Labarai




FASSARA LITTAFIN:


GIMSHIKAI SHIDA MASU GIRMA


Wallafar:


Shaikhul Islam Muhammad bn Abdulwahhab.


Fassarar:


Ibrahim Abdullahi


Dubawar:


Aliyu Muhammad Sadisu


(Hausa).


2


Gabatarwar mai fassara


Da suna Allah mai rahma mai jin kai, Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, Tsira da aminci su tabbata ga mafi daraja daga cikin talikai, da iyalansa da kuma sahabbansa masu tsarki.


Bayan haka, wannan littafi mai suna: "Gimshikai shida masu girma" wanda mujaddid Imam Muhammad Dan Abdulwahab ya rubuta ya kunshi: 1. Kyakkywar alaka tsakanin bawa da Ubangijinsa. 2. Hadin kai acikin addini da tsawatarwa game da rabuwa a cikin sa. 3. Biyyaya da da'a ga shuwagabani. 4. Bayani ga ma'abota ilimi da fahimta acikin addini. 5. Bayani akan waliyan Allah. 6. Maida martani kan shubuhar da shaidan ya sanya wa mutane wajen barin bin kur'ani da hadisi. Da wannan kwarya-kwaryar aiki muke fatan Allah mai girma da daukaka ya amfanar damu, ya sanya mana ikhlasi, ya karba mana ya kuma nauyaya mizanin ayyukanmu da shi (Amin).


3





Daga cikin mafi abin mamaki, da mafi girman alamomi wadanda suke nuni akan girman Allah mai mulki kuma mai rinjaye, shine gimshikai guda shidda wadanda Allah madaukakin sarki ya yi bayaninsu ga gama-garin mutane sama da zaton masu zato, sa'anaan mafi yawan masu wayo daga cikin 'yan adam suka kuskure (fahimtar su) sai dai kadan daga cikin marasa yawa.


Asali Na Daya: Tsarkake addini ga Allah madaukakin sarki wanda yake shi kadai ba shi da abokin tarayya, da kuma bayani game da kishiyar haka wanda shine shirka (Bauta ga wanin Allah ko hada Allah da wani) da kuma kasancewan mafi yawan ayoyin Kur'ani sun yi bayanin haka ta fuskoki da dama da irin zance wanda dolo na iya fahimta, sa'annan bayan abin da ya faru yafaru game da al'ummah, sai shaidan ya bayyanar musu ikhlasi (Yi domin Allah) ta hanyar cin zarafin bayin Allah salihai, da kuma hana su hakkokin su, kuma sai shaidan ya bayyanar musa da shirka da Allah ta hanyar soyyaya da mutanen da suke salihai tare da bauta masu.


Asali Na Biyu: Allah ya yi umurni da hadin kai a cikin addini, kuma ya yi hani game da rabuwar kai a cikin sa, sai Allah ya yi bayanin haka matukar bayani yadda gama-garin mutane za su fahimta, kuma ya hane mu da kar mu zamo kamar wadanda suka raba kawunansu kuma suka samu sabani kafin mu sai Allah ya hallaka su, kuma ya ambata cewa ya yi ma musulumi umarni game da hadin kai a cikin addini, kuma ya hane su da rabuwar kawuna a cikin sa, kuma duk abin da aka ruwaito na hadisi yana kara bayyanar da wadannan abubuwa masu ban mamaki. Sa'anan abin da ya kasan ce na alamarin mutane cewa rabuwar kawuna acikin rukunan addini da rassa shine ilimi da


4


fahimtar addini, hadin kai kuma a cikin addini babu mai jawo hankali akai sai zindiki ko mahaukaci.


Asali Na Uku: Hakika ji da bi ga wanda aka wakilta ko-da bawa ne yin haka yana daga cikin hadin kai, sai Allah ya bayyanar da haka ta nau'in bayanai a shar'ance kuma a hukunce, sa'annan irin wannan asalin mafi yawa daga cikin masu da'awar ilimi basu san shi ba, to yaya kuma za su yi aiki da shi?.


Asali Na Hudu: Bayanin ilimi da mallamai da kuma fikhu da masu ilimin fikhu, da kuma bayanin wandanda suka yi Kaman ce-ceniya da su amma ba su daga cikinsu, hakika Allah madaukakin sarki ya yi bayanin wannan asalin a cikin farkon suratul Bakara daga inda yace:





((Ya ku 'ya'yan Israila! (wato Annabi Ya’akub) ku tuna ni'mata wadda na nimta ta a gareku, kuma ku cika alkawari na zan cika maku alkawarin ku.......)) Suratul Bakara, aya ta: 40.


Har zuwa fadinsa (Allah madaukakin sarki) kafin anbaton Annabi Ibrahim tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi:





((Ya ku 'ya'yan Israila ku tuna ni'mata wadda na ni'mta ta a gareku, kuma na fifita ku a kan sauran halittu)). Suratul Bakarah, (40-47). Kuma abin da zai kara bayyanar da wannan a fili shi ne abinda ya tabbata karara a cikin sunnah (tafarkin dai-dai) game da wannan zance ya yawaita bayanin da yake


5


fayyatacce ga dolayen gama-garin mutane, sa'anan wannan ya zama wani abu banbarakwai, abubuwa suka kasance har ilimi da fahimtar addini ya zamo (wai shi ne) bidi'a da bata, kuma abin da suka zaba su, shi ne cudanya gaskiya da karya. Sai ilimin da Allah ya farlanta a kan halittu kuma ya yabe shi babu mai lura da shi sai zindiki ko mahaukaci, sai kuma wanda ya kasance mai inkari da kiyyaya game da haka, kuma ya yi gargadi da hani daga barin sa shi ne malami mai fahimtar addina.


Asali Na Biyar: Bayanin Allah madaukakin sarki game da waliyyan Allah da babbancewa tsakanin su da wadanda suka yi kama da su daga cikin munafukai masu girman kai ga umurmin Allah, Wannan aya daya ta Suratul Ali Imran ta wadatar a kan haka, fadin (Allah madaukakin sarki:





"Kace; in kun kasance kuna son Allah to ku bi ni Allah zai so ku". Suratu Ali Imran, aya ta: (31) Haka kuma da aya guda ta suratul Ma'ida, ita ce fadin (Allah madaukakin sarki): "Ya ku wadanda suka yi Imani! Duk wanda ya yi ridda daga cikin ku daga barin addininsa, da sannu Allah zai zo da wasu al'ummah suna son shi (Allah) kuma yana son su" Suratul Ma’idah, aya ta:(54). Da kuma aya a cikin suratu Yunus, ita ce kuwa fadinsa (Shi Allah madaukakin sarki):





" Ku saurara, lallai waliyan Allah babu tsoro a tare dasu haka kuma ba bakin ciki* Su ne dukkanin wadanda su ka yi Imani kuma su ka kasance masu jin tsoron (Allah)” Suratu Yunus, aya ta: (62-63).


Sa'annan mafi yawa daga cikin masu da'awar ilimi, kuma ake ganinsu su ne mafi kusa da shiriya da kuma kiyaye dokokin Allah, suka ce lalle waliyyai babu makawa sai duk sun bar bin manzanin Allah (wai su ma suna da ta su shari’ar), duk wanda ya bi su to baya tareda su.


Haka kuma sai sun bar jihadi kuma duk wanda ya yi jihadi baya tare da su, babu makawa sai anbar imani da takawa, duk wanda ya kudurta imani da takwa baya tare da su. Ya Ubangiji muna rokon ka yafuwa da lafiya, lalle kai mai jin rokone.


Asali Na Shida: Maida raddi ga shubuhar da shaidan ya Sanya wajen barin aiki da Kur'ani da kuma bin Sunnah (karantarwar ma’aikin Allah). Sai dai bin ra'ayi da son zuciya mai kawo rabuwar kai da sabani, Alkur'ani da Sunnah babu mai neman sanin su sai yankanken mujtahidi. Shi kuma mujtahidi a wurin su, shine wanda ya siffanta da kaza- da kaza da irin siffofin da kila baka samunsu baki daya ga Abubakar ko Umar (Allah ya yarda dasu), to in mutum bai kasance da irin wadannan siffofi ba, sai ya kawar da kai dole wanda babu shaku ko wata matsala acikin, duk wanda ya nemi shiriya daga Alkur'ani ko Hadisi, to wannan ko dai zindiki ko kuma mahaukaci, don wahalar fahinmta da ke cikin su.


Kai!, Tsarki ya tabbata ga Allah kuma muna gode masa, sau nawa Allah ya bayyanar da haka a shar'ance da hukunce, ta hanyar halittu da kuma al’amari bisa maida raddi ga wannan la'ananniyar shubuhar ta fuskoki da dama wadda ta yadda kowa ma zai


7


gane ya kuma fahimta, amma mafi yawan mutane basu sani ba. (Allah madaukakin sarki) yana cewa:





(( Hakika zance na gaskiya ya tabbata a kan mafi yawan su amma basu yin Imani. * Lalle mun sanya mari a wuyoyin su wanda ya cike masu zuwa habban su sai suka zamo masu daga kansu sama.* Kuma muka sanya gabansu da kuma bayansu shamaki sai muka lullube su basa ganin gaskiya.* kuma Dai-dai ne kayi masu gargandi ko baka yi musu gargadin ba, ba za su yi Imani ba.* Abin sani kadai wanda zasu amfani da gargadin su ne masu neman bin Ambato (Alkur’ani) kuma su ka ji tsoron Allah mai rahma a boye, to kayi masu bushara da samun gafara da kuma lada mai girma)). Suratu Yasin, aya ta: 7-11).


Kuma karshensa (shi wannan littafin, shi ne) Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu, kuma Allah ya yi dadin tsira ga shugabammu (Annabi) Muhammad, da iyalanshi da kuma sahabbanshi da amincewa mai tarin yawa har zuwa ranar sakamako.



Posts na kwanan nan

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA