Labarai

LOKUTAN SALLAH (1)


Gabatarwa: Wannan wani babine mai girman gaske


dudda cewa dukkan wadannan bayanai suna da matukar


muhimmanci. Su lokutan sallah saninsu yana da matukar


muhimmanci, domin ba'a yin sallah sai lokacinta ya yi kuma


ba'a bari lokacinta ya fita ba'a yi ba, asalima shigar lokaci


sharadine daga cikin sharuddan sallah kamar yadda bayanai


suka gabata kuma mukace da izinin Allah zamu kawo


bayanai akan abinda ya shafi lokutan sallah.


Lokutan Sallah: Kowacce sallah daga cikin wadannan


salloli wajibabbu guda biyar tana da lokacinta da Allah


madaukakin sarki ya iyakance mata ba za'a yi ta kafin


lokacinta ya yi idan kuma lokacin ya yi ba za'a bari sai ya


fitaba, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Lalle ita salla ta


kasance akan muminai wajibice kuma abar gayyadewa


lokaci'' Suratun Nisa'i, aya ta: 103. Umar dan Khaddab Allah


ya kara masa yarda yana cewa 'Sallah tana da lokaci da


Allah ya sansa bata inganta sai a wannan lokacin'. Sallah


tana zama wajibine idan lokacinya ya shiga kamar yadda


ayoyi masutarin yawa suka nuna, gabadayan malamai sun yi


ijima'I akan falalar dake cikin yin sallah a farkon lokaci a


dunkule, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Ku yi rigerigen


aikata alheri'' Bakara, aya ta:148 wanda yake sallah


itace babba akan dukkan wani alheri da musulmi zai gabatar.


Kowacce sallah daga cikin salloli biyar din nan tana da


lokacinta da Allah ya kayyade mata wanda kuma ya yi


daidai da halin da bayinsa suke, ta yadda zasu gabatar da


wadannan salloli a kan lokutansu ba tare da wani abu ya


4


tsare sub a asalima zata taimaka musu ne, kuma ta kankare


musu zunubai, ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su


tabbata a gareshi ya kamantata da ruwa da yake gudu wanda


mutum a kullun yake wanka a cikinsa sau biyar kana


tsammanin zaka ga wani datti a tare da shi!.


1. Lokacin Sallar Azahar: Lokacin sallar azahar shine


daga lokacin da rana ta karkata daga tsakiyar sama ta koma


zuwa bangaren yamma, zaka gane hakane ta yadda inuwarka


zata koma bangaren gabas bayan ada baka gantaba. Wato


yadda al'amarin yake alokacin da rana take gabas zaka ga


inuwa ta na yammane, lokacin da rana take kara dagowa


lokacin inuwar take kara ragewa harzuwa lokacin da rana


zata zo tsakiyar sama daidai, za kuma tad an tsaya kadan, to


adaidai wannan lokacin da take atsakiya cif zaka ga ba wata


inuwa, domin sai ranar ta karkata wani bangarene sannan


inuwar ta bayyana a wani bangaren. To daga lokcin da ranar


ta ci gaba da tafiya zuwa yamma to daga lokacin inuwa zata


ci gaba da bayyana bangaren gabas, ranar tana kara yin


yamma inuwar tana kara tsawo bangaren gabas. Daga


lokacin da ranar ta karkata zuwa bangaren yamma kuma


alamar hakan itace ka ga inuwarka ta bayyana bangaren


gabas to da ganin haka lokacin sallar azahar ya yi, ba abinda


ya rage sai dai a sallah ce ta, sai dai idan lokacin ana fama


zafin rana sai a jinkirta kadan, ma'aikin Allah tsira da


amincin Allah su tabbata a gareshi yana cewa: '' Idan zafi ya


tsananta to kudan sanyaya sallah, domin tsananin zafin nan


daga nunfashin jahannama ne''. Bukhari da Muslim da Malik


a Muwatta'u.


Wannan shine loakcin sallar azahar har kuma zuwa


inuwar komai ta zama kamar tsawonsa.


5


Kenan anan ba wata sallah mai suna karfe biyu ko karfe daya, kamar yadda lokuta suke canzawa a tsawon shekara to haka lokutan sallah suke canjawa, duk mun san wani lokaci magariba akan yita kusa bakwai na yamma wani lokacin kuma kusan shida da wani abu na yamma, to ashe kamar yadda muka yarda lokacin magariba yana canzawa to hakanan na sauran sallolin, kuma fa duk wannan a wasu yankunane kadan fa domin inda mutum ya je hajji ko umarah a inda aka saukar da sallar to da yaga wani lokacimma tuni karfe daya an gama sallah kuma da shi aka yi ta, amma idan ya dawo gida yace sai ta nuna.


2. Lokacin Sallar La'asar: Lokacinta yana farawane daga lokacin da inuwar kowanne abu ta zo kamar tsawonsa, kenan inda zaka kafa tsinke a kasa sannan sai ka ja layi a karshen inuwar to daga lokacin da tsawon tsinken ya doru kadan kan inuwar to lokacin sallah ya yi, daga nan har zuwa lokacin da inuwar kowanne abu zata ninka shi sau biyu, amma kada ka manta yinta a farkon lokaci shine abinda ya fi.


Anan ana samun manyan kura-kurai guda biyu, kuskure na farko shi yafi ko wanne muni shine daukan lokacin sallar la'asar shine: karfe uku da rabi(3:30pm), wannan kuskurene domin dayawa masu irin wannan sallar za su yita tun kafin lokacinta ya yi, kenan basu da sallah domin sun yita kafin lokaci. Kuskure na biyu kuma shine jinkirtata bayan lokacin ya shiga waishi ai yana ganin ance har inuwa ta ninka gida biyu.


3. Lokacin Sallar Magariba: Lokacin sallar magariba yana farawane daga lokaci da kaskon rana ya bace bakidayansa to daga wannan lokacin magariba ta yi ko da ana ganin haske, kuskuren da ke yi anan shine jinkirta sallar


6


har sai dare ya yi alhali kuma lokacinta takaitaccene, daga lokacin da rana ta fadi har zuwa bacewar shafaki, shi kuma shafaki: wani haskene da yake gauraya da ja anan sai jan ya bace ya bar hasken sai shima hasken ya bace.


An fi so a gabatar da kowacce sallah a farko lokacinta to hakama ita sallar magariba.


4. Lokacin Sallar Isha: Shi lokacin sallar lisha yana farawane daga lokacin da shafaki ya bace, wanda yake shine karshen muhtarin magariba har zuwa kashi daya cikin uku na dare, zuwa nan muhtarin lisha ya tsaya, amman dai lokaci na laruri yana kaiwane harzuwa lokacin da alfijiri na biyu ya kyato, wanda yake kuma shine farkon muhtarin asubahi.


Shi babban kuskuren da ake samu a sallar lisha shine wasu wuraran sun dauki karfe bakwai da rabi (7:30pm) shine lokacinta wanda yake nuna sauda yawa ana yinta kafin shigar lokacinta.


5. Lokacin Sallar Asubahi: shi lokacin sallar asubahi yana farawane daga hudowar alfijiri na biyu kuma zai ci gaba har zuwa fitowar rana, saidai kada ka manta anfi so a gabatar da ita da zarar an tabbatar da fitowar alfijir.


Kuskuren da ake samu a sallar asubahi shine yadda wasu suka maida lokacin shine karfe biyar da rabi na asuba (5:30am) wanda yake wannan babban kuskure domin sauda yawa wasu lokutan alfijir yana fitowane tun kafin biyar, ballema a wasu yankunan, kuma Karin hatsarin akwai masu azumi na nafila ko ramuwa kuma sun dogarane da kiran sallah shi kuma mai kiran sallar bai kiraba gashi kuma alfijir ya dade da fitowa.


7


Wadannan sune lokutan sallah kuma idan muka lura zamu ga kowacce sallah tana da lokutta guda biyu; Muhtari da kuma Laruri.


Muhtari: shine zababban lokaci da aka zaba domin ka gabatar da wannan sallar, ba'a yarda ka shiga lokacin laruriba sai inda larura kuma musulunci ya fayyace me ake nufida larurar, sannan shima muhtarin yin sallah a farkonshi tafi lada da samun matsayi a wurin Allah mai girma da daukaka.


Kammalawa: Atakaitaccan wannan bayani ya bayyana a fili cewar lokutan sallah lokutane da musulunci ya sanya, jindadi da walwala shine abi wadannan lokuta da musulunci ya kayyade, bai al'ummar musulmi su yi wasa da sanin lokutan sallah ba musamman ladanai domin da kiran sallar su ake barin sahur da shi kuma ake shan ruwa. Nan gaba zamu kashi na biyu na lokutan sallah, da izinin Allah.


8


LOKUTAN SALLAH (2)


Muhtarin Salloli Da Larurinsu:


1. Muhtarin Sallar Azahar shine daga lokacin da rana da gusa daga sararin sama zuwa bangaren yamma inuwa kuma ta bayyana ta bangaren gabas harzuwa loakcin da inuwa zata kai tsawon kowanne abu. Larurin azahar kuma shine daga lokacin da inuwarka ta kai tsawanka zuwa dab da faduwar rana.


2. Muhtarin Sallar La'asar daga lokacin da inuwarka ta kai tsawonka zuwa loakcin da rana zata yi fatsi-fatsi. Larurinta kuma zuwa faduwar rana.


Kenan azahar da la'asar suna tarayya a wani bangare na lokacin sallah, wannan kuma yana da matuka muhimmanci a fahimceshi saboda bayanan da zasu zo nan gaba, da izinin Allah.


3. Muhtarin Sallar Magariba: daga lokacin da rana tadi (ta bace kwata-kwata) zuwa gwargwadon abinda ka sallata, ba'a bukatar a jinkirtata. Larurinta har zuwa dab da fitowar alfijir.


4. Muhtarin Sallar Isha: daga lokacin da shafaki ya bace har zuwa kashi daya biya ukun dare. Larurinta har zuwa fitowar alfijir.


Kenan magariba da lisha suna tarayya awani yanki na lokacin sallah.


9


5. Muhtarin Sallar Asubahi: daga lokacin da alfijiri ya keto zuwa gari ya waye (ya yi haske tangaran) zuwa fitowar rana.


Kenan asubahi ita kadai take da lokacinta babu wata sallah da ta yi tarayya da ita.


Ba'ayarda mutum ya jinkirta sallah har zuwa lokacin laruriba sai idan yana da larurar da shara'a ta bayyana, idan mutum ya kuskura ya bar sallah har lokacinta ya fita to ya tafka laifi mai girman gaske, Allah madaukakin sarki yana cewa '' Sai wadansu masu mayewa suka maye musu suka wulakantar da sallah suka bi holewarsu da sannu zasu hadu da gayyah (wani kwarine a cikin wutar jahannama). Sai dai kwai wanda ya tuba''Suratu Maryam, aya ta:59-60 Allah ya tsare mu.


Larura:


Ya zama dole mu tsaya mu fahimci mecelarurar domin kada ka dauki abinda ba larura bane a shar'ance ka bashi matsayin larura.


1. Mantuwa: Duk wanda ya manta da sallah, ya dauka kamar ya yi ashe bai yi ba sai daga baya ya tuna to sai ya tsahi ya sallace ta a wannan lokacin da ya tuna, ko da lokacin sallar ya fita, kamar ya manta da azahar sai bayan ya yi sallar isha ya tuna, sai ya tashi ya kawo sallar azahar din,yin ta a wannan lokacin shine kaffarar.


2. Bacci: Idan lokacin sallah ya yi mutum sai ya yi sallah kafin ya kwanta, idan kuma lokacin sallah bai yi ba sai ya kwanta bacci bai tashiba sai da lokaci ya fita, to a wannan lokacin da ya tashi sai ya sallaceta babu wani jinkiri. Akan


10


abinda ya shafi mantuwa da bacci Ma'aikin Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi yake cewa: '' Duk wanda ya manta wata sallah, ko kuma ya yi bai yita ba, to ya sallaceta idan ya tunata babu wani abu da yake kaffara sai yin hakan''. Muslim,684. kenan ba maganar wai sai lokacin na gobe ya dawo, wannan babu shi a musulunci duk lokacin da ka tuna da sallah to a wannan lokacin zaka sallace ta.


3. Musulunta: idan mutum ya musulunta bayan muhtarin sallah ya wuce, kamar ya musulunta lokacin da rana ta yi fatsi-fatsi, to a wannan loakcin zai yi sallar azahar da la'asar, tunda sun yi tarayyar lokaci.


4. Balaga: idan ya zama yarone ya fitar da maniyyi a barci ko a farke ya zama wannan fitar maniyyin shine balagarshi a wannan lokacin to sai ya yi wanka ya sallaci azahar da la'asar idan a loakcin su ne, ko magariba da lisha idan suma a lokacin su ne.


5. Hauka: ko kuma mutumne yake fama da cutar tabin hankali sai bai sami saukiba sai abinda ya saura kafin alfijir ya fito za'a sami raka'a hudu to sai ya sallaci magariba da isha.


6.Suma: ko kuma mutumne ya suma ko aljanu suka bigeshi sai bai farfadoba sai a wadannan lokuta na laruri, idan ya zama za'a sami sallar raka'a biyar kafi rana ta fadi sai ya yi sallar azahar sannan ya kawo sallar la'asar, amma idan za'a sami raka'oi hudune kafin rana ta fadi sai ya sallaci la'asar kadai.


7-8. Jinin Al'ada Da Jinin Biki: Zuwan wannan jini da kuma lokacin da ya dauke yana da matukar muhimmanci


11


iyaye mata su kula da shi domin yana da alaka da sallar da zaki rama da kuma wacce ba zaki ramaba.


Idan jinin ya dauke mata kuma bayan ta yi wanka za'a sami gwargwadon raka'oi biyar kafin rana ta fadi to zata yi sallar azahar da kuma la'asar, idan kuma kafin alfijirine za'a sami raka'oi hudune to zata sallaci magariba da lisha. Tirkashi!. Da yawa wasu matan idan sun sami tsarki da daddare ba abinda suke tsammani sai sallar asuba, idan kuma da ranane basa ilssafa fara sallah sai magariba ta yi, wanda yake wannan danyan kuskurene kuma laifine maigirman gaske.


Wadannan sune larurorin da shara'a ta yadda da su har mutum sallah ta kai shi loakcin laruri, amma aiki a ofis ko baki balle mitin ko aikin gona ko hada-hadar kasuwanci wadannan ba laruraba a shar'ance, kawai da zarar loakcin sallah ya yi sai ka tashi kaje ka gabatar da ita.


Sallah itace mafi girman ibada da ake so mutum musulmi ya bata kulawa, ranar alkiyama idan sallah ta gyaru to da izinin Allah komai zai zo da sauki.


Amma yadda wasu suka dauka na idan sun fita harkokinsu sai sun dawo gida za su hada azahar da la'asar, sannan su biyo da magariba da lisha wannan tsantsar sabon Allah ne, babban abinda ake so mai wannan dabi'a ya tuba zuwa ga Allah ya ci gaba da gabatar da kowacce sallah akan lokacinta.


Kammalawa: Daga wadannan bayanai mun san muhtarin sallah da kuma larurinta da kuma abainda ake nufi da larurin sune wadannan abubuwa da aka lissafo, kuma mun fahimci


12


gabatar da kowacce sallah a lokacinta shine mafi alheri ga kowa da kowa, Allah ya yi mana jagora.


Rubutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu



Posts na kwanan nan

QISSAR ANNABI ISA -AM ...

QISSAR ANNABI ISA -AMINCIN ALLAH A GARE SHI- DAGA CIKIN AL-QUR'ANI MAI GIRMA

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC