
FALALAR GOMAN FARKO NA
ZUL-HIJJA
Hausa
FALALAR GOMAN FARKO NA
ZUL-HIJJA
FALALAR GOMAN FARKO NA ZULHIJJA
GABATARWA
Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai,
tsira da aminci su tabbata ga wanda aka aiko shi
rahama ga talikai, da alayensa da sahabbansa da
wanda ya bi sunnarsa, ya kuma yi koyi da
shiriyarsa har zuwa ranar sakamako. Bayan
haka:
Wannan wani taƙaitaccen saƙo ne, wanda ya
ƙunshi mafi muhimmancin abinda musulmi yake
buƙata a falalar goman farko na Zul-Hijja, mun
tattarashi dan masu ziyartar Harami biyu masu
daraja; domin su kasance cikin sani da fahimta
akan al'amuran addininsu, muna roƙon Allah
Mai karamci da Ya anfanar da shi, Ya sanya shi
mai kyau, kuma saboda Allah ne kaɗai; lallai Shi
ne Mafi alherin wanda ake roƙo, kuma Mafi
karamcin wanda ake fata.
Kwamitin ilimi na Kungiyar hidimtawa
Musulunci da yaruka daban daban.
FALALAR GOMAN ZUL-HIJJAH
Kwanaki goman Zul-Hijjah, falalarsu babba ce,
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya bayyanashi a cikin
LittafinSa, kuma ManzonSa Muhammad - tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi - ya
bayyanashi a cikin Sunnarsa, su ne kwanakan da
2
Allah - Maɗaukakin sarki - Ya rantse da su a cikin
LittafinSa da faɗinSa:
{Inã rantsuwa da alfijiri(1) Da darũruwa
gõma(2) } [al-Fajr: 1-2].
﴿
Su ne goman Zul-Hijjah kamar yadda Ibn Abbas,
da Ibn Zubair, da Mujahid, da Ibn Kathir, da Ibn
al-Qayyim, da wasu daga cikin salaf da khalaf
suka faɗa1 .
Su ne kwanakan da aiki a cikinsu yafi alheri fiye
da jihadi domin Allah - Maɗaukakin sarki -;
saboda hadisin Ibn Abbas - Allah Ya yarda da su -, ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi - ya ce: "Babu wasu
kwanakan da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi
soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan
kwanakin goma", Suka ce: Ya Ma’aikin Allah,
har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah? Sai
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi - ya ce: "Har Jihadi domin
ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya
fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da
.
komai ba"2
1Tafsirin Ibnu Kathir (4/106), da Zad al-Ma'ad (1/56).
2Bukhari ne ya ruwaito shi, da Tirmizi kuma lafazin nasa ne.
3
FALALAR AYYUKA A CIKIN KWANUKA
GOMA NA ZUL-HIJJA:
1- Aikin Hajji da Umara, suna daga mafifitan
ayyuka a cikin wannan goman; saboda faɗin
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi -: «Wanda duk ya ziyarci wannan ɗaki, bai
yi kwarkwasa ba, kuma baiyi fasiƙanci ba; zai
dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta
haifeshi». A cikin wani lafazin na Muslim:
«Wanda duk ya ziyarci wannan ɗakin, bai yi
kwarkwasa ba, kuma bai fasiƙanci ba; zai
dawo kamar ranar da mahaifiyarsa ta
haifeshi»1
. Saboda faɗinsa: (Duk wanda ya zo
wannan ɗãki) yana ɗauke da ma'anar aikin Hajji
da Umara kuma godiya ta tabbata ga Allah.
Wanda yabo da aminci suka tabbata a gareshi ya
ce: «Umra zuwa Umra kaffara ce ga abinda ke
tsakaninsu, kuma kuɓutaccen Hajji ba shi da
wani sakamako sai Aljanna»2 .
2- Na biyu: Azimin kwanaki tara, ko abin da ya
sawwaƙƙa daga cikinsu; saboda faɗin Annabi -
tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -.
«Babu wasu kwanaki da aiki na ƙwarai a
cikinsu ya fi soyuwa a wurin Allah sama da
1Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
2Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
4
waɗannan kwanaki goman». Kuma azumi yana
daga cikin mafi girman ayyukan alheri, Manzon
Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi - ya kwaɗaitar zuwa gare shi, kuma ya
kwaɗaitar, daga hakan akwai faɗinsa - tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi -: «Babu wani
bawa da zai yi azumin yini ɗaya a tafarkin Allah
sai Allah Ya nisantar da fuskarsa daga wuta
(tsawon) shekara saba'in». 1
3- Ana shar'anta yin layya a ranar babbar sallah
da kuma kwanakin Tashriƙ, haƙiƙa ya tabbata
cewa Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata
a gare shi -: «Ya yi layya da raguna biyu masu farar
fuska da baƙi-baƙi masu ƙaho, ya yanka su da
hannunsa, ya ambaci Allah ya yi kabbara, kuma ya
ɗora ƙafarsa akan fatun wuyayensu». 2
Daga A'isha - Allah Ya yarda da ita - ta ce:
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata
a gareshi - ya ce: «Babu wani aiki da ɗan Adam
zai yi a ranar babbar sallah da yafi soyuwa ga Allah
fiye da zubar da jini, kuma za'a kawo shi ranar
alƙiyama da ƙahonninsa da gashinsa da ƙafafunsa,
kuma lallai jinin yana faɗuwa a wajen Allah a wani
1Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
2Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
5
da shi»1
wuri kafin ya faɗi a ƙasa, don haka ku daɗaɗa rai
.
Kuma idan goma ga watan Zul-Hijjah ya shiga;
wanda yake son yin layya ya dakatar da cirar
wani abu daga gashinsa da fatar jikinsa; saboda
hadisin Ummu Salamah - Allah Ya yarda da ita -
daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi - cewa shi ya ce: «Idan kun ga jinjirin
watan Zul-Hijja kuma ɗayanku yana son ya yi
layya; to ya kame daga (cirar) gashinsa da
faratansa». Kuma a cikin wani Lafazin: «Kada ya
cire wani abu daga gashinsa ko faratansa har sai
.
ya yi layya»2
4- Kabbara, da Hailala, da ambaton Allah a cikin
waɗannan kwanaki goman da kwanukan
Tashriƙ; saboda hadisin Abdullahi Ibnu Umar
Allah Ya yarda da su- daga Annabi -tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi- ya ce: «Babu
wasu kwanaki da suka fi girma a wurin Allah
kuma mafi soyuwa a gare shi daga aiki a
cikinsu kamar waɗannan kwanaki goman, don
haka ku yawaita: Hailala, da Kabbara, da
Hamdala a cikinsu»3 .
1Tirmizi ne ya rawaito shi.
2Muslim ne ya rawaito shi.
3Ahmad ne ya ruwaito shi.
6
Kabbara kashi biyu ne kamar haka:
Sashe na farko: Kabbara kai tsaye, wadda ba ta
ƙayyadu da bayan salloli; sai dai ana shar'anta ta
a kowane lokaci.
Ana fara kabbara kai tsaye a idin layya daga
farkon goman Zul-Hijja zuwa ƙarshen ranar
kwanukan Tashriƙ: A dukkanin lokuta, a dare, da
rana, da hanya, da kasuwanni, da masallatai, da
gidaje, da kuma a duk wurin da ya halatta a
ambaci Allah - Maɗaukakin sarki -.
Sashe na biyu: Kabbara abar ƙayyadewa: Ita ce
wadda ake ƙayyadeta da bayan salloli a idin
layya musamman, da lokacinsa, kuma sifarta
kamar haka:
Na farko: Kabbara abar ƙayyadewa tana
farawane bayan sallar Asuba ranar Arfa, kuma
tana ƙarewa bayan sallar La'asar a rana ta uku na
kwanukan Tashriƙ. Wannan ga wanda ba
mahajjaci ba, amma mahajjaci kabbara abar
ƙayyadewa a haƙƙinsa tana farawa ne daga
Azahar ranar layya.
Na biyu: Siffar Kabbara: “Allahu Akbar, Allahu
Akbar, La'ilaha illallahu, Allahu Akbar Allahu
Akbar walillahil hamd” (Allah ne Mafi girma,
Allah ne Mafi girma, babu abin bautawa da
7
gaskiya sai Allah, Allah ne Mafi girma, Allah ne
Mafi girma, godiya ta tabbata ga Allah)1 .
5- Kula da yin sallar idi ga wanda ba mahajjaci
ba, da zuwa da wuri, da sauraron huɗuba; domin
tana daga cikin mafi girman alamomin
Musulunci; kuma saboda girman al'amarinta ne
aka umarci mata su fita zuwa gare ta har ma da
budurwai da masu haila; daga Ummu Aɗiyya -
Allah Ya yarda da ita - ta ce: «Mun kasance ana
umartar mu da mu fito ranar idi, harma mu
fito da budurwan da suke cikin budurcinsu,
har da masu haila ma mu fito da su sai su zama
a bayan mutane, sai suyi kabbara tare da
kabbarar masu sallah suyi addu`ah da addu`ar
su, suna masu fatan samun albarkar wannan
yini da kuma tsarkinsa». Kuma a cikin wani
Lafazin: «Ya umarci mata masu haila da su
nisaci wuraren sallar musulmai»2 .
6- Yawaita ayyuka na gari, daga cikin nafilfili na
ibada: Kamar sallah da sadaka, da karãtun Al
ƙur'ani mai girma, da umarni da kyakkyawa da
hani daga mummuna, da kyautatawa maƙwabta,
da sãda zumunci da sauran ayyuka na gari,
saboda faɗin Manzon Allah - tsira da amincin
1Ka duba: "al-Mughni na Ibni Qudama" (3/290), da "al-Sharhin al
Kabir tare da al-Muqni' da al-Insaf" (5/380).
2Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi.
8
Allah su tabbata a gareshi -: «Babu wasu
kwanaki da aiki na ƙwarai a cikinsu ya fi
soyuwa a wurin Allah sama da waɗannan
kwanakin goma". Suka ce: Ya Manzon Allah,
har jihadi domin ɗaukaka addinin Allah? Sai
Manzon Allah - tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi - ya ce: «Har jihadi domin
ɗaukaka addinin Allah, sai dai mutumin da ya
fita da kansa da dukiyarsa, kuma bai dawo da
komai ba». 1
Allah ne abin roƙo Ya amfane mu da abin da
muka sani, kuma Ya sanar da mu abin da zai
amfane mu, lallai cewa Shi Mai yawan kyauta ne
kuma Mai girma ne, tsira da amincin Allah su
tabbata ga Annabinmu Muhammad da iyalansa
da amincin Allah mai yawa.
1Bukhari ne ya rawaito shi, da Tirmizi.
9
Teburin bayani
Falalar goman farko na Zul-Hijja .................................... 2
Gabatarwa .................................................................................. 2
Falalar goman Zul-Hijjah .................................................... 2
Falalar ayyuka a cikin kwanuka goma na zul-hijja: ... 4