gari suka kasa biyan bashin, sai a xebo wani abu daga cikin
zunuban wanda aka zaluntar a jibga wa azzalumin. Qarshe kuma a
iza qeyyarsa zuwa wuta.
b) Tauye Haqqin Ma’aikaci: Wasu uwayen gida kuma, xabi’arsu ita
ce, tauye haqqin ma’aikaci daga haqiqanin abin da aka yi
yarjejeniya da shi tun asali. Irin waxannan mutane na da
mummunan tanadi a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala don Ya
ce:
Ma’ana:
“Bone ya tabbata ga masu tauye haqqi” (33:1).
Misalin wannan baqar xabi’a, shi ne abin da wasu masu hannu da
shuni kan yi na xauko ma’aikata daga garuruwansu na asali, su kawo su
birni da yarjejeniyar biyansu wani adadi na kuxi duk bayan wani
qayyadajjen Lokaci. Amma kuma da an fara tafiya, aiki ya fara nisa, ya
riga ya zarge wuyansu, sai ya lallava ya canza waccan yarjejeniya, ya
tauye haqqin nasu na asali. Su kuma saboda rashin makarkata ko wata
takamammar hujja a hannunsu, dole sai su haqura, a yi ta sha’ani wai an
cuci baqauye, in ji xan birni!. Iyakar abin da irin waxannan ma’aikata ke
iya yi shi ne; Allah Ya isa.
Babbar illar da ke cikin irin wannan nau’i na zalunci ita ce, idan
mai irin wannan xabi’a musulmi ne, to zai tozarta musulunci a idon irin
waxannan ma’aikata har ya cire masu sha’awar addini idan su ba
musulmi ba ne. Duk mai irin wannan xabi’a ya sani yana da zunubi a
wurin Allah.
83
c) Niqe ma’aikaci: Wasu uwayen gidan kuma, xabi’arsu ita ce niqe
ma’aikaci. Ta hanyar tsawaita lokacin aikin nasa, ko qara masa
wani aikin ba kuma tare da yayi masa wata ‘yar toliya ba a kan
jingayarsa ta asali (Over time).
d) Jinkirta Haqqin Ma’aikaci: Wasu uwayen gidan kuma, tasu xabi’ar
ita ce, jinkirta biyan haqqin ma’aikaci. Wani Lokacin ma sai
ma’aikacin ya yi kamar yana yi, ta hanyar faxi tashi, hargowa da
qorafi. Wani lokacin ma sai ya nemi ceton alqali. Manufar irin
waxannan mutane ita ce su gajiyar da ma’aikacin ya fita batun
haqqin nasa dole, su canye ko su juya shi ta hanyar Riba zuwa
wani lokaci, kafin su ba shi. Alhali kuwa irin waxannan ma’aikata
ba su da abin da za su aika wa iyalinsu da suka baro gida, suka
taho birni don nema masu abinci. Ba ma wannan ba, ko abin da za
su sayi abin karin kumallo kullum ba su da. Bone ya tabbata kan
irin waxannan azzalumai a shu’umar ranar nan mai zuwa!
Abu Hurairata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce: “Allah Ya ce: zan yi fito na fito da wasu mutane uku a
ranar qiyama: 1) Mutumin da ya rantse da sunana kuma ya sava, 2)
Mutumin da ya sayar da xa a matsayin bawa, ya kuma sa kuxin aljihu da,
3) Mutumin da ya sa wani aiki ya kuma qi biyansa jingarsa” (Bukhari).
RASHIN ADALCI TSAKANIN ‘YA’YA
Wani abu kuma da shari’ar musulumci ta haramta, kuma wasu
mutane suka yi biris da shi, shi ne Rashin Adalci tsakanin ‘ya’ya. Ta
hanyar ba wa wani daga cikinsu abin da basu ba wani ko saura ba.
Wanda hakan ke tabbatar da sun fifita shi a kan saura.
84
Wasu malamai nagartattu, na ganin cewa, idan mahaifi na da wani
qwaqqwaran dalili na yin haka, to babu haramci. Kamar xan da ya fifita
xin ya kasance ya kevantu da buqatar abin, saboda rashin lafiyar da yake
fama da ita, ko wani bashi da ake bin sa, ko ya yi masa kyautar ne a
matsayin goron qwazon hardace alqur’ani da ya yi, ko wani aiki da ya yi
qoqarin samar wa kansa. Ko saboda yawan iyalinsa, ko shagala da neman
karatu da ya yi. Ko dai wani dalili mai kama da waxannan.
Amma kuma duk da haka sun ce, ana so mahaifin ya qulla niyya a
ransa, ta ba wa wani daga cikin sauran ‘ya’yan irin wancan abu, a duk
lokacin da xaya daga cikin irin waxancan buqatoci suka kama shi. Domin
kuwa qa’idar ta asali ita ce abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke
cewa;
Ma’ana:
Ku yi adalci, shi ne mafi kusa ga taqawa (5:8)
Babban abin da ke tabbatar da rashin halaccin irin wannan xabi’a
shi ne, abin da Nu’umanu xan Bashiru Raliyallahu Anhu ya Riwaito daga
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bayan mahaifinsa ya taho da
shi wurin Manzon, inda shi mahaifin na Nu’umanu ya ce wa Manzon;
“Na ba wa xan nan nawa wani bawa da nake da shi”. Sai Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ina fatar ka ba wa gaba xayan
‘ya’yanka irinsa”. Ya karva masa da cewa: “A’a”. Daga nan sai Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa:” To, ka fasa wannan
kyauta (Bukhari: 5/211).
A wata riwaya kuma ce masa Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya yi; “Ka ji tsoron Allah ka kuma yi adalci tsakanin
85
‘ya’yanka”. Daga nan shi kuma sai ya je ya tayar da waccan kyauta.
(Fathul Bari 5/211). A wata riwaya ta uku kuma, cewa aka yi Manzon
Allah ya ce masa: “Kar ka nemi in zama shedunka a kan wannan kyauta.
Don ba zan zama sheda a kan zalunci ba” (Muslim: 3/1243).
Babu laifi a shari’a a ba wa xa namiji ninkin abin da aka ba wa
xiya mace, kamar yadda hukuncin gado yake, inji Imamu Ahmad
Rahimahullahu. (Abu Dawuda: 204).
Wannan ita ce qai’da ta shari’a. Amma sai ga shi a zamaninmu na
yau a wasu gidaje, saboda rashin tsoron Allah, uwaye maza na fifita wasu
‘ya’ya nasu a kan wasu a cikin kyauta. Sun kuma kasa gane cewa, irin
wannan banbanci da suke nunawa tsakanin ‘ya’yan na iya haifar da
hassada da qiyayya da gaba a tsakaninsu.
Wasu uwayen kan nuna irin wannan banbanci ne ta hanyar yi wa
wani daga cikin ‘ya’yan nasu wata kyauta, wai don kawai ya yi kama da
danginsa na wajen uba a halitta. Ya kuma ba wa wanda ya ya yi kama da
dangin uwarsa qasa ga abin da ya ba na farko. Ko kuma ya ba wa ‘ya’yan
wata mata fiye da abin da ya ba na wata. Ko ya xauki ‘ya’yan wata ya
saka makarantar kuxi, ya bar na saura a makarantun gwamnati. Wannan a
qarshe ko shakka babu qaiqayi zai koma wa masheqiya. Don za a wayi
gari a mafi yawan lokuta ‘ya’yan da ya tozarta su xauke shi ba bakin
komai ba, ko har ma can gaba idan Allah Ya xaukaka su, su ma su
walaqanta shi. Tabbas haka na iya faruwa, don Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce: “Hala ba ku son su ma ‘ya’yan naku su girmama
ku?” (Ahmad; 4/269).
86
ROQO BA BUKATA
Sahlu xan Hanzalata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya roqi mutane
kuxi alhali yana da abin da ke isar sa buqata, to yana roqar ma kansa
garwashin wuta ne kawai”. Sai sahabbai suka tambayi Manzon; “Mene
ne miqidarin abin da za a ce ya ishi mutum buqata har ya hana shi roqon
qari? Sai ya karva masu da cewa: “Idan ya mallaki abin da zai ci abincin
rana da na dare” (Abu dawuda: 2/281).
Haka kuma xan mas’udu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa,
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke roqon
mutane kuxi alhali yana da abinda ke isar sa biyan buqata, zai tashi Ranar
qiyama fuskarsa da farxe- farxe” (Ahmad; 1/388).
Duk da irin wannan tanadi da shari’ah ta yi wa mai roqo ba da
wata buqata ba. Wasu mutane a yau, sun sami sandar roqe-roqe har ma a
masallaci. Inda zasu je su dami mutanen da ke sallah da salati babu li
babu la. Su kan yi haka ne kuma ta hanyar shimfixa koke- koke na qarya.
Wasu daga cikin su ma har takardun qarya suke yawo da su a masallatan
sana damun mutane da dogon turanci. Wasu kuma iyalansu suke
rarrabawa a masallatan don gudanar da wannan mugunyar sana’a. Ba su
wannan masallaci ba su wancan. Alhali kuwa wasu daga cikinsu Allah ne
kawai ya san iyakar abin da suka mallaka. Sai kuwa idan sun mutu, a yi
ta jin sun bar kaza sun bar kaza. Alhali a lokacin da suke waxancan roqeroqe
suna rufe damar wasu mutane ne, da ba su mallaki komai ba, amma
tsoron Allah da tsaron mutunci sun hana su fitowa su roqa. Mutane kuma
zaton suke yi sun wadata. Qarshe sai a xauki abin da ya kamata a ba su a
ba waxannan jeqaqqin.
87
TURUN BASHI
Haqqin wani a hannun wani nada matuqar girma a wurin Allah. Ta
yadda har ta kai da mutum zai tava wani haqqi na Allah, ya kuma tuba,
Allah na iya yafe masa. Amma da zai tava haqqin wani mutum
xan’uwansa dole ne ya mayar masa da shi kafin ranar da Naira da Kobo
ba su da wani tasiri face kyakkawan aikin mutum.
Allah Ta’ala ba ya yafe wa wani haqqin wani. Saboda haka Yace:
Ma’ana:
Haqiqa Allah Yana umurnin ku ku bayar da amanoni
zuwa ga masu su (4:58).
Yawan cin bashi ba da niyyar biya ba, na xaya daga cikin
matsalolin da suka zama ruwan dare a cikin al’ummarmu a yau. Irin
wannan bashi ma wasu kan karve shi ba don suna da wata buqata ta gari
ba. Sai don kawai su faxaxa sana’o’insu, ko don su yi takarar sayen
motocin shiga ko kayan alatu ko wasu qyale-qyalin rayuwa da wasu
takwarorinsu. Wasu sukan mallaki irin waxannan kayayaki ne, ta hanyar
qulla yarjejeniyar biyansu kaxan – kaxan. A qarshe kuma sai su qare
cikin haramiya dumu- dumu.
Irin wannan xabi’a ta cin bashi a kai- akai ba kuma da niyyar biya
ba, na sa wasu mutane zama turayen bashi, wanda kuma qarshe yakan
haifar da talauci da kariyar arziqi. Don kauce wa faxawa cikin irin
wannan matsala ne, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
gargaxi Al’umarsa da cewa: “Duk wanda ya karvi kuxin mutane a
matsayin bashi, da niyyar biya Allah zai ba shi ikon biya, amma wanda
88
ya karva ba da niyyar biya ba sai don ya kaxas, Allah zai kaxas da shi’
(Bukhari: 5/54).
Da yawan mutane a yau sun xauki wannan matsala ba bakin komai
ba. Alhali kuwa babbar matsala ce a wurin Allah. Wadda har ta kai ko
shahidi, tattare da irin ladar da yake da ita, ba za a yafe masa bashin
mutane da ke kansa ba. Tabbacin wannan magana shi ne hadisin da ke
cewa: “Tsarki ya tabbata ga Allah. Don bai sanya wani tsanani a cikin
addini ba, sai a cikin sha’anin bashi. Ina rantsuwa da wanda raina yake
hannunsa, da za a kashe mutum a wurin yaqi, a raya shi a kuma sake
kashe shi, a kuma sake raya shi a kuma sake kashe shi, to ba zai shiga
aljanna ba matuqar ana bin sa bashi, sai an biya shi. (Nasa’i: 7/314).
Ya kamata duk wanda ke irin wannan xabi’a ya tuba, kafin wuri ya
qure masa.
CIN DUKIYAR HARAM
Da yawa mutanen da tsoron Allah ya yi wa kaxan a zukata, ba su
damu da ta ko wace hanya za su sami kuxi ba, balle wadda za su kasha
su a cikin ta. Abin da kawai ya dame su, shi ne yadda ajiyarsu ta banki za
ta qara kauri, koda ta hanyar haramiya ce.
Saboda cika wannan guri, sai su shiga wawure kuxaxen bayin
Allah da suke amana a hannun su. Wasu kuma su kama ‘yan sace-sace ko
fashi da makami ko damfara ko haramtattar sana’a kamar Riba, ko cin
kuxin marayu, ko bokanci. Waxansu kuma sukan kama ‘yan
tabanjamanci ko waqa, ko tatsar taskar musulmi, ko tava kayan mutane,
ko yaudararsu ta hanyar karvar kayan da qarfi, ko tsawwala wa kayan da
suke sayarwa farashi. A yayin da wasu kuma ke tsira sana’ar baracebarace
ba da wani dalili ba. Ga su nan dai.
89
Da kuxin da waxannan mutane suka samu ta waxannan hanyoyi za
su sayi abinci ko tufafi da ababen hawa, ko su gina gidaje, ko su kama
haya, wasu ma har su sayi kayan alatu su zuba a gidajen. Alhali kuwa
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk tsokar jikin da ta
ginu da haramun wuta ce mafi cancanta da ita” (Xabarani: 19/136).
Kafin haka kuma a Ranar qiyama, Allah zai tambayi ko wane
mutum a kan yadda ya sami dukiyarsa da yadda ya kashe ta. Ta haka sai
kowa ya haxu da sakamakonsa daidai da aikinsa.
Da wannan muke kiran duk wanda ya san cewa akwai wata dukiya
hannunsa ta haram ya yi gaggawar rabuwa da ita, ya mayar wa mai ita
idan ya san shi, ya kuma nemi gafarar Allah. Kafin Ranar da kuxi ba su
da wani amfani sai dai aikin qwarai.
SHAN BARASA
Allah Maxaukakin Sarki na cewa a cikin Littafinsa mai tsaki:
Ma’ana:
Ya ku waxanda suka yi Imani! Haqiqa giya da caca da reful
da kiban quri’a, duk qazanta ce kawai daga cikin aikin
shaixan, sai ku nisance ta wa la’alla ku ce nasara” (5:90).
Wannan umurni da Buwayayyen Sarki Ya bayar na nisantar
waxannan abubuwa, da suka haxa da shan Giya, Babban dalili ne da ke
tabbatar da kasancewar gaba xayan haram. Kuma kawo giya da Sarkin ya
90
yi tare da gumaka, kafaxa- da kafaxa ya tabbatar cewa, ita ma haramun
ce.
Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qara
tabbatar da haramcin shan giya, a wani hadisi da Jabir ya riwaito, inda ya
ce: “Allah Ya yi alkawalin shayar da duk wanda ya sha giya dagwalon
khibal. Sahabbai suka ce, “Ya Manzon Allah mene ne dagwalon khibal?
Sai ya ce: zufan ‘yan wuta ko rowan qurajensu! (Muslim: 3/1587). Haka
kuma xan Abbas ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce: “Duk wanda ya mutu yana mashayi, zai haxu da Allah
a matsayin mai bautar gumaka” (Xabarani 12/45).
Yawan sunayen giya da banbancin kamfunan da suka sana’anta ta
ba zai tada ita daga haramci ba. Daman dai Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce: “Wasu mutane daga cikin al’ummata zasu sha
giya suna kiran ta da wani suna” (Ahmad: 5/352). Kiranta da sunan
“Tsime” da “Burkutu” da makamanta su idan ya zama da nufin yaudara
to, mashayan ne ke yaudarar kansu. Kamar yadda Allah ya ce:
Ma’ana:
Suna (tunanin sun) yaudari Allah da waxanda suka yi imani,
alhali ba su yaudarar kowa sai kan su, kuma ba su
sakankancewa!” (2:9)
Shari’ar musulunci ta yi matuqar xaukar mataki a kan wannan
matsala ta giya da shan ta. Ta kuma warware zare da abawarta don kada
wani kokwanto ko tantama su shiga ga mutum a kai. Dubi abin da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa: “Duk abin da ke sa
maye giya ne, kuma ko wace irin giya haramun ce” (muslim: 3/1587).
91
Ka ga kenan wannan magana ta ma’aiki ta gama tabbatar mana da
cewa, duk abin da ke dagula hankali da tunani idan an sha shi to giya ne,
komai qanqantarsa. Kuma ko da an bashi sunaye daban daban, komai
yawansu dai, giya ce. Hukuncinta ko sananne ne.
A qarshe ma dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
gaya wa mashaya giya farar gaskiya mai xaci, inda ya ce: “Duk wanda ya
sha giya har ta bugar da shi, ba za a karvi sallarsa ba har kwana arba’in.
Idan kuma ya mutu a cikin wannan hali makomarsa ita ce wuta. Idan
kuma ya tuba Allah zai gafarta masa. In ya koma sha har ya yi maye,
kuma za a sake qin karvar sallarsa ta kwana arba’in. Idan kuma ya mutu a
wannan hali, wannan karon ma wuta ya yi. Amma idan aka yi sa’a ya
tuba to, Allah zai yafe masa. Haka kuma da zai sake sha ya kuma sake
buguwa, karo na uku, nan ma za a ba sallarsa baya har tsawon kwana
arba’in. Da kuma zai kwanta dama a wannan hali, ba abin da zai hana shi
shiga wuta. Da kuma zai tuba Allah zai karvi tubansa.
Amma da zai sake sha karo na huxu to, Allah Ya yi alkawalin
shayar da shi dagwalon khibal a Ranar qiyama. Sahabbai suka ce: Ya
Manzon Allah, mene ne dagwalon khibal? Ya ce: “Shi ne surkamin ‘yan
wuta” (Ibn majah: 3377).
AMFANI DA KASAKEN ZINARI DA AZURFA
Da yawa ka kan samu kasake da kwanoni na zinari ko azurfa, ko
waxanda aka yi wa ado da xayansu a gidajen masu hannu da shuni. Daxa
a manyan hotel- hotel nan ne uwa uba.
Irin waxannan kasake da ake qawatawa da wasu zane zane sun
yawaita a wasu qasashe na musulmi, saboda amfani da su da ake yi a
matsayin kyautuka na masamman. Wasu mutane da Allah bai ba ikon
92
mallakar irin waxannan kayayyaki a gidajensu ba, sai ka taras sun faxa
cikin wannan haramiya don za a gayyace su wasu gidaje don wata
hidima, qarshe a kawo masu abinci cikin irinsu.
Amfani da irin waxannan kayayyaki a irin waxannan hanyoyi
haramun ne a musulunci. Saboda haka ne Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya gargaxi dukan musulmi daga amfani da su. Ummu
Salamata ta riwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa:
“Duk wanda ke ci ko shan wani abu a cikin kaskon zinari ko azurfa yana
jefa garwashin wuta ne a cikin cikinsa” (Muslim: 3/1634).
Wannan haramci ya shafi duk wani nau’i na ababen amfani da aka
qera da zinari ko azurfa. Kamar Farantai, cokula masu yatsu, da marasa
yatsu, wuqaqe, tire- tire da makamantan su. Haka kuma ‘yan adikokin
alawa, irin waxanda ake bayarwa a matsayin kyautar alfarma ga baqi ko
amare da angwaye. Duk amfani da irin waxannan abubuwa haramun ne,
matuqar da zinari ko azurfa aka qera su.
Wasu mutane na iya cewa “To har da mu da ke kwalliya da su
kawai a cikin gilasai, abin ya shafa?” Eh, lalle ya shafe ku. Abin da kuke
yi xin nan bai halasta ba. Domin kuwa idan dai ana yalla ido a gan su, to
lalle wata rana sai an yi amfani da su. Malam Bin Baz ne ya faxi haka.
SHEDAR ZUR
Allah maxaukakin Sarki Ya ce:
Ma’ana:
93
Saboda haka ku nisanci qazantar gumaka, kuma ku nisanci
Zhedar Zur. Kuna masu tsayuwa ga gaskiya domin Allah, ba
masu yin shirka da Shi ba” (22:30-31).
Haka kuma Abdurrahaman xan Abubakar Raliyallahu Anhu ya
riwaito cewa, mahaifinsa ya ce: Wata rana muna zaune tare da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya ce : Kuna so in ba ku labarin
manya- manyan zunubbai? Ya ko maimaita tambayar har sau uku.
Sa’annan ya amsa masu da cewa: 1) haxa Allah da wani a cikin bauta, 2)
qin uwaye… Manzon Allah yana gincire sai ya tashi zaune. Sannan ya
ce: 3) Da kuma Shedar Zur. Mai riwayar (Sayyidina Abubakar) ya ce,
Annabi ya yi ta maimaita na ukun nan har muka yi sauraren ya dasa aya.”
(Bukhari: 5/261)
Gargaxi da jan kunnen mutane a kan su nisanci Shedar Zur abu ne
da shari’a ta faxa ta maimaita ta kuma nanata, saboda irin yadda mutane
ba su xauki yin hakan bakin komai ba. Duk da yake kuma an fahimci
cewa qiyayya da gaba ne kan sa wasu mutane faxa wa wannan haramiya
don fashe haushinsu akan wani wanda suke adawa da shi. Amma kuma
hakan ba ya zama hujja gare su. Musamman idan aka yi la’akari da irin
mummunan sakamakon da tagarar ke haifarwa wanda ya haxa da; i) Sa
mutane da yawa hasarar wasu haqqoqa nasu, ii) jefa wasu mutane da
yawa cikin baqar musiba ba su ji ba su gani ba, iii) share wa wasu mutane
da yawa hanyar samu da mallakar abin da ba su cancanta ba. Da
sauransu.
Wani babban misalin da ke tabbatar da irin yadda mutane ba su
xauki Shedar Zur bakin komai ba shi ne abin da kan faru a wasu
kotunanmu a yau. Nan take wani zai ce wa wani “Zo ka shede ni, ni
kuma in shede ka”. Alhali kuwa a wannan lokacin ne suka fara haxuwa.
94
Ka ga kenan ko wanensu zai shedi xaya a kan abin da bai san
komai game da shi ba, balle ya iya bayanin yadda ya faru dalla dalla.
Wato kamar ya shede shi a kan mallakar wani fili ko gida, ko ya wanke
shi daga wani bashi, alhali bai ko tava ganinshi ba kafin yau a kotu.
Turqashi!
Wannan ita ce tantagaryar qarya da Shedar Zur. Domin kuwa
Allah Subhanahu Wa Ta’ala cewa ya yi a yi sheda a kan abin da aka
sani:
Ma’ana:
Kuma bamu yi sheda ba face da abin da muka sani. Kuma bamu
kasance masu kiyaye aibi ba. (12:38)
SAURAREN KIXA
Kaxe- kaxe da waqe- waqe a idon shari’ar musulunci na xauke
hankalin masu yin su da sauraren su ne kawai daga tafarkin Allah
Subhanahu Wa Ta’ala zuwa ga na shexan. A kan haka ne xan Mas’udu
Raliyallahu Anhu yake rantsuwa da Allah Subhanahu Wa Ta’ala kan
cewa ayar nan da ke cewa:
Ma’ana:
Kuma daga cikin mutane akwai wanda ke sayen tatsuniyoyi
domin ya vatar da mutane daga hanyar Allah” (31;6).
95
Ya ce, wannan ayar tana magana ne a kan waqe- waqe. Haka kuma
Abu Amiru da Abu Maliki al- Ash’ari Raliyallahu Anhuma sun qarfafa
haramcin kixa da saurarensa, da hadisin da Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Za a samu wasu mutane a cikin
al’ummata da ke halasta zina da tufafin al-Hariri da giya da kaxe-kaxe”
(Bukhari 10/51). Haka kuma Anas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa,
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Nan gaba za a sami
girgizar qasa da aman duwatsu da shafe mutane su koma dabbobi a cikin
al’ummata, sakamakon fara shan giya da sauraren waqe-waqen mata da
kaxe-kaxen da za ayi” (Silsilah Sahiha 2203).
Ka ga kai tsaye Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya
haramta kaxe-kaxe. Sai kuma bushe bushe irin na kusumburwa da Siriqi
da sarewa duka sabgogi ne na bayyana qasaitar sarakuna da kambama su,
amma dai ba shari’a ce ta zo da su ba. Sannan kuma malamai magabata
irin su Imamu Ahmad Rahimahullahu Sun bayyana cewa, kayayyakin
kaxe kaxe da bushe bushe, irin su garaya da Goge da Molo da kwamsa da
duk masu kama da su, sun shiga cikin wannan harantawa da Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Saboda mummunan tasirin da
suke da shi ya ma fi na duk wasu kayan kixa da ake amfani da su a
zamanin duhun kai, waxanda anka ambata a cikin wasu hadisai. Kai!
Yadda wasu ma daga cikin su ke sa maye da annashawa ko giya albarka.
Kamar yadda malamai irin su Ibnul Qayyim suka faxa.
Wannan haramci na qara tsanani da qamari lokacin da aka haxa
waxannan kaxe kaxe da bushe bushe da goge goge, da muryoyin mata
mawaqa. Uwa uba kuma idan waqoqin da suke yi xin suka qunshi
kalaman bege da soyayya da qauna, da siffanta kyawon halitta. A irin
haka malamai sun ce waqoqin na matuqar haramta, saboda suna share
96
hanya ne zuwa ga alfasha. Suna kuma tsirar da munafucci a cikin zukata.
A taqaice dai, kaxe- kaxe da waqe- waqe na daga cikin manya- manyan
abubuwan da ke sa mutane na kutsa kai ga varnace varnace. Kuma ga shi
raba mutane da su na da matuqar wahala saboda ci gaban zamani ya
sakaxa su cikin abubuwan amfani da dama kamar Agogayyen hannu,
qararrawar qofa, kayan wasan yara, Na’urori masu qwaqwalwa da Tarhotarho
da sauransu. Amma kuma kar a manta haramun ne. Allah Ya agaje
mu.
TSEGUMI
Giba ko tsegumi na nufin yin maganar wani musulmi a kan wani
abu da ba ya so a ji, ko da kuwa abin gaskiya ne. Wataqila abin ya shafi
halittar jikinsa ne, ko irin riqonsa da addini, ko rayuwarsa ta yau da
kullum, ko xabiunsa. Haka kuma tattauna wasu kurakurai na wani, ko
kwaikwayon wata xabi’a tashi don a yi dariya duk na iya zama Giba.
Mafi yawan majalisu da wuraren haxuwar jama’a a yau sun zama
dandalin tsegunguma da cin naman mutane, da keta alfarmar musulmi.
Irin wannan xabi’a ko, na daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa
Ta’ala Ya haramta ga bayinsa, ta hanyar kwatanta masu ita da wani abin
da ko wace rayuwa ke qyama. Ya ce;
Ma’ana:
Kuma kada sashenku ya yi tsegumin sashe. Shin xayanku na
son ya ci naman xan’uwansa yana matacce? Ba za ku so ba.
Kuma ku ji tsoron Allah. (49:12)
97
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fito wa musulmi da
tantagaryar abin da wannan aya ke qoqarin cewa, akan haramcin
tsegumi, inda ya ce wa Sahabbai: “Ko kun san abin da ake ce wa Giba
(tsegumi)? Suka karva masa da cewa: “Allah da Manzonsa ne kawai suka
sani”. Sai ya ce, Giba ita ce ka tsegunta wani abu a kan xan’uwanka,
wanda kuma ba ya son a ji”. Sai kuma Sahabban suka sake tambayarsa da
cewa: To, me kake gani da abin da aka faxa a kansa gaskiya ne? Sai ya ce
masu: Idan abin da aka faxa a kansa gaskiya ne a lokacin giba ta tabbata.
Idan kuwa ba gaskiya ba ne ya zama qazafi kenan”. (Muslim: 4/2001).
Mutane, musamman a yau, sun yi biris da wannan lamari, sun
xauki Giba ba bakin komai ba. Alhali kuwa abu ce mai tsananin girma da
haxari a wurin Allah kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya bayyana, cewa: “Riba nau’i Saba’in da biyu ce. Mafi
qarancin zunubi daga cikinsu ita ce, wadda zunubinta ke daidai da na
wanda ya yi jima’i da mahaifiyarsa. Mafi girmanta kuma ita ce wadda
zunubinta ke daidai da na keta rigar mutuncin xan’uwa musulmi (cin
namansa)” (Silsilah Sahiha: 1871).
Maganin wannan kuwa shi ne, kada mutum ya yi. Idan kuma yana
zaune da mutane, suka sa faifan wani; suna sara da sassaqa to, ya yi
qoqarin ba shi kariya mai tsafta. Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya umurci Musulmi da yin haka inda yake cewa: “Duk wanda
ya rufa wa xan’uwansa musulmi asiri, Allah zai tsare fuskarsa daga shiga
wuta Ranar Qiyama” (Ahmad: 6/450).
GULMA
Gulma ita ce safa da marwa a tsakanin mutane, ana jekadancin
maganganun sashen su zuwa ga sashe, da nufin tayar da wata fitina da
98
haifar da qiyayya da gaba a tsakaninsu. Wannan xabi’a haramun ce.
Kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya la’anci waxanda duk ke yin ta.
Ya ce:
Ma’ana:
Kada ka bi duk mai yawan rantsuwa, walakantacce. Mai
zunxe, mai yawo da gulma. (69:10-11).
Haka kuma Huzaifata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke yawo da gulma ba ya shiga
aljanna” (Bukhari: 10/472).
Haka kuma xan Abbas ya ce: “Wata rana Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya wuce kusa da wata maqabarta a Madina sai ya ji
hargowar wasu mutane biyu, ana yi masu azaba a cikin qaburburansu. Sai
ya ce: Ai ana yi masu azaba ne, amma ba don wani babban zunubi ba.
Kai! Amma fa ko laifukan nasu manya ne. Saboda xayansu ba ya tsalki
idan ya gama bauli. Xayan kuma yana yawo ne da gulma” (Bukhari
1/317).
Wannan kenan. To kuma mafi munin Gulma duk bata fi wadda
zata haifar da matsala tsakanin mata da miji ba. Ko wadda za a tsegunta
wa wani maigida abin da ma’aikatansa ke cewa, don a haifar da wata
qullalliya tsakaninsu.
Gaba xayan waxannan xabi’u da ire-irensu haramun ne. Kuma
nisantar su ya zama wajibi.
KWARMATO
Allah maxaukakin Sarki na cewa:
Ma’ana:
Ya ku waxanda suka yi imani! Kada ku shiga gidajen da ba
gidajenku ba, sai kun sami izini, kuma kuna yi wa masu su
sallama” (24: 27).
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya warware zare da
abawar wannan aya, da ya bayyana cewa an wajabta wa musulmi neman
izni ne, kafin ya shiga gidan da ba nasa ba, don kada ya ga wani abin da
ba a so ya gani. Manzon yace: “An gindaya neman izni ne don a kange
gani” (Bukhari: 11/24).
Wannan mugunyar xabi’a ta kwarmato, ta zama ruwan dare
tsakanin jama’a a waxannan kwanuka namu. Musamman idan gidajen
mutane na kusa da juna ko ma suna xafe ta yadda qofofi da tagoginsu ke
fuskantar juna. Sai ka taras maqwabta na amfani da wannan dama suna
leqen cikin gidajen maqwabtansu a kai a kai, maimakon su riqa kau da
kansu. A yayin da waxansu kuma da ke kan tudu kan mayar da leqen
gidajen maqwabtansu da ke kware abin yi da gangan ta hanyar tagoginsu
ko wani abu mai kama da haka. Ko Shakka babu wannan cin amana ne,
kuma wuce iyaka ne a cikin haqqin da maqwabci ke da shi na walwala
(privacy). Kuma wata hanya ce da ke zama sanadiyyar faruwar wasu
abubuwa na haram masu yawa. A kan haka ne shari’ah ta xauki idon mai
kwarmato ba bakin komai ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce: “Duk wanda ya leqa gidan wasu ba tare da izninsu ba,
to ya halatta gare su su soke idaniyarsa xaya” (Muslim 3/1699).
100
A wata ruwayar ma cewa ya yi : “Su soke idaniyarsa, kuma ba
diyya ba qisasi” (Ahmad: 2/385).
WARIYA
Wariya a nan na nufin kevancewar mutane biyu daga cikin uku
don wata tattaunawa ta asiri. Wannan xabi’a ta zama kamar ado a cikin
mutane alhali kuwa wata hanya ce da shaixan kan bi, ya raba kan
musulmi, har a wayi gari wasu na qyamar wasu.
Wannan xabi’a haramun ce a shari’a, kuma Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana irin hikimar da ke cikin
haramcin ta da cewa, idan kuna ku uku, kada biyu su ware suna ganawa
su bar xaya. Su bari har sai sun yawaita. Don kada xayan ya samu
damuwa” (Bukhari: 11/83).
Sannan kuma wannan hukunci bai taqaita ga mutane biyu kawai
ba. Ba ya halatta ko mutane uku su ware su bar xaya, na huxunsu, tilo.
Haka haka. Abin da Shari’a ta haramta a nan a taqaice shi ne, warewa a
bar mutum xaya, komai ko yawan waxanda suka ware xin. Haka kuma
haramun ne mutane biyu su canza harshe suna magana da wani yare da
na ukunsu ba ya fahimta. Domin ko shakka babu hakan zai sa ya ji ya
tozarta. Kuma duk wanda kenan zai fahimci sun yi haka ne don su cuta
masa a zuci, da sauransu.
JAN WANDO A QAS
Kalmar “Isbal” kalma ce ta Larabci wadda ke nufin sa wando dogo
har ya wuce idon sau. Mutane a yau ba su xauki wannan xabi’a bakin
komai ba. Alhali kuwa komai ce a wurin Allah. Domin kuwa Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a wani hadisi da Abu zarri ya
101
riwaito: “Mutane uku Allah ba zai haxa baki da su ba gobe qiyama. Kai!
Ko kallon rahama ba zai yi masu ba, balle Ya tsirar da su. Za su tabbata
cikin azaba mai raxaxi. i) Wanda wandonsa ke wuce idon sawunsa, ii)
wanda ke yi wa mutane gori da, iii) Wanda ke rantsuwa a kan qarya idan
zai sayar da wani abu” (Muslim: 1/102).
An sami wasu mutane a yau da, idan aka yi masu tanbihi a kan
wannan xabi’a sai su ce; Ai ba don wani alfahari ko taqama na sa
wandona har ya wuce idon sau ba”. To, wannan Magana riya ce a
kaikaice. Kuma ba karvavviya ba ce. Haramcin sanya wando har ya wuce
idon sau, abu ne da ya haxe kowa. Wanda ya yi a kan fankama da
alfahari da wanda bai yi a kan haka ba. Domin kuwa cewa Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk abin da ya gota idon sau na
wando rabon wuta ne” (Ahmad: 6/254).
Wannan shi ne hukuncin wanda ya yi Isbal ba don wata fankama
da feshi ba. Kuma wanda ya yi haka Saboda girman kai da feshi da
fankama, hukuncinsa ya fi tsanani. Don cewa Manzon Allah Sallallahu
Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya zuba tufafinsa har suka ja qasa
saboda girman kai, Allah ba zai dube shi da ijiyar rahama ba ranar
qiyama (Bukhari: 3465).
Shari’ar ta tsananta hukunci ne a kan wannan saboda haxa hancin
laifi biyu da ya yi a lokaci xaya, kuma a cikin mas’ala xaya wato zuba
tufafi su wuce idon sau da kuma alfahari.
Kar ka yi mamakin shigowar “tufafi’ a cikin wannan magana
domin xan Umar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa: “Isbal” na iya
tabbata ta hanyar gyafto (wando) ko riga ko rawani. Kuma duk wanda ya
wuce iyaka da xayansu saboda alfahari da girman kai, Allah ba zai dube
shi da ijiyar rahama ba a ranar qiyama. (Abu Dawuda: 4/353).
102
Amma kuma shari’ah ta yi rangwame ga mata, su tsawaita
tufafinsu da misalin kamu xaya ko biyu, don gudun iska ya kaxa a hangi
wani abu na jikinsu. Amma ba ya halatta su wuce haka. Kamar yadda
wasunsu kan yi musamman a tufafin bukukuwansu na aure, waxanda
keda doguwar geza a baya. Ta yadda har sai abokan amarya sun kama
mata ita, ta baya.
QAWA DA ZINARI GA MAZA
Abu Musal Ash’ari Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Qawa da Siliki da zinari ta
mata ce daga cikin al’ummata. Amma an haramta su ga maza
(Ahmad:4/393).
Kasuwanninmu a yau cike suke da abubuwan amfani na maza,
kamar: Agogayyen Hannu, da Tabarau, da Aninai, da Alqalumma da
makamantansu, da aka qera da zinari mai daraja daban-daban, ko kuma
aka yave qarfen na asali da shi. Agogayen hannu a yau su ne maza suka
fi gasa da juna a cikin mallakarsu duk kuwa da kasancewarsu na zinari.
Xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ga wani namiji sanye da zoben zinari,
nan take ya karve shi ya kuma yi jifa da shi, ya ce; “Ko akwai wani daga
cikinku da zai iya xaukar garwashin wuta ya liqa ga hannunsa? (Yana
nufin duk namijin da ya sanya zoben zinari kamar ya xauki garwashin
wuta ne ya liqa a hannunsa) Da Manzon ya bayar da baya, sai wasu suka
ba wancan mutumin shawarar ya xauki zobensa mana, ya ci gaba da
amfani da shi (ta hanyar sayarwa ya amfana da kuxin) shi ko ya ce
faufau, Wallahi tunda Manzon Allah ya karve shi ya yas ba ni ba shi
(Muslim; 3/1655).
103
TSIRAICI
Wata hanya da maqiyan Musulunci ke bi suna kawo mana hareharen
ba zata a cikin siga ta zamani, ita ce hanyar qirqire-qirqiren salailai
daban-daban na kayan ado ta fuskar xinke-xinke, waxanda kullu yaumin
suke canza wa sanfari da sunan yayi, waxanda kuma aka wari gari sun
sami mutaqar karvuwa a qasashenmu na musulumi.
Irin waxannan kaya ba sa rufe komai na jikin mace. Saboda
kasancewarsu qanqana, Shar-shar kuma tani tani. Ta yadda bai kamata
macen da ta san kunya ta saka su ko gaban mace ‘yar’uwarta, ko wani
muharraminta ba. Balle wanda ba su ba. Amma kuma Alhamdu lillahi, da
ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya faxa mana irin
haka za ta bayyana ga matan qarshen zamani. A wani hadisi da Abu
Harairata Raliyallahu Anhu ya riwaito:”Akwai wani nau’i biyu na
mutanen ‘yan wuta da za su bayyana can gaba: i) Wasu mutane da ke
yawo da wasu manyan buloli masu kama da wutsan sanuwa sana bugun
mutane da su, da ii) Wasu mata masu tafiya kamar tsirara suna kakkarya
jiki, kansu kamar tozayen raqumma, a karkace. Da su da aljanna faufau.
Kai ! ko qanshinta ba za su ji ba. Duk da yake ko wanda ke nisan wuri
kaza da kaza yana jin sa (Muslim; 3/1680)
Irin waxannan mata, da dabi’unsu sun bayyana kamar yadda
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ambata, babu abin da ya
rage mana illa mu nisance su.
Haka kuma irin waxannan tufafi na tsiraici sun haxa da irin
dogayen rigunan da mata ke sakawa a yau masu tsage-tsage, da wasu
yaggwai can qasa, ga su kuma da faxin. Ta yadda da macce ta zauna
al’aurarta za ta bayyana a fili. Na farko kenan. Ga shi kuma ta yi koyi da
104
kafirai, don su aka sani da irin waxannan kaya masu nuna tsiraici. Muna
roqon Allah ya kiyashe mu.
Wasu tufafin Kuma da su ma, saka su tsiranci ne, ko da sun rufe
jiki, su ne waxanda ke da miyagun hotunan da suka haxa da kamar:
Hotunan Mawaqa da Nigogi (‘yan rawa), da kwalaben giya da hotunan
dabbobi masu rai. Waxanda dukansu haramun ne a musulunci. Wasu
kuma na xauke ne da hoton kuros ko Tamburran qungiyoyin asiri, ko dai
wasu miyagun kalamai da ba su dace da duk wani mutum mai muruwa
ba. Duk da yake wani lokacin muninsu ba zai bayyana ga waxanda ke
sanye da kayan ba. Saboda an yi rubutun ne da wani yare na mutanen
qetare.
SAJIN GASHI (Atacimen)
A idon Shari’ar musulunci, duk macen da za ta sadar da gashin kanta
na asali da wanda ba na asali ba, daxa na kanta ne, ko wanda aka yanko
daga jikin wata dabba kai tsaye kamar doki, to ta yi al-gussu. Algussu
kuwa haramun ne.
Asma’u ‘yar Abubakar Raliyallahu Anha ta ce: “Wata mata ta zo
wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta ce, Ya Manzon
Allah, akwai wata ‘ya tawa da zan wanke jibi. Amma kafin yau ta yi
wani xan zazzavi har gashin kanta ya zuba. Ko ina iya yi mata sajin
gashi?’ Ya karva mata da cewa: A’a. Allah Ya la’anci duk wadda ta yi
Sajin gashi da wadda aka yi ma shi (Muslim: 3/1676).
Haka kuma Jabiru xan Abudullahi ya ce: “Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana mace ta yi sajin wani abu ga kanta
(Muslim: 3/1679).
105
A bisa dalilin waxannan hadisai, duk wani nau’i na sajin gashi da
ake yi a yau a gidajen gyaran gashi na mata, ko wane irin nau’i ne, to
haramun ne. Haka kuma hulunan gashi da wasu taurarin ‘yan wasa ke
amfani da su a finafinai rashin tarbiyya ne, kuma haramun ne.
HARKAR ‘YAN DAUDU
Namiji ya yi qoqarin komawa mace, ko mace ta yi qoqarin
komawa namiji ta hanyar kwaikwayon xabi’un juna, mummunar xabi’a
ce a idon shari’ar musulunci.
A xabi’ance ma kamata ya yi namiji ya yi ta tattali da qoqarin
tabbata namiji. Ita ma mace, ta yi nata tattali da qoqarin na tabbata mace.
Don wannan shi ne abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya shirya
kowanen su a kai asalatan. Kuma qoqarin sava wa wannan tsari nasa na
sa nagartattar rayuwa ta ‘yan adamtaka ta yi wuya a bayan qasa. Domin
hakan zai sa amon rayuwar jama’a ya xauki wani salo irin na hatsin bara,
wato wake-wake a komai.
Irin wannan xabi’a haramun ce. Dalili kuwa shi ne, a tsarin shari’ar
musulunci, duk abin da aka ce Allah Ta’ala ko Manzonsa ya la’anci mai
shi, to ya zama haramun ke nan.
Xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ya la’anci Maza masu
kwaikwayon mata. Ya kuma la’anci mata masu kwaikwayon maza
(Bukhari: 10/332). Haka kuma xan Abbas xin ya riwaito wani hadisin da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Allah Ya
la’anci mata maza, da maza mata (Bukhari: 10/333)
“Kama” da waxannan hadisai ke ta Magana, na iya kasancewa ta
fuskar kwaikwayon kai da komowa, magana da tafiya. Haka kuma
106
hadisan na tabbatar mana da cewa haramun ne xayan jinsunan nan biyu
ya yi kama da xan uwansa, ta hanyar saka duk wani abu da, a xabi’a xaya
jinsin aka sani da shi.
A kan haka haramun ne namiji ya xaura Sarqar wuya, ko ta hannu,
ko ta qafa, ko ‘yan kunne da sauransu, kamar yadda fitsararru ke yi a
Turai. Haka kuma haramun ne mace ta yi amfani da duk wani abu da a
xabi’a na maza ne, kamar: Riguna da Jallabiyoyi, da sauransu. Abin da
ma aka fi buqata a cikin ko wace al’umma shi ne tufafin mata ya sava da
na maza kwatakwata. Domin Abu Hurairata ya riwaito wani hadisi da
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Allah Ya
la’anci namijin da ke sa kayan maza, da macen da ke sa kayan mata (Abu
Dawuda: 4/355).
BUDURWAR ZUCIYA
Buduruwar Zuciya a wannan babi, na nufin duk wani yunquri da
wanda shekarunsa suka miqa zai yi don canza wata halittar Haliqu a
jikinsa kamar hurhura, ta hanyar yi mata baqar garura, don ya koma layin
matasa.
Nagartaccen ra’ayi na malaman Sunnah ya tafi a kan cewa, irin
wannan Sabga haramun ce. Saboda wani nau’i ne na Al-gussu. Kuma an
dace da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hani musulmi
xabi’ar a cikin wani hadisi da ke cewa: “Za a yi wasu mutane a qarshen
zamani da za su riqa ture farin gashinsu da baqar garura har ya riqa
walqiya kamar gaban baqar tantabara. To, ko qanshin aljanna ba za su ji
ba. (Abu Dawuda).
Irin wannan sabga ta yawaita matuqa ga mutanen da Allah
Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wa ni’imar farin gashi tun suna da qurciya
ko waxanda mutuwa ta fara barbaxa wa gishiri. Wanda hakan ke
107
yaudarar mutane, ta hanyar mayar da tsoho yaro ko kuma tsohuwa ta
koma yarinya. Ka ga an mayar da gaskiya qarya kenan.
Ba tura farin gashi ya koma wata kala ne haramun a shari’ar
musulunci ba. A’a, ture shi ya koma baqi ne haramun. Saboda ai, ta
tabbata Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na shafa wa farin
gashinsa lalle, ya koma ja- ja- ja ko qasa –qasa. Abin ma bai tsaya ga shi
ya yi wa kansa ba, har umurni ya yi da haka. Don a lokacin da aka ci
garin Makka da yaqi, aka zo da Abu quhafata (Mahaifin Halifa
Abubakar) don su gaisa. Ya ga gemu da sajensa irin na dattijai, ya yi fari
kamar auduga sai Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku suturta
wannan farin gashi da yi masa turi. Amma kada ku sa baqi
(Muslim:3/1663).
Wannan hukunci na haramcin ture gashi ya koma baqi, ya haxa
maza da mata. Amma su ma, suna iya yin wata kalar.
ADO DA HOTUNAN ABU MAI RAI
Abdullahi xan Mas’udu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa,
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mutanen da za su
haxu da azaba mafi tsanani Ranar qiyama su ne masu sassaqa gumaka
(Bukhari: 10/382).
Haka kuma Abu Harairata ya riwaito cewa, Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ta’ala Ya ce, “Babu wanda ya
kai shisshigin wanda ke qoqarin yin halitta irin tawa. In gaskiya ne ya
halitta gero da alkama mu gani (Bukhari: 10/385). Kuma xan Abbas
Raliyallahu Anhu ya ce wani hadisi da ya karvo daga Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama: “Za a saka wa ko wane gunki da mutum ya
sassaqa rai daga ran wanda ya sassaqa shi, a yi ta azabtar da shi a cikin
108
wutar Jahannama”. Ya kuma qara da cewa: “Wanda ko duk sassaqa ta
zamo sana’arsa, to, ya tsaya ga sassaqa itace, ko wani abu maras rai”
(Muslim: 3/1671).
Ka ga kai tsaye, waxannan hadisai, sun haramta sassaqa hotuna ko
zana su ko xaukar hoton su matuqar dai na ababe masu rai ne.
Tunda kuwa haka ne, ya zama wajibi a kan duk wani musulmi na
qwarai ya karvi wannan hukunci da shari’ah ta yi da hannu biyu- biyu, ba
tare da wata jayayya ba. Duk da yake wasu na iya kafa hujja da cewa,
“Eh! To ai, mu ba bauta wa waxannan hotuna muke yi ba, don ba sujada
muke yi musu ba”.
Amma kuma duk mai hankalin da ya dubi wannan matsala da idon
basira zai tsinkayo tare da fahimtar irin hikimar da haramta irin
waxannan abubuwa ta qunsa. Saboda mafi yawan ayyukan fitsara na
faruwa ne ta hanyar hotuna. Musamman zinace-zinace. Domin ta hanyar
kallace-kallacen hotunan banza ne qwazaba ke toroqo da bululluqai, daga
nan har a kai ga varna.
Bisa wannan dalili ne ma, mala’ikun rahama ke qaurace wa duk
wani gida da ake ajiye hotuna a cikinsa. Kamar yadda Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mala’ikun Rahama ba su shiga duk
wani gida da ke akwai kare a cikinsa ko hotuna (Bukhari: 10/380).
Wani abin mamaki da xaure kai shi ne, duk da wannan haramci,
mutane a yau musamman masu hannu da shuni, ba su fasa aje gumakan
wasu dabbobi ba, kai har da na mutane, a cikin gidajensu da sunan qawa
ko ado. Alhali kuwa akwai wasu mutane da ke bauta wa wasu daga cikin
waxannan abubuwa.
To, haramcin abubuwa irin waxannan ya fi qamari da tsanani.
Sannan sauran hotunan da ake ratayewa na mutane da wasu dabbobi na bi
109
masu. Qarshe kuma waxanda ba rataye su ake yi ba suna bi masu a
haranci. Domin da yawa Sukan sa waxanda suka aje su, girmama su, da
sabunta juyayi da jimami a cikin zukatansu. Duk da yake wasu mutane
kan kafa hujja da cewa Suna aje hotunan mutanen ne, da suka haxa da na
uwayensu ko shugabanni ko malamansu, ko masoyansu ko wasu gwaraje
da suke ganin bajintar su ko suke sha’awarsu, don tunawa da su. Alhali
kuwa ita tunawa da wani abu a zuciya ake yin ta. Ba sai da hoto ko
mutum mutumi ba. Kuma mafi kyawon tunawa da mutum, bayan ya
qaura, ita ce, idan ya faxo a zuciyar wani nasa, to ya yi masa kyakkyawar
addu’a, ta hanyar roqa masa gafara da Rahamar Allah Subhanahu Wa
Ta’ala.
Saboda haka, babu wani musulmi da ke da wani uzuri na aje wani
hoto a xakinsa ko liqa shi a jikin bango ko abin hawansa. Lalle ne ya yi
waje da duk wani hoto ko mutum mutumi na mutum ko dabba da ke
gidansa. Sai fa idan hakan ta gagara. Balle kuwa ba zata gagara ba.
Hotuna irin waxanda ke jikin gwangwanaye da kwalayen abinci,
waxanda ba makawa sai musulmi sun yi ta’amuli da su, ko waxanda ke
cikin wasu littafai na karatu. Ana so mutum ya yi iyakar qoqarinsa na
ganin ba su zame masa allaqaqai ba.
Babu laifi idan an aje hotuna irin waxanda babu makawa sai an aje
su, kamar waxanda ake maqalawa ga takardun shedar qare karatu ko
katin sheda, ko lasisi, ko irin waxanda ke saqe a kan dardumai.
Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:
Sai ku bi Allah da taqawa gwargwadon abin da kuka
sami iko: (64:16).
110
QARYAR MAFARKI
Da gangan wasu mutane ke qirqira mafarki, har su ce sun ga wani
abu a cikinsa, don kawai neman girma a idon mutane ko wani abin
duniya, alhali qarya suke yi ba su ga komai ba. Kai! Ko mafarkin ma ba
su yi ba. A yayin da wasu mutanen kuma kan yi haka ne don su tsorata
wasu magabata da ke masu barazana ko wani abu mai kama da haka.
Irin waxannan qaryace-qaryace kan yaudari hankalin mutane,
saboda rashin isassar wayewa da cikakken Ilimi, da kuma imanin da suke
da shi ga mafarki.
Wannan xabi’a na xaya daga cikin xabi’un da shari’ar musulunci ta
haramta. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mafi
girman qarya ita ce danganta mutum ga wanda ba mahaifinsa ba. Ko
iqirarin ganin wani abu (a cikin mafarki) a kan qarya. Ko a jingina wa
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama abin da bai ce ba (Bukhari:
6/540).
Haka kuma ya ce: “Duk wanda ya yi qaryar ya yi mafarkin wani
abu alhalin bai yi ba za a titasta masa xaure ‘ya’yan sha’ir biyu. Ba kuma
zai iya ba (Bukhari: 12/427).
Xaure qwayar sha’ir biyu wuri xaya abu ne da baya yiwuwa.
Kamar yadda wancan mafarki da aka yi qaryar yi bai kasance ba.
TOZARTA QABURBURA
Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Da xayanku zai zauna a kan
garwashin wuta, har ya ruru ya qone tufafinsa, ya kai ga fatar jikinsa, ya
fi alheri gare shi bisa ga ya zauna a kan qabari (Muslim: 2/667).
111
Kafin zama a kan qabari ma, wasu mutane nada xabi’ar tattakawa
da yin tafiya a kansa, ba tare da wata damuwa ba. Musamman a lokacin
da aka tafi maqabarta don nufe wani. Wasu ma har da takalmi a
qafafunsu. Haka za su bi qaburburan da ke maqwabtaka da wanda suka
kai, suna tattaki a kai, ba kunya ba tsoron Allah, balle su tuna da wata
alfarma da mamatan da ke kwance wurin ke da. Alhali kuwa wannan
matsala mai matuqar nauyi ce. Musamman idan aka yi la’akari da faxar
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya ce: “Da zan yi tattaki a
kan garwashi ko kaifin takobi, ko in wanke takalmina da xayan qafata, ya
fi soyuwa gare ni bisa ga in yi tattaki a kan qabarin wani musulmi (Ibnu
majah: 1/499).
Wannan kenan. To ina ga waxanda ke yankar filin maqabarta su
gina gidaje ko shaguna? Wasu mutanen ma saboda tsananin rashin kirki
da taskai, har bayan gari sukan yi a cikin maqabarta, suna damun bayin
Allah da ke kwance wurin da qazanta. Irin waxannan mutane na
fuskantar babban haxari. Domin kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama ya ce: “Wanda ke biyan buqatarsa a cikin maqabarta daidai
yake da wanda ke biyan ta a cikin tsakiyar kasuwa (Wato asirinsa a tone
yake).
Haka kuma wannan gargaxi da kashedi ya haxa har da waxanda ke
zubar da shara a cikin maqabarta. Ta hanyar amfani da damar kasancewar
bangayen maqabartun sun zube, ko an daina amfani da su. Duk irin halin
da maqabarta take ciki, haramun ne a yi mata irin wannan tozarci.
Kai! Har waxanda ke zuwa ziyara a maqabartu wajibi ne su cire
takalminsu, matuqar dai za su ratsa qaburburan da ke ciki.
RAGGON TSARKI
112
Karantar da xan Adamu kowace irin tagara da za ta sa ya ci gaba
da zama mutum kammalalle, na daga cikin abubuwan da addinin
Musulunci ke alfahari da su. Don babu wani addini ko tsarin rayuwa da
ya riga shi a wannan fagen.
Yin cikakken bankwana da qazantar fitsari ko gayaxi a lokacin da
suka fita daga jikin mutum, ta hanyar wankewa da ruwa ko hoge tas-tas
tas, na xaya daga cikin waxannan darussa. Amma kuma mutane da dama
sun yi biris da wannan koyarwa ta musulunci. A inda suke sakaci har
jikinsu da tufafinsu su yi kace-kace da xayan wannan najasa. Ta yadda ko
sun yi sallah Allah ba zai karva ba. A qarshe kuma su taras da azaba a
cikin qaburburansu. Kamar yadda xan Abbas ya riwaito cewa: “Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wuce ta wata maqabarta a garin
Madina sai ya ji qarar wasu mutane biyu ana yi masu azaba a cikin
qaburburansu. Sai ya ce: “Ana azabtar da su ne, ba don wani babban laifi
ba. Kai! Babban laifi ne shi ma: Xayan dai ba ya tsabtaci al’aurarsa da
kyau idan ya yi fitsari. Xaya kuma ba ya da aiki sai yawo da tsegumi
(Bukhari: 1/317).
Akwai ma hadisin da Manzon Allah ke cewa a ciki: “Mafi yawan
azabar qabari a kan fitsari take (Ahmad: 2/326).
Abubuwan da kan haddasa irin wannan matsala ta rashin samun
cikakken tsarki, sun haxa da: i) Gaggawa a gama, ii) Tsugunawa Wuri
Mai Tsauri, iii) Rashin damuwa da wankewa da kyau.
Wata babbar matsala kuma da ke taka gagarumar rawa a wannan
hauji, ita ce irin yadda muka yi nisa matuqa a cikin kwaikwayon al’adun
Turawa. An wayi gari wasu wuraren da muke fitsari a yau irin na Turawa
ne, da ake xafawa a bango kuma a fili. Ta yadda ma duk wanda zai wuce
yana ganin wani abu na tsiraicin wanda ke biyan buqata a wurin.
113
Ka ga irin waxannan mutane laifinsu ya zama biyu kenan, ga
qazanta ga tsiraici.
TSINCE
Allah maxaukakin Sarki Ya ce:
Ma’ana:
Kuma kada ku yi leqen asirin (‘yan uwanku) (49:12)
Xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya tsinci maganar da
wasu mutane ke yi, ba tare da sun sani ba, za a zuba ruwan narkakkar
darma a kunnuwansa ranar qiyama (Xabarani: 11/248-249)
Idan wanda ya yi irin wannan haramtaccen aiki, ya yi ne da nufin
kai wannan magana da ya tsinta a wani wurin, don ya tayar da wata wuta,
to, Gummi ta haxu da Anka kenan; ga laifin tsince, ga kuma
annamimanci. Wannan mutum ya tave domin kuwa Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Annamimi (mai tsince don ya haxa
faxa) ba ya shiga aljanna (Bukhari: 10/472).
CUTAR DA MAQWABCI
Haqqin maqwabci a kan maqwabcinsa abu ne mai girma a wurin
Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Saboda haka ne Sarkin ya haramta cutarwa
a tsakaninsu. Inda ya ce:
114
Ma’ana:
Kuma ku bauta wa Allah, kuma kada ku haxa wani da shi,
kuma ku kyautata ma mahaifa. Kuma ku kyautata ga
ma‘abuta zumunta da marayu da matalauta, da maqwabci
na kus da na nesa, da aboki na gefe, da xan hanya, da abin
da hannuwanku na dama suka mallaka. Haqiqa Allah ba ya
son wanda ya kasance mai taqama, mai yawan Alfahari
(4:36)
Haka kuma, Abu Shuraihu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wallahi ba ya da
imani, wallahi ba ya da imani, wallahi ba ya da imani. Sahabbai Suka ce:
waye shi ya Manzon Allah? Ya ce : Wanda maqwabcinsa ba ya tsere wa
sharrinsa. (Bukhari: 10/443)
Matsayin maqwabci a wurin maqwabci abu ne mai matuqar girma.
Wanda har ta kai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa
maqwabci shi ne ma’aunin gane kirki ko rashin kirkin mutum.
Xan Mas’udu ya riwaito cewa, wani mutum ya ce wa Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya Manzon Allah, ya zan yi in gane
kirki ko rashin kirkina? Sai Ma’aki ya ce masa: “Duk lokacin da ka ji
maqwabtanka na cewa kana da kirki, to, kana da shi. Idan kuwa ka ji
suna cewa ba ka da shi, to, lalle ba ka da shi xin”. (Ahmad: 1/402)
115
Cutar da maqwabci na iya tabbata ta fuskoki da dama. Duk wanda
ya hana maqwabcinsa jingina wani katakon runfa ga bangon da ya raba
su, suke kuma da haqqi gaba xaya a cikinsa, ko ya faxaxa nasa gini, ta
yadda xayan zai sami qarancin hasken rana ko iska, ba kuma tare da
izinin xayan ba. Ko ya fasa, ko buxe tagoginsa ta yadda zai riqa leqen
gidan xayan. Yadda ba wani abu na asiri da za a iya yi a xaya gidan sai
bisa idonsa. ko ya dinga damunsa da kaxe-kaxe a kan fayafan garmaho,
ko hargowa, musamman a lokacin da yake baccin dare ko na rana, ko ya
xauki sabgar jibge shara a qofar gidan xayan. Duk wanda ke yi wa
maqwabcinsa xayan waxannan xabi’u, to, ya cutar da shi matuqa. Daxa
balle tava iyalinsa ko dukiyarsa Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallama na cewa: “Da mutum zai yi zina da mace goma can nesa, ya
fi sauqi gare shi, bisa ga ya yi da matar maqwabcinsa. Da kuma zai fasa
wasu gidaje goma can nesa, ya fi sauqi gare shi bisa ga ya fasa gidan
maqwabcinsa (Bukhari:103).
Bone ya tabbata ga mutanen da ke da xabi’ar amfani da damar
waxansu maqwauta nasu da basu kasancewa gida da dare don yanayin
aikinsu, sai su faxa gidajensu su aikata varna. Ranar qiyama sun shiga
uku.
TAUSHE HAQQIN MARAYU
Yana daga cikin dokokin shari’ar musulunci cewa, yana da
matuqar kyau mutum ya yi qoqari iyakar zarafi ya yi haqurin cutarwar da
xan’uwansa zai yi masa. Na farko kenan. Kuma haramun ne shi ya zama
farkon wanda zai yi cutar.
Taushe haqqin maraya, wani zalunci ne da cutarwa, wanda kuma
shari’a ta haramta. Abu ne mai sauqin gaske wanda za a gada ya taushe
116
haqqin wasu daga cikin magadansa, tun kafin ya mutu. Wannan na
faruwa idan ya yi amfani da sauran nunfashinsa a duniya, ya rubuta wata
wasiyya a kan abin da zai bari na dukiya. A irin wannan dama ce wasu
kan taushe haqqen wasu marayu ta hanyar kore su daga cikin magadansu
na haqiqa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi gargaxi da
babbar murya ga duk mai irin wannan hali, da ya ce: “Duk wanda ya
cutar da wani Allah zai musguna masa, duk kuma wanda ya tsananta wa
wani Allah zai tsananta masa (Ahmad: 3/453).
Wata hanyar kuma da mutum ke iya karva sunan mai taushe
haqqin marayu ita ce, a wasiyyarsa ya ware wa wani magadi, fiye da abin
da shari’ah ta yanka masa ko ya yi wasici da ba wa wani mutum fiye da
kashi xaya bisa uku na dukiyarsa.
Irin wannan matsala ma nada ‘yar dama a qasashen da musulunci
ke jagoranci. A qasashen da ko ba dokokin shari’ar musulunci ne ake
aiwatarwa ba, da yawa ake samun irin waxannan matsaloli. Kuma ko sun
faru babu yadda magadi zai yi ya karvi haqqinsa wanda Allah Ya shata
masa. Domin dokokin da kutunan da za a iya kai kuka gare su, ke
aiwatarwa, na iya xaure wa irin wannan zalunci gindi, musamman idan
da hannun wani lauya a ciki. Ga shi ko Allah Ta’ala ya ce:
Ma’ana:
Bone ya tabbata gare su daga abin da hannayensu ke
rubutawa, kuma bone ya tabbata gare su daga abin da suke
sana’antawa (2:79).
117
DARA
Dara da Ludo da Karta da Diraf da makamantansu, na duk wata
wasa, da ake dibilwa da hannu da qwaqwalwa don fitar da gwani a cikin
ta, haramun ne a musulunci. Dalili kuwa shi ne, dukansu qofofi ne da ke
kai masu wasannin zuwa ga caca. Saboda haka ne Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mana ahir da su ya ce: “Duk wanda ke
Dara daidai yake da wanda ya cava hannunsa cikin naman alade ko
jininsa (Muslim: 4/394).
Haka kuma Abu musa Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon
Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke Dara, ya sava
wa Allah da Manzonsa (Ahmad: 4/394).
LA’ANTAR MUSULMI
Mutane da yawa kan kasa ja wa halshensu lizzami lokacin da suka
fuskanta. A sakamakon haka sai nan- da nan su furta kalmomin la’anta ga
wasu mutane, ko dabbobi, ko sandararrun abubuwa. Wasu ma har
kwanaki da awoyi suke la’anta. Da makamantansu. Kai! Saboda tsananin
shaqawa da rashin taskai ma, wasu har kawukansu, ko ‘ya’yansu sukan
la’anta. Wasu ma’aura kuma kan la’anci juna lokaci xaya, ko lokuta
daban-daban.
Wannan matsala nada matuqar girma a idon shari’ah. Saboda haka
ta haramta ta. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a
wani hadisi da Abu zaidi Sabitu xan Dhahhaku ya riwaito cewa: “Duk
wanda ya La’anci mumini, to zunubinsa daidai yake da na wanda ya
kashe shi (Bukhari: 10/465).
118
Al’adance, irin wannan xabi’a ta la’ance- la’ance, ta fi yawaita a
bakunan mata a cikin ko wace al’umma. Saboda haka Manzon Allah
Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana cewa wannan xabi’a ce zata
kasance dalilin shigar mafi wayansu wuta. Kuma su, da duk wanda ke
irin wannan sabga, basu cikin waxanda zai ceto ranar qiyama.
Wani babban haxari ma duk bai fi kasancewar la’antar duk da
mutum ya yi ba bisa qa’ida ba, zata dawo kansa. Daxa kome kuwa ya
la’anta. Kaga kenan qaiqayi ya koma kan masheqiya. Da haka kuma
mutum ya nisanta kansa daga rahamar Allah.
KUKAN MUTUWA
Kukan mutuwa ta hanyar hargowa da kururuwa, da faxuwa ana
tashi, yagar fuska da keta tufafin da ke jiki, kamar an yi sabuwar hauka,
abu ne da shari’ar musulunci ta haramta.
Mata su suka fi yin irin wannnan mugunyar xabi’a. Kai! Wasu ma
daga cikinsu har aske gashin kansu sukan yi, da yin wasu xabi’u da suka
sava wa hankali. Waxanda ke nuna cewa ba su karvi wannan qaddara ta
rashi da hannu biyu ba. Kuma ba shirye suke su yarda da hukuncin Allah
kome xacinsa ba.
Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’anci duk mai irin
wannan xabi’a. Abu Umamata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa,
“Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’anci duk macen da ke
yagar fuskarta, ta kece tufafin da ke jikinta, ta yi ta hargowa, tana faxin
bone yoyo! (Ibnu majah: 1/505).
Haka kuma Abdullahi xan Masu’du Raliyallahu Anhu ya riwaito
cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke
119
yagar fuskarsa, ya kece tufafinsa, ya kuma yi kururuwa irin ta jahiliyyah,
ba ya tare da mu (Bukhari: 3/163).
Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:
“Idan mai kukan mutuwa irin na jahiliyya ta mutu ba ta tuba ba, ranar
qiyama za ta tashi da rigar qaya da maxaurin qarangiya (Muslim: 934).
MARI DA TSAGA
Wasu uwaye da malamai nada xabi’ar sa hannu ko wani abu su
mari ‘ya’yansu ko xalibansu ko masu yi masu hidima, da nufin
ladabtarwa. Ladabtarwa kuwa gaskiya ce. Amma fuskar xan Adamu na
xaya daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya karrama.
Kai mata mari kuwa tozartawa ne, da rena hikimar Allah, da walaqanta
abin da ya girmama.
Abun kan wuce mari. Wasu mutane har aska, ko wani abu mai
kaifi sukan sa su yi wa fuskar ‘ya’yansu raxam, da nufin tabbatar da wata
al’ada ta gida a matsayin alama. A yayin da wasu kuma dabbobinsu suke
yi wa tsagar, wai don a banbance tsakanin garken wane da na wane.
Kuma hakan za ta taimaka ga gane ai wannan dabbar ta wane ce. Idan ta
yi vatan kai nan take sai a mayar masa da abarsa.
Marin xan Adam haramun ne a shari’ar musulunci. Saboda hakan
kan iya sa a rasa wani abu daga cikin martabobin da Allah Subhanahu
Wa Ta’ala Ya sa a cikinta. Kamar: Gani, ko ji, ko shaqe. Wanda a qarshe
za su kai wanda ya yi abun ga nadama. Kuma diyya za ta hau kansa.
Abin da ya shafi xan Adam kenan. Ta fuskar dabbobi kuwa, su ma
shari’ah ta haramta yi masu wuta a fuska ko wata tsaga a matsayin alama.
Idan ma har ya zama dole sai an yi masu wata alama, saboda kasancewar
haka al’ada, to sai dai a yi masu a jiki ba a fuska ba, kuma ba da wuta ba.