Labarai

TAIMAMA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA


[Hausa - [هوسا


Malan Aliyu Muhammad Sadisu


2014 - 1435


2


ليمم وأحاكمه


[Hausa - [هوسا


ﻤد السادس 􀅅 􀆧 الشﻴخ : ع


2014 - 1435


3


TAIMAMA DA HUKUNCE-HUKUNCENTA


Matashiya: Hakika Allah mai girma da


daukaka ya shar'anta tsarkaka daga hadasin da


yake karami ko babba kafin gabatar da sallah,


wannan tsarkaka kuma bata yiwa sai da ruwa


mai tsarki mai tsarkakewa, gabatar da wannan


tsarki da kuma rowan da aka ambata shine


abinda yake wajibi muddin akwai dama, sai dai


akan sami wasu lokuta da ake rasa rowan


kwatakwata ko kuma ga ruwan amma idan aka


yi alwala da shi ko wanka za'a rasa wanda za'a


sha, koma yin anfani da rowan zai haifar da


wasu cututtuka da dai sauran wasu dalilai


shar'antattu da zasu hana amfani da ruwan to


akan haka aka shar'anta Taimama domin


sawwakewa al'umma, da kuma dauke dukkan


wata damuwa akan hakan.


Mecece Taimama?: Taimama itace; Shafar


fuska da hannaye a wuri mai tsarki ta yana yi


kebantacce.


Kenan ba kowacce shafar fuska da hannu


ne yake zama taimama ba, sannan kuma ba a


kowanne wuri ake yi ba, sannan ba yadda aka


ga dama ake yi ba.


Tabbatuwar Taimama: Taimama ta tabbata


daga haske na Alkur'ani da kuma Hadisan


4


ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allan su


tabbata a gareshi- kana da ijima'in malamai.


Tabbatuwarta A Kur'ani: Allah ya yi bayanini


shar'antuwar taimama a cikin Alkur'ani mai


girma a Suratun Nisa'I, aya ta 43, da kuma


Suratul Ma'idah aya ta: 6. amma ayanzu zamu


kawo bayani akan ayar suratul ma'idah, wato


aya ta shida kenan, Allah madaukakin sarki


yana cewa:


''Ya ku dukkanin wadanda su ka yi imani!


Idan kun tashi za ku yi sallah to ku wanke


fuskokinku da kuma hannayanku zuwa gwiwar


hannu, ku kuma shafi kawunanku kuma ku


(wanke) kafafuwanku zuwa idon sawu, idan kun


kasance masu janaba to ku tsarkaka (ku yi


wanka), idan kuma kun kasance marasa lafiya


ko kuna kan tafiya ko kuma daya daga cikinku


ya yi bayan gida, ko kuma kun taba mata


(janaba) baku sami ruwa ba to sai ku yi


taimama a wuri mai tsarki sai ku sahfi


fuskokinku da kuma hannayanku daga wurin,


Allah baya nufin ya sanya mukun kunci ko kaka,


saidai yanason ya tsarkake ku kuma domin ya


cika ni'imarsa a gareku domin ku gode masa.


(Ma'idah, aya ta:6).


Wannan ayar babbar ayace, ta kunshi


hukunce-hukuncen Alwala da abinda yake


karyata, da kuma janaba da yadda ake wankan


tsarki, da kuma taimama da abinda ke sawa ayi


5


taimamar da kuma yadda ake yenta, sannan da manufar da tasa Allah ya shar'anta taimamar, Allah muna gode maka, akan wannan ni'ima. Tabbatuwar Taimama A Hadisi: Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- yace: ''An bani abubuwa biyar da ba'a ba wani ba kafin ni; An taimakamin da tsoro (ma'ana sanya tsoronsa a zukatan makiya) na tafira tsawan wata guda, kuma an sanya min kasa ta zama wurin sallah da kuma tsarki, duk inda wani mutum daga cikin al'ummata sallah ta riskeshi to ya yi sallar shi'' a wata riwayar ''To anan inda yake masallacinsa yake da kuma abin tsarkinsa''. Bukhari, Hadisi na: 335, Muslim Hadisi na: 521. Wannan hadisin ba karamin hadisi bane, domin ya yi bayanin gatan da Allah ya yi wa wannan al'ummar gatan da bai yiwa wata al'ummaba, a ciki ya ambaci cewa an sanya masa kasa ta zama wurin sallah, al'ummomi da suka gabata basa sallah a ko ina sai a inda aka kebe musu, amma mu ko atsakar da ji ne sai ka tsaya ka kallaci alkibla ka yi sallar ka, kuma yace an sanya masa kasa ta zama wurin tsarki, za ka yi tsarki da ita kamar yadda bayanai suka gabata a baya akan istijmari, sannan kuma zaka yi taimama da ita kamar yadda ake kawo bayani a yanzu haka.


6


Taimama matsayine na musamman da wannan al'umma ta kebantu da ita, Allah bai sanya taimama ga wata al'ummaba kafin wannan al'ummar domin yalwatawa ga wannan al'ummar. Ijima'i: Malamai duk sun yi ijima'i akan tabbatuwar taimama. Ita taimama tana tsayawane matsayin ruwa a shar'ance lokacin da rowan ya faskara, dukkan abinda kasan ba'a yi said a ruwa to ana yi da taimama, kamar sallah, dawafi, karatun Alkur'ani da dai sauransu. Taimama Tana Tsayawa Matsayin A Lokuta Kamar: Kenan anan za'a lissafo abubuwan da suke sawa a yi taimama, domin kada kabar sallah ta wuce maka kace ai baka sami ruwa bane wannan ba zai sa ka sami sassauci ba domin sabo da hakan aka shar'anta taimama, wadannan wurare sune kamar haka:


1. Rashin Ruwa: Kasan cewa suna cikin tafiya ko suna zaune a gida sai suka rasa ruwa sun nema iya yadda za su iya basu sami ruwan ba, to anan tunda sun nema basu samu ba ba za su bari lokaci ya wuce ba su ce sai sun je gida sai su gabatar da taimama su yi sallar su, ko da a cikin su akwai masu janaba, ko matan da al'adar su ta dauke. Kuma da zarar sun gabatar da wannan taimama to sun sauke wajibinsu ko


7


da an sami ruwa ba za su sakeba. Wato shi addinin musulunci gwargwadon yadda ka gane shi a yadda yake gwargwadon yadda yake da sauki a gareka. 2. Ruwan Ba Zai Isaba: Idan kuma a tare da ku akwai ruwan amma kuna da matukar mukata domin shi zaku sha da shi zaku yi girki ko shi za ku ba dabbobi ko shi kuke sawa a injin mota ta yadda idan ku ka yi alwala da shi ba zai ishe ku wadancan bukatuba, asalima za'a iya tagayyara, ko kuma ga ruwancan kuna hangowa to amma miyagun namun dajine a wurin ko kuma matattarar barayine wurin to anan fa hukunciku duka shine wadanda basu da ruwa, saboda haka wadanda suke dashi kadan domin bukatunsu sai su sha su yi taimama. 3. Cuta: Idan ga ruwan, amma ka ji tsoron cuta a jikinka ko kuma ciwon zai sami jinkirin warkewa, sai ka yi taimama. 4. Rashin Motsi: Idan ya zamana yana fama da rashin lafiya amma zai iya alwala sai dai ba zai iya motsawaba domin ya debo ruwan alwalar kuma bai sami wanda zai debo mai ruwanba ko babu wanda zai yi mishi alwalar kai tsaye sai ya yi taimama.


5. Sanyi: Idan yana matukar jin tsoron sanyi idan ya yi anfani da ruwa, kuma ga shi yana son yin alwala ko wankan tsarki ga shi bai sami


8


abinda zai dumama ruwanba to kai tsaye sai ya yi taimama. Wadannan bayanan suna nuna mana cewa rashin lafiya bata dauke sallah, domin koda ba zai iya alwalaba saboda tsoron sanyi ko jinkirin warkewa ko dai daya daga cikin abubuwan da aka ambata to sai ya yi taimama, abin takaici shine sai ka ga dazarar mutum bashi da lafiya to abu na farko da zai ajiye shine sallah, inda zaka je gai dashi kace ya yi sallah kuwa sai ka ga ana kallonka ana nuna maka halin da yake ciki kamar kai baka da tausayi, inda kuma zaka dan shafa masa dari ko dari biyu sai ya miko hannu, Allah Ya sawwake. Hakanan inda mutum za'a tsare shi, ba zai bada hanzarin ai lokacin da suke a tsare ba'a barinsu su yi alwala to ba sai ya yi taimamaba. Idan mutum yana da ciwo a gabban alwalarsa kuma ba zai cutuba idan ya shafa hannunsa akan bandejin ko karan dorin to sai ya yi alwalar idan ya zo wurin sai ya shafa kawai ba sai ya wankeba.


Idan galibin jiki ya zama ba lafiya kamar ya zama ba inda ya raje sai hannu ko kafa to anan kai tsaye sai ya wuce zuwa taimama. Shi bayani akan abinda ya shafi wanke wasu gabobi sannan ayi shafa akan wasu gabobi sabo


9


matsanancin rashin lafiya day a shafi gabban alwala ko taimama darasine mai zaman kansa, a littafin Iziyyah shine fasali na gwoma sha-daya, malamin ya ware fasalinne domin bayanin cututtuka da zasu sami gabban alwala, kuma ya kawo fasalinne bayan ya kammala bayani akan taimama a fasali na goma, Allah ya saka masa da alkhairi. Ya halatta ka yi taimama a duk inda yake doron kasa kamar inda yake; rairayi ko jangargari ko dutse ko kamfa ko kasar gishiri ko ta kanwa ko inda yake dusar-kankarace. Siffar Taimama: Yadda ake gabatar da taimama shine; zaka wara yatsun hannayanka biyu ne sai ka buga a kasa, sannan sai ya shafi fuskassa da cikin tafikan hannunsa, sai kuma ya shafi hannayansa zuwa wuyan hannu (Ku'i), zai yi ko kari ya tabbata ya game ko'ina na fuskarsa a lokacin da yake shafar kar ya manta da karkashin gemu da kuma hannayansa, idan yana da zobe sai ya cire domin shafar ta game ko ina, idan lokacin da ya shafo kasar kwai yayi ko kura sai ya karkade, ba'ace dole sai mutum ya sa kasa a fuskarsa ba. Idan kuma ya ga dama sai ya yi shafar sau biyu to tafarko sai ya shafi fuska da ita ta biyun kuma ya shafi hannuwa zuwa gwiwar hannu.


10


Za'a ko yi yadda ake taimamane da sauran ibadu a gaban malamai, karantawa anan kadai ba zata wadatarba, su kuma malamai su ji tsoron Allah su koyawa al'umma wadannan ayyuka a'aikace, sawa'un makarantun islamiyyune ko malaman da suke koyar da darussan addinin musulunci a cikin jami'o'i ko a kwalejojin ilimi, ko kuma malamai da suke karantarwa a cikin masallatai, kada ka taba jin dan ka karantar da baki kowa ya gane, a'a sai ka yi a aikace, kada ka manta sai da ma'aikin Allah ya koyawa sahabbansa wadannan ayyuka a aikace, ka ko san idan saurin ganewane sun fika sun fi daliban da kake koyarwa. Abundake Bata Taimama; Taimama tana baci da duk abinda yake bata alwala babbane ko karami, kamar tusa fitsari…. Fitar maniyyi, jinin al'ada, sannan kuma idan uzurin da ya sa aka yi taimama ya gushe to taimama ta gushe. Wanda ya rasa ruwa kuma ya rasa kasar da zai yi taimama akanta, ko kuma ya kai wani halin dab a zai iya taba ruwaba ko kasa to shi wannan zai yi sallar ne a yadda ya sami kansa, ba tare da alwala ko taimama ba, domin Allah bai dorawa rai sai abinda zata iya.


Duk wanda ya yi taimama domin ya yi sallar farillah to ya halatta ya yi nafila da wannan taimamar. Idan mutum ya yi taimama ya yi sallah da ita sai kuma lokacin wata sallar ya yi


11


kuma gashi ba abinda ya karya mishi taimama


to sai ya sake wata taimamar kafin ya yi sallar,


domin abin nufi anan sai ya sake neman ruwa


idan bai samu ba to sai ya yi taimama.


Idan mutum ana binshi wadansu salloli da


ya manta da su to ya samu ya sallacesu da


taimama guda.


Kammalawa: wannan kadan kenan daga cikin


abubuwan da suka shafi taimama da fatan sun


wadatar, kuma za'a koma ga malamai.


Rbutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu



Posts na kwanan nan

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A ...

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA

ANNABI ISAH AMINCIN A ...

ANNABI ISAH AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GARESHI A CIKIN ALKUR’ANI 1