Labarai




NA


Mohammad Tawfik Ahmed


Tarjamar


Habu Umar Ali (Bala)


رسالة الإسلام دين الجميع بلغة الهوسا


Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jinkai


Dukkan yabo sun tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jin-kai.


Mamallakin ranan sakamako. Kai kadai muke bauta wa, kuma gare Ka kadai


muke neman taimako. Ka shiryar damu hanya madaidaiciya. Hanyar wadanda Ka


yi ni’ima a gare su, ba wadanda aka yi fushi a gare su ba, kuma ba batattu ba.


Da sunan Allah Mai rahama Mai jinkai


‘Yan uwa maza da mata:


• Shin kun taba lura da sabanin ra’ayi dake bayyana? Shin kun taba tunani


a kan lamarin addini kuwa?


• Dangane da wannan lamarin, shin kuna sane da babban makiyin da ya


mamaye dangin bil’adama kuwa? Kowa na tunanin cewa, shi ko ita ya yi


imani ne da Addinin gaskiya, koda shi/ita dutse ya/ta rika a matsayin abin


bauta?


• Shin ka taba la’akari da yadda masu tsattsauran ra’ayi suke tunani game


da imanin su kuwa?


Na tabbata, ba shakka wadannan abubuwa, sun sha maka hankali. Wata kila


ma, wadannan tambayoyi su kaika ga yanke hukumcin cewa, ingantaccen magani


na wannan abu Shine, a samu wani Addini guda daya da zai hada kan bil’adama


wuri daya, Addinin da duk kowa zai iya fahimtar sa cikin sauki.


Ya kamata duk wani dan-Adam ya gane da kansa - ba tare da wani yayi masa


jagora ba- bukatar bin wadannan gimshikai:


1- Samun wani Allah Makadaici, Wanda ake bautawa Shi kadai (domin shirka


tana iya lalata farfajiyar samaniya)


2- Wanzar da kaunar alheri a cikin mutane.


3- Imani cewa; Allah Ya aiko manzanni ne domin su karantar da wadannan


tsarkakan gimshikai da suka gabata ga ilahirin bil’adama.


Idan kayi tunani akan irin wannan lamarin, zaka tambayi kanka, ko shin,


wannan irin Addinin, yana nan kuwa? Amsar wannan tambayar itace: “i” kwarai


kuwa, wannan Addini guda daya mai hada kan mutane ya kasance tun farkon


halitta, Allah ne Ya saukar zuwa ga zababbun Annabawan Sa wadanda aka aiko


wa mutane.


Allah Ya ce:


“Tabbas Addini dai a wurin Allah Shine Islama, wadanda aka bai wa littafi basu


saba ba face lokacin da ilimi ya zo musu, saboda zalunci a tsakanin su, duk


3


wanda ya kafirce wa ayoyin Allah to lallai Allah mai saurin bincike ne” [aya ta 19


Ali-imran].


Ya sake cewa:


“Duk wanda ya riki wani addinin da ba Musulunci ba, to ba za a karba daga


gare shi ba, kuma a cikin lahira yana cikin tababbu”


[aya ta 85 Ali-imran].


Ashe ke nan dukkan addinai daga Allah suke, to amma wasu mutane bisa


kuskure suka rika rada wa addinai suna ta hanyar danganta su ga Annabawan da


suka zo da su, ko wanne da zamaninsa.


Wannan danyen aikin shine ummul’aba’isan da ya haifar da sabani da bin


ra’ayin rikau a cikin al’ummomi.


Haka kuma wannan rar-rabuwan ya sanya bil’adama mantawa da Addinin


gaskiya kwata-kwata .


Wasu sun rada wa Islama suna “Mahammadiyya” domin danganta Addini ga


Muhammadu kamar yadda sauran addinan ake kiransu da sunan Annabawansu,


duk da cewa duk Annabawa sun tabbatar da Allah guda daya kuma sun hori


mutanen su da su bauta masa shi kadai.


Koda yake ni ba mai wa’azi ba ne, amma ina jin cewa wajibi ne a gareni in


bayyana a takaice ma’anar wannan Addinin, domin idan mabiyan wasu addinai da


ba Islama ba suka jahilci Musulunci da karantarwarsa, saurin yanke hukumcinsu


akan Musulunci zai kai su ga yiwa shika-shikan sa mummunar fahimta wacce


bata da jagora.


Islama


Kalimar “Islama” ma’anarta; aminci a tsakanin bil’adama tare da mika wuya ga


nufin Allah.


Haka kuma tana nufin aminci tsakanin mutum da kansa a hannu guda, sannan


tsakanin mutum da sauran mutane a daya hannun, har ila yau, Islama na nufin


tsoron Allah Madaukakin sarki.


Wadannan ma’anoni gaba daya suna cikin Alkur’ani a inda mutum zai koyi


yadda zai yi wa kansa alheri da sauran mutane ta hanyar aiwatar da abin da


Qur’ani yake karantarwa Annabi Muhammadu (S.A.W) Shine karshen manzo


amma ba Shine kadai Annabin Islama ba.


Musulamai sun yi imani da duk Annabawan da suka gabata, sun yi imani da


Annabi Ibrahim, Annabi Musa da Annabi Isa (Allah Ya yarda dasu gaba daya).


Allah Ya aiko wadannan manzanni ne domin shiryar da mutane domin cika


manufar Allah da kuma rayuwa cikin jin-dadi.


Alkur’ani shine tsarkakakken Litafin Islama wanda ya kunshi karantarwa ta


gaskiya na sauran Litattafan Allah masu tsarki.


Allah Ya ce:


“Mun saukar maka da Littafi mai gaskata Litattafan da suka gabace shi, kuma


yayi babakere akansu, saboda haka, ka yi hukumci a tsakanin su da abin da Allah


Ya saukar, kada kabi son zuciyoyin su ga barin abin da yazo maka na gaskiya, ko


wani daya daga cikinsu an bashi shara’a da tafarki, da Allah Ya ga dama da Ya


sanyaku al’umma guda daya, “to amma bai Yi hakan ba ”, domin Ya jarrabe ku


4


cikin abin da Ya aiko muku, to kuyi tsere wajen alheri, zuwa ga Allah makomarku


take baki daya, sannan Ya baku labari game da abin da kuka kasance kuna


sabani a ciki” (Ma’ida aya ta 48).


Imani


Musulunci ya karantar da musulmai cewa suyi imani da Allah guda daya kadai,


da Mala’ikunSa, da LitattafanSa, da gaba daya AnnabawanSa, da tashi bayan


mutuwa da ranar sakamako.


Allah Ya ce:


“Ya ku wadanda kuka yi imani, kuyi imani da Allah da manzonSa da Littafin da Ya


saukar wa manzonSa, da Litattafan da aka saukar a gabaninsa, kuma duk wanda


ya kafirta da Allah da Mala’ikunSa da LitattafanSa da manzaninSa da ranar Lahira


ba shakka ya bata, bata mai nisa” (Annisa’i aya ta 136).


Musulmi sun yi imani da bam-bancin dake tsakanin alheri da sharri. Duk abin


da Allah Ya halitta alheri ne, kuma koda yake ana amfani dasu ne domin neman


yardar Allah, amma a karshe suna kai mutane ga jin-dadi.


Haka kuma idan aka yi mummunar amfani dasu zasu kai mutane ga sharri da


nadama.


Allah Ya ce:


“Wanda ya aikata aiki na gari don kan sane, wanda ya munana kuma kan sa


yayi wa, kuma Ubangijinka ba mai zalumtar bayi ba ne” (Fussilat aya ta 46).


Allah


Musulmi gaba daya sun yi imani da Allah daya wanda Ya ke Madaukaki, Masani,


Mai adalci, Mai yawan taimakon bil’adama, bai Haifa ba, ba a haife Shi ba, Shine


hasken sama da kasa, Mai rahama Mai jin-kai, Shine farko, Shine karshe, Shine


Madauwami, idan har Annabi Isa ya kira Allah “Uba” wannan kawai yana nufin


rahama da alherin da Allah Yake tattare dasu ne, ba wai yana nufin Allah ubansa


ne mahaifi ba.


Gimshikin Musulunci


Wadannan gimshikai da zan zano wajibi ne a kan musulmai.


1- Imani mai karfi cewa Allah Yana nan, kuma Shi kadai Ya ke, babu


abin bautawa da gaskiya face Shi.


2- Salla: domin tsarkake jiki da daukaka rai.


3- Azumi: saboda daidaita tsakaninn jiki da rai, azumi waraka ce ga jiki,


kuma da inganta sansancewa da ake da shi na bukatar nagartacciyar


dangantaka a tsakanin mutane, dabbobi, shuka, haka kuma zai karantar


da mutane hakuri da kuma kar-karfar anniya.


4- Zakka: domin kyakkyawar dangantaka tsakanin masu arziki da marasa


arziki, domin kuwa su masu arzikin zasu ba wadanda basu dashi kashi


biyu da rabi daga cikin dari (2.5%) a ko wace shekara ta Musulunci,


muddin dai sun mallaki dukiyar da ta kai nauyin 85gm na ma’aunin zinare


21. koda yake mai arziki zai biya abin da muka ambata, to amma yafi


kyau su kara domin kirkin su yayi galaba. Na tabbata cewa yana daga


cikin abin da ya wajaba akan musulmi, taimako da jinjina wa talaka.


5


5- Haji a makka: wajibi ne ko wani musulmi ya ziyarci makka koda sau daya


ne a rayuwar sa, idan da akwai daman, in shi ko ita na da ikon zuwa


makka. Musulmai basu bauta wa gunki ko Annabi. Suna sanya tsarkakan


ma’anoni na Islama kuma suna gode wa Allah a nan hajin, kuma wata


dama ce da zasu hadu da sauran ‘yan’uwa domin karfafa dankon


zumunicin dake tsakanin su.


Babu tilas a Islama


Alkur’ani mai girma ya karantar da mutane cewa, kada a tilasta wa wani ga


yarda da wani tunani, kuma duk wani yunkuri na ta’annuti haramun ne. har wa


yau, duk yake-yaken musulumci an yi sune domin kare Addinin Musulunci, amma


a wasu lokuta, an samu wasu shugabanni na kasashen musulmi sun yi yaki


domin neman abin duniya da cimma manufofinsu, sakamakon haka ne ma,


wadannan shugabanni suka fado daga kololuwar girmar da magabatansu


wadanda suka riki Addini, suka gina, ashe ke nan baza a zargi Islama ba akan


wannan faduwa, domin Islama da kansa bai yarda da irin wannan yakin ba, bugu


da kari, duk mabiyan sauran addinai su ma sun yi irin wannan yakin da sunan


addini alhali kuwa addini ba ruwansa da wannan fadi.


Islama ya bai wa mutane cikakken ’yanci na aiki da fada aji, ta girmama ran


dan-Adam ba tare da ta’addanci ba saboda shi ko ita zai rayu cikin aminci.


Domin ka zama musulmi ba kawai aikata wasu abubuwa na bauta ba ne, domin


Islama ba bauta ba ne kadai, amma kuma Islama Addini ne na cikakken zaman


lafiya da mutane.


Ko wane jariri daga haihuwarsa yana a matsayin musulmi.


Annabi Muhammad (S.A.W) ya ce: “kowa ana haihuwarsa ne akan “fitira” (wato


’yanci na zabi) sai dai iyayensa su mayar da shi Bayahude ko mabiyin Addinin


kirista ko maras addini” [Ahmad ne ya ruwaito].


Ni musulmi ne; Na gaji zaman lafiya


• Na yi imani da Allah daya, Shine Mai karewa, bai a iya raba Shi ba,


iliminSa kuma Yana tare damu ako ina, kuma Shi ba a kebe Yake a wani


wuri ba. Allah Ya ce:


(Shi ne Ya halicci sammai da kasa cikin kwanaki shida sannan ya daidaita a kan


Al’arshi, Yana sanin abin dake shiga cikin kasa da abin dake fitowa daga cikin sa,


da abin dake sauka daga sama da abin dake haurawa cikinta, kuma Yana tare da


ku duk inda kuke, kuma Allah na ganin abin da kuke aikatawa) [Alhadid - 4].


*Babu abin da yayi kama da Shi, kuma Shine ya halicci Dukkan komai, na yi


imani da AnnabawanSa ba tare da bambanta tsakanin Musa da Isa, da


Muhammadu [A.S]


A wurin Allah kadai nake neman agaji, shiriya da kuma gafarar zunubai na, kai


tsaye ba tare da wani ya taimaka ba ko yayi mini sakaina, ban taba fasa kiran


Allah ba, a ko wane lokaci, kuma ina jin cewa iliminSa na tare dani a duk inda


nake, Shine mai hukunta Dukkan ayyuka na, kuma ina bin dokokin Sa da aka


fada a cikin Alkur’ani mai girma.


Ina bin karantarwar Musulunci, salla azumi, zakka, hajji a makka.


Kisan kai da kunar bakin wake haramun ne a Islama, tunda Islama ta bukaci


mutane su rayu cikin aminci.


6


Bana aikata zina, kuma ina kiyaye duk wata zuga da zata kai ni ga lalacewa ko


bata daga hanya madaidaiciya, domin na san cewa dabi’ar zuciya da rauni take.


Allah Ya na cewa:


(Kada ku kusanci zina, domin ta kasance alfasha, kuma ta munana ga zama


tafarki) [Isra’i - 32].


Jin-dadi na gaskiya Shine jin-dadin da nadama bata biyo shi, irin wannan jindadin


ana samu ne ta hanyar manyan zukata da rai take kare su.


Kyakkyawan Misali a nan Shine; mutumin da ya nufi aikata zina, amma


lamarinsa bai bar shi ba, to da ya kasance a karkashin tasirin giya bai gushe ba


har sai da ya kashe mijin matan yayin da mijin yayi yunkurin shiga tsakaninsa da


zina da matan, ya kashe wanda ke kan gaskiya yayin da yake karkashin tasirin


maye, ashe ke nan giya tana iya zama asalin duk wani laifi.


* Bana caca, ko da na dan kudi kadan ne, saboda mai caca ba ya mutunta abin


dake yake samu, sanya sa’ar mutum a kan wani abu ko wasan kati ko


makamantansu abin kunya ne kuma rashin mutumci ne.


Allah Ya ce:


(Ya ku wadanda kuka yi imani, lallai giya da caca da gumaka da kiban kuri’a


kazanta ne na aikin shedan, saboda haka ku nisance su ko zaku tsira) [Ma’ida 90]


Musulmi baya ba da kudi da ruwa saboda wannan hanya ce mai gadar da bakin


ciki.


Idan musulmi yana da hali ya kamata ya bada bashi, kuma yana iya neman a


lamince masa ta hanyar jingina domin ya tabbata kudin sa zai dawo masa, amma


kuma bai halatta wanda aka bai wa jingina yayi amfani da wani abu na jingina


ba.


Allah Ya ce: (ya ku wadanda kuka yi imani kuji tsoron Allah, ku bar abin da ya


saura na riba in kun kasance muminai. idan baku aikata ba, to Allah Yana sanar


daku yaki daga gare Shi, idan kun tuba to ku karbi uwar kudinku kadai, kada kuyi


zalumci kada a zalumceku, idan wanda ya dauki bashin ya kasance a cikin tsanani


to a saurara masa har ya samu yalwa, ku bar masa sadaka, shi yafi muku alheri


in kun sani) [Albakara 278-280]


Musulmi baya zagin mutane ko maganganu na batsa game da ’yan’uwansa


musulmai, domin duk wanda yayi da dan uwansa yana kama da wandake cin


naman dan uwan sa daya mutu, wannan ya hada da wadanda suke kushe wa


mutane a bayan idonsu amma baza su iya fada musu a idonsu ba. Allah Ya ce:


(mummunai ’yan’uwan juna ne, ku shirya tsakanin ‘yan’uwantakanku, kuji tsoron


Allah ko za ku samu jin-kai. Ya ku wadanda kuka yi imani, kada wadansu mutane


suyi wa wasu mutane izgili, suna iya zama mafiya alheri, haka kada wasu mata


suyi wa wasu mata izgili domin suna iya zama fiye da su, kada ku aibanta


kawunan ku, kada ku jefi juna da miyagun lakabobi, tir da sunan fasikanci bayan


imani, wadanda basu tuba ba sune azzalumai. Ya ku wadanda suka yi imani ku


nisanci yawa-yawan zato, lallai sashen zato zunubi ne, kada kuyi leken asiri kada


sashen ku su yi da sashe, shin dayanku yana son yaci naman dan uwan sa alhali


ya mutu? To ku ki cin, ku ji tsoron Allah, lallai Allah Mai karban tuba ne Mai jinkai)


[Alhujurat 10-12]


Imani da aiki


Imani ba tare da aiki ba, ragagge ne, imani kadai ba zai wadatar ba muddin ba


a juya shi zuwa ga aiki ba.


7


Musulmai sun yi imani cewa Allah Yana hukumta ayyukansu kuma sune da


alhakin duk abin da zai biyo baya, ko anan duniya ko a ranar lahira.


Ko wani musulmi ko musulma zai dauki nauyin aikin sa, domin babu wani mai


daukar laifin wani.


Allah Ya na cewa: (Na rantse da zamani. Lallai mutum yana cikin asara. Sai dai


wadanda suka yi imani kana suka yi aiki na gari, suka yi wa juna wasiya da


gaskiya kuma suka yi wa juna wasiya da hakuri.) [Al’asar 1-4]


Islama da zamantakewa


*Matsayin mata a Musulunci


Maza da mata daga asali daya suke kuma rai iri daya gare su, kuma Allah Ya


sanya musu hankali da karfi tun ran gini tun ran zane.


A cikin Islama maza da mata suna daukar nauyi, kuma ana lura da mata cewa


su suna iya jure wa rayuwa har zuwa wata iyaka. Ya kamata maza da mata suyi


aiki a rayuwar su gwargwadon yadda ya dace da dabi’arsu.


Abin da yafi dacewa ga matan musulmi shi ne ta bi mijin ta, kuma a matsayin


ta na uwa Shine ta kula da ’ya’yanta, abin nufi Shine mace tayi amfani da


yawancin lokacin ta domin tafiyarwa da kula da gidanta domin Shine aikin ta na


hakika.


Haka kuma idan mace ta bukaci zuwa aiki dole ne ta kula da shika-shikan


Musulunci, kuma ta zabi aikin da ya dace da dabi’arta, ga musali; karantarwa,


aikin likita, ko ilimin da ke nazarin haifar jariri ko cututtukan yara da


makamantan su.


Bisa la’akari da ra’ayin Islama, ina iya cewa mata sun samu mutuntawa da


girmamawa a duk inda suke. Ashe ke nan idan aka yi wa mata mu’amala wace


bata kamata ba, a wasu wurare a gabas ko a yamma, wannan sakamakon rashin


aiki da Musulunci ne a wadannan wurare.


Allah Yace: (yana daga cikin ayoyinSa, halitta muku mata daga kawunan ku


(wato bangaren jikin ku) domin ku samu sukuni da natsuwa gare su, kuma Mu ka


sanya soyayya da tausayi a tsakanin ku lallai ne cikin wadancan abubuwa da


muka ambata akwai ayoyi ga mutane masu tunani) [Rum 21]


Zargin makiyan Musulunci


Ra’ayinnan na ban haushi da ake yadawa game da Musulunci a cikin litattafan


marubuta masu tsattsauran ra’ayi ba gaskiya bane, hakika sun ketare gaskiya


yayin da suka rungumi wannan ra’ayi na karya a rubutun su da aka watsa a


daukacin duniya.


Mai kallo da idon basira ya kamata ya sanar da kansa ko kanta da farko game


da gimshikin lamarin, domin ya iya gina ra’ayi na gaskiya game da ra’ayin.


A fili yake, a bayyane cewa, wadannan masu tsattsauran ra’ayi suna hidimar


manufar masu mulkin mallaka ne domin sun jahilci kashin kazan da kasashen


yamma suke so su goga wa kasashen gabas marasa galihu, alhalin suna karyar


cewa su bauta suke yaka da taimaka ma wahalallu.


8


Wace gyara kasashen yamma suka kayo wa kasashen gabas? Shin sun zone


domin rauna-na da lalata al’umma ta gari ta hanyar yada giya da baza karuwanci


ne?.


Daidaito da ‘yan’uwantaka a cikin Musulunci


Islama itace Addinin tauhidi da daidaito a tsakanin bil-adama domin cimma


yardar Mahaliccinsu. Koda yake akwai sabanin matsayi a tsakanin mutane amma


dai ya zama dole su hada guiwa kuma su samu kyakkyawan dangantaka a


tsakani tare da


jinjina wa juna. Alal misali, dole masu arzaki su taimaka wa marasa arziki,


wannan cudene-niya ce da ta wanzu a tsarin da ake kira tsarin rashin kymar baki.


Karkata da wariya sakamakon asali ko launi ko al’adu be da wuri a Musulunci,


alhalin ana daukar mutuntaka a matsayin dangi guda wanda bakake da farare


suka cakude suka zama tamakar abu guda daya: ’yan’uwantaka. Allah Yace: (ya


ku mutane lallai ne Mun halicce ku daga na miji da mace kuma Muka sanya ku


al’ummomi da kabilu domin ku san juna, lallai mafi daraja a cikin ku a wurin Allah


Shine wanda yafi tsoron Allah, lallai Allah Shine Masani Mai labari) [Alhujurat 13].


Cin gashin kai


Islama ya karfafa ra’ayin daidaikun mutane kuma ta mutunta akidar kowa


muddin yana cikin iyakar kya-kyawan fahimta ta Addinin gaskiya. Allah Yana


cewa: (kace ni kawai da abu daya nake yi muku wa’azi, ku tashi don Allah, biyubiyu


ko daya-daya, sannan kuyi tunani, babu wata hauka game da abokin ku


“Muhammadu” shi ba komai ba ne, face mai gargadi gare ku gabanin azaba mai


tsananin) [Saba’a 46]


Islama da kimiya


Islama yayi la’akari da neman ilimi a matsayin wajibi akan duk wani musulmi.


Allah Yace: (ya ku wadanda kuka yi imani, idan akace muku, ku yalwata a


mazauni to ku yalwata Allah zai yalwata muku, kuma idan aka ce muku, ku mike,


to ku mike, Allah zai daukaka darajojin wadanda suka yi imani da wadanda aka


baiwa ilimi cikin ku, Allah Masani ne game da abin da kuke aikatawa) [Almujadala


11].


Islama da aiki


“Ku biya ma’aikaci la’adarsa kafin guminsa ya bushe”


Wancan magana da ta gabata an ruwaito ta ne daga manzon Allah (p.b.u.h)


[Ibnu maja ne ya ruwaito].


Haka dai duk wani aiki da zai ka ga samun abin da za a rayu cikin mutunci abin


darajantawa ne, tundake rashin aiki ba abu bane mai kyau. Allah Yace: (kace:


kuyi aiki, da sannu Allah zai ga ayyukanku da manzonSa, sannan a mayar daku


zuwa ga masanin abin dake fake da wandake bayyane, sannan ya baku labarin


abin da kuka kasance kuna aikatawa) [Attauba 105].


Tattalin arziki a Islama


Ko wace gwamnati ta Islama wajibi ne ta biya wa mutanenta manyan


bukatunsu: mafaka, abinci da sutura.


Tsarin Musulunci na tattalin arziki an aiwatar a cikin karnoni da dama kuma ya


samu ga-garumin nasara.


Islama ta kiyaye wa ma’aikata la’adar aikinsu ba tare da la’akari da irin kokarin


da suka yi ba da kuma irin dabi’ar wannan aikin.


9


Arzikin mutane na musumman Shine tushen duk wani aiki na masana’anta,


dalilin ke nan da Islama ta darajanta arzikin mutane, sakamakon haka ne ma


yasa ta kare duk wasu ababa da za su habab-baka aiki kamar yadda ta kare


rayuwa.


Gado a cikin Musulunci


Tsabi’ar mutum ne da fitirarsa, yunkurin ganin cewa lallai ya wanzar da


sunansa a bayan kasa. Wannan burin yana cika idan mutum yaga ‘ya’yan sa da


jikokin sa suna kare sunan sa. Don haka ne yake kokarin yi musu hidima.


Wadannan hidimomi ana ganin cewa wasu sanadarai ne masu muhimmancin


gaske wajen ci gaba, kuma wasu gimshikai ne na gado. A hanu guda kuma, gado


wata hanya ce ta rabon arziki ko sake rabashi a cikin Islama, domin mata da


’ya’ya maza da mata suna da rabo a cikin abin da mahaifin su ya bari. Idan


mahaifin bai da da, matar sa, mahaifin sa, mahaifiyar sa, ‘yan’uwan sa da ’ya’yan


sa mata zasu gaje dukiyar sa, ashe ke nan rabon gado wata hanya ce ta raba


dukiya memakon tara wa a wasu ’yan tsirarun hannaye abin da zai ka ga haifar


da tsarin tara dukiya a wurin mutum daya. Har ila yau rabon gado yana kai ga


adalci da karfafa dankon zumunci tsakanin ’ya’ya da dangi, bugu da kari, Islama


tana kallon mutum a matsayin wakilin Allah wanda ya gaji arziki wanda alal


hakika na Allah ne, ashe ke nan wajibi ne wakili yayi iya kokarin sa domin


amfanin bil’adama.


Allah Yana cewa: (kada ku bawa wawaye dukiyar ku da Allah Ya baku damar


tafiyar wa, ku ciyar dasu, ku tufasar dasu, ku fada musu magana ta girma da


arziki) [An-nisa’a- 5]


Ashe ke nan wajibi ne a hana wawaye barna da dukiyoyinsu, koda yake mutum


yana da ’yanci ya mallaki kadarori, amma duk da haka ana ganin cewa: dukiyar


al’umma ce da ya zama dole a kare, ke nan idan musulmi yana barna da


dukiyarsa, tafiyar da wannan dukiya zata koma hanu wani wakilinsa ma kusanci


da zai kare wannan dukiyar.


Kasuwanci


Ana la’akari da kasuwanci a matsayin manyan jigogin tattalin arziki a


Musulunci, domin yana gina wajen kashi 90% na hanyoyin samun riba, dalilin ke


nan da ya sanya Islama gindaya tsauraran matakai domin kare gaskiya da amana


a harkar kasuwanci.


Manzon Allah ya ce: “Cinikayya ana yin tane da zabi (babu tilas) sai dai idan


bangarorin biyu sun rabo, idan suka yi gaskiya suka bayyana za a albarkaci


cinikin nasu, idan suka yi karya kana suka boye (abin da suka sani) za a zare


albarka daga kasuwancin nasu.” [Buhari ne ya ruwaito].


(Ihtikari)


ko kuma, tsarin yin kane-kane akan abin kasuwa


Yin kane-kane akan abinci domin yayi tsada kuma farashinsa ya haura


haramun ne a Musulunci.


Har wa yau, daga farashi haramun ne. Islama ya gindaya wasu dokoki dake


tafiyar da kasuwanci na kasa da kasa ta yadda zai dace da ‘yan’uwantar dake


tsakanin bil’adama.


Mummunan amfani da mutane


Mummunar amfani da mutane ko wani iri ne an haramta shi, domin mutane su


rayu cikin sauki, idan mammaci bai bar ishash-shiyar dukiya ba domin biyan


bashinsa ko bashinta, wajibi ne akan gomnatin Islama ya biya wannan bashin


saboda gudun rudani a harkar saye da sayarwa. Annabi Muhammadu ya ce: “Nafi


mumunai kusa da kawunan su, saboda haka duk wani mumini da ya mutu ya bar


10


bashi to biyar sa na kaina, kuma duk wanda ya mutu ya bar dukiya to na


magadan sa ne.” [Buhari ne ya ruwaito].


Riba


Riba haramun ce a Musulunci, domin gimshikin da yace: “babu riba ba tare da


wahala ba, kuma babu kudi ba tare da aiki ba”


Allah Yace: (Allah zai kwashe albarkar riba kuma zai haba-bbaka sadaka Allah


ba Ya son kowane mai yawan kafirci mai yawan laifi) [Al-bakara- 276]


An kamanta maciyin riba a cikin alkur’ani da wanda “inna” ta shafe shi (aljani


ya buge shi) ta yadda ba zai iya tashi ba.


Maciyin riba yana wanzuwa ne cikin son kai har abin ya kaishi ga rasa duk wani


jin tausayi.


Tsabi’ar Islama


Islama shine Addinin da aka turo wa daukacin bil’adama a ko wane zamani,


dalilin ke nan ma da yasa Islama ta sifantu da wadannan kebantattun siffofi:


1- Islama Addinin baligin mutum ne wandake rungumanta bayan tunani da


amfani da kaifin kwa-kwalwa ba tare da bukatar wata gabatar wa ba.


2- Islama Addini ne da Allah Ya saukar kan duk manzanin da aka aika wa


mutanen da suka bata saboda jahilcin su, rashin fahimta, da kuma bin son


zuciyoyin su da kuma yunkurin da suke yi na batar da mutane.


3- Islama ya umurci mabiyanta da suyi imani da duk Annabawa da manzanni


da Allah Ya aiko, ko sun san sunayen su ko basu sani ba.


4- Islama ta girmama hankali na kwa-kwalwa har ya kai matsayin da ya


sanya shi babban alkali idan aka yi jayayya, game da imani, zamantakewa


da halayen daidaikun mutane, ashe ke nan, an ba da hankali ne domin jinjina


masa kamar yadda ya cancanta.


5- Islama yayi kira ga kololuwar daidaito tsakanin mutane gaba daya, kuma


ya kushe wa duk wata karkata dake nufin kawo wariya a tsakanin


bil’adama, tare da fifita wani iri.


Yanzu ’yan’uwa maza da mata, ina fatan za ku karanta wannan dan littafin da


kauna kuma zaku bashi kadan daga cikin lokutanku domin ku karanci jin kan


Islama, domin a tsame bil’adama daga sabanin da ya taso ta hanyar wadanda


suke kir-kiro karai-rayi akan islam ba tare da ilimi ba.


Muna maraba da tambayoyin ku game da Musulunci, kuma zamu ji dadin amsa


kushewar ku matukar muna iyawa.





Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin-kai


Allah babu abin bauta wa da gaskiya face Shi, Rayayye Tsayayye, gyangyadi


baya kama Shi bare barci, abin dake cikin sammai da kasa duk na Sa ne, waye


11


wannan da zai yi ceto a wurin Sa? Face da iznin Sa, yana sanin abin dake gaba


gare su da abin da ke bayan su, basu kewaye sani da wani abu na ilimin Sa face


da abin da Ya ga dama, kujerarSa ta yalwaci sammai da kasa, amma duk da haka


kiyaye su basu yi Masa nauyi Shine Madaukaki Mai girma. [Al-bakara-255].


Manufofin mu


Shine yada zaman lafiya a tsakanin mutane daban-daban, mu hada addinai


gaba daya ta hanyar fahimta, domin yaki da kiyayya wace masu tsauraran ra’ayi


suka haifar, yin aiki domin jin-dadin bil’adama gaba daya kuma da shiryar da


karkatattun rayuka zuwa ga tafarki ma dai-daici da zai kai ga rayuwa ta jin-dadi


mai gamsarwa.


Tsira da amincin Allah su tabbata a gareku.



Posts na kwanan nan

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A ...

BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA