Jerin Littafan Shi’a Na 8
Mugun Nufin
‘Yan Shi’a
ga
Al’umma
Umar Labxo
1
بسم الله الرحمن الرحيم
Gabatarwa
‘Yan Shi’a suna da baqin tarihi wanda yake cike da ta’addanci da rura wutar
fitina tsakanin Musulmi da taimakon kafirai a kansu wajen yaqar su da cinye
qasashensu, domin su, kamar yadda Ibnu Taimiya yake faxi, “A koda yaushe suna
neman taimako da kafirai da fajirai wajen biyan buqatunsu kamar yadda suke
taimakon kafirai da fajirai wajen biyan nasu buqatun.”1 Wannan shi ne halin
Rafilawa a tsawon tarihinsu, a ko wane zamani, kuma a ko wane wuri.
A nan Nijeriya, an ruwaito madugunsu, Ibrahim Yaqub Alzakzaki, yana
faxa wa Kiristoci, waxanda yake gayyata wajen Maulidinsa: “Ba da ku muke faxa
ba,” yana nufin su da Musulmi suke yaqi; ba da kafirai ba. Su kafirai abokan tafiya
ne; saboda haka Kiristoci suke halartar Maulidin ‘yan Shi’a, inda suke xaga Kuros,
watau suna nuna alamar addininsu a fili ba a voyewa.
Baqin tarihin ‘yan Shi’a aiwatarwa ne ga miyagun aqidojinsu na qiyayya da
gaba ga Ahalus Sunna, da ma duk wani Musulmi wanda ba ya bin tafarkinsu.
Malaman Shi’a suna qoqarin cusa gaba da qiyayya da mugun nufi a zukatan
mabiyansu ta hanyar ruwayoyin qarya da suke dangana wa Imamansu, waxanda
suke nuna halaccin jinin duk wanda ba xan Shi’a ba,2 da yin albishir da mummunar
makomar da take jiran sa.
A wannan taqaitaccen littafi, za mu fara da bayanin mugun nufin ‘yan Shi’a
ga al’umma kamar yadda yake a cikin aqidunsu da littafan manyan malamansu.
Sa’an nan daga bisani mu kawo misalai na baqin tarihinsu wanda yake tabbatar da
qaddamar da wannan mugun nufi a aikace.
1 Minhajus Sunna na Ibnu Taimiyya, bugun Darul Kutubil Ilmiyya, Bairut, ba tarihi, mujalladi na 2 shafi na 195.
2 Duba littafinmu, Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a.
2
Babi na Xaya
Mugun Nufin ‘Yan Shi’a ga Al’umma
‘Yan Shi’a suna qudure mugun nufi ga Musulmi da Musulunci kuma
wannan yana bayyana a fili daga abinda yake rubuce a cikin littafansu da abinda ke
fitowa daga bakin manyan malamansu. Manufarsu ta qarshe ita ce ganin bayan
Musulunci baki xayansa, da hallaka Musulmi, da rushe xakin Ka’aba da
Masallacin Annabi na Madina, da mayar da alqiblar Musulmi zuwa birnin Kufa.
Wannan mugun nufi nasu yana bayyana a cikin aqidarsu ta Mahadi da irin
abubuwan da Mahadin nasu zai yi idan ya bayyana.
Aqidar Mahadi a tushenta aqida ce ta Musulunci, amma malaman Shi’a sun
sauya ta, inda suka cusa qiyayyar Majusawan Farisa a cikinta, suka mayar da ita
wani mataki na tanadin rama gayya da xaukar fansa a kan Larabawa (watau
Sahabban Annabi) waxanda suka rusa daular Majusawa ta Iran a zamanin Sarkin
Musulmi Umar binul Khaxxabi, Allah ya qara masa yarda.
Hadisan Annabi (SAW) ingantattu masu yawa sun taho da bayanin Mahadi
da sunansa da sunan mahaifinsa da sifofinsa da wurin da zai fito da lokacin da zai
bayyana da kuma ayyukan da zai gabatar idan ya bayyana. Bayyanar Mahadi tana
cikin alamomin qarshen zamani da kusantar tashin alqiyama, kuma quduri da shi
vangare ne na aqidojin Ahalus Sunna, saboda hadisan da suka zo da shi ingantattu,
mutawatirai.
Mahadi zai bayyana a qarshen zamani. Zai fito daga zuri’ar Annabi (SAW),
daga ‘ya’yan Faxima, Allah ya qara mata yarda, ta vangaren xanta Hassan (RA).
Sunansa zai zama Muhammad binu Abdillah, zai bayyana daga gabashin duniya,
kuma za’a yi masa mubaya’a a xakin Ka’aba. Zai yi mulki shekara bakwai kuma a
zamaninsa Annabi Isa (AS) zai sauko zuwa duniya ya yi sallah a bayansa. Mahadi
3
zai cika duniya da adalci a bayan an cika ta da zalunci, zai kashe alhanzir kuma zai
karya kuros. Waxan nan abubuwa uku, watau sallar Annabi Isa a bayansa da kisan
alade da karya Kuros, nuni ne ga qarshen addinin Kirista da shafewarsa. Wannan
shi ne abinda hadisai suke tabbatar da shi dangane da al’amarin Mahadi.
Abu Sa’id Alkhudri, Allah ya qara masa yarda, ya ruwaito cewa Annabi
(SAW) ya ce, “Mahadi daga gere ni yake, mai qarancin gashin goshi, mai doron
hanci. Zai cika duniya da adalci bayan an cika ta da zalunci. Zai yi mulki shekara
bakwai.”1 Jabir binu Abdillah, Allah ya qara masa yarda, ya ruwaito, ya ce: Na ji
Manzon Allah (SAW) yana cewa, “Wata tawaga daga al’ummata ba za su gushe ba
suna yaqi a kan gaskiya, suna masu rinjaye, har tashin alqiyama…Sai Isa xan
Maryamu, tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya sauko, sai sarkinsu ya ce: Wuce
ka yi mana sallah. Sai ya ce: A’a, lallai sashenku shuwagabanni ne a kan sashe,
saboda girmamawar Allah ga wanan al’umma.”2 Har yau, Abu Sa’id, Allah ya qara
masa yarda, ya ruwaito, ya ce: Manzon Allah (SAW) ya ce, “Isa xan Maryamu zai
sauko, sai Sarkin Musulmi Mahadi ya ce: Wuce ka yi mana sallah. Sai ya ce: A’a,
lallai sashenku shugabannin sashe ne don girmamawar Allah ga wannan
al’umma.”3
Wannan shi ne labarin Mahadin Musulunci, da yadda zai bayyana, da yadda
zai shugabanci duniya, ya shafe addinin Kirista, kuma ya kawo adalci da zaman
lafiya a bayan qasa.
Mahadin Shi’a ya sha bamban da Mahadin Musulunci a sunansa da
haihuwarsa da ayyukan da zai qaddamar a yayin bayyanarsa. Da farko, shi sunansa
Muhammad binul Hassan Al’askari, kuma ba haihuwar sa za’a yi a nan gaba ba,
a’a shi an riga an haife shi tun kimanin shekaru dubu da xari biyu da suka wuce.
Kuma a duk tsawon waxan nan shekaru, yana nan a voye a wani kogo a birnin
1 A duba Sunan Abi Dawud, Kitabul Mahadi.
2 Sahih Muslim, Kitabul Iman, Babu nuzuli Isa.
3 A duba Almanarul Munif na Ibnu Qayyimil Jauziyya, shafi na 147-148.
4
Samarra wanda a yau yake a qasar Iraqi. Wannan shi ne abu na farko da ya mayar
da Mahadin Shi’a almara.
Mahadin Shi’a zai fara da Larabawa, domin su ne tushen Musulunci, ya
gama da su. Muhammad Baqir Almajalisi, xaya daga cikin manyan malaman
Shi’a masu yawan talifi, ya ruwaito cewa idan Mahadinsu ya bayyana zai zubar da
jinin Larabawa kuma ya hakaito shi yana cewa, “Babu abinda ya rage tsakaninmu
da Larabawa sai yanka.”1
Dangane da sauran Musulmi Ahalus Sunna waxanda ba Larabawa ba, ‘yan
Shi’a suna da fatawa mai qarfi daga imaminsu na shida Abu Abdullahi Ja’afar
Sadiq, kan halaccin jininsu. Wani mai ruwayarsu da ake kira Dawud binu Farqad
ya ce: Na tambayi Abu Abdillahi(A.S): Me za ka ce dangane da kisan nasibi
(watau Ahalus Sunna)? Sai ya ce, “Jininsa halal ne sai dai ina jiye maka tsoro.
Idan ka samu iko ka rusa masa gini a ka, ko ka nutsar da shi a ruwa don kada a
samu shaida, to ka aikata.”2
Da yake sharhi a kan wannan ruwaya, imamin Shi’a na wannan zamani,
Ayatullahi Ruhullahi Khumaini ya yi qari kamar haka: “Idan ka samu iko ka karvi
dukiyarsa, karve ta ka aiko mana da khumusi.”3 Wannan qarin bayani daga
Khumaini yana nuna cewa wannan aqida ta ‘yan Shi’a tana nan ba ta sauya ba;
abinda kurum yake hana su aiwatar da ita shi ne rashin iko.
Wani abinda yake qara tabbatar da haka shi ne abinda Khumaini ya faxa wa
Sayyid Hussain Musawi a lokacin da ya ziyarce shi a birnin Teheran, bayan
1 Biharul Anwar na Muhammad Baqir Alajalisi, bugun Muassasatul Wafa, Bairut, 1403, mujalladi na 52 shafi na
318 da 349.
2 Biharul Anwar, mujalladi na 27 shafi na 231.
3 Kashful Asrar wa Tabri’atil A’immatil Adhar na Sayyid Hussaini Musawi, bugun Darul Iman, Iskandariyya,
2002, shafi na 89.
5
nasarar juyin juya halin ‘yan Shi’a na Iran a shekarar 1979. Musawi ya ce: A
wani zama na musamman tare da Imam ya ce mini: “Sayyid Hussain, lokaci ya yi
na zartar da wasiyar imamai, amincin Allah ya tabbata a gare su. Za mu zubar da
jinin nasibawa (Ahalus Sunna), mu karkashe ‘ya’yansu maza, mu raya matansu.
Ba za mu bar xaya daga cikinsu ya kuvuta ba daga wannan uquba. Da sannu
dukiyoyinsu za su zama ganima ga Shi’ar Ahalul Baiti. Kuma za mu shafe Makka
da Madina daga doron qasa saboda waxan nan birane biyu sun zama mafakar ‘yan
Wahhabiya. Kuma lallai ne Karbala, qasar Allah mai tsarki, ta zama ita ce alqiblar
mutane a cikin sallah. Za mu tabbatar da burin imamai, aminci ya tabbata a gare
su.”1
Kafin mu ci gaba, bari mu tuna wa mai karatu cewa, a koda yaushe ‘yan
Shi’a suka ruwaito irin wannan tavargaza suka dangana ta ga imamai, ya sani cewa
imamai barrantattu ne daga wannan qarya wacce take nuna kafirci da munafinci da
qin Allah da Manzonsa da Musulmi baki xaya. Malaman Shi’a jikokin Majusawa
suna fakewa da son imamai da Ahalul Baiti, suna xaukar wannan a matsayin wani
mayafi wanda suke lulluve kafircinsu da zindiqancinsu da shi.
Amma faxin Khumaini cewa za su rushe Makka da Madina saboda sun
zama mafakar ‘yan Wahhabiya, to wannan dalili da ya bayar na rushe Ka’aba
qarya ce kawai. Tun kafin a haifi Muhammad xan Abdulwahhab, ko a san
Wahhabiyanci, Rafilawa suna da aqidar rushe Ka’aba da Masallacin Annabi
(SAW) na Madina.
Wani mugun nufi da ‘yan Shi’a suka daxe da shi a zuci, kuma suke da niyar
zartar da shi har gobe, shi ne rushe Masallaci mai Alfarma, watau Xakin Ka’aba,
da Masallacin Annabi (SAW) a Madina da kuma sauya alqiblar Musulmi zuwa
1 Kashful Asrar na Musawi, shafi na 91-92.
6
Karbala. Malaminsu Majalisi ya ruwaito kamar haka: “Lallai Mahadi zai rushe
Masallaci mai Alfarma har sai ya mayar da shi ga harsashensa. Kuma zai rushe
Masallacin Annabi zuwa harsashensa.”1 Har yau, a wani wurin dabam, Majalisi
ya ruwaito kamar haka: “Farkon abinda zai fara da shi – yana nufin Mahadi – shi
ne ya fitar da waxan nan biyun (watau Abubakar da Umar daga kabarinsu) suna
xanyu shataf (kamar yanzu aka bunne su) ya watse su a iska, sa’an nan ya rushe
Masallacin.”2
Ita Karbala da suke burin mayar da ita sabuwar alqibla bayan rushe Ka’aba
wuri ne kusa da birnin Kufa (a yanzu tana qasar Iraqi) inda a nan ne aka kashe
Sayyidina Hussaini xan Ali binu Abi Xalib, Allah ya qara musu yarda. A
gwargwadon aqidar Shi’a, kasancewar Hussaini ya yi shahada a wannan wuri shi
ya ba wurin falala da xaukaka waxanda Rafilawa suka yi ta kambamawa har daga
qarshe suka fifita shi a kan garin Makka da Xakin Ka’aba. Daga qarerayin da suka
laqa wa wannan wuri domin su qawata shi ga jahilai, sun ce wai masallacin
annabawa ne kuma za’a kawo dutsen Hajarul Aswadu wurin bayan rushe Ka’aba.
Sun ruwaito xaya daga imamansu yana huxuba, yana cewa: “ Ya ku mutanen
Kufa, lallai Allah mai girma da xaukaka ya ba ku abubuwan da bai ba wani ba na
falala. Masallacinku shi ne xakin (Annabi) Adamu da (Annabi) Nuhu da (Annabi)
Idrisu, kuma shi ne masallacin (Annabi) Ibrahimu… Kuma kwanuka ba za su tafi
ba sai an kafa (dutsen) Hajarul Aswadu a cikin sa.”3
Girmama Karbala da xaukan ta a matsayin qasa mai tsarki da fifita ta a kan
Ka’aba qaryatawa ne qarara ga Alqur’ani mai girma. Allah Maxaukaki yana cewa:
1 Biharul Anwar na Majalisi, mujalladi na 52 shafi na 338; kuma a duba Kitabul Gaiba na Abu Ja’afar
Muhammad binul Hassan Aldusi, bugun Madabi’ul Nu’uman, ba garin bugu, ba tarihi, shafi na 282.
2 Biharul Anwar, tushen da ya gabata, mujalladi na 52 shafi na 386.
3 Alwafi na Faid Kashani, bugun Almaktabatul Islamiyya, Tehran-Iran, ba tarihi, mujalladi na 1 shafi na 215.
7
“Kuma lalle ne, Xaki na farko da aka aza domin mutane, haqiqa, shi ne wanda ke
Bakka mai albarka kuma shiriya ga talikai.” (Suratu Ali Imrana: 96).
Kuma masallacin Ibrahim wanda ya gina da umarnin Allah shi ne Xakin
Ka’aba, kamar yadda Allah ya bayyana: “Kuma a lokacin da muka iyakance wa
Ibrahim wurin Dakin (muka ce masa), “Kada ka haxa kome da ni ga bauta, kuma
ka tsarkake Xakina, domin masu xawafi da masu tsayuwa da masu ruku’u da masu
sujada. Kuma ka yi yekuwa ga mutane da wajabcin Hajji, su je maka suna masu
tafiya da qafafu da kuma a kan kowane maxankwarin raqumi masu zuwa daga
kowane rango mai zurfi.” (Suratul Hajji: 26-27). Kuma Ubangiji Maxaukaki ya
ce, “Kuma a lokacin da Ibrahim yake xaukaka harsashin gini ga Xakin, da Isma’ila
(suna cewa), “Ya Ubangijinmu, ka karva daga gare mu, lalle ne kai, kai ne mai ji,
mai sani.” (Suratul Baqara: 127).
Dangane da alqibla kuwa, Allah Maxaukaki yana cewa, “Lalle ne, muna
ganin jujjuyawar fuskarka a cikin sama. To lalle ne, mu juyar da kai ga Alqibla
wadda kake yarda da ita. Sai ka juyar da fuskarka wajen Masallaci Tsararre.”
(Suratul Baqara: 144). Watau Masallaci mai Alfarma, Xakin Ka’aba. Har yau,
yana cewa, “Kuma daga inda ka fita, to, ka juyar da fuskarka a wajen Masallaci
Tsararre, kuma inda kuke duka, to, ku juyar da fuskokinku a wajensa.” (Baqara:
150).
Wannan shi ne abinda Alqur’ani mai tsarki yake faxi dangane da qasa mai
tsarki da kuma alqiblar Musulmi wacce ba ta canjawa kuma ba ta sauyawa har
abada. Daga wannan kuma babu wata qasa mai tsarki sai Baitil Maqadis wanda
Allah yake cewa dangane da shi: “Tsarki ya tabbata ga wanda ya yi tafiyar dare da
bawansa da dare, daga Masallaci mai Alfarma zuwa ga Masallaci mafi nisa, wanda
muka sanya albarka a gefensa.” (Suratul Isra:1). Sai kuma Masallacin Annabi
8
(SAW) na Madina. Waxan nan su ne masallatai guda uku masu alfarma waxanda
ambatonsu ya zo a cikin hadisin da Manzo (SAW) yake cewa: “Ba’a xaura sirada
(domin tafiya) sai zuwa masallatai uku kawai: Masallaci mai Alfarma, da
Masallaci Mafi Nisa, da Masallacina wannan.”1
Don haka Karbala ba ta da wata alfarma kuma ba ta da tsarki, sa’an nan
babu bambanci tsakaninta da ko wace irin gama-garin qasa a duniya. Muna roqon
Allah ya buxe basirarmu tare da Shi’awa waxanda ba su yi nisa ba. Ya bayyana
mana gaskiya ya ba mu ikon bin ta. Waxanda suka yi nisa kuma, Allah ya isar wa
Musulunci sharrinsu.
Har yau, wani mugun nufi da Rafilawa suka daxe da shi a zuci kuma suke da
niyyar zartar da shi a aikace, shi ne kashe Musulmi Ahalus Sunna mafi munin kisa
ta yadda ba abinda zai rage a cikinsu sai kaxan. Qasurgumin malamin ‘yan Shi’a
wanda suke yi wa laqabi da Shaikhul Xa’ifa , watau Shaihin Qungiya, mai suna
Abu Ja’afar Muhammad binu Hassan Alxusi, ya ce, “Wannan al’amari (yana nufin
mulkin ‘yan Shi’a) ba zai tabbata ba sai ushuri tara na mutane sun tafi.”2
Duba ka gani, malam mai karatu, wannan qeta da mugun nufi da baqin
alkaba’i da yake cikin zukatan malaman Shi’a da manyan mabiyansu. Mulkinsu ba
zai tabbata ba sai sun kashe ushuri tara na mutane, watau casa’in bisa xari ke nan
(90%).
Ruwayar Majalisi ta fi ban tsoro da kaxa zuciya da tsuma jiki. Ga yadda ya
hakaito daga imaminsu na shida, Abu Abdullahi, wai ya ce, “Da mutane sun san
abinda Mahadi zai yi idan ya bayyana da mafi yawansu sun yi fata kada su gan shi
saboda yawan mutane da zai kashe… Har mutane da yawa za su riqa cewa:
1 Bukhari da Muslim.
2 Duba Kitabul Gaiba na Aldusi, tushen da ya gabata, shafi na 135.
9
Wannan ba ya cikin iyalin Muhammad; da yana cikin iyalin Muhammad da ya yi
jin qai.”1
Idan mai karatu yana so ya san su wane ne waxan nan mutanen da wannan
shu’umin Mahadi, Mahadin Yahudawa da Majusawa, zai kashe, to sai ya koma ga
maganar Ayatullahi Khumaini da muka naqalto a baya kaxan inda ya sarraha da
cewa Ahalus Sunna suke nufi. Muna fata Allah ya raba mu da ganin wannan baqin
Mahadi mai baqar aniya da mugunyar manufa.
Har ila yau, wani mugun nufi da ‘yan Shi’a suka daxe da shi a zuci kuma
suke da niyar tabbatar da shi a aikace, shi ne sauya addinin Musulunci da wani
addinin sabo da sauya Shari’arsa da wata shari’a sabuwa da kuma sauya littafinsa
da wani littafin sabo. Majalisi ya ambata a cikin littafinsa kamar haka: “Mahadi
zai bayyana da al’amari sabo, da littafi sabo, da hukunci sabo.”2
Idan kana da wani kokwanto dangane da wannan sabon al’amari, bari ka ji
ruwayar Kulaini, wanda ‘yan Shi’a suke xaukar sa kamar yadda Ahalus Sunna
suka xauki Imamul Bukhari, daga Abu Abdullahi, imamin Rafilawa na shida, cewa
wai ya ce: “Idan Mahadin iyalin Muhammadu ya bayyana, zai yi hukunci da
hukuncin (Annabi) Dawud da (Annabi) Sulaiman kuma ba zai tambayi shaida ba.”3
E, ba zai tambayi shaida ba; saboda tambayar shaida yana daga cikin sifofin
Musulmi, shi kuwa wannan Mahadin Bani Isra’ila ne ya yafa mayafin iyalin
Muhammadu (SAW), Ahlul Baiti, domin vad da bami. Saboda haka zai bar
Shari’ar Annabi Muhammad (SAW), shugaban Ahalul Baiti, ya kama ta
annabawan Bani Isra’ila.
1 Biharul Anwar na Majalisi, tushen da ya shude, mujalladi na 52 shafi na 303.
2 Biharul Anwar, tushen da ya shude, mujalladi na 52 shafi na 354.
3 Usulul Kafi na Abu Ja’afar Muhammad binu Ya’aqub Alkulaini, ta’aliqin Ali Akabar Gifari, bugun Darul Kutubil
Islamiyya, Teheran-Iran, ba tarihi, mujalladi na 1 shafi na 397.
10
Wannan shi ne mugun nufin ‘yan Shi’a ga al’ummar Musulmi kamar yadda
yake a cikin littafan malamansu waxanda suke izna da su. Kuma cewa wannan
mugunyar manufa sai Mahadinsu ya bayyana za su zartar da ita, wata dabara ce ta
koya wa mabiyansu juriya da haqurin jira da dako. Gaskiyar lamari shi ne, duk
lokacin da dama ta samu, ‘yan Shi’a suka kafa daula, ko suka samu qarfi, to
wannan ne lokacin zartar da wannan manufa. Ba sai Mahadi ya bayyana ba.
Idan mai karatu yana son tabbatar da haka, sai ya koma ga maganar Imam
Khumaini inda yake cewa, jim kaxan bayan kafa Jumhuriyar Islama ta Iran,
“Sayyid Hussain, lokaci ya yi na zartar da wasiyar imamai, amincin Allah ya
tabbata a gare su. Za mu zubar da jinin nasibawa (Ahalus Sunna), mu karkashe
‘ya’yansu maza, mu raya matansu. Ba za mu bar xaya daga cikinsu ya kuvuta ba
daga wannan uquba. Da sannu dukiyoyinsu za su zama ganima ga Shi’ar Ahalul
Baiti. Kuma za mu shafe Makka da Madina daga doron qasa saboda waxan nan
birane biyu sun zama mafakar ‘yan Wahhabiya. Kuma lallai ne Karbala, qasar
Allah mai tsarki, ta zama ita ce alqiblar mutane a cikin sallah. Za mu tabbatar da
burin imamai, aminci ya tabbata a gare su,”1 kamar yadda muka gani a baya kaxan.
Bayan kafa Jumhuriyar Islama ta Iran, ‘yan Shi’a ba su jira zuwan Mahadi
ba, amma sun ci gaba da zartar da mugun nufinsu ga al’umma, kamar yadda za mu
gani a qarshen babi mai zuwa, in Allah ya yarda.
1 Kashful Asrar na Musawi, shafi na 91-92.
11
Babi na Biyu
Baqin Tarihin ‘Yan Shi’a
‘Yan Shi’a suna aiwatar da mugun nufinsu, wanda yake qunshe a cikin
aqidunsu kamar yadda muka gani, a duk lokacin da suka samu damar yin haka.
Koda yake sun dangana yawancin miyagun manufofinsu da bayyanar Mahadi,
amma tarihi ya tabbatar da cewa bayyanar Mahadi a wajensu shi ne kawai samun
iko. A duk lokacin da ‘yan Shi’a suka samu damar kafa daula, ko bayyanar wani
shugabanci mai qarfi, to suna yin amfani da wannan don cimma manufofinsu. Don
haka muke gani a yau, qasar Iran, bayan juyin juya halin Rafilawa, ta zama babban
jigo na fitina da rashin zaman lafiya a qasashen Musulmi, musamman a Gabas ta
Tsakiya.
A wannan babi na biyu, za mu gabatar da misalai na baqin tarihin Shi’a a
qasashe dabam-daban da lokuta dabam-daban.
Kisan Shugabanni da ta da Fitinu
Kasancewar qungiyar Shi’a an kafa ta don yaqar Musulunci daga ciki,
mabiyan tafarkin Rafilanci sun qaddamar da ayyukan ta’addanci a kan Musulmi a
tsawon tarihi. Wannan ya haxa da kashe-kashe da zagon qasa ga marayar Musulmi
da kafa qungiyoyin asiri iri-iri domin yaqar Musulunci da rusa aqidarsa. Wani salo
na yaqi da suka daxe suna yin amfani da shi, shi ne kisan shugabanni
Ba ‘yan Shi’a ne suka fari kisan shugabanni ba a tarihin bil Adama, amma
sun qware a kansa, kuma sun shahara da shi. Wannan ya sa su Turawa daga wajen
su ne suka samu kalmarsu ta assassination, wacce take nufin kisan shugabanni,
kamar yadda za mu gani a nan gaba, in Allah ya yarda.
12
Abu ne da aka sani cewa shugabanni su ne kai ga ko wacce al’umma, kuma
kamar yadda jiki ba shi da amfani idan babu kai, to haka al’umma idan ba ta da
shugabanci. Wannan ya sa ‘yan Shi’a, a matsayinsu na rantsattsun masu gaba da
Musulunci, suka mayar da kisan shugabannin Musulmi sana’a wacce suka shahara
da ita
Shugaba na farko da suka kashe a tarihin Musulunci shi ne Sarkin Musulmi
Umar binul Khaxxabi, Allah ya qara masa yarda. Abu Lu’ulu’atal Majusi ne ya
kashe shi domin rama gayya ga rushe daular Farisa ta Majusawan Iran da khalifan
ya yi. Abu Lu’ulu’ata Bamajuse ne da aka ribato shi a wajen yaqi, kuma ya zama
bawan Sahabin Annabi, Mugira binu Shu’uba, Allah ya qara masa yarda, yana
zaune tare da shi a Madina. Ya shiga sahun sallah a Masallacin Annabi(SAW) da
asuba, ya soki Umar da wata wuqa mai baki biyu wacce ya sa mata dafi, a lokacin
da Umar yake limancin mutane a cikin sallah. Sa’an nan ya yi ta sukan masallata
dama da hagu sai da ya soki mutum goma sha uku, waxanda bakwai daga cikinsu
suka yi shahada.
Saboda wannan aika-aika da ya yi, ‘yan Shi’a na ko wane zamani suna
xaukar Abu Lu’ulu’ata a matsayin gwarzo, kuma suna yi masa laqabi da Baba
Shuja’uddin, watau Baba Sadaukin Addini! Gwamnatin Musulunci (wai ma!) ta
qasar Iran ta gina masa Hubbare a birnin Kashana dake tsakiyar qasar. Wannan
Hubbare da ta qunshi makeken gini mai babbar qofa, ma’abota jahilci suna ziyarar
ta daga ko ina a duniya domin tunawa da Bamajuse Abu Lu’ulu’ata da babban
aikin da ya gabatar na kashe Khalifa Umar! Har yau, gwamnatin qasar Iran ta
sanya hoton wannan Hubbaren a kan irin katin nan na aikewa da saqo (postcard)
da kuma kan-sakri na aike wasiqu (stamp) don a yaxa ta kuma a jawo hankalin
masu ziyara, da masu yawon buxe idanu, zuwa gare ta.1
Mai son ya ga hoton Hubbaren Abu Lu’ulu’ata sai ya shiga sashen Google
na yanar gizo, ya sanya sunan “Abu Lu’ulu’ah” ko “Fairuz” sa’an nan ya latsa. Zai
ga abin mamaki. Mai karatu, me zai hana ka gwada don ka gane wa idanunka!
Shugaba na biyu da Rafilawa suka kashe shi ne Sarkin Musulmi Usmanu
binu Affan, Allah ya qara masa yarda. Abdullahi binu Saba’i Bayahude, wanda ya
aza tubalin farko na ginin tafarkin Shi’anci, shi ya fari fitinar da ta kai ga kisan sa.
1 A duba Kashful Asrari na Musawi, tushen da ya shude, shafi na 88.
13
Kashe-kashen Rafilawa ga shugabannin Musulunci bai tsaya a kan Sahabbai
da magabatan Ahalus Sunna ba kawai, a’a ya haxa har da imaman Shi’a da
shugabannin Ahalul Baiti. Mafi shahara a cikinsu shi ne Imam Hussaini, Allah ya
qara masa yarda, wanda mabiyansa ‘yan Shi’a ne suka yi sanadin mutuwarsa.1
Haka nan, su suka yi sanadin mutuwar Imaminsu na bakwai, Imam Musa Alkazim,
kamar yadda su da kansu suka tabbatar.2
A taqaice kisan shugabanni, ko kuma abinda ake kira da Turanci
assassination, ya zama wata hanya ta yaqar Musulunci wacce Rafilawa suke
amfani da ita a ko wane zamani. A nan kusa-kusa sun kashe manyan malamai
kamar su Muhammad Hussaini Azzahabi mai littafin Attafsiru wal Mufassirun da
Ihsan Ilahi Zahir sanannen marubuci xan qasar Pakistan wanda ya shahara da
rubutu a kan ‘yan Shi’a. Kamar yadda suke kashe duk wani malaminsu da ya tuba
ya koma Sunna irin su Sayyid Ahmad Kasarawi da Dr Musa Musawi wanda ya
rubuta littafin A Critical Revision of Shi’ah yana kira da a yi gyara a tafarkin
Shi’anci.
A nan Nijeriya, a cikin ‘yan shekaru kaxan da suka gabata, ‘yan Shi’a sun
kashe malamai, na qarshensu Malam Umaru Xan Maishiya wanda suka kashe a
Sakkwato. Wataqila ba zai zama adalci ba idan muka dangana wa ‘yan Shi’a kisan
Malam Ja’afar kai tsaye; saboda shi yana da maqiya masu yawa. Amma muna iya
dangana musu kisan Malam Umar Xan Mai Shiyya saboda shi ba shi da abokan
gaba sai ‘yan Shi’a.
Kuma ina cikin gyaran wannan littafi don miqa shi ga masu bugu, sai aka
qara tafka ta’asar kisan gilla ga Malam Muhammad Auwal Adam Albani a ranar
Asabar 1 ga watan Rabi’ul Thani, 1435/ 1 ga Fabrairu, 2014. Muna roqon Allah
Maxaukaki ya karve shi a cikin masu shahada waxanda suka bi turbar annabawa
da magabata na-gari.
“Ya Ubangijinmu, ka yi gafara gare mu, kuma ga ‘yan uwanmu waxanda
suka riga mu yin imani, kada ka sanya qulli a cikin zukatanmu ga waxanda suka yi
imani. Ya Ubangijinmu, lalle kai mai tausayi ne, mai jinqai.”(Suratul Hashri: 10).
1 Duba littafinmu, Wa Ya Kashe Hussaini? bugun Zomo Press, Kaduna, 2010, shafi na 7-18.
2 Duba Rijalul Kasshi na Muhammad binu Umar Alkasshi dan Shi’a, shafi na 229.
14
Shaihu Ali Muhammad Sallabi ya zana wani kwami da sunayen
shugabannin Musulunci waxanda ‘yan Shi’a suka kashe a zamuna dabam-daban,
da qasashe dabam-daban, a qarshen litafinsa mai suna Daulatus Salajiqah. Kwamin
ya qunshi sunayen fitattun shugabanni 42 waxanda suka haxa da khalifofi da
sarakuna da alqalai da kwamandojin soji da manyan malamai da attajirai.1
Imam Suyuxi ma ya zana sunayen shugabannin Musulmi da ‘yan Shi’a suka
yi wa kisan gilla a cikin littafinsa, Tarikhul Khulafa.
Abinda wannan yake nunawa shi ne cewa, ‘yan Shi’a an san su da sana’ar
kisan shugabannin Musulmi waxanda ba sa bin tafarkinsu, musamman Ahalus
Sunna waxanda suke ganin jininsu ya halatta.2
Haddasa Fitina A Tsakanin Musulmi
Rafilawa suna xaukar haddasa fitina tsakanin Musulmi a matsayin wata
hanya ta yaqar Musulunci da qoqarin rusa shi. Kuma wannan abu ne da suka
shahara da shi a tsawon tarihi. Fitina ta farko da suka haddasa ita ce tawayen da
aka yi wa Sarkin Musulmi Usmanu binu Affan(RA) wanda ya qare da kisansa
kisan gilla, kuma ya haifar da faruwar savani a tsakanin al’umma wanda ya kai ga
yaqoqa masu yawa. Yaqin Jamal da yaqin Siffain da yaqin Nahrawan, da wasu
gomomi da xaruruwan yaqoqa da suka biyo bayan waxan nan, duka sakamakon
fitinar Abdullahi binu Saba’i ce wanda ya assasa tafarkin Shi’a.
Wani salon fitina da ‘yan Shi’a suka shahara da shi, shi ne taimakon kafirai a
kan Musulmi koda yaushe yaqi ya tashi a tsakanin vangarorin biyu. Misalan irin
wannan aiki nasu ba za su qidayu ba, amma wanda ya fi shahara a tarihi shi ne
yaqin Tattar a kan Bagadaza.3 A wannan zamani da muke ciki ya tabbata cewa
Rafilawan Iran sun taimaka wa Amurkawa da sauran kafiran Turai a kan yaqin
Afganistan da Iraqi, banda samar da makamai da horon soji ga qungiyoyin Shi’a
‘yan ina-da-kisa na Iraqi waxanda suke karkashe Ahalus Sunna na qasar. Waxan
nan duka abubuwa ne waxanda suke an tabbatar da su ta hanyar bincike na zahiri,
1 Duba Daulatus Salajiqah na Sallabi, bugun Darul Ma’arifa, Bairut, 1430/2009, shafi na 654-656.
2 Domin ganin fatawoyin malaman Shi’a da nassoshin imamansu da suke nuna halaccin jinin Musulmi a addinin
Shi’a, sai a duba littafinmu, Matsayin Musulmi a wajen ‘Yan Shi’a.
3 Za mu fayyace bayani a kan wannan a nan gaba kadan, in Allah ya yarda.
15
kuma bayanansu suna nan a cikin kundayen bincike na hukumomi da qungiyoyi
daban-dabam.
Kafa Qungiyoyin Asiri
Wani salon ta’addanci da ‘yan Shi’a suka xauka don yaqar Musulunci shi ne
kafa qungiyoyin asiri domin yaxa hayaniya da dambarwa da vata aqidojin
Musulunci da hana zaman lafiya a marayar Musulmi. Baqin tarihin Shi’a yana cike
da irin waxan nan qungiyoyi.
Wataqila mafi daxewa kuma mafi sharrin waxan nan qungiyoyi ita ce
qungiyar Isma’iliyya. ‘Yan wannan qungiya suna dangana kansu ga Isma’il binu
Ja’afar Sadiq, xan imamin Shi’a na shida, kuma sun yi qaurin suna da yawan
tashin-tashinar siyasa, tawaye da bore da kisan shugabanni. Bayan sun yi tawaye
ga imamin Shi’a na bakwai, Musa binu Ja’afar Sadiq, sun goyi bayan xan uwansa
Isma’il, shi ma sun ya da shi suka koma ga Almusta’ali Billah, khalifan Faximawa
‘yan Shi’a na tara a Misira, wanda shi ma suka yi masa tawaye qarqashin
jagorancin shaqiqinsa, Nizar binu Ma’ad, suka kafa wata ‘yar qaramar daula a
garin Iskandariyya na Masar.
A shekarar 1090 miladiyya, wannan ‘yar daula tasu ta rushe, sai suka yi
qaura qarqashin jagorancin shugabansu, Hassan binul Sabbah, zuwa lardin
Almautu na qasar Iran inda suka kafa qungiyar ta’addanci ta Hasshashun. Wannan
suna nasu an samo shi daga kalmar hashish wacce take nufin ganye, watau wiwi,
wanda ake sha don buguwa.
A wannan lokaci ne Isma’iliyya suka kai qololuwar ta’addancinsu, inda suka
bazu a dazuka da kan duwatsu, suna tare hanya, su kashe maza, su kame mata da
yara, su kora dabbobi waxanda suke gasawa su ci bayan sun yi maye. Idan wani
sarki ko hakimi ko mai mulki ya yi qoqarin magance ta’addancinsu, sai su aike
wanda zai yi shigar burtu ya kashe shi kisan gilla. Daga nan sunan hasshashun ya
yi dai-dai da masu kisan shugabanni, wanda Turawa suka ara suka mayar
assassins. Wannan sai ya zama wani abin “alfahari” a cikin baqin tarihin ‘yan
Shi’a cewa su ne suka koya wa Turawa, sarakan kisa, yadda ake kashe shugabanni!
16
A wannan zamani namu, qungiyar Isma’iliyya ta rikixe, ta fito da sunan
Agha Khan Foundation, inda take gina makarantu da asibitoci, tana da’awar
taimakon Musulmi marasa galihu, amma manufarta ita ce juye kansu da vata
aqidarsu. Turawa ‘yan mishan sun rungumi wannan qungiya (hedukwatarta tana
London) kamar yadda suka rungumi qungiyar Ahmadiyya, saboda manufarsu xaya
ce.
Cibiyar Agha Khan tana gudanar da nashaxinta yawanci a gabashin Afrika.
Na gani da idona irin makarantu da asibitoci da take ginawa a qasashen Uganda da
Kenya da Tanzaniya. A vangarenta na Turai kuwa, cibiyar tana lulluve ayyukanta
da mayafin bincike na ilmi da kimiyya, kamar yadda cibiyoyin Yahudawa masu
miyagun manufofi suke yi. A shekarar 2011, wannan vangare na qungiyar ya bai
wa sarkin Masarautar Qaxar dake Tekun Fasha “Lambar Yabo ta Inganta Gineginen
Musulunci Masu Tarihi.” Wannan wata hanya ce da qungiyoyin ta’addanci
(irin ta’addancin da kafiran Turai suke maraba da shi) suke sa wa kawunansu rigar
mutunci, kuma kafafen labarai na duniya su riqa kambama su, don su ji daxin
zambatar gafalallu.
Banda ta’addanci na kashe-kashe, qungiyar Isma’iliyya ta qaddamar da
ta’addancin aqida kuma, inda ta shigo da miyagun aqidu na Maguzanci cikin wasu
qungiyoyin Musulmi. Aqidar Faila ta ‘yan Tijjaniyya, ko kuma mu ce ‘yan
Inyasiyya, tana cikin irin waxan nan aqidu.1
Wata qungiyar ta’addanci da Rafilawa suka kafa ita ce qungiyar
Qarmaxiyya. Wanda ya kafa wannan qungiya shi ne Qarmax Hamdan. Asalinsa
daga lardin Khuzistan na qasar Iran yake, ya valle daga qungiyar Isma’iliyya,
kuma ya yi qaura zuwa Kufa a Iraqi inda ya kafa tasa qungiyar. Yawancin
ta’addancin Qarmaxiyya na aqida ne. Ita ce ta xauki tutar yaxa aqidar Baxiniyya
wacce take koyar da cewa Alqur’ani yana da ma’ana biyu: ta voye da ta sarari,
kuma babu wanda ya san ta voyen daga imaman Shi’a sai gausayen Xariqa.2
Addinin Baha’iyya shi ma ya samo asali daga aikin ta’addancin aqida na
‘yan Shi’a. Wanda ya kafa wannan addini shi ne Baha’ulla, wanda ya rayu tsakanin
1 Domin ganin dangantakar akidun Shi’a da Darika sai a duba Muqaddimatu Ibni Khaldun na Abdurrahman binu
Khaldun, bugun Darul Kutubil Ilmiyya, Bairut, 2003, shafi na 254 da 386. Kuma domin darasun tushen akidar Faila
a cikin kungiyar Isma’iliyya, sai a duba Altuhfatus Saniyya na Dr Tahir Maigari, shafi na 133. Na fassara wannan
littafin zuwa harshen Hausa da taken Jana’izar Tijjaniyya. Littafin ya fito a shekarar 2015; nemi kwafenka.
2 Domin karin bayani, duba littafinmu Bankaurar Sufaye.
17
shekarun 1817 zuwa 1892. An haife shi a birnin Teheran na Iran, kuma ya rasu a
garin Akka a kan gavar kogin Bahar Maliya. Asalin Baha’ulla xan Isma’iliyya ne,
amma daga bisani ya yi shelar kafa sabon addini mai zaman kansa. Aqidojin
wannan addinin da ibadojinsa gamin-gambiza ne na aqidun Musulunci da
Kiristanci da tsoffin addinan Gabas Mai Nisa, kamar Budanci da Barhamanci da
Komfusanci da sauransu. Suna gina xakin ibada a kewaye kamar rumbu, babu
mihirabi ko alqibla, saboda su sama suke kallo idan suna sallah.
Turawan mulkin-mallaka suna yabon Baha’iyyanci saboda, a faxinsu, yana
da sassauci kuma ya tattare alheran dake cikin dukkan addinai!! Yahudawa ma
suna tallan wannan addinin, suna taimaka masa da dukiya, saboda ya dace da
manufarsu ta yaqar Musulunci. A yau, hedukwatarsa ta duniya tana can a kan
dutsen Mount Carmel dake bayan garin Haifa a Isra’ila.
Durzawa, ko kuma Duruz, wata tsohuwar qungiyar ta’addanci ce da ‘yan
Shi’a suka kafa. Ta shahara da yin biyayya ga khalifan Faximawa ‘yan Shi’a na
shida, Alhakim bi Amrillah, wanda ya yi mulkin Misira tsakanin shekarun 996
zuwa 1021 miladiyya. Bayan raunin daular Faximawa, Durzawa sun zauni
duwatsun Lebanon inda suka mayar qasarsu har zuwa yau. Sun taimaka wa
Yahudawan Isra’ila a kisan qare-dangin da suka qaddamar a kan Falasxinawa a
Lebanon a shekarar 1982, kuma a yau su ne qashin bayan qungiyar ta’addanci ta
Hizbullah wacce Hassan Nasarallah yake jagoranta. Qungiyar Hizbullah ‘yan
Shi’ar Nijeriya qarqashin jagorancin Zakzaki suna da alaqa ta qut-da-qut da ita.
Har ma idan suka fito jerin gwanonsuna Maulidi, wanda wasu ‘yan xariqa da
Kiristoci suke taimaka musu, sukan xaga tutocin qungiyar don bayyana wannan
alaqar a fili.1
Wani abu da bai kamata mu wuce ba tare da mun ambace shi ba, shi ne cewa
vurvushin Durzawa suna nan a cikin mutanen nan da muke kira Kwarori waxanda
suke zaune a Nijeriya, musamman a biranen Kano da Ikko. Kuma koda yake suna
kauwame kansu, ba sa gauraya da mutane ta hanyar auratayya ko mu’amala, amma
babu laifi mu yi gargaxi da cewa suna xauke da aqidar Shi’a kuma suna taimakawa
wajen yaxa ta a fakaice.
1 Duba hoton ‘yan Shi’a suna dauke da tutocin Hizbullah a jaridar Daily Trust, fitowar Talata, 22 ga watan Mayu,
2012, shafi na 3.
18
Taimakon Kafirai wajen Yaqar Musulmi
Daga cikin abinda ‘yan Shi’a suka shahara da shi a baqin tarihinsu akwai
taimakon kafirai a wajen yaqar Musulmi, da cin qasashensu, da take haqqoqinsu,
da zubar da jininsu, da keta alfarmarsu. Wannan qaramin littafi ba zai iya tattare
abinda ya faru ba a wannan fanni, amma za mu ba da misali guda kawai.
A wajejen qarshen daular Abbasiya a qarni na bakwai bayan hijira, an yi
wani sarki Mushriki mai suna Holako, sarkin Tattar. Wannan sarki ya yaqi daular
Musulmi mai faxi, ya riqa cin gari bayan gari. Duk garin da ya ci yana rushe shi
baki xaya, ya kashe mazauna garin, ya qone gidaje da gonaki da dabbobi, ba ya
barin kome. Saboda tsananin varnar waxan nan kafirai, har wasu mutane a
zamanin sun zaci ko yajuju da majuju ne suka bayyana. Amma duk da haka,
babban birnin daular Musulmi, watau Bagadaza, tana yi wa wannan sarkin kwarjini
saboda girmanta da yawan mutanen dake cikinta da kuma qarfin sojan dake tsaron
ta. A wannan lokaci, duk duniya babu birni kamar Bagadaza. Don haka da ya iso
qasar Farisa sai ya tsaya yana tararrabi, yana shawara ya kawo wa Bagadaza hari
ko a’a.
A wannan lokaci Sarkin Musulmi shi ne Musta’asim, Khalifa na qarshe a
daular Abbasiya. Babban wazirinsa mai suna Muhammad binu Ahmad binu
Alqami xan Shi’a ne amma masu mulki sai suka yi sakaci da shi tun yana saurayi,
ya yi ta hawa muqamai har ya kai matsayin waziri. Saboda iya munafunci da
amfani da taqiya, Binu Alqami ya samu amincewar kowa a wannan daula. Amma
duk tsawon shekaru, shi dama yake jira ta rusa daular. Sai zuwan Holako da
rundunarsa ya ba shi wannan damar.
Binu Alqami ya aike wa Holako da bayanan sirri a voye, ya yi bayanin
raunin daular kuma ya yi alqawarin taimakon maharan da sharaxin cewa za su kafa
19
daular Shi’a bayan sun kawar da Khilafar Abbasiya. Lokacin da rundunar Tattar
suka iso Bagadaza suka kafa sansani a bayan gari, Khalifa Musta’asim ya tsorata
ainun, amma sai wazirinsa ya kwantar masa da hankali kuma ya nemi izini ya fita
zuwa sansanin abokan gaba domin neman sulhu da su. Bayan ya je ya qara
tabbatar da yarjejeniyarsa ta sirri da Holako, sai ya komo wajen sarkin Musulmi da
wata qarya. Ya ce Holako ya yi farin ciki da zuwansa, ya amince da sulhu da barin
yaqi kuma har ma yana son ya aurar da xiyarsa ga xan sarkin Musulmi, Yarima
mai jiran gado Abubakar. Sarki ya yi murna, aka sa ranar da za a je xaurin aure
kuma daula duka ta fita zuwa sansanin Holako domin yin shagali.
Babu wanda aka bari a baya, Sarki da Yarima da manyan wazirai da
kwamandojin soja da malamai da limamai da alqalai da attajirai da duk wani mai
faxi a ji sun fita baki xaya. Isarsu sansanin Holako ke da wuya, da ma ya shirya.
Sai ya sa aka kange mafita duka aka yanke shugabannin nan baki xaya, sai
abokinsu waziri Binu Alqami kawai ya rage. A yammaci guda sai Bagadaza, da
sauran al’umma, suka zama jiki ba kai.
Su kuwa yajuju da majuju suka shiga aiki. Kwana arba’in suna kisa, suna
qone gidaje da kasuwanni da masallatai da makarantu da xakunan karatu (laburare)
sai da kogin Dajla ya rikixe ya zama ja saboda jini. Suka kame mata da yara, suka
yi ta zina da mata sharifai Hashimawa a cikin masallatai.
Wannan shi ya kawo qarshen daular Abbasiya wacce ta yi shugabancin
duniya xaruruwan shekaru kuma daga nan Musulmi ba su sake samun wannan
matsayi ba na shugabancin duniya. Mutum miliyan xaya da dubu xari takwas
20
(1,800,000) ne suka rasa rayukansu a wan nan kisan kiyashi wanda tarihi bai tava
ganin irinsa ba.1
Marubucin tarihi xan Shi’a mai suna Mirza Muhammad Baqir Khuwansari,
ya kawo wannan qissa a cikin littafinsa, Raulatul Jannat, yana yabon Waziri Binu
Alqami a kan wannan xanyen aiki da ya tafka, kuma ya ce waxanda suka rasa
rayukansu duka suna cikin wutar Jahannama.2 Ayatullahi Khumaini ma ya yaba
wa wannan xan ta’adda, maci amana, kuma ya xauki wannan mummunan aiki nasa
a matsayin babbar hidima ga Musulunci!! Don haka ba ya ambaton sa sai ya ce:
Raliyallahu Anhu, watau Allah ya yarda da shi!3
Wannan yana nuna cewa qissar ba qage aka yi wa ‘yan Shi’a ba; su ma sun
san da ita, sun yi na’am da ita, kuma sun tabbatar da ita a cikin littafansu.
Qaryar Gwagwarmaya ta Qare
Yawancin ‘yan Shi’ar Nijeriya an yaudare su zuwa shiga qungiyar da sunan
GWAGWARMAYA. An nuna musu cewa juyin juya halin qasar Iran na shekarar
1979 juyi ne na Musulunci, kuma manufarsa ita ce qwato haqqin Musulmi da
yaqar zalunci da tabbatar da adalci.
Malam Ibrahim Zakzaki da maqarrabansa, tare da wasu ‘yan boko da wasu
malaman addini masu jimirin sauyi, duka an yaudare su da wannan farfaganda. Sai
suka xauki qasar Iran a matsayin wata jarumar qasa mai bajinta, wacce ta fito
1 Domin ganin wannan kissa, sai a duba Albidaya wal Nihaya na Abul Fida Isma’il binu Kathir, bugun Darul
Kutubil Ilmiyya, Bairut, 1408/1988, mujalladi na 9 shafi na 154; da Almuntaqa min Minhajil I’itidal na
Muhammad binu Uthman Alzahabi, ta’aliqin Muhibbuddin Alkhadib, bugun Maktabatu Daril Bayan, ba tarihi,
shafi na 298.
2 Duba Raulatul Jannat fi Ahwalil Ulama’i was Sadat na Muhammad Baqir Alkhuwansari, bugun Bairut, 1991,
shafi na 578.
3 Duba Kashful Asrar na Sayyid Hussain Musawi, tushen da ya shude, shafi na 90.
21
domin yaqar qasar Yahudu ta Isra’ila da uwargijiyarta Amurka. Ta haka ne, kuma
sannu a hankali, da yawa daga cikin waxan nan mutane suka shiga Shi’a ba tare da
sani ba.
A yau, bayan kimanin shekaru 35 da juyin juya halin na Iran, mahukuntan
qasar ‘yan Shi’a sun yaye mayafin yaudara da taqiyya, kuma sun fito fili suna nuna
mugun nufinsu na yaqar Sunna da yaxa mugunyar aqidarsu ta Shi’a. A yau tarihi
yana maimaita kansa, inda ta’addancin ‘yan Shi’a ya fito fili kuma qiyayyarsu ga
wannan al’umma ta bayyana a sarari. Qasar Iran da masu goyon bayanta a ko ina a
duniya su ke kan gaba wajen yaqar Ahalus Sunna da zubar da jininsu da taimakon
kafirai a kansu.
A nan za mu ba da misalai kaxan na irin wannan ta’addanci don masu
hankali su lura. Amma bari mu fara da bayanin rayuwar Ahalus Sunna a qasar Iran
bayan juyin juya halin ‘yan Shi’a.
Rayuwar Ahalus Sunna A Qasar Iran
Mutane da dama ba su da masaniya cewa akwai Ahalus Sunna masu yawa
dake rayuwa a qasar Iran saboda rashin jin xuriyarsu. Wannan kuwa ya faru ne a
dalilin danniya da take haqqi wanda gwamnatin Iran ta Shi’awa take yi musu.
Bayan samun nasarar juyin juya halin Iran, shugabannin Shi’a sun fara da
zartar da mugun nufin su a kan Ahalus Sunna na qasar, kafin su mayar da
hankalinsu ga sauran Musulmi na wasu qasashe. Bayanai da alqaluma masu
biyowa, waxanda suka fito daga kafafen gwamnatin Iran ita da kanta, suna tabbatar
da haka.
22
A gwargwadon qididdigar san-san ta shekarar 2008, adadin mutanen Iran ya
kai miliyan sittin da biyar, da dubu xari takwas da saba’in da biyar, da xari biyu da
ishirin da uku (65,875,223). A cikin wannan adadi, kimanin miliyan 20 Ahalus
Sunna ne. Gamin gambizar addinan qasar ya kasance kamar haka: Rafilawa: 65%,
Ahalus Sunna: 25%, Yahudawa da Kirista da Majusawa: 10%. Yawancin Ahalus
Sunna na qasar sun kasu izuwa qabilun Qurdawa da Balushawa da Turkumawa.
Akwai Larabawa kaxan a yankin qasar da ake kira Arabistan. Amma yawancin
‘yan Shi’a su Farisawa ne.
Tun kafin juyin juya halin Iran, Ahalus Sunna, kasancewarsu ba Farisawa
ba, sun fuskanci danniya da take haqqi. Wannan ya sa wasu daga cikin su suka
goyi bayan juyin da fatan za su samu sa’ida, amma bayan cin nasara sai Khumaini
ya juya musu baya har suka qwammace gidan jiya. Yawancin shugabannin Ahalus
Sunna da suka marawa juyin baya, kamar su Shaihu Ahmad Mufti Zadah, Imam
Khumaini ya sa an rataye su.
Duk da yawan Ahalus Sunna (kimanin rubu’in ‘yan qasa), kundin tsarin
mulkin qasar bai san da su ba. Maimakon haka, kundin ya bayyana qarara cewa
qasar tana bin tafarkin Shi’awa ‘Yan Dozin. A majalisar qasar mai wakilai 290,
Ahalus Sunna kujeru 12 kawai aka ba su. Wannan yana nufin cewa, ko wane xan
majalisa xaya Ahalus Sunna yana wakiltar kimanin mutane miliyan xaya da rabi
ke nan, a yayin da ko wane wakili xan Shi’a yake wakiltar Shi’awa 200,000 kacal.
Zaluncin wannan tsari ba sai an faxi ba. A haqiqa ma, waxannan kujeru 12 an
bayar da su ne kawai saboda a yi talla da cewa an bayar; idan ba haka ba me 12 za
ta yi a cikin 290?
Babu ‘yancin addini ga Ahalus Sunna na Iran. An haramta musu gina
masallatai a manyan biranen qasar, kamar Asfahan da Shiraz da Yazd. A babban
23
birnin qasar, Tehran, inda ake da Musulmi Ahalus Sunna miliyan guda, an haramta
musu gina masallaci koda guda xaya, a yayin da aka qyale Yahudawa da Kirista da
Majusawa suka gina wuraren ibada xai-xai ko wannensu. Masallatan Ahalus
Sunna da aka ba su damar ginawa a qauyuka da yankunan karkara suna qarqashin
kulawar hukuma ta dun-dun-dun. Haka nan kuma an haramta musu kafa makarantu
na kansu.
A taqaice, Ahalus Sunna a Iran an haramta musu kafatanin haqqoqinsu na
‘yan qasa. A yau, su suka fi kowa ci baya da jahilci da talauci da rashin aikin yi a
qasar.1
Tarihi Yana Maimaita Kansa
Bayan gwamnatin juyin juya hali ta Iran ta shimfixa tsarin danne Ahalus
Sunna a cikin gida, kuma a lokaci guda ta girke na’urar farfaganda domin farauto
na waje, sai ta shiga qaddamar da aikin Shi’a na tarihi: yaqar Musulunci da rushe
tafarkin Sunna.
Kuma da yake a yanzu kixa ya sauya, to sai rawa ma ta sauya. Don haka a ci
gaba da wannan yaqi na tarihi, qasar Iran a matsayinta na mai riqe da kambin yaxa
tafarkin Shi’a a duniya a yau, ta fara da ware dukiya mai yawa, wasu rahotanni
suna faxin kimanin kashi goma bisa xari (10 %) na dukkan dukiyar qasar, don
wannan manufa. (Kada a mance Iran tana cikin qasashe huxu da suka fi yawan
arziqin man petur a duniya.) Ta kafa cibiyoyi na qasa da qasa, kuma ta buxe sassa
a dukkanin ofisoshin jakadancinta dake qasashen qetare don tabbatar da wannan
aiki.
1 Alkaluman da muka bayar a sama sun fito daga Kamfanin Dillancin Labarai na Iran, IRNA. Dangane da sauran
bayanai kuma, sai a duba littafin Alshi’atu Shahidina Ala Anfusihim na Liya’uddin Alkashif, bugun Maktabatu
Ahlil Bait, 1428/2007; da littafin Ahawalu Ahalis Sunna fi Iran na Abdulhaqq Al’asfahani.
24
Sa’an nan qasar Iran ta kafa qawance da ‘yan Shi’a na sauran qasashe,
waxanda ta zama uwa a gare su, su kuma suka zama ‘ya’ya masu biyayya, saboda
haxa qarfi waje guda da samar da wani gagarumin yunquri don farfaxo da yaqin
tarihi tsakanin Sunna da Shi’a wanda ya fara tun a zamanin Sahabbai, lokacin da
aka rushe daular Farisa a qarqashin jagorancin Sarkin Musulmi Umar binul
Khaxxabi, Allah ya qara masa yarda.
Sabon yaqin Shi’a a wannan zamani ya haxe kafatanin fagage: fagen siyasa
da diflomasiyya, fagen tattalin arziki, fagen ilmi da al’adu, da kuma fagen fama.
Haka nan ya haxe dukkan nau’in makamai: makamin kuxi da abin duniya,
makamin kafafen bayanai da yaxa labaru, makamin mutu’a da taqiyya, da
makamin kisa wanda ya fara daga bindiga da bam har ya zuwa nukiliya.
Sabon Ta’addancin Shi’a
A da, qasashen Turai da Amurka suna zargin Iran da cewa ita qasa ce ta
‘yan ta’adda, mai xaurewa ta’addanci gindi, Musulmi na jin ciwo. Sai ga shi
wannan zargi ya bayyana a zahiri, ta yadda duk mai idanu yake iya gani. Sai dai
abin mamaki, a yanzu qasar Amurka tana maraba da ta’addacin Iran; saboda ta lura
cewa yawancin ta’addancin nata a kan qasahen Musulmi mabiya Sunna yake
qarewa. A yau, babu wata qasa a duniyar Musulmi wacce ta’addancin Iran bai
addabe ta ba. Ga ‘yan misalai:
Lebanon: Wannan qasa ita ce mazaunin qungiyar Hizbullah, qungiyar ta’addanci
mafi qarfi a Gabas ta Tsakiya, wacce kuma ita ce hannun daman qasar Iran wanda
take amfani da shi a wajen ayyukanta na ta’addanci a qasashen duniya.
Suriya ko Sham: Qasar Iran tana taimakon gwamnatin Bashar Asad ta tsuraru ‘yan
Shi’a wacce take kafsa yaqi da ‘yan tawaye masu bin tafarkin Sunna, waxanda
kuma su ne mafiya rinjaye, tun farkon shekarar 2011. Gwamnatin Asad ta dogara
kacokan da taimakon Iran, na kuxaxe da makamai da diblomasiyya da qwararrun
soji masu ba da shawara, wajen ta’addancinta a kan ‘yan qasarta wanda ya haxa da
25
rushe kimanin kashi biyu bisa uku na dukkan biranen qasar, kashe sama da mutane
dubu xari biyu da hamsin, kore sama da miliyan shida daga gidajensu, da amfani
da muggan makamai waxanda aka haramta a dokokin qasa da qasa.
Yaman: Qasar Iran tana taimakon ‘yan tawayen Hutsawa marasa rinjare, masu bin
tafarkin Shi’a, a qoqarinsu na vallewa daga qasar Yaman da kafa qasarsu ta ‘yan
Shi’a.
Iraqi: Iran ta taimakawa ‘yan Shi’ar Iraqi wajen kafa qungiyoyin ina-da-kisa
waxanda suka taimaki sojojin Amurka a kan kifar da gwamnatin Saddam Hussaini
da rushe biranen mabiya Sunna, kamar birnin Falluja, da karkashe su mafi munin
kisa. A matsayin sakamako, qasar Amurka ta taimaka wa ‘yan Shi’a su mulki
qasar Iraqi da da’awar cewa wai su ne masu rinjaye.
Baharain: Iran tana tallafawa ‘yan Shi’ar qasar Baharain, waxanda suke da’awar su
ne masu rinjaye wai amma mabiyan Sunna suna mulkinsu mulkin danniya. Yau
kimanin shekaru biyar ke nan babu zaman lafiya a qasar. Shekaru biyu da suka
wuce, ‘yan Shi’ar sun kusa yin nasarar tankwave gwmnatin qasar ba don taimakon
qasar Sa’udiyya ba gare su.
Nijeriya: A cikin watan Oktoba, 2010, jami’an tsaro sun kama kontena goma sha
uku maqare da miyagun makamai a tashar jiragen ruwa ta birnin Legas. Bincike ya
tabbatar da cewa waxan nan makamai sun fito ne daga qasar Iran, kuma ofishin
jakadancin qasar a Abuja ya amsa cewa xaya daga mutanen da aka kama da
makaman ma’aikacinsu ne. Bayan shari’a da ta xauki sama da shekaru biyu, an
samu mutane biyu da laifi, ciki har da jami’in jakadancin na Iran, kuma kotu ta
xaure su shekaru 17 ko wannensu.1
A cikin watan Fabrairy, 2013, jami’an leqen asiri na Nijeriya sun cafke wasu
samari da suka yi karatu a qasar Iran, suna shirin kai hare-haren ta’addanci da
nufin kashe wasu shugabannin Musulmi na qasar nan, ciki har da tsohon shugaban
mulkin soja Ibrahim Babangida, da Sarkin Musulmi mai murabus, Sultan Ibrahim
Dasuqi. Bayan bincike, ya tabbata cewa waxan nan samari suna yi wa qungiyar
1 Domin ganin wannan labari, duba jaridar Dailay Trust, fitowar 15 ga watan Mayu, 2013, shafi na 46.
26
ta’addanci da Iran ke mara wa baya, watau Hizbullah, aiki. Jaridun qasar nan da
kafafen yaxa labarai na qasashen qetare duka sun ruwaito wannan labari.1
Haka nan, a wannan shekara dai ta 2013, an gano makamai masu yawa voye
a wani gida a birnin Kano. Bayan bincike, an zargi wasu qwarori ‘yan qasar
Lebanon, waxanda ake jin suna da alaqa da qungiyar Hizbullah, da mallakar
waxan nan makaman.2 Har yanzu maganar tana kotu.
Wannan qungiya ta Hizbullah, wacce take adana makamai a Kano saboda
mugun nufi ga Musulmin qasar nan, ‘yan Shi’ar Nijeriya qarqashin jagorancin
Ibrahim Alzakzaki suna xaga tutar ta a fili a cikin jerin gwano da suke gudanarwa
a biranen qasar na.3
Abinda muka ambata a nan xan misali ne kawai na sabon ta’addancin ‘yan
Shi’a da uwargijiyarsu, qasar Iran, da kuma mugun nufi wanda suke qudure da shi
ga wannan al’umma. Muna roqon Allah ya tsare mu da sharrin bidi’a wacce take
sunce imanin mutum ba da saninsa ba.
Muhimmiyar Sanarwa
Dukkan littafan malaman Shi’a, da muka yi amfani da su a rubutun wannan
taqaitaccen littafi, akwai su a xakin karatu (laburare) na cibiyar Markazus Sahabah
dake Sakkwato. Laburaren a buxe take ga kowa da kowa.
Tare da gaisuwar xan uwanku a Musulunci
Dr. Umar Labxo
1 Gidan talabijin na Aljazeera (ta Larabci) ya watsa labarin ranar 21 ga watan Fabrairu, 2013.
2 Duba jaridar Dailay Trust, Juma’a 31 ga watan Mayu, 2013, shafi na 1 da na 5.
3 Domin ganin hoton ‘yan Shi’ar Nijeriya dauke da tutocin Hizbullah, duba jaridar Dailay Trust, fitowar Talata 22
ga watan Mayu, 2012, shafi na 3.