GABATARWAR MASU FASSARA
Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da aminci su daxa tabbata akan
shugaban talikai.
Faxakarwa dangane da iyakoki da dokokin Ubangiji Mahalicci na
daga cikin abin da musulmi ke da buqatarsa a ko wane lokaci, to, balle
kuma a wannan zamani namu da yake cike da abubuwan xaukar hankali
masu kawar da mutum daga godaben Shari’a.
To, sai dai ba kowa ne yake amfanuwa da wannan faxakarwar ba
sai wanda imani ya ratsa birnin zuciyarsa. Kamar yadda Allah ya ce;
Ma’ana:
“Ka faxakar domin, faxakarwa tana amfanin Muminai”.
Suratuz Dhariayt: 55
Wannan littafi na Sheikh Muhammad Saleh Al Munajjid yana da
matuqar muhimmanci ta wannan fuskar. Shi ya sa muka ga dacewar
mayar da shi zuwa harshen Hausa.
Roqon da muke ga Allah maxaukakin Sarki yasa mu cikin farko
waxanda ke aiki da wannan faxakarwa. Ya bamu ladar wannan aikin, ya
sanya shi cikin sikelin ayyukan alherinmu. Ya yafe mana duk wani
kuskure ko tuntuven harshe ko varin baki idan auku a cikin aikinmu.
Masu Fassara:
Muhammad Mansur Ibrahim
Da Aliyu Rufa’i Gusau
5
GABATARWAR MAWALLAFI
Godiya ta tabbata ga Allah, Abin yabo, Abin nufi da buqata.
Wanda muke neman gafararsa, muke kuma fatar Ya yi mana katangar
dutse, a tsakanin mu da sharrin zukatanmu da miyagun ayyukanmu.
Tabbas! Duk wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi. Babu kuma
mai iya shiryar da wanda Allah bai nufa da shiriya ba. Na Shaida, ba abin
bauta wa da gaskiya Sai Allah, Shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Ina
kuma shedar da cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa.
Bayan haka:
Tabbataccen abu ne cewa, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya
wajabta wasu abubuwa a kan mu, waxanda yin biris da su ba ya halasta.
Ya kuma haramta mana wasu abubuwan, waxanda su ma, yi masu kallon
hadarin kaji ba daidai ne ba. Allah a cikin ikonsa ya shimfixa mana wasu
dokoki ya shata wasu iyakoki da ba ya son a tsallake su.
A qoqarin fitowa da matsayin waxannan abubuwa biyu ne da
kuma abin da ke tsakanin su, Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce:
“Duk abin da Allah Ya halasta a cikin littafinsa shi ne halas.
Babu kuma wani abu da ke haram, sai abin da Ya haramta. Duk kuma
abin da bai ce komai a kansa ba to garavasa ne. Ku karvi wannan
rangwame na Allah da hannu biyu biyu. Don har abada Allah ba Ya
mantuwa”. Daga nan kuma, sai ya karanta wannan aya:
Ma’ana:
Kuma Ubangijinka bai kasance mai yin mantuwa ba
(19:64).
6
Da wannan bayani na Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ne, ta bayyana cewa, duk abubuwan da Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya yi wa bayinsa iyaka da su, su ne haram. Kuma yin biris da su
zaluntar kai ne. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:
:l edcba` m
Ma’ana:
Kuma wanda ya qetare iyakokin Allah to lalle ya zalunci
kansa (65:1).
Bayan wannan kuma sai Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi
tanadin wuta ga duk wanda ya qetare waxannan iyakoki da Ya shata. Ya
ce:
ÆÅÄÃÂÁÀ¿¾½m
: l
Ma’ana:
Kuma wanda ya sava wa Allah da manzonsa, ya kuma
qetara iyakokinsa, zai shigar da shi wuta, yana
madawwami a cikin ta, yana kuma da wata azaba mai
walaqantarwa (4:14).
Saboda irin qaunar da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke yi wa
bayinsa kuma, sai ya wajabta masu nisantar waxannan abubuwa ta
hanyar haramta masu su. Don kada su faxa cikin wannan azaba. A kan
haka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Ya ce:
“Duk abin da na hane ku da shi, ku nisance shi. Abin da kuma
duk na umurce ku da shi, ku aikata shi gwargwadon ikonku”. (Muslim:
130) .
7
Amma tattare da wannan irin gatanci, sai ka taras da waxanda
suka saba da biyar soye-soyen zukatansu, saboda raunin imani da
qarancin ilmi da suke da su, suna qorafe-qorafe. Da zarar an ce masu abu
kaza da kaza haramun ne a musulunci, sai su fara gunguni suna cewa:
“Kome dai haramun! Haramun!! Haramun!!! Wai wane irin addini ne
wannan da kullum yake qoqarin gasa mana aya a hannu? Kai kun dai ishe
mu. Ku ba ku da wata magana sai ta haram! Ai kamata ya yi addinin
musulunci ya zama kadaura babbar inwa, mayalwanciya, wurin hutawa,
ba aljannar masa ba. Kuma shin ko kun manta da cewa Allah Mai rahama
ne, kuma Mai jinqai?”
Irin waxannan mutane yana da kyau su sani cewa, Allah
Subhanahu Wa Ta’ala Sarki ne mai cikakken iko. Wanda ke gudanar da
mulkinsa yadda Ya so, kuma babu wanda ya isa ya tayar da wani hukunci
da Ya yi. Domin Ilminsa da hikimarsa sun kai matuqa. Yana halasta abin
da Ya ga damar halastawa, Ya kuma haramta abin da Ya ga dama. Kuma
mu, yana xaya daga cikin abubuwan da ke tabbatar da kasancewarmu
bayinsa na gari, mu yarda da duk wata doka da zai shata muna; mu miqa
wuya gare ta. Domin babu wata doka da zai yi face tana tsattsage da ilimi
da hikima da adalcinsa. Ba abu ne na sakarci da sharholiya ba. Kamar
yadda Allah Yake cewa:
Ma’ana:
Kuma kalmar Ubangijinka ta cika, tana mai gaskiya da
adalci. Babu mai musanyawa ga kalmominsa, kuma shi,
Mai ji ne, Masani (6:115).
8
Wani abun kuma shi ne: Allah Subhanahu Wa Ta’ala a cikin
wannan ilimi da hikima nasa, bai tsaya kawai ga halasta mana wasu
abubuwa da haramta mana wasu ba. Sai da ya bayyana mana qa’idar da
Yake bi a cikin yin haka. Dubi inda Yake cewa:
Ma’ana:
Kuma Yana halatta masu abubuwa masu tsarki
(waxanda suka shafi, Aqida da ibada da Mu’amala da
Ababen ci, da saurasu). Yana kuma haramta masu
qazantattun abubuwa. (7:157).
Ashe kenan Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya halatta mana wasu
abubuwa ne saboda kasancewarsu masu tsarki. Ya kuma haramta mana
wasu ne, saboda qazantar da suke da ita. Kuma irin wannan iko, na ware
wani abu a ce halas ne, ko a ware wani a ce haram ne, Allah Subhanahu
Wa Ta’ala ne kawai ke da shi. Kuma ko shakka babu, duk wanda ya naxa
wa kansa irin wannan rawani, ko ya naxa wa wani, ya tabbata kafiri.
Kafirci kuwa, laifi ne da babu kamar sa. Kamar yadda Allah Subhanahu
Wa Ta’ala ke cewa.
Ma’ana:
Ko suna da waxansu abokan tarayya (da Allah) waxanda
ke shar’anta masu, abin da Allah bai yi izini da shi ba
game da addini? (42:21).
Ba wannan kawai ba. Babu ma wanda Shari’a ta yarda ya tsoma
baki, a cikin yin sharhi a kan kasancewar wani abu halas ne ko haram,
9
face mutumin da ya naqalci asirin Alqura’ani da Sunnah. Saboda nauyin
wannan al’amari ne ma, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi kashedi da
kakkausar murya, a kan masu wanke baki su tsoma, a zancen halas da
haram, alhali iliminsu bai taka kara ya karya ba. Saurari wannan aya
kuma ka kalle ta da idon basira:
Ma’ana:
Kuma kada ku ce, wannan halas ne, wannan haram ne
akan abin da harsunanku suke siffantawa na qarya.
Domin ku qirqira qarya ga Allah. Lalle waxanda ke
qirqira qarya ga Allah ba su rabauta. (16:116).
Kuma Saboda girman wannan mas’ala ne, da kariya ga
alfarmarta, tare da tsare mutuncin musulmi, Allah Subhanahu Wa Ta’ala
Ya qididdige abubuwan da aka daddale haramcin su cikin Alqur’ani,
Sunnah kuma ta tunfaye su. Ga abin da Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:
Ma’ana:
Ka ce “ku zo in karanta abubuwan da Ubangijinku Ya
haramta a kan ku: (Wajibi ne) kada ku yi Shirkan kome
10
da shi, kuma ku kyautata wa mahaifa, kuma kada ku
kashe xiyanku saboda talauci, Mu ne muke arzuta ku, da
su, kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha; abin da ya
bayyana daga gare ta da abin da ya voyu, kada ku kashe
rai wadda Allah Ya haramta, face da haqqi. Wannan ne
(Allah) Ya yi muku wasiyya da shi, ko da zaku hankalta
(6:151).
Bayan wannan kuma, Sunnah ta zo da qididdigar wasu
haramtaccin abubuwa masu yawa. Kamar inda manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ke cewa: Haqiqa Allah Ya haramta cinikin giya, da
mushe da naman alade da kuma gumaka (Abu Dawud: 3:486).
Ya kuma ce: Duk abin da Allah Ya haramta, to kuxinsa haramun ne
(Daraquxni: 3/7).
Bayan duk wannan kuma, akwai waxansu ayoyi da suka ambaci
wasu haramtattun abubuwa, a matsayinsu na qungiya; ‘yan uwa xaya uba
xaya. Kamar inda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta wasu nau’uka
na abinci. Ya ce:
Ma’ana:
An haramta maku mushe da jini da naman alade da abin da
aka ambaci sunan wanin Allah a gare shi (wurin yanka
shi), da maqararriyar (dabba) da jefaffiya da wacce ta
gangaro da sokakkiya da abin da masu dagi suka ci, - face
11
abin da kuka yanka - da abin da aka yanka don gumaka
(shi ma haramun ne). Kuma kada ku yi rabo da kibau na
caca. Wancan fasiqanci ne.. (5:3).
Haka kuma a wata ayar, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ambaci
qungiyar wasu mata, da aka haramta wa musulmi aurensu. Inda Ya ce:
Ma’ana:
An haramta maku (auren) uwayen ku (mata) da ‘ya’yanku,
da ‘yan uwanku, da goggonninku, da innoninku, da
‘ya’yan xan uwa, da ‘ya’yan ‘yar uwa, da uwayenku
waxanda suka shayar da ku mama, da ‘yan uwanku mata
na shan mama, da uwayen matanku, da agololinku
waxanda suke cikin xakunanku, daga matanku waxanda
kuka yi baiko da su. Idan har baku riga kuka yi baiko da su
12
ba to, ba laifi akan ku (ko auri ‘ya’yan nasu). Da matan
‘ya’yanku na tsatsonku (su ma basu halatta gare ku), da
kuma ku haxa ‘yan uwa mata biyu (a lokaci xaya), sai dai
abinda ya gabata (wannan Allah Ya yafe shi). Da matan da
suke da igiyar aure (basu halatta ku aure su a wannan
lokaci) sai fa in damanku ta mallake su (kuka kamo su a
wurin jihadi da kafirai). Wannan hukuncin Allah ne gare
ku. Kuma an halatta maku duk abinda ke bayan waxannan
(da aka lisafta) ku neme (su) da dukiyoyinku kuna masu
tsari da aure, ba masu zina ba. (4:23-24).
Haka nan kuma a wata ayar Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya
ambaci irin nau’in cinikin da yake haramta ga musulmi. Ya ce:
Ma’ana:
Kuma Allah Ya halatta lafiyayyen ciniki. Ya kuma
haramta Riba (2:275).
Wannan kenan. Amma kuma wani abin farin ciki, da ya kamata
kowane musulmi ya yi godiya ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala akai shi
ne, kasancewar Buwayayyen Sarkin, Saboda tsananin rahamar da Yake
da ita ga bayinsa, Ya halasta masu wasu abubuwa masu xinbin yawa, da
yawun alqalami ba zasu iya qididigewa ba.
Saboda haka ne ma, maxaukakin Sarkin bai yi bayaninsu dalladalla
ba. Amma Ya yi bayanin haramtattun abubuwa saboda zaman su
‘yan kaxan. Domin kuma su zama rubuce raxam a kan allon zukatanmu,
har mu yi nesa- nesa da su koda yaushe. Ga abin da Yake cewa:
13
Ma’ana:
Kuma haqiqa (Allah) Ya rarrabe maku daki-daki, abin da
Ya haramta a kan ku, sai fa abin da aka buqatar da ku
zuwa gare shi bisa lalura (6:119).
Amma a taqaice, duk abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya
halasta, to Ya yarda wa musulmi shi. Matuqar dai abu ne mai tsarki da
nagarta a dai-dai lokacin. A kan sifofin waxannan abubuwa ne Yake
cewa:
Ma’ana:
Ya ku mutane! Ku ci daga abin da yake a cikin qasa, yana
a matsayin halas, mai tsarki (2:168).
Kuma ko shakka babu, yanke hukuncin da Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya yi na kasancewar komai halas a taqaice, matuqar ba a sami
wani dalili da ke haramta shi ba. Yin haka wata rahama ce da jinqayi Ya
yi wa bayinsa. Kuma wajibi ne mu miqa wuya ga haka, mu kuma gode
masa.
Haka kuma yin bayanin haramtattun abubuwa da Allah
Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi dalla-dalla, shi ma wata rahama ce, da wani
jinqayi. Don hakan na matuqar taimaka wa musulmi ga zama faxake, a
kan dokokin shari’a. Musamman irin waxanda imaninsu da kaifin
basirarsu ba su shige cikin cokali ba, a fagen addini musulunci.
Ba wannan kawai ba. Irin waxannan mutane, nada alamar buqatar
a danqa masu jadawalin duk abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala
14
Ya halasta dalla-dalla, kafin su gamsu da cewa addinin musulunci ba
kurkuku ne ba.
Wato suna so ne aya ta sauka, tana cewa: Naman Raquma da na
shanu da Tumaki da zomaye da Gada da Awaki da kaji da Xanragguwa
da Agwagwar Ruwa da Zabbi, duk, halas ne, in an yanka su da sunan
Allah. Haka kuma naman kaji da fari duk halas ne. Wata kuma ta ce:
Ababen marmari da Furanni da Ganyaye, da duk wasu ire iren masu
ciyawa halas ne. Kuma Ruwa da Madara da Zuma da Mayuka, duk halas
ne. Wata kuma ta ce: “Gishiri da Yaji da Maggi da Kori” halas ne.
Sannan kuma a samu wani nassin na aya ko hadisi da zai ce:
Amfani da katako da qarfe, ko Yashi da Duwatsu da Robobi da Gilasai
da Qarau, su ma halas ne. Wani nassin kuma misali ya ce: Amfani da
ababen hawa don yin tafiye tafiye cikin su har da Motoci da Jiragen qasa
da na sama da jiragen Ruwa, su ma sun halasta.
Wannan na dasa aya kuma sai wani Nassin ya xauka: Amfani da
Na’urorin sanyaya xaki da firijin, da Injinonin wanki da masu bushe
kaya, da injinonin niqe Hatsi su koma Gari, da Na kwava fulawa, da Na
niqe nama ko Ababen marmari, da Na’urorin binciken lafiyar mutum, da
na qere qere, da Na Lissafi, da Na Hangen Nesa, da Na Tatso Ruwa da
Mayuka da ma’adanai daga qasa da Na Tace Ruwa, da Na Xab’i da Masu
qwaqwalwa, da Makamantansu. Duk amfani da waxannan abubuwa halas
ne.
Wani Nassin kuma ya ce: Sanya Suturar da aka saqa da auduga
ko ulu ko kittani ko roba ko gashin Raqumi ko fata, halas ne.
Haka kuma suna da buqatar wani Nassin ya gaya masu a fayyace,
cewa Aure, Saye da Sayarwa, Xaukar Nauyin Wani, Yajejeniyar
15
Cinikayya a Rubuce, rubuta Risit, Haya, Sana’oin Hannu kamar Saqa,
qira, Jima, kanikanci da kiwo duk su ma halas ne,
Kai!!! Ko shakka babu idan aka ce haka za a bi duk abubuwan da
ke halas tiryan- tiryan ana lissafi sai wani zamani ya qare ba a ci rabi ba.
Ma’ana:
Me ke faruwa ga waxannan mutane da ko kusa ga fahimtar
magana ba su yi ba (sai in an yi ta dalla- dalla)? (4:78).
Wannan kenan. Mu koma ga cewar da suke ta yi, musulunci
addini ne mai sauqi da rangwame. Wannan magana ko shakka babu
gaskiya ce. Amma kuma a kaikaice mun fahimci suna son karkata akalar
maganar ne a matsayinta na gaskiya, su xaure wa qarya gindi da ita.
Domin su, a tunaninsu musulunci ba zai karva sunan addini mai
sauqi ba, sai ya tafi daidai da soye-soyen zukatansu. Alhali kuwa a
haqiqa, sauqin da addini ke da shi na samuwa ne ga mutum a lokacin da
ya bi abin duk da shari’a ta zo da shi sau da qafa. Akwai banbanci
matuqa tsakanin sauqin da ke cikin addinin musulunci, da irin wanda
waxannan mutane ke qoqarin tabbatarwa a cikinsa. Su a wurin su aikata
miyagun xabi’u da halaye, a lave bayan wasu hujjoji na qarya shi ne
sauqi. Ko alama. Ba haka abin yake ba. Sauqin da musulunci ya zo da
shi, ya shafi xaga wa musulmi qafa ne a cikin waxansu abubuwa na halas
don gudun su niqe shi. Kamar damar da aka ba shi ta haxa wata sallah da
wata, ko taqaita wata, ko ajiye azumi a cikin halin tafiya, ko shafa a kan
safa, na tsawon kwana xaya da yini ga mazaunin gida, da tsawon kwana
uku da wuninsu ga matafiyi, ko wanda ke fargaban tava ruwa a kan wata
lalura ya yi taimama, ko halatta kallon maccen da ba muharrama ba ga
16
mai neman ta aure, ko zaven xaya daga cikin: ‘Yantar da Bawa ko Ciyar
da Miskini ko Tufatar da shi ga wanda ya karya wani alwashi a matsayin
kaffara, ko cin naman mushe idan wuri ya qure, da dai sauran rangwamerangwamen
da shari’a ta zo da su masu kama da waxannan.
Babban abin da ya kamata kowane musulmi, har da irin
waxannan mutane, ya fahimta shi ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya
shata wasu iyakoki da dokoki ne, ta hanyar haramta waxansu abubuwa a
musulunci don Ya jaraba bayinsa. Kuma cin wannan jarrabawa ne, zai
banbanta su da ‘yan wuta waxanda suka qare rayuwarsu cikin biyar
qyaleqyalin duniya da son zuciya. Abubuwan da, da su ne Allah
Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wa gidan wuta qawanya. Ya kuma yi wa
gidan aljanna zoba da abubuwa masu nauyi da sosa zuciya waxanda
haquri da su ke sa a samu isa tudun mun tsira. Ka ga kenan ta wannan
hanya ce kawai Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai ware bayinsa masu
biyayya daga kangararru, ba don bai san su ba.
Sanin haka ne ya sa masu ingantaccen imani ke kallon irin
waxannan jarabawoyi a matsayin wata hanya ta samun lada da yardar
Allah. A haka sai ka taras saboda jin daxi, har tuman gada suke yi idan
suna wata xa’a ga Allah, komai nauyinta. A yayin da su kuma munafukai
ke kallon jarabawoyin a matsayin wata takurawa da musgunawa. A
sakamakon haka sai al’amarin ya niqace su, su kasa cin jarrabawar bale
su sami ladarta da yardar Allah.
Ka ga kenan, wannan bayani da ya gabata na tabbatar mana da
cewa, duk wanda ya yi xa’a ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala ta hanyar
nisantar abubuwan da ya haramta, saboda shi kawai, to Allah zai maye
masa gurbinsu da abin da ya fi wancan da ya nisanta zama Alheri. Bayan
daular zaqin da zata cika zuciyarsa.
17
Don in faxakar da musulmi a kan wasu abubuwa da Allah
Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta kuma Alqur’ani da Sunna suka
tabbatar amma mutane suka yi biris da su, na rubuta wannan taqaitaccen
littafi, ta hanyar fitowa da matsayin shari’a a kan abubuwan. Musamman
saboda kasancewar ‘yan uwa musulmi na aikata da yawa daga cikin su.
A qarshe, ina roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi mana
jagora, mazanmu da mata. Ya kuma taimake mu a kan aikata abin da Ya
umurce mu da aikatawa tare da nisantar abin da ya haramta. Ya kuma
shiga tsakanin mu da miyagun ayyukanmu. Tabbas Allah shi ne mafi
taimakon masu taimako ga shiriya. Shi ne kuma mafi jinqayin masu
jinqayi.
18
BABI NA XAYA
SHIRKA
Shirka ita ce abu mafi girma daga cikin abubuwan da Allah
Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta. Kuma haxarin da ke cikinta ya shafe
na saura. Kamar yadda Abubakar Raliyallahu Anhu ya riwaito a wani
hadisi cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa
Sahabbai wata rana: “kuna so in ba ku labarin zunubin da ba wanda da ya
kai shi girma? Muka ce, qwarai muna so ya Manzon Allah! Sai ya ce, shi
ne haxa Allah da wani abu a cikin bauta. (Bukhari: 2511).
Saboda girman wannan zunubi ne na Shirka, Allah Subhanahu
Wa Ta’ala Ya sha alwashin ba ya gafarta wa duk wanda ya yi ta.
Matuqar har ya mutu bai tuba ba. Savanin sauran zunubai da komai
yawansu Yake shirye da ya gafarta wa wanda ya aikata su, qyaftawa da
bisimillah.
Don tabbatar da wannan magana ne, Buwuyayyen Sarkin ke
cewa:
Ma’ana:
Haqiqa, Allah bai gafarta wa duk wanda ya haxa shi da wani
a cikin bauta. Amma Yana gafarta abin da bai kai wannan
ba, ga wanda Ya so (4:48).
Daga cikin nauo’an Shirka, da suka yawaita matuqa a qasashen
musulunci a yau, akwai:
19
Bautar Qaburbura
Bautar qaburbura ita ce qudurce cewa, wani waliyyi daga cikin
waliyyan da suka riga mu gidan gaskiya, na iya biyan wata buqatar
mutum ko cetonsa daga wani haxari. Saboda haka sai a riqa kiran
sunayensu don neman taimako ko agaji.
To, a idon shari’ah da aqidar musulunci ingantatta yin haka bauta
wa irin waxannan bayin Allah ne. Alhali kuwa Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya ce:
Ma’ana:
Kuma Ubangijika Ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai
shi kaxai (17:23).
Irin wannan bauta ba ta tsaya ga waliyyai da qaburburansu ba.
Har wasu Annabawa da Salihan mutane, da suka riga mu gidan gaskiya,
wasu mutane kan nufa da wasu buqatu, da suka haxa da neman agaji,
buqatar haifuwa, gyaran aure da makamantansu. Su ma sukan yi haka ne
ta hanyar kiran sunayensu a irin waxannan lokuta. Alhali kuwa ba za su
iya amfanin su da komai ba. Ga shi kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala
Ya ce:
Ma’ana:
Ko wane ne yake karva wa mai buqata idan ya kira shi,
kuma ya sanya ku mamayan qasa? Shin akwai wani abin
bauta wa tare da Allah? Kaxan ne kuke faxaka (27:62).
20
Saboda tsananin kama jikin waxansu mutane da irin wannan
Shirka ta yi, abin har ya fi qarfin qudurtawa a zuci. Wasu ma har
ambaton sunayen wasu shehunai da waliyyai suke yi idan za su zauna ko
za su tashi tsaye, ko idan suka yi tuntuve ko suka haxu da wata annoba.
Sai ka ji suna cewa: “Ya Muhammadu” ko “Ya Aliyyu’’ ko “Ya
Husaini”. A yayin da kuma wani zai ce: “Ya Badawi’’ ko “Ya jelani” ko
“Ya shazali” ko “Ya Rufai”. Wasu ma har al-Aidarus ko Sayyidah
Zainab suke kira. Alhali kuwa gaba xayansu su ma ta kansu suke yi,
kuma bayin Allah ne kamar kowa. Kamar yadda Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya ce:
Ma’ana:
Tabbas, waxanda ku ke kira ba Allah ba bayin Allah ne
kamar ku. To, ku kira su su karva maku in gaskiya ne kuke
yi (7:194).
Wasu ma har tattaki sukan yi zuwa wurin kusheyin waxannan
bayi su dinga yin xawafi gare su kamar yadda ake yi ga xakin ka’abah,
har ma su shafi kusurwoyinsu. Wasu kuma sukan har ma sunbanci
kusheyin, su kuma kai hannayensu gare su, su shafi fuskokinsu da qurar
kamar masu taimama. A yayin da wasu ko, da zarar sun tunkaro
makwantan ba abin da za su yi sai ruku’i ko su yi tsaye qyam a gabansu
suna masu tsananin ladabi da vari kamar su narke. A inda za su roqi
buqatunsu kamar neman waraka daga wata rashin lafiya, ko albarka ga
wani yaro, ko tsira daga wata matsala. A wasu lokutan ma zaka ji wasu
21
daga cikinsu na magana da mamatan suna cewa: “Ya shugabana! ga ni na
niqo gari daga uwa duniya ina fatar buqatuna sun gama biya. Alhali kuwa
da za su share shekarun Abarshi suna kiran su ba za su karva masu ba.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:
Ma’ana:
Kuma wane ne mafi vata daga wanda ke kiran wanin
Allah wanda ba zai karva masa ba, har Ranar qiyama,
alhali su (waxanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran
su (46:5).
Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk
wanda ke nufin wani da wata buqata banda Allah, makomarsa ita ce wuta
(Buhari: 8/176).
Duk bayan waxannan kiraye-kiraye kuma, qarshe sai ka ga wasu
daga cikin waxannan mutane sun karkata gefen kusheyin sun aske kansu.
Wasu kuma sun shagala da karatun xan littafinsu mai suna: “al-
Mashahid” wanda littafi ne da aka tsara yadda ziyarar qaburburran
Waliyai da Annabawa zata kasance, da karance- karancen da wasu
mutane suka ga ya dace ayi. Kamar dai Littafin “Manasik al- Hajji”
wanda gamagarin Alhazzai ke amfani da shi. Qarewa da qarau ma, wasu
daga cikin irin waxannan mutane sun yi imani da cewa a hannun
waxannan matattu linzamen harkokin duniya suke. A sakamakon haka,
suna iya amfanar da wanda suke so, su kuma cutar da wanda bai masu
daidai ba. Tarqashi! Allah mai halitta!!.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala dai cewa Ya yi
22
Ma’ana:
Kuma idan Allah Ya shafe ka da wata cuta, to babu mai
yaye ta face shi, kuma idan Yana nufin ka da alheri, to
babu mai iya hana falalarsa sauka. Yana bayar da alherinSa
ga wanda Ya so, kuma Shi ne Mai yawan gafara, Mai
Yawan jinqai (10:107).
Haka kuma duqa ma wani wanda ba Allah ba, Shirka ne. Kamar
irin duqawar da irin waxannan mutane ke yi ko ajiye fitilu da kyandirora
ga waxannan qaburbura. Bayan wannan nau’in Shirka sai kuma:
Yanka Don Wanin Allah
Xaya daga cikin yanke – yanken da mushrikai kan yi tun zamanin
Jahiliyyar Larabawa, wanda kuma ya zama wata al’ada da ta watsu a
cikin duniya shi ne yanka wata dabba don aljannu su sha jini.
Mushrikan Larabawa kan yi wannan al’ada ne, kamar idan xayan
su ya gina ko ya sayi gida, ko ya haqa wata rijiya. Sai a sami wata dabba
a yanka a bai wa aljannun da ake da imanin suna cikin gidan ko rijiyar
jini a matsayin cin hanci, don su bar abin. Wanda idan ba haka aka yi ba,
a tunaninsu, mai gidan ko rijiyar zai haxu da wata cuta.
Irin wannan Shirka ta haxa nau’in haramiya biyu: Na farko,
Sadaukar da wani abu da sunan bauta ga wanin Allah. Na biyu kuma,
yanka abin da za a yi ba da sunan Allah ba.
23
Da zuwan addinin Musulunci sai wannan al’ada ta haramta.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya musanya wa musulmi ita da bauta masa
inda Ya ce:
Ma’ana:
Saboda haka, ka yi sallah ga Ubangijika, ka kuma yi
yanka (don Shi) (108:2).
Bayan wannan kuma sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya qara daddale wannan haramci tare da qara fitowa da shi
fili, ya ce: “Allah Ya la’anci duk wanda ya yanka wani abu don wanin
Allah (Muslim: 1978).
Nau’in Shirka na gaba kuma shi ne:
Halsta Abin Da Allah Ya Haramta
Haka nan kuma yin imani da cewa akwai wani mahaluki a bayan
qasa, wanda ke da lasisin halasta wani abu da Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya haramta, Shirka ne.
Irin wannan Shirka ta haxa har da kai qara a kotunan da ba na
musulunci ba. Musamman idan haka ta kasance tare da yin imani da
cewa yin haka halas ne. Kuma an tafi can ne bisa zavin kai; babu wanda
ya tilasta hakan.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ambaci irin wannan Shirka a
cikin Alqur’ani, a matsayin Babbar Shirka, in da Ya ce:
24
Ma’ana:
Sun riqi malamansu (Yahudawa) da ruhubanawansu
(Nasara) Ubannangiji, baicin Allah (Saboda Suna yi
masu xa’a a cikin abubuwan da suka halasta masu ko
haramta masu, bisa ra’ayin kansu; ba umunin Allah ba)
(9:31).
A lokacin da Adiyyu xan Hatimu ya ji Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya karanta wannan aya sai ya ce: Ya Manzon Allah!
Ai ba bauta masu suke yi ba. “Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya karva masa da cewa: “Na ji. Amma ai suna halasta masu
abubuwan da Allah Ya haramta, su kuma haramta masu abubuwan da Ya
halasta, su kuma amince da haka ko? To, ai wannan ita ce bautar da suke
yi masu. (Baihaqi: 10/116).
Bayan wannan ma, irin wannan tavargaza, na daga cikin siffofin
mushrikai, kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya bayyana a wata
aya da ke cewa:
!, :567 lzyxwvum
Ma’ana:
Ba su haramta abin da Allah da Manzonsa ya haramta,
kuma ba su bin addinin gaskiya (9:29).
A wata ayar kuma Ya ce:
Ma’ana:
25
Ka ce, “Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar saboda ku
na arziki, sai kuka halalta wasu kuka haramta wasu?”.
“Ka ce, “Shin, Allah ne Ya yi maku izini, ko Allan ne
kuke wa qazafi? (10:59).
Nau’in Shirka na gaba kuma shi ne:
Sihiri, Bayar Da Sa’a Da Faxin Gaibi
Sihiri wani na’ui ne na kafirci, kuma Shirka ne. Yana kuma daga
cikin zunubai guda bakwai da ke durmuyar da mutun a cikin wuta. Kuma
babu wani amfani da ake samu a cikinsa. Hasali ma ba abin da yake
haifarwa ga wanda aka yi wa shi illa hasara da ci baya.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gaya mana matsayin masu
koyon sa. Ya ce:
Ma’ana:
Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma
ba ya amfaninsu (2:102).
A wata ayar kuma Ya ce:
, :89 lzyxwvum
Ma’ana:
Kuma masihirci ba ya cin nasara a duk inda ya je (20:69).
A wata ayar kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya tabbatar da cewa duk
wanda ke sihiri da tsafi kafiri ne. Ya ce:
26
Ma’ana:
Kuma sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma shaixanun su ne
suka yi kafirci, (Saboda) suna karantar da mutane sihiri
da abin da aka saukar da shi a kan mala’iku biyu a
Babila; Haruta da Maruta. Kuma babu wanda suka sanar
sai sun ce: “Mu fa fitina ne, saboda haka kada ka kafirta”.
(2:102).
Bayan wannan kuma hukuncin mai sihiri a duniya shi ne kisa,
kuma duk abin da ya samu daga wannan sana’a tasa qazantatta, shi ma
haram ne.
Amma kuma duk da irin wannan mugun matsayi na mai sihiri,
sai ka taras da wasu musulmi, saboda kantar jahilci da tsatsarsa, da raunin
imani da ke tattare da su, suna ziyarar masu wannan mugunyar sana’a
don neman su taimake su, su xauki fansa a kan wani ko kuma don su
karya wani makaru da wani ya yi masu. Alhali kuwa kamata ya yi su
fuskanci Allah Subhanahu Wa Ta’ala su nemi taimakonsa a kan
waxannan al’amurra da makamantansu. Ta hanyar karanta wasu surori na
Alqur’ani kamar Falaqi da Nasi.
Haka su ma masu bayar da sa’a, ta hanyar bayar da labarin abin
da zai faru. Su ma kafirai ne. Domin suna raya cewa sun san gaibi. Alhali
kuwa babu wanda ya san gaibi sai Allah.
27
Mafi yawan masu irin wannan sana’a sukan yi amfani ne da
qarancin ilimi da wayewar wasu mutane, su karve masu kuxaxe. Sai ka
ga suna ‘yan zane –zane ga qasa, suna jefa xiyan wuri suna karanta wasu
surkulle. Wasu kuma a qasashen Turai suna wasa da kofunan Gahawa da
wasu ‘yan kwalayen qarau da madubbai, da makamantansu. Amma kuma
a mafi yawan lokuta, sau xaya ne sukan yi nasara daga cikin sihiri xari
da suke yi, sauran xari ba xayan kuma, sun sha kunya a cikinsu. Duk da
haka, irin waxancan jahilan mutane sai su mayar da hankali a kan sihirin
nan guda da qaddara ta riga fata a cikin sa, su manta da Tasa’in da tarar.
Take Sai ka ga suna ta yin tururuwa a garaken masihirtan, suna
neman su gaya masu ko akwai sa’a a cikin wani aure ko kasuwanci da
suke shirin qullawa. Ko su taimaka masu su gane wani abu nasu da ya
vata da wasu abubuwa masu kama da wannan.
A qa’idar shari’ar musulunci kuwa gaskata mai sihiri kafirci ne.
Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk
wanda ya je wurin wani boka ko mai sihiri, ya kuma gaskata shi, to, ya
kafirce wa abin da aka saukar ga Muhammadu Sallallahu Alaihi
Wasallama (Ahmad: 2/429).
Idan kuwa har zuwa wurinsu kawai mutun ya yi, ba don ya yi
imani da abin da suke yi ba, ba kuma don ya yi amanna cewa sun san
gaibi ba. A’a ya dai tafi ne don tantancewa da ganarwa idonsa, ko don
wani abu mai kama da wannan, to bai zama kafiri ba. Amma dai ya yi
babbar hasara. Don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:
Duk wanda ya je wurin wani mai sihiri ya kuma tambaye shi wani abu to,
ba za a karvi Sallarsa ba har kwana arba’in (Muslim: 4/1751). Amma duk
da haka wajibi ne ya ci gaba da Sallar, yana kuma neman gafarar Allah a
kan laifin.
28
Bayan wannan na’ui na Shirka sai kuma:
Imani Da Taurari
Zaidu xan khalidu al-juhani ya riwaito cewa: “Wata rana a
Hudabiyya, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba mu sallar
safe, bayan an xauke ruwan sama, da aka kwana ana yi. Da ya qare sallar
ya juyo ya fuskance mu. Sai ya ce: ko kun ji abin da Unbangijinku ke
faxa? Muka ce: Allah da Manzonsa kaxai ke da sani. Daga nan sai ya ce:
“Allah Ya ce ne: Wayewar garin nan wani bawa nawa ya yi imani da ni,
wani kuma ya kafirce mani. Duk wanda ya ce: “Ruwan nan Allah ne Ya
shayar da mu a cikin ikonsa da rahamarsa”. To shi ne wanda ya yi imani
da ni, ya kafirce ma taurari. Shi kuwa wanda ya kafirce mani ya kuma yi
imani da taurari shi ne wanda ya ce: “Tauraruwa kaza da kaza ne suka
shayar da mu wannan ruwa (Buhari: 2/333).
Haka kuma duk wanda ya karanta jadawalin abubuwan da za su
faru na gaibi wanda ake kirdado dabra da kaiwa da komowar taurari, a
cikin wata jarida ko mujalla, ya kuma yi imani da abin to, babu shakka
shi ma mushriki ne. Savanin wanda karantawa kawai ya yi don nishaxi.
Shi mai laifi ne kawai. Dalili kuwa shi ne, ba abu ne yardadde a shari’a
ba, mutum ya nemi samun wani nishaxi ta hanyar karanta wasu abubuwa
da suka qunshi Shirka. Domin shexan na iya amfani da wannan dama ya
tuqa masa tuwon tulu, a wayi gari ya faxa cikin mushrikai.
Abu na gaba kuma a layin nau’o’an Shirka shi ne:
Imani da Tasirin wani Abu
Wani nau’i na Shirka kuma shi ne imani da cewa, wani abu na da
wani tasiri na amfani zuwa ga mutum. Alhali Allah Mahalicci bai tanadi
haka ba.
29
Wasu mutane sun yi imani da cewa, abubuwa irin su: Karho,
Laya, Guru da Dagumma na da wani amfani da zasu iya yi masu.
Wannan kuwa wata tsohuwar al’ada ce da suka gada tun kaka da
kakanni. Wasu kuwa yanzu ne da rana tsaka bokaye da malamansu na
tsibbu ke xora su a kan wannan aqida. A sakamakon haka sai ka tarar da
su rataye da waxannan abubuwa ga wuyansu ko sun xaura ga
kunkuransu, ko sanye ga kunnuwansu ko ga damatsansu ko na’ya’yansu.
Imanin da suka yi shi ne abubuwan na taimakonsu ga kuranye masu
hatsarin mayu da masu kandun baka.
Wasu kuma zaka ga rataya irin waxannan abubuwa suke yiga
motocinsu ko a bangayen gidajensu. Wasu kuma wasu zobba zaka gani
ga yatsunsu, waxanda aka saka wa wasu duwatsu na musamman
waxanda suka yi imani cewa, suna ba su kariya ne daga wasu matsaloli.
Alhali kuwa a haqiqanin gaskiya, waxannan abubuwa na kawai nisantar
da waxanda suka yi imani da su ne, daga kasancewa masu imani da
Allah Subhanahu Wa Ta’ala, masu dogara gare shi. A qarshe kuma ba
abin da za su qaru da shi, illa rauni da hasara da tavewa. Domin yin
hakan neman waraka ne ta hanyoyi haramtacci.
Eh! Ko shakka babu hanyoyi ne haramtacci. Domin a cikinsu
akwai Shirka, wadda ke tabbata ta hanyar neman agaji daga shexanu ko
wasu aljannu. Ko ka taras a cikin su da surkulle, na wasu zane-zane da
rubuce- rubuce. A wasu lokuta kuma zaka ga an rubuta wasu ayoyin na
Alqur’ani, an sassaqa su da wasu kalmomi na Shirka. Wani lokaci ma
akan yi waxannan rubuce-rubuce da zane- zane ne, da qazamtattun
abubuwa kamar jinin haila da makamantan sa.
Ko shakka babu, xaura irin waxannan abubuwa da amfani da su a
jikin mutum ta ko wace hanya haramun ne. Saboda Manzon Allah
30
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya xaura laya ya yi
Shirka (Ahmad: 4/156).
Qarin bayani game da wannan hadisi shi ne: Idan wanda ya xaura
layar ga misali ya qudurce cewa, tana da wani tasiri na kai tsaye, a cikin
samar da wani amfani ko wata cuta wadda Allah bai nufa ba, to, ya
aikata babbar Shirka. A yayin da wanda kuma ya xaura layar yana mai
qudurce cewa, tana zama sanadi ne kawai na amfanin ko cutar amma
tantagaryar aikin na hannun Allah. To, irin wannan ya aikata qaramar
Shirka.
Wani nau’i na Shirka kuma shi ne:
RIYA
Yana daga cikin qa’idojin da shari’a ta gindaya, ga ko wane
kyakkyawan aiki, kafin ya zama karvavve a wurin Allah, dole ne ya
kasance an yi shi ba don a nuna wa duniya ba. Kuma dole ne ya kasance
daidai da yadda sunnah ta tanada a yi shi.
A kan haka, duk wanda ya aikata wani aiki na ibada kamar Sallah
don ya nuna wa mutane cewa yana sallah, to ya yi Shirka. Kuma Allah ba
zai karvi aikinsa ba.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala ne cewa a kan haka:
Ma’ana:
Haqiqa, munafukai suna yaudarar Allah (a zatonsu) alhali
kuwa Shi ke yaudarar su ga haqiqani. Kuma idan sun tashi
zuwa sallah, sai su tashi a raggwance. Suna nuna wa mutane
31
(wai suna sallah!), kuma ba su ambatar Allah sai kaxan
(4:142).
A idon shariar musulunci duk wanda ya yi wani aiki na ibada don
labari ya kai ga kunnuwan mutane, ya faxa tarkon Shirka, kuma
sakamakonsa shi ne Allah zai taqaita ladar aikin nasa a kan haka. Kamar
yadda xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito a wani hadisi cewa,
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya aikata
wani abu don mutane su ji ko su gani Allah zai sa su jin kuma su gani
(Shi ke nan. Ba lada). (Muslim: 4/2289) .
Haka kuma yau da mutum zai yi irin wannan aiki na ibada amma
bai yi shi don mutane su gani ko so ji ba kawai. A’a har ma don Allah Ya
ji kuma Ya gani, To, shi ma irin wannan bai tsira ba. Kenan ya yi aikin
don Allah da mutane. Aikin nasa kuwa ya zama ba karvavve ba a wurin
Allah. Kamar yadda wani hadisi qudusi yake cewa, Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya ce: “Na wadaci kaina, ta yadda ba na buqatar yin tarayya da
kowa a cikin komai. Saboda haka duk wanda ya aikata wani aiki, ya ce
ya yi shi don mutane da kuma Ni, to na bar wa wanda ya haxa Ni da shi
aikin. Ni ba na so (Muslim: 2485).
Tana yiwuwa kuma, wani lokaci, mutum ya fara wani aiki, ba ya
nufin kowa da shi sai Allah. Amma kuma kafin ya qare sai shexan ya
kaxa masa tambari sai ya ji yana buqatar a gani. To, idan ya qi sauraren
wannan huxuba ta shexan Allah zai karvi aikin nasa. Amma idan ya
saurare shi har ya yi masa kari, to, mafi yawan malamai sun tafi a kan
cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba zai karvi aikin nasa ba.
Nau’i na gaba kuma daga cikin waxannan nau’o’i na Shirka shi ne;
32
CAMFI
Camfi wata tsohuwar al’ada ce ta maguzanci, da akan yi amfani da
ita don gano abin da zai faru nan gaba na alheri ko sharri, ko kuma don
yanke hukuncin dalilin faruwar wani abu da mafarinsa. Allah Subhanahu
Wa Ta’ala na cewa:
Ma’ana:
Sai idan wani abu mai kyau ya je masu, sai su ce:
“Wannan namu ne”. Kuma idan masifa ta same su sai su
ce, shu’umcin Musa ne da waxanda ke tare da shi
(7:131).
Kafin zuwan musulunci idan Balarabe ya shirya tafiya sai ya kama
wani xan tsuntsu sannan ya sake shi a sarari har tsuntsun ya yi tafiyar sa.
Idan ya fiffika ta dama, sai ya ce, akwai sa’a ga wannan tafiya. Idan
kuwa har ya fiffika ta hagu, to, shikenan, ba batun tafiya domin babu sa’a
a cikinta.
Da bayyanar musulunci, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yanke wa irin wannan camfi hukunci da cewa: “Camfi
Shirka ne” (Ahmad: 1/389).
Irin wannan haramtacciyar aqida ta camfi wadda ke takin saqa da
aqidar Tauhidi ta haxa da, qudure cewa akwai waxansu lokuta ko
ranakku ko watanni da makamantan su da babu sa’a a cikinsu faufau.
Kamar yadda wasu suka camfa watan Rajab da cewa watan rashin sa’a
ne. Saboda haka ba sa yin aure a cikinsa. Wasu kuma sun camfa ranar
33
larabar qarshen ko wane wata da cewa ita ma rana ce ta rashin sa’a, da
saukar miyagun qaddarori. Wasu kuma sun camfa wasu sunaye da wasu
lambobi, kamar 13 da wasu mutane suka camfa da cewa ba sa’a a tare da
ita.
Haka kuma camfa musakai da wasu mutane suka yi da cewa suna
tare da rashin sa’a. Shi ma wannan haramun ne. Akwai mutanen da yau
da zasu nufi kasuwa su don su buxe shagunansu. Da zarar sun ci karo da
mai- ido- xaya a hanya sai su dawo gida. Wai, ba sa’a a ranar kenan. Duk
waxannan camfe-camfe haramun ne, kuma nau’i ne na Shirka. Kuma
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, ba shi ba mai yin su.
Kamar yadda Imrana xan Husaini ya riwaito cewa, Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke amfani da tsuntsu
don neman sa’a, ko yake da wani mai yi masa haka, ko ya ke gaya masa
abin da gobe zata haifar, ko yake haka da kansa, ba ya tare da mu”. Mai
riwayar ya kuma ce: Kuma kamar na ji ya ce haka: “Ko wanda ke tsafi,
ko yake da wani mai yi masa”. (Tabarani: 18/162).
Kaffarar da wanda ya yi irin wannan aika-aika zai yi na cikin
hadisin da Abdulahi xan Ausu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya fasa yin wani abu saboda wani
camfi, ya yi Shirka. Sai sahabbai suka tambaye shi, mene ne kaffararsa?
Sai ya ce: kaffararsa ita ce, ya ce: Ya Allah! babu wani alheri sai
alherinka, babu kuma wani sharri sai wanda ka hukunta, kuma babu wani
Ubangiji sai kai kaxai. (Ahmad: 2/220).
To amma kuma a haqiqa, yin imani cewa, wani abu na iya zama
alheri ko sharri wani abu ne da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya halitta
cikin jinin xan Adamu, kai tsaye ko kaikaice. Amma kuma babban
maganinsa shi ne dogara ga Allah. Kamar yadda xan Ma’sudu
34
Raliyallahu Anhu ya ce: “Babu wanda ba ya irin wancan hasashe daga
cikinmu a wasu lokuta. Amma da zarar mun mayar da kome ga Allah sai
mu sami sukuni (Abu Dawud: 3910).
Nau’i na qarshe daga cikin waxannan nau’o’i na Shirka shi ne:
Rantsuwa Da Wanin Allah
Allah Maxaukakin Sarki shi ke da iko da damar yin rantsuwa da
duk abin da ya ga dama daga cikin abubuwan da ya halitta. Babu wani
mutum da ke da damar yin rantsuwa da wani abu da ba Allah ba. Amma
kuma duk da haka akwai mutane da dama daga cikin musulmi da ke yin
rantsuwa da wanin Allah. Yin haka kuwa ba wa abin da aka yi rantsuwar
da shi ne matsayin Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Wannan kuwa laifi ne
babba. Xan Umar ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce: Haqiqa Allah Ya haramta maku yin rantsuwa da
ubanninku. Duk wanda rantsuwa ta kama shi daga cikinku, to ya rantse
da Allah ko ya kama bakinsa. (Bukhari: 11/530). Haka kuma xan Umar
xin ya riwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “duk
wanda ya rantse da wanin Allah ya yi Shirka. (Ahmad: 2/125).
Haramun ne mutum ya rantse da: Xakin Ka’aba, ko Gaskiyar wani
ko tasa, ko Darajar wani ko tasa, ko suturar wane da wane, ko rayuwar
wane da wane, ko Mu’ijizojin wani Manzo, ko karamar wasu Waliyyai,
ko mutum ya rantse da Mahaifansa ko dai wani abu. Duk wanda ya aikata
haka to, ya yi Shirka. Babu abinda zai kankare masa wannan laifi sai sake
faxar kalmar shahada; ita ce: “La’ilaha Illal-lah”. Kamar yadda wani
ingantaccen hadisi ya ce: “Duk wanda ya yi rantsuwa da Lata ko Uzza, to
ya ce: “La’ilaha Illallah” (Bukhari: 11/536).
35
Bayan irin wannan rantsuwa da wanin Allah ta kai tsaye, akwai waxansu
kalamai da musulmi ke furtawa waxanda kuma ba wani abu a cikinsu sai
Shirka. Kalaman sun haxa da:
(i) Ina neman taimakon Allah da naka”
(ii) Wannan abu daga Allah ne da kuma kai
(iii) Ba ni da kowa sai Allah sai kai
(iv) Taqamata Allah a sama da kai a qasa”
(v) Ba don Allah da wane da wane ba..”
(vi) “….na jingine musulunci”
(vii) Shekara ta karya ni
(viii) Wannan mummunan lokaci ne”
(ix) Zamani xan mangwaro ne.
Haka kuma akwai wasu sunaye da wasu musulmi ke amfani da su,
waxanda ke xauke da amon Shirka, kamar:-
(a) Abdul- Masihi (Bawan Masihu)
(b) Abdun- Nabiyi (Bawan Annabi)
(c) Abdul- Husaini (Bawan Husaini)
Duk ire-iren waxannan Sunaye da ke danganta mutum ga wani
wanda ba Allah ba, a matsayin bawansa, haramun ne. Kamar yadda yake
haramun musulmi ya furta irin waxancan kalamai da muka faxa don sun
qunshi haxa Allah da wani, ko sukar lamirin wani lokaci tun da yin haka
suka ne ga Allah Shi kansa.
Haka kuma akwai waxansu kalamai da zamani ya zo da su
waxanda ke takin saqa da Tauhidi. Su ma duk furta su da qudurce
ingancinsu a zuci haramun ne ga musulmi. Waxannan kalamai sun haxa
da kamar:
1- Gurguzun Musulunci (Islamic Socialism)
36
2- Dimuquraxiyyar Musulunci (Islamic Democracy)
3- Ra’ayin Mutane shi ne Ra’ayin Allah
4- Addini na Allah ne, qasa kuma ta kowa ce
Da sauran su.
Haka kuma haramun ne a ambaci wani munafuki ko kafiri da xaya daga
cikin waxannan laqubba.
- Alqalin Alqalai
- Sarkin Sarakuna
- Mai gida
Haka kuma yin “da-na sani” ta hanyar amfani da kalmar “Da dai..” ko
“in da ..” haramun ne. Domin kalmar na nuna cewa mutum bai gamsu da
wani abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya riga ya hukunta ba.
Haka kuma cewa: “Allah ka gafarta mani in ka ga dama” shi ma
haramun ne.
Mai son qarin bayani da faxaxa nazari sai ya duba littafin: Mu’ujamul
Manahil Lafziyyah Na Sheikh Bakr Abu Zaidi.
37
BABI NA BIYU
Zama Da Munafukai Da Mavarnata
Wani abu kuma da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta kuma
mutane suka yi biris da shi, shi ne zama wuri xaya da munafukai da
mavarnata. Zaka sami mutane da dama saboda rashin qarfin imani suna
zamansu gaba gaxi tare da irin waxannan mutane marasa tarbiyyah da
tsoron Allah. Wani lokacin ma sukan zauna har tare da waxanda ke sukar
lamirin shari’ar Musulunci, suna zolayar addini da masu kishinsa.
Ko shakka babu irin wannan xabi’a haramun ce. Kuma abu ne da
ke rosa imanin mai yinsa. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce;
Ma’ana:
Kuma idan ka ga waxanda suke kutsawa a cikin ayoyinmu,
to, ka kau- da- kai daga gare su, sai sun shiga cikin wani
labari ba shi ba. Kuma in ma dai shexan ya mantar da kai, to
kada ka zauna a bayan tanawa tare da mutane azzalumai
(6:68).
Wannan aya ta tabbatar mana da haramcin zama tare da waxannan
mutane, koda kuwa makusanta ne na qud-da qud. Sawa’un kun haxa
zumuntar jini ko hulxar arziki. Sai fa idan za ka zauna ne a wurinsu don
ka yi masu gargaxi ko ka qalubalance su game da abinda suke yi don su
daina. Idan ba haka ba, to haramun ne mutum ya zauna da su. Allah
Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:
38
Ma’ana:
Suna rantsuwa gare ku (Su Munafukai) don ku yarda da su.
To, ko kun yarda da su haqiqa Allah ba shi yarda da mutane
fasiqai. (8:96).
Ke nan duk wanda ya zauna tare da waxannan mutane zama na
yarda da amincewa, to ya zama xaya da su.
Rashin Natsuwa A Cikin
Sallah
Wani abun kuma da shari’a ta haramta shi ne yin sallah ba cikin
cikakkar ratsuwa ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:
“Babu Babban Varawo irin wanda ke satar wani abu daga cikin sallarsa.
Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, ya za a yi mutum ya saci wani
abu daga cikin sallah”? Sai ya ce: “Idan ya qi yin ruku’i da sujuda cikin
natsuwa” (Ahmad: 5/310).
Rashin cikakkar natsuwa a cikin ruku’i da sujuda da tsayuwa
bayan ruku’i da zama tsakanin sajaddai biyu, abu ne da ya zama ruwan
dare a tsakanin musulmi yau. Babu wani masallaci da zaka leqa sai ka
tarar da irin wannan matsala birjik. Alhali kuwa natsuwa babban rukuni
ce a cikin sallah, wanda sai ya samu ne take zama karvavviya a wurin
Allah. Wannan mas’ala babba ce matuqa. Domin kuwa Manzon Rahama
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Sallar mutum ba zata zama
39
karvavviya ba har sai gadon bayansa ya zama shimfixe a lokacin da yake
ruku’i da sujada (Abu Dwuda: 1/533).
Ko shakka babu, rashin cikakkiyar natsuwa a sallah ba abu ne mai kyau
ba. Kuma duk wanda ke haka ya cancanci gargaxi da faxakarwa da
alwashin horo na musamman.
Abu Abdillahil Ash’ari ya riwaito cewa: Wata rana Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba wa shabbansa wata sallah. Da aka
qare kuma ya zauna wurin tare da wasu daga cikinsu. Suna nan zaune a
haka, sai ga wani mutum ya shigo ya kabbarta sallah, yana ta qoton
kurciya. Kafin xan wani lokaci ya sallace.
Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kun ga
yadda mutumin nan ya yi sallah ko? To, duk wanda ya mutu yana irin
wannan sallah bai mutu a kan addinin Muhammadu ba. Kuma sallarsa ba
ta da banbanci da hankaka a lokacin da take qoton jini. Mai irin wannan
sallah kuma daidai yake da mayunwacin da zai ci qwarar dabino xaya ko
biyu. Kuna ganin za su amfane shi? (Ibnu Khuzaimah 1/332).
Haka kuma Zaidu xan Wahabu ya ce: Huzaifah ya ga wani mutum
na sallah, yana ruku’insa da sujada yadda ya ga dama sai ya ce masa:
“Sallarka bata yi ba. Kuma da zaka mutu yau ka sani ba zaka mutu a kan
addinin da Allah Ya saukar wa Muhamadu Sallallahu Alaihi Wasallama
ba (Bukhari: 2/274).
Don haka, duk wanda yake da masaniya da waxannan hadisai, ya
kuma qi yin sallah cikin natsuwa, to wajibi ne ya sake ta, ya kuma nemi
gafarar Allah akan abin da ya gabata. Don ko Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce wa mai munana sallarsa: “Je ka sake wannan
sallah, don ba ta yi ba”. Amma fa ba lalle ne sai ya maimaita gaba xayan
sallolinsa da suka gataba ba.