Labarai




99


Kuma hakika da yawa daga cikin malamai da masuu bauta cikin kiristoci a da da yanzu sun karbi gaskiyar da ta Annabi Muhammad yazo da ita, kuma daga cikin wadanda sukayi sauri suka shiga musuliunci akwai sarkin habasha Annajjashi a zamanin Manzan Allah (S.A.W), kuma ya kasance cikin kiristoci kuma yana cikin wadanda suka san littattafan kiristoci masu tsarki kuma ya san busharorin da suke magana akan cewa akwai wani Annabi da za’a aiko bayan Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi, kuam ya kasance mutum ne da ke dauke da imani mai haske kuma ya rungumi ingantacciyar kiristanci mai hankali, wacce take nesa ga barin san rai, Ummu Salmah matar Annabi (S.A.W) tana cewa: “ lokacin da muka sauka a garin habasha sun amshe mu hannu bibbiyu mafi alherin su she ne Najjashi, mun aminta akan addinin mu, kuma mun bautawa Allah, ba’a cutar da mu, kuma bama jin wani abu da muke ki, lokacin da labarin haka ya isa wurin kuraishawa sai suka yanke shawarar turo mutane biyu zuwa wurin Najjashi masu karfi, kuma su kawo ma najashi kyauta cikin abunda yafi so na kayan makkah, kuma daga cikin abunda ake kawo masa da yafi kauna shi ne fatun dabbobi, sai suka tara masa fatu, kuam basu bar wani waziri ba cikin waziran sa face sai da suka zo masa da kyauta, sai suka aiko Abdullahi dan Abi Rabi’ah Almakhzumy da kuma Amru dan Aas dan wa’il Assahamy da su, kuma suka basu labarin abunda ya wajaba su aikata, sai suka ce musu: ku ba kowane waziri kyaut kafin kuyi wa Najjashi magana game da su, sai ku ba Najjashi nashi kyautan, sai ku neme shi da mika muku su kafin yayi musu magana, sai tace: sai suka fito, sai suka zo wurin najjashi


100


kuma a lokacin muna wurin shi a cikin alherin gida, kuma a wurin mafi alherin makwabci, babu wani waziri face sai da suka bashi kyautar sa kafin suyi wa Najjashi magana sai suka ce wa kowane waziri daga cikin su: hakika su wadancan sun kafurcewa addinin mu ne, kuam suka bi wani karamin yaro dan wauta, sun rabu da addinin mutanen su, su kuma basu shiga cikin adinin ku ba, kuma sun zo da wani addini sabo wanda mu bamu san shi ba haka nan ku, kuma hakika sarki ya turo mu babba a cikin mutanen su, dan ya dawo da su zuwa gare shi, in har mun ma sarki magana game da su to ku bashi shawarar ya mika su zuwa gare mu kuma kada yayi magana da su, saboda mutanen su sunfi su hangen nesa, kuma sunfi sanin abunda suka aibata su da shi, sai suka ce musu: to, sai daga baya suka kaiwa Najjashi tashi kyautar, sai ya karba, sai suka mai magana suka ce masa: ya kai sarki, lallai wasu wawayen yaran mu sun gudu ne suka zo gurin ka, sun rabu da addinin mutanen su, su kuma basu shiga adinin ka ba, kuma sun zo da sabon addini, wanda ko mu ko kai bamu sanshi ba, kuma hakika mun turo maka masu daraja daga cikin mutanen su daga iyayen su da baffannin su da dangin su, dan ka basuu su, dan sun fiso hangen nesa, kuma sunfi sanin irin aibantawan da sukeyi, kuma suka zarde su game da shi, sai tace: kuma babu abunda yafi ba Abdullah bn Arrabi’ah da Amru bn Al’aas haushi irin ac Najjashi zai saurari zancen su, sai waziran da ke tare da shi suka ce: sunyi gaskiya ya kai sarki, mutanen su sunfi su hangen nesa, kuma sunfi sanin aibantawar da suke yi, ka mika su a gare su kawai, sai su maida su zuwa garuruwan su da


101


mutanen su, sai yace: sai Najjashi ya fusata, sai yace: kada Alah ya taimake ni in ban mikasu zuwa gare su ba, kuma ni bazan ha’inci mutanen da suka zo makwabtaka da ni ba kuma suka sauka a gari na ba kuma suka zabeni suka bar kowa, har sai na kirasu inji ta bakin su game da abunda wadannan mutanen ke fada game da su, in har abunda suka fada gaskiya ne ti zan mika su zuwa gare su kuma zan maida ga mutanen su, in kuma ba haka bane to zan kare su daga gare su kuma zan kyautata makwabtaka da su matukar sunyi makwabtaka da ni, sai tace: sai ya turo yana kiran sahabban Manzan Allah (S.A.W), lokacin da dan sakon shi ya zo musu sai suka taru sai sashinsu yace wa sashi: me zamu ce wa wannan mutumin in mun zo wurin sa? Sai sukace: wallahi zamu fadi abunda muka sani ne da kuma abunda Annabin mu ya umarce mu da shi, ko mai zai faru akan haka sai dai ya faru, lokacin da suka zo- kuma lokacin Najjashi ya tara malaman sa na fada sai suka bubbude littattafan su a gaban sa- sai ya tambaye su yace: wane addini ne kuka rabu da mutanen ku saboda shi kuma ku baku shiga cikin addini na ba ko addinin wani a duniya? Sai tace: wanda yayi masa magana shi ne Ja’afar dan Abi dalib, sai yace masa: ya kai sarki, mu mun kasance mutane a jahiliyya muna bautan gumaka ne, kuma muna cin mushe, kuma muna aikata alfasha, kuma muna yanke zumunta, kuma munana makwabtaka, mai karfi na danne marar karfi a cikin mu, mun kasance akan wannan halin har zuwa lokacin da Allah ya aiko mana da wani Manzo a cikin mu mun san dangin sa da gaskiyar sa, da manar sa da kamewar sa, sai ya kiramu zuwa ga Allah dan mu kadaita


102


shi kuma mu bauta masa kuma mu bar abunda muke bautawa mu da iyayen mu koma bayan sa na duwatsu da gumaka, kuma ya umarce mu fadar gaskiya, da tsare amana, da sada zumunci, da kyautata makwabtaka, da kamewa daga aikata haramun, da kashe-kashe, kuma ya hane mu daga alfasha, da fadar karya, da cin dukiyar maraya, da yin kazafi ga kamammun mata, kuma ya umarce mu da bautar Allah shi kadai kada mu hada shi da komai, kuma ya umarce mu da sallah da zakkah da azumi- tace: sai ya lissafa masa al’amuran musulunci- sai muka gaskata shi kuma mukayi imani da shi, kuma muka bishi akan abun da yazo da shi, sai muka bauta wa Allah shi kadai muka daina hada shi da komai, kuma muka haramta abunda ya haramta mana, kuma muka halalt abunda ya halalta mana,sai mutanen mu sukayi ta’addanci akan mu sai suka azabtar da mu, kuma suka fitine mu akan addinin mu, dan su maida mu zuwa ga bautar gumaka mubar bautar Allah, kuma mu cigaba da hallata abunda muke halattawa na munanan ababe, lokacin da suka yi mana fin akrfi kuma suka zalunce mu kuam suka cutar ad mu kuam suka kangemu tsakanin mu da addinin mu, sai muka guda zuwa garin ka, kuma muka zabeka akan wanda ba kaiba, kuma muka kaunaci makwabtaka da kai, kuam muna fatar baza’a zalunce mu ba a wurinka ya kai sarki, sai tace: sai Najjashi yace masa: shin a tare da kai akwai wani abu da Allah ya saukar? Sai Ja’afar yace masa: eh, sai Najjashi yace masa: to ka karanta mun shi, sai ya karanta mai farkon suratu maryam, sai Najjashi yayi kuka har sai da wallahi ya jika gemun sa, sai suka fadawansa suka fashe da


103


kuka har sai da suka jika littattafan su, lokacin da suka ji abunda ya karanta musu, sai Najjashi yace: lallai wannan –wallahi- wannan da abunda Annabi Musa yazo da shi sun fito ne daga mahaskaka daya, sai yace wa wadanda kuraishawa suka aiko, ku koma, na rantse da Allah bazan mika muku su ba har abada kai ko sa da haka ma bazan yi ba, sai Ummu salmah tace: lokacin da suka fito daga wurin sa sai Amru dan Aas yace: wallahi gobe sai na fada masa aibun su sai ya kore su daga wurin sa, tace: sai Abdullahi dan Abirrabi’ah yace masa: kuma yafi tsoran Allahm dayan mu: kada ka aikata, domin su sunada iyan uwa a tare da mu duk da cewa su sun saba mana, sai yace: wallahi sai na bashi labare su suna cewa Annabi Isah bawa ne, tace: sai washe gari yaje wurin sa, sai yace masa: ya kai sarki lalai su na fadan wata magana mai girma game da Annabi Isah dan Maryam, to ka aika dan a tambaye su gameda abunda suke fada akan shi! Tace: sai ya tura yana tambayar su game da shi, tace: ba abunda ya same mu mai tsanani irin wannan abun, sai mutanen suka taru, sai sashin su yace wa sashi: me zaku ce gameda Annabi Isah idan ya tambaye ku gameda shi? Sai sukace: wallahi zamu fadi abunda Allah ne ya fada game da shi, da kuma abunda Amnzanmu yazo da shi, duk abunda zai faru akan haka saida ya faru, lokacin da suka zo wurin sa, sai yace musu: me kuke cewa game da Isah dan Mryam? Sai Ja’afar dan Abi dalib yace masa: muna fadan abunda Annabain mu yazo da shi ne game da shi, shi bawan Allah ne kuma Manzan sa kuma ruhin sa ne kuma kalmarsa ce da ya jefa zuwa ga Maryam mai tsarki, tace: sai Najjashi ya buga


104


hannun s ad kasa sai ya dauko wasu itace , sai yace: kamar yadda wannan icen yake haka Isah dan maryam yake kamar yadda ka fada, sai fadawan sa suka fara guna-guni lokacin da ya fadi abunda yafada! Sai yace: wallahi kun fadi gaskiya, ku tafi dan ku amintattu ne a kasa ta, duk wanda ya cutar da ku to sai an hukunta shi, sannan duk wanda ya zage ku sai na hukunta shi, ni bana bukatar ace inada zinari cike da gonakin habasha alhali ni na cutar wani daya daga cikin ku,ku maida musu da kyaututtukan su bamu da bukatar su, wallahi Allah bai amshi cin hanci daga gare ni ba lokain da ya maida mun da mulki na, kuma matukar yasa mutane sun mun biyaiyya to ni mai za sa bazan masa biyaiyya ba, tace: sai suka fita daga wurin sa suna tababbu an maida musu da abunda suka zo mai da shi, sai muka zauna a wurin sa a mafi alherin gida, tare da mafi alherin makwabci, sai tace: wallahi mu muna kan haka har lokacin da wani ya nemi kwace mai mulkin sa, sai tace: na rantse da Allahbamu taba bakin ciki ba kamar yadda zamuyi bakin ciki in akace wani yai galaba akan Najjashi, sai wani mutum da bai san hakkin mu ba kamar yadda najjashi ya san hakkin mu ba yayi rinjaye, sai tace: sai najjashi ya fita yaki da daddare, sai tace: sai sahabban Manzan Allah (S.A.W) sukace: waye zai fita yaje wurin yakin dan ya kawo mana labari? Sai Zubair dan Auwam yace:ni ne,tace: kuma ya kasance cikin mafi karanci shekarun sauran mutanen , sai tace; sai suka busa masa fata sai ya sanyata a kirjin sa, sai ya tafi cikin dare inda mutanen zasu hadu, sai yaje har ya shiga cikin su, tace: kuma muka dinga yin addu’a ga Najjashi da samun nasara


105


akan makiyan shi, da kuma tabbatar da shi akan garin sa, sai al’amarin habasha ya tabbata a gareshi daga baya, sai muka kasance a wurin sa a mafi alherin masauki har zuwa lokacin da muka koma wurin Manzan Allah (S.A.W) lokacin yana garin makkah.” Musnadul imam Ahmad.


Kuma mai adalci daga cikin ahlul kitbi bayan ya karanta abunda Alkur’ani yake fada game da Annabi Isah da mahaifiyarsa amincin Allah ya tabbata a gare su ya san cewa wannan gaskiya ne daga Allah, kuam hakika kiristocin da suke karbar musulunci sunfi yawa daga wadanda ba su ba kuma suna yadda da kusancen da ke tsakanin su da musulmai, kuam labarin hirqala sarkin ruum tare da Abi Sufyan kafin musuluntar sa shahararriya ce a cikin littattafan tarihi kuma tana nuna yadda kiristoci suka san gaskiyar manzancin Annabi (S.A.W) , Abdulllahi dan Abbas yana cewa: “ lallai abu Sufyan dan Harb ya bashi labari, cewa lallai Hirqala ya aika yana neman shi a cikin wata tawaga ta kuraishawa, lokacin su iyan kasuwa ne a garin sham a cikin lokacin da Manzan Allah (S.A.W) yayi sulhu tsakanin shi da Abu Sufyana da kuma kuraishawa, sai suka zo wurin sa a lokacin suna garin Iniyaa, sai ya kira su zuwa fadar sa, kuma a gefen shi a kwai manyan rumawa, sai ya kirasu kuma ya kira mai masa fassara, sai yace: a cikin ku waye yafi kusancin dangantaka da wannan mutumin da ke raya cewa shi Annabi ne? Sai Abu sufyan yace: sai nace: ni ne na fi su kusa da shi, sai yace: ku kawo shi kusa da ni, kuam suka kusanto da mutanen sa sai suka sanya shi a gaban shi, sai yace wa mai masa fassara: kace musu ni ina tambaya ne game da wannan mutumin, in sun mun karya to kum fada


106


mun cewa karya yake yi, wallahi ba dan kunyar ace nayi karya ba da na sharara masa karya, sai ya zama farkon abunda ya tambaye ni sai yace: yaya dangantakar sa take a cikin ku? Sai nace: shi a cikin mu yana da dangantaka madaukakiya, sai yace: shin ko akwai wanda ya taba yin irin wannan maganar da yayi a cikin ku kafin sa? Sai nace: a’a, sai yace: shin a cikin iyayen sa akwai mai mulki? Nace: a’a, sai yace: mabiyansa masu daraja ne ko kuma masu rauni? Sai nace: masu rauni ne a cikin su, sai yace: suna karuwa ne ko raguwa? Sai nace: karuwa suke yi, sai yace: shin a cikin su akwai masu ridda dan haushin addinin sa bayan ya shiga cikin sa? Nace: a’a, sai yace: shin kuna tuhumar shi da karya kafin ya fadi abunda ya fada? Sai nace: a’a, sai yace: to shin yana yaudara? Sai nace: a’a, mu yanzu haka muna cikin yarjejeniyar zaman lafiya ne da shi bamu san abunda zai aikata a ciki ba, sai yace: ban samu wata kalma ba da zan soke shi da ita ba sai dai wannan, sai yace: to kun yake shi? Sai nace: eh,sai yace: yaya yakin naku da shi ya kasance? Sai nace: yaki tsakanin mu dan zagaye ne, yana cin galaba akan mu mu ma muna cin galaba akan shi, sai yace: da me yake umartar ku? Sai nace: yana cewa ne: ku bautawa Allah shi kadai kuma kada ku hada shi da komai, kuma ku bar abunda iyayen ku ke fada, kuma yana umurtar mu da sallah da azumi da gaskiya da kamewa da sada zumunci, sai yace wa mai fassarar: kace masa: na tambaye ka akan dangantakar sa sai ka ambaci cewa shi a cikin ku yanada dangi masu daraja, hakanan manzanni ana aiko su ne daga mafi darajar dangin mutanen su, kuma na tambaye ka shin a


107


cikin ku akwai wanda ya taba fadar irin wannan maganar, si kace a’a, sai nace da ace wani ya fada irin wannan maganar kafin sa da nace shi mutum ne da yake kwaikwayon abun da wani ya fada kafin sa,, kuma na tambaye ka shin a cikin iyayen sa akwai sarki, sai kace a’a, si nace: da ace akwai sarki a cikiniyayen sa da nace mutum ne da ke san ulkin baban sa, kuma na tambaye ka shin kuna tuhumar shi da karya kafin yace shi annabi ne, sai ka ce a’a, hakika na sani cewa bazai bar karya ba akan mutane amma kuma yayi wa Allah karya, kuma na tambaye ka shin masu daraja ne ke binsa ko kuma masu rauni, sai kace masu rauni ne ke binsa, to kuma su ne mabiya manzanni, kuma na tambaye ka suna karuwa ne ko raguwa, sai kace suna karuwa ne, haka al’amarin imani yake har ya cika, kuma na tambaye ka cewa mutanen sa na ridda daga addinin sa dan jin haushibayan ya shiga, sai kace, a’a, haka ima ni yake har sai zuciya ta cakuda da dandanon sa, kuma na tambaye ka shin yana yaudra, sai kace, a’a to haka manzanni suke basa yaudara, kuam na tambayeka dame yake umurtar ku, sai kace yana umurtar ku da bautar Allah shi kadai kum kada ku hada shi da komai, kuma hana hana ku dag bautar gumaka, kuma yana umartar ku da salllah da gaskiya da kamewa, idan har abunda ka fada gaskiya ne to da sannu zai mallaki in da kafafuwa na suke dinnan, kuma ni hakika nasan zai zo amma ban tunanin cewa a cikin ku bane da ace ni na san cewa zan kai zuwa gare shi da na dau dawainiyar tafiya zuwa gare shi, kuma da zan kai wurin sa to da na wanke kafafun sa sai yace a kawo masa sakon da manzan Allah


108


(S.A.W) ya aiko masa ta hannun Dihya zuwa ga sarkin Ruum Busra, sai ya mika shi zuwa ga Hirqal sai ya karanta shi, sai ga shi a bunda ke cikin sa shi ne: da sunan Allah mai rahama mai jin kai, daga Muhammadbawan Allah kuma manzan sa zuwa ga Hirqala sarkin ruum: aminci ya tabbata ga wanda yabi shiriya, bayan haka, lalai ni ina kiranka da kira na musulunci, ka musulunta sai ka kubuta, Allah zai baka ladarka nin ki biyu, in kuma har ka juya baya to kana da zunubin arisawa a kan ka kuma: {ya ku ma’abota littafi ku taho zuwa ga wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu da ku cewa kada mu bautawa kowa sai dai Allah kuma kada mu hada shi da komai kuam kada sashin mu su riki wasu sashi ababen bauta koma bayan Allah in kuma suka juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne}. Sai Abu Sufyan yace, lokacin da ya fadi abunda ya fada, kuma ya gama karanta wasikar, sai muryoyi sukayim yawa a inda yake kuam sautuka suka dagu sai muka fita, sai nace wa abokai na lokacin da muka fito: hakika lamari dan baban Kabsha ya girmama, lallai bizandawa suna shakkar ka, ban gushe ba inada yakini cewa zai ci nasara kuma addinin shi zai yadu a nan kusa har sai gashi Allah ya sa mun san shiga musulunci.” Sahihul bukhari.


Haka nan ma lokacin da tawagar kiristocin Najran suka zo wurin manzan Allah (S.A.W) kuma su sitin ne akan abun hawa, al’amarin su na komawa ga mutane sha hudu daga cikin su, dukkan su kuma al’amuran su na komawa ga mutane uku sune mafiya darajar su da kuma jagororin su, su ne: Al aqib da Assayyid da Abu Harisa bn Alqamah, sai suka fara jayaiyya


109


game da al amarin Isah amincin Allah ya tabbata a gareshi, kuma suna raya cewa shi dan Allah ne ko kuma shi ne Allah, kuma su sun kafe akan batar su, bayan da Manzan Allah (S.A.W) ya tsaida musu hujjoji cewa Isah shi bawan Allah ne kuma manzansa ne, sai suka tambaye Annabi me yake fada game da Annabi Isah? Sai yace: shi bawan Allah ne kuma ruhinsa ne da kuma kalmar sa, sai suka ce: a’a shi ne Allah, ya saukao daga mulkin sa sai ya shiga cikin Maryam, sai ya fito daga cikin ta dan ya nuna mana ikon sa da lamarin sa,! Shin ka taba ganin wanda aka halitta ba da uba ba cikin mutane? Sai Allah madaukakai ya saukar da fadar sa: “ lallai misalin Isah a wurin Allah kamar misalin Adam ne ya halicce shi daga turbaya sa’annan sai yace masa kasance sai ya kasance”. haka Allah ya baiyyana al’amarin Annabi Isah amincin Allah ya tabata a gareshi kuma ya kirkiri halittar sa da kuma mahaifiyar sa tun gabanin haka, kuma ya umarci manzan Allah (S.A.W) da yayi mubahala da su in har basu amsa kiran sa ba kuma suka bishi bishi ba, sai Annabi (S.A.W) ya kirasu dan yin mubahala, da cewa shi zai zo da iyalan sa da yaran sa, suma su zo da iyalan su da yaran su, sai su roki Allah madaukaki da ya saukar da azabar sa da tsinuwar sa akan makaryata, sai Annabi (S.A>W) ya zo da Aliyu dan Abi Dalib da Fatimah da Hassan da Hussain Allah ya kara musu yadda, sai yace: “ wadannan su ne iyalai na”. Sai tawagar mutanen Najrana suka yi shawara a tsakanin su: shin su amsa masa ne akan hakan? Sai ra’ayin su ya zo daya akan cewa baza su amsa masa ba saboda sun san cewa in har sukayi mubahala to sun halaka su da yaran su da iyaln su, sai sukace masa: “ ya kai baban Kasim, barmu muyi shawara game da al’amarin mu, sai muzo maka da labarin


110


abunda muke so mu aikata cikin abunda ka gaiyyace mu zuwa gare shi”. Sai suka tafi suka barshi, sai suka kebe da Aqib, kuma shi ne yafi kowa hangen nesa a cikin su, sai suka ce: “ ya kai bawan Annabi Isah, mai kake gani?” sai yace:” wallahi ya ku taran kiristoci hakika kun san cewa lallai Muhammad Annabi ne da aka aiko, kuma hakika yazo muku da gaskiya game da labarin Annabi Isah, kuma ku kun san cewa babu wasu mutane da suka taba tofin Allah tsine tsakanin su da Annabin su kuma manyan su su rayu, kuam kananan su baza su girma ba, kuma wannan shi ne karshen ku in har kuka aikata, to idan har kuka ki yadda sai dai ku dauwwama akan addinin ku da kuma dogewa akan abunda kuke fada gameda Isah, to kuyi bankwana da Muhammad sai ku koma garin ku”. Sai suka zo wurin manzan Allah (S.A.W) sai suka ce: ya kai baban Qasim, munyi shawarar baza muyi tofin Allah tsine da kai ba, kuma mu zamu barka akan addinin ka zamu koma da addinin mu, sai dai muna so ka tura wani mutum daga cikin sahabban ka wanda ka yardar mana da shi, wanda zai yi hukunci tsakanin mu cikin abunda muke sabani na dukiyoyin mu, domin ku yaddar du ne a wurin mu.


111


Allah ya siffanta mabiya Annabi Isah a cikin Alkur’ani na gaskiya da rangwame da tausayi da san addini da ruko da shi, Allah madaukaki yace: “ sannan muka biyo da manzannin mu a bayan su kuma muka biyu da Isah dan Maryam kuma muka bashi Injila kuma muka sanya rangwame a cikin zukatan wadanda suka bishi da tausayi da kuma rahabaniyanci wanda suka kirkire shi wanda bamu wajabta shi akan su ba sunyi haka ne badan komai ba sai dan neman yaddar Allah amma basu kula da ita ba hakikanin kula sai muka baiwa wadanda sukayi imani a cikin su ladar su kuma da yawa daga cikin su fasikai ne (27)” suratul Hadeed, aya ta: 27.


Kamar yadda Allah madaukakai ya siffantasu a cikin Alkur’ani cewa su suna cikin wadanda sukayi gaggawar kamar gaskiya da kuma taimakon Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi wajen yada da’awar sa, sai Allah ya umarci musulmai da su zama irin mataimaka Annabi Isah kua suyi gaggawa wajen taimakon Annabi Muhammad (S.A.W) kua su agaza masa wajan yada da’awar sa, sai ya neme su da su da yin koyi da su a cikin wadannan kyawawan halayen, Allah madaukaki yace: “ ya ku wadanda sukayi imani ku zamo mataimaka Allah kamar yadda Isah dan Maryam yace wa hawariyawa waye zai taimaki Allah sai hawariyawa sukace mu ne mataimaka Allah sai wasu jama’a sukayi imani daga cikin mutanen bani isra’ila wasu kuma suka kafurta sai muka karfafa


112


wadanda sukay imani akan makiyan su sai suka zama masu cin nasara (14)” suratus Saffi, aya ta: 14.


Sannan Allah ya siffan su da cewa sune mafi kusa da kaunar musulmai cikin mutane fiye da wanda ba su ba, saboda Annabi Muhammad (S.A.W) ya zo ne bayan Annabin su, lokacin gajere ne ba kamar yadda lokacin yake ne ba tsakanin Annabi Muhammad (S>A.W) da kuma Annabi Musa amincin Allah ya tabbat a agare shi, wannan ne yasa yahudawa sukafi kiyaiyya ga musulmai, idan har yahudawa suna iyaiyya da kiristoci duk da cewa Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi zamanin shi na kusa da na Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma yana cikin dangin mutanen bani isra’ila, to ya kake tunani idan har zamani ya tsawaita kuma shi Annabi Muhammad (S.A.W) ya fito ne daga tsatsan Annabi Ibrahim amma ta bangaren dansa Annabi Isma’il amincin Allah ya tabbata a gare su baki daya!! Kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lallai zaka samu cewa mafiya tsananin gaba ga wadanda sukayi imani cikin mutane sune yahudawa da wadanda suke shirka kuma lallai zaka samu mafi kusa da kauna ga wadanda sukayi imani su ne wadanda sukace mu kiristoci ne saboda kuwa a cikin su akwai masu bauta da malamai kuma lallai su basa girman kai (82) kuma idan suka ji abun da aka saukar akan Manzo sai kaga idanun su suna kwarara da hawaye saboda abunda suka sani na gaskiya suna cewa ya ubangijin mu unyi imani ka rubuta mu cikinmasu shaida (83) kuma saboda me baza muyi imani da Allah ba da kuma abunda ya zo mana na gaskiya ba kuma muna kwadayin ubangijin mu ya shigar ad mu cikin mutane salihai (84) sai Allah ya saka musu da abunda suka fada da aljannah wacce


113


koramu ke gudana a karkashin ta suna masu dauwwama a cikin ta kuma wannan shi ne sakamakon masu kyautatawa (85)” suratul Ma’idah, aya ta: 82-85.


114


Hakika yahudawa sun saba da karyata Annabwansu cikin abunda ya gabata da kuma kashe su, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ kuma hakika mun ba Musa littafi kuma muka biyo da Manzanni a bayan sa kuma mun ba Isah dan Maryam hujjoji kuma mun karfafe shi da mala’ika Jibrilu to yanzu duk lokacin da wani manzo yazo muku da abunda rayukan ku basa kauna sai kuyi girman kai sai kuke karyata wasu kma kuke kashe wasu (87)” suratul bakara, aya ta: 87.


Saboda haka ne am sun yi yunkurin kashe Annabi Isah sosai sai dai Allah ya kare shi daga gare su, kuma lallai aqidar musulmai game da Annabi Isah dan Maryam ita cewa shi bai mutu ba kuma ba’a kashe shi ba kuma ba’a rataye shi ba sai dai shi an daga shi zuwa sama ne da ransa da jikin sa kuma lallai shi zai dawo kafin tashin alkiyama kuma ahlul kitabi zasu yi imani da shi dukkan su, kakamr yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ saboda warware alkawuran su da kafurcewarsu da ayoyin Allah da kuma kisan su ga Annabawa ba tare ad hakki ba da kuma cewar su zukatan mu sun rufe a’a Allah ne ya yi rufi akan su saboda kafurcin su basa imani sai iyan kadan (155) kuma da kafurcin su da kuma abunda suke fada gameda maryam na karya mai girma (156) da kuma fadar su cewa lallai mu mun kashe Isah dan Maryam manzan Allah su basu kashe shi ba kuma basu rataye shi ba sai dai an kamanta shi ne a gare su kuma lallai wadanda sukayi sabani a game da shi to suna cikin shakka akan shi


115


basu ad wani ilimi sai dai bin zato kuma su basu kashe shi ba da gaske (157) sai dai Allah ya dauke shi zuwa gare shi kuma Allah ya kasance mabuwayi mai hikima (158) kuma babu wani daga cikin ahlul kitabi face sai yayi imani da shi kafin mutuwar sa kuma ranar alkiyama zai zama mai shaida a kan su (159)” suratun Nisa’i, aya ta: 155-159.


Ibn Abbas Allah ya kara masa yadda yana cewa:” lokacin da Allah ya so dauke Annabi Isah zuwa sama ya fito wurin mutanen sa kuma a cikin gidan akwai mutane goma sha daya daga cikin hawariyawa, wato sai ya fito wurin su ta wata kofa daga cikin gidan, kuma kansa yana digarda ruwa, sai yace: lallai a cikin ku akwai wanda zai kafurce mun sau goma sha biyu bayan yayimimani da ni, sai yace: waye a cikin ku zai yadda a daura mai kamat asai a kashe shi a maimako na si ya kasance tare da ni a daraja ta? sai wani matashi da yafi su kankantan she karu ya mike, sai yace masa: zauna, sai kara maimaita musu abunda ya fada, sai wannan matashin ya mike, sai yace: zauna, sai ya kara maimaita musu abunda ya ce, sai wannan matashin ya mike, sai yace: ni ne, sai yace: to shi kenan kai ne din, sai aka saukar mai da kammanin Annabi Isah sai aka dauke Isah ta wani gefe na gidan zuwa sama, yace: sai gashi yahudawa sun zo neman shi, sai suka kama wanda yayi kama da shi sai suka kashe shi sai suka rataye shi sai wasun su suka kafurce masa sau sha biyu bayan sunyi imani da shi, sai suka rabu kashi uku, sai wasu sukace: Allah ya kasance a cikin mu har zuwa wani lokaci sai ya koma zuwa sama, wadannan su ne Ya’aqubiyya, sai wasu kuma suka ce: shi dan Allah ne a cikin mu ya zauna na wani lokaci a


116


cikin mu sai Allah ya dauke shi zuwa saama, wadannan sune Annasdoriyyah, sai wasu kuma suka ce: shi a cikin mu bawan Allah ne kuma Manzan sa ya zauna na wani lokaci sai Allah ya dauke shim zuwa sama, wadannan su ne musulmai, sai kungiyoyinnan biyu sukayi taimakekeniya suak hade kai akan musulmai, sai suka kashe su, musulunci bai gushe ba yana boye cikin daidaikun mutane ahr zuwa lokacin da Allah ya aiko da Annabi Muhammad (S.A.W), sai Ibn Abbas yace: kuma wannan shi ne fadar Allah madaukaki { sai muka taimaki wadanda sukayi imani akan makiyan su sai suka wayi gari suna masu nasara }.” Al bidayatu wannihaya ta Ibn kaseer.


Allah madaukaki yana cewa yana mai baiyyana hakikanin dauke Annabi Isah zuwa sama: “ sun kulla makirci kuma Allah ya na maida musu da kullin su na makirci kuma Allah shi ne mafi alheri daga masu makirci (54) lokacin da Allah yace ya kai Isah lallai ni zan kashe ka kuma zan dauke ka zuwa wuri na kuma zan tsarkake ka daga wadanda suka kafurta kuam zan sanya wadanda suka bika sama da wadanda suka kafurta har zuwa ranar alkiyama sannan wurina za’a maida ku sai inyi muku hukunci tsakanin ku cikinabunda kuke sabani a cikinsa (55) amma wadanda suka kafurta to zan azabtar da su azaba mai tsanani a cikin duniya da lahira kuma basu da mataimaka (56) amma kuma wadanda sukayi imani kuma suka aikata aiyyuka na kwarai sai a cika musu ladan su kuma Allah baya san azzalumai 957)” suratu Ali imaran, aya ta: 54-57.


Lallai aqidar cewa an kashe Annabi Isah da rataye shi da fansa a cikin kiristanci yana daga cikin abunda yahudawa suka shigar


117


da shi da kiristoci da masu bautar gumaka da mabiyan su a cikin addinin Annabi isah dan maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi,, saboda suna raya cewa wai Allah ya bada yaransa da a kashe shi da rataye shi dan ya ceci mutanebabu laifi akan kowa ya aikata baunda yaga dama hakika Annabi Isah ya dauke mai dukkan zunubai, babaumakawa wannan na daga cikin abunda ke kawo barna baya gyara mutane ta yaya rayuwar mutane zata inganta ba tare da wani tsari wanda suke tafiya a kan sa ba da kuma iyakoki da suke tsayawa a wurin su, ya za’a hada wannan da tsarin ubangiji wanda musulunci yazo da shi kuam ya baiyyana cewa lallai kowace rai tana rataye nwe da abunda ta aikata kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ ko wace rai tana rataye ne da abunda ta aikata (38)” suratul Muddassir, aya ta: 38.


Sai dai ita aqidar kisa da rataya da fansa a cikin addinin kiristanci yana daga fadin magana akan Allah ba tare da ilimi ba da kuma karya a gare shi kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ azaba ta tabbata ga wadanda suke rubuta littafi da hannayen su sai su dinga cewa wannan daga Allah ne da su dinga siyar da su da iyan kudade kadan tir da su saboda abunda hannayen su suka rubuta kuma tir da su saboda abunda suke aikatawa (79)” suratul Bakara, aya ta: 79.


Kuma hakika Allah ya dauki alkwari akan bani isra’ila da cewa suyi imani da abunda Annabi Isah yazo da shi kuma suyi aiki da shi kuma suyi imani da abunda yayi bushara da shi na cewa za’a aiko da wani manzo da zai zo a bayan sa sai dai su sun canja kuma sun juya sannan kuma sunyim sabani saisuka bijire kuma suka karyata sai Allah yayi musu ukuba da jefa gaba da


118


kikaiyya tsakanin su a nan duniya da kuma azaba a lahira kamar yadda Allah madaukaki yace: “ kuma daga cikin wadanda suka ce lallai mu kiristoci ne mun riki alkawari daga gare su sai suka manta da rabanda aka tunatar da su shi sai muka jefa gaba da kiyaiyya a tsakanin su har zuwa ranar alkiyama kuma da sannu Allah zai basu labarin abunda suka kasance suna aikatawa (14)” suratul Ma’idah, aya ta:14.


119


Yana daga cikin tabbatacciyar akidar musulmai cewa lallai Annabi Isah amincin Allh ya tabbata a gare shi zai dawo a karshen zamani zuwa kasa lokacin da ilimi zaiyi karanci kuma jahilci zai yawaita kuma mutane zasuyi nesa daga addini kuma kasa zata cika da zalunci, dan shi amincin Allah ya tabbata a gare shi ya zama shi ne mai ceto mutane daga abunda suke ciki na dagawa sai ya cikata da adlci da haske kuma zaman lafiya zai mamaye ko ina da kwanciyar hankali afadin duniya, kuma hukuncin musulunci zai yi nasara Annabi Isah zai yi hukunci da shi akan mutanen duniya baki daya zai karya gumaka wanda ke nuni a aikace akan bacin akidun kiristoci akan cewa an rataye shi ne, kuma zai kashe aladu dan yayi nuni akan bacin akidar kiristoci a game da halatta shi, sai albarka ta yawaita a zamanin sa kuma dukiya su kwararo ta ko ina kuma zukatan mutane za su cika da kana’a a zamanin sa da tsantsane har mutane zasu rasa wanda zai karbi sadaka daga wurin su, kamar yadda manzan Allah 9S.A.W) ya baiyyana haka da fadar sa: “ na rantse da wanda raina ke hannun sa, lallai Isah dan Maryam ya kusa sauka a cikin ku yana maihukunci mai adalci, sai ya karya gumaka, kuam ya kashe aladu, kuma ya sauke jiziya, kuma dukiya ta yawaita har ma babu wanda zai karba, har sujada daya zata fi alheri fiye da duniya da abunda ke cikin ta,” bukari da muslim ne suka ruwaito.


Kuma wanna dukkan sa shimfida ne na tashin alkiyama waddan a abyanta mutane ke barin rayuwar duniya mataki na


120


aiki zuwa matakin lahira matakin sakamako da kuma rayuwa madauwwamiya ta hanya dauwama a gidan aljannah ko kuma a cikin wuta ta yadda ake cika wa kowace rai sakamakon abunda ta aikata mai rabo shi ne wanda yayi shiri dan zuwan wannan ranar kuma yayi aiki dan ita ta hanyar aikata kyawawan aiyuka da kuma nisantar munanan aiyuka da kuma bin manzanni, Allah madaukaki yana cewa: “ ranar da zamu kira kowane mutane da jagoran su to duk wanda aka ba littafin sa da daman sa to wadannan suna karanta littafin su kuma ba’a zaluntar su daidai da kwayar zarra (71) kuma duk wanda ya kasance makaho a nan duniya to shi a lahira makaho ne kuma yafi mace hanya (72)” suratul Isra’i, aya ta: 71-72.


121


Lallai Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi shi ne manzo guda daya da mutane sukayi sabani mai tsanani akan sa, daga cikin yahudawa akwai masu zagin sa kuma suka zagi shi da kalmomi mafi girma na zagi kuma suka siffanta shi da mafi munin siffa kma mafi kazanta, kuma daga cikin kiristoci akwai wadanda suka wuce iyaka wurin girmama shi kuma suka raya cewa shi Allah ne da kuma cewa dan Allah ne da kuma cewa shi daya ne cikin uku, kuma yana daga falalar Allah akan al’ummar musulmai- kuma wannan falalar Allah ce yana bada ita ga wanda ya so- sai Allah ya shiryar da ita zuwa gaskiya gameda hakikanin lamari akan Annabi Isah matsaya ta tsakiya a tsakanin wadannan alummu biyu da suka gabata, sai suka girmamashi da tsarkake shi daga maganar yahudawa, kuma basu wuce iyaka ba akan shi irin na kiristoci, kuma abunda suke cewa game da shi shi ne shi bawan Allah ne kuma manzan sa kamar yadda Allah ay saukar da haka ga manzan sa a cikin Alkur’ani mai girma.


Wannan itace hakikanin Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda mu musulmai muke sansa kuma muna neman kusance zuwa ga Allah da san sa, shi manzo ne mai karamci daga tsatsan Annabawa da manzanni masu daraja kuma muna kudar cewa rashin kaunar sa da imani da shi da kuma sakon sa fita ne daga musulunci kuma karyatawa ne da Alkur’ani da kuma fiyaiyyen halitta Muhammad (S.A.W) kuma yana daga cikinabunda ke sa a dauwwama a cikin wuta.


Kuma wannan shi ne hakikanin zance game da Maryam amincin Allah ya tabbata a gare ta kamar yadda Alkur’ani mai


122


girma ya baiyyana kuma Manzan Allah (S.A.W) ya baiya cewa ita mai tsarki ce mai kame wa ce mai tsafta ce barrantacciya ce daga dukann barna da alfasha daga tsatsan gida mai daraja, kuam lallai ni inada yaki ni cea dukkan mutum ami adalci da ya karanta abunda Alkur’ani yazo da shi game ad wannan Annabin mai daraja zai tabbar da cewa wannan shi ne gaskiyar da ya kamata yabi, kuma inada yakini akan cewa babu wani littafi ko kuma addini da ya girmama kuma ya daukaka darajar wannan mutanen gidan da wannan manzan kamar musulunci, ta yadda ya aje shi a matsayin da ya dace da shi, shi ne matsayin bauta ga Allah wadda Allah ya sharrafa shi da ita kamar yadda ya sharrafa wasun sa daga cikin Annabawa, kuma hakika dukan Annbawa sun dan dana abunda suka dandana daga mutanen su – a hanyar tabbatar da wannan bautar- na bijirewa da karyatawa, daga cikin su akwai wanda aka kashe kuma daga cikin su akwai wanda aka azabtar kuma daga cikin su kwai wanda ak rufe a kurkuku, hakan kuwa saboda sun zo da abunda ke sabawa abubuwa da yawa da suke aikatawa na ibadu da kudurce-kudurce na karya da tsarin zamantakewa na zalunci kuma suna dankwafar da mafi yawa daga cikin san rai na shaidan karkatattu, Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya dandani cutarwa daga mutanen sa har sawan shekaru dari tara da hamsisai yayi hakuri kuma ya nemi ladan sa a wurin Allah sai Allah ya tsiratar da shi kuma ya hallaka mutanen sa da suka kafurta da ruwan dufana, shi kuma Annabi Ibrahim amincin Allah ya tabbata a gare shi mutanen sa sun karyata shi suka jefa shi cikin wuta sai Allah ya maidata sanyi da aminci a gare shi kuma Allah ya halaka makiyan sa kuam ya bashi nasara a kan su, shi kuma Annnabi Musa amincin Allah


123


ya tabbata a gare shi Fir’auna ya karyata shi kuma yanata kulla masa makirci dan ya kashe shi sai Allah ya tsiratar da shi kuma ya taimake shi kuma ya halakar da kuma nutsar da makiyin shi da rundunar sa, shi kuma Annabi Isah maincin Allah ya tabbata a agre shi shima yana cikin jerin wadannan manzannin wadanda suka hadu da karyatawa daga bani isra’ila da kuma fadan da bunda yake shi kubutanci ne akan sa, na cewa shi dan zina ne kuma mahaifiyar shi mazinaciya ce- Allah ya tsare shi kuma ya tsare ta daga haka- duk wannan na daga cikin yunkuri na kange mutane daga bin sa kamar yadda sukayi kokarin kashe shi da gangan sai Allah ya tsiraar da shi kuma ya dauke shi zuwa sama, shi ma kuma Annabi Muhammad (S.A.W) ya hadu da karyatawa daga mutanen sa mushirikai da kuma da yahawa daga cikin yahudawa da kiristoci da izgili da raini da yunkirin kisa sai ya tabbata sai kuma Allah ya taimake shi ya bashi nasa sai yayi rijaye akan makiyan shi kuma ya daga addinin sa ya daura shi akan sauran addinai dukan su koda kuwa kafurai basa so.


Lallai annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi shi ba kamar yadda kiristoci suke rayawa bane cewa shi Allah ne ko kuma shi dan Allah ne ko kuma shi Allah daya ne cikin uku- Allah ya daukaka kuma ya tsarkaka daga dukkanhakan- saboda da ace shi kamar yadda suke fada ne to da zai iya saukar da imani a zukatan mutane dukakn su sau suyi imani matukar shi yana da wannan darajar, kuma matukar wannan shi ne abunda ya ke kauna kuma yake fata saboda ya zai kasa tabbatar da haka?! Haka nan ma da ace shi ne Allah to wannan waen irin Allah ne da bazai iya kare kansa ba kuma ya bawa halittu dama


124


akan kashe shi?! Kuma da ace shi ne dan Allah to ya za ace Allah ya yadda a kashe dan sa- Allah ya tsarkaka?


Lallai Allah madaukaki yayi mana ni’imar hankali kuma ya sanya shi ne mai banmanta tsakanin mu da wanda ba mu ba cikin halittu, to muyi amfani da wannan hankalin kuma muyi tunani dan gaskiya ta baiyyana a gare mu daga karya da kuma ingantacce da wanda ba ingantacce ba, babu abunda ke sabawa fidira ingantacciya a cikin addinin Annabawa dukkan su da kuma lafiyaiyyen hankali, duk abunda yake irin wannan to shigo da shi akayi cikin addinin Allah kuma yana daga cikin samun damar da shaidan yayi akan iyan Adam dan ya karkaatr da su daga hanya madaidaiciya kuma ya kai su zuwa hanyar bata, to ka kasance ya kai mai karatu mai daraja cikin wadanda idan sun karanta zasuyi tunani kuma idan yayi tunani zai gwama kuma idan ya gwama sai yabi magana mai kyau dan ka zama cikin wanda Allah ya yabe su da fadar sa: “ kuma wadanda suka nesanci dagutu dan kar su bauta musu kuma suka maida al’amuran ga Allah to suna da ajannh to kayi wa bayi bushara (17) wadanda suke jin zance sai su bi mafi kyawon shi wadannan su ne wadanda Allah ya shiryar da su kuam wadannan su ne ma’abota hankula (18)” suratuz Zumar, aya ta: 17-18.


Kira ne da muke fuskantar da shi ga wanda ba musulmai ba dukkan su kuma zuwa ga ahlul kitabi a kebe kira na gaskiya da fuskantarwa na ubangiji wanda Annabi Muhammad 9S.A.W) ya kira wanda suka saba masa da ita tun tuni a baya kuma ya wayi gari alama ne na mabiyan sa a bayan sa, inda Allah madaukaki yace: kace yaku ma’abota littafi ku taho zuwa ga wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu da ku cewa


125


kada mu bauta wa kowa sai dai Allah kuma kada mu hada shi da komai kuma kada sashin mu su riki wasu sashi ababen bauta koma bayan Allah idan suka juya baya to kuce musu ku shaida lallai mu musulmai ne (64)” suratu Ali imaran, aya ta: 64.


Hakika yahudawa da kiristoci sun kasance suna bushara da zuwan wani manzo na karshe daga littattafan su kuma tunanin su she ne zai kasance ne daga bani isra’ila kuma sun san cewa zai fito ne ta bangaren madinah wacce ake kiranta da suna Yasrib a wancan lokacin, saboda haka ne suka taru a cikin madinah da kewayenta lokacin da sabanin abunda suke tsammani ya baiyyana da kuma abunda suke tunani da aiko AnnabiMuhammad (S.A.W), sai suka kafurce kuma suka juya baya, kuma Allh ya wadata da barin su kuma Allah yafi sanin inda yake sanya manzancin sa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ lokacin da wani littafi yazo musu daga Allah yana gaskata abunda ke tare da su kuma su kafin haka sun kasance suna bada labarin shi ga wanda suka kafurta lokacin da abunda suka sani yazo musu sai suka kafurce da shi to tsinuwar Allah ta tabbata a kan kafurai (89) tur da abunda suka siyawa kansu na su kafurce wa abunda Allah ya saukar dan haushin Allah ya saukar da falalar shi akan wanda ya so cikin bayin sa sai suka koma da fushi akan fushi kuma kafurai suna da azaba ta wulakanci (90)” suratul Bakara, aya ta: 89-90.


Lallai da’awar da musulmai suke dauke da ita kuma suke kokarin isar da ita ga wasun su ta fito ne ta bangaren san su ga alheri a gare su, alherin duniya ko wane iri ne saboda shi musulmi yana cikin abunda ke amfanar sa akwai tabbar abunda


126


ke kewayen sa dan iya isar da sakon ubangijin sa da kuma kokarin aiki da tabbatar da karantarwar sa wadanda suke samar da al’umma mai falala, ko kuma alheri na lahira ta hanyar abunda suke isar da shi na karantarwar ta Allah wadda zata zamo sababain shigar su aljannah da kuam tsamar da su daga wuta, kuma mai motsa wannan fuskantarwa ta ubangiji wadda ke umurtar su da haka, hakika Allah madaukaki yace: “ kuma a samu mutane daga cikin ku wadanda suke kira zuwa ga alheri kuma suna umarni da kyakkyawa kuma suna hani daga mummuna kuma wadannan su ne masu babban rabo (104)” suratu Ali imrana, aya ta: 104.


Kuma karshen burina shi ne wanna dan karamin littafin ya zama farkon binciki ne da da zai kre makauniyar biyaiyya na tunani ga wanda ke da tsananin bukata ta sanin ingantacciyar hanya, kuma fata na ta gaskiya ga dukkan mutum da ya isa zuwa ga jin dadi na gaske wadda imani da Allah ne tushen sa, inda Allha yabaiyyana haka da fadar sa: “ wadanda sukayi imani kuma zukatan su ke natuwa da ambatan Allah ku saurara da ambatan Allah ne zukata ke natsuwa (28)” suratur ra’ad, aya ta: 28.


Wadda a mtsayi na na musulmi nake kudurta cewa mutum bazai ni’imtu da ita ba sai a karkashin addini mai girma wanda ke baiwa kowane mai hakki hakkin sa a cikin abunda ya shafi mu’amalolin mutane ko kuma na jiki da na ruhi kuma wannan dukkan sa ina samunsa a cikin addinin musulunci da yawa, lallai abunda ke samun mu na bacin rai da damuwar rai a cikin al’ummar da ba musulmai ba duk da irin abunda suka kai na jindadin rayuwa da ci gaba,ya samu ne saboda nesanci da sukayi da imani da Allah da ingantaccen imani wanda aka gina


127


shi akan tauhidi, kuma rashin imani da Allah shi ne tushen tabewa da rashin rabo, kuma Allah mai girma yayi gaskiya inda yace: “ kuma duk wanda ya juya baya daga ambato na to lallai shi yana da wata irin rayuwa ta kunci kuma zamu tada shi ranar alkiyama yana makaho (124) sai yace ya ubangiji saboda me ka tadani makaho alhali da ina gani (125) sai yace haka nan ayoyin mu suka zo maka sai ka manta da su kaima haka yau za’a manta da kai (126)” suratu Daha, aya ta: 124.


Lallai nassoshin Alkur’ani mai girma sun zo a baiyyane wajen nuni akan cewa lallai addini a wajan Allah daya ne kuma lallai Allah yana aiko da Annabawa amincin Allah ay tabbata a gare su sashin su na cika sashi, tun daga Nuhu amincin Allah ya tabbata a gre shi har zuwa ga Annabi Muhammad (S.A.W) kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya baiyyana haka da fadar sa: lallai misali na da misalin Annabawan da suka gabace ni, kamar mutum ne da ya gina gida, sai ya kyautata shi kkuma ya kawata shi sai ya bar wani gefe ba bulo, sai mutane suke zagaye gidan kuma suna mamakin sa kuma suke cea: ai da ka dora wannan bulon, sai yace: ni ne bulo din, kuma ni ne karshen Annabawa.” Sahihul bukari.


Kuma karshen kiranmu shi ne cewa godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai


Kuma Allah yayi amincin ga Manzannin sa baki daya.


www.islamland.com


128



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH