Abubuwa Bakwai Masu
Halakarwa:
(1- shirka)
Gabatarwa: Awannan lokacin da izinin Allah
mai kowa mai komai muna fatan kawo wadansu
abubuwa bakwai masu halakarwa, wadannan
abubuwa Ma'aikin Allah-Tsira da aminncin Allah
su tabbata a gare shi- Shine yace masu
halakarwa ne. Lalle dukkanin abinda Ma'aikin
Allah ya ce 'Abu kaza mai halakarwane' To lalle
ya kamata mutum musulmi ya yi kokarin sanin
wannan abin, tun da sauran nunfashinshi.
Ma'aikin Allah- Tsira da aminncin Allah su
tabbata a gare shi- Ya ce "Ku nisanci
abubuwa bakwai masu halakarwa ! (Sai
Sahabban shi -Allah ya kara musu yarda
suka ce) 'Wadanne abubuwane wadannan
ya Ma'aikin Allah?. Sai Ma'aikin Allah- Tsira
da aminncin Allah su tabbata a gare shi- Ya
ce " Shirka da Allah, da Asiri da Kashe raid
a Allah ya haramta a kashe ba tare da
hakki ba, da Cin Riba da cin Dukiyar
Maraya da Ja-da-baya lokacin gumurzu, da
Yiwa mace mumina wacce ta kame kanta
wacce bata san ya ake barna ba mutum ya
yi wa irin wannan macan kazafi." Wannan
Hadisi Bukhari ya ruwaitu a wurare da dama a
cikin littafinsa. To wadannan fa sune abubuwa
bakwaidin da ma'aikin Allah- Tsira da aminncin
Allah su tabbata a gare shi- ya gargadi wannan
al'umma, yace ku yi nesa da su kada ku
kuskura ku yi kusa da su.
4
Ayanzu wadannan abubuwa bakwai su muke
fatan zamu yi bayaninsu daya bayan daya, da
yardarm Allah, muna rokonShi da sunayanSa
kyawawa da siffofinshi madaukaka da ya yi
mana jagora.
Abu Na Farko: Shirka da Allah. Itace 'hada
bautar Allah da wani' wannan ya nuna cewa
bautawa Allah Shi kadai, shine abinda yake
daidai, amma hada Allah da wani, bai taba
halatta. Wannan yasa Allah madaukakin sarki
ya dinga turo Annabawa da Manzanni do min su
tabbatar da tsan-tsar Tauhidi, haka kuma
Annabawan da Manzannin suka tsaya tsayin
daka domin tabbatar da sun isar da wannan
aike da aka yi musu, muna shaidawa da cewar
Annabawan Allah da Manzannin shi sun isar da
sakon da ya aikosu da shi.
Ma'aikin Allah ya dauki tsawan she karu goma
cur yana kira zuwa ga tsantsar Tauhidi acikin
shekaru ashirin da uku da ya yi yana raye
bayan aiko shi a matsayin Manzo, wanda hakan
ya ke nuna mana matsayin tauhidi. Ya tura
wakilai da yawa wurare daba-daban, misali ya
tura Mu'azu Dan Jabal zuwa kasar Yaman yace
"Lalle kai zaka je wurin mutanan da suna dauke
da littafi, Farkon Abin da zaka kira su akai shine
su kadaita Allah'' wannan Hadisi Bukhari ya
ruwaitoshi. Wannan bayani zai tabbatar mana
da cewa lalle ya wajaba mu tsaya domin
5
karanta da karantar da Tauhidi, domin da Tauhidi ne mutane za su rabauta duniya da lahira, da shi ne kuma za'a sami hadinkan a'ummar musulmi baki dayanta, ta zama 'Tsintsiya madaurinki daya' wanda wannan shi ne matan ko wanne musulmi. Ita shirka da Ma'aikin ya fara lissafata acikin jerin gwanon wadannan abubuwa guda bakwai, tana da matukar hadarin gaske, daga cikin manyan hatsarinta wanda ba wanda ya ke so ya afka, ita shirka tana tabbatar da mutun cikin azabar Allah har'abada. Tana sa Mutun ya rasa ceton Manzan Allah Tsira da amincin Allah su tabbata agareshi. Tana sa mutum ya yi asarar dinbin ayyukan alheri da ya yi a duniya, kamar taimakawa nakasassu, sadar da zumunci…'. Saboda haka dukkan wani aikin ibada da Allah da Manzanshi su ka yi umurni da ayi to mutum ya tabbatar ya yi shi ga Allah kadai kada ya hada kowa tare da Allah. Kuma idan akace Ibada ana nufin 'Gamamman suna ne da yake tara dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi' to kaga anan muna da nau'ukan ibada masu tarin yawa kamar, Karatun Kur'ani, Sallah, Azumi, Salatin Annabi, Is'tigfari, Hailala, Sada zumunci,Gaida mara lafiya, Yanka, Neman tsari, Neman Agaji, Tawakkali, Kauna, So da sauran su, wadanda ba'a ambata ba dukkan su na Allah ne Kadai kada mutum ya kuskura ya karkatar da wani nau'i guda zuwa ga wanin
6
Allah, domin Allah yana cewa 'Ku bautawa Allah (Shi kadai) kada ku hada shi da komai' Suratun-Nisa'i, aya ta 36, da kuma fadin Allah adai cikin Surar 'Lalle Allah baya gafarwa idan akai Shirka da shi, yana gafarta abinda bai kai haka ba, dukkan wanda ya yi shirka da Allah to hakika ya kirkiri Zunubi mai girma' Suratun –Nisa'I aya ta 48. wanna yasa Annabawa da Manzanni ba su bari anhada su da Allah wurin bautaba domin sun san basu can-canta ba, Allah kadai mabuwayi shine ya can-canta Maganganun Annabi Isah –Amincin Allah ya tabbata a gare shi- cikin suratul Ma'idah sun tabbatar da haka. Hakanan maganganun Ma'aikin Allah cikin Hadisanshi ingantattu haka kuma. KarkasuwarShirka: Malamai sun yi bayanin cewa shirka ta kasu kashi biyu; Kashi na farko: Shirkar da Take futar da mutum da musulunci (Allah ya Tsare mu) Kashi na biyu Shirkar da bata fitar da mutum daga musulunci, Amma tana da mummunan Hatsari (Allah ya tsare mu ya kare mu da su baki daya) malamai sukan yi missali kamar: Riya (Yi don again) Wannan shine mutum ya yi dukkan wata ibata ga Allah amma yana son agani domin a yaba, ko ace yana da kokari ko ya burge. Mutum ya san cewa idan ya yi aiki
7
domin a gani ya sani ya yi riya, sai ya nemi Allah ya yafe (Allah ya yafe mana baki daya) wannan yana shafan ayyuka sai ai fatan ki yayewa, haka kuma Jiyarwa: wato mutum ya yi don aji kodai ace yana da murya ko makamantan haka, ko kuma ya yi ibadar shi daga shi sai mahaliccin shi sai yazo yana bada labari, ko ana fira sai aka ganshi yana gyangyadi aka ce mallam lafiya? sai ya kada baki ya ce 'Ai na kwana na yi ina nafilfili ko ina karatun Kur'ani ko Zikiri, da sauransu, ko ana zaune yace azuminnan yana banwahala al'hali ba watan Ramadan ake ciki ba 'ka ji yana cewa ai azumin litinin da alhamis baya wuceni, da dai makamantansu, asani ba muna hukunci akan ayyukan mutane bane amma 'Gyara kayanka bai zama sauke mu raba ba' sabo da haka ayi kokarin ankyautata ayyuka domin Allah. Anan sauda yawa mutum yakan yi yunkurin zai aikata wani kyakkyawan aiki wanda Allah yake so sai ya ji kamar mutane zasu gani su yaba saboda haka bari ya hakura? Idan mutum ya samu kanshi cikin irin wannan hali ya aikata aikin da yake so ya aikata wannan tsoron da yaji shi ake bukata shaidanne yake son ya yi amfani da shi domin ya hana shi. Saboda haka kowa ya yi kokari yaga asalin niyyar sat a zama domin Allah, sauda yawa magabata sun sha yin Magana akan 'Ikhlasi' wato yi domin Allah, muna fatan Allah ya karba mana.
8
Rantsuwa da wanin Allah. Rantsewa da
wanin Allah yana daga cikin dinbin abubuwan
da Ma'aikin Allah ya hana, domin babu wani mai
girma da za'a rantse da shi Inba Allah ba.
Ma'aikin Allah cewa ya yi "Duk wanda zai rantse
to ya rantse da Allah ko kuma ya yi shiru''
hasali ma duk wanda ya rantse da wanin Allah
rantsuwar bata yi ba (bata kulluba) kuma sai ya
yi gaggawar tuba zuwa ga Allah. Amma Allah,
Sarki mabuwayi mai girma da daukaka mai
ikone akan ya rantse da komai, domin babu
wanda zai tambaye Shi, akan haka Allah Ya
rantse da rayuwar Manzan Shi Annabi
Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata
agare shi ya kuma rantse da rana, wata, hantsi,
dare. Da dai suransu.
Kammalawa : Awannan takaitaccan bayani da
yagabata na munsan hatsarin dake cikin Shirka
da Allah wacce Ma'aikin Allah ya tsoratar da mu
ita, da irin alherin da yake cikin Tauhidi. Akaro
na gaba bayani zai zo akan abu na biyu da
Ma'aikin Allah ya ce munisanta kada mu
kuskura mu yi kusa da shi wato Sihiri (Asiri)
Allah ya karemu ya kuma tabbatar da akan
karantarwar Ma'aikin Annabin Tsira Annabi
Muhammad Tsira da amincin Allah su tabbata a
gare shi.
9
Rbutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu