Labarai

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A


GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI


GIRMA


Wanda ya Rubuta: Fatin Sabri


Fassarar: M. Lu'a'i Sabri


2018


Bugu na farko


1.GABATARWA:


Lallai dukkan godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai,1 muna neman taimakonsa da kuma gafararsa kuma


muna tuba zuwa gare shi daga Zunubanmu da Munanan Ayyukanmu


Kuma na shida cewa babu wani abun bauta da gaskiya sai Allah shi kaxai wanda ba shi abokin tarayya,


kuma na shaida cewa Annabi Muhammad Bawansa ne kuma ManzonsaKuma na shaida cewa Annabi


Isa Bawansa ne kuma Manzon sa ne


wannan littafin shi ne taqaitaccen bayanin ginshiqin Saqon Annabi Isa -Amincin Allah a gare shi- kuma


shi ne Imani da Allah da bautarsa shi kaxai, yadda za'a kawo Qissar Annabi Isa da Mahaifiyarsa


Maryam da kuma kawo Dalilai da Hujjoji daga cikin Al-qur'ani da Al-taura da Linjila kan wannan Aqidar


Mai sauqi kuma tatacciya


Wannan littafin zai taimakawa masu neman Haqiqa, da kuma ma'abota Haskakan Hankula wajen sanin


cewa lallai Haqiqanin sakon da Ubangijin talikai ya aiko ta Hannun Manzannin sa ga baki xayan Al-


ummai a shuxewar Tarihi shi ne Saqo xaya ne kuma shi ne saqon kaxaita Allah tsantsa


Kuma Annabi Isa xaya ne daga cikin waxan can Manzanni Masu jin tsoron Allah waxan da sukai aiki


don shiryar da Al-umman su don kaxaita Allah tsantsa sai dai Wasu Mutanen da yawa sun kaucewa


Turbar kuma suka bi son ransu suna masu nisantar koyarwar Addinin su


2, FARKON QISSAR ANNABI ISA TA KASANCE NE DA


BAKANCEN DA MATAR IMRAN TAYI (MAHAIFIYAR


MARYAM) GA UBANGIJIN TALIKAI


Al-qur'ani: [2] 3:33-37


Lalle ne Allah Yã zãɓi Ãdama da Nũhu da Gidan Ibrãhĩma da Gidan Imrãna a kan tãlikai. (33)Zuriyya


ce sãshensu daga sãshe, kuma Allah Mai ji ne, Masani. (34)A lõkacin da mãtar Imrãna ta ce: "Ya


Ubangijina! Lalle ni, nã yi bãkancen abin da ke cikin cikĩna gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa


daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani." (35)To, a lõkacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya


Ubangijina! Lalle ne nĩ, nã haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai


zama kamar mace ba. Kuma nĩ nã yi mata suna Maryamu kuma lalle ne ni, ina nẽma mata tsari gare


Ka, ita da zũriyarta daga Shaiɗan jẽfaffe." (36)Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya


yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya rẽnonta ga Zakariyya. Ko da yaushe


Zakariyya ya shiga masallãci, a gare ta, sai ya sãmi abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: "Yã Maryamu!


1 Musulmai, Yahudawa, da kuma Nasara a gabas ta tsakiya suna anfani da sunan "Allah" don nuni


zuwa ga Ubangijin Talikai, Sunan "Allah" ya ya zo a cikin tsohon Al-qawari sau 89 (ka duba Sifr Al-


takween 2:4, kuma littafin Daniala 6: 20, da kuma Linjila ta larabci da ta Ibraniyanci)


Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda


Ya so ba da lissafi ba." (37)


3.MTSAYIN MARYAM KAMAMMIYA DA KUMA BUSHARA:


Al-qur'ani 3: 42-47


Kuma a lõkacin da malã'iku suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, Allah Ya zãɓe ki, kuma Ya tsarkake ki,


kuma Ya zaɓe ki a kan mãtan tãlikai." (42)"Yã Maryamu! Ki yi ƙanƙan da kai ga Ubangijinki, kuma ki yi


sujada, kuma ki yi rukũ'i tãre da mãsu rukũ'i." (43)Wannan yana daga lãbarun gaibi, Munã yin


wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lõkacin da suke jẽfa


alƙalumansu (domin ƙuri'a) wãne ne zai yi rẽnon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lõkacin


da suke ta yin husũma. (44)A lõkacin da malã'iku suka ce "Yã Maryamu! Lalle ne Allah Yana bã ki


bushãra da wata kalma daga gare Shi; sũnansa Masĩhu ĩsa ɗan Maryama, yana mai daraja a dũniya


da Lãhira kuma daga Makusanta. (45)"Kuma yana yi wa mutãne magana a cikin shimfiɗar jariri, da


kuma lõkacin da yana dattijo, kuma yana daga sãlihai" (46)Ta ce: "Yã Ubangijina! Yãya yãro zai


kasance a gare ni, alhãli kuwa wani mutum bai shãfe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah


yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana


kasancẽwa. (47)


4.MU'UJIZAR CIKI DA KUMA HAIHUWAR ANABI ISA -


AMINCIN ALLAH A GARE SHI-


Al-qur'ani: 19:16-35


Kuma ka ambaci Maryamu a cikin Littãfi, a lõkacin da ta tsallake daga mutãnenta a wani wuri, a gẽfen


gabas. (16)Sa'an nan ta riƙi wani shãmaki daga barinsu. Sai Muka aika rũhinMu zuwa gare ta. Sai ya


bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci.(17)Ta ce: "Lalle nĩ inã nẽman tsari ga Mai, rahama daga


gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini!" (18)Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne


dõmin in bãyar da wani yãro tsarkakke gare ki." (19)Ta ce: "A inã yãro zai kasance a gare ni alhãli kuwa


wani mutum bai shãfe ni ba, kuma ban kasance kãruwa ba?" (20)Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki


Ya ce. Shĩ, a gare Ni mai sauƙi ne. Kuma dõmin Mu sanya shi wata alãma ga mutãne, kuma wata


rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin yã kasance wani al'amari hukuntacce." (21)Sai ta yi cikinsa, sai


ta tsallake da shi ga wani wuri mai nĩsa.(22)Sai nãƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabĩniya, ta


ce "Kaitona, dã dai na mutu a gabãnin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka


manta!" (23)Sai (yãron da ta haifa) ya kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙĩƙa Ubangijinki


Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki.(24)"Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabĩnon


ya zuba a kanki yanã 'ya'yan dabĩno, ruɗabi nunannu." (25)"Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga


idãnunki. To, idan kin ga wani aya daga mutãne, sai ki ce, 'Lalle nĩ, na yi alwãshin azumi dõmin Mai


rahama sabõda haka bã zan yi wa wani mutum magana ba." (26)Sai ta je wa mutãnenta tanã auke da


shi. Suka ce: "Yã Maryamu! Lalle ne, haƙĩƙa kin zo da wani abu mai girma! (27)"Yã 'yar'uwar Hãrũna!


Ubanki bai kasance mutumin alfãsha ba, kuma uwarki ba ta kasance kãruwa ba." (28)Sai ta yi ishãra


zuwa gare shi, suka ce: "Yãya zã mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yanã


jãrĩri?" (29)Ya ce: "Lalle ne, nĩ bãwan Allah ne Allah Yã bã ni Littãfi kuma Ya sanya ni Annabi."


(30)"Kuma Yã sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka


matuƙar inã da rai." (31)"Kuma mai biyayya ga uwãta, kuma bai sanya ni mai kaushin zũciya ba


marashin alhẽri." (32)"Kuma aminci ya tabbata a gare ni a rãnar da aka haife ni da rãnar da nake


mutũwa da rãnar da ake tãyar da ni inã mai rai." (33)Wancan ne Ĩsã ɗan Maryamu, maganar gaskiya


wadda suke shakka a cikinta. (34)Bã ya kasancẽwa ga Allah Ya riƙi wani ɗã. Tsarki ya tabbata a gare


shi! Idan Yã hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cẽwa. (35)


5.ANNABTAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GRE SHI-


DA MU'AJIZOZINSA


Al-qur'ani: 5:75-76


Masĩhu ɗan Maryama bai zama ba fãce Manzo ne kawai, haƙĩƙa, manzanni sun shige dage gabãninsa,


kuma uwarsa siddika ce. Sun kasance sunã cin abinci. Ka duba yadda Muke bayyana musu ãyõyi.


Sa'an nan kuma ka duba yadda ake karkatar da su. (76)Ka ce: "Ashe kunã bauta wa, baicin Allah, abin


da ba ya mallakar wata cuta sabõda ku kuma haka wani amfani alhãli kuwa Allah Shi ne Mai ji, Masani?"


(76)


Al-qur'ani: 3"48-50


Kuma Ya sanar da shi rubũtu da hikima da Attaura da Linjĩla. (48)Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga


Bani Isrãila'ĩla (da sãko, cẽwa), Lalle ne, ni haƙĩƙa nã zõ muku, da wata ãyã daga Ubangijinku. Lalle


ne ni ina halitta muku daga lãka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hũra a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu,


da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makãho da kuturu, kuma ina rãyar da matottu, da


izibin Allah. Kuma ina gayã muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyẽwa acikin gidãjenku. Lalle ne, a


cikin wannan akwai ãyã a gare ku, idan kun kasance mãsu yin ĩmãni. (49)"Kuma inã mai gaskatãwa ga


abin da yake a gabãnina daga Taurata. Kuma (nãzo) dõmin in halatta muku sãshen abin da aka


haramta muku. Kuma nã tafo muku da wata ãyã daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku


yi mini ɗã'ã. (50)


Al-qur'ani:5:112-115


A lõkacin da Hawarãyãwa suka ce: "Ya Ĩsa ɗan Maryam! shin, Ubangijinka Yanã iyãwa Ya saukar da


kaɓaki a kanmu daga samã?" (Ĩsã) Ya ce: "Ku bi Allah da taƙawa idan kun kasance muminai."


(112)Suka ce: "Munã nufin mu ci daga gare shi ne, kuma zukãtanmu su natsu kuma mu san cewa lalle


ne, kã yi mana gaskiya, kuma mu kasance daga mãsu shaida a kansa." 113)Ĩsã ɗan Maryam ya ce:


"Yã Allah. Ubangijinmu! Ka saukar da kaɓaki a kanmu daga sama dõmin ya zama ĩdi ga na farkonmu


da na ƙarshenmu, kuma ya zama ãyã daga gare Ka. Ka azurta mu, kuma Kai ne Mafĩfĩcin mãsu


azurtawa." (113)Allah Ya ce: "Lalle ne Nĩ mai saukar da shi ne a kanku sa'an nan wanda ya kãfirta daga


gare ku, to, lalle ne Nĩ, Inã azabta shi, da wata azãba wadda bã Ni azabta ta ga kõwa daga tãlikai."


(113)


Al-qur'ani:3: 52-53


To, a lõkacin da Ĩsa ya gane kã firci daga gare su, sai ya ce: "Su wãne ne mataimakãna zuwa ga Allah?"


Hawãriyãwa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi ĩmani da Allah. Kuma ka shaida cẽwa lalle ne


mu, mãsu sallamãwa ne. (52)"Yã Ubangijinmu! Mun yi imãni da abin da Ka saukar, kuma mun bi


ManzonKa, sai Ka rubũta mu tãre da mãsu shaida. (53)


Al-qur'ani: 14:61


Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Ku kasance mataimakan Allah kamar abin da Ĩsã ɗanMaryama ya ce ga


Hawãriyãwa, "Waɗanne ne mataimakãna zuwa ga (aikin) Allah?" Sai wata ƙungiya daga Banĩ Isrã'ĩla


ta yi ĩmãni, kuma wata ƙungiya ta kãfirta. Sai muka ƙarfafa waɗanda suka yi ĩmãni a kan maƙiyansu,


sabõda haka suka wãyi gari marinjãya. (14)


6.KUTUNGUILAR DON YAQAR ANNABI ISA -AMINCIN


ALLAH AGARE SHI- DA KARIYAR ALLAH A GARE SHI:


Al-qur'ani: 3: 54-59


Kuma (Kãfirai) suka yi mãkirci, Allah kuma Ya yi musu (sakamakon) makircin, kuma Allah ne Mafi


alhẽrin mãsu sãka wa mãkirci (54)A lõkacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Ĩsa! Lalle NĨ Mai karɓar ranka ne,


kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kãfirta, kuma Mai


sanya waɗanda suka bĩ ka a bisa waɗanda suka kãfirta har Rãnar ¡iyãma. Sa'an nan kuma zuwa gare


Ni makõmarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakãninku, a cikin abin da kuka kasance kuna sãɓã wa


jũna.(55)"To, amma waɗanda suka kãfirta sai In azabta su da azãba mai tsanani, a cikin dũniya da


Lãhira, kuma bã su da wasu mãsu taimako. (56)Kuma amma waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata


ayyukan ƙwarai, sai (Allah) Ya cikã musu ijãrõrinsu. Kuma Allah bã Ya son azzãlumai. (57)"Wannan


Muna karanta shi a gare ka (Muhammad) daga ãyõyi, da Tunatarwa mai hikima (Alƙur'ãni)." (58)Lalle


ne misãlin Ĩsã a wurin Allah kamar misãlin Ãdama ne, (Allah) Yã halitta shi daga turɓãya, sa'an nan


kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa.(59)


7-KORUWAR GICCEYEWA DA KUMA KASHE ANNABI ISA -


AMINCIN ALLAH A GARE SHI-


Al-qur'ani 4: 157-159


Da faɗarsu: "Lalle ne mu, mun kashe Masĩhu ĩsã ɗan Maryama Manzon Allah," alhãli kuwa ba su kashe


shi ba, kuma ba su kẽre shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a garẽ su. Lalle ne waɗanda sauka


sãɓã wa jũna a cikin sha'aninsa lalle ne, sunã shakka daga gare, shi, bã da wani ilmi fãce bin zato


kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙĩni. (157)Ã'a, Allah Ya ɗauke shi zuwa garẽ Shi, kuma Allah Yã


kasance Mabuwãyi, Mai hikima. (158)Kuma bãbu kõwa daga Mutãnen Littafi, fãce lalle yanã ĩmãni da


shi a gabãnin mutuwarsa, kuma a Rãnar ¡iyãma yana kasancẽwa mai shaida, a kansu. (159)


8- TAUHIDI SHI NE GINSHIQIN SAQON ANNABI ISA


Al-qur'ani 3: 51


"Lalle Allah shi ne Ubangijina, kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan ce hanya


madaidaiciya." (51)


Al-qur'ani 3:79-80


Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya bã shi Littãfi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa


mutãne: "Ku kasance bãyi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance mãsu aikin ibãda da abin


da kuka kasance kuna karantar da Littãfin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantãwa." (79)Kuma


ba ya umurnin ku da ku riƙi malã'iku da annabãwa lyãyengiji. Shin, zai umurce ku da kãfirci ne a bãyan


kun riga kun zama mãsu sallamãwa (Musulmi)? (80)


Al-qur'ani 9:31


Sun riƙi mãlamansu (Yahũdu) da ruhubãnãwansu (Nasãra) Ubannangiji, baicin Allah, kuma sun riƙi


Masĩhu ɗan Maryama (haka). Kuma ba a umurce su ba fãce da su bautã wa Ubangiji Guda. Bãbu


abin bautãwa fãce Shi. TsarkinSa ya tabbata daga barin abin da suke yin shirki da shi. (31)


Al-qur'ani: 5:116-118


Kuma a lõkacin da Allah Ya ce: "Yã Ĩsã ɗan Maryama! Shin, kai ne ka ce wa mutãne, 'Ku riƙe ni, ni da


uwata, abubuwan bautãwa biyu, baicin Allah?" (Ĩsã) Ya ce: "Tsarkinka yã tabbata! Bã ya kasancewa a


gare ni, in faɗi abin da bãbu wani hakki a gare ni. Idan nã kasance nã faɗe shi, to lalle Ka san shi, Kanã


sanin abin da ke a cikin raina, kuma bã ni sanin abin da ke a cikin nufinKa. Lalle ne Kai Masanin


abubuwan fake ne." (116)"Ban faɗa musu ba fãce abin da Ka umurce ni da shi; watau: 'Ku bauta wa


Allah Ubangijina kuma Ubangijinku;' kuma nã kasance mai shaida a kansu matuƙar nã dawwama a


cikinsu, sa'an nan a lõkacin da Ka karɓi raina Kã kasance Kai ne mai tsaro a kansu, kuma Kai, a kan


dukkan kõme, Halartacce ne. (117)"Idan Ka azabta su, to lalle ne su, bãyinKa ne, kuma idan Ka gãfarta


musu, to, lalle ne Kai ne Mabuwayi Mai hikima." (118)


Al-qur'ani:4: 171-173


Yã Mutãnen Littãfi! Kada ku zurfafã a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, fãce gaskiya. Abin


da aka sani kawai, Masĩ hu ĩsa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, yã jẽfa ta zuwa ga


Maryama, kuma rũhi ne daga gare Shi. Sabõda haka, ku yi ĩmãni da Allah da manzanninSa, kuma kada


ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) yã fi zama alhẽri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah


Ubangiji ne Guda. TsarkinSa yã tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shĩ ne da abin


da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Yã isa Ya zama wakĩli. (171)Masĩhu bã ya


ƙyãmar ya kasance bãwa ga Allah, kuma haka malã'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyãmar


bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tãra su zuwa gare shi gabã ɗaya. (172)To, amma waɗanda suka


yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to zã Ya cika musu ijãrõrinsu, kuma Yanã ƙãra musu daga


falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyãma, kuma suka yi girman kai, to, zã Ya yi musu azãba,


azãba mai raɗɗi kuma bã su samun wani masõyi dõmin kansu, baicin Allah, kuma bã su samun


mataimaki. (173)


9. BISHARA DA ZUWAN ANNABI mUHAMMAD -AMINCIN


ALLAH A GARE SHI- A HARSHEN ANNABI ISA


Al-qur'ani: 6:61


Kuma a lõkacin da Ĩsã ɗan Maryayama ya ce: "Yã BanĩIsrã'ĩla! Lalle nĩ Manzon Allah ne zuwa gare ku,


mai gaskata abin da ke gaba gare ni na Attaura, kuma mai bãyar da bushãra da wani Manzo da ke


zuwa a bãyãna, SũnasaAhmad (Mashãyabo)." To, a lõkacin da ya jẽ musu da hujjõji, suka ce: "Wannan


sihiri ne, bayyananne." 6


10. WASU GAVOVIN BAYANI


1


Qissar Annabi Isa -Amincin Allah a gareshi- tana farawa ne da Bakancen da Mahaifiyar Maryam tayi


ga Kanta na cewa zata Sadaukantar da abun da yake cikinta don bautar Ubangijinta, da kuma Hidimar


Baitul Maqdis, da Kuma roqonta ga Ubangijin Talikai kan ya karva mata


2


An bada Wasiyyar Nana Maryamu ga Annabi Zakariyya bayan anyi Quri'a kan wanda zai xauki renonta,


wanda wannan Wasiyyar ta zama Wajibi na Addini, Kasancewa Nana Maryam Mahaifiyarta ce ta


Sadaukantar da ita don yin Hidimar Bait Al-Maqaddas da kuma Kaxaicewa don bautar Ubangijinta


Annabi Zakariyya ya kasance an sanshi da tsoron Allah da kuma Taqawa, kuma haqiqa Nana Maryam


ta tashi kan Imani mai Qarfi da kuma Miqa Quya cikakke ga Ubangijin Talikai


3


Xaya daga cikin Ni'amomin da Allah yayiwa Nana Maryam saboda tsantseninta shi ne lamunce mata


da Aeziqi wadatacce a kowane lokaci ya kasance ana halin Fari ga Bani Isra'ila


4


Yayin da Mala'ika Jibril ya zo mata a Surar Mutumi, sai ta nemi tsarin Allah da ya kareta daga shi, kuma


wannan shi ne Dalilin da yake nuna Kamewarta da tsantseninta


5,


Yayin da Nana Maryam ta Samu cikin Annabi Isa -Amincin Allah a gare shi- ta miqa Al-amarinta ga


Ubangijinta kuma ta nisanci Mutanen ta


6,


Kariya da rahamar ubangijin talikai sun sauka ga Nana Maryam da ya sauwaqe Mata Haihuwar da


kuma Yalwar Abin ci da abun Sha a wani wuri amintacce kusa da kututturen Dabino da Tafkin Ruwa


da yake gudana a Qarqashin ta


7,


Yayin da aka tuhumci Nana Maryam kan ta zo da wani abu mai girma, shi ne zuwanta da Xa ba tare


da Uba, sai Ubangijin ta ya Umarce ta da Lazimtar yin shiru, kuma yayi Wahayi ga Jaririn da yayi


Magana da kuma bayyana kuvutar Mahaifiyarsa Nana Maryam


8


Kuma Annabi Isa har wala Yau ya qarfafa kan Annabtakarsa da Bautarsa da Miqa wuyansa ga


Ubangijin Talikai da kuma kasancewarsa shi Mutum ne kuma Manzo ne


9


Kaxaita Allah shi ne Tushen xan ba na farko a cikin Annabtakar Annabi Isa -Amincin Allah a gare shi-


lokacin ya qarfafa samuwar Ubangiji Qwara xaya wanda bashi da abokin tarayya kuma bashi da Xa,


kuma Annabi Isa ya kirawo Mutane ga Bautar Allah shi kaxai


10


Mu'ajizozin da suka faru a Hannun Annabi Isa sun kasance da Nufin Allah ne kuma da Umarninsa;don


tabbatar da Manzantakar Annabi Isa


11


Annabi Isa ya zo ne don gasgata Saqon Annabi Musa da kuma gyara dukkan Qarairayin da Sharrin da


aka jinginwa wancan Saqon


12


lokacin da Ubangijin Talikai ya kare Annabinsa Isa daga gicciyewa kuma ya dauke shi zuwa gare shi,


kuma yayi Masa Alqawarin cewa Mabiyamsa su ne Masu rinjaye da Galaba akan Abokan gabarsu har


zuwa ranar Alqiyama


13


Lallai cewa Mu'ajizar Halittar Annabi Isa ba tare da Uba ba a Wajen Ubangijin Talikai kwatankwacin


Halittar Annabi Adam neda aka Halicce shi ba tare da Uba ko Uwa ba


14


Annabi Isa -Amincin Allah a gareshi- ba'a kashe shi ba kuma ba'a gicciyeshi ba, a'a Allah ya xauke shi


ne zuwa gare shi


15


Annabi Isa bai tava umartar wani ba kan ya bauta masa shi da Mahaifirsa koma bayan Allah, Kawai


abunda yayi ya kirawo Mutane zuwa bautar Mahalicci shi kaxai; kuma shi ne Mutane baki xaya.


16


Al-qurani ya tsare kuma ya bada Kariya ga Maryam da Xanta Annabi Isa, cikin abunda aka danganta


musu na Da'awar Allantaka, kuma ya kuvutar da su daga Wannan Zargin, aa' ma ya qarfafa cewa su


sun kasance suna kira ne ga bautar Allah shi kaxai,


17


Annabi Isa -Amincin Allah a gare shi- ya kirawo Mutanensa don kaxaita Allah tsantsa, kamar yadda ya


zo a cikin Linjila kamar Misalin:


Saboda haka sai Yasu'a ya amasa kiransa: "Lallai cewa farkon baki xayan wasiyyoyi su ne: ka sauarara


kai Isra'il Ubangiji Allanmu kuma Ubangiji ne xaya, kuma kana son Ubangiji wanda shi ne Allanka da


ba ki xayan zuciyarka, haka da baki xayan kanka, haka daga baki xayan Tunaninka, haka daga baki


xayan ikonka, wannan ita ce Wasiyyar Farko"Marqus:12:29-30"Kuma wannan ita ce Rayuwa ta har


abada:, cewa sun sanka da cewa kai ne Haqiqanin Allah kai kaxai kuma Yasu'a Al-masih wanda ka


aiko shi"(Yuhanna: 17:3)


Marqus:12:29-30


"Kuma wannan ita ce Rayuwa ta har abada:, cewa sun sanka da cewa kai ne Haqiqanin Allah kai kaxai


kuma Yasu'a Al-masih wanda ka aiko shi"


(Yuhanna: 17:3)


18


Lallai kuma Zuwan Annabtar Manzon Allah Muhammad SAW ita wani vangare ne daga Manzantakar


Al-masihu


"Kuma ni ina rokon Baban da ya baku wani wanda zai riqeku don ya zauna tare da ku har abada"(Linjilar


Yuhanna: 14"16)"Kuma ko yaushe wannan Mai qarfafa yazo muku wanda zan aiko shi zuwa gareku


daga Baba, Ruhi na gaskiya, wanda daga gurin Baba zai futo, kuma ya shaida da ni"(Linjilar Yuhanna:


15: 26)


(Linjilar Yuhanna: 14"16)


"Kuma ko yaushe wannan Mai qarfafa yazo muku wanda zan aiko shi zuwa gareku daga Baba, Ruhi


na gaskiya, wanda daga gurin Baba zai futo, kuma ya shaida da ni"


(Linjilar Yuhanna: 15: 26)


11. TACEWA:


1. Saqon da Annabi Isa ya zo da shi shi ne Saqon baki xayan Annabawa kuma shi ne saqon kaxaita


Allah tsantsaLallai Mahalicci wanda ya aiko da baki xayan Manzanni ga baki xayan Al-ummai da saqo


iri xayalallai koyarwar Aqida bayyananniya wacce ta dace da sauran addinai tushenta xaya ne shi ne


Mahalicci, amma kuma savani yana samuwa ne sakamakon Tawilin Mutane


Lallai Mahalicci wanda ya aiko da baki xayan Manzanni ga baki xayan Al-ummai da saqo iri xaya


lallai koyarwar Aqida bayyananniya wacce ta dace da sauran addinai tushenta xaya ne shi ne Mahalicci,


amma kuma savani yana samuwa ne sakamakon Tawilin Mutane


2. Saqon Mahalicci zuwa ga Halitta dole ne ya zamanto saqo iri xaya kuma doke ne ya kasance Mai


sauqi domin fahimta kuma dole ne ya kasance angina shi kan Tushen magana kai tsaye tare da


Mahalicci


3, Kalmar Islam tana nufin cikakken miqa Wuya ga Ubangijin Talikai d Bauta masa ba tare da wani a


tsakani ba, kuma haqiqa wannan shi ne saqon baki xayan Manzanni kamar yadda Tarihi ya nuna, kuma


haqqi ne na Mahalicci a bauta masa shi kaxai


4. A farkon halittar Xan Adam an yi wani Alqawari tsakaninsa da Mahaliccinsa, yayinda ya shaida Masa


da kaxaitaka da Allantaka, saboda haka akwai wani abu Viyayye a Zuciyar kowane Xan Adam da


Samuwar Mahalicci da kuma KaxaitakarsaKuma iya Fixra da Xabi'a wacce Allah ya halicci Halittunsa


akanta, saboda Rana da Taurari da Dutse da Bishiyoyi da kuma baki xayan Dabbobi sun miqa wuya


ga Mahaliccinta kuma ta shaida masa da Kaxaitaka: (Ka duba Al-qur'ani: 7"172).


Kuma iya Fixra da Xabi'a wacce Allah ya halicci Halittunsa akanta, saboda Rana da Taurari da Dutse


da Bishiyoyi da kuma baki xayan Dabbobi sun miqa wuya ga Mahaliccinta kuma ta shaida masa da


Kaxaitaka: (Ka duba Al-qur'ani: 7"172).


5. Savani tdakanin Addinai y faru ne daga sanya wasu tsakanin Mahallici da kuma Halitta a wajen


Ibada, domin baki xayan Addinai sun haxu kan Bautar Mahalicci kai tsaye ba tare da wani Xan tsakiya


ba; zamu samu samu kawunanmu mun haxa kai baki xaya kewaye da Bautar Mahallici kwara xaya,


kuma wannan shi ne mabuxin Mutuntaka wajen Haxin da kuma rungumar juna.


Ka ce: "Yã ku Mutãnen Littãfi! Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitãwa a tsakã ninmu da ku; kada mu


bauta wa kõwa fã ce Allah. Kuma kada mu haɗa kõme da Shi, kuma kada sãshenmu ya riƙi sãshe


Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun jũya bã ya sai ku ce: "ku yi shaida cẽwa, lalle ne mu masu sallamã


wa ne."Al-qur'ani 3: 64


Al-qur'ani 3: 64


6. Ubangiji Mahalicci xaya ne kuma shi kaxai ake nufa da buqata, wanda bai dace ba da ya riqi Mata


ko kuma xa, kamar yadda cewa shi bai haifa kuma ba'a haife shi ba kuma bashi da kini da yai daidai


da shi


7. Ma'anar "Xan Allah" ba'a yi anfani da shi ba ga wuri xaya, saboda Allah yayi nuni a cikin Linjila zuwa


ga Bayin Allah zavavvu da cewa "'Ya'yan Allah" lallai cewa Yahudawa sun qudurce cewa Mahalicci


xaya ne kuma bashi da xa ko Mata ta koyaya ta Kasance, kuma saboda haka cewa Ma'anar "Xan Allah"


ana nufi da shi "Bawan Allah" wasu daga cikin Mabiyan Annabi Isa da suka zo daga Asalin Rumawa


ko Yunaniyawa suka munana anfani da Ma'anar Kalmar, yadda ya zo a cikin litattafansu da Ma'anar


sanyawa Allah jiki


8. Allah shi kaxai ne ya Mallaki cika ta kai tsaye da iko na kai tsaye, kuma shi bashi da buqata ya mutu


saboda mu kamar yadda wasu suka qudurce , kuma shi ne yake bada rayuwa, kuma shi ne ya ke


karveta, saboda hakan bai Mutu ba kamar yadda kuma bai tashi daga Mutuwa ba, shi ne wanda ya


kare kuma ya tsare Annabinsa Isa daga Kashewa ko gicciyewa, kamar yadda yake yi koda yaushe ga


bayinsa nagari wajen kare su da tsare su


9. Ubangijin Talikai Mai jin qai ne ga bayinsa sama da Uwa da 'Ya'yanta, saboda shi yake gafarta musu


ko yaushe suka koma zuwa gare shi, kuma suka tuba zuwa gare shi.


10. Darasin da Allah ya sanar da Mutane lokacin karvarsa Tuban Annabi Adam saboda cin Bishiya da


aka Haramta Masa ita ce farkon Gafara ga Ubangijin Talikai ga Mutane, yadda cewa babu Ma'ana ga


Zunubin da aka gada, saboda wani rai ba ya xaukar laifin Wani Ran, saboda kowane Mutum yana


xaukar laifinsa ne shi kaxai; kuma wannan rahama ce daga Ubangijin Talikai gare mu


11. Gafara bata kore Adalci, Kamar yadda Adalci baya hana gafara


12, An haifi Mutum tsarkakke ba tare zunuvi ba kuma ya kasance abun tambaya game da Ayyukansa


tun daga farkon Balaga ko Hankali


13. Mutane daidai suke a wajen Allah babu banbanci tsakanin Balarabe da baubawa sai da tsoron


Allah, da kuma aiki nagari kuma wannan yana bayyana Suffofin Allah na Mai rahama da kuma Adalci


da wasunsu, inda yake cewa:Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma


Muka sanya ku dangõgi da kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne)


wanda yake mafĩfĩcinku a taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.Al-qur'ani:13: 4914. Xaya


daga cikin Siffofin Ubangijin Talikai shi hikima, saboda baya Halittar wani abu don wasa, tsarki da


xaukaka sun tabbata gare shi ga barin hakan, kaxai yana halitta ne da hikima da kuma Ilimi, kuma


bamu halicci sama da qasa da abunda ke tsakaninsu ba saboda wasaAl-qur'ani:21:1615. Ba'a kama


Mutum da laifin da bai yi shi ba, Kamar yadda cewa Mutum ba zai iya tsira ba sai da Imaninsa da


aikinsa nagari, Allah ya bada rayuwa ga Xan Adam kuma ya bashi "yancin zavi don jarrabawa kuma


shi ne abun tambaya kaxai danagane da Ayyukansa, Kamar yadda zamu samu a littafin Al-Tathniya:


16:24"Ba'a kashe Iyaye saboda 'ya'yansu, kuma ba'a kashe 'ya'ya saboda Iyayensu kowane Mutum


ana kasheshi ne da laifinsa"Ka duba Al-qur'ani:35: 18


Yã kũ mutãne! Lalle ne Mũ, Mun halitta ku daga namiji da mace, kuma Muka sanya ku dangõgi da


kabĩlõli, dõmin ku san jũna. Lalle mafĩfĩcinku daraja a wurin Allah, (shĩ ne) wanda yake mafĩfĩcinku a


taƙawa. Lalle nẽ Allah Masani ne, Mai ƙididdigẽwa.


Al-qur'ani:13: 49


14. Xaya daga cikin Siffofin Ubangijin Talikai shi hikima, saboda baya Halittar wani abu don wasa, tsarki


da xaukaka sun tabbata gare shi ga barin hakan, kaxai yana halitta ne da hikima da kuma Ilimi, kuma


bamu halicci sama da qasa da abunda ke tsakaninsu ba saboda wasa


Al-qur'ani:21:16


15. Ba'a kama Mutum da laifin da bai yi shi ba, Kamar yadda cewa Mutum ba zai iya tsira ba sai da


Imaninsa da aikinsa nagari, Allah ya bada rayuwa ga Xan Adam kuma ya bashi "yancin zavi don


jarrabawa kuma shi ne abun tambaya kaxai danagane da Ayyukansa, Kamar yadda zamu samu a


littafin Al-Tathniya: 16:24


"Ba'a kashe Iyaye saboda 'ya'yansu, kuma ba'a kashe 'ya'ya saboda Iyayensu kowane Mutum ana


kasheshi ne da laifinsa"


Ka duba Al-qur'ani:35: 18


16. wannan rayuwar ba ita ba ce qarshen Makoma, kuma Allah bai halicci Xan Adam ba kawai don ci


da sha da kuma hayayyafa, da haka ne da Dabbobi sun fi Mutane wajen haka tunda suna ci kuma suna


sha kuma suna hayayyafa, sai dai su ba za'a yi musu hisabin ayyukansu ba, saboda Allah ya girmama


Xan Adam da Aikin Haliftaka a bayan Qasa kuma ya xaukaka shi sama da mafi yawa daga cikin abunda


ya halitta, kuma sannan za'a saka masa Ayyukansa a Lahira.


Ina roqon Allah wannan littafin ya kasance Fitilar Shiriya


da kuma Al-barka acikin Duniya da Lahira


QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA ......... 1


1.GABATARWA:.................................................................................................................................. 1


2, FARKON QISSAR ANNABI ISA TA KASANCE NE DA BAKANCEN DA MATAR IMRAN TAYI


(MAHAIFIYAR MARYAM) GA UBANGIJIN TALIKAI .......................................................................... 1


Al-qur'ani: [2] 3:33-37 .......................................................................................................................... 1


3.MTSAYIN MARYAM KAMAMMIYA DA KUMA BUSHARA:............................................................. 2


Al-qur'ani 3: 42-47 ............................................................................................................................... 2


4.MU'UJIZAR CIKI DA KUMA HAIHUWAR ANABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- ................. 2


Al-qur'ani: 19:16-35 ............................................................................................................................. 2


5.ANNABTAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GRE SHI- DA MU'AJIZOZINSA ............................ 3


Al-qur'ani: 5:75-76 ............................................................................................................................... 3


Al-qur'ani: 3"48-50 ............................................................................................................................... 3


Al-qur'ani:5:112-115 ............................................................................................................................ 3


Al-qur'ani:3: 52-53 ............................................................................................................................... 3


Al-qur'ani: 14:61................................................................................................................................... 3


6.KUTUNGUILAR DON YAQAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH AGARE SHI- DA KARIYAR


ALLAH A GARE SHI:........................................................................................................................... 3


Al-qur'ani: 3: 54-59 .............................................................................................................................. 3


7-KORUWAR GICCEYEWA DA KUMA KASHE ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- ...... 4


Al-qur'ani 4: 157-159 ........................................................................................................................... 4


8- TAUHIDI SHI NE GINSHIQIN SAQON ANNABI ISA...................................................................... 4


Al-qur'ani 3: 51..................................................................................................................................... 4


Al-qur'ani 3:79-80 ................................................................................................................................ 4


Al-qur'ani 9:31...................................................................................................................................... 4


Al-qur'ani: 5:116-118 ........................................................................................................................... 4


Al-qur'ani:4: 171-173 ........................................................................................................................... 5


9. BISHARA DA ZUWAN ANNABI mUHAMMAD -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- A HARSHEN


ANNABI ISA ........................................................................................................................................ 5


Al-qur'ani: 6:61..................................................................................................................................... 5


10. WASU GAVOVIN BAYANI ............................................................................................................ 5


11. TACEWA: ...................................................................................................................................... 7



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH