Labarai




Me ne ne dalilin Tash idaga kabari ?


Fadin Allah Madaukaki


Yak u mutane !idan kun kasance a cikin shakka a tashin Alqiyama ,to lallai ne mu mun halittku daga turvaya ,sa’annan kuma daga gudan jinni ,sa’annan kuma daga tsoka wadda ake halittawa da wadda ba’a halittawadomin mu bayyana muku kuma muna tabbatar muku da abinda muke so acikin mahaifa zuwa wani loqaci ambatacce


Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:


Wancan ne domin lallai Allah shine gaskiya kuma lallai ne shi yake rayar da matattu kuma lallai shi mai iko ne kan dukkan komai .Sannan kuma Sa’a haqiqa lallai mai zuwa ce kuma haqiqa Allah ne yak e tayar da waxanda suke cikin kabari


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma shine ke fara yin halitta ,sa’annan ya sake ta kuma sakewar tafi sauki a gare shi


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kamar yadda muka fara a farkon halitta muke mayar da ita


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma mutum yana cewa, Shin idan na mutu lallai ne haqiqa da sannu za’a fitar dani ina mai rai


Sannan faxinsa


Shin kuma basu gani ba cewa :lallai Allah ,Wandaya halitta sammai da qasa kuma bai kasa ga halittarsu ba Mai ikonyi ne akan rayar da matattu ?Na’am, lalle Shi ,Mai ikon yi ne akan komai


Har ya zuwa qarshen Surar


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma daga cikin ayoyinsa cewa kana ganin Qasa qeqasasshiya ,to idan mun saukar da ruwa a kanta ,sai ta girgiza kuma ta kumbura .Lallai wannan da ya raya ta ,haqiqa Mai rayar da matattu ne .Lallai Shi Mai ikon yi ne akan kowanne abu.


Har ya zuwa qarshen Surar


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma daga cikin ayoyinsa cewa kana ganin Qasa qeqasasshiya ,to idan mun saukar da ruwa a kanta ,sai ta girgiza kuma ta kumbura .Lallai wannan da ya raya ta ,haqiqa Mai rayar da matattu ne .Lallai Shi Mai ikon yi ne akan kowanne abu.


Da yawa Allah yana Maxaukakin Sarki yana buga misali da yaddayake rayar da Qasa da ruwa sai ta wayi gari ta girgiza ta fitar da korayen tsirrai bayan ta mutu saboda rashin ruwa bayan ta kasance kafin nan matacciya Da wannan ne Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya buga misali a cikin hadisi mai tsaho na Aqil inda yake cewa


Rantsuwa da Ubangijinka babu wani Mutum a bayan kasa da zai Mutu ko a kashe shi sai an tsaga masa Kabari har sai ta tallafo shi ta wajen kansa sai ya Zauna yana cewa: ai maye ya faru ga ke? sabida abinda ya kasance ya saba da shi yana zaton yana zantar da Iyalansa ne sai na ce: ya Manzon Allah yaya za'a hada mu bayan mun rududduge ko kuraye sun cinye mu sai ya ce: ina baka labari ne da Ni'amomin Allah a bayan kasa kuma ita ko da ta rududduge kamar ganyen bishiya sai na ce: ba zai rayu ba? sai Allah ya aiko sama bata dade ba sai kwatatnkwacin kwanaki har ta rufe ta to sai ta zama daya kuma Rantsuwa da Ubangijinka mai iya taro ku ne daga Ruwa kamar yadda yake tare tsirrai a kasa sai ku futo daga Kaburburanku.


Hukuncin wanda ya qaryata tashi


Mene ne Hukuncin wanda ya qaryata tashi ?


Ya kafircewa Allah da Manzonsa da Littattafan sa


Allah ya yi masa Rahama


Kuma waxanda suka kafirta suka ce: ’’shin idan mun kasance turvaya mu da Ubanninmu shin haqiqa waxanda ake fitarwa ne ?


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma idan ka yi mamaki ,to mamakin kam shine maganarsu ,’’shin idan muka kasance turbaya za mu zama a cikin wata halitta sabuwa ?’’Wadan can ne wadan da suka kafircewa Ubangijinsu ,kuma wadan da akwai ququmai acikin wuyoyinsu ,kuma wadan can ne abokan wuta .Su a cikinta ,masu dawwama ne.


kuma Allah Madaukaki ya ce


‘’Waxanda suka kafirta sun riya cewa ba za’a tayar da su ba .Ka ce :Niina rantsuwa da Ubangijina ,lallai za’a tayar da ku haqiqatan ,sa’an nan kuma lallai ana labari game da abinda kuka aikata Kumawannanga Allah mai sauki ne


Acikin Sahih Muslim ya rawaito kuma cewa Zaidu Dan Arqam Allah ya Kara yarda da shi cewa Annabi tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa.


Allah Maxaukakin Sarki yace ‘’Dan Adam ya qaryata ni kuma hakan bai cancanci ya faru daga gare shi bay a zage ni kuma hakan bai kamata ya faru daga gare shi ba amma qaryatawar shi gare ni shine ya ce Allah ba zai dawo dani ba kamar yadda ya halicce ni a farko ba wai halittar ta farkon it ace mafi sauqi ba daga dawowar da su ,zagin kuma shine ya ce a kaina faxinsa Allah Madaukakin Sarki yana da da alhalin ni Daya ne wanda ake nufinsa da buqata Ban Haifa ba ,ba’a kuma haifeni ba .Kuma babu daya da ya kasance tamka a gare ni"


Dalilin busar Qaho


Me ne ne dalilin busar Qaho kuma busa nawa za’a busa cikinsa ?


Allah Madaukakin Sarki ya ce


Kuma aka busa a cikin qaho ,sai waxanda ke a cikin sammai da qasa suka suma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa ) sa’annan aka hura a cikinsa ,wata hurawa ,sai ga sun tsaitsaye ,suna kallo


A cikin wannan ayar an ambaci busa guda biyu ta farko dan suma ,ta biyu kuma ta tashi


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma ranar da ake busa qaho ,sai wanda ya ke a cikin sammai da waxanda suke a cikin qasa su firgita ,face waxanda Allah ya so


Wanda ya fassara firgita da cikin wannan aya da suma it ace busa ta farko wacce aka ambata a cikin Suratuz Zumar ,hadisin Muslim zai taimaka masa:


Sa’annan sai a busa Qaho babu wanda zai ji sai wanda ya fi kowa ji sai yace na farkon wanda zai ji shine wani mutum sai yace :sai ya suma sai mutaneduka su suma ,sai Allah ya aiko da ko kuma yace:sai Allah ya saukar da ruwan sama kai kace wata inuwa ce ta wani bangare na kaya daga sai Jikunan Mutane su tsuro san nan akuma wata busar sai Mutane su tashi suna kallo"


Hadisi


Wanda ya fassara firgita da ba tare da sum aba to busa ta uku ce wacce ta biyo bayan busa guda biyu abinda ke cikin hadisi mai tsaho kan qaho zai taimaka a ciki an ambaci busa uku: busa ta farko ta firgita sai busar suma sai kuma ta tashi zuwa ga Ubangijin Talikai.


Siffar taron tashin Alqiyama daga Alqur’ani


Yay a siffar taron tashin Alqiyama take Alqur’ani ?


Akwai ayoyi da yawakan haka daga cikinsu akwai faxin Allah Maxaukakin Sarki:


Kuma lallai ne haqiqa kun zo mana xai xai kamar yadda Muka halittaku a farkon loqaci


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma muka tara su ba mu bar kowa ba daga gare su


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


A ranar da muka tara masu taqawa zuwa ga Mai rahama suna bakin girma Kuma lallai Muna kora masu laifi zuwa Jahannama da gaggawa


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


Kuma kun kasance nau’I uku .Wato mazowa dama .Me ne ne mazowa dama ?Da mazowa hagu .Me ne ne mazowa hagu ?Da waxanda suka tsere .Su wadan da suka tseren nan sun tsere


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


Aranar nan suna biyar mai kira ,babu karkata a gare shi ,kuma sautuka suka yi kawici ga Mai rahama ,b aka sauraren komai face sautin tafiya.


Shine tafiyar sawaye zuwa wurin taruwa kamar takun Raqumi .Allah Madaukakin Sarki yana cewa :


Kuma wanda Allah ya shiryar to shine shiryayye ,kuma wanda y avatar to ba zaka sami waxansu masoya gare su ba bayan shi Kuma zamu tara su a Ranar qiyama akan fuskokinsu


Da wasun wadan nan daga Ayoyi.


Siffar taron tashin qiyama daga Sunnah


Yay a siffarsa take daga Sunnah ?


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Za’a tashi mutane akan qungiyoyi guda uku masu kwadayi masu addiniguda biyu kuma akan raqumi ,uku ma akan raquma da hudu ma akan raquma ,sai a tara sauran a wuta ta yi musu loqacin da suka yi Magana ,ta wayi gari da su loqacin da suka wayi gari,ta yi yammaci da su loqacin da suka kai yammaci.


Daga Anas xan Malik Allah ya yarda da shi ya ce: wani mutum ya ce ya Annabin Allah ta yaya za’a tashi kafiri akan fuskarsa sai Yace:


Shin wanda ya tafiyar da shi a duniya kan qafafu biyu a duniya ba mai iko bane ya tafiyar da shi akan fuskarsa ranar Alqiyama?


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:


Za’a tashe ku ranar tashin Alqiyama mara sa takalma matsiraita kamar yadda aka halittamu farkon halitta zamu koma


Farkon wanda za’a suturta daga ababan halitta ranar tashin Alqiyama shine Annabi Ibrahim ‘’Hadisi sai Aisha Allah ya qara yarda da ita ta ce :Ya Mnzon Allah Maza da Mataduka sashensu yana kallon sashe ?’’Sai Ya ce al’amarin ya fi haka tsanani ballantana wannan ya dame su ‘’


Siffar wurin tsayawa ranar tashin Alqiyama daga Littafi


Yay a siffar wajen tsayawa take daga LIttafi ?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Kuma kada kayi zaton Allah Mai shagala ne daga abinda Azzalumai suke aikatawa .Abin sani kawai ,Yana jinkrita musu ne zuwa ga wani wuni ,wanda idanuwa su ke fita tsuru tsuru a cikinsa .Suna masu gaggawa,masu xaukaka kawunan su zuwa sama kiftawar ganinsu bata komawa gare su .Kuma zukatansu wofintattu .


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ranar da Ruhi da mala’iku za su tsaya a cikin sahu ,babu mai Magana sai wanda Allah ya yiwa izini ,kuma ya faxi abinda ke daidai


Allah Madaukaki ya ce


Kuma ka tsawatarsu Ranar Alkiyama lokacin da Zukata suka zo iya wuya suna masu hadiye fushi kuma lallai Azzalumai basu da Abokakan Arziki ko wani Mai ceto da ake binsa.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Acikin yini wanda gwargwadonsa ,shekara dubu Hamsin ne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Za mu xauki lokaci saboda ku ,yak u masu nauyin halitta biyu !


Da wasun haka masu yawa:


Siffar tsayuwar tashin Alqiyama daga Sunnah da siffar hisabi daga Alqur’ani


Yaya siffar tsayuwar tashin Alqiyama daga Sunnah ?


Akan haka da akwai hadisai dayawa daga ciki an karvo daga Ibn Umar Allah ya qara yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Yinin da mutane ke tashi zuwa ga Ubangijin halitta


Sai ya ce :’’Xayansu zai tashi a cikin gumi zuwa kunnensa


Da hadisin Abi huraira Allah ya yarda dashi daga Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Mutane za su yi gumi ranar tashin Alqiyama har sai gumi yazo yana gudana a qasatsahon zira’I saba’in sa’annan ya rufe su ya kai har kunnen su


Yaya siffar bijirowa da hisabi daga Alqur’ani ?


Allah Madaukaki ya ce


A ranar nan za’a bijiro da ku (domin hisabi ),babu wani rai ,mai voyewa ,daga cikinku ,wanda zai iya voyewa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma a gitta su ga Ubangijinka suna sahu guda ,(mu ce musu ))lallai ne haqiqa kun zo Mana ,kamar yadda Muka halittaku a farkon lokaci.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma a ranar da Muke Tarawa daga kowacce al’umma,wata qungiya daga waxanda suke qaryata ayoyinMu,sai gas u ana kange su (ga kora) Har idan sun zo (Allah)zai ce ,’’Ashe kun qaryata ayoyinNa,kuma ba ku kewaye su da sani ba? To me ne ne kuka kasance kuna aikatawa?’’


kuma Allah Madaukaki ya ce


A ranar nan mutane za su fito daban-daban domin a nuna musu aiyukansu. to Wanda ya aikata gwargwadon kwayar zarra na alheri zai gan shi. Kuma wanda ya aikata gwargwadon kwayar zarra na sharri zai gan shi


kuma Allah Madaukaki ya ce


To rantsuwa da UbangijinKa !Haqiqa ,Muna tambayar su gaba daya game da abin da Suka aikata


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma ku tsayar da su ,lallai su ,waxanda ake yiwa tambaya ne


To ya ya sifar hakan ta ke?


Akwai hadisai masu yawa:


Faxar Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ta gabata


Wanda aka binciki Hisabin sa za’a yi masa Azaba


Aisha Allah ya qara mata yarda ta ce :Shin ba Allah ne ya ce ba :to za’a yi masa hisabi ,hisabi mai sauqi .sai Ya ce :’’wannan shine bijirowar’’


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Za’a zo da kafiri ranar tashin Alqiyama sai a ce dashi shi :shin da za’a ce kana da zinari cikin qasa shin zaka yi koyi dashi ?sai yace na’am ,sai ace dashi an tambayeka abinda yafi wannan sauki –Awata ruwayar kuma haqiqa an tambayeka abinda yafi wannan sauqi cewa kar kayi shirka ga Allah amma sai kaqi kayi shirkar


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Babu xaya daga cikinku face sai ya yi Magana da Ubangijinsa babu wani tafinta a tsakaninsu sai yayi duba zuwa daman sa ba zai ga komai ba face abinda ya aikaata yayi duba zuwa hagu shim aba zai ga komai ba face abinda ya aikata ya yi duba zuwa geffansa ba zai ga komai ba sai wuta tana haxuwa da fuskarsa ku ji tsoron wuta koda kuwa da gutsiren Dabino ne koda kuwa da kalma mai kyau ce ‘’


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce


‘’Xaya daga cikinku ,yana nufin mumini zai sunkuyawa Ubangijinsa har sai ya sanya kafaxarsa akansa sai yace da shi ka aikata kaza da kaza sai yace na’am ya kuma cewa ka aikata kaza da kaza sai yace :na’am sai ya miqar dashi sannan yace :na suturtaka a duniya a yau kuma na gafarta maka ita ‘’


Da wasun wadan nan daga Hadisai.


Siffar watsa takardu dagaLittafi


Yaya siffar watsa takardu daga Littafi ?


Allah Madaukaki ya ce


Kuma kowanne mutum Mun lazimta masa abin rekodinsa a cikin wuyansa kuma mMu fitar masa a ranar tashiin qiyama da littafi wanda zai hadu da shi budadde.Ka karanta Littafinka ,ranka ya isa ya zama mai Hisabi a kanka a yau


kuma Allah Madaukaki ya ce


Idan takardun ayyuka aka watsa su (ga masu su)


Allah Madaukaki ya ce


Kuma aka aza Littafin ayyuka ,sai kaga masu laifi suna jin tsoro daga abinda ke cikinsa ,kuma suna cewa kaiconmu !Me ne ne ga wannan Littafi ,baya barin qarama,kuma baya barin babba ,face ya qididdige ta?kuma suka sami abinda suka aikata halarce kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa.


Allah Madaukaki ya ce


Amma wandaaka bawa littafinsa a damansa ,sai y ace wa (makusantansa )’’ku karva ,ku karanta Littafina’’har zuwa faxinsa :masu ganganci


Acikin ayar suratul Inshiqaq kuma


To ,amma wanda aka bawa Littafinsa a damansa


Kuma ya ce:


Kuma amma wanda aka bawa Littafinsa daga wajen bayansa


Wannan yana nuni kan cewa duk wanda ya karbi Littafinsa da Damansa za’a bashi ta gabansa wanda kuma aka bashi da hannun Hagu za’a bashi ta bayan sa ne muna neman tsari da Allah Maxaukakin Sarki


Siffar watsa takardu daga Sunnah


Mene ne dalilin hakan daga Sunnah ?


Akwai hadisai masu yawa kan haka daga cikinsu akwai :faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ‘’Mumini zai sunkuya ga Ubangijinsa har sai ya sanya kafaxarsa akan shi sai


ya miqar da shi daga sunkuyon nasa yace dashi kasan zunubi kaza? sai yace na sani yace haka ga Ubangijinsa sau biyu na sani ,sai yace na suturta shi a duniya ,a yau kuma na gafarta maka su ,sai a naxe takardar aiyukansa na alheri ,amma sauran ko kuma kafirai sai a kira musu manyan masu shaida su ce


‘’Waxannan ne suka yi qarya ga Ubangijinsu ‘’


Aisha Allah ya qara yarda a gare ta ce n ace da Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi shin masoyi zai ambaci masoyinsa ranar tashin Alqiyama ?sai yace ya Aisha amma a waje uku ,amma a wajen mizani har sai yayi nauyi ko ya yi rauni ,amma wajen watsa takardu ko dai ka karva da Dama ko kuma ka karva Hagu da kuma lokacin da ake fitar da wuya daga wuta.


Ahmad ne ya rawaito hadisin da Abu Dawud da wasun waxannan daga hadisai


Dalilin Mizani daga Littafi da Siffarsa take


Dalilin Mizani daga Littafi da Siffarsa take


Allah ya yi masa Rahama


Kuma Muna aza ma’aunan adalci ga ranar qiyama ,saboda haka ba’a zaluntar rai da komai .Kuma koda ya kasance nauyin qwaya daga komayyane Mun zo da ita .kuma Mun isa zama Masu hisabi


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma awo a ranar nan gaskiya ne .to ,wanda sikelansa suka yi nauyi ,to waxannan su ne masu cin nasara,kuma wanda sikelansa suka yi sauqi,to waxannan ne waxanda suka yi hasarar rayukansu, suna madawwama a cikin jahannama


Allah Maxaukakin Sarki yace game da kafirai


Ba zamu tsayar musu da awo ba a ranar qiyama


Da wasun waxannan daga ayoyi.


Me ne ne dalilin Siraxi daga Sunnah da Siffarsa ?


Akwai hadisai masu yawa:


Daga ciki akwai hadisin kati wanda cikinsa akwai shahada guda biyu tana da feji saba’in na munanan aiyuka kuma kowacce takarda anyi rubtu a cikin iyakar ganin idonka


Daga ciki akwai faxin Manzon Allahkan Ibn Mas’ud Allah ya yarda dashi:


‘’Kuna mamakin takun qafafu ne to ,a mizani nauyisnsu yafi nauyin wani xayan ‘’


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


‘’Haqiqa za’a zo da wani mutum mai girma mai qiba ranar tashin Alqiyama amma a wajen Allah ba za’a gwada shi ba ma da fiffiken Sauro ‘’sai yace :ku karanta


Ba zamu tsayar musu da awo ba a ranar qiyama


Da wasun waxannan daga Hadisai.


Dalilin Siraxi daga Littafi


Me ne ne dalili kan Siraxi da Littafi ?


Fadin Allah maigirma da Daukaka:


Kuma babu kowa daga gare ku sai mai tuzga mata.Ya kasance wajibi ga UbangijinKa hukuntacce Sa’annan kuma Mu tserar da waxanda suka yi aiki da taqawa ,kuma mu bar azzalumai a cikinta gurfane


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ranaar da za ka ga Muminai Maza da Muminai Mata haskensu na tafiya a gaba gare su


Dalilin Siraxi daga Sunnah da Siffarsa


Me ne ne dalilin Siraxi daga Sunnah da Siffarsa ?


Akwai hadisai masu yawa:


Daga ciki akwai faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare cikin hadisin ceto:


Za’a zo da Gada sai a sanya ta tsakanin bayan Jahannama sai muka ya Manzon Allah me ce ce Gada ?sai yace: mai rinjaya ce


Hadisin ya zo a cikin Sahih


Abu Sa’id Allah ya qara yarda da shi yace : na sami labara cewa wannan Gadar tafi gashi siranta kuma tafi takobi kaifi.


Dalilin kan Haud daga Littafi


Me ne ne dalili kan Haud daga Littafi ?


Allah ya yi masa Rahama


Lallai ne ,Allah ba Ya zaluncin gwargwadon nauyin zarra ,idan ta kasance alheri ce ,zai rivanyata kuma Ya kawodaga gunsa ijara mai girma.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Yau ana sakawa kowane rai a game da abinda ta aikata babu zalunci a yau .Lallai ne Allah mai gaggawar hisabi ne har zuwa faxin Allah :Allah yana yin hukunci ne da gaskiya


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma akayi hukunci a tsakaninsu da gaskiya ,alhalin kuwa sub a za’a zalunce su ba.


Dalilin Haud daga Sunnah


Me ne ne dalili kan Haud daga Sunnah?


Akwai hadisai masu yawa daga ciki akwai:


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Farkon abinda za’a fara hukunci a kanshi tsakanin mutane shine Jini ‘’


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Duk wanda ya san ya zalunci Dan uwansa to, ya biya shi a yau saboda ranar lahira babu Dinari ko Dirhami da zai bawa xan uwansa sai dai a Dauka daga kyawawan aikinsa idan bashi da kyawawan aiyuka sai a xebi munanan aiyukan Dan uwansa sai a zuba masa"


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Za’a fito da mumini daga wuta sai ajiye su tsakanin Aljannah da wuta sais u bawa sashensu labarin wani zalunci da ya kasance a duniya a tsakaninsu har lokacin da za’a tafi da su a tsarkake su sai a yi musu izini da shiga Aljannah


Dukkannin waxannan yana cikin Sahih da wasunsu da yawa


Dalilin kan Tafki daga Littafi


Me ne ne dalili kan Tafki daga Littafi ?


Allah Madaukakin Sarki yana cewa Manzonsa Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi:


Lallai ne Mu ,Mun yi maka kyautar Alkausara


Dalilin Tafkin Alkausara daga Sunnah


Me ne ne dalili kan Tafkin Alkausara daga Sunnah?


Akwai hadisai masu yawa akan haka daga ciki akwai faxin Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Ni zan rigaku zuwa Tafkin Alkausara


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Haqiqa ni rigaku gaba kuma ni mai shaida ne a gare ku Na rantse da Allah ina ganin Tafkin Alkausara ta a yanzu ’’


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Tafkin Alkausara ta tafiyarsa Wata daya ne kuma Ruwansa Fari ne yafi Nono fari kuma Kamshinsa yafi Almiski kofunansa yawan Adadadin Taurarin Sama kuma duk wanda ya sha shi bai kara jin kishi har Abadan"


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Na je ga wata Qorama tana da qofar Lu’u lu’u rufaffe sai n ace me ne ne wannan ya Jibril?sai yace wannan shi ne Alkausara’’


Da wasun wadan nan daga Hadisai masu yawa akan shi .


Da wasun waxannan daga hadisai masu yawa akan shi.


Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta? Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta?


AllahMadaukaki ya ce


Ku ji tsoron wuta wadda makamashinta mutane da duwatsu nean yi tattalinta domin kafirai Kuma ka bayar da bushara ga waxanda suka yi Imani ,kuma suka aikata ayyuka na qwarai,cewa lallai ne suna da gidaje a Aljannah Qoramu na gudana daga qarqashinsu


Ya zo a cikin ingantacce daga addu’ar Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Sallar dare ‘’godiya tabbata gare kaKai gaskiya ne kuma alqawarinka gaskiya ne kuma gamuwa da kai gaskiya ne ,faxarKa gaskiya ce ,Aljannah gaskiya ce ,wuta ma gaskiya ce ,Kuma Annabawa gaskiya ne kuma Annabi Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi gaskiya ne kuma ranar tashin Alqiyama gaskiya ce ‘’.Hadisi


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Duk wanda ya shaida cewa babu wani Ubangiji da ya cancanci a bauta masa sai Allah shi kadai wanda bashi da abokin tarayya, kuma Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne kuma kalmarsa ne da ya jefa ta ga nana Maryamu kuma Ruhi ne daga gare shi, kuma Aljanna Gaskiya ce haka wuta ma, to Allah zai shigar da shi Aljanna akan kowane irin aiki ya Mutu.


Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta? Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta?


Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta? Me ne ma’anar Imani da Aljannah da Wuta?


Ma’anarsa shine Imani tabbatacce da samuwarsu ba zai gushe ba zai shiga ciki nhar abada sannan duk abinda suka qunsa a daga ni’imomi da Azaba


Dalili kan samuwr Aljannah da wuta


Me ne ne dalili kan samuwar Aljannah da


Allah Madaukakin Sarki ya bamu labari cewa su an tanada su ne Sai yace akan Aljannah


An tanade ta ne ga masu taqawa


Ya ce akan Wuta


An tanade ta ne ga kafirai


An bamu labari cewa Allah Maxaukakin Sarki ya zaunar da Adam da matarsa Hauwa a Aljannah kafin su ci Bishiya kuma Allah ya bamu labari cewa kafirai za’a ke bijiro da su ga Wuta safe da maraice


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Na tsinkaye a cikin Aljannah sai nag a mafiya yawan ahalinta talakawa ne ,Na leqa Wuta kuma sai nag a mafiya yawan ahalinta mata ne


Hadisi


Ya gabata akan fitina da Azabar kabari


‘’Idan Dayanku ya mutu za’a bijiro masa da mazaunin sa


Hadisi


Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce


‘’Ku sanyaya da yin Sallah saboda tsananin zafi yana daga numfashin Jahannama’’


Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce


Wuta ta kai kukanta ga Ubangijinta Maxaukakin Sarki tace ya Ubangiji na sashe na yana cin sashe sai Allah ya bata izinin yin numfashi sau biyu xaya a lokacin sanyi daya kuma a lokacin zafi shine mafi tsananin zafin da zaku ji lokacin zafi da kuma tsananin sanyin da zaku ji lokacin sanyi


Manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi yace zazzabi yana daga numfashin Jahannama ku sanyaya shi da ruwa


Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce


‘’yayin da Allah Madaukakin Sarki ya halicci Ajannah da Wuta sai ya aiki Jibril zuwa ga Aljannah sai ya ce je ka kayi duba zuwa gare ta’’


Hadisi


An bijiro da su ga Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a inda yake zaune ranar da rana tayi kusufi kuma an bijiro masa dasu a daren Isra’I game da haka akwai Hadisai ingantattu da yawa da bazasu kirgu ba.


Dalili kan samuwr Aljannah da wuta har Abada


Me ne ne dalili kan wanzuwar Aljannah da Wuta har abada ?


Allah Madaukakin Sarki ya ce a cikin Aljannah


Suna Madawwama a cikin ta ,wannan shi ne rabo babba


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma ba zasu zama masu fita daga cikinta ba


Allah Madaukakin Sarki ya ce akanta


Kyauta wacce bata yankewa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ba su yankewa kuma ba’a hana su


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lallai wannan,haqiqa azurtawarMu ce ,bata yankewa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lallai masu taqawa suna cikin matsayi amintacce


Zuwa fadin sa:


Ba su Dandanar mutuwa, a cikinsu ,face mutuwar farko


Allah Madaukakin Sarki ya bada labarin tanadarsu da rayuwa madawwamiya ga ahalinta da rashin yankewarta gare su da kuma rashin fitarsu daga cikin ta


Haka kuma Allah yana cewa game da Wuta


Sai dai hanyar Jahannama ,suna masu dawwama a cikinta har abada


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lallai Allah ya la’ani kafirai kuma Yayi musu tattalin wata Wuta mai kuna basu samun majibinci ,kuma ba zasu samu mataimaki


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma wanda ya sabawa Allah da Manzon sa kuma ya qetare iyakokinsa zai shigar dashi Wuta ,yana madawwami a cikinta


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma ba zasu zama masu fita daga Wutar ba


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ba’a saukakar da ita (Azabar )daga gare su alhalin kuwa su a cikinta ,masu kasa Magana ne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ba zai karbi ransu ba ballantana su Mutu kuma bazai Saukake musu Azaba ba


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lallai shi wanda ya je wa Ubangijinsa yana mai laifi ,to lallai ne yana da Jahannamabaya mutuwa a cikinta kuma baya rayuwa


Da wasun waxannan daga Ayoyi.


Allah Madaukakin Sarki ya bamu labara a cikin waxannan ayoyin da misalansu cewa yan Wuta an halitta Wuta dominsu itama kuma an halittata dominsu zasu dawwama acikinta har abada Allah Ta’ala ya shafe fitarsu daga cikinta da faxinsa : kuma ba zasu zama masu fita daga cikinta bay a kuma shafe yankewarta daga gare su da faxinsa :Ba’a saukakar musu da Azabar ta ,Ya kore shafe karewar zamansu a cikinta da faxinsa :Ba za su mutu ba acikinta ba kuma zasu rayu ba


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Amma yan Wuta wadanda suka kasance sune ahalinta haqiqa sub a zasu mutu ba a cikinta kuma ba zasu rayu ba ‘’Hadisin


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :''Ida’’yan Aljannah suka tafi zuwa Aljannah ,yan Wuta kuma suka tafi zuwa ga Wuta sai a zo da mutuwa a sanyata a tsakanin Aljannah da Wuta sai a yanka ta sai mai kira ya yi kira yace: ‘’yak u yan Aljannah babu mutuwa ,yak u yan Wuta babu mutuwa sai hakan ya qarawa yan Aljannah farinciki kan farincikinsu ,sai kuma ya qarawa yan Wuta bakinciki kan bakincikinsu ‘’a wani lafazin kuma :kowa zai dawwama cikin abinda ya kasance a cikinsa


Acikin wata ruwayar sai Annabi tsira da aminci su qara tabbata a gare shi ya karanta:


Kuma kayi musu gargadi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al’amari alhalin kuwa suna a cikin vata ,kuma bas u yin Imani


Ya zo kuma a cikin Sahih acikin hadisai waxanda bamu ambace su ba


Dalili kan cewa Muminai za su ga Ubangijinsu tsarki da xaukaka su tabbata gare shi a gidan lahira


Me ne ne dalili kan cewa Muminai zasu ga Ubangijinsu tsarki da Daukaka su tabbata gare shi a gidan lahira?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Wasu fuskokin a ranar nan masu annuri ne Suna Kallon Ubangijin ta


kuma Allah Madaukaki ya ce


Wadanda suka kyautata yi ,suna da abu mai kyau da kuma kari


Allah Madaukakin Sarki yace:


AAha Lallai cewa su ababan Shamaki ne ga barin ganin Ubangijinsu


Idan ya sanya shamaki tsakaninsa da maqiyanSa ba zai sanya tsakaninSa da masoyansa ba


Ya zo a cikin ingantattu guda biyu daga Jarir Bn Abdullah Allahyayarda da shi yace :Mun kasance muna zaune tare da Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi sai yayi duba zuwa ga Wata daren goma sha huxu sai Yace: ‘’Haqiqa zaku ga Ubangijinku gani kamar yadda kuke ganin wannnan idan kun sami dama kuyi Sallah kafin fitowar Rana da kafin faduwarta ku aikata ‘’kamar yadda kuke ganin wannan ‘’yana nufin ai kamar yadda kuke ganin wannan Watan an yi kamanceceniyar gani da gani ba wai kan abinda ake gani da abin ganin ba ,kamar fadinsa a hadisin Allah yayi Magana da Wahayi ‘’Mala’iku sun yi duka da fukafukansu da fadinsa kamar sarqa ce ‘’wannan Kamanceceniya ce ta sauraro da sauraro ba ta abinda ake saurare ba da saurare, Allah ya xaukaka ya kamanta Zatinsa ko ya SiffarSa da wani abu da ya halitta ,Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya tsarkaka ya riqi wani abu a zancenSa ya kamanta Allah alhalin shi yafi kowacce halitta sanin Allah ,a cikin wani hadisin na Suhaiba cikin Muslim ‘’Sai a yaye musu hijabi ba ‘a basu wani abu ba mafi soyuwa a gare su sama da ganin Ubangijinsu Madaukakin Sarki ‘’sai ya karanta wannan ayar:


Wadan da suka kyautata suna da kyautaye da kuma kari


Awannan babin akwai hadisai masu yawa kuma ingantattu baxaxxu mun ambaci wasu a sharhin "Sullamul Wusoul‘’ hadisai arba’in da biyar daga Sahabbai fiye da talatin ,wanda ya mayar da wannan ya kafircewa Qur’ani da abinda Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya zo da shi ,yana daga cikin waxanda Allah Madaukakin Sarki yake fada akansu


A’aha ! Haqiqa ,lallai ne su daga Ubangijinsu ,a ranar nan waxanda ake shamakancewa ne


Muna roqon Allah afuwa da gafara ,ya kuma azurta mu da samun jin xaxin ganin fuskarsa


Ameen


Dalilin Imani da Ceto Wa ye zai yi ceton ga su wa ceton zai kasance kuma da yaushe Ceton zai kasance?


Me ne ne dalilin imani da Ceto Su wane ne za su yi Ceton ga su wa Ceton zai kasance kuma yaushe Ceton zai kasance


Lallai Allah Maxaukakin Sarki yayi maganar Ceto a wurare da dama a cikin Littafinsa ,Allah ya bamu labari da cewa tana qarqashin mulkinSa shin mamallakinta babu wani da yake da iko da ita sai shi.Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


‘’Kace: ceto gabaxaya ga Allah yake


To amma yaushe zata kasance ?Allah Maxaukakin Sarki ya bamu labari da cewa ba zata kasance ba sai da izininSa kamar yadda Allah yace


Wa ne ne wanda yake iya yin ceto a warinSa ,in bada da Izininsa?


Babu wani maceci face a bayan IzininSa


Kuma da akwai daga cikin Mala’iku da yawa a cikin sammai cetonsu baya wadatar da komai face bayan Allah ya yi izni (da shi )ga wanda yake so ,kuma ya yarda


Kuma wani ceto baya amfani a wurinSa face fag a wanda Ya yi izni gare shi


Amma ga wadanda zata kasance shine kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki ya bamu labari cewa ba zata kasance ba sai bayan yayi izni Ya kuma bamu labara iznin baya kasantuwa sai ga masoyanSa yardaddunSa ga labarin kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya faxa:


Ba su Magana sai wanda Allah Ya yi masa izni ,kuma ya fadi abinda yake dai dai.


Kuma ya ce:


Ba su mallakar ceto face wanda ya riqi alqawari a wurin mai rahama


Amma ga wanda zata kasance an bamu labari cewa babu wanda za’a ceta sai wanda Ubangiji ya yarda dashi kamar yadda Ya fada


Kuma basu yin ceto face ga wanda Ya yarda


A yinin nan ceto baya yin amfani face wanda Mai rahama Ya yi masa izini kuma Ya yarda dashi da Magana


Kuma Allah Subhanahu wa ta’ala ba Ya yarda sai ga ma’abota tauhidi da Ikhlasi .amma waxanda suke sabanin haka Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa:


Kuma babu wani mai ceto da za’a yiwa Da’a( ga cetonsu)


Allah Madaukakin Sarki yace akanta


Saboda haka ba mu da wadansu maceta.Kuma bamu da aboki,masoyi.


Allah Madaukakin Sarki yace akanta


Saboda haka ceton masu ceto ba zai amfane su ba


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya bamu labari cewa haqiqa an bashi ceto sai ya bamu labari da cewa zai zo zai yi sujuda a qarqashi Al’arshi sai ya godewa Ubabgijinsa da godiyar da shi kadai ne Ya santa ba zai fara da ceto daga farko ba har sai an ce da shi ‘’Daga kanka Ka fada Yana jin ka Ka kuma tambaya za’a baka Ka roqi ceto za’a baKa ceton ‘’Hadisin.Sai aka bada labarin cewa ba zai ceci gabakidayan masu sabo ba daga ma’abota tauhidi a loqaci daya ba sai dai Yace :’’An sanYa min wata iyaka za’a sanya su a Aljannah ‘’sai Ya koma Yayi sujuda kamar haka sai a sanya masa iyaka har zuwa qarshen hadisin.Sai Abu Huraira yace da shi Allah ya qara yarda dashi wane ne mafi farincikin mutane da cetonKa ?Sai Yace : ’’wanda duk yace :La’ilaha illallahu yana mai ikhlasi har cikin zuciyarsa


Nau’ikan ceto da mafi girmanta


Nawa ne nau’ikan ceto kuma wacce ce mafi girmanta ?


Mafi girmanta Ceto ranar tashin Alqiyama ceto mai girma a filin Alqiyama Allah Maxaukakin Sarki zai zo Ya yi hukunci a tsakanin bayinsa, ceto kawai ya kevanta ne kawi ga Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi itace muqami abin godewa da Allah Maxaukakin Sarki Ya yi masa alqawari kamar yadda Allah Ya faxa:


Akwai tsammanin UbangijinKa ya tashe ka a matsayi godadde


a yayin da mutane suka shiga cikin takura a wurin tsayuwa , kuma tsayuwa ta yi tsayi da yawa, Damuwa ta tsananta, Gumi ya shanye su, sai su nemi ceto kan Allah ya rarrabe tsakanin su , sai su jewa annabi Adamu sa`annan Nuhu sa`annan Ibrahim sa`annan musa sa`annan Isa dan Maryam dukkanin su na cewa: Ta kaina na ke. Har su tuke ga annabin mu Muhammad mai tsira da aminci take sai ya ce: Ni nake da shi kamar yadda ya zo a bayyane cikin sahihai guda biyu (Bukhari da Muslim) da wasun su


Na biyu :wajen buxe qofar Aljannah ,farkon wanda zai fara buxe qofar Aljannah shine Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi farkon waxanda za su fara shiga Aljannah daga al’umatai su ne Al’ummarSa


Na Uku :ceton waxansu mutane an yi musu umarnin shiga Wuta sai ace kar su shige ta


Na huxu :Waxanda suka shiga Wuta daga ma’abota tauhidi su fito daga cikinta sai a fito da su sun koma gawayi sai a tsoma su cikin kogin rayuwa sai jikinsu ya tsiro kamar yadda qwaya take tsirowa cikin mafi kyawun yanayi.


Na biyar: ceto wajen xaukaka darajar waxansu mutane daga yan Aljannah ,amma waxannan ukun basu kevanta ba kawi ga Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi sai ma shine zai fara ta bayanshi kuma sai sauran Annabawan sai Mala’iku da Waliyyai sai mutane suma za su yi ceto ,sai Allah Mxaukakin Sarki da rahamarsa Ya fitar da mutane daga Wuta ba tare da ceto ba Ya shigar dasu Aljannah yawansu ba wanda zai iya irgawa sai Allah


Na shida :ceto wajen sauqaqa azabar waxansu kafirai wannan kaxai ta kevanta ne ga Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ga Baffansa Abi Xalib kamar yadda ya zo a Muslim da wasun sa Wutar Jahannama ba zata gushe ana jefa mat aba tana cewa akwai qari har sai Allah Maxaukakin Sarki Ya sanya QafafunSa ya danne ta sashenta ya haxu da sashe sai tace ya isa ya isa da girman izzarKa sai wasu mutane daga waxanda ba zasu shiga Aljannah bas u shige ta akan wannan akwai nassoshi da ba za su irgu ba wanda ya so ya sansu zai same su a Alqur’ani da Sunnah.


Tasirin aiki wajen shiga Aljannah da tsira daga Wuta


Shin wani zai shiga Aljannah ko ya tsira daga Wuta saboda aikinsa?


Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Ku kusato ku yi aiki haqiqa ba bu xaya daga cikinku da zai tsira saboda aikinsa sai suka ce ya Ma’aikin Allah har kai ma yace har Ni ma face sai dai Allah Ya lulluve ni da rahama daga gare shi da falalarsa.Acikin wata ruwayar: ’’Ku kusato ina yi muku bushara cewa babu wani da aikinsa zai shigar da shi Aljannah sai suka ce har kai Ya Ma’aikin Allah ?sai Yace har ni sai dai in Allah Ya lullube ni da rahamarsa kuma ku sani mafi soyuwar aiki a wajen Allah shine wanda aka dawwama yinsa komai qanqantarsa.


Aiyuka na qwarai sababi ne na shiga Aljannah


Me ne ne hadi tsakanin wannan Hadisin da fadin Allah Madaukakin Sarki :’’kuma aka kira su ,da cewa :Waccan Aljannah an gadar da ita gare ku saboda abinda kuka kasance kuna aikatawa ?


Alhamdulillahi babu cin karo da juna a tsakanin su, domin harafin (B) da yake tabbace cikin ayar harafi ne na sababi; Saboda su ayyuka na kwarai sababi ne na shiga aljanna baza a sami aljanna ba sai da su (ayyuka na kwarai) ta yadda abin da samuwar sa ke da sababi to dole sai an samar da wannan sababin, abin korewa a cikin Hadisin ita ce harafin (B) da take nuna kima, domin da ace bawa zai rayu tsawon duniya gaba dayan ta yana azumi da rana yana kuma tsaiwa da daddare yana nesantar sabo baki daya to da gabaki dayan aikin na shi ba zai fanshi daya bisa dubbai na mafi kan-kantar ni`imar Allah akan shi ba wadda take ta a fili da boye, to ta yaya (ayyukan) nashi za su zama sun kai kimar da za`a shigar da shi aljanna


Ka gafarta mana ,kuma kayi mana ,kuma kaine mafi alherin masu tausayi


Dalilin Imani da qaddara mai kyau


Dalilin Imani da qaddara a dunkule


Allah ya yi masa Rahama


Kuma umarnin Allah ya kasance abin qaddarawa tabbatacce


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma domin Allah Ya hukunta abinda yake ya kasance abin aikatawa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma umarnin Allah ya kasance abin qaddarawa tabbatacce


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma abinda ya same ku ranar haxuwar jama’a biyu,to da izinin Allah ne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma abinda ya same ku ranar haxuwar jama’a biyu,to da izinin Allah ne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Waxanda idan wata musiba ta same su sai su ce: ’’lallai ne mu ga Allah muke ,kuma lallai ne mu zuwa gare Shi muke komawa ‘’.Waxannan akwai albarka a kansu daga Ubangijinsu da wata rahama, kuma waxannan sune shiryayyu.


Ya zo a cikin hadisin Jibril ‘’Ka yi Imani da qaddara alherinta da kuma sharrinta ‘’


Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Kuma ka sani duk abinda ya same to dama can bai kasance zai kuvuce maka ba,abinda kuma ya kuvuce maka dama can bai kasance zai same k aba ‘’


Manzon Allah yace: ’’idan wani abu ya same ka kar kace da na aikata kaza da kaza da kaza ne zai faru sai dai kace: haka Allah ya qaddara abinda ya so shi yake aikatawa’’


Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :’’Kowanne abu an qaddara shine har rauni da nuna jin dadi ‘’da wasun haka daga hadisai


Matakan Imani da qaddara


Nawa ne matakan Imani da qaddara?


Matakan Imani da qaddara guda hudu ne:


Mataki na farko :Yin Imani da cewa ilimin Allah ya game dukkan komai wanda wani ma’aunin Zarra ba zai yi nisa ba daga gare shi acikin sama ko acikin qasa,kuma Allah Madaukakin Sarki Ya san gabakidayan halittarsa tun gabanin Ya halicce su ,Ya kuma san Arziqinsu da ajalinsu ,da maganganunsu,da aiyukansu ,da bakixayan motsinsu da zamansu ,da sirrikansu ,da abin da yake bayyane ,kuma su waye daga cikinsu yan Aljannah kuma su waye yan wuta daga cikinsu .


Mataki na biyu :Imani da rubutu cewa Allah ya rubuta gabakidayan abinda iliminSa ya gabata dama samamme ne ,daga cikin abinda ya kunshi wannan Imani da Allo da Alqalami .


Mataki na uku:Imani da cewa abinda ya so shi yake faruwa wanda ya shiga dukkan komai ,da qudurarsa da ta game dukkan komai ,abubuwa ne guda biyu ababan lazimta ta vangaren abinda ya kasance da wanda zai kasance ,babu lazimta kuma tsakaninsu kan abinda bai kasance ba ko kuma bai zamo daga kasantattu ba ,abinda Allah Maxaukakin Sarki Ya so to, kasantacce ne da qudirarsa babu wani haufi ,kuma abind Allah bai so b aba zai kasance ba saboda rashin sonSa ,ba wai saboda rashin ikon Allah Maxaukakin Sarki akanshi ba ,Allah ya xaukaka ga hakan .


Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayarSa ba acikin Sammai da kuma qasa ,lallai shi ne Ya kasance Masani,Mai ikon yi.


Mataki na hudu Imani da cewa Alkah Madaukakin Sarki shine mahaliccin dukkan komai kuma cewa babu wata zarra a sama ko a qasa ko a cikin abinda ke tsakaninsu face ta kasance Alkah ne Mahaliccinta,kuma Mahaliccin motsinta da zamanta Tsarki ya tabbata gare shi babu wani Mahalicci bayan shi babu wani Ubangiji kamarSa


Me ne ne dalili kan mataki na farko wanda shine Imani da ilimi?


AllahMadaukakin Sarki ya ce:


Shi ne Allah ,wanda babu wani abin bautawa face Shi,Masanin fake da bayyane


kuma Allah Madaukaki ya ce


Haqiqa Ya kewaye dukkan komai da sani


kuma Allah Madaukaki ya ce


Masanin gaibi gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare shi a cikin sammai kuma bata nisanta a cikin qasa kuma babu mafi girma face yana a cikin Littafi bayyananne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma mabudan gaibu suna gurinsa ba wanda ya sansu sai daishi…


kuma Allah Madaukaki ya ce


Allah shi ne mafi sanin inda Yake ajiye manzancinSa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lallai ne UbangijinKa shine mafi sani ga wanda yake bacewa daga hanyarSa kuma shine mafi sani ga masu shiryuwa.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Shin Allah bai zamo Mafi sani ba ga masu godiya


Shin Allah bai zamo Mafi sani ba daga abinda yake cikin zukatan talikai


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma aloqacin da UbangijinKa Ya ce ga mala’iku ‘’lallai ne ,Ni Mai sanya wani halifa ne a cikin qasa ‘’suka ce :’’ashe zaka sanya a cikinta ,wanda zai yi varna a cikinta ,alhalin mu muna yi maka tasbihi tare da gode maka ,kuma muna tsarkakewa gareka ‘’yace :’’lallai ne Ni Na san abinda baku sani ba


kuma Allah Madaukaki ya ce


Akwai fatar cewa ku qi wani abu ,alhalin shine mafi alheri a gare ku ,kuma akwai fatar cewa ku so wani abu ,kuma shine mafi sharri a gare ku,kuma Allah ne Yake sani ,kuma ku baku sani ba


Ya zo a cikin Sahih wani mutum yace :Ya Manzon Allah shin shin za’a iya sanin yan Aljannah daga yan Wuta ?sai Yace na’am .sai Yace akan me masu aiki suke yin aiki ?sai yace :’’kowa yana aiki ne akan abinda aka halitta shi ko aka hore masa’’


Akanshi aka tambayi Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi kan yayan mushirikai sai yace :’’Allah shine Mafi sanin abinda suka kasance suna aikatawa


Yazo a cikin Muslim Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yana cewa ‘’Lallai Allah ya halittawa Aljannah ahalinta an haliccesu domin ta tun suna tsatson iyayensu ,kuma an halittawa Wuta ahalinta an halicce sune dominta tun suna tsatson iyayensu"


Akan shi dai Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace:cewa mutum zai yi aiki aiki irin na yan Aljannah abinda ya bayyana ga mutane amma kuma yana daga cikin yan wuta ,wani mutum kuma zai yi aiki aiki irin nay an Wuta daga abinda ya bayyana ga mutane amma kuma yana cikin yan Aljannah


Akan hakan kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi yace :Babu wata rai daga cikinku face Allah Maxaukakin Sarki ya san mazauninta a Aljannah ko a Wuta ‘’sai suka ce:ya Ma’aikin Allah ba sai mun yi aiki ba sai mu dogara,sai yace ‘’ku yi aiki dukkanin komai mai sauqi ne kan abinda aka halitta gare shi ‘’sannan ya karanta:


To,amma wanda ya yi kyauta ,kuma ya yi taqawa,kuma ya gasgata kaima mai kyawu.To,za Mu sauqaqe masahar ya kai ga sauqi.


Da wasun waxannan daga Hadisai.


Me ne ne dalili da mataki na biyu shine Imani da rubutun qaddarori ?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Kuma kowanne abu Mun qididdige shi a cikin babban Littafi Mabayyani.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lallai wancan yana cikin Littafi


Allah Maxaukakin Sarki Yana cewa acikin qarar Musa da Fir’auna:


Yace:’’To mene ne halin qarnonin farko? sai Yace :’’saninsu yana a wurin Ubabgijina ,Ubangijina ba Ya vacewa kuma ba Ya mantuwa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma wata mace ba ta yin ciki,kuma bata haihuwa ,face da saninSa ,kuma ba za’a rayar da wanda ake rayarwa ba,kuma ba za’a rage tsawon ransa ba face yana a cikin Littafi .Lallai wancan mai sauqi ne ga Allah.


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce: ’’Babu wata rai da take numfashi face Allah Maxaukakin Sarki Ya rubuta wurinta a Wuta ko a Aljannah in ko bah aka ba to an rubuta ita xin yar Wuta ce ko yar Aljannah ‘’Muslim ne ya rawaito,kuma dai kan hakan Suraqa Bn Malik ya ce :ya Manzon Allah Ka bayyana mana addininmu kamar yanzu aka halicce mu, me ne ne aikin yau a kuma kan me Alqalami zai bushe a kan me qaddarori za su gudana ko kuma akan me zamu fuskanto ?sai Ya ce: ’’ku yi aiki gabaki xayan komai mai sauqi ne a wata ruwayar kowanne mai aiki abin sauqaqawa ne ga aikinsa ‘’da wasun haka daga hadisai


Abinda ke shiga cikin matakin rubuta qaddarori


Nawa ne yake shiga wannan matakin na rubuta qaddarori ?


Abubuwa biyar ne suke shiga wannan matakin kuma dukkaninsu suna komawa ne zuwa ga ilimi :


Qaddarawa ta farko :Rubuta haka tun gabanin halittar sama da qasa da shekara dubu hamsin ,a loqacin da Allah Ya halicci Alqalami ,wannan shine qaddarawa ta farko.


Na biyu :qaddarawa ta shekaru ,loqacin da aka dauki alqawari,


Shin ba Ni ne Ubangijinku ba ?


Na uku :qaddarawar shekaru kuma dai a yayin halittar gudan Jini a cikin mahaifa.


Na hudu: qaddarawa na shekara a Lailatul qadr


Na biyar :qaddarawa ta rana ,shine aiwatar da kowanne daga cikinsu a wurinsa


Dalilin qaddarawa ta Azal


Dalilin qaddarawa ta Azal


Me ne ne dalilin qaddarawa tun Azal?


Wata masifa ba za ta auku ba a cikin qasa ko a rayukanku face tana a cikin Littafi a gabanin Mu halitta ta


Ya zo kuma a cikin Sahih Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce :Allah Ya rubuta qaddarorin abin halitta tun gabanin ya halicci sammai da qasa da shekara dubu hamsin,Wanda Al’arshin Ya ke kan ruwa Ya ce:


Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’ Haqiqa Abinda Allah Ya fara halittawa shine Alqalami sai Ya ce da shi :Rubuta sai Ya ce Ubangiji me zan rubuta? sai Ya ce :ka rubuta qaddarorin dukkanin komai har zuwa ranar tashin Alqiyama ‘’Hadisin Yana cikin Sunan


Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’Ya Aba Huraira Alqalami ya bushe ga duk wani abin halitta ‘’Hadisin yana cikin Bukhari da wasun shi da yawa.


Dalilin qaddarawar shekaru ranar alqawari


Me ne ne dalilin qaddarawar shekaru ranar alqawari?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Kuma a loqacin da Ubangijinka Ya karvi (alqawari) daga Diyan Adam daga bayinsa a zuriyarsu ,kuma Ya shaidar da su akan rayukansu (Ya ce):shin ba Ni ne Ubangijinku ba? suka ce: Na’am !Mun yi shaida


Ishaq Dan Rahawaihi ya rawaito cewa wani mutum ya ce :Ya Manzon Allah ‘’shin aiyuka za’a fara su ko kuma hukunci ya rigaye su ?sai Ya ce: ’’haqiqa Allah Maxaukakin Sarki loqacin da ya fitar d zurriyya


Adam daga bayansa Ya shaidar da su akan rayukansu sai Ya ce: wadan nan yan Aljannah ne wadannan kuma yan Wuta ne ,yan Aljannah za’a yassare musu alyukan yan Aljannah m,yan Wuta kuma za’a yassare musu aiyukan yan Wuta"


Ya zo a cikin Muwadda cewa Umar Dan Khattabi Allah ya yarda da shi an tambaye shi kawannan ayar


Kuma a loqacin da UbangijinKa Ya karvi (alqawari )daga xiyan Adam ,daga bayinka ,a zurriyarsu kuma Ya shaidar da su akan rayukansu ,(Ya ce ):’’shin ba Ni ne Ubangijinku ba ?’’su k ace :Na’am !Mun yi shaida !’’(ya ce ):kada ku ce a Ranar tashin Alqiyama :lallai ne mu daga wannan gafalallu ne


Sai Umar dan khaddabi ya ce: na ji manzon Allah mai tsira da aminci ana tambayar shi gameda ita (wannan aya) sai manzon Allah mai tsira da Aminci ya ce: “Lallai Allah wanda sunan sa ya yi albarka kuma ya daukaka ya halicci annabi Adamu sai ya shafi bayan sa sai zuri`a suka fito daga gareshi, sai ya ce: Na halicci wadannan saboda wuta, kuma za su rika aiki irin aikin `yan wuta” Hadisin da tsawon sa. Ya zo cikin (littafin) Tirmizi daga Hadisin Abdullahi dan amru Allah ya kara yarda da su (su biyun) ya ce: Manzon Allah mai tsira da aminci ya fito mana a hannun sa akwai littafi guda biyu sai yace: shin kun san wadannan littafai guda biyu na menene? Sai muka ce: a`a yaa Manzon Allah sai dai idan ka bamu labari, sai ya fada gameda na hannun daman sa: wannan littafi ne daga ubangijin halitta baki daya, a cikin sa akwai sunayen `yan aljanna da sinayen iyayen su da kabilun su. Sa`annan ya tattara su har karshen su ba za`a kara wani a cikin su ba, ba za`a kuma rage wani daga cikin su ba har abada. Sa`annan ya fada ga wanda yake hannun hagun sa: “wannan littafi ne daga ubangijin halitta baki daya, a cikin sa akwai


Dalili kan qaddarawar rayuwa wanda yake tun farkon halittar gudan Jini


Me ne ne dalilin qaddarawar rayuwa tun farkon halittar gudan Jini?


Allah ya yi masa Rahama


Shi ne Ya fi saniga abinda keg are ku a loqacin da Ya qaga halittarku daga qasa ,kuma a loqacin da kuke tayuna a cikin cikin uwayenku.Saboda haka kada ku tsarkake kawunanku,Shi ne Mafi sani ga wanda ya yi taqawa


Ya zo a cikin Sahihul Bukhari da Muslim cewa Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: ’’Cewa dayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa har kwana arba’in yana Maniyyi sannan ya zama gudan jinni misalign haka, sannan ya zama gudan tsoka misalign haka sai a aiko masa da Mala’ika sai ya busa masa rai,sai a umarce shi da kalmomi guda hudu da arziqinsa, da Ajalinsa,da aikinsa,kuma shi Dan Wuta ne ko Dan Aljannah,Na rantse da wanda babu wani Allah bayan shi,haqiqa xayanku zai yi aiki aiki irin na yan Aljannah har sai ya kasance tsakaninshi da tsakaninta sai dai zara’I sai Littafi ya rigaye shi sai ya yi aiki aiki irin nay an Wuta sai ya shige ta,cewa Dayanku zai yi aiki aiki irin nay an Wuta har asi ya kasance tsakaninshi da tsakaninta sai dai zira’I sai Littafi ya rigaye shi sai yayi aiki aiki irin nay an Aljannah sai ya shige ta


Akwai ruwayoyi da yaw aba wannan ba daga Jama’a ta Sahabbai da lafuzza daban – daban amma ma’anar daya ce.


Dalilin qaddarawa na shekara a kan Lailatul qadri


Me ne ne dalilin qaddarawar shekare kan Lilatul qadri?


Allah Madaukakin Sarki ya ce: A cikinsa (shi daren )ake rarrabe kowane umarni bayyananne.Umarni ne daga wurin Mu Ibn Abbas Allah ya qara yarda da shi ya ce :Ana rubutawa daga Ummul Kitabi a daren Lailatul qadri abinda zai faru a shekara na daga mutuwa da rayuwa da arziqi da ruwa hatta Alhazai za’a ce Wane da Wane za su yi aikin Hajji,haka Alhassan xan Jubair da Muqatilda Abu Abdurrahman As Salmi da wasunsu.


Dalilin qaddarawar Rana


Me ne ne dalili kan qaddarawar Rana?


Allah Madaukaki ya ce


Akullum Allah na a cikin wani sha’ani


Abdullahi dan Abbas Allah ya kara yarda a gresu ya fada a cikin sahihul hakim: “Lallai yana daga cikin abin da Allah madaukaki ya halitta allo abin kiyayewa (ya halicce shi daga) farin lu`u lu`I, gefunan sa guda biyu daga jan yakutu, alkalamin sa haske ne, rubutun sa ma haske ne ana duba shi a kullum duba dari uku da sittin ko sau dari uku da sittin, a kowane duba daga cikin duban da ake yi masa; ana yin (sabuwar) halitta, ana azurtawa, ana rayarwa ana matarwa, ana daukakawa, ana kaskantarwa, yana aikata abin da ya so. Wannan shi ne fadin Allah madaukaki:


Akullum Allah na a cikin wani sha’ani


Dukkanin wadannan qaddarorin kamar rabo ne na qaddarorin da suka gabata,shine Azal wanda Allah Madaukakin Sarki Ya umarci Alqalami a loqacin da Ya halicce shi da ya yi rubutu a Lauhul Mahfuz,da wannan ne Ibn Umar da Ibn Abbas Allah Ya qara yarda da suka fassara fadin Allah Ta’ala


Lallai Mu,Mun kasance Muna sanya rubutun tamkar abin da kuka kasance kuna aikatawa


Dukkanin wannan tushensa yana daga ilimin Alllah waanda siffarsa ce Maxaukakin Sarki


Abinda qaddarorin na azaba dana jin dadi suka qunsa


Me ne ne abinda qaddarori suka qunsa na daga azaba da jin daxi?


Xaukacin Littattafai da suka zo daga sama da Sunnar Annabi sun hadu kan cewa qaddara ta rigaya kuma hakan ba zai hana aiki ba kuma baya wajaba dogaro kan hakan,sai dai yana wajabta jajircewa da qoqari da kwadaitarwa kan aiki na gari ,da wannan ne loqacin da Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya bawa Sahabbansa labari cewa qaddara ta rigaya sannan Alqalami ya bushe da ita sai sashensu yace :’’Shin ba zamu dogara akan Littafin mu bar aikin ?sai Ya ce :’’Ku yi aiki komai mai sauqi ne’’sai Ya karanta:


To,amma wanda ya yi kyauta,kuma ya yi taqawa


Allah mai tsarki da daukaka ya kaddara kaddarori ya kuma tanadar da sababan su, kuma shi gwani ne da abin da ya kafa na daga sababai a cikin wannan rayuwar da kuma makoma, Hakika kuma ya saukakewa kowa daga halittar sa ga abin da aka halitta saboda shi a cikin duniya da kuma lahira, shi an yi tanadi gareshi kuma an saukake a gareshi. Idan bawa ya san cewa duk abin da ya ke nema a lahira yana daure ne da sabubban da za su kaishi ga samun wannan masalahar ta shi to zai kasance mafi tsananin dagewa a cikin aikata ta da tsayuwa da ita,mafi girma daga wannan a cikin bin sabubban rayuwar sa da masalahohin sa na duniya. Lallai tabbas ya fahimci wannan dukkan fahimta wanda ya fadi wannan daga cikin sahabbai a lokacin da ya ji hadisan da suke (Magana) kan kaddara, ya ce: Ban kasance mafi tsananin dagewa (akan yin aiyuka na gari ba) kamar yanzu. Annabi mai tsira da aminci ya fada: “ka yi kwadayi bisa abin da zai amfane ka, kuma ka nemi taimakon Allah kuma kada ka gajiya”. Manzon Aallah mai tsira da aminci ya kuma cewa yayin da aka cemasa: Ya kake ganin magungunan da muke yin magani da su da kuma tawaida da muke yin tofin ta shin tana juyar da kaddarar Allah? Sai ya ce: “Ita ma tana cikin kaddarar Allah” yana nufin cewa Allah madaukaki ya kaddara alheri da sharri da kuma sabubban kowanne daga cikin su


Dalilin mataki na uku shine Imani da Mashi’ar Allah Ta’ala


Me ne ne dalili kan mataki na uku wato Imani da Mashi’ar Allah Ta’ala ?


Allah Madaukakin Sarki ya ce


kuma ba za ku so ba face sai Allah ya so


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma kada lallai ka ce ga wani abu,lallai ni mai aikatawa ga wancan gobe sai Allah ya so


kuma Allah Madaukaki ya ce


Wanda Allah Ya so Yana vatar da shi ,kuma wanda Ya so zai sanya shi kan hanya madaidaiciya


kuma Allah Madaukaki ya ce


Da Ubangijinka Ya so da dukkannin waxanda ke doron qasa sun yi Imani


Kuma da Allah Ya so da ba za su yaqi juna ba


Kuma da Allah Ya so da Ya ci nasara a kansu


kuma Allah Madaukaki ya ce


Mai aikata abinda Ya so ne


Umarninsavidan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai,’’Ka kasance ‘’ sai Yana kasancewa


MaganarMu ga wani abu idan Mun nufe shi,Mu ce masa,’’Ka kasance ‘’sai yana kasancewa


Domin haka wanda Allah Ya yi nufin Ya shiryar da shi sai Ya buxa qirjinsa domin Musulunci,kuma wanda Ya yi nufin vatar da shi sai Ya sanya qirjinsa mai qunci matsattse


Da wasun haka daga ayoyi waxanda ba za su qididdugu ba


Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’Zuciyoyin bayi suna tsakanin yan yatsu guda biyu daga yan yatsun Mai Rahama kamar zuciya guda xaya Yana juya su yadda Ya so ‘’


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce a cikin baccinsa a wani wadi ‘’Lallai Allah Maxaukakin Sarki Ya na karvar rayukanku a loqacin da Ya so Ya kuma dawo muku da su a loqacin da Ya so’’


Yana cewa :’ku yi ceto za ku sami sakamako Allah Ya na hukunci ne akan harshen Manzonsa da abinda Ya so’’


Ya na kuma cewa ‘’kada ku ce haka Allah Ya so sannan kuma haka wane ya so :sai dai ku ce haka Allah Ya so shi kadai’’


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce :’’Wanda Allah Ya so sai Ya fahimtar da shi a Addini


‘’Ian Allah Ya so wata Al’ummah da rahama sai Ya dauki ran Annabinta gabaninta ,idan kuma Ya so Ya hallakar da itaSai Ya azabtar da ita alhalin Annabinta Yana raye"


Da wasun wadan nan daga hadisai da aka ambaci Mashi’ar Allah da ikonsa wadanda ba za su irgu ba


Amsa ga wanda Ya ce ta ya ya Allah zai so abinda bai yarda da shi ba kuma ba Ya sonsa


Allah Maxaukakin Sarki ya bamu labari cikin Littafinsa ta harshen Manzonsa daga abinda ya sanar damu daga siffofinsa cewa Yana son masu kyautatawa da masu taqawa da masu haquri,Ya kuma


yarda da waxanda suka yi Imani suka kuma yi aiki nagari,ba kuma Ya son kafirai ko azzalumai,kuma bai yarda da kafirci ba daga bayinsa,kuma ba Ya son varna.


Tare da cewa duka wannan sun kasance da nufin Allah da ikonSa,lallai cewa da bai so ba hakan ba zata kasance ba,domin duk wani abinda ba Ya so baya kasancewa a cikin mulkinsa,me ne ne amsa ga wanda ya ce Ta ya ya zai so abinda bai yarda dashi ba kuma baya son shi ?


Ka sani cewa Son Allah ya zo a nassoshi da ma’ana biyu :So na kasancewar abu da ikonSa da qudurarSa,shine mashi’arSa,babu wani rabewa tsakaninta da soyayya da yarda,sai dai kafirci da Imani duk suna shigarta,da kuma biyayya da savawa, da yardajje da abin so,da abin qi da kishiyarSa wannan Iradar babu wani da ya fita daga cikinta kamar faxinSa Maxukakin Sarki


Domin haka wanda Allah Ya yi nufin Ya shiryar da shi sai Ya buxa qirjinsa domin Musulunci,kuma wanda Ya yi nufin Batar da shi sai Ya sanya qirjinsa mai qunci matsattse


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma wanda Allah Ya yi nufin fitinarsa,to ba zaka mallaka masa komai ba,daga Allah.wadannan ne waxanda Allah bai yi nufin Ya tsarkake zukatansu ba.


Nufi na addini na shari’a, ya kevanta ne kawai kan abinda Allah Yak e so Ya kuma yarda da shi ,daga cikin abinda ta qunsa akai umarnin Allah da kuma hani ga bayinSa kamar faxin Allah Madaukakin Sarki


Allah Yana nufin sauqi gare ku,kuma baya nufin tsanani gare ku


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Allah Ya yi nufin Ya bayyana muku\,kuma Ya shiryar da ku hanyoyin waxanda suke a gabaninku kuma Ya karvi tubarku.Allah Masani ne Mai Hikima.


Wannan nufin yana haifar da bin shi sai ga wanda nufi na kasantuwa ya rigaye shi.


Irada kauniyya da shar’iyya suna haxuwa acikin hakkin Mumini mai biyayya,sannan Irada kauniyya ita kaxai tana zamowa a hakkin bawa mai savo,Allah Maxaukakin Sarki ya kira bayinsa xaukacinsu zuwa ga abubuwan da Ya yarda dasu da shiryawa dan amsa masa amma wanxanda Ya so daga cikinsu ,kamar yadda Ya ke faxa:


Kuma Allah Yana kira zuwa ga gidan aminci,kuma Yana shiryar da wanda Ya ke so zuwa ga tafarki madaidaici


Allah Maxaukakin Sarki Ya game kira ,amma Ya kevance shiriya ga wanda Ya so :


Lallai ne UbangijinKa shine mafi sani ga wanda yake bacewa daga hanyarSa kuma shine mafi sani ga masu shiryuwa.


Dalili kan mataki na huxu shine Imani da qaddara itace mataki na halitta


Dalili kan mataki na huxu shine Imani da qaddara itace mataki na halitta


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Allah ne ne Mai halitta dukkan komai,kuma Shi ne wakili akan komai


kuma Allah Madaukaki ya ce


Shin akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da qasa?


kuma Allah Madaukaki ya ce


Wannan shi ne halittar Allah. To ku nuna mini, mene ne wadannan da ba shi ba suka halitta?


kuma Allah Madaukaki ya ce


Allah ne wanda ya halicce ku, sa’an nan ya arzurta ku, sa’an nan ya matar da ku, sa’an nan ya rayar da ku. Ashe daga cikin abubuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga wadannan abubuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ya daukaka bisa ga abin da suke yi na shika


kuma Allah Madaukaki ya ce


Allah shine wanda Ya halicce ku da abinda kuke aikatawa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Da rai da abinda ya daidaita shi.Sa’annan ya sanar da shi fajircinsa da


kuma Allah Madaukaki ya ce


Wanda Allah Ya shiryar,to shi ne Mai shiryuwa,kuma wanda Y avatar,to waxannan su ne masu hasara


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma amma Allah Ya soyar muku da Imani a gare ku,kuma Ya qawata shi a cikin zukatanku,kuma Ya qyamatar da kafirci da fasiqanci da savo


Yazo a cikin Bukhari halittr aiyukan bayi daga Huzaifa ‘’Lallai Allah Yana sana’anta dukkanin mai sana’a da abin sana’arsa ‘’Annabi tsira da Amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: ’’Ya Allah Ka bawa rai na tsoronta kuma ka tsarkake ta Kai ne Mafi alherin Mai tsarkake ta Kaine masoyinta kuma shugabanta ‘’da wasun waxannan daga Hadisai


Ma’anar faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ‘’Alkhairi dukkaninsa Yana hannunKa sharri kuma baya daga gare Ka


Me ne ne ma’anar faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ‘’Alkhairi dukkanin shi yana hannunKa,sharri kuma baya daga gare Ka ‘’ tare da cewa Allah Maxaukakin Sarki shine mahaliccin komai ?


Ma’anar wannanshine aiyukan Allah Maxaukakin Sarki gabadayan su alkhairi ne kebantacce ta vangaren siffanta su da Shi da jingina su gare shi babu sharri acikinsu ,saboda Allah Madaukakin Sarki Mai hukunci ne mai adalci Yana halitta abubuwa a bigiren da ya dace da su kamar yadda suke sannannu a wajenSA Madaukakin Sarki,duk wani abu da yazo wa bawa na sharri,to yana vangaren jinginawa bawa kan abinda dama an halitta shi gare shi na daga ababan hallakarwa wannan kuwa yana daga abinda hannayensa suka aikata sakamako ne wanda ya dace da aiyukansu,kamar yadda Allah Maxaukakin Sarki Ya ce:



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH