka ce: eh haka ne, sai ya mike ya ciko
raka'a biyun sa'annan yayi sujjada biyu na rafkanuwa ”
buhari ne ya rawaito shi.
• Kuma ba ma'asumi bane cikin mu'amular sa da ijtihadin
san a mutum ta yadda yana dacewa yana kuma yin kuskure, sai
dai ma'asumi ne cikin abunda yake isarwa na wahayi akan
Allah, hakika manzon Allah ya wuce wurin bishiyan dabino sai
yaga mutane suna barbarian dabino, sai yace:
“ menene haka suke aikatawa? ” sai sukace suna daukan
namiji ne su hadashi da mace, sai yace: “ bana tunanin
hakan yana amfanar da wani abu ” sai hakan ya isa zuwa
garesu, sai suka daina aikata hakan, sai dabinon su ya
lalace suka sanar da manzon Allah s.a.w sai yace: “ ai
tsammani ne, idan yana amfanar da wani abu ku aikata, ni
mutum ne irin ku, kuma me zato yana dace wa kuma
yanayin kuskure, sai dai bance maku Allah yace ba, saboda
bazanyi karya ga Allah ba ” muslim ne ya rawaito shi.
• Manzon Allah s.a.w yana tsayawa a matsayin mutum
cikin mu'amalar sa da mutane, yadda yake cewa:
“ ya Allah! Lallai Muhammad mutum ne yana fushi kamar
yadda mutane ke fushikuma lallai na rike alkawari agunka
wanda baka sabamun shi ba, duk wani muminin da na
cutar dashi ko kuma na zage shi ko na duke shi kasanya
hakan ya zama kaffara ce a gareshi da kuma kusanci
wanda zaka kusanto shi zuwa gareka dashi rana alkiyama ”
muslim ne ya rawaito shi.
• Kuma mutum ne cikin hukuncin sa dayake masu da
kuma akan sa, yadda yake cewa:
“ lallai ni mutum ne kuma kuna kawomun sa'in san ku na
maku hukunci, me yuwa wasu sufi wasu karfin hujja sai na
bashi gaskiya na hukunta mashi wannan abu gwargwadon
abunda naji, to duk wanda ya bashi hakkin dan uwan sa
kada ya amsa saboda yanki ne na wuta nabashi ” buhari ne
ya rawaito shi.
• Kuma mutum ne cikin rayuwan sa na al'umma yana aure
kuma yanason zuriya kmaar yadda sauran annabawa suke
wanda suka gabace shi, Alah madaukaki yana cewa:
“ hakika mun aika da manzanni gabanin ka kuma mun
sanya masu mata da zurriyya, kuma babu wani manzo da
zai iya zuwa da wata aya sai da izinin Allah, ko wani ajali
an rubuta shi cikin littafi ” suratul ra'ad ayata 38.
• Kuma a wannan gabar zamu kawo wasu bangarori na
mu'amalar sa a matsayin mutum da iyalan sa:
1. Manzon Allah me karamci yana yin yafiya game da
kurakuran iyalan sa:
Kishi dabi'a ce ta mutum manzon Allah s.a.w ya kasance yana
tunkaran sa daga iyalan sa da budaddiyar zuciya annan kuma ya
magance shi da hikima da kuma hakuri, Anas Allah ya kara
masa yarda yana cewa: manzon Allah s.a.w ya kasance a
wurin daya daga cikin matan sa, sai daya daga cikin su ta
aika masa da kwano da abinci aciki, wai matar dayake
gunta ta bigi hannun dan sakon sai wannan kwano ya fadi
ya fashe, sai manzon Allah s.a.w ya tattara shi sai ya fara
tattara abincin cikin kwanon yana cewa: (mahaifiyar ku
tana kishi) sa'annan ya tsayar da wannan dan sako har sai
da aka kawo sabon kwano irin wannan wanda yake gidan
wannan mata inda yake, sai yaba wannan dan sakon
wannan kwanon me kyau ya rike wannan wanda ya fashe a
wannan gidan wacce ta fasa. Buhari ne ya rawaito shi.
2. Manzon Allah me karamci ya kasance yana cika
alakwari ga iyalan sa:
Cika alkawari da kiyaye soyayya da kuma rashin inkarin me
kyau sifface wacce take nuna akan asalin me ita da kuma
kyauwun halayen sa hakika manzon Allah s.a.w ya kasance:
“ idan aka ambaci Khadija sai ya yabe ta kuma ya kyautata
yabon ta, sai yace: wata rana sai kishi ya kamani akan sai
nace me yasa kake yawan ambaton me jan haba bayan
Allah ya canza maka da wacce ta fita alheri. Sai yace Allah
be canzamun ba da wanda tafita alheri ba hakika tayi
imani dani a lokacin da mutane suka kafurce mun kuma ta
gasgatani a lokacin da mutane suka karyta ni, kuma ta
yalwatamun da dukiyar ta a lokacin da suka haramtamun
dukiyar su kuma Allah ya azurtani da yaronta a lokacin
daya haramtamun yaron sauran mata. Bayanin ingancin
hadisin ya gabata a baya.
3. Manzon Allah s.a.w yayi mu'ama me kokoluwan
kyau da iyalan sa:
Cikin rayuwan sa baki daya tun gabanin bashi annabta zuwa
bayan bashi annabta ba'a taba hakaitowa ba cewa ya daga
hannun sa masu albarka ya duki mace wannan kenan mu'amalar
sa da jama'an gari yaya kake gani to zai kasance tare da iyalan
sa kuma mun sani cewa gidan ma'aurata dai baka raba shi da
yar matsala kuma gidan manzon Allah s.a.w irin haka ne shima
bawai ya sabama asali bane amma kasancewar be taba dukan
daya daga cikin matar sa ba ko kuma ya fada mata magana
mara dadi Aisha Allaha ya kara mata yarda tace:
“ manzon Allah be taba dukan wata mace ba ko sau daya ”
sahihu Ibn hibban da baihaqi da nasa'I ne suka rawaito shi.
Kuma Aisha ta kara fadi har wayau Allah ya kara mata yarda: “
be taba dukan wani dan aiki ba ko sau daya ko kuma wata
mace, kuma manzon Allah be taba dukan wani abu ba da
hannun sa ko sau daya sai dai yayi jihadi domin Allah,
kuma ba'a taba bashi zabi ba tsakanin abu biyu face ya
zabi wanda yafi sauki daga cikin su matukar bas abo bane
hakan, idan hakan ya kasance sabo ne to ya kasance wanda
yafi koma nisantar haka, kuma manzon Allah s.a.w be taba
daukan fansa ba akan laifin da akayi mashi a karon kansa
sai dai idan an keta hurumin Allah madaukaki sai ya dau
fansa akan hakan ” silsilatul sahiha.
Taya hakan bazai faru ba bayan shine wanda aka aiko shi
rahama ga talikai, wannan Sahal ne dan Sa'ad yana cewa: “
naga manzon Allah s.a.w a lokacin da aka karya masa
hakoran sa na gaba da ji masa rauni a fuska aka kuma
karya kariyan da yasa akai, lallai nasan wanda ya wanke
masa jinin fuskan sa, da wanda yake zuba masa ruwa da
abunda da aka sanya masa a raunin har jinin ya tsaya,
fadima diyar manzon Allah s.a.w ta kasance tana wanke
jinin fuskan sa Aliyu kuma yana zuba mata ruwa, bayan ta
wanke jinin fuskan mahaifinta sai ta kona ciyawa bayan ya
zama toka sai ta dauka wannan toka ta sanya masa a
fuskan say a tsayar da wannan jini, sa'annan yace: a
wannan rana fushin Allah ya tsananta akan mutanen da
suka jima fuskan manzon Allah s.a.w rauni, sa'annan ya
zauna na tsawan awa daya, sai yace: ya Allah ya gafartawa
mutane na lallai basu sani bane ” silsilatul sahiha.
4. Manzon Allah s.a.w yana tausayin iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance mijin mata tara wanda yake da
dalilai da kuma abunda ya sanya shi hakan daga cikin dalilan
hakan shine rahama da tausayi da kuma sanin da aka masa da
kyautatawa ga wanda yayi imani dashi ya kuma bishi ya kuma
hadu da cutarwa ta sanadiyyar haka daga cikin irin wannan
dalili ne yasa ya aure Saudat diyar zam'ata Allah ya kara mata
tana da shekaru hamsin da biyar a lokacin kuma hakika
mutanen makka sunyi mamaki akan wannan aure saboda bata
kasance ba tanada kyau ko kuma wani abunda da maza suke so
ba tare da ita kuma tana da yara biyar amma tausayin sa na
mutum ya sanya tausayama halin ta, da kuma tausayi akanta da
karramata da kuma dauke mata hatsarin dake biye da ita na
dawowan ta daga habasha da kuma rasuwan mijin ta, manzon
Allah yaso ya sake ta bayan wasu lokuta masu yawa saboda
tausayin dayake yi nata na ganin kada ya daura mata nauyi na
rayuwan aure wanda bazata iya dauka ba amma alokacin da taji
haka sai tace manzon Allah s.a.w: kada ka sake ni ka rike, ka
sanya ranaku na ga Aisha, sai ya aikata hakan sai aya ya sauka
cewa:
“ babu laifi a garesu da suyi sulhu atsakanin su kuma sulhu
alheri ne ” saboda kwadayin da takeyi na ganin an tashe ta
cikin matan manzon Allah s.a.w ranan alkiyama ” . Tirmizi
ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
5. Manzon Allah s.a.w da rahamar sa ga iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya shiga masallaci sai yaga igiya an
daura su a tsakanin ginshikin masallaci guda biyu sai yace:
wannan igiyar kuma fa, sai sukace: igiyar Zainab ce ta
daura idan tana salla ta gaji sai ta jingina ajiki domin ta
dawo cikin nishadin ta, sai manzon Allah s.a.w yace: “ ku
kwancw ta lallai dayanku ya rika salla cikin nishadin sa
idan ya gaji sai ya zauna ” sahihu muslim da Abu dawud da
nasa'i da Ibn Hibban ne suka rawaito shi.
Addinin ne daga Allah manzon Allah bayason iyalan sa su
daurama kan su wani Ibadan da bazasu iya ba wanda hakan zai
tasirantu cikin harkokin sun a rayuwa taya hakan bazai faru ba
bayan shine me fadin ga sahabin sa wanda ya shagaltu da aikin
bauta yabar duk wani abubuwan dadin rayuwan duniya na
halal: “ lallai idanun ka suna da hakki akan ka, kuma jikin ka
yana da hakkin akanka, kuma matar ka tanada hakki akanka,
kuma bakon ka yanada hakki akanka, kuma abokin ka yanada
hakki akanka ” hadisi ne ingantacce Nisa'i ne ya rawaito shi
kuma albani ya ingantashi.
6. Manzon Allah s.a.w yana neman yardan iyalan sa:
Hakika manzon Allah s.a.w ya kasance wanda yafi kowa hakuri
musamman ga iyalan say a kasance yanajin abunda zai bata
masa rai daga garesu sai ya kawar dakai kuma yana ganin
cutarwa daga garesu yayi hakuri da yin yafiya daga abunda
suke aikatawa na laifi matukar be sabama shari'a ba yana
tunkarar haka da murmushi wacce take kara dankon soyayya da
yafiya da tausayi, kayi nazarin wannan tsabar hakuri na manzon
Allah s.a.w ka gani akan matan sa lokacin da Aisha Allah ya
kara mata yarda ta daga muryanta akansa cikin wani magana da
suke yi a tsakanin su sai Abubakar Allah ya kara masa yarda
yaji haka sai ya shiga yana neman ta ya bugeta yace mata bazan
ina ganinki ba kina daga sautin ki ga manzon Allah s.a.w ya
kyale ki, sai manzon Allah s.a.w ya koma kareta kada ya duketa
sai Abubakar ya fita cikin fushi sai manzon Allah s.a.w yace a
lokacin da Abubakar ya fita:
“ ya kika ganni ina kareki daga wani kada yadukeki ” sai
Abubakar ya zauna na tsawon wasu kwanaki sa'anan ya
nemi izinin manzon Allah s.a.w na shigowa sai ya same su
sun sasanta sai yace masu: ku sanya ni cikin sulhun ku
kamar yadda kuka sanya ni cikin fadan ku sai manzon
Allah s.a.w yace: “ hakika mun aikata hakika mun aikata ”
Abu dawud ne ya rawaito shi.
7. Manzon Allah s.a.w yana saukakawa iyalan sa:
Ya kasance manhajin manzon Allah s.a.w na mu'amala tare da
mutane yin sauki da rangwane da tausasa masu, an karbo daga
Abu huraira Allah ya kara masa yarda yace:
“ wani bakauye ya shiga masallaci… kawai ba'a farga ba
sai akaga yana fitsari a wani bangare cikin masallaci, sai
mutane sukayi masa ca akai, sai manzon Allah s.a.w ya
hanasu yace: lallai an aiko ni ne domin saukakewa ba dan
tsanantawa ba, ku zuba bokitin ruwa akan fitsarin nasa ”
hadisi ne ingantacce Abu dawud ne ya rawaito shi.
Aisha Allah ya kara mata yarda uwar muminai tana cewa game
da saukin da tausayin manzon Allah akan iyalan sa:
“ an kawo mana kyautan abinci ni da Hafsa kuma muna
azumi sai daya daga cikin su tace ma dayar: shin zaki iya
karya azumin? Sai tace: eh, sai suka karya azumin su biyu,
sai ga manzon Allah s.a.w ya shigo sai tace mashi: ya
manzon Allah! An kawo mana kyautan abinci sai ya bamu
sha'awa muka karya azumin mu, sai yace: babu komai
akan ku, ku azumci wani rana a maimakon sa ” Ibn hibban
ne da abu dawud suka rawaito shi, albani yace: hadisi ne me
rauni, shu'aibu alarnut yace: silsilan sa ingantacce ne akan
sharadin muslim.
8. Manzon Allah s.a.w yana tausasawa wajen mu'amala
da iyansa:
Lallai daukan abinci da hannun ka zuwa bakin matar ka da
kuma bata ruwa bawai kawai aiki ne wanda yake nufin
mallakan zuciyar matar ka da kuma nuni akan kyakyawan
mu'amala tare da ita da nuna mata so bane kawai hakan sadaka
ne wanda ake baka lada akai daga Allah kuma a sanadiyyar
haka akwai kulla akala tsakanin abunda yake na duniya ne da
kuma na lahira wanda yake ci gaba da dauke kewa kuma yana
tafiyar da damuwa da kuma samarwa iyalai da natsuwa da
kwanciyar hankali, manzon Allah s.a.w yace ma Sa'ad dan abi
waqqas:
“ kuma baka ciyar da wani ciyarwa wanda kake neman
yardan Allah d ahakan face an baka lada akanta hatta
lomar da kake sanyawa abakin iyalinka ” buhari ne ya
rawaito shi.
9. Manzon Allah baya nuna rashin kula ga iyalan sa:
Lura da yanayi dalili ne na tsabtar zuciyar mutum manzon
Allah s.a.w ya kasance yana lura da yanayin iyalan sa baya
daure fuskan sa daga labarin da suke bashi wanda ya fita daga
abunda suke so, Ammar dan yasiri Allah ya kara masa yarda
yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya yada zango domin baccin karshen
dare da hutawa cikin tafiyar sa sai mutane suka sauka cikin
wani wuri da ake kira da suna aulatul jaishi tare dasu
akwai Aisha matar sa sai sarkanta ya fadi wanda aka kawo
mata daga kasar yeman sai ya tsare mutane anan wurin
domin neman wannan sarka nata har hasken alfirir ya fito
kuma mutane basu da ruwan yin alwalla sai abubakar ya
kausasa mata mata yace mata kawai kin rike mutane a
wurin nan kuma basu da ruwa sai Allah ya saukar da ayar
sauki dayin taimama da kasa sai musulmai suka tashi tare
da manzon Allah s.a.w suka shafi kasa da hannun su ba
tare da sun goge dattin ba suka shafa a fuskar su da
hannun su har zuwa kafada da kuma cikin hannun su har
zuwa hammatan su ” . Ahmad da abu dawud da nasa'I ne suka
rawaito hadisin kuma albani ya inganta shi.
10. Manzon Allah s.a.w yana kwalliya da tsabta da sanya
turare domin iyalin sa:
Lallai shiga me kyau da kamshi yana daga cikin abunda yake
dadada rai da kawo natsuwar zuciya da kuma ido ke jin dadi da
natsuwan kallon sa, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ kaman ina kallon farfashi na turaren miski akan manzon
Allah s.a.w yana cikin haraman aikin hajji a cikin gashin
kansa s.a.w ” . buhari da muslim ne suka rawaito shi kuma
lafazin na buhari ne.
Kuma a lokacin da aka tambayi Aisha Allah ya kara mata
yarda cewa: dame manzon Allah s.a.w yake faraway idan
ya shiga gida wurinku? Sai tace yakasance idan ya shigo
asuwaki yake farawa dashi ” . Ahmad da abu dawud da Ibn
majjah ne suka rawaito shi kuma albani ya ingantashi.
Kuma hakika turare tsabta ya kasance dabi'ar manzon Allah
s.a.w cikin dukkanin halin sa hatta a halin baccin sa baya
kwanciya sai da tsarki da tsabta, me masa hidima Anas dan
Malik wanda ya samu daukaka da masa hidima na shekaru
goma yana cewa:
“ ban tama jin wani irin kamshi ba wanda yafi kamshin
manzon Allah s.a.w. kuma bantaba taba wani abuba me
taushi hatta Hariri wanda yakai hannun manzon Allah
s.a.w taushi ” muslim ne ya rawaito shi.
11. Manzon Allah s.a.w yana bayyana soyayyar sag a
iyalan sa:
Kunya baya zuwa sai da alheri kamar yadda manzon Allah
s.a.w ya fadi sai wanda ya kasance sababi na buye wani
al'amari cikin addinin musulmai ko kuma na rayuwan sun a
duniya, manzon Allah s.a.w ya kasance yana bayyana soyayyar
sag a iyansa domin bada tarbiyya ga mabiyan sa dan su rika
babbaya son su akan iyalan su domin daurewar soyayya da
rayuwan aure, Amru dan Aas yana cewa:
“ nazo wurin manzon Allah s.a.w sai nace masa: wani ne
kafi so cikin mutane? Sai yace: “ Aisha ” , sai nace cikin
maza fa? Sai yace: “ mahaifinta ” , sai nace sai kuma wane?
Sai yace: “ Umar ” , sai ya irga mutane sai nayi shir daga
nan ina tsoron kada ya sanyani a karshen su ” . Buhari da
musulim ne suka rawaito shi kuma lafazin na buhari ne.
12. Manzon Allah s.a.w yana tsoron wani abunda zai
cutar da iyalan sa:
Tsoro abune na dabi'ar mutum kuma abune na fidira matukar be
wuce tsoro na dabi'a ba amma abunda ya wuce hakan to ciwo
ne, kuma manzon Allah s.a.w ya kasance yana tsoron abunda
zai cutar da iyalan sa kuma yana kokarin ganin wani abun ki be
same su ba, Anas yana cewa:
“ sun fita tare da manzon Allah da Abu dalha, kuma tare
da manzon Allah akwai safiyyat wanda ya daurata a bayan
sa akan rakumi, akan hanyar su sai wannan rakumi ta
zauna sai manzon Allah s.a.w ya firgita da matar, kuma
abu dalha yace: ina tsammanin sun fadi a kasa, Sai yazo
wurin manzon Allah s.a.w yace: ya annabin Allah Allah ya
sanyani fansa a gareka, wani ya sameka? Sai yace: “ a'a
babu abunda ya same ni amma dai ka kula da matar ” sai
abu dalha ya jefa rigan sa akan fuskar matan ya nufi wurin
ta, sai ya jefa mata rigan sa, sai ta tashi, sai ya daura su
akan abun hawar sa. buhari ne ya rawaito shi.
13. Manzon Allah s.a.w yana himmatuwa akan tsarin
iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasanc eyana son alheri ga iyalan sa
yana kuma kokari wurin kara masu alheri musamman ma
abunda zai gadar masu da yardan ubangijin talikai da kuma
kusantar dasu zuwa aljanna ya kuma nisantar dasu daga wuta
wannan shine rabon da Allah yayi bayanin sa cikin fadin sa
cewa:
“ ko wace rai sai ta dandani mutuwa kuma ana baku ladan
ku ne a ranan alkiyama duk wanda aka nisantar dashi daga
wuta aka shigar dashi aljanna to hakika ya rabauta rayuwa
duniya kuma ba komai bace face jin dadi na rudu ” suratu
al'imran ayata 185.
Manzon Allah ya kasance yana bibiyan iyalan sa da nuna masu
hanyar alheri da kuma shiryar dasu zuwa gareta, Ummu
salmata matar manzon Allah s.a.w tana cewa: manzon Allah
s.a.w ya tashi cikin dare a firgice yana cewa:
“ tsarki ya tabbata ga Allah menene abubuwan da Allah ya
saukar na dumbin rahamar sa, kuma menene ya saukar na
fitina! Wanene zai tayar da mutanen dakin sa watan iyalan
sa suyi salla, me yuwa kaga mutum cikin ni'ima a duniya
amma a lahira ya kasance cikin akasin haka ” buhari ne ya
rawaito shi.
14. Manzon Allah s.a.w baya shigo ma iyalan sa babu
sanarwa ko izini:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana kyamar bazata ko kuma
kishi wanda ya wuce iyaka na dabi'a kuma yanason ganin
iyalan sa cikin yanayi me kyau da kamala hakan yan afaruwa
ne domin kwadayin say a ganin ya tabbatar masu da alaka na
soyayya tare dasu, ya kasance baya zuwa masu bazata idan ya
dawo daga tafiya, dabi'ar sa shine sanar da isowar sa domin ya
kasance iyalan sa sunada lokaci me yalwa wanda zasuyi
kwalliya da tsabta da kuma shiryawa tarban sa sai yaga iyalan
sa cikin siffa me kyau da yanayi domin tabbatar da alakar
soyayya, jabir dan Abudllahi yana cewa mun kasance tare da
manzon Allah s.a.w cikin tafiya lokacin da muka kusa shigiwa
gari sai yace:
“ ku sassauta tafiyar ku domin mu isa cikin dare domin
masu gashi su gyara kuma macen da mijinta yayi tafiya ta
aske gashin jikin su ” buhari da muslim ne suka rawaito shi.
15. Manzon Allah s.a.w yana gabatar da alheri ga iyalan
sa:
An daura shi akan dabi'a na karamci da kyauta ya kasance yana
gabatar da iyalan sa akan karon kansa yana kuma basu abunda
aka kawo mashi kyauta ko kuma wanda ya samu, taya bazai
zama haka ba bayan shine me fadin cewa:
“ idan Allah yaba dayanku alheri to ya fara da kansa da
iyalan gidan sa ” dabari ya rawaito shi kuma albani ya
ingantashi.
Maganar sa bawai kawai na fatan baki bace a'a ya kasanc eyana
aiwatar da abunda da yake fadi a kasa, Anas Allah ya kara
masa yarda yana cewa:
“ Ummu sulaim ta aikeshi da kwano a ciki akwai dabino
yakaima manzon Allah s.a.w, sai ya rika debo wannan
dabino da hannun sa yana aikawa zuwa ga matan sa kuma
yana sha'awar wannan dabino ya aikata hakan sau da
dama alhali yana sha'awar abun ” Ahmad da Ibn Hibban ne
suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
16. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana Kankan dakai
ga iyalan sa:
Duk wanda ya Kankan dakan sa domin Allah, to zai daga
darajar sa da wannan kalmomi ne manzon Allah s.a.w yake
yima sahabban sa magana kuma ya kasance yana aiwatar da
haka a aikace cikin mu'amalar sa tare da mutane kuma be
haramtawa iyalan sa haka ba, maganar Anas:
“ Cikin hadisin san a dawowar su madina tare da manzon
Allah daga khaibara tare da manzon Allah s.a.w akwai
matar sa safiyya Allah ya kara mata yarda yana rike da
abayarta a bayanta, sa'annan yana tsugunawa ta taka shi
tahau kan abun hawa ” buhari ne ya rawaito shi.
17. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana yafema iyalan
sa laifin da sukayi:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana daraja kishin matar sa
baya fushi idan suna kishi kuma baya kyamatar sakamakon
wannan kishin na ayyukan su sai dai yana magance hakan ne da
salo na daki daki wanda yake nuni akan kwarewa da kuma
hikima, Anas dan Malik yana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance a dakin daya daga cikin
matar sa sai daya daga cikin su ta aiko maa da kwano da
abinci aciki sai ta bigi hannun manzon Allah s.a.w wannan
kwano ya fadi ya fashe, sai manzon Allah s.a.w hada
wannan kwano wanda ya fashe ya fara tattara abincin yana
cewa: “ mahaifiyar ku tayi kishi kuci sai sukaci! Sai ya rike
wannan kwano anan gidan ya aikama wancen matar da
kwanon wannan gidan me kyau ita kuma ya bata wannan
kwanon data fasa ya zama nata ” buhari ne ya rawaito shi.
18. Manon Allah s.a.w yana sanin labarin zuci wanda
iyalan sa ke ciki:
Saukin sa ta kula da kuma aikin say a sanya manzon Allah
s.a.w yana jin damuwar iyalan sa kuma yana jin abunda sukeji
sai ya tare abunda yake mara kyau aciki da lafiya da hakuri,
Aisha uwar muminai Allah ya taka mata tarda tace manzon
Allah s.a.w yace mata:
“ ni ina sanin idan kina cikin annashwa dani, kuma idan
kina fushi dani shima nasani ” sai tace: sai nace taya kasan
haka? Sai yace: “ idan kina cikin fara'a kina cewa ne: a'a
ina rantsuwa da ubangijin Muhammad, amma kuma idan
kina cikin fushi cewa kikeyi: a'a ina rantsuwa da ubangijin
Ibrahim ” , sai tace: sai nace kwarai kuma wallahi haka ne
ya manzon Allah bana kaurace maka sai sunan ka kawai ”
buhari ne ya rawaito shi.
19. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana adalci a
tsakanin iyalan sa:
Hakika adalcin sa tare da iyalan sa yakai kololuwa ya kasance
yana masu adalci cikin dukkanin al'amuran sa cikin tafiyar sa
da lokacin da yake gida, Aisha Allah ya kara mata yarda tace:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance baya fifita wasun mu akan
wasu wurin raba kwana kuma ya kasance cikin ko wani
rana yana kewaya mu sai tsuguwa har sai ya koma zuwa
dakin wacce yake wurin ta… ” abu dawud ne ya rawaito shi
kuma albani ya inganta shi.
Kuma baya sakace ina bada mahaifiyata da mahaifina fansa a
gareshi wurin yin adalci wanda Allah ya halicce sa akan haka
hatta a lokacin rashin lafiyar sa, Aisha Allah ya kara mata yarda
tana cewa:
“ lallai manzon Allah a lokacin rashin lafiyar sa wanda
mutuwa yazo masa aciki, yana cewa: “ a ina nake gobe, a
ina nake gobe ” yana son yaji ance dakin Aisha, sai matan
sa suka masa izini daya zauna a inda yake so, sai ya
kasance a gidan Aisha har mutuwa yazo mashi anan ”
buhari ne ya rawaito shi.
• Manzon Allah s.a.w ta bangaren
zamantakewa da iyalan sa.
1. Mazon Allah s.a.w ya kasance me sauki da tausayi ga
iyalan sa:
Sauki be taba shiga cikin wani abu ba face ya daga darajarsa
kuma sauki be taba fita daga cikin wani abu ba face sai abun ya
lalace, karantarwan manzon Allah me daraja wanda ya
tarbiyyanci mutanen sa akai, ya kasanc eme sauki cikin
dukkanin al'amuran sa yanason sauki kuma yana umurtan
iyalan sa dashi baya umurtan su kuma baya sauraro daga wurin
su kuma baya daura masu abunda zai tsananta masu, Aisha
Allah ya kara mata yarda tana cewa manzon Allah s.a.w yace
mata:
“ ya Aisha ki saukaka domin lallai Allah idan ya so
mutanen wani gida da alheri sai ya shigar masu da sauki ”
Ahmad ne ya rawaito shi kuma albani ya inganta shi cikin
littafin al sahiha 523.
2. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana hidimar iyalan
sa:
Daga cikin kyawawan halayen sa ya kasance baya barin
hidimar iyalan sa da kuma tayasu wasu ayyuka, hakika an
tambayi Aisha Allah ya kara mata yarda:
“ menene manzon Allah s.a.w yake aikatawa a gidan sa? sai
tace: yana dinke takalmin sa kuma yana aikata abunda
namiji yake aikatawa agidan sa. acikin wata ruwaya kuma
tace: abunda wanin ku yake aikatawa agidan sa: yana
dinke takalmi kuma yana wanke kayansa da dinki. [buhari
ne ya rawaito shi cikin littafin adabul mufrad.
3. Manzon Allah s.a.w yana yima kansa hidima:
Kowa a cikin mu yana da lalurorin sa wanda suka shafe shi
manzon Allah s.a.w ya kasance yana ayyukan san a hidimar sa
domin saukakewa iyalan sa da kuma taimakon su, Aisha Allah
ya kara mata yarda tana cewa a lokacin da aka tambayeta:
“ menene manzon Allah yake aikatawa a gidan sa? sai tace:
ya kasance mutum ne cikin mutane yana duba kayansa ko
akwai datti, kuma yana tatsan nonon daga akuya da kan sa
da kuma yima kansa hidima ” . [Buhari ne ya rawaito shi
cikin littafin adabul mufrid].
4. Manzon Allah s.a.w yana ciyar da iyalan sa:
Kyauta da ciyarwa shi ginshiki ne wanda yake dasasu cikin
zukatan mabiyan sa yana cewa:
“ lallai Allah me karamci ne kuma yana son masu karamci
kuma me yalwa ne da kyauta yana san masu yalwata wa ”
silsilatul sahiha 1378 da 1626.
Ya kasance yana yalwatawa iyalan sa wurin ciyarwa baya masu
rowa yana cewa:
“ dinarin da ka ciyar domin daukaka Kalmar Allah da
kuma dinarin da ka ciyar wurin yanta wuya da kuma
dinarin da kayi sadaka dashi ga miskini da dinarin daka
ciyar da iyalan ka dashi, wanda yafisu lada shine wand aka
ciyar da iyalan ka dashi ” muslim ne ya rawaito shi.
Be tsaya nan ba kawai ya sanya shi hakki ne na wajibi akan
namiji ga iyalan sa a lokacin da wani sahabi ya tambaye shi
cewa ya manzon Allah menene hakkin matan dayan mu akan
shi? Sai yace:
“ ya ciyar da ita idan yaci abinci kuma ya tufatar da ita
idan ya tufatar da kan sa ” Ahmad ne da abu dawud da nasa'I
da ibn majja suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
5. Manzon Allah s.a.w yana son iyalan sa su rika
hutawa:
Ya kasance s.a.w yana neman hutun iyalan sa yana kuma aiki
wurin ganin ya tabbatar dashi musamman a halin tafiya wanda
ya kasance matattarin wahalada gajiya yana ji masu tsoron
gajiyan tafiya, Anas dan malik yana cewa: manzon Allah s.a.w
ya kasance acikin tafiya sai wani yaro yana ya fara masu waka
da sauti me kara wanda ake kira da suna Anjashata sai manzin
Allah s.a.w yace masa: “ bi a hankali ya Anjashata kada ka
karya kwalabe - anan wurin kwalabe ana nufin mata
saboda zuciyar su saurin karaya yake dashi kamar kwalba
shi yasa manzon Allah s.a.w daya ga yana sauri yace masa
yabi a hankali saboda mata kada su gaji - ” buhari ne ya
rawaito shi.
hakan saboda iyalan manzon Allah sun kasance cikin wata yar
bukka akan rakumi idan kuma ana masu waka da sauti babba
sai rakumi ta fara sauri wurin tafiya sai manzon Allah s.a.w yaji
tsoron kada wani abu ya sami iyalan sa.
6. Manzon Allah s.a.w yana hakuri da danniya akan
rikicin iyalan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance yana kalubalantar rikicin iyalan
sa da tarairaya da kuma musifar su da sakin fuska da kuma
kaurace warsu da soyayya yana masu hakuri da yafiya akan
abunda suka aikata na kura kurai wanda be sabama shari'a ba
kumayawan rashin sani baya kara masa komai a gunsa face
hakuri, Umar dan kaddab Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ mun kasance jama’ar kuraishawa muna da rinjaye akan
mata, amma bayan mun dawo madina sai mukaga su
mutane ne wanda mata ke da rinjaye akan su, sai matan
mu suka fara daukan halayen matan madina, sai nayima
matata tsawa sai ta rika maimaitamun magana tana
kallona sai nayi inkarin haka, sai tace: me yasa kake
inkarin maimaita maka maganar dana keyi? Na rantse
matan manzon Allah s.a.w suna maimaita masa magana,
kuma wata daga cikin su tana kaurace masa na tsawon yini,
sai hakan ya fusatani na tafi wurin Hafsa nace mata: wai
dagaske ne kuna sa'in sa da manzon Allah s.a.w na tsawon
yini? Sai tace: eh, sai nace: hakika kinyi asara kuma kin
tabe, shin yanzu kin yarda da fushin Allah domin fushin
manzon sa sai ki halaka? Ki daina neman dayawa daga
wurin manzon Allah kuma ki daina maimata masa magana
kuma kada ki kaurace masa, ki rika tambayata duk abunda
kike so ” buhari ne ya rawaito shi.
7. Manzon Allah yana tabbatar da abunda iyalan sa
suke so:
Ya kasance mafi gaggawa cikin tabbatar da abunda matar sa ke
so da kuma jawo masu farin ciki hakika Aisha ta tambayi
manzon Allah s.a.w tace: ya manzon Allah dukkan matan ka
suna da sunan shagube bandani sai amnzon Allah s.a.w yace
mata:
“ zan maki sunan shagube da yaron ki Abdullahi yana
nufin dan zubair kece maman Abdullahi ” ya kasance yana
kiranta sa suna mamar Abdullahi har yam utu bata taba
haihuwa ba ” buhari ne ya frawaito shi cikin littfain adabul
mufrid kuma albani ya ingantashi.
8. Manzon Allah s.a.w yana yima iyalansa likitanci:
Mutum yanada bukata matuka da hakan da kuma lura dashi da
tashi tukuru da sha'anin sa cikin halin lafiyar sa wanda a halin
rashin lafiya da rauni yafi bukatar haka, kuma hakika manzon
Allah s.a.w ya kasance be manta da wannan bangare ba yana
bibiyan iyalan sa cikin halin rashin lafiyar su domin yi masu
likitanci da hatsarin da suke ciki da kuma girmama su, Aisha
uwar muminai Allah ya kara mata yarda tana cewa:
“ manzon Allah s.a.w ya kasance idan daya gada cikin
iyalin sa ba lafiya yana mata tofi da kula'uzzai (watan yana
karanta masu suratul ikhlasi da falaki da nasi ya tufa
masu). A lokacin daya kwanta rashin lafiyar sa ta ajali sai
ya fara yi masa tofi ajikin sa sai na tofa a hannun san a
shafa masa domin hannun sa yafi nawa albarka ” muslim ne
ya rawaito shi.
9. Manzon Allah yana nuna kula ga iyalan sa:
Duk da yawan ayyukan da yake dashi masu yawa na
shugabancin mutanen sa amma hakan baisa ya manta da iyalan
sa ba da kuma shagaltuwa da mantawa dasu ba , Umar dan
kaddab yana cewa: manzon Allah s.a.w ya kasance idan yayi
sallar asuba sai ya zauna a wurin da yayi salla mutane su zo su
zauna a gefen sa har sai rana ta fito daganan sai ya tashi ya
shiga gida wurin matan sa yabi dakin kowa cikin su daya bayan
daya yana masu sallama da masu addu'a idan ranan daya ne sai
ya zauna a dakinta. Dabarani ne ya rawaito shi cikin ausat.
10. Manzon Allah s.a.w yana shawarantan iyalan sa:
Manhajin sa da dabi'ar sa itace yin shawara cikin al'amuran sa
wanda suka shafe sa da kuma ayyukan da suka shafi jama'a ya
kasance yana shawartan iyalan sa da amfana daga ra'ayoyin su
da hangen nesan su yana tarayya dasu har acikin al'amuran sa
shugabancin jama'a sai ya duba shawarar da tafi acikin su da
wanda tafi dacewa kafin ya yanke hukunc na karshe, an karbo
daga Urwata dan Zubair daga Mirwan dan Hakam da miswara
dan makhrama cewa sun fada masa cewa, an Ambato labarin su
a sulhul hudaibiya sunce: bayan an gama rubuta yarjejeniya
na sulhun hudaibiya sai manzon Allah s.a.w yace: yaku
mutane! Ku mike ku yanka dabbobin ku sannan kuma ku
cire ihramin ku, wallahi babu wanda ya tashi saboda abun
haushin daya kama mutane, sai manzon Allah s.a.w yace:
ku yanka dabbobin ku kuma ku cire haraman ku wallah
babu wanda ya tashi daga cikin su, ya kara maimaita
hakan har sau uku babu wanda ya tashi, sai manzon Allah
s.a.w ya tashi ya shiga wurin ummu salimata yace mata: ya
ummu salimata! Bakiga abunda ke faruwa bane ina
umurtan mutane amma sunki aikata abunda na umurce su
dashi? Sai tace masa: ya manzon Allah! Kada ka damu
dasu domin mutane lallai wani abu babba ya shiga cikin
zuciyar sun a ganin ka daura kanka akan sulhun nan,
abunda za'ayi ka fita ne ya manzon Allah! Kada kayiwa
kowa magana har sai ka yanka dabbarka sannan ka cire
haramar ka, domin mutane idan sukaga ka aikata hakan
zasu aikata da sauri, beyima kowa magana ba ya wuce aka
kawo masa hadayar say a yankata sai yayi aski, a lokacin
da mutane sukaga manzon Allah ya aikata hakan sai kowa
ya tashi ya yanka hadayar sa, wasu daga cikin su sukayi
kwal kobo wasu kuma sukayi saisaiye, sai manzon Allah
s.a.w yace: Allah ya gafartawa wanda sukayi kwal kobo, sai
wani yace: ya manzon Allah! Da wanda sukayi saisaye
suma? Sai ya ambaci masu kwal kobo sau uku sannan ya
fadi cikin na ukun da masu saisaye. Buhari ne ya rawaito shi.
11. Manzon Allah s.a.w yana neman izinin iyalan sa:
Allah me girma yayi gaskiya dayake siffata shi da cewa: “
lallai kana kan halaye na kwarai masu girma ” suratul
kalam (4).
Daga cikin girman halayen sa s.a.w be bar yin adalci ba a
tsakanin matan sa hatta a lokacin rashin lafiyar sa be bar raba
masu kwana ba sai bayan ya nemi izinin su suka amince masa
suka yafe masa hakkokin su, Aisha Allah ya kara mata yarda
tace: “ lallai manzon Allah s.a.w ya aika zuwa ga matan sa a
lokacin rashin lafiyar sa suka zo suka taro sai yace:
“ bazan iya yawo ba a tsakanin ku idan kunga zaku iyamun
izini na kasance a gun Aisha ina neman haka sai suka masa
izini da hakan ” abu dawud ne ya rawaito shi kuma albani ya
ingantashi.
12. Manzon Allah s.a.w yana son sanya farin ciki ga
iyalan sa:
Lallai sanya farin ciki da murna ga zuciyar mutane abune
wanda shari'a tayi umurni dashi kuma wannan umurnin yafi
karfi a bangaren yan uwa wanda yafi kusa haka haka, Aisha
uwar muminai Allah ya kara mata yarda tace alokacin danaga
annashawa a fuskar manzon Allah s.a.w sai nace ya manzon
Allah ka mun addu'a sai yace:
“ ya Allah ka gafartawa Aisha abunda ta aikata na zunubai
da kuma wanda zata aikata da wanda tayi a bayyane da
wanda tayi a asirce ” sai Aisha tayi dariya har dan kwalinta
ya fadi saboda dariya sai manzon Allah s.a.w yace: “
wallahi addu'ar danake yima al'ummata kenan cikin
dukkanin sallata ” ibn hibban ne da hakim suka rawaito shi,
kuma albani ya inganta shi cikin littafin “ al sahiha ” (2254).
13. Manzon Allah s.a.w yana koya ma iyalan sa ladabi:
Duk da irin wannan zaman takewa tashi na taushi da mu'amala
me sauki wada yakeyi ma iyalan sa ya kasance kuma me
hikima cikin mu'amalar sa da kuma ayyukan sa ta yadda
zamanta kewa me kyau ta kasance me amfani wurin tsara zance
idan kuma ya kasance cewa ladabtar tafi cancanta idan akwai
wani kuskure bazai yiwu ba shawo kan hakan da tsawa da
tsoratarwa da kuma hani, Aisha Allah ya kara mata yarda tace
nace ma manzon Allah s.a.w:
“ ai kaza ya isheka daga safiyya- matar manzon Allah
s.a.w- watan kaza da kaza- tana nufin! Ita gajeruwa ce- sai
manzon Allah yace: “ hakika kin fadi wata kalma wacce da
za'a cudanyata da ruwan rafi da sai ta batashi ” abu dawud
ne da tirmizi suka rawaito shi kuma albani ya inganta shi.
14. Manzon Allah s.a.w yana kyautatawa wajen magance
matsalar iyalan sa:
Salon san a magance matsala iyalan sa karkashin hukunce
hukuncen musulunci ya sanya su suna muwafaka da yarda da
ita, dan me yasa hakan ma zabai faru ba bayan yana masu
magana ne ta hankali da fasaha wanda yake magance matsala,
Anas dan malik Allah ya kara masa yarda yana cewa:
“ labari yazo kunnen safiyyat cewa Hafsat tace mata
yarinyar bayahude, sai tayi kuka, sai manzon Allah s.a.w ya
shigo ya sameta tana kuka, sai yace mata me yasa kike
kuka?! ” sai tace: Hafsat ce tace mun ni yarin yan
bayahudiya ce, sai manzon Allah s.a.w yace: “ lallai ke
yarinyar annabi ce kuma baffanki annabi kuma kina auren
annabi, to kuma dame zata maki alfari dashi?! Sa'annna
yace: kiji tsoron Allah ya hafsa ” tirmizi ne ya rawaito shi
kuma albani ya inganta shi.
15. Manzon Allah s.a.w yana karban uzirin iyalan sa:
Kuskure dole ne musamman ma ga wanda kake zama dashi
kullum kuma karban uzri dalili ne na tsarkin zuciya da kyawun
ta wanene yafi ka kyawun zuciya ya manzon Allah, ya kasance
yana jiran Aisha sai ta bata mashi lokaci sai yace:
“ me ya rike ki ne? ” sai tace ya manzon Allah: na kasance
inajin karatun wani mutum ne wanda bantaba jin murya
me dadin nashi ba, sai manzon Allah s.a.w ya tashi yaje ya
saurare shin a dan lokaci sai ya dawo yace: “ wannan salim
ne maula abu huzaifa godiya ya tabbata ga Allah daya
sanya irin wannan cikin al'ummata ” . Bazzar ne ya rawaito
shi kuma haisimi ya kawo shi cikin littafin “ al mujamma'a ”,
kuma bazzar yace: mutanen cikin hadisin mutanen cikin littafin
sahihul buhari ne.
16. Manzon Allah s.a.w yana sanya farin ciki ga iyalan
sa:
Ya kasance yanason fadama iyalan sa abunda zai sanya su farin
ciki da murna da saukar da natsuwa da kwanciyar hankali a
cikin zukatan su, Aisha Allah ya kara mata yarda tana cewa
manzon Allah yace mata:
“ bazaki yarda ba ace kin zama matata a nan duniya da
kuma lahira? Sai tace zan yarda, sai yace: to ke matatace
anan duniya da lahira ” hakim ne ya rawaito shi cikin
mustadrak kuma albani ya inganta shi.
17. Manzon Allah s.aw ya ksance me tausasawa wurin
mu’amala da iyalan sa:
Hakika mu'amalar manzon Allah s.a.w ya kasance tare da
mutanen da suke rayuwa dashi cikin kololuwan kyawu da sauki
da tausayi da kamala kamar yadda ubangiji ya siffatashi da
hakan yace:
“ hakika kana kan halaye na kwarai masu girma ” suratul
kalam (4).
Iyalan sa sun kasance masu rabo me waya cikin haka, Aisha
Allah ya kara mata yarda tana cewa akan mu'amalar manzon
Allah s.a.w tare da ita: “ na kasance inasha ruwa cikin
kwarya ina cikin al'ada sai mikama manzon Allah sai ya
sanya bakin sa akan wurin dana sa baki na shima yasha
ruwan kuma niacin kasha ina cikin al'ada sai na mikawa
manzon Allah s.a.w yasa bakin sa a wurin dana sa baki na
shima yace ” nisa'I ne ya rawaito shi kuma ingantacce ne
hadisin.
18. Manzon Allah s.a.w ya kasance yana da saukin hali
ga ilayan sa:
Manzon Allah s.a.w ya kasance mutum ne me saukin hali da
saukin kai cikin dukkanin al'amuran sa yana amsan kuskure
koda kuwa da gangan aka aikata kuma har yayi ma mutum uziri
koda kowa daya daga cikin sahabban sa ne ko kuma makiyan
sa ne, iyalan sa ma sun kasance suna da rabo acikin yafiyan sa
me girma, ya kasance yana shiga gida wurin iyalan sa bayan
hantsi sai yace: “ shin kuna da abincin rana? ” sai suce: a'a,
sai yace: “ to ina azumi ” nasa'I ne ya rawaito shi kuma albani
ya ingantashi.
Babu tsawatarwa kuma babu kunyatarwa sai raddi wanda yake
kunshe da sauki da kuma kyauwun amsan uzirin su.
Alaka tsakanin namiji da mace a musulunci alaka ce ta soyayya
da kuma girmama wa da rahama da darajawa, soyayya ga mace
a mastayin mata da tausayi a gareta kamar yarin ce da kuma
girmamata da darajata kamar uwa, lallai mace a cikin
musulunci duk lokacin da shekarunta yaja haka darajata zai
kara da kuma girmamata, a cikin musulunci babu matsala a
tsakanin namiji d mace ko wanne daga cikin su an halice sa ne
domin dayan domin samun kamalar sa ko wanne daga cikin su
yana da siffar sa wanda ya banbanta dashi akwai siffofi na
tawaya ga namiji wanda mace take cike masa shi kuma akwai
siffofi na tawaya ga mace wanda namiji ke cike mata shi
saboda haka ne musulunci ya wajabta wa mace wasu wajibai na
shari'a da zamantake wa wanda zai dace da ita da kuma yanayin
ta na jiki ne ko kuma na zuciya kuma Kaman haka ne shima na
miji an wajabta masa irin haka, sannan kuma ya sanyawa
namiji hakkoki nashi da kuma wanda suka wajaba akan sa
wanda zai dace da dabi'ar sa haka itama mace take nata hakkoki
wanda zai dace da dabi'ar ta a karkashen wannan kwatantawan
da musulunci ya wajabta a tsakanin su ake samun natsuwa da
kwanciyar hankali da so da kauna a tsakanin su, Allah
madaukaki yana cewa