Labarai




70


Hakika Alkur’ani ya siffata Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi da wasu irin siffofi da suke nuni akan darajar wannan manzan mai karamci a wurin Allah madaukaki kuma hakika shi ya tattaru siffa ta kamala ta dan dam wanda ke nuni akan wannan darajar mai girma, kamar yadda Alllah ya baiyyana haka da fadar sa: “ kuma sai biyo da Annabi Isah dan Maryam a bayan su yana mai gaskata abunda ya gabace shi na Attaura kuma mun bashi Injila a cikin ta akwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda ya gabace shi na Attaura kuam shiriya ne da tunatarwa ga masu takawa (46)” suratul Ma’idah, aya ta: 46.


Kuma Alkur’ani mai karamci ya bada labari cewa lallai wannan manzan abun karfafawa ne daga Allah madaukaki kuma abun tsarewa ne da tsaran sa, Allah madaukaki yace: “ kuma hakika mun baiya Musa littafi kuma muka biyo da Annabawa a bayan sa kuma muka baiya Isah dan Maryam hujjoji baiyyanannu kuma muka karfafa shi da mala’ika Jibrilu to yanzu duk lokacin da wani manzo yazo muku da abunda ranku basa so sai kuyi girman kai wasun su ku kashe su wasun su kuma ku karyata (87)” suratul Bakara, aya ta: 87.


Kuma manzan Allah (S.A.W) ya siffanta shi da cewa shi abun koyi ne mai kyau kuam misali ne lafiyayye wurin imani da ibada da iklasi ga Allah madaukaki, kuma lallai saukar sa a karshen zamani alama ne me girma cikin alamun tashin alkiyama kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “


71


lokacin da aka sanya dan Maryam abun buga misali sai ga mutanen ka suna kangewa daga gare shi (57) kuma sukace shin allolin mu sun fi alheri ko kuwa shi basu buga wannan misalin ba sai dai dan jayayya a’a su mutane ne masu san yin jayaiyya (58) shi bawa ne wanda mukayi ni’ima a gare shi kuma muka sanya shi ya zama misali ga mutanen bani isra’ila (59) kuma da ace mun so da mun sanya mala’iku daga cikin ku suna mayewa a ban kasa (60) kuma lallai shi alama ne na tashin alkiyama to kada kayi jayayya da ita kuma ku bini wannan ita ce hanya madaidaiciya (61)” suratuz Zukruf, aya ta: 57-61.


Amma siffar sa kuwa ta jiki hakika manzan Allah (S.A.W) ya siffanta shi sai yace:” annabawa iyan uwan juna ne iyayen su mata daban daban ne amma kuma adinin su daya ne, kuma lallai ni ne nafi kowa cancanta gameda Isah dan Maryam, domin babu wani annabi tsakani na da shi, kuma lallai shi zai sakko, in kun ganshi to ku gane shi: mutum ne matsakaici kuma kalar sa tsakanin fari da baki take, zai zo yana sanye da kaya biyu masu kalan shudi, kansa na zubar da ruwa koda kuwa bai zuba ruwan a kansa ba saboda tsafta, zai karya gumaka, kuma ya kashe aladu, kuma ya sanya jiziya, kuma zai kira mutane zuwa ga musulunci, kuma a lokacin sa Allah zai hallaka addinai dukkan su sai dai musulunci kawai, kuma Allah zai halaka Dujal a zamanin sa, sai aminci ya wanzu a ban kasa, harma a samu rakumi na kiwo tare da zaki,damisa da kuma shanu, da kyarkyace tare da dabbobi, kuma kananan yara zasu dinga wasa da macizai amma baza su cutar da su ba, zai zauna


72


tsawan shekaru arba’in, sai ya rasu kuma musulmai suyi masa sallah.” Duba cikin umdatut Tafseer.


Kuma manzan Allah (S.A.W) yace a cikin wani hadisi na daban: “naga Isah da Musa da Ibrahim, amma shi Isah, ja ne shi, yana da cukwikwiyayyen gashi, yana da fadin kirji, amma shi kuma Musa, baki ne, maii kiba ne, gashin shi mai santsi ne, kamar shi daga cikin mazajen zaddi ya fito, amma shi kuma Ibrahim to ku kalli mutumin ku, yana nufin kan sa.” Sahihul Jami’i.


Kuma Manzan Allah (S.A.W) ya baiyyana cewa yin imani da shi na daga cikin ababen da ke cika imani kuma yana daga cikin dalilan da ke sa a shiga aljan nah, inda yace: “ duk wanda ya shaida cewa lallai babu abun bauta da gaskiya sai Allah shi kadai yake bashi da abokin taraiyya, kuma lallai Muhammad bawansa ne kuma manzan sa ne, kuma lallai Isah bawan Allah ne kuma manzansa nekuma kalmar sa ce da ya jefa ta ga Maryam kuam ruhi ne daga gare shi, kua aljannah gaskiya ce, kuma wuta gaskiya ce, to Allah zai shigar da shi aljannah akan abunda yake kai na aiki.” Al bukhari.


Haka nan kuma imani da shi na daga cikin dalilan rubanya lada da daraja, inda Manzan Allah (S.A.W) yace: “ in mutum ya tarbiyyantar da baiwar sa sai ya kyautata tarbiyyanta, kuma ya kuyarda ita ya kyautata koyarda itan, sai ya iyanta ta kuma ya aure ta to yana da lada nin ki biyu, kuma idan yayi imani da Isah, sai kuma yazo yayi imani da ni to yanada lada ninki biyu, kuma bawa idan yaji tsoran


73


ubangijin sa kuma yayi biyaiyya ga mai gidan sa to yanada lada ninki biyu.” Al bukhari.


Kuma Annabi (S.A.W) ya baiyyana irin tsarkin zuciya da wannan manzan mai karamci yake da ita wacce hassada bai bata ta ba o keta ko kiyaiyya, wacce take cike da kyautata zato ga mutane da kuma girmama Allah da kwarzanta shi, inda yace: “ Annabi Isah yaga wani mutum yana sata sai yace masa: kana sata ne? Sai yace: a’a ina rantsuwa da wanda babu abun bauta da gaskiya sai shi, sai Isah yace: nayi imani da Allah kuma idanu na sunyi karya.” Al bukhari,


74


Alkur’ani ya baiyana cewa saukowar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi a karshen zamani alama ce daga cikin alamun kusantowar tashin alkiyama kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa:“ lokacin da aka sanya dan Maryam abun buga misali sai ga mutanen ka suna kangewa daga gare shi (57) kuma sukace shin allolin mu sun fi alheri ko kuwa shi basu buga wannan misalin ba sai dai dan jayayya a’a su mutane ne masu san yin jayaiyya (58) shi bawa ne wanda mukayi ni’ima a gare shi kuma muka sanya shi ya zama misali ga mutanen bani isra’ila (59) kuma da ace mun so da mun sanya mala’iku daga cikin ku suna mayewa a ban kasa (60) kuma lallai shi alama ne na tashin alkiyama to kada kayi jayayya da ita kuma ku bini wannan ita ce hanya madaidaiciya (61)” suratuz Zukruf, aya ta: 57-61


Kuma saboda falalar shi ne Allah zai aiko shi dan ya kashe Dujal da kuma yada musulunci da kuma kira zuwa gare shi, hakan kuwa zai faru ne in kasahe-kashe yayi yawa kuma fidirar mutane ta gurbata kuma kyakkyawan abu ya zama mummua mummuna kuma ya koma kyakkyawa, kuma dan ya tsayar da adalci kuma ya yada aminci a karshen zamani kamar yadda Annabi Muhammad (S.A.W) ya baiyyana haka da fadar sa: “ ya ku mutane! Lallai babu wata fitina a ban kasa tun lokaci da Allah ya halicci zurriyyar Adam wacce tafi girma irin fitinar Dujal. Kuma lallai Allah madaukaki bai taba iako wani Annabi ba face sai ya tsawatar da mutanen sagameda Dujal, kuma ni ne na kaeshen Annabawa, kuma kune na


75


karshen al’ummu, to shi a cikin ku zai fito babu makawa, in har ya baiyana alhali ina cikin ku, to ni ne zan kare kowane musulmi, in kuma ya fito a bayana ne, to kowa ya kare kansa, kuma Allah shi ne halifa na akan dukan musulmi, kuma lallai shi zai baiyyana ne ta wata kofa tsakanin sham da iraqi, sai yayi yekuwa dama da hagu, ya ku bayin Allah! ya ku mutane! To ku tabbata dan zan siffanta muku shi siffantawar da babu wani Annabi da ya taba siffanta shi irin haka,.... zai ce: ni ne ubangijin ku, amma ku baza ku ga ubangijin ku na har sai kun mutu, kuma shi yana da ido daya ne, kuma ubangijin ku ba ido daya gare shi ba, kuma an rubuta a tsakanin idanun sa: kafuri, kowane mumini zai karanta, ya iya karatu ko bai iya ba, kuma daga cikin fitinarsa lalai zai zo tare da shi akwai aljannah da wuta, wutarsa aljannah ce, kuma aljannarsa wuta ce, duk wanda aka jarabce shi da wutar sa to ya nemi agajin Allah, kuma ya karanta ayoyin farko na suratul Kahfi...... kuma daga cikin fitinar sa zai ce wa mutumin kauye: ya kake gani in na dawo ma da mahaifin ka da mahaifiyar ka to zaka shaida cewa ni ne ubangijin ka? Sai yace: eh, sai shaidanu biyu su siffantu da siffar mahaifin sa da mahaifiyar sa, sai suce masa: ya kai yaran mu ka bi shi, domin shi ne ubangijin ka, kuma daga cikin fitinar sa, zai samu iko akan wata rai ya kashe ta, zai tsagata da zarto har sai gangan jikin ya rabu biyu, sai kuma yace:kuyi dubi zuwz ga wannan bawan nawa, ni zan tada shi sai kuma ya traya cewa yana da wani ubangiji ba ni ba, sai Allah ya tada shi, sai mabarnacin ya ce masa: waye ubangijin ka? Sai yace: ubangiji na shi ne Allah,


76


kuma kai makiyin Allah ne, kai ne Dujal, wallahi ni ban taba samun tabbaci ba akan ka irin yau, kuma daga cikin fitinar sa zai umarci sama tayi ruwa, sai kuma ta zubar da ruwa, kuma ya umarci kasa ta fitar da tsirrai sai ta fitar da tsirrai, har ma dabbobin su a wannan ranar zasu koma masu kiba fiye da yadda suke a sauran kwanakin kuma zasu fi tudu da fadi kuma da hantsa cike da nono, kuma babu wani wuri da zai yi saura a cikin kasa face sai ya shige shi yayi gallaba akan sa, sai dai makkah da madiinah, babu wata kofa da zai zo tasu face sai ya samu cewa akwai mala’iku da takubba a zare, har ya sauka a wani wuri mai jan kala, wurin da kasar gishiri ta yanke, sai madinah ta girgiza sau uku, babu wani munafuki ko munafuka da zasu rage a cikin ta face sai sun fito zuwa gare shi, sai ta kore abarnatan da ke cikin ta, kamar yadda zugazugi ke kore dattin karfe, kuma wannan ranar ana kiranta ranar gamawa, sai aka ce: to ina larabawa suke a wannan lokacin? Sai yace su a wannan lokacin iyan kadan ne..... kuma shugaban su mutumin kirki ne, wata rana shugaban su zai shiga gaba dan ya jagoranci sallar asubah, sai ga Annabi Isah dan Maryan zai sauka a gare su da asubah, sai wannan shugaba nasu zai ja da baya dan Isah ya jagorance su, sai Isah ya daura hannunsa a kafadar sa, sai yace masa zo kayi sallah, domin takace kai akyi wa iqama, sai shugaban su yayi musu sallah, idan ya idar sai Isah yace: ku bude kofa, sai a bude kofa a bayanta a kwai Dujal, tare da shi a kwai yahudawa dubu saba’in, dukkan su suna dauke da takubbah masu ado da kuam kaho, idan Dujal ya hango Annabi Isah sai ya zagwanye kamar yadda gishiri ke


77


zagwanyewa a cikin ruwa, sai ya juya zai gudu..... sai Annabi Isah ya tare shi a kofar ludd ta gabas, sai ya kashe shi, sai Allah ya eusa yahudawa, babu wani abu da Allah ya halitta da bayahude zai boye a bayan sa face sai Allah yasa yayi magana, babu duwtsu ko bishiya ko bango ko kuma dabba, sai dai tumfafiya, domin ita tana cikin bishiyoyin da bat magana, face sai yace: ya kai bawan Allah musulmi ga wani bayahude nan zo ka kashe shi, sai Isah dan Maryam ya zama a cikin al’umma ta mai hukunci mai adalci, kuma shugaba mai adalci yana karya gumaka, kuam ai yanka aladu, kuma zai sanya jiziya, kuma zai bar sadaka, baza a fita neman akuya ba ko kuma rakumi, kum a dauke mugunta da kiyaiyya, kuma a cire cutarwa dukkan dabba mai cutarwa, har dan karamin yaro zai tura hannun sa cikin ramin macijiya amma baza ta cutar da shi ba, kuma iyar karamar dabba zata hadu da zaki amma bazai cutar da ita ba, kuma kyarkeci zai shiga cikin dabbobi kamar shi ne karan su, kuma kasa ta cika da zaman lafiya kamar yadda a ke cika kofi da ruwa, kuma kalma zata hadu ta zama daya, ba’a bautawa kowa sai Allah, kuma yaki zai kwanta, kuma kuraishawa zasu karbi mulkin su, kuma kasa zata zama kamar kwallan azurfa, zata fitar da tsirranta kamar yadda take fitarwa a zamanin Adam, har ma mutane su taru su ci inabi reshe daya kuma ya ishe su, kuma wasu tawaga na mutane su taru akan rumman guda daya kuma ya kosar da su, kuma bijimin sa zai zama kaza da kaza da kaza na dukiya,kma doki ya koma iyan dirhami kadan.....kuma lallai kafin fitowar Dujal akwai wasu shekaru uku da za’a samu masu tsanani, yunwa mai


78


tsanani zata kama mutane a cikin su, a shekara ta farko Allah zai umarci sama da ta rike daya bisa uku na ruwanta, kuma ya umarci kasa da ta rike daya bisa uku na shukar ta, sai Allah ya umarci sama da rike kashi biyu cikin uku na ruwanta a shekara ta biyu, kuma ya umarci kasa da rike biyu bisa uku na shukarta, sai kuma Allah ya umarci sam ada rike ruwan sama dukkan shi a cikin shekara ta uku, ko dugo daya na ruwan sama bazai sauka ba, kuma ya umarci kasa da rike tsirranta dukka ko ciyawa daya baza ta fito ba, babu abunda zaiyi saura mai hanta face sai ya mutu sai dai abunda Allah yaga dama kawai, sai akce: to da me mutane zasu rayu a wannan lokaci? Sai yace: hailala, da kabbara, da hamdala, kuma wannan zai kosar da su kamar abinci.” Sahihul Jami’i.


79


Allah yana aiko da manzannni kuma yana karfafa su da mu’ujizozi wadanda ake iya gani dan su zamo ayoyi an gaske masu gaskata manzancin su, kuma lura da cewa wadannan mu’ujizozin wadanda ake gani ne to hakika sun kare tare da karewar zamunan su kuma ba wanda yayi imani da su sai wanda ya gan su, lokacin da sakon Annabi Muhammad 9S.A.W) yazo kuma sakon sa ya kasance na duk duniya ne kuma na karshe sai ya ama ba maka ta zama mu’ujiza mai dauwwama wacce zata wanzu komai dadewan lokaci har zuwa tashin alkiyama dan ta tsaida hujja akan mutane baki daya kuma ta zama mai shaida akan mutanen zamuna masu zuwa da nuna gaskiyar manzancin Annai Muhammad (S.A.W), saboda haka ne mu’ujizar shi bata zama zbunda ake gani ba kamar irin mu’ujizar sauran Annabawa gabanin sa, saboda mu’ujizar da ake gani baza ta iya tsayawa da wannan aikin ba kua bata ingant ba ga wannan aikin, saboda ita tana yankewa da yankewar aikinta kuma ba mai imani da ita sai wanda ya ganta, saboda haka ne mu’ujizar Annabi Muhammad (S.A.W} ta kasance wahayi ne da ake saukar masa kuma ana karanta hi har zuwa tashin alkiyama, hakika yazo da wani rirn zance mai keta al’ada wurin usulubin shi da balagar shi dukda cewa ya zo ne da shi a wani lokaci wanda an san mutanen sa da fasaha da iya magana, kuma duk da dogewar masu saba masa a zamanin sa da kuma ma dukkan zamuna a bayan sa akan bijire masa da kuma kokarin tabbatar da rashin mu’ujizancin maganar da akayi masa wahayi, sai dai su sun kasa zuwa da wata sura irin sa ko kuma wata aya daya irin sa, kuma dag cikin mu’ijizar Alkur’ani mai karamci shi cewa lallai shi ya bada labarurruka


80


na gaibi, shi Alkur’ani mai girma shi ne mu’ujizar Annabi Muhammad (S.A.W) madauwwamiya, Annabi (S.A.W) yana cewa yana mai bayanin wannan hikakanin zancen: “ babu wani Annabi face sai anbashi wani abu wanda zai sa mutane suyi imani da shi, kuma ni abunda aka bani shi ne wahayi da Allah yake yi mini, to ni ina fatan in fi su yawan mabiya ranar alkiyama.” Sahihul bukhari.


81


Kamar yadda muka ambata a baya cewa wasu mutane suna jayaiyya da kuma kafurce wa manzanni amincin Allah ya tabbata a gare su kuma basa imani sai da hujjoji da ido ke iya gani, saboda haka ne Allah ya karfafa manzanni da mu’ujizozi wadanda suke nuni akan gaskiyar sakonsu da Allah ya turo su da shi, sai dai mu sani cewa ko wce mu’ujiza tana aukkuwa ne da ikon Allah da izinin sa da karfafawar sa, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “kuma hakika mun aika da manzanni gabanin ka kuma muka sanya musu mata da zurriyya kuma bai kamata ba ga wani manzo yazo da wata aya ba sai da izinin Allah kowane abu yanada lokaci (38)” suratu Ra’ad, aya ta: 38.


Haka nan ma mu’ujizozin da Allah ke gudanar da su ta hanyar manzannin sa ta bangaren abunda mutanen su suka shahara da shi, mutane Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi sun shahara da tsafi sai mu’ujizar Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gre shi ta zama sanda wacce ke hadiye abunda bokaye suka hada, ta yadda bokayen suke ta jefa sandnan su da igiyoyin su akan kasa sai daga baya su koma suna tafiya kamar macizai,, sai suka tsafe idanun mutane sai suke ganin sanduna da igiyoyi kamar macizan gaske, har shi ma Annabi Musa sai da yaji tsoro a ransa lokacin da ya gansu, Allah madaukaki yana cewa: “ sai bokayen Fir’aua suka zo sai sukace muna da kyauta in mu kasance mu ne masu nasara (113) sai yace eh ai lallai ku kuna cikin makusanta (114) sai sukace ya kai Musa kodai ka jefa ko kuma mu muama masu jefawa (115)


82


sai yace ku jefa lokacin da suka jefa sai suka tsfe idanun muta kuma suka tsoratar da su kuma suka zo da sihiri mai girma (116) sai mukayi wahayi zuwa ga Musa cewa ka jefa sandar ka sai gashi tana hadiye abunda suke jefawa (117) sai gaskiya ta baiyana kuma baunda suka kasance suna aikatawa ya baci (118) sai akayi galaba akan su a wannan wurin sai suka juwa suna kaskantattu (119) sai bokaye suka fadi suna masu sujada (120) sai sukace munyi imani da ubangijin talikai (121) ubangijin Musa da Haruna (122)” suratul A’araf, aya ta: 113-122.


Haka nan ma Annabi Isah amincin Allah ya tabbata agare shi an aike shi zuwa ga wasu mutane da basa imani sai da abun da ido ke iya gani wanda suke gani karara da idanun su,kuma hakika wasu cututtuka sun yadu a cikin su, sai mu’ujizrsa ta zama ta dace da wannan, sai Allah ya karfafa shi da wasu mu’ujizozi masu girma masu tunatarwa akan ikon Allah kuma tana karfafa imani da shi, sai yayi magana da mutane yana tsumman goyo kuma ya kasance yana halittar tsuntsu daga tabo sai yayi busa a cikin sa sai ya zama tsutsu da izinin Allah, kuam ya kasance yana warkar da mai kyasfi da kutare, kuma yana raya matattu da ikon Allah, kuma yana ba mutane labarin ababen da suke ci da wanda suke adanawa a gidajen su, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lokacinda Alah ya ce ya kai Isah dam Maryam ka tuna ni’imata a gare ka da mahaifiyarka lokacinda na karfafe ka da mala’ika Jibrilu kana magana da mutane a tsumman goyo da kuma bayan ka tsufa da kuma lokacin da na sanarda kai littafi da hikima da Attaura da Injila da kuma lokacinda kake halitta daga turbaya lamae tsunstu sai kayi busa a


83


cikin sa sai ya zama tsutsu da iko na kuma kana warkar da mao kyasfi da kuturu da iko na da kuma lokacinda kake raya matattu da iko na da kuma lokacin da na kange bani isra’ika daga gare ka lokacin da kazo musu da gaskiya sai wadanda suka kafurta daga cikin su suka ce wannan ba komai bane sai dai sihiri mabaiyyani (110)” suratul Ma’ida, aya ta: 110.


kuma daga cikin mu’ujizozin sa da karamar sa wadda Allah yayi masa kyautar su she ne cewa lallai shi an amsa addu’ar sa lokacinda mabiyansa suka nemi a saukar musu da wani faranti na abinci daga sama dan zukkztan su su samu natsuwa kuma su tabbatar da gasiyan manzancin sa, Allah madaukaki yace: kuma lokacin da nayi wahayi zuwa hawariyawa cewa kuyi imani da ni da kuma manzo na sai sukace munyi imani kuma ka shaida cewa lallai mu musulmai ne (111) lokacin da hawariyawa sukace ya kai Isah dan Maryam shin ubangijin ka zai iya saukar mana da wani teburi na abinci daga sama sai yace kuji tsoran Allah in har kun kasance ku muminai ne (112) sai sukace muna so ne muci daga gare shi kuma zukatan mu su samu natsuwa kuma mu tabbatar da cewa gaskiya ka fada mana kuma mu zama masu shaida a kanta (113) sai Isah dan Maryam yace ya Allah ka saukar mana da wani teburi na abinci daga sama dan ya zama idi a gare mu ga nafarkon mu da na karshen mu da kuma aya daga wurinka kuma ka azurtamu dan kaine mafi alherin masu azurtawa (114) sai Allah yace lallai ni zan saukar da she a gare ku to duk wanda ya kafurce bayan haka daga cikin ku to lallai ni zan azabtar da shi wata irin azabar da


84


bazan taba yiwa wane irinta ba cikin talikai (115)” suratul Ma’ida, aya ta: 111-115.


85


Lallai tushen addinin Manzanni baki dayan su guda daya ne saboda tushensa daga Allah ne, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ ko sun riki ababen bauta ne koma bayan sa to kace musu ku zo da hujjojin ku wannan shi ne tunatarwar wadanda suke tare da ni da wadanda suka gabace ni sai dai da yawan su basu san gaskiya ba sai suka koma suna juya baya (24) kuma bamu aiko wani manzo ba gabanin ka face sai munyi wahayi zuwa gare shi cewa lallai babu abun bauta dagaskiya sai ni to ku bauta mini ni kadai (25)” suratul Nbiya’i, aya ta: 24-25.


Tauhidi shi ne abuda dukkan karantarwar shari’ar musulunci ke zagaye a kan sa kamar yadda haka yake a cikin dukkanin shari’o’in sama da suka gabata, kirane zuwa ga kadaita Allah da kuma tsarkake bauta a gare shi shi kadai, kuma wannan shi ne abun da Allah ya halicci mutane domin sa kuma aka halicci aljannah da wuta saboda shi, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ an shar’anta muku addini irin abunda akayiwa Nuhu wasiyya da shi da kuma abunda mukayi wahayi zuwa gare ka da kuma abunda mukayi wa Ibrahim wasiyya da shi da Musa da Isah cewa ku tsaida addini kuma kada ku rarraba a cikin sa abunda kuke kira zuwa gare shi yayi girma akan mushirikai Allah yana zabar wanda ya so a gare shi kuma yana shiryarwa zuwa gare shi wanda ya koma zuwa gare shi (13)” suratush Shura, aya ta: 13.


Kuma wannan itace wasiyyar Annabawa baki dayan su ga mutanen su dukkan su da kuma zurriyyar su a kebe da yin


86


tauhidi da kuma tsrkake bauta ga Allah shi kadai, kamar yadda Alah ya bada labarin haka gaemda Yaqub amincin Allah ya tabbata a gare shi da fadar sa: “ shin ko kuna nan ne lokacin da mutuwa ta riski Ya’qub lokacin da yace wa yaran sa me zaku bautawa baya na sai sukace zamu bautawa ubangijin ka da kuma ubangijin iyayen ka Ibrahim da Isma’ila da Ishaq duka abun bauta ne guda daya kuma masu mika wuya ne a gare shi (133)” suratul Bakara, aya ta: 133.


Ingantaccen mandiki da kuma lafiyaiyyen hankali suna kin shirka ga Allah domin shika tawaya ne kuma wannan abu ne korarre ga Allah mahalicci wanda ya samar da wannan duniyar, idan shirka ta zama daga cikin abaebn da halittu basa kauna cikin abunda ke tsakanin su to me kak tunani game da ubangijin halittu, ita wasa ce da warge kuma bata kamata ga Allah, Allah madaukaki yana cewa: “ kuma bamu halicci sammai da kasa da abunda ke tsakanin su ba dan wasa (16) da ace mun so mu riki wasa da mun rikeshi daga gare mu in har mun kasance masu aikatawa (17) a’a mu muna jefa gaskiya akan karya sa ta ruguza ta sai ta wayi gari rusasshiiya kuma kuna da zaba saboda abunda kuke siffanta shi (18) kuma abunda ke cikin sammai da kasa nashi ne kuma wadanda suke tare da shi basa girman kai daga bautar sa kuma basa hasara (19) suna tasbihi dare da rana kuma basa yankewa (20) shin ko sun riki ababen bauta ne a kasa su ne suke tayar da su (21) da ace a cikin su akwai ababen n bauta koma bayan Allah to da sun lalace tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin al’arshi daga abunda suke siffantawa da shi (22) ba a tambayar sa game da


87


abunda yake aikatawa sune ake tambayar su (23)”suratul anbiya’i, ayata:16-23


Allah ya kasance abun tsarkakewa daga wasa da wargi da shagala kuma shi abun tsarkakewa ne daga rike wani a matsayin yaro saboda daga cikin ababen da suka tabbata a hankalce cewa samuwar yaro yana yana hukanta samuwar mata kuma wannan abu ne korarre ga Allah kuma abun tsarkakewa ne daga gare shi, samuwar mata da yaro ma’anar sa shi ne suma sunada zati na allantaka kamar zatin Allah kuma su samammu ne tuntuni ba farko kuma ba karshe, kuma wannan korarren abu ne, mahalicci daya ne shi ne Allah madaukaki bashi tamka ko kuma makamanci, kuma duk wanda ke da bukatar mata to dan me bazai riki wasu mata ba da kuma masoya ba mace daya ba kawai! Kuma shi Allah madaukaki tsarkakakke ne daga wannan dukkan sa, kamar yadda rike yaro ke nuni akan rauni da bukatuwa zuwa ga taimako daga wannan yaron to kuma dan me zai riki yaro daya kawai ba yara da yawa ba sai kuma jikoki da dangantaka! Kuma shi Allah tsarkakakke ne daga bukatuwa zuwa ga wani kuma tsarkakakke ne daga wannan dukkan sa, kuma duk wanda yake da yaro ma’anar haka shi ne yanada iko akan haihuwa kenan to kuma wannan ke nuna cewa shima haifan sa akayi, duk wanda keda yaro to hakika shima yana da baba ko kuma mahalici, kuma hakan dkkan sa korarre ne daga Allah mahalicci shi daya makadaici wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba, kuma duk wanda ya riki yaro to wannan na nuna cewa shi zai tsufa kuma yaronsa nada gado a cikin kayan sa da zai bari, wannan dukkan sa korarren abu ne daga Allah mahalicci shi kadai makadaici, Allah madaukaki yana cewa: “ makagin halittan sammai da kasa ta yaya zai zama yanada


88


yaro alhali bashi da mata kuma shi ne ya halicci dukkan komai kuma shi masani ne ga dukkan komai (101) wannan shi ne Allah ubangijin ku babu abun bauta da gasikiya sai shi mahaliccin dukkan komai to ku bauta masa kuma shi wakili akan dukkan komai (102) gani baya iya riskansa kuma shi ne yake riskan gani kuma shi ne mai tausasawa mai bada labari (103)” suratul An’am, aya ta:101-103.


Kuma abu ne sananne cewa bukatuwa zuwa ga abokin taraiyya na nuni ne akan rauni ga dayan abokin taraiyyan kowane dayan su na cika da dayan, shi kuma Allah madaukaki baya bukartar wani daga cikin halittun sa dan ya cika tawayar da ke tare da shi ko kuma dan ya taimake shi wajan gudanar da wannan duniyar da kula da lamuran halittun sa sai dai halittunsa ne ma ke da bukatuwa zuwa gare shi suna kwadayin abunda ke wurin sa tsarki ya tabbata a gre shi shi ne mawadaci, Allah madaukaki yana cewa: “ kuma kace godiya ta tabbata ga Allah wanda bai riki wani yaro ba kuma baida abokin taraiyya a cikin mulki kuma bashi da wani maji dadi na daga kaskanci kuma ka girmamashi girmamawa (111)” suratul Isra’i, aya ta: 111.


Kuma hakika Alkur’ani ya baiyyana shirka a game da hakkin Allah wanda shi ne ya samar da wannan duniyar, kuma ya tabbatar da sabubba na lafuzza da hankali wanda ingantaccen mandiki ke karba kuma lafiyaiyyen hankali ke yarda da su:


• Yawaitar ababen bauta yana hukunta cewa kowane daya daga cikin su na da cikakken iko saboda cikakken iku siffa ce ta abun bauta, shirka na hukunta cewa kowanen su zai bukaci wani abu sabanin dayan sai sakamakon


89


haka jayaiya ya auku da sabani da fada tsakanin masu taraiyya biyu wanda zai haifar da lalacewar duniya dukkan ta, Allah ya yi girman da za’a ce yana da wanda ke taraiyya da shi a cikin mulkin sa saboda shirka barna ce sai a tsarkake Allah daga gare ta, kuma hakika Alkur’ani mai girma ya baiyyana haka sai Allah madaukaki ya ce: “ shin ko sun riki wasu ababen bauta ne a doran kasa su ne suke tada su (21) da ace a cikin su akwai wani abun bauta da ba Allah ba to da sun lalace tsarki ya tabbata ga Allah ubangijin al’arshi daga irin abunda suke siffanta shi (22)” suratul Anbiya’i, aya ta: 21-22.


• Lallai samuwar wasu ababen bauta daban tare da Allah yana hukunta cewa kowanne daya daga cikin su yana da karfin da zai iya yin galaba da yaki a tsakanin su dan samun iko da kuma juya duniya wannan shi ne abun da Alkur’ani ya kore shi, Allah madaukaki yana cewa: “ kace da ace akwai wani abun bauta tare da shi kamar yadda suke cewa kenan da sun nemi hanya zuwa ga darewa kan kujerar mulki (42) tsarke ya tabbatan masa kuma ya daukaka game da abunda suke fada daukaka mai girma (43) sammai bakwai suna tasbihi a gare shi da kasa da abunda ke cikin su kuma babu wani abu face yana tasbihi da gode wa ubangijin sa sai dai bakwa fahimtar tasbihin su lallai shi ya kasance mai yawan hakuri mai yawan gafara (44)” suratul Isra’i, aya ta: 42-44.


• Lallai samuwar wasu ababen bauta tare da Allah yana hukunta raba duniyar tsakanin su su biyu dan kowannen


90


su ya kebanta da abunda ya halitta kuma hakan korarre ne ga Allah, Allah madaukaki yana cewa: “ Allah bai riki wani ba a matsayin yaro kuma babu wani abun bauta tare da shi kenan da kowannen su ya tafi da abunda ya halitta kuma da sashinsu yayi rinjaye akan sashi tsarki ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffanta shi (91)” suratul Muminuun, aya ta: 91.


Saboda haka ne shirka ta zama daga cikin mafi girman zunubain da Allah baya gafarta wa ga wanda ya mutu akai kuma lali aljannah haramtacciya ce a gare shi kuma matabbacin sa wuta kuma tir da makoma saboda haka ne mafi yawan ayoyin Alkur’ani suna tsawatarwa daga wannan zunubin wanda mukace kamar yadda ya gabata tawaya ne ga Allah kuma zance ne a gare shi ba tare da ilimi ba, Allah yana cewa: “ lallai Allah baya gafarta wa in akayi shirka da shi kuma yana gafarta abunda bai kai haka ba ga wanda ya so kuma duk wanda yayi shirka da Allah to hakika ya kirkiri zunubi mai girma (48)” suratun Nisa’i, aya ta: 48.


91


Alkur’ani mai girama ya baiyyana cewa Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi Annabi ne kamar sauran Annabawa halittane kuma bawan Allah ne, kuma hakika ya kasance cikin masiu kira zuwa ga tauhidi bai kasance yana tabbatar da mutanen sa ba akan abunda suke kai ba na shirka, ya kira mutanen sa zuwa ga imani da Allah shi kadai da watsar da duk abunda ba shi ba na sauran ababen bauta kuma ya baiyyana musu da yawa cikin abunda bani isra’ila suke sabani a cikin sa na shari’u, Allah madaukaki yace: “ lokacin da Isah ya zo musu da hujjoji sai yace hakika nazo muku da hikima kuma dan i baiyana muku wasu daga cikin abunda kuke sabani a cikin sa to kuji tsoran Allah kuma kuyi mun biyaiyya (63) lallai Allah shi ne ubangijina kuma ubangijin ku to ku bauta masa shi kadai wannan itace hanya madaidaiciya (64)” suratuz Zukruf, aya ta: 63-64.


Kuma Alkur’ani ya barrantar da shi akan cewa zai kira mutanen sa zuwa ga shirka da shi ko kuma yayi umarni da shi kuma ya baiyana cewa lalai shi zai tsaya gaban ubangijin talikai ranar alkiyama kuma a gaban halittu dukkan su dan ya kore abunda bani isra’ila suke tuhumar shi da shi na cewa hi ne ya kira su da su bauta masa shi da mahaifiyar sa, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “ kuma lokacin da Allah yace ya kai Isah dan Maryam shin kaine kace wa mutane ku rikeni da mahaifiyata ababen bauta koma bayan Allah sai yace tsarki ya tabbata a gare ka bai kamace ni ba in fadi wani abu wanda bani da hakki indai har ni na fadi haka to


92


hakika ka sani da shi kana sanin abunda ke cikin raina ni kuma bana sanin abunda ke cikin ranka lallai kai masani ne ga abunda yake boye (116) ban ce musu komai ba sai a bunda ka umarce ni da shi cewa ku bautawa Allah ubangiji na kuma ubangijin ku kuma na kasance mai shaida akan su lokacinda nake cikin su lokacin da ka dau rayuwta ka kasance kaine mai kula da su kuma kai mai shaida ne akan dukkan komai (117) in ka azabtar da su to lallai su bayin ka ne in kuma har ka gafarta musu to lallia kai ne mabuwayi mai hikima (118)” suratul Ma’idah, aya ta: 116-118.


93


Alkur’ani mai girma ya baiyyana cewa lallai Allah madaukaki ya riki alkawari akan dukkan manzanni cewa sashin su zasu gaskata sashi, da kuma cewa in Allah ya aiko da wani manzo yana gaskata abunda ya ke tare da su to suyi imani da shi kuam su gaskata shi kuma su riki wannan alkawarin ga mutanen su, su Annabawa amincin Allah ya tabbata a gare su Allah ya wajabta musu da cewa sashen su yayi imani da sashi, kuma sashinsu ya gaskata sashi saboda duk abunda ke tare da su daga Allah yake, Allah madaukaki yace: “ lokacin da Allah ya riki alkawari akan Annabawa cewa saboda abunda na baku na littafi da hikima sai wani manzo yzo muku yana gaskata abunda ke tare da ku cewa lallai ku zakuyi imani da shi kuam lallai zaku taimake shi sai yace shin kun tabbatar da haka kuma kun riki alkawari akan haka sai suka ce mun tabbatar sai yace ku shaida kuma ni ina tare da ku cikin masu shaida (81) duk kuma wanda ya juya baya a bayan haka to wadannan su ne fasikai (82) shin yanzu wani addini da ba na Allah ba suke kauna kuma alhali gareshi ne duk wanda ke cikin sammai da kasa suka mika wuya suna so da kuma basa so kuma gareshi zasu koma (83)” suratu Ali imran, aya ta: 81-83.


Kuma Alkur’ani yazo da wasu ayoyi da suke kiran wadanda ba musulmai ba musamman ma ahlul kitabe daga cikin su (yahudawa da kiritoci) zuwa ga yin imani da Annabi Muhammad (S.A.W) da kuma bin sakon sa, kamar yadda Allah


94


ya baiyyana haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: “ ya ku bani isra’ila ku tuna ni’imata da nayi muku kuma ku cika alkawari na a zan cika alkawarin da nayi muku kuma kuji tsorona ni kadai (40) kuma kuyi imani da abunda na saukar yana gaskata abunda ke tare da ku kuma kada ku kasance na farkon kafurce masa kuma kada ku siyar da ayoyi na da iyan kudi kadan kuma kuji tsorona ni kadai (41) kuma kad ku cakuda gaskiya da karya kuma sai kuke boye gaskiya alhali kuna sane (42)” suratul Bakara, aya ta: 40-42,


Kuma hakika Annabi Isah ya amsa umarnin Allah saboda kuwa yayi bushara da da wani manzo da zai zo a bayan sa kuma ya baiyyana wa mutanen sa cewa shi manzo ne na bani isra’ila kawai, hakika yazo a cikin Injilar Matta 15/24 lallai shi yace: “ ni ba’a aiko ni ba sai dai zuwa ga battan gidaje bani israila kawai”.


Kuma daga cikin maganar saamincinAllah ya tabbata a gare shi hakikanin gaskiyar abubuwa biyu zasu baiyyana:


gaskiya ta farko: lallai shi ba’a aike shi ba dan mutane baki daya sai dai shi an aike shi ne zuwa fga wasu mutane kebantattu a wani zamani kebantacce, kuma wannan shi ne abun da injiloli suka ruwaito.


To idan wannan shi shi ne abun da Injilolin su suek fada to saboda me da’awar kiristoci bata takaita akan bani isra’ila ba kawai (yahudawa) da kuma kiran su zuwa ga kiritanci dan tabbatar da maganar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi mai makon su sabawa maganar Annabi Isah amincin


95


Allah ya tabbata a gare shi kum su koma kiristantar da wadanda ba bani isra’ila ba?!


Kuma lallai wannan nassin na Injila a cikin sa akwai dalili a fili akan cewa kiristanci ba addini ne na duniya baki daya ba kuma lalli bushara da shi baya cikin rukunnan addinin kiristanci.


Gaskiya ta biyu: shi ne cewa matukar dai shi ba’a aiko shi ba sai dai zuwa ga wasu batattu daga cikin bani isra’ila wannan ke nuna cewa akwai wani Annabi da za’a aiko a bayan sa kuma da’awar sa zata zama ta duniya ce baki daya kuam shi ne zai zama na karshe, kuma wannan shi ne abunda Annabi Isah yayi bushara da shi ta yadda ya zama daya daga cikin aiyyukan Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi shi ne bushara da zuwan annabi na karshe Muhammad (S.A.W), ta yadda Alkur’ani ya baiyyana wannan gaskiyar, Allah madaukaki yana cewa:” kuma lokacinda Isah dan Maryam yace yaku bani isra’ila lallai ni manzan Allah ne zuwa gare ku ina mai gaskata abunda ya gabace ni na Attaura kuma ina bushara da wani manzo da zai zo a baya na sunan sa Ahmad lokacin da yazo musu da hujjoji sai sukace wannan sihiri ne mabaiyyani (6)” suratus saffi, aya ta: 6.


Kuma mutum mai adalci wayaiyye wanda ya iyanta hankalin sa daga makauniyar biyaiyya ga wanin sa da kuma sake linzami ga addinin iyaye da kakanni zai tambayi kansa cewa shin akwai wani abu da zai hana manzan Allah (S.A.W) zama Maznzo aiyakke daga Allah madaukaki kuma hakika an aiko Annabawa da Manzanni da yawa kafin sa? Idan dai har amsar ta zama cewa babu wani abu da zai hana a hankalce da kuma shar’ance to saboda me ake inkarin Manzancin sa da Annabcin sa


96


amincin Allah ya tabbata a gare shi ga mutane baki daya amma kuma aka tabbatar da manzancin Annabawan da suka zo kafin sa?!.


97


Hakika da yawa daga cikin malamai da masu bauta na kiristoci sunyi imani da Manzan Allah Muhammad (S.A.W) bayan sun san cewa abunda Annabi Muhammad yazo da shi gaskiya ne, hakika littattafan su masu tsarki sunyi bushara da baiyyanar wani manzo bayan Annabi Musa da Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gre su, duk da irin abun da ya shiga wadannan littattafan na canji da juyarwa da wasannni wurin tarjama a tsawon lokuta mabanbanta da kuma bacewar asalin bugun su sai dai siffofin Annabi Muhammad (S.A.W) dawan syu sun rage a cikin su kuma su siffofi ne da ke nuni akan sa nuni mabaiyyani babu kokwanto a cikin su, saboda haka ne har zuwa yau ake samun adadi mai yawa na kiristoci da suke shiga cikin addinin musulunci duk da irin batashi da ake yi da gangan ta bangaren kafofin sadarwa na zamani na turawa, Allah madaukaki yace: “ su ne wadanda suke bin manzo Annabi wanda baya rubuto ko karatu wanda suke samunshi a rubuce a wurin su a cikin Attaura da Injila yana umartar su da kyaikkyawa kuma yana hana su daga mummuna kuma yana halatta musu abubuwa masu dadi kuma yana haramta musu abubuwa masu cutarwa kuma yana sauke nauyin da ke kansu da kuma kulli da ke wuyan su to duk wanda sukayi imani da shi kuma suka bashi kariya kuma suka taimake shi kuma suka bi hasken da ak saukar tare da shi wadannan sune masu rabauta (157)” suratul A’araf, aya ta: 157.


98


Hakika Annabi (S.A.W) ya baiyyana wa sahabban sa cewa shi busharar dan uwan sa ne Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi lokacin da suka tambaye shi sai suka ce: ya manzan Allah ka bamu labarin kanka, sai yace: ni ne addu’ar mahaifina Ibrahim kuma busharar Isah, kuma lokacin da mahaifiyata ta dauki cikin na ta ga kamar wani haske ya fita daga gare ta sai ya haskaka manyan gidajen busra na kasar sham.” Tafsirin Alkur’ani na Ibn kaser.


Lokacin da aka aiko Annabi Muhammad (S.A.W) wanda suka imani da shi sun yi imani kuma wadanda suka kafurta suka kafurta ciin mutanen ahlul kitabi, Safiyyah iyar Huyaiyyi dan Akhtab Allah ya kara mata yadda matar Manzan Allah (S.A.W) tana cewa kuam ita bayahudiya ce kafin ta musulunta: “ babu wani daga cikin yaran mahaifi na da mahaifiyata da suka fi soyuwa a gare su kamar ni, ban taba zuwa wurin su tare da sauran yaran su ba face sai sun dauko ni sun bar sauran, lokacin da Manzan Allah (S.A.W) ya zo qubq- kauyen bani Amru bnAuf- sai mahaifi na ya tafi wurin sa da dan uwan baba na Abu Yasir bnAkhdab da duku-duku, wallahi basu dawo wurin mu ba sai bayan faduwar rana, sai suka dawo mana jikin su yayi sanyi kasalallu gajiyayyyu suna tafiya a hankali, sai na je tarbar su kamar yaddda nakeyi kullum wallahi ba wanda ya kalleni a cikin su, sai naji baffa na Abu Yasir yana cewa mahaifi na: shin shi ne kuwa? Sai yace: eh wallahi! Kana gane shi da kamar sa da kuma siffar sa? Sai yace: eh wallahi! Sai yace: to me ye a ranka game da shi? Sai yace” kiyaiyyar sa wallahi matukar ina raye.” Sirah ta Ibn Hisham 2/165 da kuma Baihaqi a cikin Addala’il 2/532.



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH