Labarai

Karauniya A Cikin Salllah


Wani abun kuma da shari’a ta haramta mai kama da rashin


natsuwa a cikin sallah shi ne karauniya. Wato haxa gudu da susar katara.


Wannan kuwa ita ma wata matsala ce da ta zama ruwan dare ga musulmi


masallata kuma tabbas abin da ke kawo haka shi ne, rashin biyar umurnin


Allah sau da qafa, kamar inda ya ce:


Ma’ana:


Kuma ku tsayu kuna masu qanqan da kai ga Allah (2:238).


Ga kuma cewar da Allah ya yi


Ma’ana:


Haqiqa, Muminai sun samu babban rabo. Waxanda suke a


cikin sallarsu masu qanqan da kai ne (23:1-2).


Babu wani aiki da ke halasta a cikin sallah, koda na taimakon


sallar ne, matuqar shari’a bata aminta a yi shi ba. An tambayi Manzon


Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan matsayin share wurin sanya


goshi domin yin sujuda a lokacin da aka sunkuyo, sai ya ce, kada ayi


haka matuqar dai an riga an fara sallah. Idan kuwa har yin hakan ya zama


tilas to, kar a wuce ture tsakuwa kawai (Abu Dawuda: 1/581).


A kan haka ne malamai suka tafi a kan cewa, duk wani motsi nan


da can a cikin sallah, wanda ya wuce wuri, to yana vata sallah.


To, tunda kuwa har haka ne, me zai sa wasu mutane su yi biris da


wannan matsala? Har a same su suna tsaye gaban Allah kuma a lokaci


xaya suna duba agogo ko gyaran riga ko wasa da hanci ko su riqa


41


waiwaye wawaiye, suna rabon ido kamar maye ya yi baqo? Ba su gudun


Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya makantar da su, ko shexan ya vata masu


sallah?


Shiga Gaban Liman A Cikin Sallah Da Gangan


Wani abin kuma da shari’a ta haramta shi ne, shiga a gaban liman a


wajen aikata ayyukan sallah. Xan Adam akwai gaggawa. Shi ya sa


Maxaukakin Sarki ya ce:


Kuma mutum ya kasance mai gaggawa (17:11)


Gaggawa a idon shari’a abu ce maras kyau. Kamar yadda Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Tsanaki abu ne daga Allah. Amma


gaggawa aikin shexan ce (Baihaqi: 10/104). Sau da yawa idan mutum na


sallah cikin jama’a zai lura da wasu mutane a hagunsa da damansa suna


rigan liman wajen ruku’i ko sujuda ko kabbara, saboda tsananin gaggawa


da wutar ciki. Wasu mutane ma har sallama suke rigan liman.


Kuma ga dukkan alamu mutane ba su xauki wannan xabi’a a bakin


komai ba. Alhali kuwa saboda nauyinta ne Manzon Allah Sallallahu


Alaihi Wasallama ya yi garagaxi yana mai cewa: “Waxanda ke


xaukakowa da kansu kafin liman ba su gudun kada Allah Ya mayar da


kanunsu irin na jakai? (Muslim: 1/320-321).


Babu shakka irin tsanakin da ake nema ga wanda ke sallah yana da


yawa. Domin tun daga zuwa wurin sallar an neme shi da natsuwa da


tsanaki, to ina kuma bayan ya shiga cikin ta?


42


A vangare xaya kuma sai ka tsinkayi wasu masallatan suna jinkiri


sosai bayan liman ya yi wani aiki kafin su, su yi. A nasu tunani wannan


shi ne irin tsanakin da ake nema. Ba ko haka abin yake ba.


Malaman fiqihu sun faxi yadda ake koyi da liman a cikin sallah,


yadda ba za a shige makaxi da rawa ba, ba kuma za a zama kurar baya


ba. Suka ce Mamu zai fara abin da zai yi ne bayan liman ya gama furta


gavar qarshe ta kabbara. A lokacin ne aka halasta wa mamu motsawa. Ba


kafin haka ba, ko bayan haka da nisa. Haka sahabban Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama suka kasance, suna matuqar qoqarin ganin


ba su riga shi yin komai a sallah ba.


Wani sahabi da ake kira Bara’u xan Azibu Raliyallahu Anhu ya ce:


“A duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya


xaukako kansa daga ruku’i babu xaya daga cikinmu da zai karya qashin


bayansa don sujuda sai in Manzon Allah ya xora goshinsa a qasa. A


lokacin ne kowa zai sunkuya ya yo tasa sujudar (Muslim: 474).


Saboda irin tsananin muhimmancin da biyar liman sau da qafa a


cikin ayyukan sallah gaba xaya ke da shi. Ko bayan da Manzon Allah ya


samu jikinsa da nauyi saboda gabacin shekaru bai yi izni ga sahabbai da


su riga shi wajen aiwatar da kome a cikin sallah ba. Kai! Har ma jan


kunne ya yi masu a kan haka, da cewa: “Ina maku kashedi kada ganin


jikina ya fara nauyi, ya sa ku riga ni yin ruku’i ko sujada” (Baihaqi:


2/93).


Shi kuwa liman, shari’ah ta xora masa yin kabbarorinsa na sallah


kamar yadda sunnah ta tanada. Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya


riwaito a wani hadisi cewa: “Duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu


Alaihi Wasallama ya tashi yin sallah, ya kan yi kabbarar harama ne


bayan ya gama tsayuwa cik, ko duqawa. Idan kuma zai tafi sujuda yakan


43


sunkuya ne tare da furta kabbara. Haka zai yi wajen xaukakowa da kansa.


Haka kuma zai yi idan zai tafi sujuda ta biyu, da kuma xaukakowa daga


gare ta. Haka zai yi ta yi har ya qare sallar. Kuma yakan yi kabbara bayan


qare tahiya ta farko don miqewa tsaye (Bukhari, 785).


Wato a taqaice liman zai yi kabbara ne tare da aiki a cikin mafi


yawan ayyukan sallah su kuma mamu suna biye da shi kamar yadda


qa’ida ta tanada. Kuma ta haka ne kawai sallar jama’a zata karva sunanta.


Zuwa Masallaci Da Warin Albasa Ko Tafarnuwa


Wani abu kuma da shari’a ta haramta shi ne, zuwa masallaci bayan


mutum ya qare kalaci da albasa ko tafarnuwa. Wanda hakan za ta sa


warin jikinsa ya dami mutane. Alhali kuwa shari’a ta yi umurni da


tabbatar da cikakkiyar tsafta ga musulmi kafin ya tinkari masallaci,


kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:


Ma’ana:


Ya ku xiyan Adamu! Ku riqi qawarku a wurin ko wane


masallaci (7:31).


Kuma Jabir Raliyallahu Anhu na cewa: “Manzon Allah Sallallahu


Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya ci tafarnuwa ko albasa kada ya


matso mu, kada kuma ya zo masallacinmu. Ya tsayawarsa a gida


(Bukhari: 2/339).


A wata riwaya ta Muslimu kuma ya ce: “Manzon Allah Sallallahu


Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya ci albasa ko tafarnuwa ko


Kurrasi kada ya matso kusa da masallacinmu. Domin kuwa mala’iku na


qyamar duk abin da ‘yan Adam ke qyama (Muslim: 1/395).


44


Watarana kuma Halifa Umar xan khaxxabi ya yi wa mutane


huxubar juma’a, har yake cewa: “Ya ku mutane! Haqiqa kukan ci wasu


abubuwa biyu, da nake zaton tsirrai ne qazantacci, wato albasa da


tafarnuwa. Na lura a duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya ji mutum na warin xaya daga cikinsu a cikin masallaci


yakan umurce shi da ya fita waje, ya koma Baqi’a. Saboda haka daga yau


duk wanda ke son ya ci waxannan abubuwam to ya dafa su sosai har


warinsu ya vace (Muslimu: 1/396).


Wannan hukunci a wannan zamani namu ya haxa har da mutanen


da ke da xabi’ar wucewa masallaci daga wurin ayyukansu. Musamman


zaka tarar hamutansu da safar da ke qafarsu suna aman wani irin wari.


To, mafi munin su ma, ga tayar da hankali da takura masallata su ne


mashaya taba sigani, wadda ma ita a karan kanta haram ce. Su kuma sha


ta, sannan su nufato masallaci suna warinta, suna xaga hankalin mala’iku


da mutane.


ZINA


Kiyaye alfarmar yaxuwar xan Adamu a bayan qasa ta hanyar


samar da zuri’a mai nagartaccen asali, na xaya daga cikin manufofin


shari’ar musulunci. Saboda haka ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya


haramta zina, da duk wani abu da ke iya kai mutum ga faxawa cikinta.


Ya ce:


Ma’ana:


Kuma kada ku (ko) kusanci zina. Haqiqa, ta kasance alfasha


ce, kuma ta munana ga zama hanya (17:32).


45


Da wannan aya ne, da ire- irenta shari’ar musulunci ta haramta tare


da rufe ko wace irin kafa wadda ke iya zama sanadin aikata zina. Shari’ar


ta kuwa yi haka ne ta hanyar kwaxaitarwa ga sa hijabi da kau da kai daga


xiyan jinsin da bai halatta ba. Da kuma haramta kaxaita tsakanin jinsunan


biyu, da sauransu.


Saboda daqushe kaifin wannan mummunar xabi’a ne, da hana ta ci


gaba da yaxuwa shari’a ta tanadi hukuncin kisa ga mutumin da ya aikata


ta alhali yana da aure. Don ya xanxani azaba sakamakon abin da ya


aikata, kuma gaba xayan jikinsa ya ji xacin abun kamar yadda


annashawar da ake samu a sakamakon saduwa, ta game shi irin gamewar


da jini ke yi ga jiki. Shi kuwa wanda bai yi aure ba, shari’ar ta yanke


masa hukuncin bulala xari (100), a bainar jama’a ba tare da rufa- rufa ba.


Bayan haka kuma za’a yi masa xaurin shekara xaya ko ya bar garinsu na


tsawon wannan lokaci.


Wannan a duniya kenan. Idan kuma aka zo barzahu; cikin qabari,


mazinata na da wata uquba ta quntata masu makwanci, da gasa jikinsu da


wata wuta da za a hura a qarqashinsu bayan an yi ko sama ko qasa da


likkafaninsu. Haka za a yi ta dafa su, suna narkewa suna kumfa


gwargwadon zafin wutar, har sai kumfan ya yi kamar zai yi ambaliya ya


tunbutso zuwa waje, sai kuma wutar ta faxa. A kuma sake juyawa. Haka


za a yi ta jujjuya su har ranar tashin mutane zuwa farfajiyar alqiyama.


To babbar matsala ma duk ba ta fi mutum ya mayar da zina sana’a


ba. Ba shi da aiki sai yin ta har tsufa ya kama shi, mutuwa ta fara barbaxa


masa gishiri, amma ya kasa tuba, ya bari. Alhali kuma Allah Ya ba shi


ikon yin haka. Matsalar ita ce, da zarar mutuwa ta rutsa da shi a cikin irin


wannan hali, to, ba shi fa ba rahama da gafarar Allah. Saboda Abu


Hurairata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama


46


ya ce: “Akwai wasu mutane uku da Allah ba zai haxa baki da su ba ranar


qiyama, ko kallonsu kuma ba zai yi ba, balle, ko sanyi su ji.


Matsananciyar azaba ita ce sakamakon su. Na farkon su shi ne: Tsoho


Mazinaci. Na biyu: Maqaryacin shugaba. Na uku: Talaka mai girman kai


(Muslim: 1/102-103).


Wannan ke nan, Sannan kuma wani mugun abun kama shi ne, a


idon shari’ar musulunci, mafi sharri da rashin albarkar kuxi su ne


waxanda mace ta samu ta zina. Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba zai karvi


addu’o’in su ba a lokacin da yake buxe qofofin sama don karvar


addu’o’in bayinsa a tsakkiyar dare. Wannan garavasar ba da karuwai ba a


ciki, ba kuma da kwartayensu ba.


Talauci da fatara da wasu karuwai ke kafa hujja da shi, a matsayin


dalilinsu na wannan mugunyar sana’a ba hujja ba ne a wurin Maiduka.


Balle hakan ya zama wani lasisi na yi wa wata dokar Allah karan tsaye.


Bari ma batun ta Zina. Magabata cewa suka yi: “Da mace marar miji ta


shayar da wani jinjiri nono, gara an soke ta da wuqa”. To, ina ga ta kasa


al’aurarta a faifai a kasuwa?


Amma kuma tattare da haka, sai ga shi, abin takaici, abin kuka,


abin kuma tayar da tuta da sa riga da koda babu cuna, an wayi gari


shexan da ‘yan barandarsa sun buxe gaba xayan qofofin fitsara da batsa


da rashin arziqi a faxin duniya. Wanda hakan ta sawwaqe wa mutane


aikata ko wane irin savo, duk inda ka jefa idonka mata ne ke yawo kamar


tsirara akan tituna. Su kuwa maza sai zuba idonsu suke yi akansu. Inna


Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’una.


A yau ne zaka ga cuxanya tsakanin maza da mata bata zama abin


qyama ba. Mujallun batsa da fayafan Talabijin na tsiraici kuwa babu


kama hannun yaro. Hakan kuwa ta haxa har da masu sha’awar ziyartar


47


qasashen qetare. Saboda tsananin kai wa matuqa ma har kasuwanni ake


buxawa a yau, da ba su da wata safara sai karuwanci.


Irin waxannan abubuwa ne suka haifar da hauhawar keta mutunci


da alfarmar ‘yan Adamtaka ta hanyar yawaita haihuwar shegu da zubar


da cikkunan banza.


Ya Ubangiji! Muna roqonka ka zubo rahamarka gare mu, ka kare


mu daga faxawa cikin miyagun xabi’u. Muna roqon ka tsarkake


zukatanmu da al’aurunmu, ka yi katangar qarfe tsakaninmu da haramiyya


baki xaya.


LIWAXI


Wani abu kuma da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta amma


mutane suka yi biris da shi, shi ne liwaxi. Wato saduwar namiji da xan


uwansa namiji. Irin wannan baqar xabi’a ce dai ta haxa Allah Subhanahu


Wa Ta’ala da mutanen annabi Luxu Alaihis Salamu har Sarkin Ya labarta


wa duniya abin da ya faru, inda ya ce:


Ma’ana:


Kuma ka faxi labarin Luxu a lokacin da, ya ce wa


mutanensa: “Haqiqa ku, kuna je ma alfasha wadda ba wanda


ya riga ku yin ta a cikin talikai?” “Haqiqa ku, kuna je wa


maza, kuma ku yi fashin hanya, kuma ku aikata abin da ba


48


shi da kyau a wuraren zaman ku? Ba wata amsar da


mutanensa suka bayar sai dai suka ce: “Ka zo mana da


azabar Allah in har da gaske ka ke yi?” (29:28-28).


Saboda qazantar wannan xabi’a ta liwaxi da kasancewar ta wani


nau’i na dabbantaka ne, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya saukar da wasu


azabobi guda huxu, da bai tava saukarwa a game ba a kan waxannan


mutane na annabi Luxu Alaihis Salamu. Da farko sai da Allah Ya


makantar da su. Sannan ya yi wa garinsu juyin masa. Ya kuma bi shi da


ruwan duwatsun wuta da balbalin azaba, da tsawa mai tsanani.


A musulunci kuma duk wanda aka kama da aikata laifin liwaxi


hukuncinsa shi ne kisa da takobi. Wannan shi ne ra’ayin da ya fi amo a


tsakanin malamai. Shi ne kuma hukuncin da zai hau kan wanda aka yi


liwaxin da shi matuqar ba tilasta shi aka yi ba. Xan Abbas ya riwaito


cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda


kuka kama yana aikata irin aikin mutanen Luxu, to ku kashe shi, ku kuma


kashe wanda yake yi da shi (Ahmad: 1/300).


Ko shakka babu miyagun ciwarwata masu wuyar magani da suka


zama ruwan dare a wannan zamani namu musamman “qanjamau” sun


yaxu ne sanadiyyar wannan yamutsa hazo a duniyar halittu. Kuma


wannan na daxa fitowa fili da gwanintar shari’a da ta zartar da hukuncin


kisa ga wanda ya qazanta kansa da wannan bala’i don kada ya yaxa shi.


49


QIYO


(Hana Wa Miji Kai)


Qiyo; hana wa miji kai don biyan buqatar aure, sava wa Allah ne.


Amma kuma tattare da sanin haka, wasu mata sun sa qafa sun take


haramcin.


Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “idan mutum ya gayyaci matarsa


zuwa ga shimfixarsa ta qi, ya kwana cikin hushi da ita, Allah zai ci gaba


da la’antar ta har a wayi gari (Bukhari: 6/314).


Duk da irin wannan mummunan tanadi da Allah Subhanahu Wa


Ta’ala Ya yi wa mace mai yi wa mijinta qiyo, wasu matan kan qaurace


wa mazajensu, idan wata ‘yar tankiya ta shiga tsakaninsu. Wataqila har


mazan sun xan yi masu wani horo koda na so-kanki ne. Alhali kuwa irin


wannan mataki, kan iya haifar da aukawar miji cikin wata babbar


haramiya ko qarshe ma ya yi tunanin ya auri wata.


Don gudun faruwar xaya daga cikin waxannan abubuwa ko


dukansu wajibi ne mace ta yi gaggawar karva gayyatar mijinta idan ya


nemi wannan buqata, a matsayin biyayya ga umurnin Allah da


Manzonsa. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Idan mutum ya


gayyaci matarsa zuwa ga shimfixarsa, to ta karva masa, koda kuwa tana


kan raqumi ne (wato komai aikin da take yi) (Majma’uz Zawaidi: 2/181).


Shi kuwa miji wajibi ne ya yi matuqar kula da matarsa, ta hanyar


lelenta, musamman a lokacin da take fama da wata rashin lafiya ko take


da juna biyu. Haka zai qara yauqi da danqon soyayyar da ke tsakaninsu,


ta gane lalle yana ji da ita. Sadoba haka ba zata rena shi ba, balle ya ce ta


yi, ta ce ta qi.


50


NEMAN SAKI


Wata haramtacciyar xabi’a kuma a shari’a ita ce, mace ta nemi miji


ya sake ta, ba da wani qwaqqwaran dalili ba. Kamar idan mijin ya hana


mata wasu kuxi da ta nema daga gare shi.


Wasu matan sukan tayar da irin wannan fitina ne ta neman saki,


bayan wasu vata- gari daga cikin danginsu sun yi masu fanfo, ko wasu


miyagun maqwauta sun harzuqa su a kan lalle su qalubalanci mazan


nasu. Ai dole ne idan masara ta ji wuta ta yi daxo. A wasu lokutan ma har


naqalta masu ake yi abin da za su faxa sukan yi; ki ce masa; “In ka haihu


ka sake ni” Da zarar hakan ta faru, idan an yi rashin sa’a da wa’adin


auren ya qare sai ka ji an raba gari, Gida ya watse, yara su rinqa ragaita


rariya- rariya. Wanda kuma a mafi yawan lokuta ma’aurata kan sami


kansu cikin nadama idan haka ta faru bayan bakin alqalami ya riga ya


bushe. Saboda haka ne shari’a ta haramta irin wannan aiki.


Saubanu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk matar da ta nemi saki daga


mijinta ba tare da wani qwaqqwaran dalili ba, ko qanshin aljanna kam ba


zata ji ba. (Ahmad: 5/277).


Haka kuma Uqbatu xan Amiru Raliyallahu Anhu ya riwaito


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa; “Duk matar da ke


neman mijinta ya sake ta da wadda har abada bata gode wa miji,


munafukai ne (Xabarani: 17/339).


Amma idan akwai wani qwaqqwaran dalili kamar mijin ya kasance


baya sallah ko yana shan giya ko miyagun qwayoyi ko yana tilasta mata


aikata waxansu abubuwa na haramun. Ko yana musguna mata da zaluntar


ta, ta hanyar hana mata wasu haqqoqin nata na shariah. Kuma ya qi jin


51


shawarwarin, balle ya sassafta mata. A irin wannan hali babu laifi ga


matar don ta nemi a sake ta. Don ta tsira da mutuncinta da addininta.


ZIHARI


Zihari wata xabi’a ce da Larabawa kan yi tun zamanin Jahiliyyarsu


ta farko, don su cutar da matansu. Da zarar xayansu ya gaji da mace, sai


ya dube ta ya ce “Kin haramta gare ni yadda gadon bayan mahaifiyata ya


haramta gare ni”. Ko ya ce mata: “Kin haramta gare ni yadda ‘yar uwata


ta haramta gare ni”.


Wannan mugunyar al’ada na xaya daga cikin al’adun jahiliyyar


Larabawa da suka wanzu a cikin wannan al’umma har ila yaumina haza.


Shari’ah ta haramta wannan al’ada da duk wani abu mai kama da


ita, da ke cutar da mata ta ko wane hali. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na


cewa a cikin Alqur’ani:


Ma’ana:


Waxanda ke yin Zihari daga cikinsu game da


matansu, su matan nan ba uwayensu ba ne, uwayensu


kam su ne waxanda suka haife su. Suna faxar abin


qyama na magana da qarya. Kuma haqiqa Allah Mai


yafewa ne, Mai gafara (58:27).


Hukuncin duk wanda ya aikata irin wannan laifi a matsayin


kaffara, a shari’ar musulunci, shi ne irin kaffarar da wanda ya kashe wani


a kan kuskure, ko ya taki matarsa a cikin watan azumi da rana zai yi.


52


Kuma haramun ne ya kusanci matar sai bayan ya yi kaffara Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa:


Ma’ana:


Waxanda ke yin Zihari game da matansu, sa’annan su


koma wa abin da suka faxa, to akwai ‘yanta wuya a


gabanin su shafi juna. Wannan ana yi maku wa’azi da shi.


Kuma Allah mai qididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa.


To, wanda bai samu (Abin da zai ‘yanta wuyan da shi)


ba, sai (ya yi) azumin wata biyu jere a gabanin su shafi


juna, sa’annan wanda bai sami ikon yi ba, to, sai ya ciyar


da miskinai sittin. Wannan domin ku yi imani da Allah da


Manzonsa. Kuma waxannan hukunce-hukunce iyakokin


Allah ne. Kuma kafirai suna da azaba mai raxaxi (58:3-4).


JIMA’I A LOKACIN HAILA


Haramun ne a shari’ar musulunci mutum ya je wa matarsa a lokacin


da take al’ada. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:


53


Ma’ana:


Kuma suna tambayar ka game da haila. Ka ce: Ita cuta ce. Saboda


haka ku nisanci mata a lokacin da suke haila; Kuma kada ku ku


sance su sai sun yi tsarki” (2:222)


Kenab ba ya halatta namiji ya sadu da matarsa sai ta sami


xaukewar wannan jini, ta kuma yi wanka. Kamar yadda Allah


Subhanahu Wa Ta’ala ke cewa:


Ma’ana:


To, idan sun yi wanka sai ku je musu ta inda Allah Ya


umurce ku” (2:222).


Qazanta da haxarin da ke cikin sava wa wannan umurni na Allah


Subhanahu Wa Ta’ala na daxa fitowa fili idan muka dubi cewar da


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya sadu


da mace tana haila, ko ta baya gare ta, ko ya tafi wurin wani boka, to ya


kafirce wa abin da aka saukar wa Muhammadu” Sallallahu Alaihi


Wasallama (Tirmidhi: 1/243).


Da qaddara zata sa mutum ya afka wa iyalinsa cikin wannan hali; ba


da gangan ba cikin rashin sani babu wata kaffara da zai yi (sai dai ya yi ta


istigfari). Amma idan aikin da gangan ne ya yi, tare da ya san hakan


haramun ne, to, manyan malamai sun ce, kaffararsa ita ce yin sadaqa da


dinari xaya, ko rabinsa. Wasu kuma suka ce: a’a, zai yi dai sadaqa ne da


dinari xaya a yayin da ya sadu da iyalin nasa a farkon al’adar. Wato


54


lokacin da suka fi tsiyaya. Amma idan qarshen al’adar ne abin ya faru;


lokacin da zubar jinin ta sassafta, to sai ya yi sadaqa da rabin dinari.


A wannan zamani namu dinari xaya na daidai da gwal mai nauyin


25.4 gram. Saboda haka shi ne abin da za a bayar sadaqar, ko


kwatankwacinsa.


ZO WA MACE TA BAYA


An samu wasu mutane da qarancin imaninsu ya sa basu damuwa


da zo wa matansu ta baya. Wannan kuwa babban zunubi ne. Kuma abu


ne da shari'ah ta haramta. Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya la'anci mai yin sa. Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya


riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: "Allah


Ya la'anci duk wanda ke zo wa mace ta baya" (Ahmad: 2/479) Haka


kuma Manzon Allah ya ce: "Duk wanda ya sadu da mace tana haila, ko ta


bayanta, ko ya tafi wurin boka, to ya kafirce wa abin da aka saukar wa


Muhammadu" (Tirmidhi: 1/243)


Sai dai kuma Alhamdu lillahi, akwai waxansu nagartattun mata


masu hankali, da ke qin yarda da mazansu idan sun nemi su zo masu ta


baya.


Wani abu kuma kishiyar wannan shi ne, akwai wasu maza da kan


yiwa irin waxannan mata barazamar sakin su, a sakamakon haka. Wasu


kuma sukan yi iyakar qoqarinsu su gamsar da matan akan cewa, ai babu


wani laifi a cikin yin haka. Haka za su rinqa yi yau da gobe, har su ci


qarfin mata su yaudare su. Musamman idan aka yin rashin sa’a, matan


suka yi nauyi bakin yin fatawa ga malaman sunnah, kafin su bayar da kai


bori ya hau.


55


A qoqarin irin waxannan mazaje na gamsar da matansu a kan wannan


mugunyar tagara har kafa masu hujja sukan yi da ayar da ke cewa:


Ma’ana:


Matanku gonaki ne a gare ku, saboda haka ku je wa


gonakinku yadda kuka so" (2:223).


A tunanin waxannan mazaje, da na wasu vatattu irinsu, kalmar


"Anna shi’itun" a cikin wannan aya na nufin: "Ta inda duk kuka so”,


alhali kuwa ingantattar ma'anarta ita ce: "Yadda kuka so" kamar yadda ya


gabata.


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ya tabbatar da


haka, cewa, halas ne mutum ya zo wa matarsa ta yadda duk ya so;


ma’ana su yi gaba-da-gaba, ko ta ba shi baya, matuqar dai zai shiga ta ne,


ta inda ake haihuwa.


Wannan mugunyar xabi'a, qazantatta, ta shigo cikin al'ummar


musulumi ne, ta wasu da suka musulunta alhali ba su yi bankwana da


miyagun al’adunsu na jahiliyya ba, da suka gada daga iyaye da kakanni,


waxanda kuma a musulunci haramun ne. Kamata kuwa ya yi a ce sun


watsar da su, sun tuba ga Allah, tun shigowarsu a cikin musulunci.


Wani abin da ya kamata a lura da shi kuma shi ne, ba yadda za a yi


wannan baqar xabi'a ta halast, koda kuwa mtar da dmijin sun aminta da


ita. Domin babu wata yarjejeniya ko haxin baki da suka isa su mayar da


haram ta koma halas.


56


RASHIN ADALCI TSAKANIN MATAN AURE


Tabbatar da adalci tsakanin matan aure na xaya daga cikin


abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’alaYa yi umurni da su a cikin


littafinsa Mai tsarki (Alqur’ani) inda Ya ce:


Ma’ana:


Kuma ba za ku iya yin adalci (wajen so) a tsakanin mata ba,


ko da kun yi kwaxayin yin haka. Saboda haka kada ku


karkata, dukan karkata (ga wata a zahiri) har ku bar wata


kamar wadda aka rataye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma


kuka yi taqawa, to lalle ne Allah Ya kasance mai gafara, Mai


jinqai” (4:129).


Adalcin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke umurnin ko wane miji


da tabbatarwa tsakanin matansa, shi ne na daidaitawa a tsakaninsu a


wajen kwana da tufafi da xan abin vatarwa. Amma ba so da qauna ba.


Wannan kam xan Adamu ba ya da wani iko a cikin sa.


Tattare da wannan umurni da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi,


zaka taras wasu mazajen da ke auren mata da dama sun fi matuqar mayar


da hankali da kulawa da wata daga cikin su ta hanyar bata mafi yawan


lokaci, da abin aljihu, xayar kuma ko sauran sai abinda hali ya yi, su da


banza duk xaya. Wani lokacin ma har ta fi su. Irin wannan xabi’a kuwa


haramun ce a shari’ar musulunci kuma sakamakon duk mutumin da ke


haka shi ne abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa,


57


in ji Abu Hurairata cewa: “Duk wanda ke da mata biyu, ya kuma fi


karkata ga xaya zai zo ranar qiyama sashen jikinsa yana shanyayye”


(Abu Dawuda: 2/601).


KAXAITA DA MATAR DA BA MUHARRAMA BA


Har ko wane lokaci shexan, qoqarin yake ta ko wace hanya ya sa


mutum ya sava wa Ubangijinsa, ta hanyar sa shi aikata wani abin da


sarkin Ya haramta. Saboda wannan dalili ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala


ke jan kunnen bayinsa tare da yi masu kashedi, inda yake cewa:


Ma’ana:


Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin


shaixan. Kuma wanda ke bin hanyoyin shaixan, to haqiqa


shi yana umurni da yin alfasha, da abin qi” (24:21)


Wannan gargaxi da jan kunne da maxaukakin Sarki Ya yi wa


mutane musulmi, ko shakka babu abun kula da yin hattara ne, tare da


kaffa-kaffa. Domin kuwa Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ba shaixan


dama da ikon shiga cikin jikin mutum ya yawata kamar yadda jinni ke


yawo a cikin jikin.


Wannan dama ce shexan kan yi amfani da ita ya qawata masa wata


mata da ba halaliyar sa ba, har a qarshe ya kaxaita da ita, sai ya kai shi ya


baro.


Don kaucewa da tsere wa wannan matsala da haxari ne, shari’ar


musulunci ta xaukar wa al’amarin mataki tun da wuri. Ta kuwa yi haka


58


ne ta hanyar haramta wa mace da namiji kaxaita in babu igiyar aure da ta


haxa su. A kan haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke


cewa: “Babu wani mutum da zai kaxaita da matar da bata halatta gare shi


ba, face shaixan ne na ukunsu” (Turmizi: 3/474).


Haka kuma xan Umar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa wata rana


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya masu cewa: “Daga


yau kada wani daga cikinku ya sake shiga gidan wata mata da mijinta ba


ya nan sai fa idan yana tare da wani ko wasu” (Muslim: 4/1711).


A kan haka, haramun ne mutum ya kaxaita da matar da ba


muharramarsa ba, a cikin wani gida ko xaki ko mota. Matan xan uwansa


da na baransa duk sun shiga cikin wannan haramci. Haka kuma bai


kamata ba likita namiji ya kaxaita da mace maras lafiya, da sunan duba


ta. Wannan idan babu likitoci mata ke nan. Idan ko har akwai su, kuma


suka wadatar to, haramun ne likita namiji ya duba wata macein ba


muharramarsa ba.


Duk da irin haxarin da ke tattare da wannan matsala, mutane da


yawa a yau, sun yi ko-oho da wannan. Wasu na jin sun fi qarfin shexan


ne. Ko kuma suna da wasu dalilai na yin haka. Amma kuma a qarshe,


mafi yawansu na faxawa cikin abin da ake gudu. Wanda kan haifar da


gurvacewar nasabobin mutane, tare da haihuwar baqin haure.


GAMA HANNU DA MATA


Gaisuwa tsakanin maza da mata, ta hanyar yin musabaha hannu da


hannu, na xaya daga cikin mIyagun al’adun da mutane suka fifita a kan


dokokin Allah Subhanahu Wa Ta’ala a yau. Zaka sha matuqar mamaki, a


matsayinka na mai da’awa ko mai gargaxi da faxakarwa, idan ka yi


qoqarin ganar da mai yin irin wannan xabi’a cewa hakan bai halatta ba.


59


Domin zai buxi baki ne ba kunya ba tsoron Allah ya soki lamirinka, ya


kuma kalle ka xage a matsayin wanda kansa bai waye ba. Har kuma ya


zarge ka da qoqarin raba kan ‘yan’uwa. Don wai idan ka ce kada su riqa


gaisawa hannu da hannu, kamar kana cewa ne babu aminci a tsakaninsu.


Wannan irin mummunan tunani ya sa irin wannan xabi’a ta zama


kamar ruwan dare a cikin al’ummarmu. Amma idan aka dubi abin da


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa da idon basira, za a


fahimci irin haxarin da ke kewaye da mai wannan xabi’a. Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “Da za a kafa wa xayanku qusa


inci tara a maxiga, zai fi sauqi gare shi, (Bisa ga azabar da zai haxuwa da


ita) a kan ya tava jikin macen da bata halasta gare shi ba” (Xabarani:


25/212).


Ko shakka babu haxa hannu da mace, da sunan gaisuwa ko


rangwaxa irin wadda ‘yan boko da wayayyun mutane ke yi a kan tituna


ko cikin jami’o’i, wani nau’i ne na zina. Dalili kuwa shi ne, cewar da


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Ana iya yin zina da


idanu ko hannuwa ko qafafu. Uwa uba in an haxa al’aura” (Ahmad:


1/412).


In don kuwa tsarkin zuciya da qarfin imani da wasu ke gadara da


shi ba hujja ba ne. Domin babu wanda ya kai ga Manzon Allah Sallallahu


Alaihi Wasallama tsarkin zuciya da qarfin imani. Amma kuma ya tabbata


wa duniya cewa: “Ban tava gama hannu da mace ba” (Ahmad: 6/357).


Ya kuma ce: Sallallahu Alaihi Wasallama: “Ni ban tava hannu ko wace


mace” (Xabrani: 24/342). Haka kuma Sayyida Aisha Raliyallahu Anha ta


ce: “Wallahi hannun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava


shafar hannun wata mata wadda ba muharramarsa ba. Ko mubaya’ar da


mata suka yi masa da baki ya karve ta kawai” (Muslim: 3/489).


60


Da wannan ne kuma muke kira da babbar murya ga mazajen da ke


yi wa matansu barazanar sakinsu, idan sun qi musabaha da ‘yan’uwan su


maza, da cewa su ji tsoron Allah.


Haka kuma ya kamata jama’a su faxaka cewa, safar da wasu matan


ke amfani da ita, ko wasu qyallaye, duk ba su hana wannan xabi’a zama


haram.


SHAFA TURARE GA MATA LOKACIN FITA


Irin wannan xabi’a ta shafa turare ga mata lokacin da za su fita,


bayan sun cava ado, ta yawaita a waxannan kwanuka. Alhali kuwa


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gargaxi al’ummarsa da


babbar murya a kan haka, inda ya ce: “Duk macen da ta shafa turare


lokacin da zata fita ta shiga mutane, da nufin ta xauki hankalinsu da shi,


ta sunanta mazinaciya” (Ahmad: 4/418)


Amma duk da wannan gargaxi na Manzon Allah, wasu matan ba


su xauki wannan xabi’a bakin komai ba. Musamman idan za su fita tare


da direbobinsu ko na haya, ko za su kai yaransu makaranta, da sauransu.


Halas ne ga mace ta shafa duk kalar turaren da take sha’awa idan


tana zaune a cikin gidanta. Amma idan fita ta kama ta, shari’ah cewa ta yi


ta yi wanka irin na janaba. Ko da kuwa masallaci zata tafi. Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama cewa ya yi: “Duk matar da ta shafa turare


lokacin da zata fita zuwa masallaci, da niyyar ta xauki hankalin mutane


da shi, to Allah ba zai karvi sallarta ba. Har sai, ta yi wanka irin na


janaba” (Ahmad: 2/444).


A kan wannan ko shakka babu Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai


isar wa mutane a kan irin qanshin turaren Bakhur da wasu mata ke kashe


su da shi a lokacin bukukuwan aure da walima. Da kuma irin turaren


61


zamani da wasunsu ke baxawa, masu tsananin qarfi da tayar da hankali,


idan za su tafi kasuwanne, ko za su hau motocin sufuri, ko zasu halarci


waxansu wurare, inda za su haxu da maza, kamar masallattai, musamman


a dararen watan azumi.


Musulunci bai hana mace ta shafa turare ba, kamar yadda muka


faxa a baya kaxan. Amma sai ya ce wanda zata shafa ya kasance mai


launi ne amma ba mai tashin qamshi ba.


Muna roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sa mu tsira da


mutuncinmu. Kada kuma Ya kama mu da laifin da wawaye daga cikin


maza da matanmu suka aikata. Ya kuma xora mu a kan hanya


madaidaiciya.


TAFIYAR MACE BA TARE DA MUHARRAMI BA


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba ya halasta


ga macen da ta yi imani da Allah da Ranar qiyama ta yi tafiyar kwana


xaya ba tare da wani muharrami ba” (Muslim: 2/977).


Wannan hani da shari’ah ta yi, ta yi shi ne don kare martaba da


alfarmar mata. Saboda a duk lokacin da mace ta bar gari ita kaxai, raunin


xabi’arta da halittarta za su ba maza masu raunin imani damar qoqarin


taya ta. Suna kewayar ta suna lasar baki kamar maye ya ga kurwa.


Wanda a qarshe ko ba su sami damar sun zubar da mutuncinta ba, sun dai


takura ta.


Wannan haramci ya haxa har da matar da zata hau jirgin sama.


Koda kuwa wani zai raka ta zuwa filin jirgi, a can kuma inda zata sauka


wani zai tarbe ta. To wa ye zai zauna tare da ita, kafaxa da kafaxa a cikin


jirgin? Ko kuma ya zata yi idan wata matsala ta faru ga jirgin hakan


62


kuma ta tilasta karkata akalansa zuwa wani filin jirgi, ko jirgin ya


makara, ko… ko… ko…?


Matsaloli marasa daxin ji sun sha faruwa sanadiyyar irin wannan


sakaci da riqon sakainar kashi da ake yi wa mata.


Wani abin lura kuma shi ne, ba ko wane mutum ne, shari’a ta


lamunce ya zamo mata muharrami abokin tafiya ba, sai in ya kasance: 1)


Namiji, 2) Musulmi, 3) Mai qarfin kare ta kuma 4) Mai kamun kai.


Abu Sa’id al-Khudri ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya ce: ‘Kada wata mace da ta yi imani da Allah da Ranar


qarshe ta yi tafiyar da ta kai kwana uku ko fiye, ba tare da mahaifinta ko


xanta ko xan’uwanta ko wani muharraminta ba’” (Muslim: 2/977).


KALLON WANDA BA MUHARRAMI BA DA GANGAN


Kallon wanda ba Muharrami ba, namiji ko mace, ga ko wanensu


haramun ne, matuqar hakan ta kasance da ganganci. Allah Subhanahu


Wa Ta’ala Ya ce:


Ma’ana:


Ka ce wa muminai maza su kau da ganinsu, kuma su tsare


farjojinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Haqiqa,


Allah, mai qididdi gewa ne ga abin da suka sana’antawa


(24:30).


63


Kallon wanda ba muharrami ba ta irin wannan siga wani nau’i ne


na zina, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:


“Mugun kallo shi ne zinar idanu” (Bukhari: 11/26).


Shari’ar Musulunci bata hana kallo mai ma‘ana, a kan kuma wani


dalili na shari’ah ba. Kamar kallon da wani zai yi wa wata da nufin aure.


Ko wanda likita zai yi wa wata da nufin duba lafiyarta. Da sauransu.


Ba maza kawai ba. Haka su ma mata an haramta masu kallon


mazajen da ba su halasta gare su ba, irin wannan mugun kallo na da


gangan. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:


Ma’ana:


Kuma ka ce wa muminai mata su kau da ganinsu kuma su


tsare fajojinsu (24:3).


Haka kuma shari’ar musulunci ta haramta wa namiji ya kalli


xan’uwansa namiji, kallo irin na kwaxai, irin wanda wasu kanyi wa


hansari daga cikin matasa. Haka kuma haramun ne namiji ya dubi


al’aurar xan’uwansa namiji, ko mace ta kalli al’aurar ‘yar uwarta mace.


Ka ko ga duk abin da kallonsa ya haramta, ko shakka babu haramcin


tavinsa tabbatacce ne, koda kuwa akwai wani shamaki (kamar qyalle) a


tsakani.


Wata hanya kuma da shexan kan bi, ya iza mutane ga faxa wa


wannan haramiya ita ce, saka masu tunanin cewa, kallon hotunan mata a


cikin mujallu, da kallonsu a finafinai, bai shiga qarqashin wannan


haramcin ba. Saboda ba abu ne da ke faruwa a zahiri ba. Alhali kuwa irin


waxannan kallace-kallace na motsa qwazaba da tayar da hankali.


64


RASHIN KULA DA TARBIYYAR IYALI


Da gangan, a zamaninmu na yau, wasu magidanta ke yin biris da


tarbiyyar iyalinsu, musamman ‘ya’ya mata. Ta hanyar sa masu ido suna


cuxanya da mazajen da ba su halatta gare su ba. Suna cika masu kunnuwa


da zukata da maganganun soyayya. Abu mafi muni ma, wasu magidanta


har matansu na aure suke ba irin wannan dama. Ko kuma iyalin nasu su


kaxaita da wani ajanabi daga cikin direbobinsu ko masu yi masu hidima.


A yayin da wasu yaran ma, irin wannan sakaci na mahaifansu, kan ba su


cikakkar dammar fita ba da nagartaccen hijabi ba, ta yadda kowa zai iya


gane su. Wasu daga cikinsu kuma ma har mujallu da finafinan batsa suke


kawowa a gidajen babu ma ice masu kul.


Irin waxannan magidanta na fuskantar babban haxari gobe qiyama.


Saboda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Akwai


waxansu mutane uku da Allah Ya haramta wa aljanna: 1) Mashayin giya,


2) Maras biyayya ga uwaye, da 3) Wanda ba ya kula da tarbiyar iyalinsa”


(Ahmad: 2/69).


GURVATA ZURI’A


Gurvata zuri’a da yamutsa hazonta na xaya daga cikin abubuwan


da shari’ar musulunci ta haramta.


Bai halatta ba a musulunci, mutum ya danganta kansa ga wani a


matsayin mahaifi, savanin ubansa wanda ya haife shi da cikinsa. Ko ya yi


qaryar zama xan wata qabila wadda ba tasa ba.


Wasu mutane kan yi waxannan qaryace-qaryace ne, da guje wa


danginsu, na asali don kawai neman abin duniya. A qoqarin haka ma har


takardun sheda sukan nema don xaure wa qaryar tasu gindi a hukumance.


65


A yayin da kuma wasu uwaye su kan zama sanadiyyar ‘ya’yansu


su xauki irin wannan mataki, idan suka yi watsi da su tun suna qanana.


Su ma irin waxannan uwaye sun aikata haram. Domin irin wannan aiki


nasu ka iya gurvata zuri’a kwatakwata. Ta hanyar kawo tajin-tajin da


fitsara ta hanyoyi daban-daban. Kamar kasa gane wanda yake muharrami


ga wani. Wanda a sanadiyyar haka za a yi ta kabra da kai a cikin


auratayya da gado, da wasu matsaloli masu kama da wannan. Kuma ga


shi Sa’adu da Abubakar Raliyallahu Anhuma sun riwaito cewa, Manzon


Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya danganta kansa


ga wanda ba mahaifinsa ba da gangan, ba zai shiga aljanna ba” (Bukhari:


8/45).


Haka kuma haramun ne a shari’ah, a gurvata ma mutum asali, a


qashin kansa ko abin da ya haifa. Kamar abin da wasu mazaje ke yi, idan


suna son yi wa matansu ciwon baki, a yayin da wata ‘yar hayaniya ta


haxa su. Sai kawai su yi masu qazafin alfasha, ko su kore ‘ya’yansu daga


zama nasu. Alhali kuma ba su da wani qwaqqwaran dalili a kan haka.


Domin kuwa ko gadajensu na kwana na shedar cewa ‘ya’yan jininsu ne


ba inki ba wai.


A xaya vangaren kuma akwai wasu fanfararrun mata, dakarai da ke


gurvata zuri’ar musulmi ta hanyar cin amanar da ke tsakaninsu da


mazajen su, su yo ciki da wasu mazan daban su liqa masu ‘ya’yan.


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi gargaxi da hani


akan wannan xabi’a. Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito, cewa a


lokacin da ayar li’ani ta sauko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya ce: “Duk matar da ta kawo wani baqon haure a cikin wata


zuri’a, to ta yi bankwana da Allah. Shi kuma ya yi bankwana da ita.


Kuma ko labarin aljannarsa ba zata ji ba. Haka Shi ma duk namijin da ya


66


kore xansa daga zama nasa, shi ma Allah zai yi hushi da shi, Ya kuma


tona masa asiri kowa ya gama da ganinsa” (Abu Dauda: 2/695).


RIBA


Riba na xaya daga cikin manyan laifukan da Allah Subhanahu Wa


Ta’ala Ya haramta. Saboda ma girman sha'aninta ne, ta zama abu xaya


qwal, da Allah Ta'ala Ya shelanta yaqi da masu shi, a cikin alqur'ani.


Inda Yake cewa:


Ma’ana:


Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa kuma


ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance masu


imani. Idan ko ba ku aikata ba, to, ku sani akwai yaqi daga


Allah da Manzonsa” (2:278-279).


Ko shakka babu wannan gargaxi da Allah Maxaukakin Sarki Ya


yi, ya ishi ko wane mutum musulmi gane irin yadda Allah Ya xauki mai


cin riba. Kuma duk mai hankali zai iya gano mugun tasirin da Riba ke da


shi, a rayuwar xaixaiku da ta al’umma. Irin yadda wasu mutane suka


zama turayen bashi, ta yadda ko shexa sai da qyar suke yi, matsalolin


tattalin arziki, yawan rashin aikin yi, durqushewar kanfunna, da


ma’aikatu, duk waxannan na daga cikin ayubban da Riba ta haifar a


duniya.


Kai! Dubi irin yadda wasu mutane ba su da aikin yi kullum sai


fama da baqin cikin yadda za su yi su biya kuxin ruwan da ke yi masu


67


ambaliya na bankuna. Kuma aka wayi gari al’umma ta kasu gida biyu,


‘yan Bora da na Mowa, saboda irin yadda ‘yan tsirarun suka mallake


mafi yawan arziqin qasa. Kuma irin waxannan matsalolin kusan na daga


cikin nau’o’an yaqin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sha alwashin


gwabza wa da duk al’ummar da ke mu’amala da Riba. Domin kuwa


aiwatar da Riba ba zai yiwu ba, sai da sa hannun vangaroran mutane da


dama, har su talakawan.


Bayan wannan kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama


ya la’anci duk wanda ke da hannu ko masosa a cikin aiwatar da wannan


haramiya. Daxa ko jigon hulxar ne ko jekada ko xan dako. Jabir


Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya ce: “…wanda ke cin riba da wanda ke bayar da ita, da


wanda ke rubuta ta da wanda ke sheda duk uwarsu xaya ubansu xaya”


(Muslim: 3/1219).


A kan wannan nagana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ke nan, haramun ne ga mutum musulmi ya yi ko wane aiki,


matuqar dai yana da alaqa ta qud-da- qud da Riba. Wato kamar ya zama


magatakardan wasu kanfunna da ke ta’amuli na Riba. Ko ya zama mai


karva ko bayar da ita, ko kai saqonta ko gadinta. Wato a taqaice, haramun


ne mutum ya kasance yana da wata alaqa ta kai tsaye ko ta kaikaice da


Riba.


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi matuqar


bayyanawa al’ummarsa munin Riba. Yana cewa a wani hadisi da


Abdullahi xan Mas’udu Raliyallahu Anhu ya riwaito: “Akwai Riba nau’i


saba’in da uku. Mafi sauqi daga cikinsu ita ce wadda zunubinta yake


daidai da na wanda ya tara da mahaifiyarsa. Mafi girmanta kuma ita ce


68


wadda zunubinta yake daidai da na wanda ya keta alfarmar musulmi”


(Hakim: 2/37).


Haka kuma Abdullahi xan Hanzalata Raliyallahu Anhu ya riwaito


cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Cin dirhami


xaya ta hanyar Riba da gangan, ya fi zunubi a kan yin zina har sau talatin


da shida” (Ahmad: 5/225).


Wani kuma abin da ya kamata a lura da shi shine, haramcin


mu’amala da Riba bai taqaita tsakanin “Ni da kai” ba, kamar yadda wasu


mutane ke zato. A’a, haramcinta, haramci ne na game gari. Ya shafi


mutane baki xaya a matsayinsu na xaixaiku ko kamfuna ko ma’aikatu da


sauransu.


Manyan mutane kuma hamshaqan ‘yan kasuwa waxanda Riba ta


zama ajalinsu, ta fuskar ma’amalar kuxi da bankuna da manyan


kanfanoni, ba su da iyaka. Dole ne al’ amarin ya zama haka. Kuma ba


wani mamaki a ciki. Domin kwashe albarkar dukiya da lalata ta shi ne


bala’i mafi qaranci da Riba ke haifarwa. Kamar yadda Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk yadda dukiyar Riba ta yawaita


qarshenta rashi” (Hakim: 2/37).


Kuma wannan mummunan qarshe da dukiyar Riba zata yi, ba wai


sai an tara ta da yawa ba. Ko da ‘yar kaxan ce, to, ta haramta. Kuma


Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai tayar da duk wanda ke ma’amala da ita,


Ranar qiyama kamar wanda ya sha banjo, ko wanda shexan ya yi


sukuwar sallah a kansa.


Amma kuma a cikin rahamar Allah, duk irin wannan matsala da ke


tattare da Riba, Sarkin bai bar mu da ita ba. Sai da Ya faxa mana yadda


wanda ya faxa cikinta zai yi ya kuvuta. Ga abin da Yake cewa:


69


Ma’ana:


Kuma idan kun tuba, to, kuna da asalin dukiyoyinku


(uwar kuxi) ba zaku zalunta ba, kuma ba za a zaluntar ku


ba” (2:279).


Wannan shi ne tantagaryar adalci; Kuma a kan haka wajibi ne duk


musulmi ya nisanci wannan babban zunubi, ya kuma yi imani da cewa


mu’amalar haramun ce. Koda kuwa dole ta sa ya kai kuxin ajiya a wani


banki da ke irin wannan mu’amala ta Riba, to kada ya kuskura ya ji cewa


hakan ta halasta. Kuma idan ba don tsoron kuxin nasa su halaka ta hanyar


sacewa ko wata qaddara ba, to bai halatta ya kai ajiya a irin waxannan


bankuna ba. Kuma lalle ne idan haka ta faru ya xauki kansa matsayin


wanda tsananin yunwa ya sa cin naman mushe, ko wani laifi fiye da shi,


kuma a lokaci xaya wajibi ne a tsare istigfari tare da qoqarin neman wata


hanya ta halas da zai adana dukiyarsa ta ita. Yin hakan wajibi ne a kansa


matuqar yana da iko.


Wani abun kuma shi ne da Allah zai sa bankin ya kasa saka masa


nasa kaso na Ribar a cikin uwar kuxinsa, to ba ya halatta gare shi ya bi


kadinta balle ya qalubalance su. Idan kuma ya tarar cewa sun saka masa


baki alaikum, to lalle ne ya gaggauta sanin yadda ya yi da su. Ba ya


halatta ya yi sadaqa da su. Ko ya yi kuma, Allah ba zai karva ba. Don shi


mai tsarki ne, ba Ya kuma karvar abinda ba mai tsarki ba. Haka kuma, ba


ya kamata ya yi amfani da kuxin ruwan nan ya ciyar da iyalinsa, ko ya


shayar da su, ko ya yi masu sutura, ko ya saya masu abun hawa ko wani


sabon gida. Haka kuma ba ya halatta ya cika wani alkawali da ya yi da


70


kuxin, ga matarsa ko xansa ko mahaifiyarsa, ko ya yi zakka ko ya biya


haraji da su, ko ya kare kansa da su a kotu.


A taqaice dai, ba ya halasta gare shi shi, ya yi amfani da waxannan


kuxi ta ko wane hali. Magani shi ne, ya xaure hannunsa da dutse daga


gare su, don ya tsira daga azabar Allah.


ALGUSSU


Algussu a cikin sha’anin saye da sayarwa na xaya daga cikin


abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta, kuma Manzon


Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar, amma mutane da yawa a


yau, sun yi biris da haramcin.


Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi


kicivis da wani xan sakai ya baje hajarsa, ta kayan abinci. Saboda


tabbatar da nagarta da xauke haqqin shugabanci, sai ya cusa hannunsa


cikin wani kwando, sai ya ji sanyin ruwa a qasa. Nan take, ya tambayi


mai kayan: “Ya aka yi haka? Shi kuma ya karva masa da cewa: “Ruwan


sama ne ya dake shi jiya Ya Manzon Allah”. Daga nan sai Manzon ya ce:


“To me ya hana ka zuba mai sanyin a sama don mutane su zama ala


basiratin game da shi? Ka sani duk wanda ke yaudarar jama’a ba ya tare


da mu”(Muslim: 1/99)


Kinin irin wannan algussu na faruwa a wannan zamani namu.


Wasu ‘yan kasuwa da tsoron Allah bai ishe su ba kan yi qaru- qaru su


voye aibin da kayan sayarwarsu ke da shi, ta hanyar canza masa takarda


ko su saka kayan da ba su da kyau qasan akwati su xora na gari a sama.


Bayan sun yi wa na qasan asin-da-asin da kaloli da zanen da, da an kalle


su sai a xauka na qwarai ne. Wasu kuma sukan shaqe kukan wasu


injinoni, ta yadda aibinsu ba zai fito zahiri ga mai saye ba. Sai ya


71


kinkimo ya kawo gida, sa’annan ya gane kurensa. A yayin da wasu ‘yan


kasuwa kuma ke canza ajullan kayan sayarwarsu na haqiqa (Expiring


date). Ko su ce wa mai saye su ba a jarraba kayansu kafin a saye. Kamar


masu sayar da motoci da wasu na’urori, sai dai kawai a biya a xauka.


Duk abin da mai saye ya taras na aibi a cikinsu daga baya, wai ruwansu


Irin waxannan halaye da xabi’u gaba xaya haramun ne. Domin


kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Musulmi duk


xan’uwan musulmi ne. Saboda haka ba ya halatta musulmi ya sayar wa


xan’uwansa musulmi da wani abu mai aibi ba tare da ya gaya masa ba”


(Ibnu Majah: 2/752)


Wasu ‘yan kasuwar kuma suna tunanin cewa idan suka siffanta wa


mai saye kayan nasu, siffantawa ta zahiri kuma jumlace kamar wanin ya


ce: Ina da dalar tama ta sayarwa, in kana saye”. Suna jin idan suka yi


haka sun gama komai. Alhali kuma irin wannan siffantawa ba ta


wadatarwa. Kuma duk cinikin da aka qulla a kan irin haka to xebabben


albarkar ciniki ne. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya ce: “Mutum biyu masu ciniki na da cikakkar damar yi ko


fasawa matuqar ba su rabu ba. Idan gaba xayansu sun yi gaskiya cikin


cinikin sun kuma bayyana duk abin da kayan ya qunsa (na aibi) to, Allah


zai sa wa cinikin albarka. Idan kuwa suka yi qarya suka kuma yi algussu,


Allah zai xebe masa albarka” (Bukhari: 4/328).


KERI


Wata mummunar xabi’a kuma da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya


haramta ita ce tayar da farashin kaya ba kuma da nufin saye ba, sai dai


kawai don a yaudari wanda ya zo saye, ya saye da mugunyar tsada.


72


Yin haka haramun ne. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama


na cewa: “kar ku tayar da farashi da gangan” (Bukhari: 10/484).


Qarawa ko tayar da farashi da gangan, wani nau’i ne na yaudara.


Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Qarshen


yaudara da cuta shi ne shiga wuta” (Silsilah: 1057).


Dillalai a gidajen sayar da motoci kan sami kuxaxen haram masu


yawa ta wannan hanya. Sukan haxa baki ne da su wasu su xora wa


motocin toliya, farashinsu ya xaga sama daidai yadda nasu kaso zai fito.


Shi kuwa mai saye, ko oho. Ko kuma su haxa baki su kayar da farashin


kayan nan take, don su yaudari wanda ya kawo nasa don sayar wa. Wani


lokacin ma har shigar burtu suke yi su taho da sigar masu saye, su yi


barazana kamar zasu saye, alhalin baqon ne ake son cuta. Wannan


haramun ne.


CINIKI BAYAN KIRAN SALLAR JUMA’A


Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:


Ma’ana:


Ya ku waxanda suka kayi imani! Idan an yi kiran salla ranar


Juma’a, sai ku tafi zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar


ciniki. Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance


kuna sani” (62:9)


Xabi’a ce da ta zama ruwan dare a yau ka ga mutane na ta


harkokinsu na saye da sayarwa a cikin shaguna da kan tebura, alhali an yi


73


kiran sallar Juma’a (Kira na biyu). Babban abin ban takaiki ma, wasu


baki da hanci suke da masallatan. Duk wanda ke da hannu a cikin irin


wannan ciniki, yana da nashi kamisho na zunubi, ko da kuwa asawaki ne


ake saya a lokacin. Tabxijan! An ko shiga uku ke nan.


A fahimta mafi nagarta, a tsakanin malamai, duk cinikin da aka


qulla a irin wannan lokaci vatacce ne. Abin da wasu masu gidajen sayar


da abinci ke yi, da masu gidajen burodi da kanfunna, na tilasta ma


ma’aikatansu aiki a daidai lokacin sallar Juma’a haramun ne. kuma kuxin


da suke samo na aikin daidai wannan lokaci ba zai yi albarka ba; zai


zame masu hasara.


Su kuma ma’aikatan nasu wajibi ne, su san cewa bin koyarwar


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sau da qafa a cikin ko wane


aiki shi ne wajibi. Kamar yadda ya ce Sallallahu Alaihi Wasallama


“Babu xa’a ga wani abokin halitta a cikin sava wa Mahalicci” (Ahmad:


1/129).


CACA


Caca na xaya daga cikin manyan laifukan da Allah Subhanahu Wa


Ta’ala Ya haramta, in da Ya ce:


Ma’ana:


Ya ku waxanda suka yi imani! Haqiqa giya da caca reful da


kiban quri’a duk qazanta ne daga cikin aikin shaixan. Sai ku


nisance su, don ku ci nasara (5:90).


74


Caca wata daxaxxar al’ada ce ta jahiliyya. Hanya mafi shahara ta


gudanar da ita a wancan lokaci ita ce: Mutum goma za su haxa kuxi daidai


wa dai-da su sayi raqumi. Qarshe kuma a saka shi caca tsakaninsu, ta


hanyar zana wasu kibau. A inda mutane bakwai daga cikinsu ka iya tashi


da raqumin. Ko su kuma da kaso daban-daban. Sauran ukun kuma su


tashi tsula.


A zamanin nan namu na yau kuma caca na da salailai da dama.


Kaxan daga cikinsu sun haxa da:


(a) Reful: Wani nau’i ne na caca da mutane ke zuba kuxi su


sayi lambobi. Waxanda za a rubuta a can voye, cewa


lamba kaza ita ce matsayin ta xaya, wata kuma ta biyu.


Haka haka, har qarshe.


Irin wannan caca haramun ce, ko da kuwa za a yi sadaqa da kuxin


da aka ciwo cacar ne.


(b) Sayen wani abu da ya qunshi abinda ba a sani ba. Ko


sayen wata lamba don ta zo da cikin wani abu na amfani.


(c) Inshora: Wannan kuma wani nau’i ne na cacar zamani.


Wato kauce wa qaddara. A kan kuma yi ta ne wa:


Rayuwa ko abun hawa ko wasu kayayyaki. Ko kuma a yi


ta don tsere wa hasarar gobara ko sata. Kuma akwai ta


falan xaya, akwai kuma mai fal uku, da makamantansu.


Kai qarewa da qarau ma har muryar wasu mawaqa ake yi wa


inshora a yanzu. Kowa ya daxe a duniya sai ya ga daxai!


A wannan zamani namu har qungiyoyi ke akwai waxanda ba su da


aiki sai caca. A mazaunansu (Clubs) har tebura ke akwai na musamman


waxanda ake wa laqabi da “Korayen Tebura” da babu mai zama kan su


sai kartagai da ‘yan korensu. Wani nau’in kuma na cacar zamani shi ne


75


wadda ake qullawa a kan dawakin sukuwa da wasu wasanni. Ko a kan


injinun niqe ababan marmari a gidajen shaqatawa na yara. Haka kuma


wasu malamai sun saka sauran gasanni na zamani a wannan layi.


SATA


Sata haramun ce. Ga kuma hukuncin da Allah Subhanahu Wa


Ta’ala Ya yanke wa duk wanda aka kama da laifin yin ta, namiji ne ko


mace:


Ma’ana:


Kuma Varawo da Varauniya, sai ku yanke hannayensu, bisa


sakamako ga abinda suka tsirfata, a matsayin azaba daga


Allah. Kuma Allah Mabuwayi ne. Mai hikima (5:38).


Mafi munin sata a idon shari’a ita ce, satar kayan Mahajjata da


masu aikin Umrah, a mafi tsarkin wuri a bayan qasa, kuma kusa ga Xakin


Allah mai alfarma. Duk wanda zai yi sata a irin wannan wuri, to, ta


babbata cewa bai san girman Allah da dokokinsa da birnin Makka ba.


A wani rahoto da aka bayar da wata sallah ta kisfewar wata da


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya jagoranta, an ce an ga ya


xan ja da baya. Ya kuma yi bayanin cewa: “Da kuka ga na xan ja da


baya, wuta ce aka kusantto da ita. Don kada zafinta ya kai gare ni. Kuma


a daidai wannan lokaci na hangi wani mutum da sanda mai gwafa, ana


jan hanjin cikinsa qasa a cikin wutar. Laifinsa shi ne satar kayan


Mahajjata da yakan yi da sandar tasa. Idan sun ganshi sai ya ce a’a


76


gwafar ce ta sagale kayan shi bai sani ba. Idan kuma ba a faxaka da shi


ba, satar ta tabbata kenan”.


Wata satar kuma mai muni a idon shari’a ita ce, satar kuxin


Gwamnati. Wadda wasu masu yin ta kan kafa hujja da cewa “Ai ba gare


mu farau ba”. Babban haxarin dake cikin irin wannan sata, wanda kuma


masu yinta suka kasa ganowa shi ne, suna yi wa gaba xayan jama’a sata


ne Domin dukiyar gwamnati ta kowa ce. Kuma ba wannan ba, ko dukiyar


kafirai da waxansu musulmi ke sata wai don masu itan na kafirai,


haramun ne, balle ta musulmi tsintsa. Kafiran kawai da aka halasta mana


cin dukiyarsu ta ko wane hali su ne waxanda muke cikin yaqi da su; Ka


ga waxanda ba haka ba, a matsayin xaixaiku ko cikin taron Jama’a sun


tsira.


Wani nau’in satar kuma da shari’ah ta haramta shi ne “Tsame”.


Wasu varayi kan shiga gidajen wasu mutane a matsayin masu ziyara.


Amma a qarshe su tsame su. A yayin da wani lokacin ko, masu gidajen


ne za su tsame baqin. Wasu kuma mata ne da kan shiga shagunan mutane


su sace wasu abubuwa, su turo cikin aljihunsu ko wani cikin jikunna.


Wasu mazan ma sukan yi haka. An ma samu wasu mutane a yau da ke jin


irin waxannan ‘yan sace-sace qanana ba komai ba ne. Alhali kuwa


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ya la’anci


Varawon da zai saci qwai ko igiya a yanke masa hannu” (Bukhari:12/81).


Wajibi ne ga duk wanda ya saci wani abu, farko ya tuba ga Allah.


Sannan ya mayar wa mai abu da abunsa kai tsaye ko a kaikaice, ta hanyar


wani. Koda ko a asirce. Idan kuwa har ya yi iyakar qoqarinsa ya ka sa


gane mai shi, ko magadansa, to sai ya yi sadaqa da shi, da niyyar ladar ta


je ga mai shi.


77


CIN HANCI


Bayarwa da Karvar Cin Hanci haramun ne a shari’ar musulunci.


Kamar mutum ya ba alqali wani abu ko da na magana mai daxi ne, don


ya kawar da kansa daga wata tabbatattar gaskiya ko ya xaure wa wata


qarya gindi, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta irin haka don tana


qarewa ne ga zaluntar mai gaskiya. Tana kuma watsa varna a cikin


al’umma. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:


Ma’ana:


Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakanin ku ba da gaskiya


ba, kuma don ku bayar da cin hanci ga mahukunta sai ku ci


wani yanki na dukiyoyin mutane da zunubi alhali kuna


sane” (2:188).


Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a


wani hadisi da Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito: “Allah Ya


la’anci duk wanda ya bayar da hanci da wanda ya karve shi a kan wata


shari’ah” (Ahmad: /307).


Amma kuma yana da matuqar muhimmanci a nan, a lura cewa,


abin duk da mutum zai bayar don qwato wani haqqi nasa da ke son


salwanta, ko ya tunkuxe wani zalunci da ake son yi masa qahran, ba


hanci ba ne, matuqar dai babu wata hanya da zai iya tabbatar da haqqinsa


sai ta haka.


78


Wani abin ban takaici ma duk, bai fi irin yadda mutane a yau suka


yi biris da wannan haramci ba. Har aka wayi gari hanci ya zama wata


babbar hanya ga waxansu mutane, ta samun kuxin shiga fiye da


albashinsu na yau da kullun. Kai! Ta kai ma wasu kanfunna, kasafinsu na


shekara- shekara ba zai kammala ba sai sun ware na hanci. Don waxansu


hulxoxin ko xanbansu ba za a xiga ba sai an lanqwashe hancin aljihu.


Wasu kuwa ko an fara qarewar ba zata yiwu ba da hanci ba a hannu.


Yawaitar sabgar bayar da hanci da karvarsa na haifar da matsaloli


da dama, musamman ga masu xan qarfi. A yayin da dokoki da dama ba


sa kai labari saboda shi. Lalacewar tarbiyya da rashin ta, duk kan haifu ne


sanadiyyar cin hanci. Sai ka ga tsakanin maigida da ma’aikatansa babu


girma babu girmamawa. Saboda ba za a tsaya a yi wa duk wanda yaqi


bayar da hanci aiki na gari ba. Qarshe sai an vata masa lokaci, kuma aikin


da zai samu ya zamo rubabe- rubabe.


Yau da zaka zo a wata ma’aikata makare, zaka iya rigan wanda ya


yo sammako samun biyan buqata, matuqar zaka bayar da na goro (hanci).


Da yawa zaka taras a kamfani, kuxaxen da ya kamata su tafi aljihun mai


shi, sun qare a hannun dillalansa na ciki da na waje. Ko shakka babu


la’akari da waxannan matsaloli da musibu da cin hanci ke haifarwa, na


hana mutum mamakin abin da ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi


Wasallama ya roqi Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya nisanta duk wanda


ke da hannu a cikin wata ma’amala ta cin hanci daga rahamarsa.


Abudullahi xan Umar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah


Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “La’anar Allah ta tabbata a kan duk


wanda ya bayar da hanci ko ya karve shi” (Ibnu Majah: 2313).


79


QWACEN FILI


Idan ba sa’a aka yi tsoron Allah ya cika zukatan masu iko da qarfi


da basira ba, sai hakan ta zama wata masifa gare su. Domin kuwa za su


qarasa ne ga zaluntar wasu mutane, ta hanyar qwace masu ababen


mallakarsu kamar Fili.


Hukuncin da shari’ar musulunci kuwa ta tanadar wa mai irin


wannan xabi’a mai tsanani ne. Domin Abdullahi xan Umar ya riwaito


cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “Duk wanda ya


qwaci filin da ba halaliyarsa ba Allah zai sa qasa ta rusga da shi har qasa


ta bakwai a ranar alqiyama” (Bukhari: 5/103).


Haka kuma Ya’ala xan Murrata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa,


Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya qwaci


filin wata qasa, koda kamu xaya ne zulman. To, Allah zai tilasta masa


gino faxinta har qasa ta bakwai, ya kuma xauke ta a kai har a qare hisabi


ranar qiyama. (Amma a cikin Xabari cewa aka yi, za a tilasta masa


dawowa da ita)” (Xabarani: 22/270).


Haka kuma wannan haramci ya haxa har da baje iyakar gonaki ko


filaye, tare da canza masu bigire, don handama da babakere da nakkasa


haqqin makwabci. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa:


“La’anar Allah ta tabbata kan duk wanda ya canza iyakar fili” (Muslimu:


13/141).


CI DA CETO


Ko Shakka babu samun wani muqami a cikin mutane wata baiwa


ce ta Allah Subhanahu Wa Ta’ala da yake yi wa wanda ya so daga cikin


bayinsa. Musamman idan wanda aka yi wa xin ya gode.


Babbar hanyar da irin wannan bawa ke iya bi don tabbatar da


godiyarsa ga Allah a irin wannan hauji, shi ne hanyar amfanar da sauran



 



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA