HUKUNCE-HUKUNCEN
SALLAR IDI
حاكم صلاة العيد
[Hausa - [هوسا
Malan Aliyu Muhammad Sadisu
2014 - 1435
2
HUKUNCE-HUKUNCEN
SALLAR IDI
Gabatarwa: Dasunan Allah Mai yawan rahama maiyawan jinkai, tsira
da amincin Allah su tabbata ga fiyayyan halittar Allah Annabin tsira
Annabi Muhammad, da Iyalan shi da Sahabban shi baki daya. Bayan
haka a wannan karon za mu karkata akalar mu zuwa wani bangare da
ya ke hararomu a 'yan kwanakin nan, wannanan bangaran kuwa shi
ne na SALLAR IDI! Domin mu ga yadda musulunci ya tsara mana
komai abinda ya rage kawai a garemu shi ne bi, komai angama, Allah
tabbatar da duga-dugammu akan tafarkin Ma'aikin Allah.
Mecece Sallar Idi:''Ita sallar idi sallace da ake gabatar da ita a wani
lokaci kebantacce, awata siffa kebantacciya, sau biyu a shekara''.
Kafin mu kai ga fashin bakin wannan ta'arifi na sallar idi, bari mu
gabatar da tabbatuwarta tukunna.
Tabbatuwar Sallar Idi: Sallolin idi guda biyu da musulunci yake da
su (Karamar Sallah da Babbar Sallah) kowacce ta tabbata a shara'a,
ba wai bikine haka kwai na gargajiyaba.
Tabbatuwar Karamar Sallah: itace sallar da ake gabatarwa a ranar
1 ga Shawwal, don godiya ga Allah akan baiwar da ya yi mana na
kammala azumin watan Ramadan, wannan sallar ta tabbata a Suratul-
A'alah aya ta:14-15, Allah madaukakin sarki yana cewa: ''Tabbas
duk wanda ya bayar da zakka (Fidda-kai) ya rabauta. Kuma ya
anbaci sunan UbangijinSa sannan kuma ya yi sallah''. Sai
malamai sukace 'Zakka da aka anbata a ayar farko itace zakkar fiddakai,
Sallah kuma da aka anbata a aya ta biyu itace, karamar sallah
domin itace ake fitar da zakkar Fidda-kai kafin a ta fi, sannan kuma ga
zikirin da aka an'anbata shine wanda ake yi lokacin tafiya sallar idin'.
Tabbatuwar Babbar Sallah: Ita kuma sallah ce da ake gabatar da
ita a ranar 10 ga watan Zul-Hajji. Ita ma babbar Sallah ta tabbata a
Suratul-Kauthar a aya ta: 2. a inda Allah madaukakin sarki yake cewa
''Ka yi Sallah domin Ubangijinka, kuma ka soke (abin
hadayarka)'', malamai sukace 'Babbar Sallah ce domin an hada
Sallah da Yanka' a ayar kamar wacce ta gabata an'hada Zakka da
3
Sallah. Wannan tabbatuwar wadannan sallolike nan ta ayoyin
alkur'ani, hakanamma sun tabbata ta ayyukan Ma'aikin Allah –Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi-, Bukhari da Muslim da Abu-Daud
da Nasa'i duk sun ruwaito daga Jabir-Allah Ya kara masa yarda yace
''Na harci Sallar idi tare da Ma'aikin Allah –Tsira da amincin
Allah su tabbata a gareshi- sai ya fara gabatar da sallah kafin
Huduba ba tare da an yi kiran sallaba ko an tada Ikama''. Haka
shima Bara'u dan Azib –Allah Ya kara masa yarda yace ''Ma'aikin
Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya yi mana
huduba a ranar babbar sallah, bayan ya idar da sallah sai yace
''Duk wanda ya yi wannan sallar tamu, kuma ya yi yanka irin
namu to yankanshi ya yi daidai, wandako ya yanka kafin ayi
sallah to wannan bashi (da ladan) yanka''. Wannan hadisin
malaman Hadisi bakwaine suka ruwaito shi.
Hukuncin Sallar Idi: Hukuncin sallar idi shine, Sunnace mai karfin
gaske, domin Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a
gareshi- ya aikata ta kuma ya lizimceta, hakanan kuma ya fitar da
mata da kanan yara zuwa halartar wannan sallah. Saboda haka bai
kamata mutum ya yi sakaci da itaba har ya rasa samun wannan sallah
wanda saboda ita nema aka bada hutu a kasa baki daya, ka rufe
shagonka na kasuwanci ka dakatar da ayyukanka.
Lokacin Sallar Idi: Kamar yadda bayani ya gabata a ta'arifi cewa
sallace da ake gabatarwa a lokaci kebantacce to wannan lokacin kuwa
shine ''Daga lokacin da rana ta fito ta daga kamar tsawon
sandar mashi harzuwa lokacin da rana zata karkata daga
tsakiyar sama''. Amma malamai sukace 'An fi so a babbar sallah a yi
ta da wurwuri domin mutane su samu su koma gida domin su yanka
layyarsu a daidai lokacin walaha, sannan kuma su ci abinci domin basu
ci ba suka fito sallah. Amma akaramar sallah an fi so a dan jinkirta
sallar domin mutane su samu su gama fitar da Zakkar su ta fidda-kai,
su kuma ci abinci domin iti an fi so a ci kafin a fito sallah'.
Ladubban Sallar Idi: Akwai wadansu ladubba da yakamata a ladabtu
da su, wadannan ladubba suna da yawa daga ciki akwai:
1. Yin wanka da sanya turare da kuma sanya tufafi masu kyau
sababbine ko nada.
2. Hakanan yana daga cikin labudda a ci abinci kafin a fita sallar idi a
karamar sallah, da kuma jinkirta cin abinci a babbar sallah har sai an
yi sallah, da kuma cin wani abu na hantar dabbar layyah ga wanda ya
yi. Ankarbo daga Buraidah –Allah Ya yarda da shi- yace; ''Ma'aikin
4
Allah –Tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi- ya kasance baya
fita zuwa masallcin idi a karamar sallah har sai ya ci abinci, kuma ya
kasance baya cin abinci a babbar sallah har sai ya dawo daga
masallacin idi, sai ya ci wani abu na dabbar layyarsa''.wannan Hadisi
Tirmizine ya ruwaito.
3. Kana yana daga cikin ladubba yin kabarbari, kuma lafazinta shine:
Allahu Akbar, Allahu Akbar, La'ilaha Illallahu, Allahu Akbar,
Allahu Akbar, Walillahil Hamd.
4. Yin gaisuwar sallah wato kacewa dan'uwanka musulmi ''Allah Ya
karba mana ya karba muku''.
Siffar Sallar Idi: Kamar yadda ya gabata a farkon bayani cewa
sallace da ake gabatar da ita a wata siffa kebantatta, wannan siffa
kuwa itace; wannan sallah ana yin ta ne Raka'a biyu, kuma ana
bayyana karatun, ba tare da angabatar da kiran sallah ba, ko tada
ikama, sannan kuma ba'a gabatar da nafila kafin sallar ko bayan
sallar. A raka'ar farko bayan kabbarar harama anayin kabarbari shida
kafin fara karatu (wato kabarbari bakwai kenana). A Raka'a ta biyu
bayan kabbarar tasowa sai a yi kabarbari biyar, kafin fara karatu
(wato kabarbari shida kenan), wadannan kabarbari liman da mamu
duk suna yinsu sai dai mamu baya karatun sallah saboda karatun
liman, sannan sai ayi sallar kamar sauran salloli, bayan liman ya yi
Tahiya ya yi sallama sai ya gabatar da Huduba, sannan yana da
matukar muhimmanci a tsaya a saurari hudubar, wadannanfa sune
ayyukan ranar, amma wacce gaggawa mutane suke yi suke barin
sauraron Hudubar?.
Wanda bai samu sallar idi ba ya samu ya yi sallah Raka'a
hudu kamar nafilfili, idan kuma ya ga dama ya yi ta a siffar sallar idi.
Idan kazo ka sami liman yana Tahiya sai ka zauna tare da
shi, idan ya yi sallama sai ka mike ka kawo raka'oinka biyu a siffar su
da ta gabata.
Wadansu Mas'aloli: A yanzu za'a kawo wadansu halaye da mutum
yakan samu kanshi a ciki idan ya zo ya samu tuni anfara sallah.
1. Idan mutum ya zo ya sami liman ya kammala kabarbari ya fara
karatu ya zai yi?. Amsa: Anan zaka yi wadannan kabarbarin,
kasancewar ba abune mejan lokaci ba, sannan sai ka raurari karatun
liman.
2. Idan ka zo ka sami liman ya fara kabarbari amma bai gamaba, to
anan zaka yi sauran kabarbarin da suka ragewa liman tare da shi,
sannan sai ka kawo wadanda suka wuceka, koda liman ya fara karatu,
5
kenan anan ba zaka yi wadanda suka wucekaba a lokacin kabarbarin
liman.
3. Idan kazo ka sami liman yana Ruku'u sai ka yi kabbarar harama
kadai ka bishi, ba sai ka kawo sauran kabarbarinba.
Tambihi: Ya kamata mu san girman wadannan salloli da matsayinsu a
addini, tunda har yakai Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su
tabbata a gareshi- yana cewa a fita sallar har da mata da kananan
yara, har mata marasa tsarki idan sun je sai su yi nesa da wurin sallah
idan anzo huduba suma sai su anfana. Kada mu sha'afa akan wannan
sallarne aka bada hutu duka kasa, aka rufe shaguna kada mutum ya
shagala a wannan lokaci da abinda zai hana mishi samun wannan
sallah. Sannan kuma a kula da yara da irin suturar da za su sa, domin
idan ka ga wadansu yaran ba kace 'ya'yan musulmi bane, wannan
baidace ba kuma baikamata, wasu kuma rawa kamar mazari, Allah Ya
sawwaka, amin.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata ya bayyana a
garemu cewar sallar idi ba wata gargajiya bace ibadace da Allah ya
shar'anta ta ta harshen fiyayyan halitta Annabi Muhammad –Tsira da
amincin Allah su tabbata a gareshi-, itako ibada anayinta akan yadda
aka tsarata ne, Allah ya karbi ibadarmu ya sa ayi sallah lamilafiya ya
tsaremu ya tsare mana imaninnu, amin.
Rbutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu