ALAKA TSAKANIN AHLUL - BAITI
DA SAHABBAI
Gabatarwar mai fassara:
A ranar 29 ga watan Ramadan na wannan shekarar ne
ta 1423B.H. na hadu da wani dattijo a cikin babban
masallacin Makka mai alfarma, kuma sauraron karatu ne
ya hada mu da shi. Wannan dattijon dai daga baya na
fahimci cewa, shi ma malami ne kuma alKali a wata
babbar kotun shari`a ta garin Kadif a Kasar Saudiyyah.
Saduwarmu da wannan malami ke da wuya sai na
fahimci irin kishin da ya ke da shi game da yada addinin
musulunci da gusar da yana daga aKidunsa. Nan take dai
wannan bawan Allah ya fito da wani dan littafi Karami ya
ba ni kyautarsa. A lokacin da na koma masaukina na samu
natsuwa na karanta wannan littafi, sai na taras littafi ne mai
matuKar amfani wanda ya tara ilmi mai yawa da hujjoji
Kwarara masu kare martabar sahabban manzon Allah
(S.A.W) daga abin da ake jingina ma su, na Kiyayya da
gaba a tsakaninsu da Ahlul Baiti – iyalan gidan Manzon
Allah (Allah Ya jiKansu baki daya). Ga shi kuma littafin
4
ya Kunshi labarai masu dadi a kan zamantakewa da huldar
da ke a tsakaninsu.
A lokacin da na sake nazari akan wannan littafin sai
na gane ashe wanda ya ba ni littafin nan dai shi ne
mawallafinsa. Don haka na yanke shawarar zan nemi
izninsa akan fassara wannan littafi zuwa harshenmu na
Hausa domin amfanin jama`armu. Alhamdu Lillahi, a
kashegari na samu izni daga wurinsa. Allah Ya saka ma sa
da mafi kyawon alherinsa, Ya ba mu aljanna firdausi akan
wannan aiki mai amfani.
A nan zan so in sanar da mai karatu cewa, na yi sauye
-sauye da dama a cikin wannan littafi amma ban canza ma
sa ma`ana ba, sai na kusanto shi sosai zuwa ga dan uwana
malam bahaushe, ta yadda mai karatu ba zai rinKa jin wani
harshe ne ma a ke fassara ma shi ba. Saboda haka na Kara
ma littafin nau`oin ado na magana irin ta Hausa don Kara
nashadantar da mai karatu ta yadda ba zai Kosa ko ya
gajiya daga karatun ba.
Kamar haka ne dai kuma na Kara inganta littafin ta
hanyar koma ma littafan da mawallafin ya yi nazarinsu a
wajen rubuta shi, sawa`un littafan Ahlus Sunna ko na
Shi`ah, har ma na sanya lambar sifili da shafukan da aka
nazarta – ga in da bai sanya ba - domin mai buKatar ya
5
koma ga resu. Haka kuma ban yi rowa ba game da duk
wani Karin haske ko sharhi wanda zai gamsar da mai
karatu, amma kuma wannan sai na sanya shi a Kasan
littafin, kuma da Karamin rubutu.
Fatar da ni keyi daga mai karatu ya yi mani tukuici da
addu`a ta alheri, ni da mawallafinsa idan har littafin ya
kasance mai amfani a ga reshi. Idan kuwa hakan ba ta samu
ba, to, uzurinmu dai shi ne, mun so mu yi nasiha ne ga
jama`ar musulmi, kuma muna fatar ba za mu rasa ladar
wannan kyakkyawar niyyar ba.
Yanzu dai sai in ce, dan uwa a yi karatu lafiya.
Muhammad Mansur Ibrahim
Sakkwato
28 ga Zul Ki`dah 1423B.H.
6
Gabatarwar Mawallafi:
Babu shakka cewa, Manzon Allah shi ne fiyayyen
talikkai. Wannan abu ne da duniya duka ta sani, Kuma
wata ni`imar Allah ce da Ya hada Musulmai akan sanin
haka. A nan ba mu kulawa da maganganun wasu `yan
tsiraru da su ke fifita sashen Imamai1 ko Waliyyai akan
Manzon Allah ta fuskar ilmi ko wani abu. Irin wadannan
kalamai za ka iske wadanda suka yarda da masu fadarsu
ma tawilanta su su ke yi ko kuma su raunana su.
Babu wanda yake shakka game da matsayin da Allah
Ya ba ManzonSa na kasancewarsa ma`abocin ceto mafi
girma, ga kuma tafkin da Allah Ya ba shi na Alkausar da
sauran darajojinsa na duniya da lahira.
Haka kuma babu shakka cewa, wadannan albarkoki
da alherori na Manzon Allah sun shafi iyalansa da
makusantansa wadanda suka gaskata shi kuma suka
taimake shi.
Saboda haka zamu ga darajojin iyalan gidan Manzon
Allah suna da yawa, kuma sun zo a cikin AlKur`ani da
Hadissai da dama, kuma sun hada da duk iyalansa na
lokacinsa da kuma zuri`ar da suka haifa har ranar
1 Al majlisi a cikin Bihar al Anwar ya Kulla babi da ya sa ma sa
suna: "Babi a kan cewa, Imamai sun fi Annabawa ilmi" (2/82).
Duba kuma: Usul al Kafi na Kulini (1/227). – Daga mai littafi.
7
AlKiyama. Sa`annan kuma duk wasu nassoshi da suke
bayyana falalar Sahabbai, to iyalan Manzon Allah na
cikinsu.
A cikin littafinmu na farko mun yi bayanin darajjojin
wadannan Sahabbai. A cikin wannan dan littafi kuwa zamu
bayyana kyakkyawar alaKar da ke tsakanin Ahlul Baiti da
Sahabbai. Bai kamata mu gajiya da Magana a kan
abokantaka da manzon Allah da irin falalarta ba, da
lizimtar da ke tsakanin wannan manzo mai albarka wanda
albarkar zama da shi su ka samu martabar zama sahabbai.
Darajojinsu kuma sun banbanta ne a aljanna daidai
gwargwadon ayyukansu da jihadinsu tare da shugaban
manzanni.
Haka ma a nan duniya sahabbai sun kasu kashi uku:
Muhajirai da Ansarai da na bayansu kuma duk Allah Ya yi
mu su alKawalin shiga aljanna. Kamar yadda Madaukakin
Sarkin Ya fda in da Ya ce:
Ma'ana:
Wanda ya ciyar a gabanin cin nasara, kuma ya yi
yaKi a daga cikinku, bay a zama daidai (da wanda
8
bai yi haka ba). Wadancan ne mafifita girman
daraja bisa ga wadanda suka ciyar daga baya
kuma su ka yi yaKi. Kuma dukansu Allah Ya yi
mu su wa'adi da (sakamako) mai kyau, kuma
Allah Masani ne ga abin da ku ke aikatawa.
Suratul Hadid, Aya ta 10.
Haka ne. Dukkansu su na da falalarsu da darajarsu.
Kuma tilas ne a kanmu mu gane girma sahibantar manzon
Allah (S.A.W), mu gane cewa, wani matsayi ce mai zaman
kansa. Sahabbai magabata wadanda su ka fara rungumar
musulunci su na da daraja mafi daukaka. Wadanda kuma
Allah Ya hada ma su biyu: tsakanin sahibtaka da zumunta
– Ahlul Baiti kenan- su na da darja biyu kenan. Kuma
darajojinsu na daidai da aikin ko wanensu. Allah Ya yi
tsira ga resu da yarda baki daya.
Ya kai dan uwana mai karatu!
Yana da kyau ka sani cewa, tare da abin da Allah Ya
Kaddara a tsakanin wadannan zababbun mutane – wadanda
suka abokanci fiyayyen talikkai – na fitina da sabani wanda
har ya kai zuwa ga yaKar junansu, bai hana su Kauna da
rahama ga junansu ba. Wannan kuwa yana nuni zuwa ga
cewa da yawan ruwayoyi da Kissoshin da ake yadawa a
kansu ba gaskiya ba ne, duk kuwa da ya ke wasu marasa
9
hankula da nazari da kuma wasu masu ra`ayoya na son
zuciya sun yi anfani da wadannan ruwayoyi domin cim ma
gurinsu na fadada sabani da rikice-rikice a cikin wannan
al`umma.
Kira
Zuwa ga wadanda su ka damu da yin bincike da
rubutu a kan tarihin wannan al'umma, da masu kira zuwa
ga hadin kan musulmi.
Zuwa ga masu Magana a kan ci gaban wannan
zamani da hadarin da al'ummar musulmi ta ke fuskanta
wanda ya wajabta mu hada kanmu don tunkarar
matsalolinmu.
Zuwa ga duk wani mai kishin ci gaban wannan
al'umma ni ke cewa, me ya sa mu ke tsokano matsaloli na
tarihin al'umma da ya gabata alhalin kuwa yin haka ya na
iya haifar da gaba da Kiyayya a tsakaninmu ? Me ya sa mu
ke yin haka ba tare da yin nazari da bincike ba ? Don me ne
ne ? Don neman jama'a ? Ko don kwaikwayon wasu ? Ko
don neman wani abin duniya ?.
Sai ka tarar da wasu marubuta da masu bincike suna
kashe lokaci mai yawan gaske wajen tsokaci game da wasu
mas`aloli na tarihi wadanda aka gina su akan ruwayoyi
masu rauni, ko aka rubuta su bisa ga son zuciya. A daidai
10
lokacin da suke ganin sun yi KoKari akan wannan bincike
in da za ka tambaye su me ne ne fa`idar abin da suka gano
kuma da me ne ne zai Karashi wannan al`umma ? ba zaka
samu wata amsa ba face dai wannan bincike nasu zai Kara
fadada baraka da rarraba da jin takaicin juna a cikin
wannan al`umma. To, a bisa wane harsashe na ilmi su ka yi
wannan bincike ?.
Mun fada a littafin da ya gabata akan sahabbai cewa,
aikin Manzon Allah ne wanda Allah Ya dora masa ya yi
tarbiyyar wadanda Allah Ya girmama su da samun
musulunta a hannunsa da abokantakarsa – wato Sahabbai –
kamar yadda Allah buwayayyen Sarki Yake cewa:
Ma`ana:
(Allah) Shi ne Wanda Ya aika a cikin jahilai wani
Manzo daga gare su, yana karanta ayoyinSa a
kansu, kuma yana tsarkake su, kuma yana sanar
da su littafin (AlKur`ani) da hikima (Sunna), ko
da yake sun kasance daga gabaninsa lalle suna a
cikin bata bayyananne.
Suratul Jum`ah, Aya ta 2.
11
Wadannan su ne wadanda manzon rahama da shiriya
ya tsayu a kan tarbiyyarsu da karantar da su. Mun yi
magana a kan lizimtar da ke tsakanin jagora (shi ne annabi
(S.A.W) da rundunarsa). Manzon Allah shi ne abin
koyinsu, kuma shi ne maKwaucin da su ka yi rayuwa da
maKwautaka tare da shi. Manzon Allah (S.A.W) shi ne
shugaban da suka kasance KarKashinsa. Su ne
talakawansa, kuma su ne sahabbansa. Wannan bayanin ya
gabata a littafi na farko.1
1 Sahabbai su ne almajiran Manzon Allah wadanda aka ce ya
tsarkake su. Idan mun kira shi Liman, to su ne Mamunsa, Idan
kuma mun ce kwamanda, to su ne sojojinsa. Idan ya kasance
shugaba, har wa yau su ne talakawansa. Idan kuma an umarci
Manzo da ya karbi zakka to daga wurinsu ne zai karba. Idan kuma
an ce ya bayar da ita, su din ne zai bai wa. Haka ma idan an umurce
shi da ya kyautata ma maKwauta, to su ne maKwautan nasa. Don
haka, ba zai yiwu a raba daya biyu ba. Idan har mutun ya yi suka ga
wadannan almajirai to, yana zargi ne da tuhuma ga malaminsu. Mu
kam dai Ahlul Sunnah mun yi amanna cewa, Manzon Allah
(S.A.W) ya yi aikin da aka dora ma sa na yi masu tarbiyya
kyakkyawa wadda a sakamakonta ne suka siffaitu da kyawawan
dabi`un da suka hada da Kaunar junansu da jin tausayi a tsakaninsu
har suka zamo al`umma mafi alheri wadda aka fitar ma mutane.
(Duba AlKur`ani, Suratu Ali Imrana, Aya ta 110). Siffofin
wadannan Sahabbai kyawawa suna da tarin yawa. Kuma duk wanda
yake karanta AlKur`ani ya san da haka.
12
Ya dan uwa mai karatu!
Babu shakka a wurinka cewa manzon nan (S.A.W) ya yi
kyakkyawar tsayuwa a kana bin da Allah Madaukakin Sarki Ya
umurce shi na isar da manzanci da tarbiyyar sabbai da
karantar da su da sauransu. Kuma sakamakon wannan
tarbiyya ce su ka sami kyawawan dabi'un da a ka sansu da
su, kai har ma Allah Ya kira su
Ma'ana:
"mafi alherin al'ummar da a ka fitar saboda mutane".
Suratu Ali Imran, Aya ta 110.
Lura da cewa :"a ka fitar". Wa ya fitar ? Wa ya ba su
wannan matsayi ?. Wannan ayar dai dai ta ke da wata ayar
in da Allah Ya ke cewa:\
Ma'ana:
Kuma kamar haka ne Mu ka sanyan ku al'umma
matsakaiciya domin ku kasance masu bayar da
shaida a kan mutane. Kuma Manzo ya kasance
mai shaida a kanku.
Suratul BaKara, Aya ta 143.
13
Ayoyin da Allah Ya saukar a kan yabonsu su na da tarin
yawa. Ga kuma wasu sun gabata ba sai mun maimaita ba.
Wannan littafi:
A cikin wannan dan littafi zan yi magana akan siffa
daya ce kacal daga cikin siffofin da AlKur`ani ya bayyana
Sahabban Manzon Allah da su. Wannan siffar kuwa ita ce
Rahama wato tausai a tsakaninsu. Zan taKaita magana
akan wannan siffa saboda dalillai kamar haka:
1- Saboda muhimmancin wannan siffa da girman
ma`anonin da ta tara, kasancewarta daya daga cikin
siffofin Allah da siffofin ManzonSa.
2- Allah (S.W.T) ne da kanSa Ya zabi wannan siffa a
wajen yabo ga wadannan bayi naSa, Yana mai kore
zace – zace da Karyace-Karyacen maruwaita. Ka
duba yadda Allah Ya sifaita su da wannan siffa a
cikin Suratu Muhammad in da buwayayyen Sarkin
Ya ke cewa:
14
Ma`ana:
Muhammadu manzon Allah ne. Kuma wadannan
da ke tare da shi masu tsanani ne a kan kafirai,
masu rahama ne a tsakaninsu, ka na ganinsu suna
masu ruku'i masu sujada, suna neman falala daga
Ubangijinsu, da yardarSa. Alamarsu tana a cikin
fuskokinsu, daga kufan sujuda.
Suratul Fathi, Aya ta 29.
3- Dalili na uku kuwa – ya kai dan uwana mai karatu –
shi ne, la`akari da yawan gurbatattun ruwayoyi masu nuna
cewa, akwai adawa da gaba a tsakanin Sahabbai har ma
mutum ya kan zaci ana magana akan wasu dabbobin daji
ne ba wasu mutanen kirki da Annabin rahama yayi ma su
tarbiyya ba, wannan kuwa ya kan haifar da mummunar
adawa da Kyama a cikin zukatan masu karatu akan
magabatan nan nasu na kirki. Alhali kuwa Allah Mahalicci
Ya neme mu ne da mu so wadannan bayin naSa, mu yi ma
su addu`a, mu kuma nisanci Kyama da tsanuwa akansu,
kamar in da Allah Ya ke cewa:
15
Ma`ana:
Kuma wadanda suka zo daga bayansu (bayan
Muhajiruna da Ansar da aka ambata a ayoyin da
su ka gabata) suna cewa, `Ya Ubangijinmu ! Ka
yi gafara a gare mu, kuma ga `yan `uwanmu
wadanda suka riga mu yin imani, kada Ka sanya
wani Kulli a cikin zukatanmu ga wadanda suka
yi imani. Ya Ubangijinmu ! Lalle Kai ne Mai
tausayi, Mai jinKai.
Suratul Hashri Aya ta 10.
4- Sanin dukkan wani mai bincike ne cewa, ana buKatar
a tace ruwayoyi ta hanyar nazari game da
maruwaitansu da kuma duba gundarin abin da suka
Kunsa. To amma kuma sai ya kasance ire-iren
wadannan ruwayoyi ana ta yada su ba tare da la`akari
da wadanda suka ruwaito su din ba tare da
kasancewar galibinsu daga cikin shahararrun
maKaryata ne. Ga kuma uwa uba zamowar wadannan
ruwayoyin sun zo da akasin abinda AlKur`ani kansa
ya ke tabbatarwa na tsarkin zukatan wadannan bayin
allah da Kaunatar juna da ke a tsakaninsu. Idan ma
har ka binciki littafan da aka samo wadannan
16
ruwayoyi a cikinsu sai ka taras irin littafan nan ne da
aka wallafa su domin shaKatawa da bayar da
labarurruka na ban mamaki da makamantansu, ba wai
littafai ne na ilimi wadannan Malamai magadan
Annabawa su ka rubuta ba.
Ya kai dan uwana mai karatu ! Ina fatar kada ka yi
gaggawar yanke hukunci da yin suka da zargi don kawai
abin da ya ke a cikin tunaninka na labaran tarihi, ka dakata
har sai ka ji irin hujjojin da ni ke sonn in fada ma ka,
domin hujjoji ne wadanda ba a saba da su ba, duk da
bayyanarsu da kusancinsu da kuma Karfinsu. Haka kuma
ina son in ba ka shawarar ka sake komawa a karo na biyu
zuwa ga ayoyin da muka ambata ma ka a sama, ka yi ma su
karatun mai basira domin ka gane maganar da ni ke fada
ma ka. Musamman ma dai ka sake nazarin wadannan
ayoyin guda biyu:
Aya ta farko:
Ma`ana:
Muhammadu manzon Allah ne. Kuma
wadannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan
kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, ka na ganin
suna masu ruku'i masu sujada, suna neman falala
daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alamarsu tana a
cikin fuskokinsu, daga kufan sujuda.
Suratul Fathi, Aya ta 29.
Aya ta biyu:
Ma`ana:
Kuma wadanda suka zo daga bayansu (bayan
Muhajiruna da Ansar da aka ambata a ayoyin da
su ka gabata) suna cewa, `Ya Ubangijinmu ! Ka
yi gafara a gare mu, kuma ga `yan `uwanmu
wadanda suka iga mu yin imani, kada Ka sanya
wani Kulli a cikin zukatanmu ga wadanda suka
yi imani. Ya Ubangijinmu ! Lalle Kai ne Mai
tausayi, Mai jinKai.
18
Suratul Hashri Aya ta 10.
Karanta wadannan ayoyi, ka sake nazarinsu. Allah Ya
yi ma ka jagora. Amin.
19
BINCIKE NA DAYA: AKAN SUNAYEN SAHABBAI
Abin da mu ka sani ne cewa, sunan mutum shi ne
adireshinsa wanda ya ke nuna ko shi wane ne ko kuma
wane iri ne. Da sunan mutum ka ke gane addininsa da irin
hankalinsa. Misali ai ba mu taba ganin wani bayahude ya
sanya sunan Muhammadu ba. Ko ka taba ganin Musulmi
da sunan Lata ko Uzza?.
Saboda haka Suna yana da muhimmancin gaske.
Kuma da sunan mutum ne iyayensa da danginsa da sauran
jama`a su ke kiransa. Da shi ne kuma mutum ya ke
banbanta da wanda ba shi ba. Don haka ne ma addinin
Musulunci ya yi umurni ga uba da ya kyautata zaben suna
ga `ya`yansa. Kai har ma Annabin Rahama (S.A.W) ya
canza ma wasu sahabbai maza da mata sunayensu saboda
rashin dacewarsu, domin iyayensu ba su zaba ma su sunaye
na gari ba. Bugu da Kari babban birnin da Manzon Allah
ya yi hijira zuwa ga reshi sai da ya canza ma sa suna daga
Yasriba sunan da akwai ma`anar zunubi a cikinsa zuwa
Daiba mai ma`anar daddadan birni.
Kamar haka ne kuma Manzo (S.A.W) ya yi nuni
zuwa ga kyawawan sunaye kuma dadadansu har ma ya fadi
wadanne sunaye ne mafifita a Musulunci wato Abdullahi
da Abdur Rahman. Kuma ya yi nuni ga wasu sunaye da ba
20
su dace ba kamar "Sarkin sarakuna" da makamantansu.
Wannan ya sa malamai sun yawaita bincike a kan mas'alar
sunaye, kuma sun wallafa littafai da dama a kan haka.
To, a nan zan yi tambaya ga reka ya kai mai karatu :
Da me ka ke kiran `ya`yanka? Shin da irin sunayen da ka
ke so kuma ka ke Kaunar ma`abotansu? Ko kuma da
sunayen maKiyanka wadanda ka ke adawa da su kuma ka
ke Kyamar su?!. Idan ka amsa wannan tambaya to, me za
ka ce idan ka san cewa, Sahabban nan da ka ke jin a tarihi a
na cewa, su na adawa da gaba sunayen junansu su ke
sanyawa?. Ina fatar kada ka yi gaggawa har sai ka yi
nazarin misalan da ni ke son kawo ma ka. Idan ka duba su
sai ka yi amfani da hankalinka da basirar da Allah Ya ba
ka, na tabbata za ka hango abin da na hanga a cikin yardar
Allah.
Ga wasu `yan misalai a gurguje:
1- Sayyiduna Ali dan Abu Talib (R.A) yana da `ya`ya
ukku wadanda ya sanya ma su sunayen Abubakar da
Umar da Usman kuma dukkansu sun yi shahada a
Karbala` tare da dan uwansu al- Hussain (Allah ya
jiKansu baki daya).1
1 Al`amarin da ya faru a Karbala` yana da ban takaici a cikin
tarihin wannan al`umma. Amma kuma Allah Ya riga Ya rubuta
faruwarsa, ya kuma faru din a bisa ga yadda Allah Ya Kaddara shi.
21
2- Al Hassan dan Ali dan Abu dalib shi ma yana da
`ya`ya masu sunaye kamar haka: Abubakar da Umar
da Talha su ma kuma suna daga cikin wadanda
sha`anin Karbala` ya rutsa da su (Allah Ya jiKansu).
3- Al Hussaini dan Ali dan Abu dalib (wanda aka kashe
a bisa zalunci da Keta a Karbala`) shi ma yana da da
mai sunan Sayyiduna Umar.
4- Ali dan Hussaini dan Ali dan Abu dalib (Wanda aka
fi sani Zainul Abidin) yana da `ya mace wadda ya
sanya ma ta sunan A`ishah, yana kuma da da namiji
mai suna Umar.
Ya kai dan uwa mai karatu ! ko akwai buKatar in ci
gaba da jera irin wadannan sunaye? Ko hankalinka zai
yarda cewa, wadannan bayin Allah suna adawa da junansu
Wajibinmu a yanzu shi ne, mu kwatanta adalci a game da jingina
laifin kisan Husaini da `yan uwansa da wasu daga cikin iyalinsa.
Dalili kuwa shi ne, ruwayoyi sun sha banban da juna akan wannan
lamari. Kuma babu shakka cewa, Yazidu dan Mu`awiyah bai yi
umurni da a kashe su ba, bai kuma yi farin ciki akan kisan su ba.
Abin da ya yi umurni da shi shi ne a hana su isa IraKi in da `yan
shi`a su ka yi alKawalin nada Husaini a matsayin shugaba na biyu
bayan kuwa ga tsayayyen shugaba wanda ke gudanar da mulki,
wato Yazidu. To, a fagen nan fa na tare su daga isa birnin IraKi
Allah Ya hukunta al`amarinSa in da wasu tsiraru su ka kai farmaki
akan su bayan duk tattaunawar da aka yi ba ta ci nasara ba. Yazidu
kuma ya nuna damuwa ainun akan wannan abin da ya auku, ya
kuma yi rantsuwa cewar bai yi umurni da haka ba, kuma ba haka ya
ke nufi ba. Amma ina abin yi bayan mai aukuwa ta riga ta auku?.
Allah Ya kare mu daga fitina.
22
ne amma kuma su ka sanya ma `ya`yansu sunayen abokan
adawarsu domin wata manufa ta siyasa ko wani abu?. Ka ci
gaba da bincike kuma a cikin tarihin zuri`oin Ahlul Baiti
kamar gidan Abbas dan Abdul Muddalib da zuri`ar Ja`afar
dan Abu dalib kuma Kanen Sayyiduna Ali da zuri`ar
Muslim dan AKilu dan Abu dalib da sauran Ahlul Baiti za
ka yi mamakin gaske idan har kana cikin masu zaton akwai
adawa a tsakaninsu da sauran Sahabbai musamman ma
Khalifofin Manzon Allah guda ukku na farko(Allah Ya
yarda da su).
Mene ne matsayin `yan shi`a akan wannan lamari?
To, daga cikin shi`awa akwai wadanda suka musanta
wannan magana cewa, Sayyiduna Ali da `ya`yansa sun
sanya sunayen manyan khalifofin Manzon Allah (S.A.W)
guda ukku da Nana A`ishah diyar SiddiKu da
makamantansu daga cikin makusantan Manzon Allah
(S.A.W) domin wannan ya ci karo da abin da su ka ba da
gaskiya gare shi na haifuwar adawa da gaba a tsakaninsu.
Sai dai kuma malaman Shi`a kansu sun mayar da martani
akan wannan magana kasancewarta a rubuce a cikin
manyan littafansu, al`amarin da wasu daga cikinsu ke
ganin dasisa ce ta Ahlus Sunna. Idan ko su ka bude ma
kansu wannan Kofa to, mu kuma za mu tuhumce su da
23
rashin aminta da littafansu wadanda suka bayyana sunayen
nan da mu ka ambata musamman ma dai wadanda suka yi
shahada a Karbala` kamar Abubakar dan Ali dan Abu dalib
da Abubakar dan Hassan dan Ali. Wasu ruwayoyin ma sun
bayyana Umar dan Ali da Umar dan Hassan a matsayin
manyan barade wadanda suka nuna zarunta mai yawa a
filin daga ranar Karbala`. To, da yaya Ahlus Sunna su ka
miKa hannuwansu a cikin wadannan littafai naku su ka
soka wadannan bayanai? Ashe kenan ku ma ba ku aminta
ba da littafanku. Don haka sai ku bar su domin ku koma ga
gaskiya. Allah Ya sa mu dace.
To, daga cikin malaman Shi`a wadanda suka nuna
amincewa da gaskiyar wadannan ruwayoyi akwai masu
ra`ayin cewa, Sayyiduna Ali ya sanya wa `ya`yansa
wadannan sunaye ne domin taKiyyah ma`ana wai yana son
ya nuna wa wadannan khalifofi cewa yana tare da su alhali
a haKiKanin gaskiya shi maKiyinsu ne. Wannan maganar
kuwa ita kanta suka ce babba ga matsayin Sayyiduna Ali
da irin jaruntakar da aka san shi da ita, ace jin tsoronsa da
rauninsa sun sanya shi har yana daukar matakai na kada
aga laifinsa!. Wannan suka ce babba wadda muke nisantar
da darajar Sayyiduna Ali daga irinta.
TUSHEN BAYANI:
24
Duba wadannan sunayen da ma wasu ba su ba a cikin
littafan Shi`a din kan su kamar:
1- Kashful Gummah (2/334)
2- Al fusulul Muhimmah shafi na 283
3- A`lamul Wara na Tabarsi shafi na 203
4- Al Irshad na Mufid shafi na 186
5- Al Tarikh na Ya`Kubi shafi (2/213) da sauran su.
Sakamakon Bincike:
Wannan al`amari ya tabbata haka shi ke, shahararrun
magabata daga cikin Ahlul Baiti su na farin cikin sanya ma
`ya`yansu sunayen Abubakar da Umar da A`ishah da Talha
da makamantansu domin Kaunatayyar da ke tsakaninsu da
sanin matsayinsu da darajarsu wadanda su ka ribata a
sakamakon kusancinsu da Manzon Allah (amincin Allah ya
tabbata gare shi). Gaskatar wannan magana kuwa yana nan
a cikin AlKur`ani a cikin ayoyin da suka gabata da kuma
Karshen Suratu Muhammad in da Ya ke cewa:
Ma`ana:
Muhammadu manzon Allah ne. Kuma
wadannan da ke tare da shi masu tsanani ne a kan
25
kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu, ka na ganin
suna masu ruku'i masu sujada, suna neman falala
daga Ubangijinsu, da yardarSa. Alamarsu tana a
cikin fuskokinsu, daga kufan sujuda.
Suratul Fathi, Aya ta 29.
Sake karanta wannan aya ka Kara tunani a kan
rahamar da Allah Ya ce akwai a tsakaninsu.
26
BINCIKE NA BIYU : GAME DA AURATAYYA
A TSAKANINSU:
Dangantaka a tsakanin `yan adam iri biyu ce:
dangantakar jini da ta auratayya. Allah Ta`ala Yana cewa:
Ma`ana:
Kuma (Allah) Shi ne wandaYa halitta mutum
daga ruwa, sai ya sanya shi zumunci da sarakkuta,
kuma Ubangijinka Ya kasance Mai iko ne.
Suratul FurKan Aya ta 54
Sanin kowa ne cewa, aure alama ce ta yarda. Misali
mutum ba zai dauki `yarsa ya bayar ga wanda ya ke
shawaraki ne ba ko mutumin banza ballantana ma a ce
maKiyinsa wanda ma shi ne ya kashe uwar yarinyar ko dan
uwanta.
Matsayin Larabawa game da Sarakkuta:
Sarakkuta tana da wani matsayi na musamman a
wajen Larabawa domin kuwa ba su aurar da `ya`yansu
mata sai ga wanda ya yi daidai da irin matsayin ubannensu
ta fuskar dangantaka domin kada ta wulaKanta. Kishin da
balarabe ya ke da shi akan `ya`yansa mata da jin sauna
akan su gamu da wulaKanci shi ne ya haifar ma su da
27
mugunyar dabi`ar nan ta turbude `ya mace da ranta da
lafiyarta, al`adar da addinin Musulunci ya rosa ta, ya mayar
da Larabawa bisa ga dabi`u managarta. A bisa gaskiya ma
an yi ta samun yaKe-yaKe a tsakanin Larabawa wadanda
musabbabinsu shi ne kishi akan `ya mace.
Matsayin musulunci game da Sarakkuta:
Haka ma a addinin Musulunci za mu samu cewa, an
yi umurni da mutum ya zabi mace ta gari, haka shi ma
uban diya ya nema ma ta miji na gari. Malaman FiKhu sun
tsawaita bincike akan mas`alar Kafa`ah wato irin namijin
da ya cancanta waliyyin mace ya amince da daura ma sa
aure da ita. An yi maganganu daban-daban akan sana`ar
mutum da dangantakarsa da makamantansu. Amma abin
da babu sabani a kansa shi ne, wajabcin la`akari da addini
ga duk wanda za`a ba shi auren mace musulma.
A game da kishi akan `ya`ya mata kuwa, Annabi
(S.A.W) ya ce, duk wanda aka kashe shi a wajen kariyar
irlinsa (Matarsa ko `yarsa) to, wannan mutum ya yi
shahada. A dalilin keta mutuncin `ya mace guda ne Annabi
(S.A.W) ya ba da sanarwar yaKi da yahudawan KainuKa`a
a lokacin da wani daga cikinsu ya kware ma ta zane a
kasuwa. Annabi (S.A.W) ya yi haka ne kuwa bayan ya
Kulla alKawalin zaman lafiya da su, amma sai ya dauki
28
wannan keta mutuncin `ya macce musulma da daya daga
cikinsu ya yi a matsayin kwance alKawali daga bangaren
yahudawan tare da abin da ya biyo bayan wannan na
kashewar da wani musulmi ya yi wa wancan bayahuden
dan ta'adda da kuma kashewar da shi ma yahudu su ka yi
ma sa.
Haka ma idan mu ka yi la`akari da wasu hukuncehukunce
na Shari`a kamar shardanta waliyyin macce ga
daura aure da wajabta shedu da haramta zina da sanya
haddi ga wanda ya yi ta, duka wadannan su na nuna yadda
kariyar mutuncin macce ya ke da matsayi a Musulunci.
A dalilin sarakkuta ma Shari`a ta kan haramta ma
mutum auren wasu mata na har abada ko ta hana shi auren
wata matuKar yana aure da wata.
Ya kai dan uwana mai karatu ! duk abin da ya gabata
shinfida ce mai nuna maka cewa, auratayyar da ta gudana a
tsakanin Sahabbai da Ahlul Baiti babbar alama ce ta
amincewa da junansu da Kauna a tsakaninsu. Bari dai anan
ma mu ba ka wasu `yan misali. Ko ka san:
1- Sayyiduna Ali dan Abu dalib ya aurar da Ummu
kulsum Kanwar Hassan da Hussaini ga Khalifa Umar
dan Khaddab? Ita ce kuma ta Haifa ma sa Zaidu dan
Umar da RuKayyah diyar Umar. Ko kana mamakin
29
wannan ? Me ya sa Umar ba zai auri diyar Fatima ba
alhalin kuwa shi kansa baban Fatima (S.A.W) ya auri
`yarsa, ita ce Hafsah Uwar muminnai ? Ko ka na
ganin tsoro ne ya sa sayyiduna Ali ya aurar da 'yarsa
–jikanyar manzon Allah (S.A.W)- ga surukin
manzon Allah –sayyiduna Umar ? Ina jaruntakar ta
sa? A wurin azzalumi ya kai ta ? Ina tsoron Allansa
da kishin addininsa ? Ko ko dai ka yarda cewa, Ali ya
aurar da 'yarsa ne ga Umar da ya aminta da shi da
kuma addininsa ? domin ba komai a tsakaninsu ban
da Karairayin 'yan shi'ah ?.1
2- Muhammadu dan Abubakar SiddiKu ya haifi da
AlKasim wanda shi kuma ya ba da auren `yarsa
Ummu farwah ga Muhammad dan Ali dan Hussain
dan Ali dan Abu dalib (Wato dai jikanyar Abubakar
SiddiKu ce aka hada ta aure da jikan sayyiduna Ali
kuma jikan Manzon Allah (S.A.W). Ummu farwa
kuwa ita ce ta haifi Ja`afar al SadiK wanda `yan
Shi`ah suke dogara kacokan ga ruwayoyinsa. An
ruwaito shi Ja`afar al SadiK yana cewa, Sayyiduna
Abubakar ya haife ni sau biyu. Me ya sa haka?
1 Bayan rasuwar sayyiduna Umar (R.A) Abdullahi dan Ja'afar dan
Abu dalib shi ne ya aure ta.
30
Domin daman can ita mahaifiyarsa Ummu farwa
uwarta ita ce Asma`u diyar Abdul Rahman dan
Abubakar SiddiK.
3- Zaidu dan Harisah – wanda shi kadai ne sunansa ya
zo cikin alKur'ani- maula ne, ba baKuraishe ba.
Amma saboda darajar musulunci da sahibtakar
manzon Allah (S.A.W) shi ne ya auri Zainab diyar
Jahsh – 'yar uwar Nana Khadijah (R.A) – wadda
bayan sun rabu da ita Allah Ya daura ma manzonSa
aure da ita kamar yadda ya zo a cikin suratul ahzab.
4- Usamah dan zaidu dan Harisah – wanda babansa ya
gabata- manzon Allah ne ya aurar da Fatima diyar
Kais – BaKuraisha – a ga reshi.
5- Salim – maulan abu Huzaifa – abu Huzaifa ya aurar
ma sa da diyar dan uwansa, ita ce, Hindu diyar al
Walid dan Utbah. Gidansu kuwa ya na cikin mafi
girman gidajen Kuraishawa.
Auratayya a tsakanin dangin manzon Allah (Kuraishawa)
da zuri'arsa a daya bangaren da kuma sauran sahabbai a
bangare na biyu ta na da yawa Kwarai da gaske. Wadannan
misalai ne kawai.1
1 Daga cikin auratayyar da ya kamata mu sani a tsakaninsu akwai
auren da Sayyiduna Ali dan Abu dalib ya yi da matar Khalifa
Abubakar SiddiKu a bayan rasuwarsa. Wannan matar ita ce
31
Matsayin Malaman Shi`a akan auren Ummu kulsum da
sayyiduna Umar:
A game da aurar da Ummu kulsum `yar Sayyiduna
Ali zuwa ga Khalifa Umar kuwa wasu daga Malaman Shi`a
kamar al Mufid sun ce, wai da Karfi ne Sayyiduna Umar ya
dauke ta daga gidansu. Haka dai shi ma Kulini ya fada a
cikin Furu`ul Kafi (6/115) A yayin da al Majlisi a cikin
Asma`u Bintu Umais wadda daman can matar Ja`afar ce Kanen
Sayyiduna Ali kafin ya samu shahada a yaKin Mu'uta wanda
manzon Allah ya tura shi. Bayan rasuwarshi sai ta auri Abubakar.
Asma`u kuma ita ce ta haifi Muhammadu dan Ja`afar, sa`annan da
ta auri Abubakar shi ma ta haifa ma sa Muhammadu. A wata rana
wadannan `ya`yan nata sun yi jayayyar daraja a gaban mijinta
Sayyiduna Ali, sai ya ce ma ta, ki raba ma su gardama mana! Ita
kuma sai tace, to, kai dan Ja`afar Babanka ba irinsa a cikin matasa.
Kai kuma dan Abubakar Babanka ba irinsa a cikin dattijai. A cikin
raha da nashadi irin na mata da miji sai Ali ya ce ma ta, to wa ya
rage kenan? Yana nufin shi a wane matsayi ta ajiye shi?.
To, a yanzu dan Uwa ko ka lura da yadda sarakkuta ta ke a
tsakanin Ahlul Baiti kansu da sauran Sahabbai? Ko ka shaKi
Kanshin wata adawa tana gudana a tsakaninsu? Ko ko dai ka lura
al`amarin nasu yadda Allah Ya fade shi ne a ayoyin da malam ya
kawo ma ka su a baya?
Ko ka na iya lura tare da ni cewa, wanda ya ke suka ga
surukanka kai din ne ya ke suka a gare ka? Manzon Allah (S.A.W)
da kansa ne ya auri `yar gidan Abubakar (Nana A`ishah), sa`annan
ya auri `yar gidan Umar (Nana Hafsah), sa`annan ya aurar da `yarsa
RuKayyah ga Usman, da Allah Ya yi ma ta cikawa sai ya sake ba
shi wata `yar ta sa Ummu Kulsum, ita ma a lokacin da ta cika
Annabi (S.A.W) yace ma sa, a yanzu ba ni da wata `ya da na Kara
ba ka ita. To, saboda Allah idan `yan Shi`a su ka ce, wadannan
mutanen, Abubakar da Umar da Usman duk ba mutanen kirki ba ne
to, wa su ke nufin ba ya da kirki?!.
32
Mir'atul UKul (2/45) ya ke ganin wannan kuskure ne. Abin
da dai ya faru ga cewarsa, shi ne, Sayyiduna Ali ya bayar
da aurenta ne akan tilas bisa ga taKiyyah wato saboda jin
tsoro ke nan !!. To, amma kuma Safiyyuddin al TaKtaKi ya
tabbatar da wannan aure a cikin littafinsa wanda ya saw a
sunan al Tusi (shafi na 58). Shi ma al Raja'i ya cirato daga
Abul Hassan al Umar (Jikan Umar dan Ali dan Husaini)
wanda ya ce Abbas ne dan Abdul Muttalib ya bayar da ita
aure ga Sayyiduna Umar bisa ga yarda da amincewar
babanta. Amma kuma shi ne ya ruwaito cewa, wai wata
aljana ce ta ke fitowa da kamannun ita Ummu Kulsum a
duk lokacin da mijin na ta zai sadu da ita. Ta haka ne har ta
Haifa ma sa da Zaidu!!!.
Har wayau dai game da wannan aure, wani Malamin
Shi`ah a wannan zamani ya ba da amsa da cewa, auren dai
dai ya ke da auren Manzon Allah (S.A.W) ga Ummu
Habiba diyar Abu Sufyan alhalin yana mushriki..1
1 Wannan magana abar haushi ce, abar dariya!. Domin kuwa shi
Manzon Allah shi ne ya aura, ba aurar ma Abu Sufyan ya yi ba.
Kuma ita Ummu Habiba musulma ce shi ya sa manzon Allah Ya
aure ta. To, a ina ku ka sami musulmi ya aurar da 'yarsa ga wanda
ku ka ce kafiri ne ?.
Malam bai yi magana game da matsayin malaman shi'ah ba a
game da auren manzon Allah (S.A.W) da wadannan tsarkakakkun
`ya`ya na Abubakar da Umar (Ina nufin Nana A`ishah da Nana
Hafsah), a kan haka na ga ya dace in yi taKaitaccen sharhi a kai.
33
Sakamakon Bincike:
Tabbas dai Sahabbai sun kasance suna sarakkuta da
junansu ba tare da wani fargaba ba. Haka kuma su kansu
Ahlul Baiti sun kasance suna bayar da auren `ya`yansu ga
sauran Sahabbai. Babu shakka kuma duk mai hankali ya
san wannan abu ne mai nuna aminci da Rahama da Kauna.
Duk tawilolan da Malaman Shi`ah su ka yi babu wanda ya
ke da wata makama ta hankali wadda ake dogara ga re ta.
Domin aure abu ne da ba shi yiwuwa sai da Kauna da
soyayya a tsakanin ma`aurata, sa`annan da fahimta da
mutuntawa a tsakanin dangogansu. Abin da muka kawo na
misalai kuwa kadan ne daga cikin abin da manazarta tarihi
za su iya tsokaci a game da shi musamman auratayya a
tsakanin dangin Banu Umayyah da na Banu Hashim za`a
iya tattara littafi akanta. Allah Ya sa mu dace. Amin.
To, a haKiKanin gaskiya malaman shi'ah ba su fitowa fili su yi suka
ga auren wadannan mata da manzon Allah (S.A.W) yayyi, amma su
kan yi suka ga su matan a cikin littafansu. Misali Ni`imatullah al
Jaza`iri a cikin littafin Al Anwar al Nu`maniyyah (1/108) ya yi suka
ga Nana A`ishah da cewa, wai tana adawa da Nana Fatima diyar
Manzon Allah (S.A.W). Haka ma Muhammad BaKir al Majlisi a
cikin littafin Mir`atul UKul (3/305) cewa ya yi ta na adawa da
Allah da ManzonSa da duk Ahlul Baiti. A yayin da shi kuma Abdul
Hussain al Najfi a littafinsa al Gadir (6/79) suka ya yi ga Nana
Hafsah yana mai cewa, wai ba ta san wankan janaba ba !
Subhanallah ! To, wane ne bai koya ma ta ba kenan?!
34
TUSHEN BAYANI:
Dubi tabbacin abin da muka fada na auratayya a
tsakanin Sahabbai da Ahlul Baiti a cikin littafan Sunna
kamar:
1- Siyar A`lam al Nubala` na Dhahabi (6/258-260).
2- Tarikh al Islam na Dhahabi (6/46-47)
Sa`annan ka duba littafan Shi`ah kamar haka:
1- Al Gadir fil kitab wal Sunnah wal Adab na Abdul
Hussain al Najfi (6/79).
2- Al Kafi na Kulini tare da sharhinsa Mir`atul UKul na
Majlisi (3/305).
3- Al Anwar al Nu`maniyyah na Ni`imatullah al Jaza`iri
(1/80).
35
BINCIKE NA UKKU AKAN YABO A TSAKANIN
SU:
Ya kai dan Uwana mai karatu ! Ko ka taba zama a
wasu cikin abokan tafiya a aikin Hajji ko neman karatu ko
tafiyar aiki ko fatauci ? Ya ya ka ji rayuwar baKunci tare
da abokan tafiya?
Ko ka taba samun kanka a cikin wani matsatsi ko
Kunci a gidan kaso ko a sarari? Ya ya ka ga rayuwa tare da
abokai a cikin wahala? Ko ka lura da irin kusanci da
Kaunatayyar da wannan zamantakewa ta ke haifarwa?
To, me za ka ce game da zamantakewar Sahabbai a
Makka lokacin da fadar kalmar La`ilaha Illallahu ya
kasance dalilin shiga wani Kunci da wahala?. Ka tuna
tarayyar Sahabbai (irin su Abubakar SiddiKu da Ali dan
Abu Dalib da Usman dan Affan da Zaidu dan Harisa) a
mabuyarsu ta Darul ArKam a lokacin da ba zai yiwu ma a
bayyana karatun lKur`ani ba. Sa`nnan ka tuna tarayyarsu a
cikin wahalhalu da azaba da Mushrikai su ka rinKa gana
ma su. Sai kuma hijirar da suka yi har sai biyu domin
kubuta da addininsu zuwa Kasar Habasha. Ka tuna yadda
su ka sami kansu a garin baKunci da kewa a lokacin da su
ka je Madina suna masu barin dukiyoyi na gidaje da
36
bisashe da Kaddarori daban daban, kai da ma iyalan wasu
daga cikinsu.
Ka tuna irin zamantakewar Muhajirai da masu
masaukinsu wato Ansar da abin da Allah Ya fada a game
da su na zabin `yan uwansu akan kawunansu ga abin da su
ke so kuma su ke da buKata zuwa ga reshi.
Ka tuna tarayyarsu a tafiye tafiyensu na Jihadi da
Hajji tare da Manzon Allah (S.A.W) a lokacin da a Kafa
ake tafiya da kuma kan raKuma, sa`adda ayari ya ke yin
kwana goma a tsakanin Makka zuwa Madina kawai. A
lokacin da ake tsoron dabbobin dawa ta yadda matafiyi ba
zai yi shishishigin tafiya nesa da ayarinsa ba don gudun
aukuwar hakan. Duba irin yadda su ke yi wa junansu
murna da san barka a lokacin da suka rinjayi Mushrikai a
yaKin Badar da Khaibar da makamantansu da lokacin da
su ke jajanta ma junansu a yayin da Allah Ya jarabce su a
Uhud da Hunain. Ashe duk wadannan ba abubuwa ne da ke
Karfafa danKon Kauna da zumunci ba? Duba yadda
Buwayayyen Sarki Ya ke cewa:
37
Kuma Ku tuna ni`imar Allah a kanku, a lokacin
da kuka kasance maKiya, sai Ya sanya soyayya a
tsakanin zukatanku, saboda haka ku ka wayi gari,
da ni`imarSa, `yan uwan juna.
Suratu Ali Imran Aya ta 103.
Haka shi ke. Ni`imar Allah ce a kansu da Ya fitar da
su daga shirka wadda ta sanya su Kiyayya da gaba da yaKar
junansu, Ya mayar da su ga tafarkin Musulunci suna
Kaunar junansu da tausayin junansu.
Ya kai dan uwana mai karatu ! me zai hana ka yarda
da abin da Allah Ya fada:
Ma'ana:
Sai (Allah) Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku,
saboda haka kuka wayi gari, da ni`imarSa, `yan
uwan juna.
Suratu Ali Imran Aya ta 103.
Ya kai dan uwa ! me zai hana ka kyautata zato ga
wadannan bayi na Allah wadanda Ubangijinsu Ya ke mu su
sheda, Ya ke tunatar da su da falalar da Ya yi a kansu, Ya
na cewa, sun wayi gari su na 'yan uwa, zukatansu na hade,
38
Kauna ta ke a tsakaninsu. Duba yadda Ya ce ma AnnabinSa
a kansu:
Ma`ana:
Kuma idan (Mushrikai) sun yi nufin su yaudare ka,
to, lalle ma`ishinka Shi ne Allah. Shi ne Wanda Ya
Karfafa ka da taimakonSa, kuma (Ya Karfafa ka) da
Mummunai. Kuma Ya sanya soyayya a tsakanin
zukatansu. Da ka ciyar da abin da ya ke a bayan
Kasa, gaba daya, da ba ka sanya soyayya a tsakanin
zukatansu ba, kuma Allah Ya sanya soyayya a
tsakaninsu. Lalle Shi ne Mabuwayi, Mai hikima. Ya
kai annabi! Allah ya ishe ka da kuma wadanda su ka
bi ka daga Muminai.
Suratul Anfal Aya ta 62-64.
Sai ka sake karanta wannan ayar ka gani wace irin
falala ce Allah Ya yi akan ManzonSa ta hanyar Karfafa shi
da Sahabbai, Kuma ya ya Allah Ya sanya Kauna a
tsakaninsu, aikin da duk dukiyar duniyar nan idan an yi
amfani da ita kwalliya ba za ta biya kudin sabulu ba. Har
yanzu dai kana nan kana gaskata gurbatattun ruwayoyin
39
Shi`ah masu nuna Sahabbai a matsayin masu adawa da
gaba?! Ya Allah Ka ba mu basira.
Bari kuma in ba ka wani labari wanda ya fito daga
daya daga cikin littafan da su ne madogarar shi`ah, ina
nufin littafin Kashful Gumma na Arbulli wanda aka buga
shi a Iran (2/78):
An karbo labari daga Imam Ali dan Hussaini
(Zainul Abidin) yace, wasu mutane sun zo daga IraKi
wurin Imam (yana nufin Ja`afar al SadiK) sai suka rinKa
aukawa a cikin mutuncin Abubakar da Umar da Usman
(R.A). To, a lokacin da suka Kare kalamansu sai Imam
yace da su: Ku ba ni labari su wane ne ku? Shin ku ne
Muhajirai na farko da Allah Ya ce:
Ma'ana:
(Ku yi mamaki) ga matalauta masu hijira
wadanda aka fitar daga gidajensu da dukiyoyinsu,
suna neman falala daga Allah da kuma yarda,
kuma suna taimakon Allah da manzonSa!
Wadannan su ne masu gaskiya.
Suratul Hashri, Aya ta 8.
Sai su ka ce, A`a. Ya ce: to, ku ne:
Ma'ana:
Da wadanda suka zaunar da gidajensu (ga
musulunci) kuma (suka zabi) imani, a gabanin
zuwansu, suna son wanda ya yi hijira zuwa gare
su, kuma ba su tunanin wata buKata a cikin
Kirazansu daga abin da aka bai wa muhajirai,
kuma suna fifita wadansu a kan kawunansu, kuma
ko da suna da wata larura. Kuma wanda aka
kiyaye shi daga rowar ransa to, wadannan su ne
marabauta.
Suratul Hashri, Aya ta 9.
Sai su ka ce, A`a. Ya ce: To, ga shi ku kun sheda ba
ku cikin wadannan biyun. Ni kuma na shaida ba ku
cikin na ukkun su ne:
Ma'ana:
Kuma wadanda suka zo bayansu, suna cewa, "Ya
Ubangijinmu! Ka yi gafara a gare mu, kuma ga
'yan uwanmu, wadanda suka riga mu yin imani,
41
kada Ka sanya wani Kulli a cikin zukatanmu ga
wadanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle
Kai ne Mai tausayi, Mai jinKai.
Suratul Hashri, Aya ta 10.
Sa`annan ya ce da su: Ku fita ku bani wuri. Allah
Yayi mu ku kaza da kaza (ma`ana yayi addu`a maras
kyau akansu).
Ko da yake na sani duk irin wadannan ruwayoyi da su
ka zo daga Ahlul Baiti `yan shi'ah su kan dauke su a
matsayin taKiyya, amma mai hankali yana iya gane cewa,
wannan bawan Allah gaskiya ce ya fada, don haka ba
dalilin tuhumarsa da munafucci akan ya fadi gaskiya. Allah
Ya sa mu dace.
Ga abin da shi kansa sayyiduna Ali ya ke cewa akan
sahabbai:
Lalle, naga sahabban Annabi Muhammadu
(S.A.W) kuma ban taba ganin wanda ya yi kama
da su ba daga cikinku, domin su idan ka gan su da
safe sai ka raina kamarsu alhalin kuwa sun kwana
su na sallah. Su na da alamomi a goshinsu da
kumatunsu (Alamun sallah da kukan tsoron
Allah). Idan dayansu ya tuna alKiyama sai ka gan
42
shi kamar wanda ya taka garwashi (yana zufa).
Idan kuma a ka ambaci Allah sai hawaye ya
dararo ma dayansu har ya jiKe rigarsa, ya rinKa
girgiza irin girgizar ganye idan iska ya kada duk
saboda tsoron azaba da Kaunar lada.
Kalamansa da na `ya`yansa suna da yawa akan yabon
sahabban Annabi (S.A.W). Jikansa Zainul Abidin Ali dan
Husaini ya na da wani littafi wanda ya ke yabonsu a cikinsa
ya na kuma yi mu su addu`a. Haka ma duk wani shugaba
daga cikin mutanen kirki za ka taras ya na yawaita yabo a
gare su musamman ma khalifofi shiryayyu da iyayen
muminai (matayen manzon Allah (S.A.W).1
1 Wani abu mai muhimmanci da ba a cika mayar da hankali gare
shi ba shi ne, ayyukan da sayyiduna Ali (R.A) ya yi a KarKashin
gwamnatocin da su ka gabace shi. Sai kuma yaKoKan da ya yi tare
da su kamar yaKin ridda wanda sayyiduna Abubakar ya yi a kan
Banu Hanifa in da can ne sayyiduna Ali ya samu kuyangar da ta
Haifa ma sa shahararrren dan nan nasa Muhammad wanda a ke ce
ma sa Ibnul Hanafiyyah (a cikin bangaroran shi'ah akwai wadanda
su ke sanya shi cikin Imamai goma sha biyu). Ko ka yarda cewa,
duk cikin bai yarda da sahihancin mulkinsu ba ne ya yi ma su aiki,
kuma ya yi yaKi tare da su har ya halaltar da samun rabo a cikin
bayi ?
43
BINCIKE NA HUDU : MATSAYIN AHLUS
SUNNAH GAME DA AHLUL BAITI :
1. Su wane ne Ahlul Baiti ?
Fassarar Ahlul Baiti ita ce iyalan gida. Iyalan ko wane
gida kuwa su ne wadanda ke cikinsa. Matar mutum ta na
cikin iyalansa, haka ma `ya`yan cikinsa da ya Haifa. Malam
Shari`a su kan ce Ahlul Baiti ne ga Iyalan gidan manzon
Allah (S.AW) . To, amma har wa yau malamai sun yi
zantuttuka mabanbantan juna dangane da su wane ne iyalan
gidansa?.
Kafin mu je zuwa ga maganganun malaman sunna –
ma`abuta gaskiya- ya dace mu yi nuni zuwa ga cewa,
malaman shi`ah sun taKaita iyalan Annabi kawai akan
`yarsa Nana Fatima da mai gidanta Ali da `ya`yansu Hassan
da Husaini, sai kuma cikon imamai goma sha biyu daga
cikin zuri'ar Ali.1 Akwai kuma sabani mai yawan gaske a
tsakaninsu game da wannan mas`ala. Ka duba littafin
FiraKul Shi`ah na Nubakhti.
To, ga ra`ayoyan Ahlus sunna akan wadanda sunan
Ahlul Baiti ya Kunsa :
1 Sauran `ya`yan manzon Allah guda shida da matayensa da har
sauran zuri`ar Ali din kansa kamar Ummu kulsum diyar Fatima
wadda sayyiduna Umar ya aura duk ba su samu shiga a ciki ba
saboda son ran `yan shi`ah.
44
Ra`ayi na daya:
Su ne wadanda Annabi (S.A.W) ya hana su cin sadaka
daga cikin danginsa. Wadannan sun hada da duk zuri`ar
Banu Hashim da Banul Muddalib.
Ra`ayi na biyu:
Su ne `ya`yansa da matansa da kuma zuri`arsa.
Wannan shi ne zancen da Malam Ibnul Arabi ya zaba, kuma
ya kafa hujjoji a kansa.
Ra`ayi na uku:
Su ne dukkan mabiyansa tun daga sahabbai har zuwa
ranar tashin alKiyama. Wannan shi ne zancen da Malam
Nawawi ya Karfafa. Haka ma mawallafin littafin al Insaf.
Wasu kuma da su ka zabi wannan zance cewa su ka yi ana
nufin da Ahlul Baiti ma su taKawa daga cikin muminai.
Amma zance mafi rinjaye (ta wajen hujja) shi ne zance na
farko.
45
2.Matsayin Ahlul Sunna a game da Ahlul Baiti :
Idan ka dauki ko wane littafi daga cikin littafan Ahlul
Sunna wadanda su ke koyar da aKida, to, za ka tarar akwai
wannan mas`ala a ciki saboda muhimmancinta.
Ba zan tsawaita ma mai karatu bayani ba, amma zan
taKaita ne a kan maganar shaihun malamin nan (Ahmad
dan Abdul Halim wanda a ka fi sani da) Ibnu taimiyyah.1
Ga maganar ta sa kamar haka:
3. Me ne ne haKKoKan Ahlul Baiti a kan musulmi ?
Iyalan gidan manzon Allah (S.A.W) su na da matsayi
mai girma wanda ya wajabta ma su haKKoKa a kan
musulmi kamar haka:
HaKKe na daya: Jibintarsu da Kaunarsu. Kamar yadda
dan uwana mai karatu ya sani cewa, son musulmai duka
wajibi ne. Kuma "Muminai maza da mata majibintan juna
ne". To, amma kuma su Ahlul Baiti sun kebanta da wani
matsayi saboda kusancinsu ga Manzon Allah (S.A.W)
1 Maganar wannan malami a nan ta na da muhimmanci Kwarai da
gasket saboda dalillai guda uku:
1- Domin taKaicewarta
2- Domin gamewar ma`anarta
3- Domin malamin ya na cikin wadanda `yan shi`ah su ke ganin
kamar ya fi kowa adawa da su, saboda littafinsa da ya wallafa
Minhajul Sunnatin Nabawiyyah wanda ya ragargaza aKidunsu
a cikinsa da hujjoji mabayyana.
46
kamar yadda mu ka fahimta daga maganar Ibnu taimiyyah
wadda ta gabata. Allah Mabuwayin Sarki Y ace:
Ma`ana:
Ka ce ba ni roKonku wata lada a kansa (kiran da ni
ke yi mu ku) sai dai Kauna a dangina.
Suratul Shura, aya ta 23.
Wannan shi ne ma`anar hadisin da ya gabata wanda ya
ce, "Ba za su yi imani ba har sai sun so ku domin Allah da
kuma kusancina". Domin manzon Allah ya hada zumunta
da dukkan rassan Kuraishawa. Kuma a nan a na nufin
soyayya da jibinta sama da wadda ta tabbata ga sauran
musulmi.
HaKKe na biyu: Yin salati a gare su. Iyalan gidan manzon
Allah (S.A.W) su na shiga a cikin salatin da Allah
Madaukakin Sarki Ya yi umurni a yi wa manzon naSa in da
ya ke cewa:
47
Ma`ana:
Lalle Allah da mala`ikunSa Su na salati ga
annabi. Ya ku wadanda su ka yi imani ! ku yi
salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin
amintarwa a gare shi.
Suratul Ahzab, Aya ta 56
Dalilin shigar Ahlul Baiti a cikin wannan salati kuwa
shi ne hadisin da Muslim ya ruwaito a cikin ingantaccen
littafinsa daga Abu Mas`ud al-Ansari (Allah Ya Kara ma sa
yarda) wanda ya ke cewa : Manzon Allah (S.A.W) ya same
ni a wurin zaman Sa`adu dan Ubadah, sai Bishru dan Sa`ad
y ace ma sa : Ya manzon Allah ! Allah Ya umurce mu da
mu yi ma ka salati, to, yaya za mu yi ma ka salatin? Sai
annabi ya yi kawaici har sai da mu ka yi fatar bai tambaya
ba. Sa`annan sai manzon Allah (S.A.W) y ace : "Ku ce : Ya
Allah ! Ka yi tsira ga Muhammadu da iyalan Muhammadu
kamar yadda ka yi tsira ga Ibrahim da iyalan Ibrahim.
Kuma ka yi albarka ga Muhammadu da iyalan Muhammadu
kamar yadda ka yi albarka ga Ibrahim da iyalan Ibrahim a
cikin talikkai. Lalle Kai mai godiya ne, Mai girma". Ya ce :
Sannan ku yi sallama kamar yadda ku ka sani.
(Sahihu Muslim, Hadisi na 405).
48
Daga cikin dalillan da ke bayyana wannan haKKin na
Ahlul Baiti kuma akwai hadisin Abu Humaidin al Sa`idi
wanda Buhari da Muslim su ka ruwaito. Hujjoji dai a kan
wannan batun su na da yawa.
Malam dan Kayyimu ya ce :
Wannan haKKi ne na su ban da sauran al`umma,
ba tare da sabani akan haka ba a tsakanin
Malamai.
(Jala`ul Afham Fil Salati ala khairil anam )
HaKKe na uku: Bayar da humusi gare su kamar yadda
Allah Ya ce:
Ma`ana:
Kuma ku sani, abin sani kawai, abin da ku
ka samu na ganima daga wani abu, to, Allah Ya
na da humusinsa kuma don manzo, kuma saboda
masu zumunta da marayu da miskinai da dan
hanya…
Hadissai kuma a maganar humusi su na da yawa.
Kuma rabon ya kebanci danginsa ne su kadai. Kuma ya
tabbata a gare su bayan rasuwar Manzon Allah (S.A.W).
49
Wannan shi ne zancen jumhurin malammai, kuma shi ne
ingantacce.
(Al Mugni 9/288)
Fa`ida:
HaKKoKan Ahlul Baiti su na da dama. Amma dai
wadannan su ne mafi muhimmanci. Kuma duk wanda
nasabarsa daga manzon Allah (S.A.W) ta tabbata, kuma ya
kasance musulmi, to, wadannan haKKoKan sun tabbata a
gare shi. Amma kuma dole ne a kula da kyawon aiki, domin
nasaba ita kadai ba ta wadatarwa. Manzon Allah (S.A.W)
ya kasance ya na tsoratarwa dangane da dogara a kanta. Ga
kuma abin day a aikata a makka – a cikin labarin day a
shahara- in da manzon Allah (S.A.W) ya tara danginsa ya
ce ma su:
Ya ku jama'ar Kuraishawa ! ku sayi kawunanku
daga wuta, domin ni ba ni wadatar da ku da komai
daga Allah. Ya Abbas dan Abdul Muddalib ! ba
ni wadatar da kai da komai daga Allah. Ya
Safiyyah gwaggon manzon Allah ! ba ni wadatar
da ke da komai daga Allah. Ya Fatima diyar
Muhammadu (S.A.W) ki roKe ni abin da ki ke so
daga dukiyata, ba ni wadatar da ke da komai daga
Allah.