Labarai




WALLAFAR


ABDURRAZAQ BN ABDULMUHSIN AL-BADR


FASSARAR: TAJUDDIN ISA IBRAHIM


WANDA YAYI BITA: SURAJ BALA UMAR


AN BUGA DA DAUKAR NAUYIN WASU DAGA MUHSINAI


ALLAH YAYI MUSU SAKAYYA DA ALHERI YA GIRMAMA LADANSU


BUGU NA FARKO


1432H – 2011M


~ 3 ~


DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI


Godiya ta tabbata ga Allah, muna gode maSa, muna neman taimakonSa,


kuma muna neman gafararSa. Muna neman tsarin Allah daga sharrukan


kawunanmu da munanan ayyukanmu, wanda Allah Ya shiryar to babu maiiya batar


dashi, kuma wanda Ya batar to babu mai iya shiryar dashi. Kuma ina shaidawa


cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ba Shi da abokin tarayya,


kuma ina shaidawa lallai Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne,


Allah Yayi tsira gareshi da alayensa da sahabbansa baki daya, yayi aminci, aminci


mai yawa.


Bayan haka:-


Lallai taken wannan sakon: [Wajibin mu game da sahabbai masu girma –


Allah Ya yarda da su], shi wajibi ne mai girma, kuma abin nema ne babba, yana


cancanta garemu baki daya mu kiyaye shi iyakar himmar mu, kuma mu lura da shi


matukar lura.


Kuma mai karatu mai girma ya sani, lallai wajibinmu game da sahabbai


wani bangare ne daga wajibinmu game da addininmu, addinin Musulunci wanda


Allah Ya yarda dashi ga bayinSa, kuma bazai karbi wani addini wannisa daga


garesu ba, kamar yanda- Madaukakin Sarki- Ya ce: {Lalle ne, addini a wurin


Allah, shine Musulunci.} [al-Imran: 19], kuma kamar yanda -Madaukakin Sarki-


Ya ce: {Kuma wanda ya nemi wanin Musulunci ya zama addini, to, ba za’a karba


daga gare shi ba. Kuma shi a Lahira yana daga cikin masu hasara} [al-Imran: 85],


kuma kamar yanda- Madaukakin Sarki- Ya ce: {A yau Na kamala muku


addininku, kuma Na cika ni’imaTa a kanku, kuma Na yarda da Musulunci ya


zama addini a gare ku} [al-Ma’idah: 3].


To wannan addinin tsayayye da hanya mikakkiya, addinin Allah –Madaukakin


Sarki-, hakika Allah Ya zabar masa mai isarwa amintacce, kuma mai nasiha mai


hikima, Manzo mai girma, na’am shine (Annabi) Muhammad –tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi-, sai ya isar da wannan addini mafi cikar isarwa, kuma


ya bayyanashi mafi kamalar bayani, kuma ya tsaya da abinda Ubangijinsa -


alherinSa ya yawaita kuma Ya daukaka - Ya umarceshi da shi akan mafi cikar


fuska,kuma mafi kamalar hali, AllahYa fada gare shi:{Ya kai Manzo! Ka iyar da


abinda aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijin ka}.[al-Ma’idah:67], sai ya isar


~ 4 ~


da sako, ya bayar da amana, ya yiwa al’umma nasiha, ya yi jihadi cikin lamarin


Allah hakikanin jihadinsa har mutuwa tazo masa, bai bar wani alkhairi ba face ya


shiryar da al’umma akansa, kokuma wani sharri face ya tsawartar dashi daga gare


shi, Allah –Madaukakin Sarki- ya fada Yana Mai yin baiwa ga bayinSa: {Shine


wanda Ya aikowa (Larabawa), ummiyai (wadanda basa karatu da rubutu)


Manzo daga cikinsu yana karanta musu ayoyinSa, kuma yana tsarkake su,


kuma yana sanar da su Alkur’ani da Hikima ko da yake sun kasance daga


gabaninsa lalle suna cikin bata mabayyani} [Suratal-Jumu’ah:2].


Annabin mu –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya isar da addini


Allah akan cika da kamala, yayi nasiha ga al’umma matukar nasiha, kuma ya


bayyana musu hujjah kuma ya bayyana musu hanya, tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi.


Kuma hakika Allah –Madaukakin Sarki- Ya zabi sahabbai masu girma ga wannan


Manzo mai girma, kuma mataimaka adalai, kuma al’umma amintattu, sun taimake


shi, kuma sun girmama shi, sun karfafe shi,sun taimaki addinin Allah –alherinSa


ya yawaita kuma Yadaukaka - sai suka kasance –Allah Ya kara yarda agare su-


mafi alkhairin sahabbai ga mafi alkhairin wanda ya rayu a bayan kasa – Manzon


Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-sun kasance sahabbai ne masu


da’a, kuma ‘yan uwa masu karamci, mataimaka karfafa, sun taimaki addinin Allah


–Madaukakin Sarki- sun karfafeshi, sai suka kasance mafiya alkhairin mataimaka


ga yada shi da kuma taimakonsa.


Mamakin ni’imar su da karamcin su! mamakin ni’imarsu da daukakar darajar


su! Mamakin girman matsayin su! Mamakin kokarin da suka yi wajen taimakon


addinin Allah – alherinSa ya yawaita kuma Ya daukaka -!.


Allah Ya zabi wadannan sahabbai ga annabin sa –tsira da amincin Allah su


tabbata gare shi- akan ilimi da hikima, ya zabar masa adalai, sun kasance da


shaidar Ubangijin talikai da shaidar Manzo mai girma –tsira da amincin Allah su


tabbata gare shi- mafiya alkhairin mutane bayan annabawa, kamar yadda Allah –


Madaukakin Sarki Ya fada: {Kune mafi alherin al’umma wadda aka fitar daga


mutane} [al-Imran: 110], kuma farkon wadanda zasu shiga cikin wannan sune


sahabban annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- su suna shiga cikin


wannan yabon shiga na farko.


~ 5 ~


Yazo cikin (SAHIHAIN)1 daga annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi- yace: “Mafi alherin mutane karnina, sannan masu biyo mu su, sannan ma


su biyo musu”.


Wannan zabi ne da sahabbai da Ubangijin talikai Yayi musu shaida da shi,


kuma Manzon Allah mai girma –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yayi


musu shaida da shi, sun kasance tabbas zababbu, adalai, amintattu, matabbata,


shuwagabanni, shiryayyu, Allah Ya kara yarda a gare su.


Don haka, ya wajaba a gare mu mu kiyaye cewa zance game da sababbai –


Allah Ya yarda a gare su- da abinda ya wajaba a kanmu a game dasu,shi wani


yanki ne daga addini, kuma sashe ne daga akidar Musulunci, kuma sashe ne daga


imani wanda muke bautawa Allah – alherinSa ya yawaita kuma Ya daukaka- da


shi, domin idan aka duba littattafan akida wadanda shuwagabanni magabata suka


rubuta a da can da yanzu, ba zaka sami littafi daga cikin su daya wofinta daga


bayanin akida dangane da sahabbai ba.


❖ TAMBAYAR DA TAKE TASOWA:


Me yasa wajibin mu game da sahabbai ya zamo bangare ne daga wajibin mu game


da addini?!


Ina cewa: Lallai sahabbai –Allah Ya yarda da su- sune madauka wannan addinin


masu nakalto shi ga al’umma, hakika Allah –Madaukakin Sarki- Ya daukaka su,


kuma Ya girmama su da jin addinin sa daga Manzon Allah –tsira da amincin Allah


su tabbata a gare shi- kuma Ya daukaka su da ganin bullowar shi da ganinsa -tsira


da amincin Allah su kara tabbata a gare shi - kuma Ya daukaka su da jin zancensa


daga gare shi ba tare da wata wasidah ba, sai suka gan shi, suka ji hadisinsa, suka


haddace shi,suka kiyaye shi, sukaciratoshi ga al’ummar Musulunci.


Shin za’a samiwani hadisi daga hadisan Annabi –tsita da amincin Allah su


kara tabbata a gare shi- da zasuyi daidai a zance ko a aikace- daya sadu damu bata


hanyar sahabbai-Allah Ya yarda da su ba-?!


Idan ka bude littattafan sunnah, (Sahihul Bukhari) ko (Sahihu Muslim) ko


(Sunan) ko (Masanid) ko (Ma’ajim) ko bangarori na hadisai, zaka samu isnadi


yana farawa ne daga mawallafi: Wane ya bamu labari daga wane daga wane har


1 Bukhari(2652), da Muslim (2533) daga hadisin Ibn Mas’ud- Allah Ya yarda da shi-


~ 6 ~


zuwa ya sadu zuwa ga sahabin daya rawaito daga annabi –tsira da amincin Allah


su kara tabbata a gare shi. Dukkannin hadisai da suka inganta suka tabbata daga


Manzon Allah –tsira da amincin su tabbata a gare shi- a hanyar mu zuwa ga annabi


–tsira da amincin Allah su kara tabbata agare shi- (ta hanyar) wani sahabi ne


babba.


❖ ADALAR SAHABBAI:


Sahabbai –Allah Ya yarda da su- gaba dayansu adalai ne, Allah-Madaukakin


Sarki- Ya addalasu kuma Ya amintar da su a cikin littafinSa, kuma annabinSa-


tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- ya amintar da su, da wannan ne


hanyar shuwagabanni da magabata da malaman sunnah ta gudana a hadisan da aka


rawaito daga annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- suyi bincike a


adalar marawaitan su, da matsayin su na daga aminci da rauni, kuma suyi bincike


cikin halin ko wane maruwaici a isnadi, shin amintacce ne ko mai rauni ne, shin


adali ne ko ba adali bane, kuma idan isnadi ya sadu izuwa ga sahabi ba’a bincike a


wannan mas’alar, domin sahabbai –Allah Ya yarda da su- adalai ne amintattu,


saboda haka idan ka duba cikin littattafan Ilal da littattafan Rijal tun daga zamanin


tabi’ai da wadanda suke bayan su zaka sami ko wane daya daga cikin su suna


magana ne game da halinsa, suna cewa: Wane amintacce ne, wane tabbatacce ne,


wane hafizi ne, wane mai rauni ne, wane kaza…… sai fa sahabbai babu wani


wanda yake magana a kansu , shin su adalai ne ko ba adalai ba ne, shin amintattu


ne ko ba amintattu ba ne?


Sababi a wannan cewa su dukkan su ababen addalawa ne, Ubangiji –


Madaukakin Sarki- Ya addala su da ManzonSa –tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi-, kuma wannan a cikin ayoyi ne da yawa daga Al-kur’ani, da hadisai masu


yawa daga Manzo mai girma–tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-.


❖ SAHABBAI –ALLAH YA YARDA DA SU- SUNE MACIRATA


WANNAN ADDININ:


Sahabbai –Allah Ya yarda da su- sune macirata wannan addinin, sun jiyo shi


daga Manzon Allah –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma sun


kiyaye shi kamar yanda suka jiyo shi, kuma sun isar da shi ga al’umma da dukkan


amana da aminci, kuma harshen halin kowane daya daga cikin su yana cewa:


wannan shine abinda muka ji daga Manzon Allah –tsira da amincin Allah su


~ 7 ~


tabbata a gare shi- kuma mu muna isar da shi gare ku a cike a kammale kamar


yanda muka jiyo shi.


Wadancan sahabbai sun sami hazzi mai yawa da rabo cikakkedaga addu’ar


annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yayin da yace “Allah Ya


ni’imtar da mutumin da ya jiyo wani hadisi daga gare mu sai ya kiyaye shi har ya


isar da shi”2, shin kun san wani daya daga wannan al’ummar daya rabauta da


wannan addu’ar mai girma irin yanda sahabbai – Allah Ya yarda da su - suka


rabauta da ita?


Sun kiyaye addini kuma sun kiyaye hadisan Manzo mai karamci- tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma sun riskar da su ga al’umma tsarkakku,


tatattu, cikikku kammalallu, da dukkan amana da aminci da dukkan zurfafawa da


kula, haka nan sha’anin su yake –Allah Ya yarda da su-.


Sun kasance tare da annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- suna


lazimtar majalisansa, kuma suna gogayya akan halartar su da jin hadisan sa, kuma


suna haddace su, zuciyoyin su suna kula da su, kuma suna cirato su ga al’ummar


Musulunci.


❖ HADISI DAGA SAHABBAI –ALLAH YA YARDA DA SU- SHI


HADISI NE DAGA ADDINI:


Idan sahabbai-Allah Ya yarda da su- sun kasance da wannan martabar


madaukikiya, da matsayi mai girma, shin hadisi daga gare su bazai zamo wani


bangare daga hadisi daga addini ba, alhali sune maciratan sa kuma madaukan sa ga


al’umma? kowane hadisi da yake isowa garemu daga annabi-tsira da amincin Allah


su tabbata a gare shi- to daya daga sahabbai yana tsaka-tsaki a cikin isowarsa


izuwa garemu, sai hadisi daga garesu ya zamo wani bangare daga hadisi a cikin


wannan addinin.


2 Abu Dawud ne ya rawaito(3662), da Tirmizi(2656), da Ibn Majah(230) daga hadisin Zaid bn Thabit-Allah Ya kara


yarda a gare shi-, kuma an rawaito shi daga jama’a daga sahabbai da lafuzai mabanbanta kuma Albani ya inganta shi


a cikin (SAHIHA)(404).


~ 8 ~


❖ SUKA GA SAHABBAI-ALLAH YA YARDA DA SU- SUKA NE GA


ADDINI:


A daya bangaren kuma, lallai suka gare su –Allah Ya yarda da su- suka ne ga


addinin kansa, kamar yanda malamai suka ce: (Suka ga mai ciratowa suka ne ga


abin ciratowar). Idan wanda ya cirato addini izuwa garemu sune sahabbai – Allah


Ya yarda da su- abin suka ne agaresu kuma abin magana ne a adalarsu, kuma abin


magana ne a amincinsu da amanarsu, to ta yaya sha’anin addini zai kasance, idan


wanda ya cirato addini izuwa garemu zai kasance abin suka? Addini a zatin sa zai


kasance abin suka ne, saboda wannan malami mai girma kuma hafizi mai daraja


Abu Zur’ah al-Razi – Allah Yayi masa rahma-yace: ‘Idan kuka ga mutum yana


tauye daya daga sahabban annabi –tsira da amincin Allah su tabbata a gare


shi-, to ku sani shi zindiki ne, wannan domin Manzo- tsira da amincin Allah


su tabbata a gare shi- gaskiya ne a wajenmu, kuma Al-kur’ani gaskiya ne,


kadai sahabban Manzon Allah –tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare


shi- su suka isar da wannan Al-kur’anin izuwa gare mu da sunnah, kadai


suna so su raunata shaidun mu don su bata Al-kur’ani da sunnah ne, kuma


raunatawa gare su shi yafi, kuma su zindikai ne3.


Idan sahabbai –Allah Ya yarda da su- suka kasance ba amintattu ba ba kuma


adalai ba, to ina ga addinin da muke bautawa Allah da shi?


Kuma wasu jama’a daga mutane suna kutsawa cikin bata, sai su dinga suka ga


sahabbai gaba dayan su sai jama’a kadan suna kirga su da yatsu, to sai ace musu:


Idan al’amari ya kasance a wannan hali, to ina addinin (yake)? Ta yaya za’a san


addinin Allah? Ta yaya za’a bautawa Allah? Ta yaya za’a yi maSa sallah ayi maSa


sujjadah? Ta yaya za’a bada farillanSa? Ta yaya za’a yi hajji izuwa ga dakinSa? Ta


yaya za’a tsaya ga yi maSa biyayya?!Ta yaya za’a kare daga umarnin Sa? Idan aka


yi suka ga maciratan kuma madaukansa sune sahabban annabi mai girma, -tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi-.


Don haka, yake wajaba a kan mu damu kiyaye cewa suka ga macirata addini-


sune sahabbai- suka ne ga addinin kansa, kuma mu kiyaye a cike cewa wajibin mu


game da sahabbai wani sashe ne daga wajibin mu game da addinin mu, domin su


su suka cirato shi, to idan akayi suka gare su anyi suka ga addini.


3 (Al-kifayah fi ilmil ruwayah) na Khadib al-Bagdadi (shafi na 49).


~ 9 ~


❖ ADALAR SAHABBAI:


To ta yaya za’a yi suka gare su alhali wanda ya addala su shine Ubangijin


talikai a littafinSa mabayyani a ayoyi masu yawa daga gare shi, bari dai Ubangiji –


Madaukakin sarki- Ya bada labari cewa Ya yarda dasu suma sun yarda da Shi,


Allah –Madaukakin Sarki Ya ce: {Magabata na farko daga Muhajirina da Ansar


da wadanda suka bi su da kyautatawa Allah Ya yarda daga gare su su kuma sun


yarda daga gare Shi} [al-Tauba:100].- Madaukakin Sarki- Ya bada labari cewa Ya


yarda da su, shin Allah Zai yarda da wanda bai kasance amintacce ba a cikin


nakalto addini? Shin –Madaukakin Sarki- Zai yarda da wanda yake maha’inci cikin


isar da zancen Manzo mai girma - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-?!


Faufau-faufau! A’a ba haka ba! Allah Ya yarda da su, domin su amintattu ne


adalali, kuma domin su shuwagabanni ne zababbu, kuma domin su masu isar da


addininSa ne ta mafi cikar fuska da mafi kyawun hali,{Allah Ya yarda da suma sun


yarda da Shi}.


Kuma –tsarki ya tabbatar maSa- Ya fada cikin wata ayar daban: {Lalle ne


hakika, Allah Ya yarda da muminai a lokacin da suke yi maka mubaya’a a


karkashin itaciyar nan} [al-Fathi:18], adadin su ya kasance ya kasance sama da


dubu, kumadukkansu hakika Allah Ya yarda dasu.


Kuma –tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya fada a cikin sha’anin


ma’abota Badar: “Kuma me ya sanar da kai watakila Allah Ya kasance ya yi


tsinkaye akan ma’abota Badar, sai Yace: ku aikata abinda kuke so, hakika Na


gafarta muku”4, to wannan tsarkakewa ce a bayan tsarkakewa, da yabo a bayan


yabo, da yabo mai girma mai bi a cikin Al-kur’ani mai girma da sunnar annabi –


tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, baza’a’iya kusa da kiyaye ayoyi da


hadisan da suke yabo ga sahabbai- Allah ya kara yarda dasu - ba.


Bari dai yabo ga sahabbai bai zo a cikin Al-kur’ani kadai ba, bari lallai yabo


garesu ya rigayi samuwarsu akan kasa, hakika yabo gare su yazo a Attaura da Injila


tun kafin a haliccesu, kuma tun kafin a samar da su. A cikin wata ayar daban daga


surar Al-Fathi Allah Ya fada game da sahabbai –Allah Ya yarda dasu -:


{Muhammadu Manzon Allah ne. Kuma wadanda da ke tare da shi masu tsanani ne


a kan kafirai, masu rahama ne a tsakanin su, kana ganin su suna masu ruku’i masu


4 Bukhari ne ya fitar dashi (3007), da Muslim (2494) daga hadisin Aliyu-Allah Ya kara yarda a gare shi-.


~ 10 ~


sujjada, suna neman falala daga Ubangijin su, da yardarSa. Alamar su tana a cikin


fuskokinsu, daga kufan sujjuda}. To Ubangiji- Madaukakin Sarki- Yana yabo ga


sahabbai, to ina irin wannan misalin kuma a wane littafi?- Madaukakin sarki Yana


cewa: {Wannan shi ne siffar su a cikin Attaura. Kuma siffar su, a cikin Injila


itace kamar tsiron shuka wanda ta fitar da reshenta, sa’an nan ta karfafa shi,


yayi kauri, sa’an nan ta daidaita a kan tushiyarta, tarika kayatar da manoma


domin, (Allah) Ya fusatar da kafirai game da su. Kuma Allah Ya yi wa’adi ga


wadanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan kwarai, daga cikinsu, da


gafara da lada mai girma}. [Surar al-Fathi: 29], wannan yabo ne mai kamshi ga


sahabbai masu girma -Allah Ya yarda a da su- abin ambata a Attaurah, kuma abin


ambata a Injila.


To wannan ayar mai girma tana bayyana maka –ya kai dan uwa musulmi- cewa


Ubangiji Mai girma Yayi yabo ga sahabbai kuma Ya tsarkake su kuma Ya addala


su a Attaurah da Injila da Al-kur’ani, yabo mai girma da yabo madaukaki da


tsarkakewa madaukakiya ga wadannan zababbu da shuwagabanni adalai, sai Ya


yabe su tun kafin a same su, kuma Ya yabe su tun kafin a halicce su a yayin da Ya


saukar da littafinSa Attaurah ga (annabi) Musa- tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi-, da yayin da Ya saukar da littafinSa (annabi) Injila ga (annbi) Isah-tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi-, sannan Yayi yabo gare su alhalin su suna a


bayan kasa a littafinSa Al-ku’ani wanda Ya saukar ga (annabi) Muhammad- tsira


da amincin Allah su tabbata a gare shi-.


Haka nan muna karanta wani yabo daban ga sahabbai-Allah Ya yarda da su-


daga Ubangijin talikai a surar al-Hashri a yayin da Allah –Madaukakin Sarki-


Yake cewa: {(Za’a bayar da dukiyar) ga mataulata masu hijira wadanda aka


fitar dasu daga gidajen su da dukiyoyin su, don neman falala daga Allah da


kuma yardarSa, kuma suna taimakon (addinin) Allah da ManzonSa! Wadannan


sune masu gaskiya} [Surar al-Hashri: 8]. Sai Allah –tsarki ya tabbatar maSa- Ya


siffantasu da fadinSa {Wadannan sune masu gaskiya}, sannan Yace game da al-


Ansar (Mutanen Madina): {Da wadanda suka tanadi gida (mutanen Madina) kuma


suka (karbi) imani gabaninsu (masu hijira), suna son wadanda sukayi hijira zuwa


garesu}, ai suna son al-Muhajirun (wadanda suka yi hijira), {Kuma basa samun


wani kyashi a cikin kirazan su daga abin da aka baiwa muhajiruna, kuma suna


fifita (masu hijira) a kan kawunansu, kuma ko da suna da wata larula. Wanda


~ 11 ~


aka kiyayeshi daga son kansa, to wadannan su ne masu babban rabo} [Surar al-


Hashri:9].


To wannan yabo ne ga Muhajirun da Ansar, kuma sahabbai- kamar yanda baya


buya- kaso biyu ne; Muhajirun da Ansar.


Muhajirun: Mutanen Makkah wadanda suka bar dukiyoyin su da gidajen su


suka yi hijira saboda Allah, {Suna neman falala daga Ubangijinsu, da kuma


yardarSa, kuma suna taimakon (addinin) Allah da ManzonSa!}. Sai suka bar komai


a bayansu kuma suka zo Madina suna taimakon Allah da ManzonSa, sai Allah Ya


fada game da su: {Wadannan sune masu gaskiya}, ai a cikin imaninsu, da cikin


abotakarsu,da cikin biyayyarsu, da cikin binsu da addinin Allah –alherinSa ya


yawaita kuma Ya daukaka-.


Allah –Madaukakin Sarki- Ya ce: {Daga muminai akwai wadansu mazaje da


suka cika abinda suka yiwa Allah alkawari da shi, sa’an nan a cikinsu, akwai


wanda ya hadu da ajalinsa, kuma daga cikin su akwai wanda ke jira. Kuma


basuyi kowace irin sabawa ba (game da alkawarin)} [al-Ahzab:23].


Wadannan sune sahabbai -Allah Ya kara yarda agare su-, Ubangiji –


Madaukakin Sarki- Yana yin yabo garesu (irin) wannan yabon mai albarka mai


kamshi.


Kuma kamar yanda Allah Yayi yabo ga Muhajirun, haka kuma Yayi yabo ga


Ansar, sai Ya ce: {Wadanda suka tanadi gida (mutanen Madina)}, abin nufi da


gida: Madina, kuma Ansar sun zauna a Madina tun kafin Muhajirun, sai dai mai


Ansar suka aikata a yayin da Muhajirun sukazo musu? Sun raba dasu cikin


abubuwan mallakarsu, sai ya zamo (mutum) Ansar guda daya yana bawa (mutum)


Muhajir rabin gidansa, da rabin dukiyarsa, kuma wannan fifitawa wadda Allah Ya


yabe su da ita: {kuma suna fifita masu hijira a kan kawunan su, kuma koda suna da


wata larura}, kuma Ansar da Muhajirun sun hadu akan taimakon addinin Allah-


alherinSa ya yawaita kuma Ya daukaka-, dukkan su mataimaka ne ga addinin


Allah, {kuma basu musanya ba, musanyawa}.


~ 12 ~


❖ MATSAYAR MUSULMI DANGANE DA SAHABBAI-ALLAH YA


YARDA DA SU:-


Wannan shine sha’anin su, to yaya ga sha’anin wadanda suka zo a bayan su-


wato muminai wadanda suka bisu da kyautatawa-?


Babu makawa mu fadakar da ku a nan; domin cewa Allah –Madaukakin Sarki-


da sannu Zai bayyana manhajin da ya kamata mumini ya zamo a kansa tare da


Muhajirun da Ansar a bayan zamanin su.


Allah Ya ce: {Kuma wadanda suka zo daga bayan su} ai bayan Muhajirun


da Ansar, {Suna cewa, Ya Ubangijin mu! Ka yi gafara agare mu, kuma ga


‘yan’uwanmu, wadanda suka riga mu yin imani, kuma kada ka sanya wani kulli


a cikin zukatanmu ga wadanda sukayi imani. Ya Ubangijin mu! Lalle Kai ne


Mai tausayi, Mai jin kai} [Surat al-Hashri:10].


To wannan ayar tana bayyana manhajin da ya wajaba ko wane mumini ya


kasance a kansa dangane da sahabbai -Allah Ya yarda da su-.


Kuma wannan wajibin yana takaita ne a cikin al’amura duga biyu -ka fadaka da su


sosai Allah Zai amfanar da kai dasu:-


Al’amari na farko: Kubutar zuciya dangane da sahabbai, zuciyarmu ta


kasance kubutacciya dangane da su, babu wani gilli ko hikidi ko kullaci, kuma


babu wata kiyayya ko adawa a cikinta, kadai a cikinta akwai soyayya da


kyautatawa da tausayi da kauna, kuma wannan muna karbarsa ne daga fadinSa:


{Kuma kada ka sanya wani gilli a cikin zukatan mu ga wadanda suka yi imani}. Ai


ka sanya zukatanmu su zama kubutattu dangane da wandanda suka rigayemu da


imani, sune ‘yan uwanmu, bari dai mafi alkhairin ‘yan uwanmu Allah Ya kara


yarda agare su, kuma saboda wannan Ya ce: {Kuma wadanda suka zo daga


bayansu, suna cewa, Ya Ubangijin mu! Kayi gafara agare mu, kuma ga ‘yan


uwan mu, wadanda suka rigamu yin imani}. A wata ayar daban kuma Ya ce:


{Magabata a na farko daga Muhajirun da Ansar} [al-Taubah:100], wannan ne


Allah -Madaukakin Sarki- Ya kebance su da shi.


Mu a yanzu muna cikin karni na goma sha hudu kumatsakanin mu da su akwai


karni da yawa, kuma su sun kasance tare da annabi-tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi- tun daga sanda aka turo shi, kuma suka taimake shi, kuma suka


~ 13 ~


girmama shi suka karfafe shi, kuma sun kasance tare da shi gefe da gefe, to mu


yanzu a ina muke daga gare su?!


Sun rigaye mu da imani, kuma sun rigaye mu da taimakon addini, kuma sun


rigaye mu da cewa Allah -Madaukakin Sarki- Ya daukakasu da abotakar annabi


mai girma- tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, kuma saboda wannan-


kuma kai kana addu’a ga sahabbai- ka tina rigayen su, kuma wannan ishara ce a


cikin aya mai girma yayin da Yace: {Ya Ubangijin mu! Kayi gafara agare mu,


kuma ga ‘yan uwanmu, wadanda suka rigamu yin imani} suna da wani hakki a


kanka a cikin wannan rigayen mai girma, kuma domin kasan darajarsu, ka halarto


da rigayensu wanda Allah -Madaukakin Sarki- Ya yabesu da shi: {wadanda suka


rigayemu da imani}.


Abin nufi dai hali na farko: Shine kubutar zuciya dangane da sahabbai, kuma


wannan muna rikarsa ne daga fadinSa: {Kuma kada ka sanya wani kulli a


zukatanmu ga wadanda suka yi imani}.


Hali na biyu: Kubutar harshe, babu zagi kuma babu alfasha babu la’anta kuma


babu suka, kadai addu’a, muna rikar wannan daga fadinSa: {Suna cewa Ya


Ubangijin mu! Kayi gafara garemu, da ‘yan uwanmu, wadanda suka rigamu}, shin


suna zagin wadanda suka rigayesu da imani?! Shin suna sukarsu?! Shin suna cin


mutuncinsu?! A’a ba haka ba, wannan baya daga sha’anin muminai, bari dai


sha’aninsu, kamar yanda Allah Ya fada ne: {Kuma wadanda suka zo daga


bayansu, suna cewa, Ya Ubangijinmu! Kayi gafara agare mu, kuma ga


‘yan’uwanmu, wadanda suka rigamu yin imani, kuma kada Ka sanya wani kulli


a cikin zukatan mu ga wadanda suka yi imani. Ya Ubangijinmu! Lalle Kai ne


Mai tausayi, Mai jin kai} [Surar al-Hashri:10].


Saboda haka ne, manhajin ma’abota imani dangane da sahabbai -Allah Ya


yarda da su-yake takaita a nukudodi guda biyu:


Ta farko: Kubutar zuciya.


Ta biyu: Kubutar harshe.


Na’am, zuciya tsarkakkiya, da harshe tatacce dangane da sahabbai masu girma -


Allah Ya yarda da su-.


~ 14 ~


❖ FALALAR SAHABBAI DA HARAMCIN ZAGIN SU:


Hadisi yazo cikin (SAHIHAIN) daga annabi -tsira da amincin Allah su tabbata


agare shi- yana tsawatar da al’umma daga zagin shabbai, kuma a daidai lokacin


yana bayyana musu matsayinsu, tsira da amincin Allah su kara tabbata agare shiya


fa ce: “Kada ku zagi sahabbaina, ina rantsuwa da wanda raina yake a


hannunSa, da dayanku zai ciyar da misalin dutsen Uhud na zinare, ba zai kai


mudun dayansu ko rabinsa ba”5.


Da daya daga sahabbai-Allah Ya yarda da su-, zaiyi sadaka da mudu daya


daga abinci ga miskinai, kai kuma kazo da misalin dutsen Uhud na zinare- kuma


wannan babu wanda zai iya daga cikinmu duk yanda dukiyarsa ta kai daya zo da


misalin Uhud na zinare yayi sadaka da shi-, kuma watakila da ace zinare zaizo


masa kwatankwacin dutsen Uhud, da sai ya fitineshi, ya fuskantoshi kuma ya wayi


gari yana mai kwauronsa yana mai rowa, sai dai, da za’a kaddara cewa daya daga


cikinmu yana da zinare misalin dutsen Uhud kuma yayi sadaka da shi to da ba zai


kai mudun daya daga sahabbai ba, to ku fadaka, kuma ku san darajar sahabbai da


matsayinsu -Allah Ya yarda da su-.


(Kada ku zagi sahabbai na), wannan zancen annabi ne-tsira da amincin Allah


su tabbata agare shi- kuma ba zancen daya daga mutane bane ko daga malamai,


kadai zancen Manzo ne-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, yana yiwa


al’umma nasiha kuma yana tsawatar da ita daga afkawa daya daga sahabbai ko


tauyewa daya daga cikinsu - Allah Ya yarda da su -, kuma yana fadakar wa izuwa


sanin darajarsu da matsayinsu.


Kuma hadisai daga gare shi-tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- a


cikin wanann babin suna da yawa sosai, yana bayyana sha’anin sahabbai da


matsayinsu da darajarsu a cikinsu, har sai da sashen malamai idan yana son ya


ware darajojin sahabbai a cikin wani littafin, ba zai iya tarawa ba a cikin mujalladi


daya, bari dai zai bukaci mujalladai da dai mujalladai da yawa, da manyan


littattafai da dai manyan littattafai domin yawan hadisai tabbatattu daga annabi-


tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin yabo ga sahabbai daidaiku da


jama’u.


5 Bukhari (3673) daga hadisin Abu Sa’id al-Khudary-Allah Ya yarda da shi-, da Muslim (2540) daga hadisin Abu


Hurairah-Allah Ya yarda da shi-.


~ 15 ~


Baubu abin bautawa da gaskiya sai Allah! Mamakin girman darajarsu,


mamakin girman matsayinsu, mamakin daukakar sha’aninsu, mamakin girman


wajibcin musulmai dangane da su, Allah Ya yarda da su.


To Allah -tsarki Ya tabbatar ma Sa-, Ya umarci ma’abota imani da addu’a ga


sahabbai da nema musu gafara sai suka aikata, sai dai sashen mutane sun akasta


umarnin sun juwa shi a baya, sai suka aikata akasin abinda aka nema daga gare su


a cikin Al’kur’ani, da akasin abinda aka nema daga garesu a cikin sunnar anabi -


tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi-, sai suka sanya zagi a maimakon


istigfari, suka a maimakon yabo, saboda haka ne yazo cikin (SAHIH MUSLIM)6


cewa A’isha -Allah Ya yarda daita- ta fadawa Urwatu dan Zubair: Ya kai dan ‘yar


uwata!An umarcesu da sunemawa sahabban annabi – tsira da amincin Allah


su tabbata agare shi –gafara amma sai suka zage su”.


Sai dai akwai wata hikima ga Allah – Madaukakin sarki a hakan, A’isha -


Allah Ya kara yarda a gareta- kamar yanda Ibn al’Asir ya kawo cikin littafinsa


(JAMI’UL USUL)7-: daga Jabir bn Abdallah- Allah Ya yarda da su- ya ce:


Ancewa A’isha: “Lalle wasu mutane suna sukar sahabban annabi -tsira da


amincin Allah su tabbata a gare su-, har Abu bakar da Umar, sai ta ce: To


menene kuke mamaki a wannan? Aiki ne ya yanke daga gare su, sai Allah Ya


so kar lada ya yanke daga garesu”.


Ta yaya haka? Mu muna sani, sani a bayyane daga sunnah cewa, wanda yake


suka ga waninsa tabbas za’a cire wannan daga kyawawan ayyukansa, ai daga


kyawawan ayyukan wannan mai sukar kuma a bawa wanda aka soka ba tare da


hakki ba, kamar yanda yazo a cikin hadisin maiwasoso, har kana sani daga cikinsa


me zai faru a ranar alkiyama ga wanda yake suka ga sahabbai. Annabi-tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi- ya fada ga sahabban sa wata rana: (Shinkun


san wanene mai wasoso?) Sukace: Ya Manzon Allah! Mai wasoso a cikinmu


shine wanda ba shi da dirhami ko kaya, sai yace: (Lallai mai wasoso daga


al’ummata zai zo ranar alkiyama da sallah da azumi da zakkah, kuma zaizo


lallai ya zagi wannan, yayi wa wannan kazafi, yaci dukiyar wannan, ya zubar


da jinin wannan, ya doki wannan, sai a bawa wannan daga kyawawan


6Lamba ta (3022).


7 Lamba ta (6366) amma bai ambaci wanda ya fitar da shi ba, kuma Ibn Asakir ya rawaito shi a tsarin musnad a


cikin (Tarikhu Dimashk) (44/387), da Khadib a cikin (Tarikhu Baghdad) (5/147).


~ 16 ~


ayyukansa, da wannan daga kyawawan ayyukansa, idan kyawawan


ayyukansa suka kare kafin abiya abinda yake a kansa, sai a dakko daga


kusakuransu sai a jefa a kansa sannan a jefashi cikin wuta)8. Muna rokon


Allah lafiya da aminci.


Wannan ga wanda yake zagin daidaikun musulmai kenan, to ina ga wanda


yake zagin sahabban annabi mai girma-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-


?! Na’am, mamakin girman musiba kuma mamakin tsananin musiba mai girma! A


yayin da wannan mai zagin zai gabato a ranar lahira sai a dakko daga kyawawa


ayyukansa a baiwa sahabbai masu girma, idan kyawawan ayyukansa suka kare a


dakko daga munanan ayyukan wanda ya soka a jefo a kansa, sai a jefa shi cikin


Jahannama. Babu abin bautawada gaskiya sai Allah! Ya mamakin girman musibar


wanda yake sukar sahabbai! Kuma mamakin bala’insa kuma mamakin razanin


babbar musibarsa a yayin da zaizo ranar alkiyamayana mai wasoso! Abu Bakar-


Allah Ya yarda da shi- zai karba daga kyawawanayyukansa, Umar ma -Allah Ya


yarda da shi-, zai karba daga kyawawan ayyukansa, Usman ma -Allah Ya yarda da


shi- zai karba daga kyawawan ayyukansa, matan annabi ma - Allah Ya kara yarda


a gare su- zasu karba daga kyawawan ayyukansa, hakanan sauran sahabbai masu


girma - Allah Ya yarda da su -.


Abin mamaki, Uwar muminai A’isha -Allah Ya yarda da ita- bata kubuta daga


sukarsu ba, tare da cewa Allah Ya kubutar da ita a cikin Al-kur’ani daga abinda


ma’abota kage suka jefeta da shi. Kuma (Allah) Ya saukar da aya a wannan a cikin


surat al-Nur, ana karantawa a harabobin musulmai har zuwa ranar alkiyama. Tare


da haka bai gushe ba, ana samun wanda yake suka gare ta. To mai zai kasance ga


A’isha a ranar alkiyama?lallai rabo ne mai girma daga kyawawan ayyuka, sannan


wannan mai sukar zai zo ranar alkiyama yana mai wasoso, domin cewa shi ya


maida kansa mai yawan suka, mai yawan la’anta ga sahabban annabi-tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi-, har wani sashen mutane yana wayar gari yana


tafiya yana mai suka da la’anta ga sahabban Manzon Allah -tsira da amincin Allah


su tabbata a gare shi-, - (muna neman) tsarin Allah-; Wannan yaya halinsa zai


kasance a ranar alkiyama a yayin da zai gamu da Allah - Madaukakin Sarki -!


Har ta kai sashen su yana cewa: Allah Ka la’anci gumakan Kuraishu guda biyu


da Dagutansu guda biyu da Kibdawansu guda biyu da ‘ya’yayensu, (sune) Abu


8 Muslim ne ya rawaito shi (2581) daga hadisin Abu Hurairah-Allah Ya yarda da shi-.


~ 17 ~


Bakar da Umar, tare da cewa annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-


ya fada game da sha’anin mumini gaba daya: “Mumini bai zamo mai yawan


suka ba, kuma bai zamo mai yawan la’anta ba, kuma bai zamo mai alfahsha


ba, kuma bai zamo mai zancen banza ba”;9 Bari dai a yayin da akace da annabi -


tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi-: Ya Manzon Allah!


kayimummunar addu’a akan mushrikai, yace: “Lallai ni ba’a turo ni mai yawan


la’anta ba”10; Sannan wasu jama’a daga tababbu suzo suna zabar tsarkakkun


wannan al’umma da zababbunta suna la’antar su! Muna neman tsarin Allah daga


tabewa.


❖ FIFIKO TSAKANIN SAHABBAI:


Hakika hadisi ingattace yazo daga annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi- wanda sama da sahabi daya daga sahabbai suka rawaito, daga cikinsu


akwai Aliyu bn Abi Dalib-Allah Ya yarda da shi- yana cewa: Tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi ya ce: “Abu Bakar da Umar sune shuwagabannin


gwarazan ‘yan aljanna daga (mutanen) farko da na karshe sai dai annabawa


da Manzanni”11, saboda wannan, lallai mafi alherin mutane a cikin aljanna bayan


annabawa da manzanni (sune) Abu Bakar da Umar-Allah Ya yarda da su-, kuma


sune mafifitan mutane bayan annabwa.


Yazo cikin (SAHIHUL BUKHARI)12 daga Ibn Umar-Allah Ya yarda da su-,


yace: “Mun kasance muna zaba tsakanin mutane a zamanin annabi -tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi-, sai muke zabar Abu Bakar, sannan


Umar ibn al-Khaddab, sannan Usman bn Affan-Allah Ya kara yarda a gare


su-“13, a wani karin a wurin waninsa: “Sai hakan ya isa zuwa ga annabi -tsira


da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- baya inkarin sa”.


9Ahmad ne ya fitar da shi (3949), da Bukhari a cikin {al-Adabul mufrad} (312), da Tirmizi (1977), da Hakim (1/12)


daga hadisin Ibn Mas’ud -Allah Ya kara yarda a gare shi-, Tirmizi ya fada: {Hadisi ne Hasan Garibi}, kuma Hakim


ya fada: {Sahihi ne akan sharadin Malamai biyu (Bukhari da Muslim)} kuma Zahabi ya dace da shi, kuma Albani ya


inganta shi a cikin {al-Sahiha} (312).


10 Muslim ne ya rawaito shi (2599) daga hadisin Abu Huraira-Allah Ya kara yarda a gare shi-.


11Ahmad ne ya fitar da shi(602), da Tirmizy(3666), da Ibn Majah(95), kuma an rawaito daga jama’a daga sahabbai,


kuma hakika Albani ya inganta su da dukkanin hanyoyin sa a cikin (al-Sahiha)(824).


12Lamba ta (3655).


13(al-sunnah) na ibn Asim (993), da (al-Musnad) da Abi Ya’ala (5604), da Dabarani cikin (Musnadul shamiyyin)


(1764) kuma ita kari ce ingatacciya, Albani ya ingantata a cikin (Zilalul Jannah) (1193).


~ 18 ~


Bari dai yazo a cikin (SAHIHUL BUKHARI)14 daga Muhammad bn al-


Hanafiyyah yace: Nace da babana-Aliyu bn Abi Dalib-Allah Ya yarda da shi-:


“Wane mutum ne mafi alkhairi bayan Manzon Allah-tsira da amincin Allah


su tabbata agare shi-? yace Abu Bakar, nace: Sannan wa? Yace; sannan


Umar, sai naji tsoron yace Usman, nace; Sannan kai! Yace: Ni ban zamo ba


face mutum daga musulmai”, wannan shine Aliyu-Allah Ya yarda da shi-.


Bari dai yazo daga Aliyu -Allah Ya yarda da shi- kamar yanda yazo cikin (AL-


SUNNAH)15 na Ibn Abi Asim- cewa yace: “Baya isowa gare ni daga wani daya


da yake fifitani akan Abu Bakar da Umar, face nayi masa bulala haddin mai


kage”, wannan zancen Amirul muminina ne, khalifa shiryayye Aliyu bn Abi


Dalib-Allah Ya yarda da shi-.


Don haka, yake kamata gare mu mu sani cewa daga wajibin mu game da


sahabbai, mu san fifikon dake tsakaninsu, kuma menene jerantawar da take


tsakanin su a fifiko; domin mu bawa ko wane mai hakki hakkinsa, shin ba Allah ne


Ya fada ba a Alkur’ani: {Wanda ya ciyar a gabanin bude (Makka), kuma yayi


yaki, baya zama daidai (da wanda bai yi haka ba). Wadannan su sukafi girman


daraja bisa ga wadanda suka ciyar daga baya kuma suka yi yaki, kuma


dukkansu Allah Yayi musualkawarin aljanna, kuma Allah Masani ne ga abin da


kuke aikatawa} [Surat al-Hadid:10], mai kyau wato aljanna, kuma cin nasara


shine bude Makkah, ance: Abin nufi dashi sulhun Hudaibiyyah. Wadanda suka


yiwa annabi-tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- mubaya’a a


karkashin wannan bishiyar a ranar sulhun Hudaibiyyah, basa zama daidai a imani


da matsayi, da sha’ani, da daraja tare da sahabban da suka musulunta bayan cin


nasara kuma suka yi yaki, banancine tsakanin wadancan da wadancan, kuma


dukkansu sahabbai ne, kuma dukkansu ma’abota imani ne, kuma dukkansu suna


aljanna.


❖ TO SAHABBAI AKWAI FIFIKO A TSAKANIN SU:


Mafifitan sahabbai: wadanda sukayi mubaya’a a karkashin wannan bishiyar,


kuma mafifitan wadannan: wadanda suka halarci Badar, kuma mafifitan


wadannan dukkan su,goma da aka yi wa albishir da aljanna, wadannan goma ne


daga sahabban annabi-tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi-,da yayi


14Lamba ta (3671).


15Lamba ta (1219), kuma Ahmad ya rawaito shi cikin (Fada’ilul Sahabah) (49).


~ 19 ~


musu shaida -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi-a majlisi daya da


cewa suna cikin aljanna, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- ya nassanto


nassin daya kara musu daukaka cewa su suna cikin aljanna madawwamiya a


majlisi daya, kamar yadda yazo a cikin hadisin da Tirmizi ya rawaito shi da Imam


Ahmad da wasunsu, daga Abdurrahman bn Auf-Allah Ya kara yarda a gare shi-


yace: Naji Manzon Allah -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yana cewa:


“Abubakar yana cikin aljanna, Umar yana cikin aljanna, Usman yana cikin


aljanna, Aliyu yana cikin aljanna, Dalha yana cikin aljanna, Zubair yana


cikin aljanna, Abdurrahman bn Auf yana cikin aljanna, Sa’ad bn Abi


Wakkas yana cikin aljanna, Sa’id bn Zaid bn Amr bn Nufail yana cikin


aljanna, kuma Abu Ubaidah bn Al-Jarrah yana cikin aljannah”,16 to wadnnan


goman, annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yayi musu shaida da


cewa suna cikin aljanna a majlisi daya, sai suka kasance suna tafiya akan kasa


alhali su suna sanin cewa suna cikin aljanna, mai gaskiya amintacce-tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi- yayi musu shaida, kuma mamakin girman ta


kuma mamakin karamcin ta daga shaida, yana tafiya a bayan kasa alhalin yana


sanin cewa shi ranar alkiyama yana daga ‘yan aljanna.


Kuma mafifitan wadannan goman: Khalifofi hudu, kuma mafifitan


khalifofin hudu: Abu Bakar da Umar, kuma mafificin sahabbai kai tsaye: Abu


Bakar al-Siddik, mai yawan gasgatawar al’umma.


Hakika an kebance Abu Bakar-Allah Ya yarda da shi- daga sahabai gaba


dayansu da cewa an nassanta suhubarsa a cikin Alkur’ani: {Alokacin da yake cewa


da sahibinsa:{Kada kayi bakin ciki, lalle ne Allah Yana tare da mu} [al-Taubah:


40] baza’asamu wani daga sahabbai da aka nassanto suhubarsa a Alkur’ani ba face


Abu Bakar- Allah Ya yarda da shi-mai gasgatar al’umma, shine na farko daya


musulunta daga maza, ya zamo mai yawan gasgatawa, babu wani abu da yake


zuwar masa daga annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- face ya


gasgata shi, har sai da mushrikai a yayin da annabi yazo-tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi-, ya basu labari cewa anyi tafiya da shi cikin dare zuwa Baitil


Makdis, kuma aka hau da shi izuwa sama, kuma yahau kan Buraka, sunji labaran


da ba zasu iya gasgatasu ba, sai suka zo izuwa Abu Bakar-Allah Ya yarda shi-, sai


suka ce: Shin kasan abinda abokinka yake fada? Yana cewa kaza da kaza, yace:


16 Ahmad ne ya rawaito (1675), da Tirmizi (3747), da Nasa’i a cikin (al-Kubrah) (8194) daga hadisin Abdurrahman


bn Auf-Allah Ya yarda da shi-, kuma Albani ya inganta shi a cikin (Sahihul Jami’i) (50).


~ 20 ~


“In har ya kasance ya fadi haka, to hakika yayi gaskiya!”17;Shine mai yawan


gasgatawar al’ummah -Allah Ya yarda da shi- babu wanda ya kai matsayin sa a


cikin gasgatawa.


Allah –Madaukakin sarki- Ya face: {Kuma wadanda suka yi imani da Allah


da manzanninSa, wadannnan sune masu gasgatawa} [al-Hadid:19], to farkon


al’umma a cikin shiga wannan daukakar da wannan lakabin: Abu Bakar al-Siddik-


Allah Ya yarda da shi-, kuma babu wanda ya kai matsayinsa a wannan.


Kayi duba ga wannan siffar mai isuwa: Wani lokacin-tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi- yana bawa sahabbansa labari, kuma a lokacin Abubakar da


Umar basa wajen- basu kasance suna wajen ba-, Abu Hurairah -Allah Ya yarda da


shi- yace: “Manzon Allah -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi- yayi


sallar Asuba, sannan ya fuskanto mutane, sai yace: “A tsakankanin wani mutum


yana koro wata saniya, a yayin da ya hau ta sai ya doke ta, sai tace: Lallai mu


ba’a halicce mu don wannan ba, kadai an halicce mu ne don noma, sai


mutane suka ce: Subhanallah! Saniya tana magana!! Sai yace to lallai ni


inayin imani da wannan ni da Abu Bakar da Umar- kuma su basa wajen-.


Kuma tsakankanin wani mutum yana cikin dabbobinsa, a yayin da wata


kerkeci tayi ta’addanci, saiya daukewata akuya daga gareta, sai ya nema har


ya kasance kamar ya tseratar da ita daga gare ta (kerkecin), sai kerkercin


tace da shi: Wannan, ka tseratar da ita daga gareni; to wa ke gare ta ranar


zakoka, ranar da babu wani mai kiwo gare ta in ba ni ba, sai mutane suka ce:


Subhanallah! Kerkeci tana magana!!Yace: to lallai cewa ni inayin imani da


wannan, da Abu Bakar da Umar-kuma su basa wajen –“18.


To kayi duba izuwa ga al-Siddik da imanin sa, kuma ka duba cikar shiriyar


sahabbai-Allah Ya yarda da su-.


Da mun fara muna magama game da falalolin Abu Bakar da Umar-Allah Ya


yarda da su- a kebance daga tsakankanin Alkur’ani da tsakankanin sunnar annabi-


tsira da amincin Allah su tabbata a agare shi-, da lacca daya ko laccoci basu


ishemu ba, kuma da darasi daya ko darussa da yawa basu ishemu ba domin yawan


17 Hakimu ne ya fitar da shi (3/65), da Abu Nu’aim a cikin (Ma’arifatul sahabah) (1/82), da Baihaki a cikin


(Dala’ilul Nubuwwah) (2/321) daga hadisin A’isha-Allah Ya yarda da ita- kuma Hakimu ya inganta shi, Zahabi ya


dace da shi, kuma Albani ya inganta shi a cikin (Sahiha) (306).


18 Bukhari ne ya rawaito (3471).


~ 21 ~


falaloli, da yawan darajoji da aka kebanci wadannan sahabbai biyu da su-Allah Ya


yarda da su-.


Saboda haka ne, muke fuskantowa zuwa ga Allah-Mai girma da buwaya-,


muke rokonSa da sunayenSa kyawawa da siffofinSa madaukaka, kuma da cewa


Shine Allah wanda babu abin bautawa da gaskiya sai Shi, kada Ya sanya gilli a


zukatan mu ga wani daya daga sahabban annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi-, ko wani daya daga muminai, kuma Ya gafarta mana da ‘yan uwanmu


wadanda suka rigayemu da imani, kuma muna rokonSa-Madaukakin Sarki-, da


sunayenSa kyawawa da siffofinSa madaukaka,Ya tashemu a ranar alkiyama tare da


annabinSa mai girma, da sahabbansa na gari, kuma muna rokonSa-Madaukakin


Sarki- Ya tashemu a ranar alkiyama tare da Abu Bakar, da Umar, da Usman, da


Aliyu, da matayen Annabinmu -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-,-Allah


Ya yarda da su-, kuma Ya tashemu a ranar alkiyama tare da sahabbai gaba daya,


ma’abota daraja madaukakiya da masaukai madaukaka da matsayu madaukaka.


❖ NASIHA: (KULAWA DA KARANTA SIRAR SAHABBAI-ALLAH YA


YARDA DA SU-)


Kuma yana kamata gare mu- ya ku ‘yan uwan Musulunci!- mu kula da


karantar halayen sahabbai, da darajojinsu, da falalolinsu, farawa da abinda yazo a


cikin Alkur’ani mai girma, sannan da abinda yazo a cikin sunnar annabi mai girma


-tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-, sannan -kuma- da abinda yazo na


gurabe (hadisai) masu albarka da abubuwan da aka cirato masu girma-wadanda


shuwagabannin Musulunci suka rubutasu da malaman addini cikin littattafan


hadisi- misalin abinda yazo cikin (SAHIHUL BUKHARI) da cikin (SAHIHU


MUSLIM), da cikin (SUNAN GUDA HUDU), da cikin (MASANID), da


(MA’AJIM), da (AL’AJZA’U), da littattafai kebantattu wadanda aka waresu a


cikin falalolin sahabbai, domin cewa mu zamu fa’idantu da al’amura masu yawa


daga wadannan karatuttukamasu yawa daga cikin su akwai:


Nukda ta farko: Cewa kai idan ka karanta game da sahabbai da labaransu da


sirorinsu da hadisansu masu kamshi, to lallai kai zaka kara soyayya garesu da yabo


garesu da nema musu yarda, da nema musu gafara da ambatonsu da alkhairi, kuma


wannan ya isa fai’ida.


~ 22 ~


Fa’idah ta biyu: Kayi kwadayi duk sanda kake karanta sirorinsu, akan kayi


kamanceceniya da su, to duk sanda kafi kamanceceniya da sahabbai, zaka fi


kusantuwa izuwa ga alkhairi, kuma duk sanda ka kara kamanceceniya da sahabbai


da shiga hanyar su da riko da takunsu, zaka kasance mafi kusancin mutane izuwa


ga alkhairi, domin Allah -Madaukakin Sarki- Ya ce: {Kune mafi alherin al’umma


da aka fitar ga mutane} [al-Imran:110], kuma annabi -tsira da amincin Allah su


tabbata a gare shi-ya ce: “Mafi alkhairin mutane, karni na”19. To wadannan Allah


Yayi musu shaida da alkhairi, kuma ManzonSa-tsira da amincin Allah su tabbata


agare shi- yayi musu shaida da ita, duk sanda ka kara kamantuwa da su, to zaka


zama mafi kusanci zuwa ga alkhairi.


Fa’idah ta uku: Cewa kai da sannu zaka zamo nesa, mafi tsananin nisa daga


sukarsu ko afkawa (da muni) cikinsu ko suka ko makamancin wannan, kai an


umarceka da nema musu gafara da yabo da girmamawa da kyautatawa da soyayya


da girmamawa dangane da sahabban annabi-tsira da amincin Allah su tabbata


agare su-. To karanta sirorinsu da sannu zasu kara maka soyayya garesuda yabo


garesu da gairmamasu, da nema musu yarda da nisanta daga zance cikinsu ba tare


da wani hakki ba.


❖ MATSAYAR MUSULMAI DANGANE DA ABINDA YA FARU (NA


SABANI) A TSAKANIN SAHABBAI:-


Kuma a nan, ga mas’ala ta karshe, itace abinda yake da alaka da abinda ya


kasance tsakanin sahabbai na sabani, to me ke a kanmu cikin wannan matsaya


dangane da abinda ya saba tsakanin sahabbai-Allah Ya yarda da su-.


Zamu ambaci fadin zancen daya daga magabata a hakan lokacin da aka


tambaye shi akan wannan al’amari, sai yace: “Wancananka wata fitina ce da


Allah Ya tsarkake takubbanmu daga ita, to sai mu tsarkake harsunan mu


daga gareta”20.


Sannan an tambayi daya daga magabata21 daga irin wannan, sai ya karanta


fadin Allah Madaukakin Sarki: {Waccan, wata al’umma ce, ta riga ta shige,


19Bukhari ne ya rawaito (2602, 3651, 6429), da Muslim (2533) daga hadisin Ibn Mas’ud-Allah Ya yarda da shi-..


20 An rawaito daga Umar bn Abdul’aziz-Allah Yayi masa rahama - ka duba(Hilyatul Auliya)(9/114), da (al-


Mujalasah)(1965) da lafazin:(Wadannan wasu jinane ne da Allah Ya tsarkake hannuna daga gare su,to me ke gare


ni da zan tsoma harshe na ciki?).


21 Shine Imam Ahmad, duba (al-sunnah) na al-Khallal (2/481).


~ 23 ~


abinda ta aikata mallakarta ne, kuma abinda kuka aikata nakune, kuma ba za’a


tambaye ku ba daga abin da suka kasance suna aikatawa} [Suratal-Bakara:


134].


Mu kaddara ma cewa daya daga sahabbai yayi kuskure, to shin Allah-


Madaukakin Sarki- zaiyi masa hisabi ne ranar alkiyamaakan wannan kuskuren?


Madaukakin Sarki Ya ce: {Kuma ba za’a tambaye ku ba daga abin da suka


kasance suna aikatawa}, to don me kake kutsa kanka cikin wannan abinda ya saba


tsakanin sahabbai alhali kai ba mai hisabi ne akan su ba, kuma ba mai kiyayewa


ba, {Waccan, wata al’umma ce, ta riga ta shige, abinda ta aikata mallakarta ne,


kuma abinda kuka aikata nakune, kuma ba za’a tambaye ku ba daga abin da


suka kasance suna aikatawa}.


Sannan wani al’amarin daban, wanda yana da matukar muhimmanci: Wannan


kuskuren, wanda muke kaddarawa cewa an samu wajen sashen sahabbai da muke


sanya shi a mizanin Musulunci, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- yana


cewa: “Idan mai hukunci yayi hukunci sai yayi kokari, sannan ya dace, to


yana da lada biyu, kuma idan yayi hukunci, sai yayi kokari sannan yayi


kuskure, to yana da lada daya”22, saboda wannan, lallai al’amura wadanda ake


ciratowa daga sahabbai na daga sabani ko kuskure basa wofinta daga halaye biyu:


Ko dai karya ce akai musu, kuma wannan shine mafi yawan abinda ake ciratowa.


Ko kuma ingantacce ne tabbatacce, kuma abinda ya inganta daga garesu na


daga wannan, to su mujtahidai ne a cikinsa, to sai dayansu ya kasance ko dai


mujtahidi daya dace, yana da lada biyu, ko kuma mujtahidi mai kuskure yana da


lada daya kuma zunubinsa abin gafartawa ne.


To baya kamata ga mutum a lokacin ya kutsa cikin wani abu na daga abinda


ya saba tsakanin sahabbai, sai idan yayi nufin ya basu kariya ya kare mutuncinsu,


kuma ya bayyana matsayinsu da darajarsu da sha’aninsu, Allah Ya kara yarda a


gare su.


Sannan ni, ina cika wannan sakon da wannan addu’ar, sai nake cewa:


Ya Allah Kayi salati ga (Annabi) Muhammad da alayen (Annabi) Muhammad,


kamar yanda Kayi salati ga (Annabi) Ibrahim da alayen (Annabi) Ibrahim, lallai


22Bukhari ne ya rawaito shi (7352), da Muslim (1712) daga hadisin Amr ibn al-Aas-Allah Ya yarda da shi-.


~ 24 ~


Kai abin yabo ne Mai girma. Kuma Kayi albarka ga (Annabi) Muhammad da


alayen (Annabi) Muhammad, kamar yanda Kayi albarka ga (Annabi) Ibrahim da


alayen (Annabi) Ibrahim, lallai Kai abin yabo ne Mai girma.


Ya Allah Kayi yarda ga Khalifofi shiryayyu, da shuwagabanni masu


shiryarwa, Abu Bakar al-Siddik, da Umar al-Faruk, da Usman Zunnurain, da Abul


Hasanaini Ali, Ya Allah Ka yarda da sauran (sahabbai) goma da akayi musu


albishir da aljanna, Ya Allah Ka yarda da matayen annabin Ka-tsira da amincin


Allah su tabbata a gare shi-, Ya Allah Ka yarda da sahabban annabinKa wadanda


suka halarci Badar, da sahabban annabinKa da suka halarci Bai’atul Ridwan, Ya


Allah Ka yarda da sahabban annabinKa gaba daya, Ya Allah Ka yarda da wadanda


suka bisu da kyautatawa.


Ya Ubangijinmu, Kayi mana gafara da ‘yan uwanmu wadanda suka rigayemu


da imani, kuma Kada Ka sanya gilli a zukatanmu ga wadanda suka yi imani, Ya


Ubangijinmu lallai Kai Mai rangwami ne Mai jin kai.


YaAllah, lallai mu muna kubuta izuwa gare Ka, kuma muna neman tsarinKa-


Ya Ma’abocin girma da karamci-, daga tafarkin wanda yake afkawa (da nufin


muni) cikin wani daga cikin sahaban annabi-tsira da amincin Allah su tabbata a


gare shi-.Ya Allah lallai mu muna kubuta izuwa gareKa daga hanyar wadannan,


kuma muna neman tsarinKa -Ya Ma’abocin girma da karamci- daga hanyarsu,


kuma muna rokonKa Ya Ma’abocin girma da karamci, Ka raya zukatanmu da son


sahabban annabinKa gaba daya, kuma Ka tashe mu tare da su a ranar alkiyama- Ya


Ma’abocin girma da karamci-.


Ya Allah Ka gafarta mana gaba dayanmu, Ya Allah Ka datar damu ga abinda


Ka Ke so kuma Ka yarda (da shi), Ka taimake mu akan biyayya da takawa.


Ya Allah, lallai mu muna rokonKa abubwan da suke wajabta rahamarKa, da


ayyukan da suke karfafa gafararKa, da ganima daga dukkan ayyukan alheri, da


kubuta daga dukkan laifi, da rabauta da Aljanna, da kubuta daga wuta.


Ya Allah, Ka gyara mana addininmu wanda shine tsarin al’amuranmu, kuma


Ka gyara mana duniyarmu wacce a cikinta ne rayuwarmu take, kuma Ka gyara


mana lahirarmu wacce a cikinta ne makomarmu take, Ka sanya rayuwa kari


garemu a cikin kowane alheri, mutuwa kuma hutu garemu daga dukkan sharri.


~ 25 ~


Ya Allah Ka gyaratsakanin mu, kuma Ka hade tsakanin zukatan mu, Ka shiryar


da mu hanyoyin kubuta, Ka fitar da mu daga duffan (kafirci) zuwa hasken


(Musulunci), kuma Kayi albarka garemu a cikin jinnanmu da gannanmu, da kuma


karfafe-karfefen mu har abada muddin dai Ka rayamu.


Ya Allah Ka taramu akan biyayyar Ka-Ya Ma’abocin girma da karamci-, da


abinda zai kusanto zuwa gareKa, kuma Ka nauyaya ma’aunanmu da shi-Ya


rayayye Ya Mai tsayuwa da komai, Ya Ma’abocin girma da karamci-.


Ya Allah Ka sanyamu daga cikin wadanda suke sauraron zance, sai subi mafi


kyawunsa, wadannan sune wadanda Allah Ya shiryar, kuma wadannan sune


ma’abota hankula.


Karshen addu’ar mu, cewa godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai, Allah Yayi


salati da aminci da albarka da ni’ima ga bawanSa kuma ManzonSa, aannabinmu


Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.23


23 Asalin wannan sakon wata lacca ce da akayita a cikin masallacin Kubah a Madinatul Munawwarah, kuma lallai an


fidda ita daga kasset, kuma nayi gyare-gyare ‘yan kadan akan ta, kuma na fifita ta wanzu a salon ta yanda akayita,


kamar yanda take a laccar, Allah ne Shi kadai Mai datarwa.





 



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH