Labarai




da sunan allah mai rahama mai jin kai


godiya ta tabbata ga allah, tsira da amincin allah su tabbata


ga annabi muhammad da iyalansa da sahabbanshi.


DAN UWANA MAKARANCI:


acikin wannan littafin na yi kokarin tattara wasu daga cikin


abubuwan da musulunci ya kebanta dasu a takaice domin ya


zama mabudi don yin bincike da kuma da zurfafa tinanin masu


bincike akan hakikanin, wadda kuma ya tabbata cewa da masu


adalci daga cikin wadanda ba musulmai ba da ya zama


sanadiyyar musuluntarsu tare da wasu sharuddah kaman


hakan:


= niyya ta gaskiya domin neman gaskiya da saninta da kuma


bin ta, ba wai farautar laifuffuka ba da kuma bincikensu, domin


lallai allah madaukakin sarki ya jibinci shiryar da wanda yake


neman gaskiya domin ya shiryu, hakan zai zama ne ta hanyar


samun jin dadi da budewar kirji da kuma sawwake hanyoyin da


zasu kaishi ga hakan, allah yace; duk wanda allah yake son ya


shiryar dashi sai ya budemai kirjinshi ga musulunci, wanda


kuma yayi niyyar batar dashi saiya sanya kunci akirjinshi da


kuma laifi, ya zama kaman wanda zai tashi zuwa sama, hakane


allah yake sanya datti a zukatan wadanda basuyi imani ba.


= rokon allah na gaskiya gareshi shi kadai, da kuma maimaita


hakan a gareshi domin sanin gaskiya da samun dacewa wajen


ansan aikin, allah madaukakin sarki yana cewa: mutane sun


kasance a farkonsu alumma ce guda daya, sai allah ya aiko


annabawa da manzanni suna masu bushara da kuma gargadi


kuma ya saukar da littafi tare dasu da gaskiya domin suyi


4


hukunci tsakanin mutane cikin abinda skayi sabania cikinshi,


ba abinda ya sanyasu sabani face abinda aka basu na daga


littafi domin kiyayya ko hassada a tsakaninsu, sai allah ya


shiryar da wadanda sukayi imani daga cikinsu bisa ga abinda


sukayi sabani acikinshi daga bin gaskiya tare da izininshi,


kuma allah yana shiryar da wanda yaso zuwa ga hanya


madaidaiciya, suratul baqara aya ta 213.


= barin son kai na addini da makahuwar biyayya ga addinin


iyaye da kakanni wanda aka ginashi ba akan ilimi ba da lura,


da karanta littafan koyar da addinin musulunci da hankali da


kuma ilimi ba tare da wani raayi ba na addini da wasu hanyoyi


na tinani wadda aka gada, allah yana cewa; idan aka ce musu


su bi abinda allah ya saukar sai suce mu dai zamubi abinda


muka samu iyayanmu akanshi ne, ko dai ana tinanin iyayansu


basa hankaltar komai ne ko kuma basu da shiriya. suratul


baqara aya ta 170.


dole ne mai bincike wanda ba musulmi ba yasan cewa lallai


musulunci ba na larabawa bane kawai, shidai na duka duniya


ne gaba daya, babu bangaranci a musulunci, duk wanda yayi


imani dahsi kuma yayi aiki to shine musulmi koda kuwa ya


kasance a karshen duniya yake, ko ya zama farar fata ne ko


baqi, haka kuma duk wanda baiyi aiki dashi ba kuma baiyi


imani dashi ba bai zama muslmi ba koda kuwa ya kasance


daga tsatson annabin musulunci annabi muhammada tsira da


amincin allah su tabbata a garesghi, sahabi bilal dan rabah


allah ya yarda dashi ya kasance mai kiran sallah ga annabi


muhammad allah ya karin tsira a gareshi kuma bawa ne dan


qasar habasha, shi kuma suhaib mutumi qasar room ne, shi


kuma salman dan qasar faris ne, kaman yadda musulunci bai


takaitu ga garin makkah, madina da yankin larabawa ba


kawai, ko wace daula inta gina muslunci to sunanta daular


musulunci koda kuwa ta kasance a qasashen afirka.


5


= daukan musulunci da yin hukunci acikinshi itace hanya ko


sharia cikakkiya amman ba daukanshi ko hukunci akanshi aiki


ne na mutum daya ba ko wani gari da ba wajibinsu bane,


akwai qasashe da dama da kuma bangarori na addinai


wadanda suke jingina kansu da musulunci amman a hakika


musulunci yayi hannun riga dasu, da kuma wadda take da


tasiri mai girman gaske wajen jirkita musulunci ingantacce da


kuma koran wdanda ba musulmai ba daga gareshi da kuma


toshe hanyoyin isa zuwa gareshi saboda dalilin wasu ayyuka ko


abubuwan da aka qudurce da kuma ayyuka kodai na magana


ko kuma na aiki da suke aikatawa ta fadi a baki amman


zukatansu ba haka bane, kuma hankali ingantacce baya


daukansu, kuma halitta mai inganci tana kin hakan da kuma


zamantakewar zamani kuma su alakantata da musulunci, akan


hakane ya kamata asan cewa duk wani abin qudurcewa ko


aikin da yake cin karo da ingantaccen hankali da cikakkiyar


halittar dan adam kuma dandano madaukaki ya ki wannan


abun kuma musulmia basuyi ittifaqi akan wannan abun ba to


tabbas wannan abun ba musulunci bane, domin musulunci


kadaita allah ne kawai ba abinda ke cudanya dashi na daga


shirka, da kuma bautar da babu riya acikinta, da dabiun da


babu fitsara acikinsu, da tsari na rayuwa wanda babu batanci


acikinshi, da bayanin da babu rudu acikinshi, saidai musulmai


suna shan baban wajen ansan abu ko qinshi, wani yanayi ne


kadan wani kuma da yawa, allah yayi bayani haka cikin qurani


inda yake cewa; sannan muka gadar da littafinmu ga wadanda


muka zaba cikin bayinmu, daga cikinsu akwai mai zalintar


kanshi, akwai kuma mai kyakyywara niyya sannan akwai mai


rigegeniya da alkhair da izinin allah, wannan shine rabo mai


girma, suratul fadir aya ta 32.


= daukan ilikmomin addini ta hanyar bincike da neman


gaskiya ba ta hanyar sadar da zumunta ba wadda take ba mai


adalci ba, ko kuma wasu mutane da masu kama dasu, hakan ya


6


zama wajibi ga mai neman sanin musulunci ya nemeshi ta


hanyoyinshi ingantattu da kuma inda aka samoshi na asali


wato qurani mai girma da hadisai ingatattu sannan kuma


abinda alummah suka tafi akanshi a karkashin fadin annabi;


na bar muku abubuwa biyu indai kukayi riko dasu bazaku bace


ba, littafin allah ya sunnata wato hadisanshi ingantattu’ albani


yace hadisi ne mai kyau.


= ko wani mutum yana neman cikakken abu mai kyau dangane


da alamuranshi na duniya, kuma wannan haline na rai na dan


adam, wadda akanta allah ya halicci mutum kuma hakan yana


faruwa ne ta bangaren lura da yake da abinda yafi falala a


gareshi ta bangaren fifikon da yake samu cikin abinda zai


dauka ko kuma ya jefar, haka kuma ya dace ace yana neman


abinda yafi ko wanne ingaanci a addininshi wanda da shine zai


samu natsuwar zuciyarshi da kubutar da jikinshi da


hankalinshi, da mutuncinshi sannan kuma dukiyarshi, hakan


kuma bazai smu ba saita dalilin karatu mai natsuwa da kuma


kimantawa mai kyau da kuma rashin gaggawa wajen hukunci


dauan hukunci lokacin da hukuncin ke hannunka


= ya sani sani na hakika lallai halin da mutum zai shiga bayan


mutuwa kodai ya zama zuwa aljannah wadda fadinta kaman


fadin sama da qasa, ko kuma zuwa wuta wadda ake rurata


wadda makamashinta sune mutane da duwatsu akanta akwai


malaiku masu tsananin karfi wadanda basa sabawa allah cikin


umarnin da ya basu kuma suna aikata abinda ya musu umarni,


allah madaukakin sarki yana cewa; hakane kuma muka maka


wahayin alqurani da harshen larabci domin ka gargadi


maabota wanann alqaryar (makkah) da kewayenta kuma kayi


gargadi ga ranar da babu shakku acikinta wasu sashin na


mutane suna aljannah dayan sashin kuma suna jahim (wuta)


suratu shura aya ta 7.


7


ina rokon allah ga duk wanda ya karanta wannan littafi da


allah ya datar dashi da kuma budewar kirji domin karban


gaskiya da binta


www.islamland.com


8


musulunci shine mika wuya ga allah ta yadda zai zama kaman


yadda allah yayi umarni dashi kuma yadda yakeso a bautamai


da barin hadashi da wani abokin tarayya da aikata umarninshi


da kuma barin abubuwan da ya hana, musulunci shine tsani


tsakanin bawa da ubangijinshi, yana ganawa dashi sau biyar a


rana daya a dare da rana acikin sallolin da allah ya farlanta


akan bayinshi, wanda ya hada da sauran sunnonikaman yadda


ya zama akwai alaqa sosai tsakanin allah da bawanshi wadda


mai ci gaba ce a cikin adduoin da zikirori wadda mutum ke


fadansu acikin ayyukanshi na yau da kullun wadda kuma taje


kara karfin alaqarsu, akwai anbaton allah na cin abinci, da


kuma bayanshi, da kuma adduar shiga bayi da adduar fitowa


daga bayin, da adduar shiga gida da adduar fitowa daga


gidan, da adduar bacci da adduar tashi daga bacci, da adduar


yin alwala da adduar gamawa, da addua yayin saduwa da


iyali, da adduar hawan abin hawa, rayuwar mutum gaba


dayanta tana daure ne da bin hanyoyin ubangiji kaman yadda


allah yake cewa; kace lallai sallah ta da yankana da rayuwata


d mutuwa ta suna ga allah ubangijin talikai


Surat Al-An‘aam Aya ta 162


9


duk da cewa ddinin musulunci shine addinin karshen da allah


ya saukar kuma shine addinin da allah bai yarda a bautamai


ba sai dashi, kaman yadda yace; duk wanda ya nemi wani


addini koma bayan musulunci to lallai ba zaa karba mai ba


kuma aranan qiyama yana daga cikin masu asara, hakan yada


wannan addinin ya kebanta da wasu abubuwa ta yadda zai


kasance tare dasu ta bangaren inganci har zuwa ranar qiyama,


daga cikin wadanna kebantattuun abubuwa akwai;


1- cikar hankali;


addinin musulunci addinine na cikar hankali lafiyayye wadda


akanta ne allah ya halicci mutane wadda ta zama mai girma


wajen abinda mutum zai qudurce na tabbatar da samuwar


allah abin bauta wadda ta hanyarshice zai tabbatar da


samuwar allah da sanin niimominsu da tinaninsa acikin


wannna duniyar wadda zata kaimu gareshi, allah yana cewa;


ka tsayar da fuskarka akan addini kana mai bin gaskiya kuma


kana kin qarya, halittar allah ce daya halicci mutane akanta,


kuma babu mai canza halittar allah, wannan shine tsayayyen


addini amman da yawan mutane basu sani ba, suratu rum aya


ta 30.


wannan shine asalin akan halitta gaba daya kuma wannan


halittar ta mutum akwai abubuwa da zasu iya yin tasiri cikin


abubuwan da suke kewaye da mutum saita zagayeta acikin


tafiyarta ingantacciya sai hakan yasa ta karkace daga hanya


mai kyau har mutum yayi shirka da allah ko ya bautama


waninshi ko ya musanta samuwarshi, manzan allah tsira da


amincin allah su tabbata a gareshi yana cewa; babu wani abin


10


halitta face an haifeshi akan asalin cikar mutum ta musulunci,


amman saidai iyayanshi su mai dashi koo bayahude, ko


banasare, ko bamajuse,maana iayyanshi su mayar dashi


bayahude k o bamajuse bisa gwargwadon yadda suke bin


addinin kuma ya burgesu.


2- KADAITAWA


musukunci shine addinin kadaitawa da tsarkake ibada ga allah


shi kadai ba tare da abokin tarayya ba hakan saiya hafar da


alaka ta kai tsaye tsaknin allah da bawanshi wadda ta tsayu


aka imanin tsantsa da kuma komawa zuwa ga allah shi kadai,


wajen neman biyan buqatu da neman gafara da taimako daga


gareshikai tsaye ba tare da shamaki ba ko tsani, kuma hakan


ya rusa duk abinda ake sawa na tsaknin allah da bawanshi


domin mena kusanci zuwa ga allah kuma ya aibanta mushrikai


na bubuwan da suke sawa tsakninsu da allah, allah yana cewa;


lallai ku saurara domin addini na allah ne his kadai kuma a


tsarkakeshi, wadanda suka riki wasu abubuwan neman kusanci


ga allah sun acewa bas bauta musu dan komai sai dan su


kusantar dasu zuwa ga allah, suratu zumar aya ta 3.


kalmar tauhidi wato ‘la ilaha illallah’ tana nufin babu abin


bautawa da gaskiya sai allah kuma wanna kalmar itace


mabudin shiga addinin musulunci, kuma saaboda ita ne allah


ya halicci dukkan halittu domin su bautamai, kuma ta dalilinta


ne allah ya halicci aljannah da wuta, kuma itace abinda


annabwa sukayi kira da ita tin daga zamnin annabi nuhu zuwa


ga cikamakon annabawa manzan allah annbai muhammad


tsira da amincin allah su tabbata agareshi, allah yana cewa;


babu aika gabanainka ba cikin annabawa face sai mun yi musu


wahayin cewa babu abin bautawa da gaskiya sai allah kuma ku


bautamun, suratul anbiyai aya ta 25


11


KALMAR TAUHIDI TANA NUFIN:


= kadaita allah shi kadai cikin bautarshi ba tare da abokin


tarayya ba dukanshi da kuma tabbatar da ita gareshi da


kadaitashi cikin bauta ba tarea da anyi mai shirka da komai ba


cikin bautarshi, allah yana cewa; wancananku shine allah


babu abin bautawa da gaskiya saishi shine mahaliccin komai


da komai ku bauta mai, kuma shine mai wakilci akan komai,


suratul an’am aya ta 102.


= kadaita allah cikin abubuwan da ya halitta da kuma qudurta


cewa shine mamallakin komai da komai kuma wanda ya halicci


dukkan halittu kuma shine mai azurtasu kuma shine mai rayasu


kua mai kashesu kuma hsine zai tashesu ranar da babu shakku


acikin aukuwarta, babu mamallaki ko mahalicci ko mai sarrafa


abubuwa kamanshi acikin wannan duniyar, babu mai tsara


yadda zaayi rayuwa ko muamala amatakin mutum daya ko


kuma duka dukkan halittu saishi, kuma babu mai haramtawa ko


halattawa saishi, allah yana cewa; shine rayayye babu abin


bautawa da gaskiya saishi ku rokeshi kuna masu tsarkake


zuciyarku gareshi acikin addini, godiya ta tabbata ga allah


ubangijin talikai, suratul gafir 65.


= kadaita allah cikin sunayanshi da siffofinshi tare da duka


siffofinshi da suka dace dashi ba tare da wani aibu ba ko


tawaya da kuma tsarkakeshi daga dukkan wwata halitta kar


tayi kama dashi ko shige dashi, allah yana cewa; shine wanda


ya kirkiri halittar sammai da kassai kuma ya halitta muku


mataye daga gareku haka kuma ya halicci mataye ma cikin


dabbobi domin ya dinga halittarku daga garesu, babu abinda


yayi kama dashi kuma shine maiji mai gani, suratu shura aya


ta 11.


12


3- BAUTAR ALLAH


allah madaukakin sarki bai halicci bayinshi ba sai dan su


bauta mai kaman yadda yace; ban halicci mutane da aljanu ba


sai dan su bauta mun, suratu dur aya ta 56.


buqatuwar mutane zuwa ga allah buqata ce wadda ya halicesu


akanta kaman yadda jikinsu suke da buqata zuwa ga abinci da


kuma abinsha domin su rayu, kaman hakane rayukansu suke da


buqata zuwa ga bautar allah domin kwanciyar hankali da


nutsuwa, anan ne zamuga ni a fili cewa lallai su halittun allah


ba tare da cire kowa ba suna da buqatar abin bautar da zai


dinga biya musu buqatunsu na yau da kullun, tare da


kwanciyar hankali da nutsuwa domin komawa gareshi tin daga


zamanin annabi adam zuwa lokacin annabi nuhu allah


madaukakin arki kawai ake bautama wa ba tare da shirka ba,


daga wannan lokacin ne aka fara samun shirka cikin bautama


allah sai aka samu masu bautama duwatsu da bishiyoyi da


kuma wasu dabbobin, da wasu abubuwa na rayuwa, hakan sai


yasa allah ya aiko da manzanni domin su mayar da mutane


zuwa ga bautar allah shi kadai, har wanda yake ganin ma babu


allah – allah ya tsarkaka daga wannan batu- shima duk da


haka yana da abinda yake bauta mawa wato zuciyarshi da


kuma shaidanin da yake sashi aikata wadannan abubuwan, da


kuma abinda zuciyarshi ke sanya mai na shaawa, wannan


kuma shine karshen zalincin da mutum zaima kanshi da kuma


waninshi, domin shi mai yin haka yana rayuwa ne cikin


wannna duniyar ba tare da wata manufa ba, da kuma


kekashewar zuciya, kuma a lahira sakamakonshi itace wutar da


ake rurata, babu mai shiganta sai shakiyyi, wanda ya karyata


ayoyin allah kuma ya juya musu baya, kuma hakan zalici ne ga


waninshi domin komai zai daura alhakinshine akan waninshi,


13


kuma bazai samu abinda zai iya bi ba, ko kuma inda zai tsaya,


kuma bazai san abinda ya dace ba da wanda bai dace ba,


hakan yana gasgata fadin allah ne; shin ka bani labarin wanda


ya riki abin bautarshi itace zuciyarshi kuma hakan yasa allah


ya batar dashi daga sanin wani ilimi kuma allah ya shafe


zuciyarshi yasa mata murfi shin waye zai shiryar dashi bayan


allah?? shin bakwa tinani ne, suratul jasiya aya ta 23.


a bisa yanayi na duniya ka duba gefenka zakaga wanda baya


bautawa allah kuma yana mai shirka wanda ba musulmi ba


maabota aqida ingantacciya wadanda suka bautawa allah shi


kadai, yahudawa sun canza addini suna kiran uzairu wato dan


allah ne, haka nasara suma sun canza addini suna kiran isa


almasihu cewa dan allah ne, banda ma wadanda suke bautawa


abinda ko a hankalce bai dace ba, da kuma cikakkiyar halittar


mutun, kuma zukata na gaskiya suna kin wannan abun, daga


bautar gumaka ko dabbobi da taurari allah yayi gaskiya inda


yake cewa; lallai abinda kuke kira koma bayan allah suma bayi


ne kaman ku, ku kirasu mana su ansa muku indai kun kasance


masu gaskiya, suratul aaraf aya ta 194.


4- HANKALTUWA


musulunci addinine na girmama hankali da tinani, akwai ayoyi


da dama na qurani da suka zo da lura da hankalin mutum


kuma allah ya kira mutane domin yin tinani da hankaltuwa


akan halittarshi yake cewa; shin bazaku hankalta ba, shin


bazaku yi tinani ba, shin bazaku sani ba, shin ba zaku lra


ba,,,,,,,,,,,,,,,,,allah yana cewa; lallai acikin halittar sama da


qasa akwai abubuwan lura ga masu imani, acikin halittarku da


kuma abubuwan da allah ya watsa muku na dabbobi akwai


ayoyi ga masu yaqini, da kuma canje-canjen dare da yini da


abinda allah ya saukar na daga ruwan sama wanda yake rayar


14


da qasa dashi bayan mutuwarta akwai abubuwan lura ga masu


hankali, suratul jasiya aya ta 3-5.


saidai allah madaukakin sarki ya kididdiga iya inda ya kamata


mutun yayi amfani da hankalinshi, baya halatta sai cikin


abinda ana iya fahimtarshi da gabobin nan guda 5 na jikin dan


adam, kaman abinda mutum zai iya gani, ko yaji da wasunsu,


amman abubuwan gaibu wanda allah ne kawai ya sansu wanda


mutum baya iya ganinsu ko jinsu, babu daman yin amfani da


hankali acikinsu domin gasgata su, domin amfani da hankali a


cikinsu ya zama abinda mutum baida halin aikatashi ne, kuma


mutum bai isa yasan hakan ba aita hanyar wahayin da allah


yama manzanni, allah yana cewa; allah shine masanin gaibu(1)


kuma bayan bayannawa kowa shi, saidai wanda ya yarda dashi


daga cikin annabawa domin sine wanda zai iya anuna mai abu


a gabanshi, suratul jinni aya ta 26.


duka koyarwatr musulunci suna, hankalin dan adam yana


shaidah gaskiyarsu da kuma ingancinsu da amfaninsu a wajen


dan adam domin duka umarnin allah da abubuwan da ya hana


adalcine babu zalinci acikinsu, allah bai taba umarni da wani


abu ba face akwai amfani acikinshi kuma zai zama akwai


alkhairi acikinshi, haka bai taba hani ba ga wani abu face ya


zama sharri nw da barna acikinshi, kuma wannan baya boyuwa


ga wanda yayi tinani ga ayoyin allah, da kuma hadisan annabi


tsira da amincin allah su tabbata a gareshi.


5- UBANGIJINTAKA


1-SUNE ABUBUWA NA BOYE WANDA BA WANDA YA SANSU SAI ALLAH MADAUKAKIN SARKI,


AMMAN AKWAI ABUBUWA NA BOYE DA ALLAH KE NUNAMA WANDA YASO CIKIN


BAYINSHI MANZANNI SU KUMA SUBA MUTANE LABARI.


15


koyarwar musulunci cikin abubuwan da allah ya halitta ada


kuma aqida da bauta da haqqoqin suna nan tabbatattu babu


abinda zai canza su ko sauyawa, allah yana cewa; shi qurani


saukakkene daga wajen allah, suratul waqia aya ta 80.


ba aikin mutum ane wanda zai iya samun cikas ko ko kuskure


da tasirantuwa da wasu abubuwa na waje wanda suke kewaye


da mutum na cigaba da abunda aka gada na zamantakewa,


allah yana cewa; shin hukuncin jahiliyya kuke nema, waye zaifi


allah iya hukunci a wajen masu yaqini, suratul maida aya ta


50.


musulunci shi kadaine addinin da babu wani abu daya shigeshi


na canzawa ko juyawa, kuma hujjojinshi sun kubuta daga ragi


ko qari abubuwan da ake hujja dasu a cikin musulunci sune:


1- qurani mai girma shine dai yadda yake tin da aka saukarwa


manzan allah tsira da amincin allah su tabbata gareshi, da


harufanshi da ayoyinshi da surorinshi kuma ba bu wani abu da


aka canza ko aha juyashi ko ragi ko qari, kuma an cirantoshi


ne daga jamaa masu yawan gaske wanda alada bata yadda da


cewa su taru dukansu akan karya ba, kuma ya zama sun


jinginashi ga abu wanda mutum zai iya gani, ta hanyar


haddaceshi acikin littafai da zukatan mutane, kuma musulai


sun kwadaitar dukkan kwadaitarwa akan littafin allah wajen


kula dashi da kuma koyanshi da koyar dashi domin alkhairin


da annabi ya fada cikin hadisi yace; mafi alkhairinku shine


wanda ya koya qurani kuma ya koyar dashi, bukhari ya


ruwaitoshi.


kuma qurani ya zama shine ake bautawa allah da haddaceshi


da kuma karantar dashi manzan allah yana cewa; duk wanda


ya karanta wai harafi acikin qurani yana da lada goma, ita


goman kuma zaa ninka mai ita, bana cewa alif lam mim harafi


daya ne, ah ah saidai alif harafi ne, lamun ma harafi ce, haka


16


mimun ma harafi ce, imam tirmizi ya ruwaitoshi, kuma yaa


cikin littafin sahihul jami mai lamba ta 6469.


2- Hadisan annabi muhammad tsira da amincin allah su


tabbata a gareshi itace hujja ta biyu wajen gina shariar


musulunci kuma mai bayanin qurani kuma mai fassara wasu da


yawa cikin hukunce hukuncen shi, kuma hakika an kareta daga


baraka ko qarya wajen shigar duk wani abun da ba daga


gareshi ba, kuma hakan ya faru ne dagawajen wasu mazaje


amintattu masu adalci, wanda suka bada lokacinsu da


rayuwarsu wjen karantar hadisa annabi da kuma karantar


isnadin wadannan hadisai da lafuzzansu da kuma darajojinsu


daga inganci zuwa rauni, da halayen masu ruwaitosu ta


bagaren adalcinsu ko kuma illarsu, sai suka tsaftace dukkan


hadisai wadanda aka ruwaitodaga manzan allah, basu bar


komai ba face wadanda suka inganta daga gareshi, kuma suka


iso garemu suna sua masu inganci.


6- GAME DUNIYA


addinin musulunci addinine na duka duniya ba tare da cire


wasu ba, bakaken fata da farare, larabawa da kuma ajamawa,


ako wani lokaci da kuma zamani, shine addinin da kowa da


kowa aka zama daya ba banbancin launi, ko yare, ko gari, ko


dangi, ko zamani balle kuma lokaci, shidai kadai aqida ce guda


daya bayyananniya kuma tabbatacciya kuma itace ta hadasu


suka zama daya, domin duk wanda yayi imani da allah shine


abin bauta, kuma yayi imani da musulunci shine addinin


gaskiya, kuma yayi imani da manzan allah shine annabi


gaskiya, ya shiga karakashin inuwar wannan addinin a ko wani


zamani kuma ako wani guri, amman sauran addinai koda su yi


ittifaqi da musulunci wajen suna amman su suna kebantane


kawai ga wasu mutane daban, kuma a wani lokaci da ban,


17


baya wuce wannan zamanin nasu zuwa wasunsu, annabi musa


ba zuwa ga bani israila kawai aka aikeshi ba, allah yana cewa;


mun baiwa annabi musa littafi kuma muka sanyashi shiriya


akan bani israila cewa kada su riki wani a matsayin mai


jibintar lamarinsu koma bayan allah, suratul israi aya ta 2,


lokaci da zamani ya ja akan banu israila bayan annabi musa


sai suka caza addininsu da annabi musa ya bayyana musu shi


kuma suka bace hanya, sai allah ya aiko anabi isa domin ya


mayar dasu zuwa ga gaskiya kuma ya canza musu addininsu


zuwa ga musulunci, allah yace; kuma muka hada a karshensu


da annabi isa dan nana maryam, yana mai gasgata abinda ya


gaba ceshi na daga attaura, kuma mun basahi littafin injila


acikinshi akwai shirya da haske kuma yana gasgata littafin


attaurar da ya gaba ceshi tareda shirya da waazantarwa ga


masu tsoron allah, suratul maidah aya ta 46.


sannan bayan wani lokaci mai tsayi allah ya aiko annabi


muhammad tsira da amincin allah su tabbata a agareshi kuma


ya aikoshine gaba daya zuwa ga mutane da aljanu kuma


dashine aka rife dukan manzanni, maana babu wani manzo


bayanshi, allah yana cewa; albarkun allah su tabbata gareshi


shine wanda ya saukar da qurani mai rarrabe qarya da gaskiya


domin ya zama abin gargadi ga dukkan talikai, suratul furqan


aya ta 1.


shi addinin musulunci duk da wannan game duniya da yayi


baya tilasta mutane wajen sai sun shigeshi, saidai shi yabar ma


kowa daman yayi zabi ga wanda addinin ya riskeshi wajen ya


ansheshi ko ya barshi, amman kuma du da haka ya bayyana


makomar wanda ya juya mai baya, allah yana cewa; ka fada


gaskiya daga ubangijinka, duk wanda yaso yayi imani, wanda


kuma yaki ya kafirce, mudai mun taadarwa azzalumai wuta


wadda makamashinta suka gewayeta, idan suka nemi agaji ana


agazamusu ne da wani ruwan da yake zagwanyar musu da


18


fuska, tir da abin shansu kuma makomarsu tayi muni, suratul


kahfi aya ta 29.


7- TSAKA TSAKIYAR ADDINI DA YANAYINSHI


daga ciki abubuwan da suka taimaka wajen wanzuwar


musulunci shine abinda ya kebantashi na tsaka tsakiya, da kua


daidaito da kuma saukakawa wajen fahimtarwa, da saukin


koyanshi da kuma rangwantawa wajen muamala, annabi ya


bayyanasu da cewa; mafi soyuwan addini zuwa ga allah shine


banbance qarya da gaskiya, da kuma rangwantawa. bukhari ya


ruwaitoshi.


hanyar koyarwar musulunci itace umartan kowa da kowa


abinda zai iya aikatawa, kuma shine addinin asalin halittar


mutum, wanda yake bibiyar da ita kuma yake kwaikwayonta


domin ibadojin gwargwadon yadda zai iya yinsu, da halayenta,


allah yana cewa; kuma allah bai sanya muku wani abu cikin


addini da yake na gajiyarwa ba, suratul hajji aya ta.


kuma rangwamen addinin musulunci tana bayuwa ne ta


banhgaren saukin hukunce hukuncenshi da saukin ibadojinshi


dakuma saukin da dukkan wadannan hukunce hukuncen, kuma


ya dauke duk wani laifi da tare dukkan wata wahala, domin ya


zama kowa yana da halin aikata wannan bautar, duka umarnin


allah na sharia sunzo ne a yanayin da kowa zai iya aikatasu,


kuma basu fi karfin mutum ba, tare da cewa duka umarnin da


allah yayi na bauta suna iya sauka akan mutum a lokacin


lalura, wadda itama tana da hkunce hukuncenta da ban, allah


yana cewa: duk wanda ya shiga hali na lalura ba mai


taaddanci ba ko wuce gona da iri babu laifi a tare dashi,


suratul baqara aya ta 172.


19


hakan bai kasance ba face shariar da allah ya saukar da ita ga


bayi kuma yasan su din sunada rauni, kuma abubuwan da zasu


iya yi a kididdige suke, shiyasa shariar musulunci take lura da


halin mutane da abubuwan da zasu iya aikatawa bisa ga


dabiarsu tayau da kullun kaman yadda allah yace: allah yana


son ya saukaka muku domin an halicci mutum ne mai rauni,


suratun nisai aya ta 28.


duk umarnin musulunci sun ginu ne akan wadannan qaidoji na


ubangiji da sawwakewa jamaa rayuwarsu ta ibada kaman


yadda yace: ubangiji baya dora ma wata rai abinda ba zata ita


aikatawa ba, tana da ladan aikin da tayi haka kuma tana da


laifi abinda ta aikata na zunubi, suratu baqara aya ta 286.


manzan allah tsira da amincinallah ya tabbatar da cewa: duk


abinda na haneku ku barshi, duk abinda na umarceku kuma ku


aikatashi daidai iyawarku, domin abinda ya halakar da


mutanan da suke gabaninku shine yawan tambayoyinsu da


kuma sabaninsu ga annabawansu, bukhari da muslim suka


ruwaitoshi.


rangwantawa da saukakawa na shariah hakan baya nufin a


rusa wasu daga cikin amanufofin shariah da addini to kaga


mutum ya zama yana halasta haram, shi kuma haram yana


halastashi, ko kuma wuce gona da iri wajen ayyukan shariah


ko wajen aikata umarnin allah, ko kuma rusa fahimtar shariah


akan wasu abubuwa, da ladubba na gaba daya, amman yafi


son saukakawa wadda tayi nesa akan wahalarwa ko takurawa


akan laifi da kiyayya, nana aisha allah ya kara mata yarda


tana cewa: manzan allah baa taba bashi zabin tsakanin wasu


ayyuka guda biyu ba face ya dauki mai saukinshi muddin bai


zama zunubi bane, amman inya zama laifi ne to ya fi kowa


nesa-nesa dashi, bukhari da muslim suka ruwaitoshi, abinda


ake nufi da alamura guda biyu shine alamuran duniya ko kuma


duniya da addini.


20


8- KAMMALUWA DA CIKAR ADDINI


addinin musiulunci shine cikakken addini wanda allah ya


cikashi akan saukan addininai da suka gaba ceshi kuma akan


hakan ne niimar allah ta cika da yardarshi akan bayinshi,


ainda yake cewa: yaune na cika muku addininku kuma na cika


muku niimata kuma na yardar muku da musulunci shine addini,


suratul maidah aya ta 3.


da wannan ayar ne aka goge duk wani addini da yazo gabanin


manzan allah, kuma allah baya karban wani addini daga


bayinshi face wannan din, domin duk sauran sharioin da suka


gabata sun kasance masu asali na ruhin mutum wadda suke


isar da sako zuwa gareta kuma take kira zuwa ga tsarkake ita


rai, kua suna kira ne zuwa ga abinda zai zama maslaha da


alamuran duniya da tsarata da wayar da kai sabanin shi kuma


musulunci da yazo domin ya cika duka bangarorin dan adam


na rayuwarshi, ya kunshi abubuwa na duniya da na addini


duka, manzan allah ya bayyana hakan cewa lallai musuunci


shine kadai addini agun allah kuma dashine ya aiko duka


annabwa da manzanni sashinsu yana cika sashi farawa tin


daga zamanin annabi nuhu zuwa ga manzan allah tsira da


amincin allah su tabbata a gareshi domin dashine aka rife


annabci kuma ya cika shariah, yana cewa acikin hadisi: lallai


mislai na da misalin sauran annabawa kaman misalain mutum


ne ya gida gida uma ya ingata gininshi amman sai waje daya


baa cike ba, har gidan ya burge mutane suna ta yabawa


amman suna cewa inama ace ka cike inda akwai hujin nan, sai


annabi yace: to nine cikon wannan hujin da ya rage, bukhari


da muslim suka ruwaito.


bugu da kari, bayan wannan cikar da addini yayi da


kammaluwarshi allah yayi alkawarin cika musulunci har


21


lokacin da allah zai karar da duniya da abubuwan dake cikinta


sabanin addinan da suka zo kafin musulunci allah baiyi


alkawarin kiyayesu ba, domin su sun sauka ne ga wasu mutane


daban, kuma a wani zamani daban, allah yana cewa: lallai


mune muka saukar da qurani kuma mune zamu bashi kariya,


suratul hijr aya ta 9.


9- BAYYANAR ALAMURAN ADDINI


addinin musulunci addini ne a bayyane babu rudani acikinshi


ko boye-boye hakan kuma aka siffanta qurani wanda shine


madogara ta farko wajen bayanin musulunci da cewa shi littafi


ne mabayyani kuma shiriya ne ga mutane kuma shine mai


bayyana komai acikin addini, allah yana cewa: hakika haske


da littafi bayyananne yazo muku daga wajen ubangijinku,


suratul maidah aya ta 15.


ko wani mutumi yana da haqqin tambaya abinda bai gane ba


cikin addini ko kuma abinda ke mai yawo cikin tinaninshi bai


gamsu dashi ba, domin babu abinda zai hana shi tambaya,


amman muslunci bai sa hakkin ansa tambayoyin masu tambaya


ba a hannun kowa face maabota ilimi da masaniya ta addini,


da wadanda suka karanci shariah sosai da sosai wadanda suka


bada lokacinsu wajen karantar addinin da bincike acikinshi,


domin ilimin magunguna ana nemanshi ne agun likitoci, haka


ilimin kere-kere ana nemanshi ne wajen injiniyoyi, haka ilimin


shariah ana nemanshi ne wajen cikakkun mallamai masana


ilimin addini, allah yana cewa: ba mu aiko kowa gabaninka ba


face mazaje wadanda muke musu wahayi, ku tambayi maabota


sani indai baku san abu ba, suratun nahli aya ta 43.


acikin musulunci babu wata mas’alar da ba bayyananniya


bace, kuma zamuyi imani dasu kuma bazamu yi tambaya ba


22


saidai abinda hankalin mutum bazai iya kaiwa gareshi ba na


abubuwan gaibu, wadanda allah bai bayyana mana su ba,


kuma wannan itace amfanin imani da abubuwan boye na gaibu


wanda allah ya yabi wadanda suka siffanta da ita, kuma shine


gurin da ake banbance tsakanin mumini da wanda ba mumini


ba, allah yana cewa: alif lam mim, wancan littafi babu shakku


acikinshi shiriya ne ga masu jin tsoron allah, wadanda suke


imani da abin boye wato gaibu kuma suke tsayar da sallah


sannan suna ciyarwa daga cikin abin da muka azurtasu, kuma


sune masu imani da abinda aka saukar gareka da wanda aka


saukar gabaninka kuma game da lahira su masu yaqini ne, su


wadannan suna kan shiriya ta ubangijinsu, kuma sune masu


samun babban rabo, suratul baqara aya ta 1-5.


10: CIGABAN MUSULUNCI:


shari'ar musulunci a yanayinta da 'dabi'arta mai samun nasara


ce ba mai rafkana bace akaran kanta, ba kuma mai karkata


bace ga barin abunda ke kewaye da ita na samammu (halittu),


bari dai ita dai shari'a ce bu'da'd'diya tana umurni da ya'da


kyautatawa da kuma son alkhayri ga waninka, kasancewar


musulmi akaran kansa baya isa, dole sai ya kasance mai samar


da masalaha ga waninsa, mai tasirantuwa ga al'ummar da


yake rayuwa acikinta, mai ya'da alkhayri acikin al'ummar, ya


koyar da jahili (wanda bai sani ba), kuma ya nusar da


'batacce, yana kuma mai umurni da alkhayri, yana kuma mai


hani da mummuna, yana kuma mai qira zuwa ga bautar allah


da ka'daita shi, allah ma'daukakin sarki yana cewa: kuma wata


jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alkhayri,


kuma suna umurni da alkhayri, kuma suna hani daga abunda


ake 'ki, kuma wa'dannan sune masu cin nasara." suratul aliimran


aya ta 104..


23


sai dai a shari'ar kyautatawa ga mutane da kuma son alkhayri


gare su na daga cikar ibada, saboda fa'din manzon allah


(saw): " kaso wa mutane abunda kasowa kanka zaka kasance


musulmi." tirmizi da ibn majah suka ruwaito shi, kuma albani


ya inganta shi- 930.


saboda tasirin wannan tabbatarwa da kuma 'karfafata shari'ar


musulunci ta sanya falala mai girma ga mai ya'da alkhayri,


manzon allah (saw) yana cewa: " wanda yayi 'kira zuwa ga


shiriya to ya kasance yana da lada kwatankwacin ladan


wa'danda suka bisa kuma ba za'a tauye wani abu ba daga cikin


ladansu ba, hakanan kuma duk wanda yayi 'kira zuwa ga 'bata


to za'a basa zunubi kwatankwacin zunubin wanda suka bisa


kuma ba za'a tauye wani zunubi daga zunubansu ba.


11- TABBACI DA KUMA CIGABA


lallai musulunci addini ne da yake zama maslaha ga kowane


zamani da kuma kowane muhalli, to addinin musulunci yazo da


dokoki da tushe na baki 'daya da kuma qa'idodi da tusheshina


gamammu baki 'daya tabbatattu basa musanyuwa kuma basa


chanzuwa da chanzawar zamani ko kuma muhalli a aqida da


ibadu kamar sallah da adadin raka'o'inta da kuma lokutanta da


kuma zakka da kuma gwargwadonta da kuma abunda take


wajaba acikinsa da kuma azimi da lokacinsa da kuma hajji da


siffarsa da kuma lokacinsa da kuma haddi.... abubuwanda suka


zama fararru kuma yake sabunta na daga abubuwan bu'kata a


rayuwa to an bijiro dasu ga alqur'ani mai girma da kuma


abunda ya inganta daga manzon allah (saw) idan ya samu to


yayi riqo dashi ya kuma bar waninsa, idan kuma bai samu ba


to yayi bincike da kuma duba na tsanaki ga 'ko'karin malamai


masu ilimi ako wani zamani da kuma muhalli na daga abunda


zai tabbatar da maslaha gamammiya kuma ya dace da


24


abubuwan bu'katar zamanin su da kuma halin al'ummarsu duk


wa'dannan ta hanyar duba zuwa ga alqur'ani da sunnah da


kuma bijiro da abunda yake sabuntawa abisa qa'idodi ta


shari'a wanda aka cirota daga alqur'ani da sunnah, wannan da


manufar isa zuwa ga abunda amfaninsa zai dawo ga 'dan adam


ba tare da cin karo da wani nassi na shari'a ba, don musulunci


ya zamto yana tafiya daidai da kowane zamani, kuma yana tare


da abubuwan bu'kata na kowace al'umma.


12 - CIKAR ADDINI


lallai musulunci yana amsa bu'katun 'dan adam na ruhi da jiki


da daidaito na ban mamaki kuma yana 'kin zaluncin wani


'bangare akan wani, allah ma'daukakin sarki yana cewa":kuma


ka bi'da, acikin abunda allah ya baka, gidan lahira, kuma kada


ka manta da rabonka daga duniya. kuma ka kyautata, kamar


yadda allah ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nemi


'barna acikin 'kasa, lallai ne allah ba ya son masu 'barna."


suratul qasas aya ta 77.


a mahanga ta addinin musulunci allah ya halicci ran 'dan


adam kuma ya halifantar dashi a bayan 'kasa saboda yi masa


ibada da kuma tabbatar da shari'ansa kuma ya halicci gangan


jiki ga wannan ran cikakke tsararre saboda rai yayi abunda


allah ya umurce sa da yi ta hanyar wannan jikin na daga ibada


da kuma ha'k'ko'ki da kuma jagoranci a bayan 'kasa wanda


allah ya halifantar dashi aciki, allah ma'daukakin sarki yana


cewa; kuma shine wanda ya sanya ku masu maye wa juna ga


'kasa. kuma ya 'daukaka sashenku bisa ga sashe da darajoji:


domin ya jarraba ku, acikin abunda ya baku, lalkai ne allah


mai gaggawar uquba ne kuma lallai ne shi ha'ki'ka mai gafara


ne mai jin 'kai." suratul an'am aya ta 165.


25


a musulunci babu rahbaniyyah (barin jin duniya da kuma


ka'daituwa ga barin ahlinta) da kuma daina bin komai sai


ibada da kuma yankewa ga barin duniya da kuma barin


da'da'da da kyawawa abubuwanda allah ya halitta ga bayin sa


kuma ya halattasu gare su, allah ma'adaukakin sarki yana


cewa: kace: wanene ya haramta 'kawar allah, wadda ya fitar


saboda bayinsa da masu da'di daga abinci? kace: su domin


wa'danda suka yi imani suke acikin rayuwar duniya, suna


ke'bantattu a ranar 'kiyama. kamar wannan ne muke bayyana


ayoyi daki-daki ga mutanen da suke sani." suratul aaraf aya ta


32.


abunda zamu fuskanta anan shi ba addinin fuskantar duniya


bane da kuma kwa'dayi zuwa ga sha'awowinta da kuma


jinda'dinta ba tare da dokokin kiyaye hakan ba, sai dai shi


musulunci addini ne na dai-daito da kuma tsakatsakiya wanda


ya ha'da da addini da duniya wani 'bangaren bazai yi rinjaye


akan wani ba, anyi umurni da daidaito tsakanin rai da jiki sai


aka umurci musulmi ahalin sonsa cikin al'amuran duniya da


tuna bu'katuwarsa na rai ta yin abunda allah ya wajabta masa


na daga ibada, allah ma'daukakin sarki yana cewa:


"ya ku wa'danda suka yi imani idan anyi 'kira zuwa ga sallah


daga ranar jumma'a, sai kuyi aiki zuwa ga ambaton allah kuma


ku bar ciniki, wancan dinku ne mafi alkhayri agare ku idan kun


kasance kuna sani." suratul jumu'a aya ta 9.


aka nema daga garesa acikin ha'din 'ko'karinsa da himmatuwa


cikin ibada ya ringa tuna bu'katuwarsa na jiki da rai da daga


samu da kuma neman arziki, allah ma'daukakin sarki yana


cewa ":sa'annan idan an 'kare sallah sai ku watsu cikin 'kasa


kuma ku nema daga falalar allah kuma ku ambaci sunan allah


da yawa tsammaninku ku samu babban rabo." suratul jumu'a


aya ta 10.


26


kuma musulunci yabi dukkanin wa'dannan siffofi guda biyu,


allah ma'daukakin sarki yace ":wa'dansu maza wa'danda wani


fatauci ba ya shagaltar dasu, kuma sayarwa bata shagaltar


dasu daga ambaton allah da tsaida sallah da bayar da zakkah,


suna tsoron wani yini wanda zukata suna bibbirkita acikinsa da


gannai." suratul noor aya ta 37


musulunci ya kiyaye ha'k'ko'kin rai da kuma gangar jikk daidai


da shari'ar allah babu wuce gona da iri ayin hakan, kamar


yadda aka nema daga musulmi lura da ransa da kuma yiwa ran


nasa hisabi akan ayyukan ran nasan da kuma dukkanin abunda


yake bijirowa daga ran nasa saboda yin aiki da fa'din allah


ma'daukakin sarki:


"to wanda ya aikata wani aiki gwargwadon nauyin zarra na


alkhayri zai ganshi* wanda kuma ya aikata gwargwadon


nauyin zarra na sharri zai ganshi." suratul zalzala aya ta 7-8.


hakanan an nema daga garesa kiyaye jikinsa ta hanyar


ni'imtuwa da abunda allah ya halatta na da daga da'da'dan


abincine wannan abun ko abun sha ko tufafi ne ko abun aure


da kuma da kuma kiyaye ni'imtuwa da wa'dannan da'da'da tare


da rashin 'barna wanda cutuwarsa baya 'boyuwa ga jiki, allah


ma'daukakin sarki yace:


"ya 'dan adam, ku riqi qawarku a wurin ko wani masallaci,


kuma kuci kuma ku sha kuma kada kuyi 'barna lallai ne shi


(allah) baya son masu 'barna." suratul a'araf aya ta 31.


ka lura a hane hanen musulunci daga cikinsu akwai al'amuran


da aka hana da kuma wa'danda aka haramta su a shari'a. anas


'dan malik (ra) yana fa'da cewa ":wasu mutane guda uku sunzo


gidajen matayen manzon allah (saw) suna tambaya dangane da


ibadar manzon allah (saw) yayin da aka basu labari sai suka


ga kamar tayi ka'dan, sai suka ce mu asuwa ga annabi (saw)


27


alhalin an gafarta masa zunubansa abunda ya gabata na


zunubansa da abunda zai zo nan gaba (amma yana ibada) sai


'daya daga cikinsu yace: "ni zanyi tayin sallah ko wane dare


baki 'dayansa har'abada" sai 'dayan yace: "zan tayin azumi


duka sheka bazan sha ruwa ba" sai 'dayan yace: "ni kuma zan


nisanci mata bazanyi aure ba har'abada" sai manzon allah


(saw) yazo yace: kune wa'danda kuka ce kaza da kaza ko? to


na fiku tsoron allah kuma na fiku cikakkiyar biyayya ga allah,


sai dai ni ina azumi kuma ina shan ruwa kuma ina sallar dare


kuma ina yin bacci kuma ina auren mata, duk wanda ya


'yamaci sunnata to ba ya tare dani." bukhari ya ruwaito.


13- CI GABA DA WANZUWA


tare da cewa shari'ar musulunci ita ce cikamakin shari'o'in da


allah ya sauqar daga sama kuma ta qarshensu ta yadda ta


tattara dukkanin koyarwar allah kuma wadda ta zama ma'kura


wajen zama maslaha ga kowane zamani da kumamuhalli, allah


ya wajabta ma ta wanzuwa da kuma cigaba har izuwa lokacin


da allah zai tashi 'kasa da abunda ke kants, kuma ya ji'binci


kiyayeta da kansa sa'banin sauran shari'o'in, kuma ba tare da


wani abu na chanji ya sameta ba. alqur'ani shine reference na


farko a shari'a allah ya ji'binci kiyayesa ba tare da anyi wani


'kari acikinsa ba ko kuma a tauye wani abu da yake acikinsa,


kuma shi alqur'ani mu'ujizar manzon allah ce madawwamiya


sa'banin mu'ujizozin sauran annabawa kafinsa wanda


mu'ujizarsu take 'karewa da shu'dewar zamaninsu, kuma take


kasancewa shaida akan gaskiyar manzancinsu a lokacinta sai


wanda ya ganta yayi imani da ita. amma shi alqur'ani mu'ajiza


ne da take tafiya har izuwa tashin al'kiyama, kuma shi


alqur'ani shaida ne akan gaskiyar manzon allah (saw), allah


ma'daukakin sarki yana cewa":lallai mune muka sau'kar da


28


ambato (alqur'ani) kuma lallai mu masu kiyayewa ne agare


shi." suratul hijri aya ta 9.


manzon allah (saw) kuma yana cewa ":wata jama'a daga cikin


al'ummata bazasu gushe ba ana taimakonsu akan gaskiya, guje


musu bazai cutar dasu da komai ba har tashin al'kiyama."


muslim ya ruwaito shi.


wannan shine abunda ake lura dashi na chanzawar da yawa


daga cikin ma'abota sauran addinai ga musulunci duk da rauni


na jiki da ake samu wajen gabatar da shi da kuma taimako na


jikin 'dan adam da ake samu wanda bashi da iyaka domin


ya'karshi da toshe duk wata hanyar ru'dani daga ma'kiyansa


hakanan ka'dan suke fita daga cikinsa bayan rungumarsa


14- GAMEWA


addinin musulunci a 'dabi'arsa ya game dukkanin 'bangarori


na rayuwa sai yazo da tsaruka da kuma shari'o'i wadda take


daidaita al'umma bata bar wani 'bangare daga cikin


'bangarorin rayuwar 'dan adam da dukkan 'bangarorin ta na


raine 'bamgarorin ko na gangar jiki, na addini ne ko na duniya


ne, na 'dai'dai kun mutane ne ko na jama'a da yawa ne face ta


tsara masa hanya mafificiya. allah ma'daukakin sarki yana


cewa:


"kuma mun sau'kar da littafi akanka domin yin bayani ga


dukkan komai na shiriya da rahama da bushara ga masu mi'ka


wuya (musulmai)." suratul nahl aya ta 89.


sai musulunci ya tsara ala'kar musulmi tare da ubangijinsa da


kuma al'ummarsa da kuma halittun da suke kewaye dashi, daga


cikin abubuwan da suke nuni abisa wannan 'dabi'ar shine


damuwarsa da kulawarsa ga 'kananan am'dabi'u wa'danda


29


suke da alaqa da rayuwar 'dan adam, manzon allah (saw)


yace: ankar'bo daga abu-hurairah (ra) yace: "manzon allah


(saw) yace: "imani yanki saba'in da 'doriya ne ko kuma yanki


sittin da 'doriya ne mafificiyarta. (a wata ruwayar kuma


ma'daukakiyarta) itace fa'din la'ilaha illallahu (babu wani sai


allah), mafi 'kas'kantarta kuma shine 'dauke abun cutarwa


daga hanya, kunya wani yanki ne daga imani." bukhari da


muslim ne suka ruwaito amma wannan lafazin na muslim ne.


)bidi'un) abunda ke tsakanin biyu zuwa goma. (shu'abatun)


'dabi'a. (ima'datul-aza) gusar da wani abu na cutarwa.


sai aka wayi gari aka gina wa'dannan 'dabi'u ma'abociyar


banbanci daga cikinsu:


★ Karrama 'dan adam ta yadda allah ya fifita shi akan


dukkanin halittu a wannan duniya kuma ya hore shi. allah


ma'daukakin sarki yace: "kuma lallai ne mun girmama 'dan


adam kuma muka 'dauke su acikin 'kasa da teku kuma muka


azurtasu daga abubuwa masu da'di kuma muka fifita su akan


masu yawa daga wa'danda muka halitta, fifitawa." suratul


isra'i aya ta 70.


★ Sanayyar juna sai aka kwa'daitar da samar da ala'ko'ki


masu kyau tare da al'ummar musulmi da kuma al'umman da


suke kewaye dashi na kyakykyawar ma'kotaka da kyautatawa


da son alkhayri da musayar abunda zai zama maslaha. allah


ma'daukakin sarki yace: "ya ku mutane lallai ne mu mun


halittaku daga namiji da mace kuma muka sanya ku dangogi da


'kabiloli domin ku san juna, lallai mafificinku daraja awurin


allah (shine) wanda ya fiku taqawa (tsoron allah) lallai allah


masani ne mai 'kididdigewa." suratul hujurat aya ta 13.


★ Tabbatar da 'daukan nauyi na zaman tare ta yanda aka


wajabta akan musulmi lura da kulawa ga halin 'yan uwansa


30


abisa dukkanin wani mataki. manzon allah (saw) yana cewa:


zaka ga mumini acikin jin'kan junansu da son junansu da


taimakon junansu kamar jiki ne guda 'daya idan wata ga'ba ta


kai 'kara na wuta cuta sai ya kaiwa dukkanin jiki da rashin yin


bacci da kuma zazza'bi." muttafaqun alaihi.


)tarhamuhum) jin'kan sashensu ga sashe.(tawaduhum) son


junansu ga junsnsu. (ta'adifuhum) taimakon junansu.


(aljasadu) jiki guda 'daya ta hanyar duba ga dukkanin


ga'b'bansa. (ishtaka udwan) saboda wata cuta da ta same sa


shi jikin. (tada'a) tayi tarayya dashi cikin abunda yake cikinsa.


(as-saharu) rashin yin bacci saboda ra'da'di.


' ★ yanci wanda yake abun lura da dokokin addini ya


banbanta da 'yanci na dabbanci wanda bai da wani tsari na


lura da kulawa. saboda haka gini akan wannan 'yanci zai bawa


kowa dama kamar haka:


1-'yancin yin tunani da bayyana ra'ayi tare da lura cikin hakan.


allah ma'daukakin sarki yana cewa": ya ku wa'danda kuka yi


imani kubi allah da taqawa kuma ku fa'di magana


madaidaiciya." suratul ahzab aya ta 70.


2-'yancin mallakar wani abu da kuma samun halal, allah


ma'daukakin sarki yana cewa:


"kuma kada kuyi gorin abunda allah ya fifita sashenku dashi


akan sashe, maza suna da rabo daga abunda tsirfanta, kuma


mata suna da rabo daga abunda suka tsirfanta." suratul nisa'i


aya ta 32.


3-'yancin ilimi da koyo, manzon allah (saw) yana cewa:


"neman ilimi wajibi ne akan kowane musulmi." sahihu ibn


majah.


31


4-'yancin amfanuwa da abunda allah ya sanya a wannan


duniya na alkhayrai, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "shi


(allah) ya sanya muku 'kasa horarriya sai ku tafi cikin


sasanninta, kuma zuwa gare shi ne tashi yake." suratul mulk


aya ta 15.


★ Tabbatar da aminci gamamme wanda ya halatta ga


abubuwa masu zuwa:


→aminci akan addini ta hanyar rashin yin shirka da allah da


kuma zuwa ibadarsa, allah ma'daukakin sarki yana


cewa":kuma ku ya'ki wa'danda suke ya'kanku acikin hanyar


allah kuma kada kuyi tsokana lallai ne allah baya son masu


tsokana." suratul baqara aya ta 190.


→aminci akan ran 'dan adam, allah ma'daukakin sarki yana


cewa: kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci to


sakamakonsa jahannama yana madawwami acikinta kuma


allah yayi fushi akansa kuma la'ance shi kuma yayi masa


tattalin azaba mai girma." suratul nisa'i aya ta 93.


→aminci akan dukiya, allah ma'daukakin sarki yana cewa:


kada kuci dukiyoyinku a tsakaninku da 'karya kuma ku sadu da


ita zuwa ga mahukunta domin kunci wani yanki daga dukiyoyin


mutane da zunubi, alhali kuwa ku kuna sani." suratul baqara


aya ta 188.


→aminci abisa mutunci, allah ma'daukakin sarki yana cewa: "


kuma kada ku kusanci zina lallai ne ita ta kasance alfasha ce


kuma ta munanana ga zama hanya." suratul isra'i aya ta 32.


→aminci ga hankali ga barin sha'awace-sha'wace kamar giya


da kayan shaye-shaye. allah ma'daukakin sarki yana cewa: "ya


ku wa'danda kuka yi imani, abun sani kawai giya da caca rufe


32


da kiban 'kuri'a 'kazanta ne daga aikin shai'dan sai ku nisance


shi wa la'alla kuci nasara." suratul ma'idah aya ta 90.


★ Ji'bintar haqqoqii ta yadda musulunci ya wajabta haqqoqi


tsakanin halittu abisa sassa'bawar matsayinsu/ matakansu


domin ha'din kai ya tattaru gare su kuma amfanikan addini su


tabbata gare su kuma al'amuransu na addini si daidaita to


wannan ya kasu kashi biyu:


(a) HAQQOQI KE'BANTATTU,


Allah ma'daukakin sarki yana cewa: "kuma ku bautawa allah


kuma kada ku ha'da wani dashi, kuma ga mahaifa kuyi


kyautatawa, kuma ga ma'abocin zumunta da marayu da


matalauta da maqobci macabocin kusanta da maqobci


manianci d aboki. gefe da 'dan hanya d abunda hannayenku na


dama suka mallaka lallai ne allah baya son wanda ya kasance


mai taqama mai yawan alfahari." suratul nisa'i aya ta 36.


(b) HAQQOQI GAMAMMU,:


Manzon allah (saw) yace: "kada kuyi hassada kada kuyi


tanajushi kada kuyi 'kiyayya kada ku juya baya kada sashinku


yayi ciniki akan cinikin sashenku, ku kasance bayin allah 'yan


uwa, musulmi 'dan uwan musulmi ne kada ya zalunce sa kada


ya wulaqanta shi kada ya qasqantar dashi tsoron allah yana


nan (sai ya nuna qirjinsa sau uku) ya ishi mutum sharri ya


qasqantar da 'dan uwansa musulmi, dukkanin musulmi


haramun ne ya fitar da jinin 'dan uwansa da kuma dukiyarsa


da kuma mutuncinsa." muslim ne ya ruwaito.


(tanajushi) shine mutum ya yabi hajarsa don ya siyar da ita ko


kuma yayi 'kari acikin 'kimarta kuma baya son sayar da ita.


★ Rahama ta yadda ta tattara halittu daga cikinta:


33


→jin'kai ga 'dan adam, manzon allah (saw) yana cewa: "masu


jin'kan mutane allah yana jin'kansu ku ji'kan wanda suke 'kasa


daku wanda suke sama zasu ji'kanku, zumunta wanda ya sadar


da ita allah zai sadar dashi wanda kuma ya yanketa allah zai


yankesa." ahmad da abu-dauda da hakim ne suka rawaito


albani kuma ya inganta shi.


→rahama jin'kai ga dabbobi, ta yadda jin'kai gare su ya zama


sababi na gafarta zunubai da shiga aljannah, manzon allah


(saw) yace: "lokacin da wani mutumin yakai makurar jin kishi


sai ya shiga wata rijiya,sai yasha ruwan har ya koshi, yana


fitowa sai yaga wani kare yana zaro harshenshi ta kai har yana


cin qasa saboda tsananin jin kishi, sai mutumin yace a ranshi:


lallai wannan karen yakai inda na kai sanda nake jin kishi, sai


ya kara shiga rijiyar ya ciko takalminshi da ruwa, sai ya ba


karen yasha kuma ya gode ma allah, sai ubangiji ya gafarta


mai, sai sahabbai suka ce ya manzan allah har acikin dabbobi


ma muna iya samun lada ?? sai annabi yace: acikin duk wata


halitta mai hanta akwai aikin lada." bukhari da muslim suka


ruwaito shi.


(yalhas) yana nishi da 'kyar ko yana fito da harshensa saboda


tsananin qishin ruwa. (assara) ji'ka'k'kiyar 'kasa ko kuma


gwaguyar 'kasa. (wa ina lana fil bahaimu ajran) shin an samu


lada a shayar da dabbobi da kuma kyautata musu. (fi kulli


kabidin) acikin kyaitatawa ga duk wanda yake cikin qunci.


(radbatun) a mayar da wani abu 'danye bayan ya bushe.


★ yin shawara ta yadda ya umurci mabiyansa ya ri'ke hakan


tsari gare su acikin dukkanin al'amuran addini dana duniya na


ciki da na waje, allah ma'daukakin sarki yana cewa :saboda


wata rahama ce daga allah kayi sanyin hali agare su kuma da


ka kasance mai fushi mai kaurin zuciya da sun watse daga


gefenka, sai kayi yafevmusu laifinsu kuma ka nema musu


34


gafara kuma kayi shawara dasu acikin al'amarin, sannan kuma


idan kayi niyyar zartarwa toh ka dogara ga allah lallai ne


allah yana son masu tawakkali." suratul ali-imran aya ta 159.


★ daidaito tsakanin mutane baki 'daya a tsakanin halittarsi


mazansu da matansu farinsu da ba'kinsu larabawansu da


wa'danda ba larabawa ba, babu banbanci a tsakaninsu sai dai


wanda yafi wani taqawa. allah ma'daukakin sarki yana cewa:


"ya ku mutane, kubi ubangijinku da taqawa wanda ya halicce


ku daga rai guda kuma ya halitta daga gare shi, ma'auransa


kuma ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata, kuma


kubi allah da taqawa wanda kuke roqon juna da sunan shi da


kuma zumunta, lallai ne allah ya kasance akanku mai tsaro


ne." suratul nisa'i aya ta 1.


★ gamammen adalci ga rai da kuma mutane, allah


ma'daukakin sarki yana cewa ":lallai allah na yin umurni da


adalci da kyautatawa da baiwa ma'abocin zumunta kuma yana


hani ga alfasha da abunda aka 'ki da rarrabe jama'a yana yi


muku garga'di tsammaninku kuna tunawa." suratul nahli aya ta


90.


★ yin aminci gamamme akan matakin ciki da na waje, manzon


allah (saw) yana cewa ":shin bana baku labarin mumini ba


shine wanda mutane suka aminta dashi akan dukiyarsu da


rayukansu, musulmi shine wanda mutane suka ku'buta daga


harshensa da kuma hannunsaai jihadi kuma shine wanda yaqi


ransa wajen yiwa allah biyayya, mai hijira kuma shine wanda


ya 'kauracewa zinubai da sa'bo." sahihi ne hadisin ibn majah


ya fitar dashi da ibn hibban (assahiha 549).


★ kwa'daitarwa da yin aiki da kuma samun da'da'da, manzon


allah (saw) yana cewa' ":dayanku ya 'dauki igiyarsa yaje yayi


kirare ya sayar dasu, allah ya karesa ta dalilin wa'dannan


35


kiraren kada mutuncin fuskarsa ya gushe kuma ya qasqantar


da kansa da tambayar mutane, hakan yafi alkhayri gare shi


akan ya tambayi mutane su bashi ko su hanashi." bukhari ne ya


ruwaito.


)fa kayya fallahu biha wajhahu) mutane su hanasa kuma allah


ya karesa ta dalilin yin tambaya.


★ yin tsafta koyarwar musulunci tana kwa'daitarwa da yinta


kuma tana umurni da ita ta hanyar wasu halaye daga cikinsu:


→tsaftace baki bayan cin abinci da kuma lura da tsaftar


haqora ta hanyar kwa'daitarwa da yin aswaki, saboda fa'din


manzon allah (saw): "ba don kada na tsanantawa al'ummata


ba, da na umurce su da yin aswaki yayin ko wace sallah."


musulm ne ya ruwaito.


→gusarwa da tsaftace abunda sha'aninsa ne ya kasance


matsaya da mstabbata na 'kwayoyin cuta da kuma dukkanin


dau'duka, manzon allah (saw) yana cewa":sunnoni biyar: yin


kaciya, da aske gashin gaba, da cire gashin hammata da rage


gashin baki da yanke farce." muttafaqun alaihi.


)al-istihidadu) aske gashin gaba, shine gashin da ke kewaye da


farjin namiji ko mace. (al-ibdu) hamnata. (taqleem) an samo


kalmar ne daga qallama shine yankewa ko ragewa.


→tsaftace abunda ke fita daga mafita guda biyu (fitsari da


bayan gida) salman (ra) yana cewa":manzon allah (saw) ya


hanemu mu fuskanci alqibla domin yin fitsari ko bayan gari, ko


kuma muyi tsarki da hannun dama ko kuma muyi tsarki da


dutse 'kasa da guda uku, ko kuma muyi tsarki da kashin


dabbobi ko 'kashi." muslim ya ruwaito shi.



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA