BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA 2
Lallai abunda 'Yan Shi'a suke yi a cikin Ranar Ashura na Bugun kirji, da Marin fuskoki, da yanka kawunansu da Takubba da zubar da jininsu, da Zane Jikinsu da Sarkoki, abubuwa ne fararru wadan da basu da Asali a Addinin Musulunci , kuma Annabi ya hane su, kamar yadda bai koyar da Al'ummarsa ba yin wani abu da ya yi kama da wadan nan ba, saboda Mutuwar wani Babban Mutum, ko rashin wani da yayi Shahada, ko yaya kuma Matsayinsa ko Darajarsa. Take.
Kuma hakika da yawa a lokacin Rayuwarsa wasu sun Rasu -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi - Manyan Sahabbansa wadan da ya yi Bakin cikin Rashin su, Kamar Hamza Dan Abdulmutallib da waninsa, kuma bai yi wani abu ba daga cikin irin wadan nan Munanan Ayyukan.
Kuma Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a g areshi - ya ce: “Baya tare da mu duk wanda ya Mari kumatun sa - Saboda rakin wata Masifa da ta same shi- ko ya yaga Aljihunsa kuma yayi aiki irin na lokacin Jahiliyya”. Bukhari (1294) da Muslim (103)
BIDI’AR ‘YAN SHI’A A RANAR ASHURA 4
To wadan nan Ayyuka Munanan Ayyuka ne wadan da 'Yan Shi'a suke aikatawa a Ranar Ashur (10 ga Watan Muharram) basu da wani Asali a Musulunci, kuma Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi bai yi su ba haka babu daya daga cikin Sahabbabnsa ko kuma Iyalansa.
Kuma ba'a samu wani daya daga cikin Iyalan gidan Annabi ya yi su ba Sabo da Mutuwar Sayyadi Ali ko kuma Hassan kai har ma Hussain Allah ya yarda da su.