بسم الله الرحمن الرحيم
الحمد لله رب العالمين، والصلاة والسلام على نبينا محمد وعلى آله وصحبه أجمعين.
Gabatarwa: Da sunan Allah mai yawan rahama mai yawan jinkai,
dukkan godiya ta tabbata a gareshi. Kuma tsira da amincin Allah su
kara tabbata ga Annabin mu Annabi Muhammad , da iyalanshi da
sahabbanshi baki daya.
Bayan haka, matashiyar da zan gabatar da jawabi akai ita ce:
Falalar Birnin Madinah. Wanda nake rokon Allah da dukkanin
sunayansa mafiya tsarki da siffofinsa mafiya kamala da ya yi mini
jagora, ya kuma albarkaci wannan zama na mu da ya karba mana
ayyukammu, amin.
Wannan jawabi zai tattaru ne akan:
- Gabatarwa.
- Shinfida.
- Falalar Birnin Madinah.
- Ladubban Zama A Birnin Madina.
- Falalar Sallah A Masallacin Ma'aikin Allah ().
- Abubuwan Yi A Birnin Madina.
- Ibadu.
- Wuraren Ziyara Da Takaitaccan Tarihinsu.
Wanda ya gabatar;
Aliyu Muhammad Sadisu,
Minna – Nigeria.
FALALAR BIRNIN MADINAH
2
(+2348064022965).
* Shinfida. Lalle Madina wacce take birnine na Ma'aikin Allah inda
kuma take masaukar wahayi, inda Mala’ika Jibrilu amintaccan Allah
ya dinga sassauka ga Manzon Allah , birnin da yake shi ne
matattarar imani, mahadar dukkanin wadanda suka yi hijira da
wadanda suka tarbesu, hedikwatar musulunci ta farko, wanda yake
anan ne aka kafa tutar jihadi, daga nan ne kuma aka fita domin a fitar
da mutane daga duhu zuwa ga haske, daga nan dinne duniya ta dau
haske baki daya, nanne kuma Allah Madaukakin sarki Ya zabawa
Manzan Shi ( ) ya zama wurin hijirarshi, a wannan birni kuma ya
rayu, kuma a nan ya koma ga Mahaliccin shi , anan kuma kabarinshi
yake, wanda yake babu wani mutum da zai iya tabbatar da inda
kabarin wani Annabi yake in banda kabarin shi ( ). Allah Ya kai mu
wannan birni na Ma'aikin shi lafiya, amin.
A yanzu haka za mu bi wadancan gabobin da suka gabata dayabayan-
daya Allah, Ya yi mana jagora, amin.
* Falalar Birnin Madina: Hakika wannan birni yana da dunbun daraja
da falala wadda take Allah kadai ya san iyakarsu, a yanzu haka ga
kadan daga cikin abinda ya tabbata daga Ma'aikin Allah () na falalar
wannan birni:
(1) Allah madaukakin sarki ya sanya shi Harami ne amintacce, kamar
yadda ya sanya birinin Makkah harami amintacce, Allah madaukakin
sarki yana cewa dangane da birnin Makkah:
FALALAR BIRNIN MADINAH
Ma'ana: ''Kuma suka ce: Har in muka bi gaskiyar dake tare da kai za'a
fitar da mu daga kasar mu. (Sai Allah ya ce): Yanzu shin ba mu
tabbatar musu da wani Harami (na musamman) wanda yake
amintacce ba, ana shigo da dukkan nau'ukan 'ya'yan itatuwa wanda
yake arziki ne daka gare mu?, sai dai mafi yawan su ba su sani ba''.
(Suratul-Kasas, aya ta:57). Allah madaukakin sarki ya fadi haka a
wurare da dama dan gane da Makkah.
Kuma Ma'aikin Allah () yana cewa dangane da Madinah:
Ma'ana: Lalle (Annabi) Ibrahim ya haramtar da Makkah, Kuma lalle ni
na haramtar da Madinah)). Wannan Hadisi Muslim ne ya ruwaito shi.
(2) Ma'aikin Allah () ya kira wannan birni da suna ''Taibah'', wato
daddadan abu, wato kenan birni ne mai dadi, mai albarka.
(3) Imani yana tattarewa ya koma wannan birni mai albarka,
Ma'aikin Allah () yana cewa:
Ma'ana: "Lalle Imani yana tattara zuwa madina kamar yadda
macijiya take tattara a raminta". Bukhari da Muslim suka ruwaito.
FALALAR BIRNIN MADINAH
4
(4) Birni ne da yake hadiye sauran birane. Ma'aikin Allah () ya siffanta ta da cewa garine da yake cinye garuruwa, kamar yadda yake cewa ''An umarceni –da yin hijira zuwa-wani gari da yake cinye garuruwa, suna kiranshi da: Yasriba-wato-Madina''. Bukhari da Muslim suka ruwaito.
Yasriba shi ne sunan Madina kafin isar Ma'aikin Allah (), da ya isa sai ya canza sunan garin, Allah madaukakin sarki yana cewa –A lokacin da yake fada mana maganar munafukai aranar Gwalalo:
Ma'ana: Kuma a lokacin da wata tawaga daga cikinsu (su munafukai suka ce) Ya ku mutanan Yasriba baku da matsaya ku koma….)
(5) Birnine da Allah ya zabe shi ya zama wurin hijirar manzonshi ().
(6) Yadda Ma'aikin Allah () ya nuna darajarta da girman sabawa Allah a cikinta, Ma'aikin Allah yana cewa:
Ma'ana: Madina Haramce daga (Dutsan) Air zuwa (Dutsan) Saur, duk wanda ya aikata barna a cikinta ko ya baiwa mabarnaci mafaka to tsinuwar Allah ta tabbata a kanshi da Mala'iku da mutane baki daya''. Bukhari da Muslim.
FALALAR BIRNIN MADINAH
5
(7) Addu'ar Albarka. Yana daga cikin falalar wannan birni addu'ar albarka da ya samu daga ma'aikin Allah (), ma'aikin Allah yana cewa:
Ma'ana ''Ya Allah ka sanya mana albarka a 'ya'yan itatuwan mu, ka sanya mana albarka a Madinar mu, ka sanya mana albarka a Sa'immu, kuma ka sanya mana albarka a mudun mu''. Muslim ne ya ruwaito.
(8) Annoba da Jujal basa shiga Madinah. Ma'aikin Allah () yana cewa ''Mala'iku ne akan ganuwowin madinah Annoba ba ta shigarta hakanan ma Jujal''. Bukhari da Muslim.
Wannan kadan kenan dangane da birnin Madinah banda abinda ya gabata tun a shinfida, sabo da lokaci.
* Ladubban Zama A Madinah: Lalle duk wanda Allah ya kaddari cewa yana cikin wadanda za su zauna kwana ko awanni a cikin wannan birni mai albarka to lalle ya sani cewa wannan ba karamar falala ba ce da Allah ya yi masa, sabo da haka sai ya godewa Allah akan wannan falalar, ya kuma kula da ladubban zama a wannan birni mai daraja kamar haka:
(1) Ka so wannan gari sabo da falalar da yake da ita, da son da Ma'aikin Allah () yake yi masa.
FALALAR BIRNIN MADINAH
6
Anas Ibnu Malik () yana cewa ''Lalle Ma'aikin Allah () ya kasance idan ya dawo daga tafiya sai ya hango gine-ginen Madinah sai ya gyara abin zamansa, in kuma yana kan dabbane sai ya motsa ta, saboda son da yake yi mata (wato madina).
(2) Ka kwadaitu da tsayuwa a kan al'amarin Allah, ka zama mai lizimtar biyayyah ga Allah da Manzan Allah (), kana mai tsananin kaucewa sabon Allah da bidi'oi domin wadannan al'amurra yin su a harami ba karamin zunubi ba ne.
(3) Lizimtar Sallah a cikin masallacin Ma'aikin Allah (), kamar yadda bayani zai zo.
(4) Ka zama kyakkyawan abin koyi, domin fa kana inda daga nanne hasken ya haskaka duniya baki daya.
(5) Ka tuna fa kana inda nanne masaukar wahayi, kuma inda Allah ya zabawa Manzan shi ya zame masa wurin hijira, kana inda yake nanne matattarar imani, kana inda nance makarantar da sahabban Ma'aikin Allah () su ka yi karatu, kada ka yi wani aiki da ya saba wa na makarantar su da malaminsu ().
(6) Kada kaga tsuntuwa ka dauka sai dai idan zaka yi cigiya ne.
*Falalar Sallah A Masallacin Ma'aikin Allah ().
Hakika sallah a wannan masallaci da wannan Annabi ya gina tana da matukar falala wacce bai kamata wanda ya sami kanshi a inda wannan masallaci yake ba ya yi sakaci, hadisai tabbatattu sun yi bayanin matsayin wannan masallaci da matsayin sallah a cikin shi.
FALALAR BIRNIN MADINAH
7
Na farko dai wannan masallaci yana cikin masallatai uku da ake nikar-gari domin ziyartar su, kamar yadda Ma'aikin Allah () yake cewa a hadisin Bukhari da Muslim.
Ma'ana: ''Ba'a nikar gari (don ziyara) sai masallatai uku; Masallaci mai alfarma (dake Makkah), da kuma wannan masallacin nawa, (dake birnin Madina) da kuma masallacin can nesa (wandake Kudus).Bukhari da Muslim.
Abinda Ya Shafi Falalar Sallah a wannan masallacin, Ma'aikin Allah () yana cewa;
Ma’ana:''Yin Sallah a cikin masallacin nan nawa ya fi salloli dubu a (masallacin) da ba shi ba, in banda masallacin harami (dake Makkah)''. Bukhari da Muslim.
Lalle wannan ba karamar garabasa ba ce da rahamar Allah ga bayinsa, kuma yana da kyau mu fahimci abubuwa kamar haka:
(a) Wannan ninkin ladan da abinda yafi dubu ba wai ya takaitu da farilla bane banda nafila, ko ko nafila banda farilla, a'a ya shafi duka, raka'a biyu ta farilla acikinsa ta fi raka'oi dubu na farilla a inda ba
FALALAR BIRNIN MADINAH
8
shiba in banda haramin Makkah, haka kuma raka'a biyu ta nafila sun fi raka'o'i dubu na nafila a inda ba nan ba.
(b) Wannan ladan bawai ya takaitu a iya inda masallacin yake a lokacin Ma'aikin Allah () kawai bane, ya shafi har fadada shin da aka yi ne.
(c) Sai dai duk wanda ya bi sallah a wajan masallaci yana da ladan jam'i, amma baida wancan ladan da aka anbata domin a waje ya yi sallah ba a ciki ba. Anan nake cewa irin sakacin da ake yi na a zauna a waje ayi ta fira ko aje a sayo kaya niki-niki jami'ai su hana a shiga masallaci da shi mutum ya yi sallah a waje bakaramar asara ba ce.
(d) A cikin masallacin akwai wani wuri wato Raudha, Ma'aikin Allah () a hadisin Bukhari da Muslim ya siffanta wurin da cewa Dausayi ne daga cikin dausayin aljanna. Kebance wannan wuri da irin wannan siffa lalle ya nuna falalarsa doruwa akan sauran wuraren.
* Abubuwan Yi A Birnin Madinah: Lalle ilalla a yanzu kasan takaitaccan bayani dangane da birnin Madinah falalar birnin da ladubban zama a birnin. To yanzu idan Allah ya sa ka isa wannan birni menene abinyi? kada ka manta tafiyarka ba tafiyar bude ido bace. Saboda haka babban abinda ya kaika shi ne ziyarar wannan masallaci da wannan Annabi cikamakin Annabawa farin jakada ya gina, da hannuwansa masu albarka, saboda haka kada hankalinka ya dauku daga barin salloli da karatun Alkur'ani da zikiri a cikin wannan masallaci, domin duk ibadar da ka gudanar a cikin wannan masallaci
FALALAR BIRNIN MADINAH
9
ladanta ya nin-ninka wacce aka yi a wajan wannan masallaci inbanda masallacin Ka'abah.
Sannan yanzu bari a kawo abinda ake yi a birnin Madinah:
Ibadu. Idan akace ibadu to jam'I ne na ibada, ita kuma ibada ''Gamamman suna ne da ya tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi na ayyuka ko na Magana na zahiri ko na badini''.
Yanzu munsan mecece ibada, kuma lura da ta'arifin ta lalle munsan tana da nau'i daban-daban, kadan daga ciki sune:
(1) Ikhlasi: Yi domin Allah, kada ka kuskura ka yi wani aiki a wannan birni mai tarin albarka wanda yake badon Allah ba, ko Allah bai saka ba, lalle mutum zai yi asara, ba'a lissafawa Allah ayyuka ko ayi mishi gori wadannan suna lalata ayyuka.
(2) Salloli A Kan Lokaci: Lalle wanda ya sami kanshi a wannan birni mai albarka kada ya kuskura ya sake da sallah, to yanzu wanda ya yi sake da sallah a inda aka saukar da sallar to a inane ba zai yi sake da ita ba?, musamman a cikin wannan masallaci maitarin albarka.
(3) Yawaita Karatun Alkur'ani: Anan ba wai sai ka haddace ba ko ka sauka a'a, iya inda ka iya ka nace da karanta shi, wannan ba karamin alkhairi ba ne.
(4) Yawaita Zikiri, Istighfari, Salatin Annabi (): Zikiran safe da na yamma, kada ka manta da su, saboda wadannan al'amura kabar kasarka, wurin aikinka, ka rufe shagonka kada mutum ya yi wasa da
FALALAR BIRNIN MADINAH
10
wadannan ayyuka musamman a cikin wannan masallaci da ake nunnunka ayyuka.
(5) Taimakon Juna: Lalle kada zuciyar mu ta yi nesa da taimakawa juna abune mai mahimmanci tabangaren guzuri shawara, nasiha ga juna, zaburar da juna, neman …''
* Wuraren Ziyara Da Takaitaccan Tarihinsu: Yana dakyau mu tsaya mu yi karatun ta-natsu a kan abinda ya shafi ziyara a Makkah ko a Madinah kada harkar ziyara ta sa ka rasa sallah a cikin wadannan masallatai wadanda suke sune jigo uban-tafiya. Yanzu za'a lissafo wuraren ziyara, kamar haka:
(1) Masallacin Ma'aikin Allah (). Wannan masallaci Ma'aikin Allah Ya sayi filin wurinne da kudinsa sannan ya aza harsashin gininshi da hannayen sa masu albarka, masallacin ya zama nanne wurin sallah nanne kuma makaranta inda yake karantarwa kuma a nanne yake alkalanci (), anan yake tarbar bakinshi.
Yadda Ake Ziyara a wannan masallaci shi ne, dazarar kun isa Madinah an kaiku masauki kowa ya ajiye kayansa, sai a nufi wannan masallaci mai albarka, idan aka je sai a fara gabatar da kafar dama lokacin shiga, sai kai addu'a ka ce:
Sannan sai ka yi sallah raka'a biyu, idan ka tarar ana farilla sai ka bi ta, ta wadatar maka, idan kuma ka isa an idar da sallah sai ka yi farillar.
FALALAR BIRNIN MADINAH
11
(2) Kabarin Ma'aikin Allah () Da manyan sahabbanshi biyu: wadannan kabarurruka suna cikin dakin Sayyida Aisha ne –Allah ya kara mata yarda- kamar yadda kowa ya sani ne, masallacin Ma'aikin Allah() daban yake, dakunan iyalanshi ma daban suke, wato gini ya rabasu, bayan da Allah ya karbi rayuwar wannan Annabi mai daraja a dakin Sayyida Aisha Allah ya kara mata yarda, sai aka yi masa kabari a dakin, haka kuma wadannan manyan sahabbai na shi guda biyu, wadanda zaka ji yana cewa na kasance ni da Abubakar da Umar, na yi kaza ni da Abubakar da Umar, Allah ya kara musu daukaka da karamci da kuma yarda, amin.
Yadda Ake Ziyara anan, mutum zai zo ta gaba sai ya fuskanci kabarin Ma'aikin Allah () sai ya ce:
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Ma'aikin Allah da rahamarsa da albarkarsa, Allah ya kara maka salati da aminci da kuma albarka, ya saka maka da mafificin abinda ya sakankawa wani Annabi dangane da al'ummarsa.
Mutum zai yi haka ne ba tare da daga murya ba, domin ba'a daga wa ma'aikin Allah murya yana da rai ko bayan ya rasu, Allah madaukakin sarki yana cewa:
FALALAR BIRNIN MADINAH
Sannan sai ya dan yi dama kadan sai ya ce:
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya Abubakar maigaskiya.
Sannan sai ya danyi dama kadan, sai ya ce:
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareka ya wannan gwarzo Umar.
Sai mutum ya yi musu adda'a domin sun yiwa wannan addini hidima da duk abinda za su iya, Allah ya kara musu daukaka.
(3) Makabartar Baki'a: ita wannan kushewa ba ta da nisa da masallacin Ma'aikin Allah () bai wuce taku kadan ba, ita ce babbar kushewar Madinah nan aka binne su; Nana Aisha da Nana Fatima da Sayyidina Usman da manya-manyan sahabban Ma'aikin Allah () Allah ya kara musu yarda, nan kuma aka binne su Imamu Malik, Allah ya kara musu yarda, amin.
Idan mutum ya je wannan makabarta zai ce ne :
FALALAR BIRNIN MADINAH
13
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareku ya mutanan wannan gida da suke muminai, mu ma in Allah ya yarda munanan za mu tarar da ku, Allah ya gafarta mana ya kuma gafarta muku.
(4) Shuhada'u Uhud: Kushewar shahidan Uhudu kushewace dake dab da dutsan Uhudu, anan ne aka yiwa sahabban Ma'aikin Allah wadanda suka yi shahada a wannan yaki mai cike da darussa janaza, wanda a cikinsu akwai Sayyidina Hamza wanda Allah yaba da labarinsa a cikin suratul Ali-Imrana.
Siffar yadda ake ziyara anan ita ce irin yadda aka yi a baki'a, wato idan kaje makabartar sai ka ce:
Ma'ana: Amincin Allah ya tabbata a gareku ya mutanan wannan gida da suke muminai, mu ma in Allah ya yarda munanan za mu tarar da ku, Allah ya gafarta mana ya kuma gafarta muku.
(5) Masallacin Kuba: Wannan shi ne masallacin da Ma'aikin Allah () ya gina kafin ya shiga birnin Madinah, domin ya yi kwanaki anan kafin ya shiga, anan ne kuma ya yi sallar juma'a ta farko a musulunci.
FALALAR BIRNIN MADINAH
14
Falalar Masallacin Kuba: wannan masallaci yana da falala ta musamman da Ma'aikin Allah () ya bayyana, Abdullahi dan Umar () ya ce: ''Ma'aikin Allah () ya kasance yana zuwa masallacin Kuba a duk ranar asabar wani lokacin ya tafi a kafa wani lokacin kuma ya hau abin hawa, sai ya yi sallah raka'a biyu''. Bukhari da Muslim.
Hakanan an karbo daga Sahal dan Hunaif () ya ce; Ma'aikin Allah () ya ce:
''Duk wanda ya yi tsarki daga gidanshi, sannan ya je (masallacin) Kuba ya yi sallah a cikin shi to ya kasance yana da ladan Umarah''.Ibnu Majah da wasu suka ruwaito.
Wadannan sune wuraran ziyara shar'antattu su biyar (5), biyu masallatai (Masallacin Ma'aikin Allah da masallacin Kuba), uku makabartu.
Amma akwai wasu wurare da mutane suke zuwa da sunan ziyara wadannan wurare sun kasu kashi biyu:
(1) Akwaishi A Tarihi: Kamar kiblatani, wannan a kwai shi a tarihi sai dai masallacin da ake kira kiblataini a yau shi ne wanda tarihin ya nuna?. To wannan malamai masana Sirah da Tarihi sun karawa juna sani akan haka.
(2) Babu Shi A Tarihi: A kwai wuraren da suke inda zaka karade littattafai dakyar ka ji duriyarsu domin babu su, an same su ne a zamanin wadansu dauloli da suka wuce.
FALALAR BIRNIN MADINAH
15
Nasiha:
Ni ina gabatar da nasiha ga 'yan-uwa kamar haka:
1. Riko da abinda ya kaika.
2. Kada ka dauki wannan tafiya a matsayin yawon bude ido.
3. Lizimtar Ibadah a wadannan masallatai.
4. Sanya lokacin ziyara ya kasance da safe, domin kada ka rasa sallah a masallacin Ma'aiki .
5. Kimanta lokaci.
6. Abokantaka da wanda yake da himma.
7. Barin shiga kasuwa sai an idar da sallar isha.
8. Daraja wannan wuri domin Allah ya daraja shi
9. Ba'a dawafi a Madinah domin a Ka'abah kawai ake dawafi, Allah madaukakin Sarki yana cewa: چ ڭ ڭ ۓ چ
وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم.
FALALAR BIRNIN MADINAH
16
Abubuwan dake ciki.
- Gabatarwa. ……………………………………………….……………… 2
- Shinfida. ………………………………………………………….……….. 3
- Falalar Birnin Madinah………………………………………….…… 3
- Ladubban Zama A Birnin Madina…………………………..….. 6
- Falalar Sallah A Masallacin Ma'aikin Allah ()……………. 7
- Abubuwan Yi A Birnin Madina……………………………….…… 9
- Ibadu...………………………………………………………………….….. 10
- Wuraren Ziyara Da Takaitaccan Tarihinsu………………….. 11
- Nasiha……………………………………………………………………….. 16
- Abubuwan dake ciki ………………………………………………..… 17
FALALAR BIRNIN MADINAH
17