Labarai



Da sunan Allah mai  rahama mai  jinkai.  ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA.







 





Description: Une image contenant texte, capture d’écran, logo, Police
<br/><br/>
<br/><br/>Description générée automatiquement





﴿الٓمٓ١ ذَٰلِكَ ٱلۡكِتَٰبُ لَا رَيۡبَۛ فِيهِۛ هُدٗى لِّلۡمُتَّقِينَ٢ ٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِٱلۡغَيۡبِ وَيُقِيمُونَ ٱلصَّلَوٰةَ وَمِمَّا رَزَقۡنَٰهُمۡ يُنفِقُونَ٣ وَٱلَّذِينَ يُؤۡمِنُونَ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡكَ وَمَآ أُنزِلَ مِن قَبۡلِكَ وَبِٱلۡأٓخِرَةِ هُمۡ يُوقِنُونَ ٤ أُوْلَٰٓئِكَ عَلَىٰ هُدٗى مِّن رَّبِّهِمۡۖ وَأُوْلَٰٓئِكَ هُمُ ٱلۡمُفۡلِحُونَ ٥ [البقرة: 1-5]





{ALIF, LAM, MIM





Wannan littafi ne da babu wani kokwnto a cikinsa, shiriya ne ga masu takawa. Su ne wadanda suke yin imani da gaibu, kuma suke tsayar da sallah, kuma suke ciyarwa daga  abinda muka azurta su da shi. Da kuma wadanda suke yin imani da abinda aka saukar maka, da kuma abinda aka saukar a gabaninka, dan gane da lahira kuma  masu sakankancewa ne. Wadannan suna kan shiriya daga Ubangijinsu, kuma wadannan su ne masu samun babban rabo} [Bakara, aya ta: 1-5]





﴿ٱللَّهُ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡحَيُّ ٱلۡقَيُّومُۚ لَا تَأۡخُذُهُۥ سِنَةٞ وَلَا نَوۡمٞۚ لَّهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَمَا فِي ٱلۡأَرۡضِۗ مَن ذَا ٱلَّذِي يَشۡفَعُ عِندَهُۥٓ إِلَّا بِإِذۡنِهِۦۚ يَعۡلَمُ مَا بَيۡنَ أَيۡدِيهِمۡ وَمَا خَلۡفَهُمۡۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيۡءٖ مِّنۡ عِلۡمِهِۦٓ إِلَّا بِمَا شَآءَۚ وَسِعَ كُرۡسِيُّهُ ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضَۖ وَلَا يَـُٔودُهُۥ حِفۡظُهُمَاۚ وَهُوَ ٱلۡعَلِيُّ ٱلۡعَظِيمُ٢٥٥ [البقرة: 255]





{Allah shi ne wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, rayayye ne kuma wanda ya tsayu da kansa ne, gyangyadi ba ya kama shi balle barci, shi ke da duk abinda yake a sammai da kassai, babu wanda zai yi ceto a wurinsa sai da izininsa, ya san abinda yake gabansu da kuma bayansu, (su) bayi ba sa sanin wani abu na iliminsa sai abinda ya ga dama su sani, Kursiyunsa ya yalwaci sammai da kassai, kuma ba ya  yi masa nauyi kiyaye su, shi madaukaki ne maigirma.} [Ayatul Kursiy, Bakara aya ta:255.]





﴿ءَامَنَ ٱلرَّسُولُ بِمَآ أُنزِلَ إِلَيۡهِ مِن رَّبِّهِۦ وَٱلۡمُؤۡمِنُونَۚ كُلٌّ ءَامَنَ بِٱللَّهِ وَمَلَٰٓئِكَتِهِۦ وَكُتُبِهِۦ وَرُسُلِهِۦ لَا نُفَرِّقُ بَيۡنَ أَحَدٖ مِّن رُّسُلِهِۦۚ وَقَالُواْ سَمِعۡنَا وَأَطَعۡنَاۖ غُفۡرَانَكَ رَبَّنَا وَإِلَيۡكَ ٱلۡمَصِيرُ٢٨٥ لَا يُكَلِّفُ ٱللَّهُ نَفۡسًا إِلَّا وُسۡعَهَاۚ لَهَا مَا كَسَبَتۡ وَعَلَيۡهَا مَا ٱكۡتَسَبَتۡۗ رَبَّنَا لَا تُؤَاخِذۡنَآ إِن نَّسِينَآ أَوۡ أَخۡطَأۡنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تَحۡمِلۡ عَلَيۡنَآ إِصۡرٗا كَمَا حَمَلۡتَهُۥ عَلَى ٱلَّذِينَ مِن قَبۡلِنَاۚ رَبَّنَا وَلَا تُحَمِّلۡنَا مَا لَا طَاقَةَ لَنَا بِهِۦۖ وَٱعۡفُ عَنَّا وَٱغۡفِرۡ لَنَا وَٱرۡحَمۡنَآۚ أَنتَ مَوۡلَىٰنَا فَٱنصُرۡنَا عَلَى ٱلۡقَوۡمِ ٱلۡكَٰفِرِينَ٢٨٦ [البقرة: 285-286]





{Manzon Allah yã yi ĩmãni da abin da aka saukar zuwa gare shi daga Ubangijinsa, da mũminai. Kõwanensu yã yi ĩmãni da Allah, da mala'ikunSa, da littattafanSa, da manzanninSa. Bã mu rarrabẽwa a tsakãnin daya daga manzanninSa. Kuma (mũminai) suka ce: "Mun ji kuma mun yi dã'a; (Muna nẽman) gãfararKa, yã Ubangijinmu, kuma zuwa a gare Ka makõma take "





Allah ba ya dorawa rai sai abinda za ta iya, tana da (ladan) abin da ta aikata, kuma tana da (ukubar laifin) da ta aikata. Ya Ubangijinmu kada ka kamamu idan muka manta ko kuskure. Ya Ubangijinmu kada ka dora mana nauyi kamar yadda ka dora shi ga wadanda suka zo kafin mu. Ya Ubangijinmu kuma kada ka dora mana abinda ba za mu iya ba, ka yi mana  afuwa ka gafarta mana, kai ne majibintin al'amuran mu, ka taimaka mana akan mutanan da suke kafirai.} [Bakara, aya ta: 285- 286]





﴿حمٓ١ تَنزِيلُ ٱلۡكِتَٰبِ مِنَ ٱللَّهِ ٱلۡعَزِيزِ ٱلۡعَلِيمِ٢ غَافِرِ ٱلذَّنۢبِ وَقَابِلِ ٱلتَّوۡبِ شَدِيدِ ٱلۡعِقَابِ ذِي ٱلطَّوۡلِۖ لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ إِلَيۡهِ ٱلۡمَصِيرُ٣ [غافر: 1-3]





{HA MIM





Saukar da littafi daga Allah mabuwayi, Masani. Mai gafarta zunubi kuma mai karbar tuba, mai tsananin ukuba ma'abocin ni'ima, babu abin bautawa da cancanta sai shi, gare shi makoma take} [Ghafir, aya ta: 1-3]





﴿هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَۖ عَٰلِمُ ٱلۡغَيۡبِ وَٱلشَّهَٰدَةِۖ هُوَ ٱلرَّحۡمَٰنُ ٱلرَّحِيمُ٢٢ هُوَ ٱللَّهُ ٱلَّذِي لَآ إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡمَلِكُ ٱلۡقُدُّوسُ ٱلسَّلَٰمُ ٱلۡمُؤۡمِنُ ٱلۡمُهَيۡمِنُ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡجَبَّارُ ٱلۡمُتَكَبِّرُۚ سُبۡحَٰنَ ٱللَّهِ عَمَّا يُشۡرِكُونَ٢٣ هُوَ ٱللَّهُ ٱلۡخَٰلِقُ ٱلۡبَارِئُ ٱلۡمُصَوِّرُۖ لَهُ ٱلۡأَسۡمَآءُ ٱلۡحُسۡنَىٰۚ يُسَبِّحُ لَهُۥ مَا فِي ٱلسَّمَٰوَٰتِ وَٱلۡأَرۡضِۖ وَهُوَ ٱلۡعَزِيزُ ٱلۡحَكِيمُ٢٤ [الحشر: 22-24]





{Shi ne Allah ,wanda babu wani abin bautawa face Shi, Masanin boye da sarari, shi ne mai yawan rahama mai yawan jinkai.





Shi ne Allah wanda babu abin bautawa da cancanta sai shi, shi ne Sarki, Mai tsarki mai aminci, mai amintarwa, mai kula da komai, mabuwayi, mai karfin iko akan komai, mai ji-da-isa, tsarki ya tabbata ga Allah daga barin abinda suke ra shi da shi. Shi ne Allah mahalicci, mai kagar halitta mai surantawa, yana da sunaye mafiya kyau, duk abinda yake sammai da kasa suna masa tasbihi, shi ne mabuwayi mai hikima} [Suratul Hashr, aya ta: 22-24]





﴿قُلۡ هُوَ ٱللَّهُ أَحَدٌ١ [الإخلاص: 1]





{Ka ce: "Shi ne Allah Makaɗaĩci."}





﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلۡفَلَقِ١ [الفلق: 1]





{Ka ce "ina neman tsari daga Ubangijin safiya."}





﴿قُلۡ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ١ [الناس: 1]





{Ka ce "ina neman tsari daga Ubangijin mutane."}





cikakkakkiyar surar ake karantawa, kafa  uku (3).





«أعوذ بكلمات الله التامات من شر ما خلق»





"Ina neman tsari daga kalmomin Allah cikakku daga sharrin abinda ya halitta. "





Sau uku (3).





«بِسْمِ اللهِ الَّذِي لاَ يَضُرُّ مَعَ اسْمِهِ شَيْءٌ فِي الأْرْضِ وَلاَ فِي السَّمَاءِ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ»





"Da sunan Allah, wanda babu wani abu mai cutarwa da sunansa a sama ko a kasa . Kuma shi ne Mai ji Masani"





Sau uku (3).





«رضيت بالله ربًّا وبالإسلام دينًا وبمحمد صلى الله عليه وسلم نبيًّا»





"Na yarda da Allah Ubangiji, da  Musulunci addini, kuma Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi annabi."





Sau uku (3).





«أصبحنا وأصبح الملك لله والحمد لله لا إله إلا الله وحدة لا شريك له. له الملك وله الحمد وهو على كل شيء قدير. رب أسألك خير ما في هذا اليوم وخير ما بعده. وأعوذ بك من شر ما في هذا اليوم ومن شر ما بعده. ربِّ أعوذ بك من الكسل والهرم وسوء الكِبَر. وأعوذ بك من عذاب النار وعذاب القبر»





"Mun wayi gari kuma mulki ya wayi gari na Allah ne , godiya ta tabbata ga Allah, babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake, ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne, godiya tasa ce, kuma shi mai iko ne akan komai. Ya Ubangiji ina rokonka alherin wannan yini da alherin dake bayansa, ina kuma neman tsarinka daga sharrin wannan yini da sharrin dake bayan sa. Ya Ubangiji ina neman tsarinka daga kasala da tsufa, da mummunan girma, ina neman tsarinka daga azabar wuta da kuma azabar kabari."





Da yamma kuma sai ya ce: Mun kai yammaci, kuma mulki ya kai yammaci na Allah ne. sai kuma ya ce:





«أمسينا وأمسى الملك لله»





"Ya Ubangiji ina rokonka alherin wannan daren.... zuwa karshe, maimakon: Mun wayi gari  ya wayi gari. Da kuma (wannan yini)."





«اللهم بك أصبحنا وبك أمسينا وبك نحيا وبك نموت واليك النشور»





"Ya Allah gareka muka wayi gari, kuma gareka muka yi yammaci, kuma gareka muke rayuwa kuma gareka muke mutuwa, kuma gareka Makoma take."





«اللهم بك أمسينا وبك أصبحنا وبك نموت وبك نحيا وإليك المصير»





"Da yamma kuma sai ya ce: Ya Ubangiji gareka muke yammaci , kuma gareka muka wayi gari, kuma gareka muke mutuwa, kuma gareka muke komawa."





«اللهم ما أصبح بي من نعمة أو بأحد من خلقك فمنك وحدك لا شريك لك فلك الحمد ولك الشكر»





"Ya Ubangiji duk abinda ya wayi gari a gareni na ni'ima ko ga wani cikin halittarka to daga gareka ne, kai kadai, baka da abokin tarayya, yabo naka ne kuma godiya taka ce."





Da yamma kuma sai ya ce:





«ما أمسى بي»





"Abinda ya yi yammaci a gare ni."





«اللهم إني أصبحت في نعمة وعافية وستر. فأتم نعمتك عليّ وعافيتك وسترك في الدنيا والآخرة»





"Ya Ubangiji na wayi gari cikin ni'ima da lafiya da rufin asiri, ka cika ni'imarka a gareni da lafiyarka da rufin asirinka duniya da lahira."





Sau uku (3).





Da yamma kuma sai ya ce:





«اللهم إني أمسيت»





"Ya Ubangiji ni na kai maraice: zuwa karshe."





«اللهم إني أعوذ بك من الهم والحزن. وأعوذ بك من العجز والكسل. وأعوذ بك من الجبن والبخل. وأعوذ بك من غلبة الديْنِ ومن قهْر الرجال»





"Ya Ubangiji ni ina neman tsarinka daga damuwa da bakin ciki, ina neman tsarinka daga gajiyawa da kuma kasala, ina kuma neman tsarinka daga tsoro da rowa, ina kuma neman tsarinka daga rinjayar bashi da kada mutane su fi karfi na."





«اللهم إني أسألك العافية في الدنيا والآخرة. اللهم إني أسألك العفو والعافية في ديني ودنياي وأهلي ومالي. اللهم استر عوراتي وآمن روعاتي. اللهم احفظني مِن بين يديَّ ومِن خلفي وعن يميني وعن شمالي ومن فوقي. وأعوذ بعظمتك أن أُغتال من تحتي»





"Ya Ubangiji ni ina rokonka yafiya anan duniya da kuma lahira, Ya Ubangiji ni ina rokonka afuwa da yafiya a addinina da duniyata da iyalina da kuma dukiyata, Ya Ubangiji ka suturta al'aurata, ka amintar da tsorona. Ya Ubangiji ka tsare ni ta gabana da ta bayana, ta damata da ta haguna da kuma ta samana, ina kuma neman tsari da buwayarka kada a halakani ta kasa ta."





«اللهم أنت ربي لا إله إلا أنت. خلقتني وأنا عبدك. وأنا على عهدك ووعدك ما استطعت. أعوذ بك من شر ما صنعت. أبوء لك بنعمتك علي. وأبوء بذنبي. فاغفر لي. فإنه لا يغفر الذنوب إلا أنت»





"Ya Allah ! kai ne Ubangiji na, babu abin bautawa da cancanta sai kai, kai ka halicceni ni bawanka ne, ni kuma ina kan al'kawarinka gwargwadon iko, ina neman tsarinka daga sharrin abinda na aikata, ina tabbatar da ni'imarka a gare ni, ina tabbatarda zunubi na, ka gafarta mini, domin babu mai gafarta zunubai sai kai."





«اللهم فاطر السماوات والأرض. عالم الغيب والشهادة. ربَّ كل شيء ومَلِيكه. أشهد أن لا إله إلا أنت. أعوذ بك من شر نفسي ومن شر الشيطان وشركه وأن أقترف على نفسي سوءاً أو أجُرَّه إلى مسلم»





"Ya Ubangiji ! mahaliccin sammai da kasa, masanin boye da sarari, Ubangijin komai kuma mamallakinsa, ina shaidawa da babu abin bautawa da cancanta sai kai, ina neman tsarinka daga sharrin kaina da kuma sharrin shaidan da abin shirkarsa, da kuma kada in aikatawa kaina mummunan abu ko in kai shi ga wani Musulmi."





«اللهم إني أصبحت أُشهدُك وأشهد حملة عرشك وملائكتك وأنبياءك وجميع خلقك بأنك أنت الله لا إله إلا أنت وأن محمدًا عبدك ورسولك»





"Ya Ubangiji ni na wayi gari ina shaida maka ina kuma shaidawa (Mala'iku) masu dauke da al'arshinka da Mala'ikunka da Annabawanka da dukkanin halittunka da cewar kai ne : Allah wanda babu abin bautawa da cancanta sai kai, kuma lalle (Annabi) Muhammad bawanka ne kuma Manzonka ne."





Da yamma kuma:





«اللهم إني أمسيت»





"Ya Ubangiji ! ni na kai maraice: zuwa karshe," (sau hudu) (4).





«لا إله إلا الله وحده لا شريك له. له الملك وله الحمد. وهو على كل شيء قدير»





"Babu abin bautawa da cancanta sai Allah, shi kadai yake ba shi da abokin tarayya, mulki nasa ne kuma godiya tasa ce, kuma  shi maiiko ne akan komai."





Sau dari (100), da safe da kuma yamma.





«حسبي الله لا إله إلا هو عليه توكلت وهو رب العرش العظيم»





"Allah ya isar mini, babu abin bautawa da cancanta sai shi, a gare shi na dogara, kuma shi ne Ubamgijin Al arshi mai girma."





Sau bakwai (7).





«حسبي الله وكفى. سمع الله لمن دعاء ليس وراء الله مرمى»





"Allah ya isar min, kuma ya wadatar, Allah ya ji duk wanda ya roke shi, babu mafaka in ba wurin Allah ba."





«سبحان الله وبحمده»





"Tsarki ya tabbata ga Allah hadi da gode masa."





Sau dari (100), da safe ko da yamma, ko kuma dukkan su.





«أستغفر الله وأتوب إليه»





"Ina neman gafarar Allah ina tuba zuwa gare shi."





Sau dari (100).





Wannan shi ne gwargwadon abin da ya sawwaka da aka rubuta, ina rokon Allah madaukakin sarki ya anfanar da shi.





Wanda ya rubuta shi ne: Muhammad dan Salih Al usaimin, 20/1/1418 (Bayan Hijira).



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA