HUKUNCE-HUKUNCEN
KIRAN SALLAH
Menene Kiran-sallah ?: Kiran sallah shine: Sanar da shigar
lokacin sallah ta farilla da lafuzza kebantattu.
An shar'anta wannan kiransallah a tun shekarar farko
bayan hijira, kuma sanadiyyar shar'antuwarta kuwa shine
alokacin sanin lokaci ya ta'azzara ga sahabbai sai aka yi
shawara akan wacce alama za'a yi anfani da ita domin sanar
da al'aumma shigar lokacin sallah, bayan wadannan
shawarwarine sai aka nunawa Abdullahi dan Zaid kiran
sallar a mafarki kuma Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah
su tabbata a gareshi ya tabbatar.
Dukkanin lafuzzan kiran sallah lafuzzane da suka kunshi
zikiri kuma suka kunshi tsantsar akidar musulunci, kama
daga girmama Ubangiji da tabbatar da kadaituwarsa kana ga
tabbatar da manzanci manzan Allah Annabi Muhammad
tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi, sannan kuma
kiran al'umma zuwa gabatar da sallah wacce take itace
ginshikin addini, ga kuma addu'a da fatan samun babban
rabo wanda yake shine rabauta da tabbatuwa a cikin ni'ima
matabbabaciya, sannan kuma a kammala kiran sallar da
girmama Ubangiji da tsantsanta kalmar ikhilasi wacce take
tana cikin mafificin zikiri.
Hadisai masu tarin yawa sun yi bayanin falalar kiran
sallah, da masu kiransallar, amma falalar zata tabbatane a
lokacin da aka gabatar da kiran a yadda yake, mai kiran
sallah ya kusanci malamai domin sanin hukunce-hukuncen
kiran sallah, ya dinga tantance lokaci. Idan muka yi la'akari
4
kiran sallah bawai ya takaitu ga sallah bane kadai a'a, da
yawa masu azumi suna dakatar da sahur dinsu ne sakamakon
kiran sallar asuba, haka nan kuma ba'a gabatar da budabaki
sai bayan kiran sallar magariba, kenan idan lokaci bai yi bai
kira sallah aka gabatar da budabaki ya kake gani kenan, ko
kuma lokacin kiran sallah ya yi domin a dakatar da sahur
amma kuma bai kiraba ya zakace, wannan kuma ba wai ya
shafi watan Ramadan kadai bane domin ai akwai masu
ramuwa akwai masu nafilfili a wajan Ramadan.
Bai halatta a kira sallah kafin loakcinta ya yi, domin ai an
shar'antatane domin sanar da shigar lokacin sallah, saidai
sallar asuba ya halatta a kira sallah kafin lokacin ya yi domin
mutane su kintsa su kuma shirya, sannan idan lokacin sallar
ya shiga sai a sake kiran sallar, wannan ke nuna mana ita
sallar asuba kiran sallah biyu ake yi mata.
An sunnanta ga dukkan wanda ya ji kiran sallah ya fadi
kwatankwacin abinda mai kiran sallar ya fada ba kari ba raji
sai dai a lokacin da mai kiran sallah yace ''Hayya alas Salah''
sai kace ''La haula wala kuwwata illa billah''.
Bai halatta ga wanda yake cikin masallaci ya fita bayan an
kira sallah ba tare da wani uzuri ba, idan kuma mai kiran
sallah ya fara kiran sallah to bai kamata wanda yake a zaune
ya tashiba domin kada ya yi kamanceceniya da shaidan.
Yanada matukar muhimmanci ga dukkan wanda ya ji ankira
sallah ya kama hanyar zuwa masallaci yabar dukkan
ayyukan dake gabanshi ya je ya gabatar da na lahira
tukunna.
Bayanai akan kiran sallah suna da dama, wanda hakan
yake nuna muhimmancin wannan ibada, sannan kuma
kusantar malamai shine abinda zai warwarw dukkan wata
matsala, domin shi kiran sallah ba aikine na marasa aikiba.
5
Mun taba gabatar da rubutu na musamman akan abinda ya
shafi kurakurai a kiran sallah.
Kammalawa: Takaitattun wadannan bayanai da suka gabata
sun tabbatar mana da cewa lalle kiran sallah al'amarine da
musulunci ya kula dashi domin yana da alaka da ibadar da
tafi kowacce ibada a gurin musulmi, sannan kuma ba'a yenta
da kah, ko a koya a kan titi, sai an je makaranta malami ya
biya maka ka maimaita a gabansa har zuwa lokacin da zaice
ma ya yi daidai, wanda ko ya fara bai koyaba sai ya koma
wurin malamai domin su gyara masa.
Rubutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu