Labarai

SHAHARARRUN SUNNONIN DA SUKA YADU NA AKIDAR RABAUTACCIYAR TAWAGA MAI NASARA


Hafiz Bn Ahmad Alhakami


Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai


Dukkan yabo ya tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa kuma ya sanya duffai da haske,


sa’an nan kuma wadanda suka kafircewa Ubangijinsu suke karkacewa. Shi ne wanda ya halicceku


daga laka, sa’an nan kuma ya yanka wani Ajali, alhali wani ajalin ambatacce yana gurinsa. S’an nan


kuma ku kuna yin shakka. Kuma shi ne Allah a cikin sammai, kuma a cikin kasa, yana sanin asirinku


da bayyananku, kuma yana sanin abin da kuke yi na tsiwurwuta


Kuma ina shaidawa babu abin bautawa da cancanta sai Allah shi kadai ba shi da abokin tarayya


Makadaici ne wanda ake nufi da bukata bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba kuma babu daya da ya


kasance tamka a gare shi bari ma abin da yake cikin sammai da kasa duka ga re shi suke da’a shi ya


kirkiri sammai da kasa kuma idan ya nufi wani al’amari to sai kawai ya ce da shi kasance sai yana


kasancewa kuma Ubangijinka ne yake halittar abin da ya so kuma ya zaba, zabi bai kasance a wajansu


ba tsarki ya tabbata ga Ubangiji kuma ya daukaka ga abin da suke yin shirka, ba a tambayarsa game


da abin daya aikata kuma su ne ababan tambayar.Kuma ina shaidawa cewa shugaban mu kuma


Annabin mu Muhammad Bawansa ne kuma Manzansa ne kuma ya aiko shi da shiriya da kuma Addinin


gaskiya domin ya rinjayar da shi a kan Addinai dukansu kuma koda Mushirikan sun ki hakan.Tsira da


amincin Allah su tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa wadanda suka yi hukunci da gaskiya


kuma da shi ne suka kasance suna adalci, da kuma wadanda suka bi su da kyautatawa wadanda ba


sa kaucewa ga barin sunna bari dai ita kadai suke bibiya kuma da ita ne suke ruko kuma a kanta suke


soyayya kuma suke kiyayya kuma a wajanta ne suke tsayawa, kuma ga barinta suke korewa kuma


suke kariya da kuma dukkan wanda ya bi hanyarsu har zuwa ranar da za a tashe suBayan haka to


wannan wani abin takaitaccen littafi ne mai girmma kuma mai anfani, mai girman fa’ida mai tarin


abubuwan amfani,wanda yake tattare da ka’idojin addini, kuma yana kunshe da asalan tauhidi wanda


Manzanni suka yi kira izuwa gare shi kuma aka saukar da littattafai da shi kuma babu tsira ga wanda


yake yin addini da waninsa, kuma yana shiryarwa izuwa ga bin hanya mai haske kuma tsarin gaskiya


ne mabayyani na yi bayanin al’amuran imani da dabi’unsa a cikinsa, da kuma abin da yake gusar da


shi baki daya koma ya kore cikarsa.kuma na ambaci kowace mas’ala a cikinsa tare da dalilanta, domin


al’amarinta ya bayyana kuma hakikaninta ya fito sarari kuma hanyarta ta bayyanu, kuma na takaita a


cikinsa abisa matafiya ta sunna kuma na wofantu da maganganun ‘yan bin son zuciya da ‘yan bidi’a,


domin ita ba a ambatonta face don yin raddi a gare ta, da kuma harba kibiyar sunna a kanta, kuma


hakika manyan shuwagabanni sun toshe ga yayewar aibinta, kuma suka rubuta littattafai masu zaman


kansu a cikin raddinta da nisantata tare da cewa ana gane kishiya da kishiyarsa kuma ya fita da gane


hakikaninsa shi kadai, to idan Rana ta fito yini baya bukatuwa zuwa mai kafa Dalili da ita.kuma idan


gaskiya ta bayyana ta fito sarari to babu abin da yake bayanta face bata kuma na tsara shi a bisa


hanyar tambaya domin Dalibi ya farka kuma ya fadakuSannan na raba masa da amsa wacce Al’amarin


zai bayyana da ita kuma ba zai rikitar ba kuma na Saka Masa suna "Futattun Sunnoni da suka yadu,


don kudircewar tawagar da ta ke cin Nasara"Kuma Allah nake roko ya sanya shi don Girman sa mafi


daukaka, kuma ya amfane mu da abin da muka sani, kuma ya sanar da mu abin da zai amfane mu


saboda ni’ima daga gare shi da falala cewa shi a bisa dukkan komai mai iko ne kuma ga Bayinsa mai


tausasawa ne masani, kuma makoma tana izuwa gare shi kuma shi ne majibincinmu to madalla da


Majibinci kuma madalla Mataimaki.


Farkon abin da ya wajaba akan bayin Allah


Farkon abin da yake wajaba a kan Bayi sanin al’amuran da Allah ya haliccesu da shi, kuma ya riki


alkawari da shi a kansu kuma ya aiko Manzanninsa da shi izuwa gare su, kuma saboda shi ne ya halicci


Duniya da Lahira da Aljann da Wuta da shi ne za a yi kiran gaskiya kuma mai afkuwa ta afku kuma a


cikin sha’aninsa ne za a kafa Ma’aunai kuma takardu su dinga tashi kuma a cikinsa tsiya da arziki take


kasancewa kuma a bisa hisabinsa ake raba haskeKuma duk wanda Allah bai sanya masa Haske ba to


bashi da wani guri da zai samo Hasken


Al’amarin da Allah ya halicci halittu saboda shi


wane abu shi wancan al’amarin da Allah ya halicci halitta saboda shi?


Allah Madaukaki ya cekuma ba mu halicci Sammai da kasa da kuma abin da yake tsakaninsu wasa ba


bamu halicce su ba face da gaskiya kuma sai dai mafi yawansu ba su sani bakuma Allah Madaukaki


ya cekuma ba mu halicci Sama da Kasa da abin da yake tsakaninsu ba da gaskiya ba wancan zato ne na wadanda suka kafircekuma Allah Madaukaki ya ceKuma Allah ya halicci Sammai da Kasa da gaskiya kuma don a sakawa kowace rai abin da ta tsiwurwurta kuma su ba za a zalunce su bakuma Allah Madaukaki ya ceKuma bamu halicci Mutum da Aljan ba sai don su Bautamun


Ma’anar Bawa


me ake nufi da Bawa?


Bawa idan ana nufi da shi abin bautarwa wato ababan kaskantarwa to shi da wannan ma’anar ya tattare dukkan ababan halitta na daga talikai na sama da na kasa mai hankali da waninsa da danye da busashshe da mai motsi da mara motsi da bayyanane da boyayye da mumini da kafiri da managarci da fajiri da wadansun wadannan duka ababan halitta ne na Allah mai girma da daukaka ababan bauta ne gare shi mai horewa ne da horewarsa mai tsari ne da tsarawarsa, kuma kowanne daga cikinta wata alama ce da ya tsaya a gare shi kuma iyaka ce da ake tikewa izuwa gare shi kuma kowanne yana tafiya saboda wani ajali abin Ambato ba zai tsallake shi ba gwargwadon nauyin kwayar zarraWannan kaddarawar Mabuwayi ne Masanitsari ne na Adalci na mai Hikima, kuma idan ana nufi da shi mai ibada abin so an kebance wannan da muminai su ne Bayinsa ababan girmamawa, kuma masoyansa masu takwa, wadanda babu tsoro a kan su kuma ba za su kasance suna bakin ciki ba.


Ma'anar Ibada


Mecece Ibada?


Ibada it ace: suna ne wanda ya game dukkan abinda Allah yake so kuma ya yarda da shi na daga fadi da aiyuka na zahiri da na badini da kuma kubuta daga abin da yake kore wancan kuma yake kishiyantarsa.


Yaushe ne aiki yake kasancewa Ibada


?Yaushe ne aiki yake kasancewa ibada


Idan abubuwa biyu suka cika a cikinsa kuma sune cikar so tare da cikar kaskanciAllah Madaukakin Sarki ya cekuma wadanda suka yi imani su suka fi tsananin soyayya ga Allahkuma Allah Madaukaki ya ceLalle ne wadanda suke masu sauna sabo da tsoran UbangijinsuKuma Hakika Allah ya tattare wadan nan a fadinsaLalle ne su, sun kasance suna gudun tsere zuwa ga ayyukan alheri. Kuma suna kiranmu a kan kwadayi da fargaba. Kuma sun kasance masu saunar (aikata sabo) gare Mu.


Alamar soyayyar Bawa ga Ubangijinsa Mai girma da daukaka


Mecece Alamar soyayyar Bawa Ubangijinsa Mai girma da daukaka?


Alamar hakan : ya so abin da Allah Madaukaki yake so kuma ya yi fushi da abinda yake fusatar da shi kuma ya dinga misalta abubuwan da ya yi umarni da shi kuma ya nisanci hane hanensa kuma ya so masoyansa kuma ya yi ki ga makiyansa, kuma da wannan ne ya kasance mafi karfin imani shi ne so saboda Allah da kuma ki saboda shi.


yadda Bayi za su gane abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi


Da wane abu ne Bayi za su gane abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi?


Za su gane shi Madaukaki ta hanyar aiko da Manzanni kuma da saukarwarsa littattafai yana mai umartarsu da abin da Allah yake so kuma ya yarda da shi yana mai hana su ga barin abin da yake


kinsa kuma da wancan ne hujjojinsa masu karfi suke tsayawa a kansu, kuma Hikimominsa isassu suka bayyana


Allah Madaukakin Sarki ya ceManzanni masu bayar da bushara kuma masu gargadi domin kada wata hujja ta kasancega mutane a kan Allah bayan manzanninkuma Allah Madaukaki ya ceKa ce: in kun kasance kuna son Allah to ku bi ni sai Allah ya so ku kuma ya gafarta muku zunubanku kuma Allah mai gafara ne mai jinkai ne


Sharadan Ibada


Nawa ne sharadan ibada?


Uku ne:na farko: gasgata niyya kuma shi sharadi ne a cikin samuwarta, kuma na biyu: tsarkake niyya, kuma na uku: dacewar shari’a wanda Allah madaukaki ya yi umarni da kada a yi masa addini sai da shi, kuma su ne sharadai biyu a cikin karbarta


Gaskiyar Niyya


Menene shi gaskiyar Niyya?


Shi ne barin kiwa da kuma jinkiri da yin matukar kokari wajen gasgatawar fadinsa da Aikinsa


AllahMadaukakin Sarki ya ceyaku wadanda suka yi imani don me kuke fadin abin dab a ku aikatawa? Ya girma ga zama abin kyama a wurin Allah, ku fadi abin da ba ku aikata.


Ma’anar tsarkake Niyya


menene ma’anar tsarkake Niyya?


Shi ne nufin Bawa ya kasance baki dayan fadinsa da aikinsa na zahiri da na badini don neman yardar Allah Madaukaki


Fadin Allah maigirma da Daukaka:Kuma ba'a Umarce mu ba sai Mu bautawa Allah muna masu tsarkake Addini a gare shimuna masu kaucewa Bata, kuma mu tsaida Sallah kuma mu bada Zakka.kuma Allah Madaukaki ya ceKuma babu wani a wurinsa yake da bashin wata Ni'ama da zai saka Masa Kawai sai dai neman yardar Ubangijinsa Madaukakikuma Allah Madaukaki ya ceMuna ciyar da ku ne kadai domin neman yardar Allah kawai, ba mu nufin neman wani sakamako daga gare ku, kuma ba mu Neman godiya


kuma Allah Madaukaki ya ce


wanda duk ya kasance yana nufin noman Lahira za Mu kara masa a cikin nomansa, wanda kuma ya kasance yana nufin noman duniya za Mu sam masa daga gar eta,alhali kuwa ba shi da wani rabo a cikin Lahira


Shari’ar da Allah ya yi umarnin kada a bauta masa sai da ita


Mecece shari’ar da Allah ya yi umarnin kada a bauta masa sai da ita?


Ita ce Al-hanifiyya wato hanyar Annabi Ibrahim


Allah Mai tsarki da daukaka ya ce


Lallai kadai Addini a wajen Allah shi ne Musulunci


kuma Allah Madaukaki ya ce


To wanin Addinin Allah suke zaba? kuma fa gare shi duk abin da yake sama da Kasa ya mika Wuya yana Mai bi cikin Yarda ko Tilastawa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma Babu wanda zai kyamaci Tafarkin Annabi Ibrahim, face wanda ya wawaitar da kansa


kuma Allah Madaukaki ya ce


kuma wanda ya zabi wanin musulunci ya zama addini, ba za a karba daga gare shi ba kuma shi a Lahira yana daga cikin masu hasara


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ko suna da wasu Abokan Tarayya ne da suke Shar'anta musu Addini abin da Allah bai musu Izini da shi ba


Matakan Addinin musulunci


nawa ne Matakan Addinin musulunci?


yana Matakai uku ne: musulunci da imani da ihsani kuma kowa ne daya daga gar eta idan aka sake shi sai ya tattare Addinin baki dayansa


Ma’anar musulunci


Menene ma’anar musulunci?


Ma'anarsa shi ne mika wuya ga Allah da kadaitawa, da kuma bin dokokinsa da yi masa biyayya, da kuma kubuta daga Shirka.


Allah ya yi masa Rahama


Kuma wane ne ya fi kyau ga Addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma wanda ya mika fuskarsa zuwa ga Allah, alhali kuma yana mai kyautatawa to lalle ya yi riko ga igiya amintacciya


kuma Allah Madaukaki ya ce


Sa’an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne guda daya sai ku mika masa wiya. Kuma ka yi bushara ga masu kankantar da kai.


Dalili a bisa gamewar musulunci addini dukkansa ya yin da aka saki


Menene dalili a bisa gamewar musulunci addini dukkansa ya yin da aka saki?


Allah Madaukaki ya ce:


Lallai kadai Addini a wajen Allah shi ne Musulunci


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Musulunci ya fara bako kuma da sannu zai koma yana bako kamar yadda ya fara


Kuma Mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce


Mafificin musulunci shi ne imani da Allah


Ma'anar musulunci da rukunansa biyar


Menene dalili a bisa arrafa shi da rukunansa biyar a wajan rarrabewa?


Fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin hadisin tambayar da Jibrilu ya yi masa ga addini


Musulunci shi ne ka shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa Annabi Muhammadu manzansa ne kuma ka tsaida salla kuma ka ba da zakka kuma ka azimci ramadana kuma ka ziyarci dakin Allah idan ka sami ikon tafarki izuwa gare shi


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


An gina musulunci a bisa abubuwa biyar


sai ya ambaci wannan sai dai cewa shi ya gabatar da hajji a bisa azimin ramadana kuma dukkanninsu suna cikin Bukahari da Muslim.


Matsayin Kalmomin Shahada biyu daga addini


menene mahallin shahada biyu daga musulunci?


Bawa ba zai shiga addini ba face da su


Allah Madaukaki ya ce


kadai Muminai wadanda suka yi imani da Allah da Manzonsa


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


An umarce ni na yaki mutane har sai sun shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa Muhammadu Bawansa ne kuma Manzonsa ne


Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


Menene dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?


Fadin Allah Madaukaki


Allah ya shaida cewa shi babu abin bautawa face shi kuma Mala’iku da ma’abota ilimi sun shaida, yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face shi, Mabuwayi, Mai hikima


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


To ka sani, cewa babu abin bautawa face Allah


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


kuma babu wani abin bauta face Allah


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Allah bai riki wani abin haihuwa ba kuma babu wani abin bauta tare da shi


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


Ka ce da akwai wadansu abubuwan bautawa tare da shi, kamar yadda suka fada a lokacin,da sun nemi wata hanya zuwa ga ma’abocin Al’arshi


Ma’anar shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


Menene dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah?


Ma’anarta: korewa cancantuwar ibada ga duk wanda ba Allah ba da tabbatar da ita ga Allah Mai girma da daukaka shi kadai ba shi da Abokin tarayya a cikin bautarsa kamar inda kuma cewa ba shi da abokin tarayya a cikin mulkinsa


Allah Madaukakin Sarki Yace


ذلك بأن الله هو الحق وأن ما يدعون من دونه هو الباطل وأن الله هو العلي الكبير


Sharadan cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


Menene sharadan shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah wacce ba ta amfanar mai fadinta face da haduwarta a cikinsa?


Sharadanta bakwai ne:


Na farko: sanin ma’anarta halin korewa da tabbatarwa


kuma na biyu: yakinin zuciya da ita


na uku: jawuwa a gare ta a zahiri da badini


na hudu: karbarta alhalin ba za a komar da wani abu daga abubuwan da ta lazimta ba da kuma ta hukuntar


na biyar: tsarkaka a cikinta


Na shida: Gaskiya daga cikin kokon zuciya ba kawai fada da Baki ba


na bakwai: soyayya a gare ta da kuma ahalinta, da kuma jibinta da gaba saboda ita.


Dalilin sharadanta sani da La’ilaha illallahu


menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?


Fadin Allah Madaukaki


face wanda ya yi shaida da gaskiya


Yana nufin Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


kuma su suna sani da zukatansu ma’anar abin da harsunansu suka yi furuci da shi


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


da kuma fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi


Dalilin sharadanta sani da La’ilaha illallahu


menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?


Fadin Allah maigirma da Daukaka: Cewa kadai Muminai sune wadanda suka yi imani da Allah da Manzonsa sannan kuma basu yi kwakwanto ba


Zuwa fadin sa:Wadannan sune masu gasgatawa


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma cewa ni Manzon Allah ne ba wani Bawa da zai hadu da Allah da su baya kokonto a cikinsu face Allah ya shigar da shi Aljanna


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ga Abu Huraira


wanda ka hadu da shi a bayan wannan shingen yana mai shaidawa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma zuciyarsa tana mai yakini da ita to ka yi masa bushara da Aljanna


Dukaninsu biyun suna cikin sahihul Bukhari.


Dalilin sharadanta sani da La’ilaha illallahu


menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?


Allah ya yi masa Rahama


Kuma wanda ya mika fuskarsa zuwa ga Allah, alhali kuma yana mai kyautatawa to lalle ya yi riko ga igiya amintacciya


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Imanin dayanku ba zai cika ba har sai son zuciyarsa ya kasance mai bi ga abin da na zo da shi


Dalilin shardanta karbar Kalmar Shahada


menene dalilin sharadanta Karbar Kalmar Shahada daga Kur’ani da sunna?


Allah Madaukaki ya ce cikin sha’anin wanda bai karbeta ba


Ku tara wadanda suka yi zalunci, da abokan hadinsu, da abinda suka kasance suna bautawa


Zuwa fadin sa:


Lalle su sun kasance idan an ce musu babu abin bautawa face Allah sais u dora girman kai kuma suna cewa shin mu lallai masu barin gumakanmu ne saboda fadin wani mawaki mahaukaci?


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


kwatankwacin abinda Allah ya aiko ni da shi na Shiriya da Ilimi kamar Ruwan Sama ne da ya sauka a kasa wacce ta kasan ce kyakkyawa kuma sai ta karbi Ruwan ta futo da ciyawa da tsirrai Masu yawa kuma ya kasance da kwarurruka a cikinsa wanda zai tare Ruwa sai Allah ya amfanar da Mutane da wannan Ruwan sai suka sha kuma suka shayar kuma sukai Shuka kuma ya Ruwan ya samu wata Kasar kuma Fako wacce bata rike Ruwa kuma bata futo da tsiro, to wannan kwatankwacin wanda yayi Ilimin Shari'a ne kuma ya Amfana da shi abinda Allah ya aiko ni da shi sai ya sani kuma kwatankwacin wanda bai ko daga kai ga wannan ba, kuma bai karbi shiriyar Allah ba da ya aiko ni da shi ba.


Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


To Addini tsarkakakke na Allah ne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Saboda haka ka bautawa Allah kana mai tsarkake addini a gare shi.


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Mafi rabautar mutane da cetona wanda ya ce La’ilaha illallahu yana mai tsarkaka daga zuciyarsa


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Lalle Allah Madaukaki ya haramtawa wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu yana mai neman yardar Allah da ita


Dalilin shardanta gaskiya cikin Kalmar Shahada


menene Dalilin shardanta gaskiya cikin Kalmar Shahada daga Kur’ani da sunna?


AllahMadaukakin Sarki ya ce:


A. L .M. Ashe mutane sun yi zaton a bar su su ce, mun yi imani alhali kuwa ba za a fitine su ba? Kuma lalle mun fitini wadanda ke a gabaninsu, domin Allah ya san wadanda suka yi gaskiya, kuma lalle ya san makaryata


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Babu wani Bawa da zai shaida babu abin bauta wad a gaskiya sai Allah kuma cewa Muhammad Manzon Allah ne halin kasancewarsa mai gaskiya daga zuciyarsa face Allah ya haramta masa shiga wuta


Kuma ya fada ga wani mutumin kauye wanda ya sanar da shi shari’o’in musulunci izuwa fadinsa na rantse da Allah ba zan dada ba kuma ba zan rage ba daga gar eta sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce


Ya rabauta idan ya yi gaskiya


Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Yak u wadanda suka yi imani wanda ya bar addininsa daga ku to Allah zai zo da wasu mutane yana sonsu su kuma suna sonsa


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Abu uku wanda suka kasance tare da shi ya samu zakin imani da su: Allah da Manzansa su kasance mafi soyuwa a gare shi daga waninsu, kuma ya so mutum ba yana sonsa ba ne sai dan Allah, kuma ya ki komawa cikin kafirci bayan Allah ya tserar da shi daga cikinsa kamar yadda yake ki a jrfa shi cikin wuta


Dalilin jibinta Saboda Allah da gaba saboda shi


Menene dalilin jibinta don Allah da gaba saboda shi?


Fadin Allah maigirma da Daukaka:


ya ku wadanda suka yi imani kada ku riki yahudu da nasara majibinta sashinsu majibincin sashi ne kuma wanda ya jibince su daga gare ku to lalle ne shi yana daga gare su.


Zuwa fadin sa:


Abin sani kawai, majibincinku Allah ne da Manzonsa da kuma wadanda suka yi imani


kuma Allah Madaukaki ya ce


yak u wadanda suka yi imani kada ku riki iyayenku da ‘yan uwanku majibinta idan sun so kafirci a kan imani


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ba za ka sami mutane masu yin imani da Allah da ranar lahira suna soyayya da wanda ya sabawa Allah da Manzonsa ba


kuma Allah Madaukaki ya ce


Yaku wadanda suka yi imani kada ku riki makiyina kuma makiyinku masoyi


Dalilin shahadar cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah


Menene dalilin shaidawa cewa Muhammad Manzan Allah ne?


Fadin Allah Madaukaki


Lalle ne hakika Allah ya yi babbar falala a kan muminai, domin ya aika a cikinsu Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinsa a gare su, kuma yana tsarkake su, kuma yana karantar da su littafi da hikima


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Lalle ne hakika Manzo daga cikinku ya je muku, abin da kuka wahala das hi mai nauyi ne a kansa. Mai kwadayi ne saboda ku. Ga muminai mai tausayi ne mai jin kai


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Kuma Allah yana sane da lalle kai, hakika Manzansa ne


Menene ma’anar shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne?


Menene ma’anar shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne?


Shi ne gasgatawa yankakke daga cikin zuciya mai dacewa da fadin harshe da cewa Muhammad Bawansa ne kuma Manzansa ne izuwa baki dayan mutane mutanensu da AljanunsuMai shaida ne kuma Mai bushara ne kuma Mai gargadi ne kuma Mai kira ne izuwa Allah da izininsa kuma fitila Mai haskakawaTo ya wajaba a gasgata shi cikin gaba dayan abin day a bada labara das hi na daga labaran abin da ya gabata da kuma labaran abin da zai zo da kuma cikin abin da ya halatta daga halal kuma ya haramta daga haram da kuma misaita da jawuwa ga abin day a yi umarni das hi da kuma kamewa da hanuwa ga abin day a yi hani ga buransa da kuma bin shari’arsa da kuma lazimtar sunnarsa a boye da sarari tare da yarda da abin da hukunta da mika wuya a gare shi kuma da’arsa ita ce da’ar Allah kuma saba masa sabawa Allah nedomin cewa shi mai isar da sakon Allah ne kuma Allah bai karbe shi ba har sai da ya cika addini da shi ya kuma isar da sako mabayyani kuma ya bar al’ummarsa a bisa hanya mai haske darenta kamar yininta babu wanda zai karkace ga buranta a bayansa sai dai halakakke kuma a cikin wannan babi akwai mas’aloli da sannu za su zo in Allah ya so.


Menene ma’anar shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne?


Sharadan shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzan Allah ne


Menene sharadan shaidawa cewa Muhammad tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi Manzon Allah ne kuma shin za a karbi shaidar farko ba tare da ita ba?


Dalilin Salla da Zakka


menene dalilin Salla da Zakka?


Allah Madaukakin Sarki ya ce


Sa’an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin addini


kuma Allah Madaukaki ya ce


Sa’an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin addini


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma ba'a Umarce mu ba sai Mu bautawa Allah muna masu tsarkake Addini a gare shimuna masu kaucewa Bata, kuma mu tsaida Sallah kuma mu bada Zakka.


Dalilin Azumi


Menene dalilin Auzimi?


Allah Madaukakin Sarki ya ce


Ya ku wadanda suka yi imani ! An wajabta azimi a kanku kamar yadda aka wajabta shi a kan wadanda suke gabaninku


kuma Allah Madaukaki ya ce


To wanda ya ga wata daga cikinku, sai ya Azumce shi


da kuma Hadisin Mutumin kauye: ka bani labarin abin da Allah ya wajabta min na daga azimisai ya ceWatan Ramadana sai dai in kayi tadauwu’in wani abu


Dalilin Hajji


Menene dalilin azimi?


Allah Madaukakin Sarki ya ce


kuma ku cika hajjin da umara domin Allah


kuma Allah Madaukaki ya ce


kuma akwai hajjin Dakin domin Allah akan mutane ga wanda ya sami ikon zuwa a gare shi


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Lalle ne Allah Madaukaki ya wajabta a kanku Hajji


Hadisin yana cikin Bukhari da Muslim kuma hadisin Jibrilu ya gabata da kuma Hadisin


An gina musulunci a bisa abubuwa biyar


Hukuncin wanda ya musa daya daga cikin rukunan musulunci


Menene hukuncin wanda ya musa daya daga cikin su ko kuma ya tabbatar da shi kuma ya yi girman kai ga buransa?


Mene ne hukuncin wanda ya musa daya daga cikin su ko kuma ya tabbatar da shi kuma ya yi girman kai ga buransa?


Hukuncin wanda ya yayi Ikirari da Rukunan Musulunci sannan kuma ya barsu sabida Kasala ko wani Tawili


Mene ne Hukuncin wanda ya yayi Ikirari da Rukunan Musulunci sannan kuma ya barsu sabida Kasala ko wani Tawili?


Amma salla duk wanda ya jinkirta tag a barin lokacinta da wannan sifar to shi ana neman tubansa idan ya tuba idan kuma ba haka ba sai a kashe shi kisan haddi, saboda fadinsa Madaukaki:


Sa’an nan idan sun tuba kuma suka tsayar da salla kuma suka bada zakka to ‘yan’uwanku ne a cikin Addini


An umarce ni na yaki Mutane


Amma zakka idan mai hanata ya kasance yana daga wadanda ba makami a gare shi sai shugaba ya karbeta da rinjaye, kuma ya yi masa horo da karbar wani abu daga dukiyarsa, saboda fadin Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi


kuma dukkan wanda ya hanata to mu zamu karbeta da wani yanki na daga dukiyarsa tare da ita


In kuma sun kasance jama’a ne kuma suna da makami ya wajaba a bisa shugaba yakarsu har sai sun bada ita saboda ayoyi da hadisan da suka gabata da wasunsu da kuma aikinsa Abubakar da sahabbai Allah ya yarda da su baki daya.


Amma azimi babu wani abu da ya zo a cikinsa sai dai kuma shugaba zai ladabtar da shi ko wakilinsa da abin da zai kasance tsawatarwane gare shi da kuma misalinsa


Amma Hajji to dukkan rayuwar bawa lokacinsa ne bay a tserewa sai da mutuwa kuma abin da yake wajibi a cikin sa gaggautawa, kuma hakika narko na lahira ya zo a cikin wulakantawa a cikinsa, kuma wata ukuba a kebe a cikinsa a duniya bai zo ba.


Dalilin Imani da Manzan ni


Menene ma’anar Imani da Allah?


Imani fadi ne da kuma aiki fadin zuciya da harshe da kuma aikin zuciya da harshe da gabobi, kuma yana karuwa da da’a yana kuma raguwa da sabo kuma ahalinsa suna da fifiko a cikinsa


Dalili a bisa kasancewar imani fadi ne da kuma aiki


Menene dalili a bisa kasancewarsa fadi da aiki?


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Kuma amma Allah ya soyar da imani a gare ku, kuma ya kawata shi a cikin zukatanku


kuma Allah Madaukaki ya ce


to ku yi imani da Allah da Manzansa


Kuma wannan shi ne ma’anar shahada biyu wadanda Bawa ba zaishiga addini ba sai da su, kuma ita daga aikin zuciya ne a kudiri, kuma aikin harshe ne a furuci bata amfani said a dacewa da su


kuma Allah Madaukaki ya ce


kuma Allah bai kasance mai bata imaninku ba


yana nufin sallarku izuwa baitil makdisi kafin juya alkibla, an ambaci salla dukkanta imani kuma ita ta tattare aikin zuciya da kuma na harshe da na gabobi.


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya sanya jihadi da tsayuwar daren lailatul kadri da azimin ramadana da tsaya masa da bada khumusi da wasunsu daga imani, kuma an tambayi Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi: wane aikin ne ya fi falala? Ya ce imani da Allah da Manzonsa


Dalili a bisa karuwar imani da tawayarsa


Menene dalili a bisa karuwar imani da tawayarsa?


Allah Maxaukakin Sarki yana cewa:


Domin su kara imani tare da Imaninsu


Kuma muka kara musu shiriya


kuma Allah yana karawa wadanda suka nemi shiryuwa da shiriya


kuma wadanda suka nemi shiriya zai kara musu shiriya


Kuma wadanda suka yi imani su kara Imani


To amma wadanda suka yi imani to ta kara musu Imani


Don haka ku ji tsoransu sai (wannan Magana) ta kara musu Imani


Kuma wannan bai kara musu komai ba face imani da sallamawa


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Da cewa ku zaku dinga kasancewa a cikin kowane hali kamar halinku a gurina da Mala’iku sun dinga yi muku musafaha


kokamar yadda ya ce


Dalili a bisa fifikon ma’abota imani a cikinsa


Dalili a bisa fifikon ma’abota imani a cikinsa


Allah Madaukaki ya ce


Da wadanda suka tsere. Su wadanda suka tseren nan, wadancan su ne wadanda aka kusantar


Da mazowa dama. Mene ne mazowa dama?


kuma Allah Madaukaki ya ce


To amma idan ya kasance daga makusanta, sai hutawa da kyakkyawan abinci da Aljannar ni’ima, kuma amma idan ya kasance daga mazowa dama, sai( a ce masa) aminci ya tabbata gare ka daga mazowa dama


kuma Allah Madaukaki ya ce


Sa’an nan daga cikinsu akwai mai zalunci ga kansa kuma a cikinsu akwai mai tsakaitawa, kuma daga cikinsu akwai mai tserewa da aiyukan alheri da izinin Allah


Kuma a cikin hadisin ceto


Cewa Allah zai fitar daga wuta wanda ya kasance a cikin zuciyarsa akwai nauyin dinare na daga imani, sannan wanda a cikin zuciyarsa akwai rabin dinare na daga imani


Kuma a cikin wata riwaya za a fitar daga wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu kuma ya kasance a zuciyarsa akwai na daga alheri abin da zai kai nauyin kwayar sha’ir sannan za a fitar daga wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu kuma a cikin zuciyarsa akwai na daga alheri abin da zai kai nauyin kwayar alkama sannan za a fitar daga wuta wanda ya ce La’ilaha illallahu kuma ya kasance a cikin zuciyarsa akwai na daga alheri abin da zai kai nauyin kwayar zarra


Dalili a bisa cewa imani ya tattare Addini baki daya


Menene dalili a bisa gamewar musulunci addini dukkansa ya yin da aka saki?


Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi yace: wanda ya rataya wani abu to an jingina shi a gareshi


Ina umartarku da imani da Allah shi kadai ya ce: kun san menene imani da Allah shi kadai? Suka ce: Allah da manzonsa ne suka fi sani. Ya ce: shaidawa babu abin bauta wad a gaskiya sai Allah kuma cewa Muhammad Manzan Allah ne, da kuma tsayar da salla, da bada zakka, kuma ku bayar daga abin da aka samu na ganima daya bisa biyar


Dalili a bisa bada imani da rukunai shida


Menene dalili a bisa arrafa shi da rukunansa biyar a wajan rarrabewa?


Fadin Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya yin da Jibrilu aminci ya tabbata a gare shi ya ce: ba ni labari ga imani


ya ce:ka yi Imani da Allah da Mala’ikunsa da littattafansa da Manzanninsa kuma ka yi imani da kaddara alherinsa da sharrinsa


menene dalilin sharadanta sanin daga Kur’ani da sunna?


Fadin Allah Madaukaki


Bai zama addini ba domin kun juyar da fuskokinku wajen gabas da yamma, kuma amma addini shi ne ga wanda ya yi imani da Allah da ranar lahira da Mala’iku da littattafan sama da Annabawa


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


Lalle mu, kowane irin abu mun halitta shi a kan tsari


Kuma da sannu in Allah ya so za mu ambaci kowanne a bisa kadaitakarsa


Ma’anar imani da Allah Mai girma da daukaka


Menene ma’anar imani da Allah Mai girma da daukaka?


Shi ne gasgatawa yankakkiya daga cikin zuciya da samuwar zatinsa Madaukaki wanda bai rigayu da kishiya ba kuma ba zai yi karshe da ita ba ,shi ne na farko kafin shi ba kowa, kuma shi ne na karshe bayan shi ba kowa kuma shi ne Bayyananne burbushinsa babu kowa kuma Boyayye koma bayansa babu kowa Rayayye Makadaici abin nufi da bukata


bai Haifa ba kuma ba a haife shi ba kuma babu daya day a kasance tamka a gare shi


Kuma kadaita shi da Allantakarsa da rububiyyarsa da sunayensa da siffofinsa.


Kadaitarwar Allantaka


menene kadaitarwar Allantaka?


Shi ne dayanta shi Mai girma da daukaka da ga baki dayan ibada ta zahiri da ta badini, fadi da kuma aiki da kuma kore bauta ga duk wani ba Allah ba Madaukaki kuma ko wanene, Allah Madaukaki ya ce


Ubangijinka ya hukunta kada ku bauta wa kowa face shi


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma Bautawa Allah kuma kada kuyi masa shirka ko daya


kuma Allah Madaukaki ya ce


Lalle ni, Ni ne Allah. Babu abin bautawa face ni. Sai ka bauta mini, kuma ka tsayar da salla domin tuna ni


kuma wannan hakika cewa Shaidawa babu abin bautawa da gaskiya face Allah ta cika da shi


kishiyar kadaita Allah


menene kadaitarwar Allantaka?


Kishiyarsa shirka kuma shi nau’I biyu ne: mafi girma yana kore shi baki daya da kuma karami yana kore cikarsa.


Shirka mafi girma


menene shirka mafi girma?


Shi ne Bawa ya riki wanin Allah tamka ya dai dai ta shi da Ubangijin Talikai ya dinga sonsa kamar yadda yake son Allah ya kuma dinga jin tsoransa kamar yadda yake tsoran Allah kuma ya dinga fakewa izuwa a gare shi kuma ya dinga rokonsa kuma yana jin tsoransa kuma yana kwadayi a wajansa kuma ya din dogaro da shi ko ya yi masa da’a a cikin sabon Allah ko ya bi shi a bisa abin da ba yardar Ubangiji ba, da kuma wadansunsu


Kuma Madaukaki ya ce


Lalle ne, Allah ba ya gafarta a yi shirka game da shi, kuma yana gafarta abin da yake bayan wannan ga wanda yake so, kuma wanda ya yi shirka da Allah, to lalle ne ya kirkiri zunubi mai girma.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma wanda ya yi shirka da Allah to hakika ya bace bata mai nisa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma wanda ya yi shirka da Allah to hakika Allah ya haramta Aljanna a gare shi kuma makomarsa wuta ce


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yana kamar abin da ya fado daga sama, sa’an nan tsuntsaye su cafe shi, ko iska ta fada da shi a cikin wani wuri mai nisa


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Hakkin Allah a bisa Bawa su bauta masa kada kuma su yi shirkar wani abu da shi kuma hakkin Bayi a bisa Allah ba zai azabtar da wanda bai shirkar wani abu da shi ba


kuma shi yana cikin Bukhari da Muslim, kuma yana dai dai acikin fita daga wannan shirkar ga barin addini wanda ya bayyana da shi kamar kafiran kuraishawa da wasunsu, da kuma wanda ya boye a gare shi kamar munafukai mayaudara wadanda suke bayyana musulunci kuma suke boye kafirci.


Allah ya yi masa Rahama


Lalle ne, munafukai suna a magangara mafi kaskanci daga wuta. Kuma ba za ka sama musu mataimaki ba. Sai wadanda suka tuba, kuma suka gyara , kuma suka nemi fakuwa ga Allah , kuma suka tsarkake addininsu domin Allah,to wadannan suna tare da muminai


Shirka karama


Menene shirka karama?


Shi ne riya mai sauki mai shiga cikin kyautata aiki wanda Allah ake nufi da shi


Allah ya yi masa Rahama


Saboda haka wanda ya kasance yana fatan haduwa da Ubangijinsa,to, sai ya yi aiki na kwarai. Kuma kada ya hada kowa ga bauta wa Ubangijinsa.


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


Mafi tsoran abin da nake tsoro a kanku shirka karama


An tambaye shi a kanta sai ya ce riya


Sannan ya fassara shi da fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata agare shi


Mutum zai tashi yin salla sai ya kawata sallarsa saboda abin da ya gani na daga kallon wani mutum izuwa gare shi


kuma yana daga ciki yin rantsuwa da wanin Allah kamar rantsuwa da iyaye da kishiyoyi da Ka’aba da amana da wasunsu


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:


kada ku rantse da iyayenku maza ko kuma da iyayenku mata ko kuma da kishiyoyi


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:


kada ku ce na rantse da ka’aba sai dai ku ce da Ubangijin ka’aba


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:


kada ku rantse face da Allah


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce


wanda ya rantse da amana to ba shi daga gare mu


:Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce


Wanda ya rantse da wanin Allah to hakika ya kafirta ko ya yi shirka a cikin wata riwayar kuma ya yi shirka


kuma yana daga gare shi fadin Allah ya so ka so. Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya fada ga wanda ya fada masa wannan


ka sanya ni kishiya ga Allah kadai ka ce Allah ya so shi kadai


kuma yana daga ciki fadin ba don Allah da kai ba, da kuma me ke gare ni sai Allah da kai da kuma ni zan shiga don Allah don kuma kai da misalin wancananka,


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi Ya ce:


Kada ku kuskura kuce: Allah ya yarda wane ma ya yarda, kuce: Allah ne ya yarda Sannan kuma wane kuma ya yarda.


Ma’abota ilimi sun ce kuma ya halatta a ce ba don Allah ba sannan wane, kuma bai halatta a ce ba don Allah da wane ba


Menene banbanci tsakanin da da kuma sannan a cikin wadannan lafazan?


Domin cewa hadawa da da yana hukunta hadawa da daidaitawa sai ya kasance wanda ya ce Allah ya so da kai ya hade soyayyar Allah da soyayyar Bawa daidaice da ita sabanin ya yi hadin da sannan wacce take hukuntar da bi, to wanda ya ce Allah ya so, sannan kuma ka so to hakika ya tabbatar da cewa soyayyar Bawa mai bi ce ga soyayyar Allah Madaukaki bata kasancewa face bayanta kamar yadda Madaukaki ya ce


kuma ba za ku so ba face sai Allah ya so


Kuma haka nan sauran


Tauhidin Kadaita Allah


maye kishiyar kataita allah


Shi ne tabbatarwa yankakkiya da cewa Allah Madaukaki Ubangijin komai kuma mamallakinsa kuma mahaliccinsa kuma mai tsara shi kuma mai sarrafa shi ba shi da abokin tarayya a cikin mulkin,


Allah Madaukakin Sarki ya ce:


Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya halicci sammai da kasa, kuma ya sanya duffai da haske


kuma Allah Madaukaki ya ce


Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin Talikai


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ka ce wane ne Ubangijin sammai da kasa? Ka ce Allah. Ka ce Ashe fa kun riki wadansu masoya baicin shi, wadanda ba su mallaka wa kansu wani amfani ba, kuma haka ba su ture wata cuta? Ka ce shin makaho da mai gani suna daidaita? Ko shin, duhu da haske suna daidaita? Ko sun sanya ga Allah wadansu abokan tarayya wadanda suka yi halitta kamar halittarsa, sa’an nan halittar ta yi kama da juna a gare su? Ka ce, Allah ne mai halittar komai, kuma shi ne Makadaici, Marinjayi


kuma Allah Madaukaki ya ce


Allah ne wanda ya halicce ku, sa’an nan ya arzurta ku, sa’an nan ya matar da ku, sa’an nan ya rayar da ku. Ashe daga cikin abubuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga wadannan abubuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ya daukaka bisa ga abin da suke yi na shika


kuma Allah Madaukaki ya ce


Wannan shi ne halittar Allah. To ku nuna mini, mene ne wadannan da ba shi ba suka halitta?


kuma Allah Madaukaki ya ce


Shin an halitta su ne ba daga komai ba, ko kuwa su ne masu yin halitta? Shin sun halitta sammai da kasa ne? A’a ba su dai yi imanin yakini ba


kuma Allah Madaukaki ya ce


Shi ne Ubangijin sammai da kasa da abin da yake tsakaninsu to sai ka bauta masa, kuma ka yi hakuri ga bautarsa. Shin ka san wani takwara a gare shi


kuma Allah Madaukaki ya ce


Da Babu abinda yayi kama da Allah kuma shi ne Mai ji kuma mai gani


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma kace godiya ta tabbata ga Allah wanda Bairiki da ba baida abokin tarayya cikin mulkinsa kuma baida wani majibincin al amarinsa kaskanci baikasance agare shi ba ka girmama ubangijin ka girmamawa.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kukirayi wadan da kuke zatan abubuwan bautawa ne ba Allah ba basu mallaki komaibadaidai da kwayar zarra ba cikin sammai da kassai kuma cikin su basu da wani abokin tarayya kuma bashi da wani mataimaki daga garesu ,ba wani ceto da zai amfani a wajansaba sai dai wanda akayimasa izini harsai


kishiyar kadaita Allahntakar


maye kishiyar kataita Allah


Shi ne Kudurcewa Allah mai girma da Daukaka shi ne mai juya komai na gudanar da Halittu wajen Samar da su ko kashe su ko raya su ko kashe su, ko samar musu da amfanuwa ta Alkairi ko ije Sharri ko wanin hakan daga cikin Ma'anonin Allahntaka, ko kudurce wani wanda zai ja da Allah a cikin wani abu na abubuwan da ya hukunta ko sunayensa ko Sifofinsa Kamar Ilimin Gaibu, da kuma kamar Girma da kuma daukaka, da mai kama da shi.


kuma Allah Madaukaki ya ce


Duk abin da Allah ya bayar ga Mutane na Rahama to babu mai iya hana ta kuma duk abinda ya hana babu wanda ya isa ya bayar da su bayansa kuma shi ne Mabuwayi kuma mai Hikima ya ku Mutane ku tuna ni'amar Allah akanku shin bayan Allah akwai wani mai Azurtaku daga Sama da Kasa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Idan Allah ya sama wata cuta babu mai yayema saishi Allah kuma idan yana nufinka dawani alkhairi babu wanda zaimayal da falalarSa


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kace bakwa ganin abinda kuke bautawa koma bayan Allah in Allah ya nufe ni da Cuta shin akwai mai iya yaye mun Cutar in ba shi ba ko kuma ya Nufeni da Rahama shin akwai wanda ya isa ya tare Rahamar ta sa, kace Allah ya Ishe ni kuma gare shi masu Dogara suke Dogara.


Allah Mai tsarki da daukaka ya ce


Kuma mabudan gaibu suna gurinsa ba wanda ya sansu sai daishi…


kuma Allah Madaukaki ya ce


Ka ce: wanda suke sammai da kassai basu san gaibu ba sai Allah


kuma Allah Madaukaki ya ce


Kuma babu wanda ya isa yakewaye da Iliminsa sai abinda ya so


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Allah Madaukaki ya ce Girman kai Kwajalle na ne kuma Daukaka Mayafi na ne to duk wanda yayi Jayayya dani cikin daya daga cikinsu to zan saka shi a Wuta


Hadisin ya zo a cikin Sahih


Kadaita Allah cikin sunayensa da siffofinsa


menene kishiyar tauhidin sunaye da siffofi?


Hadisin ya zo a cikin Sahih


yana sanin abin da yake tsakanin gabansu da kuma abin da yake bayansu kuma su ba su kewaye sani da shi ba


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


da Babu abinda yayi kama da Allah kuma shi ne Mai ji kuma mai gani


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


Hadisin ya zo a cikin Sahih


kuma acikin Tirmizi daga Ubayyu dan Ka’abu Allah ya yarda da shi cewa mushirikai sun ce da Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi – yana nufin yayin da ya ambaci Allolinsu- ka sifanta mana Ubangijinka sai Allah madaukakin sarki ya saukar da


Kul huwa Allah Ahad “ka ce shi ne Allah Makadaici”Allah wanda ake nufinsa da bukatakuma Assamad shi ne wanda bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba


Domin cewa shi babu wani abu da za’a Haifa face sai ya mutu kuma babu wani abu da zai mutu face an gaje shi kuma lalle Allah Madaukakin sarki ba zai mutu ba kuma ba za’a gaje shi ba


kuma babu daya da ya kasance tamka a gare shi


Allah ya ce babu wanda ya kasance mai kama da shi ko kuma kwatankwacinsa, kuma babu wani abu da yayi tamkarsa.


Dalilin sunayansa kyawawa daga Alkur’ani da kuma sunna


Menene dalilin sunayansa kyawawa daga Alkur’ani da sunna?


Fadin Allah maigirma da Daukaka:


Kuma Allah yana da sunaye masu kyau sai ku roke shi da su ku bar wadanda suke yin ilhadi a cikin sunayensa


Kuma tsarki ya tabbatar masa ya ce


Ka ce, ku kirayi Allah ko kuwa ku kirayi Mai rahama. Kowanne kuka kira, to yana da sunaye masu kyau


Fadin Allah maigirma da Daukaka:


Allah babu abin bautawa face shi. Yana da sunaye mafiya kyau.


Da wasun su daga Ayoyi.


Sai yace da shi haqiqa Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi


lalle Allah yana da sunaye casa’in da tara duk wanda ya kiyayesu zai shiga Aljanna


kuma shi yana cikin Bukhari. Kuma Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce


ina rokanka ya Allah da kowane suna naka, wanda ka ambaci kanka da shi, ko ka saukar das hi a cikin littafinka, ko ka sanar das hi da wani daga cikin halittarka, ko ka kebance kanka da saninsa a cikin ilimin fake dake wurinka daka sanya Alkur’ani mai girma ya zama kaka ga zuciyata


Misalin sunayen Allah masu kyau daga Alkur’ani


Menene misalin sunayen Allah mafiya kyau daga Alkur’ani?


Misalin faxin Allah Madaukakin Sarki:


Lalle Allah ya kasance Madaukaki Mai girma


Lalle Allah ya kasance Mai tausasawa Mai labartawa.


Lalle Allah ya kasance Masani Mai iko


Lalle Allah ya kasance Mai ji Mai gani


Lalle Allah ya kasance Mabuwayi Mai hikima


Lalle Allah ya kasance Mai gafara Mai jin kai


Lalle shi ne Mai tausayi Mai jin kai gare su.


kuma Allah Mawadaci ne Mai hakuri


Lalle shi abin godewa ne, Mai girma


Lalle Ubangijina a bisa dukkan komai Matsari ne


Lalle Ubangijina Makusanci ne Mai karbawa


Lalle Allah ya kasance Mai dako ne a kanku


kuma Allah ya isa ya zama Wakili


kuma Allah ya isa Mai lissafi


Kuma Allah ya kasance a kan dukkan komai Mai kayyade lokaci


Lalle shi a bisa dukkan komai Mai shaida ne


Lalle shi ga dukkan komai Mai kewayewa ne


kuma Allah Madaukaki ya ce


Allah babu wani abin bautawa sai shi Rayayye Mai tsayuwa da komai


kuma Allah Madaukaki ya ce


Shi ne na farko, Na karshe Bayyananne, Boyayye, kuma shi Masani ne ga dukkan komai


Allah Madaukakin Sarki yana cewa:


Shi ne Allah wanda babu wani abin bautawa face shi, Masanin fake da bayyane shi ne Mai rahama Mai in kai. Shi ne Allah wanda babu abin bautawa face shi, Mai mulki Mai tsarki, Aminci, Mai amintarwa, Mai tsarewa, Mabuwayi, Mai tilastawa, Mai nuna isa. Tsarki ya tabbata a gare shi daga abin da suke yin a shirka da shi. Shi ne Allah Mai halitta, Mai ginawa, Mai surantawa, yana da sunaye masu kyau


Da wasun su daga Ayoyi.


Misalin sunayen Allah masu kyau daga Sunnah


Menene misalin sunayen Allah mafiya kyau daga Sunnah?


Faxar Manzon Allah tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ta gabata


babu wani abin bautawa face Allah Mai girma Mai hakuri babu wani abin bautawa face Allah Ubangijin Al’arshi mai girma, babu wani abin bautawa da gaskiya face Allah Ubangijin sammai kuma Ubangijin kasa kuma Ubangijin Al’arshi mai yawan baiwa


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


ya Rayayye ya Mai tsayuwa da komai ya Ma’abocin daukaka da girma ya Makagin sammai da kasa


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


da sunan Allah wanda da sunansa wani abu a sama ko a kasa baya cutarwa. Kuma shi ne Mai ji Masani


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


ya Ubangiji masanin fake da bayyane Mahaliccin sammai da kasa Ubangijin dukkan komai kuma mamallakinsa


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


ya Allah Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al’arshi mai girma ya Ubangijinmu kuma Ubangijin dukkan komai mai tsaga kwayar hatsi da ta dabino wanda ya saukar da Attaura da linjila da Alkur’ani ina neman tsarinka daga dukkan sharrin mai sharri wanda kai kake rike da makwarkwadarsa.kai ne na farko babu wani abu kafin ka, kuma kai ne na karshe babu wani abu bayanka, kuma kai ne bayyananne babu komai birbishinka kuma kai ne boyayye babu wani abu da yake boyuwa a gareka


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


ya Allah godiya ta tabbata a gareka kai ne hasken sammai da kasa da kuma abin da yake cikinsu kuma godiya ta tabbata a gareka kai ne mai tsai da sammai da kasa da abin da yake cikinsu


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


ya Allah ina rokanka, saboda ni na shaida cewa kai ne Allah, babu abin bautawa da gaskiya sai kai,kai kadai tal,wanda ake nufa da dukkan bukatu, wanda bai Haifa ba kuma ba’a haife shi ba, kuma babu wani tamka a gare shi


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Ya Mai juyar da zukata


Da wasun haka masu yawa:


Da wadansun wadannan masu yawa


a bisa nau’i nawa sunayen Allah mafiya kyau suke shiryarwa da shi?


ita tana shiryarwa ne a bisa nau’ika uku: shiryarwarta a bisa zati a dacewa, da kuma shiryarwarta a bisa siffofi ababan cirowa daga gareta a kunshe, da kuma shiryarwarta a bisa siffofi wacce ba’a ciro daga gareta ba a lazimtawa


Menene misalin wancananka?


Misalin wancananka: sunansa Madaukaki Mai rahama Mai jin kai yana shiryarwa a bisa zatin abin Ambato shi ne Allah Mai girma da daukaka a dacewa da kuma a bisa siffa abar cirowa daga gareta ita ce Rahama a kunshe kuma a bisa watanta daga siffofi wacce ba’a cira daga gareta ba kamar Rayuwa da iko a lazimtawaHakanan kuma sauran sunayensa,to wannan sabanin ababan halitta ne domin akan ambaci wani da mai hikima alhali kuma jahili ne ko kuma mai hukunci alhali kuma Azzalumi ne ko kuma


mai isa alhali makaskanci ne ko kuma mai alfarma alhali kuma mara alfarma ne ko kuma mai karamci alhali kuma mara karamci ne ko kuma managarci alhali kuma ba managarci ba ne ko kuma mai arziki alhali kuma matsiyaci ne ko a kira shi da Zaki ko kuma mai daci amma kuma ba haka yake ba, tsarki ya tabbata ga Allah da kuma gode masa shi kamar yadda ya siffanta kansa yake kuma sama da yadda halittarsa suka siffanta shi


Shiryarwar sunayensa mafiya kyau ta fuskar kunsa


a bisa kaso nawa shiryarwar sunayen Allah mafiya kyau suka kasu ta fuskar kunsa?


ita ta kasu kaso hudu:


Shi ne Allah Mahalicci Mai ginawa Mai surantawa


Shi ne Allah Mahalicci Mai ginawa Mai surantawa


da kuma makamancin wannan, kuma bai taba zuwa mai bi ga waninsa ba daga sunayen


Na biyu: abin da ya kunshi siffar zatin Allah Mai girma da daukaka kamar sunansa Mai ji wanda ya kunshi jinsa mayalwaci ga dukkan saututtuka, daidai ne a gurinsa boyayyiyarta da bayyananniyarta kuma sunansa Mai gani wanda ya kunshi ganinsa mai zarcewa a cikin dukkan gannai daidai ne zurfafanta da mabayyananta kuma sunansa Masani wanda ya kunshi saninsa mai kewayewa wanda


Masanin gaibi gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare shi a cikin sammai kuma bata nisanta a cikin qasa kuma babu mafi girma face yana a cikin Littafi bayyananne


Gwargwadon zarra bat a nisanta daga gare shi a cikin sammai, kuma bat a nisanta a cikin kasa, kuma mafi karanci daga wancan kuma babu mafi girma


kuma sunansa Mai iko wanda ya kunshi ikonsa a bisa dukkan komai a samarwa da rasantarwa da wasun wadannan


Na uku: abin da ya kunshi siffar aikin Allah kamar Mahalicci Mai azurtawa Mai ginawa Mai surantawa da wadansun wadannan.


Na hudu: abin da ya kunshi tsarkinsa Madaukaki daga dukkan tawaya kamar sunansa Mai tsarki, Mai aminci.


Kaso nawa sunayen mafiya kyau ta fuskar sakinsu a bisa Allah Mai girma da daukaka suka kasu?


daga cikinta akwai wanda ake sakinsa a bisa Allah kadai ko tare da waninsa kuma shi ne wanda ya kunshi siffar cika ta kowace fuska kamar Rayayye Mai tsayuwa da kome Makadaici Abin nufi da bukata da makamantansu, kuma yana daga cikinta abin da ba’a sakinsa a bisa Allah face tare da mukabilinsa shi ne wanda idan ya kadaita zai wahamtar da tawaya kamar Mai cutarwa Mai amfanarwa, Mai kaskantarwa da Mai daukakawa da Mai bayarwa da Mai hanawa da Mai buwayarwa da Mai kaskantarwa da makamancin wadan nan To bai halatta sakin Mai cutarwa ko kaskantarwa ko hanawa kowanne a bisa kadaituwarsa ba, ba’a taba sakin wani abu daga gare taba a cikin wahayi hakanan babu a cikin littafi babu ma a cikin sunna, kuma yana daga ciki sunansa Madaukaki Mai ramuwa ba’a sake shi a cikin Alkur’ani ba face tare da muta’allikinsa kamar fadinsa Madaukaki


Lalle mu masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi


ko da raba Ma’aboci a sifa abar cirowa daga gare ta kamar fadinsa Madaukakin sarki


kuma Allah shi ne Mabuwayi Ma’abocin ramuwa


Misalin siffofin zati daga Alkur’ani


ya gabata cewa siffofin Allah Madaukaki akwai na zati da kuma na aiki to menene misalign siffofin zatin daga Alkur’ani?


Misalin faxin Allah Maxaukakin Sarki:


Misalin fadinsa Madaukakin sarki


Kowanne abu mai halaka ne face Fuskarsa


Kuma Fuskar Ubangijinka Mai girman jalala da karamci ita ce take


Kuma domin a rike ka da kyau a kan idoNa


Menene ya yi ganinsa da jinsa


Hakika nai ina tare da ku ina ji kuma ina gani


yana sanin abin da yake tsakanin gabansu da kuma abin da yake bayansu kuma su ba su kewaye sani da shi ba


Kuma Allah yayi magana da Musa Magana sosai


kuma a lokacin da Ubangijinka ya kira Musa kajewa mutanan nan azzalumai


kuma Ubangijinsu ya kira su shin ban hana ku ba daga waccan itaciya,


kuma ranar da yake kiran su, sa’annan ya ce, mene ne kuka karba wa manzanninku


da kuma wadansunsu.


? Misalin siffofin zati daga Alkur’ani


Menene misalin siffofin zati daga sunna?


Kamar fadinsa tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi


Hijabinsa haske ne da zai yaye shi da jalalar Fuskarsa ta kone abin da ganinsa ya tuke a gare shi na daga halittarsa


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


Daman Allah a cike take,ciyarwa bazata tauyeta ba mai yawan baiwa ne dare da rana ba kwa ganin abin day a ciyar tun lokacin day a halicci sammai da kasa, cewa shi babu abin da zai tauye abin da ke cikin damansa kuma Al’arshinsa yana kan ruwa kuma a daya hannun nasa baiwa take ko kuma rikewa yana daukakawa kuma yana kaskantarwa


Kuma faxin Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi a cikin Hadisin Dujal


Lalle Allah ba zai buya daga gare ku ba cewa shi ba mai Ido daya ba ne


sai yayi nuni da hannunsa izuwa idonuwansa, haka kuma a cikin hadisin istihara


Ya Allah lalle ni ina neman zabinka da iliminka ina neman iyawarka da ikonka kuma ina rokanka daga falalarka mai girma domin cewa kai kake da iko ni bani da iko kuma kai mka sani ni bani da wani sani kuma kai ne Masanin abubuwan da suke fake


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


cewa ku ba kurma kuke kira ba ko kuma fakakke kuna kiran Maiji Maigani Makusanci


Kuma Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce:


‘’Idan Allah Madaukakin Sarki ya yi niyyar wahayi kan wani abu sai yayi magana da wahayi‘’


Kuma a cikin hadisinTashi daga Kabari


Allah Madaukakin sarki zai ce: Ya Adamu sai ya ce amsawarka


da kuma hadisan zancan Allah ga bayinsa a cikin matsaya, da kuma maganarsa ga ‘yan Aljanna da wadansu wadannan wanda baza su kididdigu ba.


Misalin siffofin aiyuka daga Alkur’ani



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH