Labarai




HUKUNCE-HUKUNCEN ALWALA


Gabatarwa: Alwala ibadace mai zaman kanta wacce Allah


madaukakin sarki ya sahar'antata kafin gabatar da wadansu ibadu


musammamma sallah, mutum yana samun cikakken ladan alwala


idan ya yi ta cikakkiya, Allah madaukakin sarki ya saukar da


hukunce-hukuncen alwala a cikin littafinsa mai girma alkur'ani:


'' Ya ku dukkanin wadanda suka yi imani, idan kuka ta shi za


ku yi sallah to ku wanke fuskokinku da hannayanku zuwa gwiwar


hannu ku kuma shafa kawunanku da kafafanku zuwa idan sawu


(idan kafa)…'' Suratu Ma'ida, aya ta:6.


Tabbas wannan aya ta ti bayanin wajibcin alwala lokacin da


za'a yi sallah, kuma ta bayyana gabban da ya zama wajibi anwanke


ko kuma anshafa, sannan kuma ayar ta iya kance ko wanne


mahalli, sannan kuma Ma'aikin Allah –Tsira da amincin Allah su


tabbata a gareshi- ya bayyana siffar yadda alwalar take da


maganarsa da kuma aikinsa bayanin da yake gamsasshan bayani.


Ka sani lalle ita wannan alwala tanada falala da kuma sharudda


da kuma farillai sannan tana da sunnoni da kuma mustahabbai,


sharuddannan da farillai tabbas a tabbata ansame alokacin gabatar


da alwala iya gwargwado domin da sune alwala zata zama


karbabbiya, amma su sunnoni da mustahabbai suna cika alwalarne


ta inda matsayinsu bai kai matsayin sharuddai da farillaiba.


Falalar Alwala: Dudda cewa alwala wajibice wannan kadai ya


isheta samun matsayi a musulunci domin dukkan abinda akace


4


farillane to wannan matsayi ne me zaman kansa, bayan hadisi na


62 a cikin Muwadda'u Malik yana cewa: '' An karbo daga


Abdullahi As-Sunaabihi, lalle ma'aikin Allah –Tsira da amincin


Allah su tabbata agareshi yace:


''Idan bawa mumini ya yi alwala sai ya yi kuskurar baki


dukkanin laifukan dake bakin sun fice, idan kuma ya face laifukan


(Day a shaka) sun fice, to idan kuma ya wanke fuskarsa laifukan


da ke fuskar ta sa sun fice, har wadanda ke karkashi girar shi, idan


ya wanke hannayansa laifukan dake hannayansa sun fice, har


wadanda ke karkashi faratansa (jam'in farce), to idan kuma ya


shafi kanshi laifukan dake kan nashi sun fice har wadandake


kunnuwansa, to idan kuma ya wanke kafafuwansa duk laifukan


dake kafafuwan nasa sun fice, har wadanda ke karkashi farcen


kafafun nashi. Sannan kuma tafiyar da ya yi zuwa masallaci ya


zama wani karine da yake da shi''.


Lalle wannan bakamar falala bace da alwala take da shi,


domin mai alwala zai kasance yana kammala alwala zunubanshi


suna digewa a kasa, amma gudu ba hanzariba wannan ladan zai


tabbata ne ga wanda ya yi alwala da shara'a ta tabbatar da ita ba


wacce ya tsinta a kan titi ba.


Sharuddan Alwala: Sharuddan alwala sune abubuwan da ake so


mai alwala ya cika su kafin ya fara alwalar, sune kamar haka:


(1) Musulunci, kenan idan wanda ba musulmiba ya yi alwala


bata yi ba.


(2) Hankali, idan mahaukaci ya yi alwala itama bata yi ba.


(3) Wayau, idan dan karamin yaro mara dabara ya yi bata yi ba.


(4) Ruwan ya zama mai tsarki, idan ya zama ruwane mara


tsarki to alwalar bata yi, bayanai sun gabata akan hukuncehukuncen


ruwa.


5


(5) Ruwan ya zama na halas, idan ruwane da mutum ya sata ko ya same shi bata shar'an tacciyar hanyaba to alwalar bata yi ba. (6) Ya kasance mai tsarki, idan mai alwala ya kasance ya yi fitsari ko bayan gida misali wato ya kasance mara tsarki kafin alwala to ko ya yi alwalar bata yi ba. (7) Gusar da duk abinda zai hana ruwa shiga, kenan idan mutum ya kasance yaba sanye da wani abunda zai hana ruwa ya kai ga fatar jiki to dolene ya cire shi, kamar tabo (laka)…'. Farillan Alwala: (1) Niyyah: Domin a banbance wanda ya sa ruwa donin sanyaya jiki, ko domin gusar da datti, duk wannan ba niyyace ta alwalaba. (2) Wanke Fuska: ita kuma fuska ta bangaren tsawo tana farawane daga matsirar gashin kai (banda sanko) zuwa karshen mukamiki, amma ta fuskar fadi tana farawane daga kunnan dama zuwa kunnan hagu, wannan shine abinda yake amsa fuska, kenan dole mai alwala ya tabbatar ko ina ya sami ruwa kamar kasan haba, gefan ido da gefan kunne da matsa-matsin karan hanci, ayi hattara sosai domin wasu alwalarsu kamar alwalar yarace. (3) Wanke Hannaye Zuwa Gwiwar Hannu. Mai alwala mace ko namiji ya tabbata ya wanke hannayansa tun daga saman yatsunsa (farce-akaifa) harzuwa gwiwar hannu ya tabbata gwiwar ta shiga inda ya wanke, anamma akwai manya masu alwalar yara. (4) Shafar Kai: Ka tabbata ka hada yatsunka sannan kuma ka fara shafar daga goshi (daidai matsirar gashi) sannan ka shafa zuwa keya. (5) Wanke Kafa: Hakanan mai alwala ya tabbata ya wanke kafarsa harzuwa idon sawu, wato wadannan kasusuwan guba biyu dake gefan kafafuwa sun shiga cikin inda aka wanke.


6


(6) Cudanyawa: Mai alwala ya tabbata ya cudanya duk inda ya wanke ya dirza ruwa ya shiga ko ina. (7) Yinsu Baidaya: Abinda ake nufi shine alokacin da ka fara alwala to ka dakatar da komai sai ka kammala, amma kana alwala kana kuma wata sabga daban wannan bai yi ba. Mai alwala ya tabbata ya gabatar da wadannan ayyuka a lokacin da yake alwala ta yadda idan aka rasa daya daga cikin su to alwalarsa ta shiga hadari. Sinnonin Alwala: (1) Wanke Hannaye Kafin A Tsoma Su A Ruwa. Ta yadda mai alwala zai karkato butar alwala domin ya wanke hannayansa zuwa Ku'u wato wuyan hannu. (2) Kuskurar Baki: mai alwala ya tabbata ya sanya ruwa a bakinsa sannan kuma ya kada ruwan a baki, wannan shi ake kira da kuskurar baki. (3) Shaka Ruwa: Shine mai alwala ya shaki ruwa ruwan ya shiga hancin sa sosai, sai dai kawai idan yana azumine sai yayi kadan. Amma yadda mutane suke shafar hancinsu wai da sunan shaka ruwa wannan baiba. (4) Facewa: mai alwala zai shaki ruwanne da hannun dama sai ya sa hannun haku akan karan hancinsa, sannan sai ya fyato ruwan da ya shaka. (5) Shafar Kunne; Mai alwala ya tabbata ya shafi cikin kunnensa da wajan kunnan, zaka/ki sanya yatsanka 'yar-manuniya a cikin kunnan sannan ka babban yatsa a wajan kunnan sannan sai ka shafa, Dirkashi!. (6) Sake Taba Ruwa: Alokacin da zaka shafi kunne shin zaka shafi kunnanne da ragowar danshin hannuka da ka yi shafar kai da shi? Ko ko zaka sake taba ruwa na musamman domin shafar kunne, malamai sun karawa juna san, ko wanne ka yi ya yi daidai.


7


(7) Dawo Da Shafar Kai: Ka tsaya ka fahimta, ita shafar kai


farillace, amma dawo da shafar kai sunnace daga cikin sonnonin


alwala.


(8) Jeranto Farillai: Ta yadda zaka kawosu daya-bayan-daka


kamar yadda aka lissafosu, kada ka dauki na uku ya zama shine na


farko sannan ka biyo shi dana biyar, misali…'.


Wadannan matsayisu bai kai matsayin farillaiba, amma suna


cikin manyan abubuwan da suke cika alwala.


Mustahabban Alwala:


Wannan shi ke biye da mataki na sunnoni, kenan sunnoni sun fi


mustahabbai karfi, wadanda suke dukansu biyun farillai na


gabansu, babu daya daga cikin sunnoni ko mustahabbai da mutum


zai yi sakaci da su, domin kowannanmu so yake ya yi ibada


cikakkiya kammalalliya, to ko tunda hakane bai kamata yace ai


wannan mustahabbine ya daukeshi kamar wani kankanin abu.


Su mustahabban alwala suna da yawa, amma yanzu ga kadan


daga cikinsu:


(1) Anbaton Allah yace ''Bismillah'', adaidai loakcin da zaka


fara alwala, amma idan mutum ya manta saida yake tsakiyar


alwalar ya tuna bakomai sai ya yi a lokacin.


(2) Addu'a bayan kammala alwala, itace kuma kamar haka:


أشَْهدَُ أنَْ لا إلِهَ إلِا لَله وَحْدَه لا شَرِيكَ لهَ،ُ وَأشَْهدَُ أنََّ مُحَمَّدًا عَبْدُه وَرَسُولهُ،ُ الَلهَّمَُّ


اجَْعَلْنيِ مِنَ الَتوََّّابيِنَ، وَاجْعَلْنيِ مِنَ الَْمُتطََهرِِّينَ .


Ma'ana: ''Ina shaidawa da babu abinbauta da cancanta sai


Allah, kuma shi kadai yake bashi da abokin tarayya, kuma ina


shaidawa lalle (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma


manzansa ne, Ya Allah ! ka sanya ni daga cikin masu yawan tuba,


kuma ka sanya ni daga masu neman tsarkaka.''


(3) Karanta Ruwa: Bawai ana nufin mai alwala ya shasshafa gabbansa bane, a'a, ana bukatar ya yi anfani da ruwa amma kada


8


ya malalar da shi, domin yana daga cikin tsarin musulunci tattali da tsimi da tanadi. (4) Gabatar Da Asuwaki: Bayani kuma dama ya gabata akan asuwaki, ana yi da danye ko da busasshe, idan bai samuba sai ayi da yatsa, amma mu sani asuwaki daban kuskurar baki ma daban. Hakanan kuma ko da mutum lokacin sallah ya yi kuma amma yana da alwala to abinda ake so shine ya yi asuwaki. (5) Wuri Mai Tsarki: An so inda zaka yi alwala ya zama wurine mai tsarki. (6) Dama Kafin Hagu: abin nufi shine ka fara wanke hannun dama kafin hannun hagu, hakanan ka fara wanke kafar hagu kafin ta dama. (7) Jerantawa: Wato jeranta kowacce sunnah tare da 'yar-uwarta, kamar fara gabatar da kuskurar baki kafin shaka ruwa. (8) Wankewa Sau Uku: Ma'ana wanke wuraran da ake wankewa sau uku, mu sani wankewa sau uku zai zama mustahabbine idain wankewar farko ta game ko ina, amma idan ta farko bata gamaba to ta biyu tananan amatsayin wajibi, haka namma idan ta biyun idan bat agama ba to ta uku tana nan a matsayin wajibi. Ya zama wajibi mai alwala mace ko namiji ya kula sosai ya cuccuda inda ya kamata ya sa ruwa ba tare da barnaba. Amma shi kais au daya ake shafarsa, ba'a shafar kai sau uku. Sannan kuma mutum ya tabbata a wadannan wankewa da akace ya yi sau uku bai kara akan hakan ba, ya yi iya kokarinsa ya ga guda ukun sun kammala. Wadannan kadan kenan daga cikin mustahabban alwala, kuma wadannan bayanai sun mata kamar yadda suka shafi maza, sai dai mata su sani gashin kansu da sangalin hannuwansu duka al'aurane, saboda haka bai halatta su bayyanar da su ga maza, ken an idan zaki yi alwala sai ki sami wuri ki kawwame kanki.


9


Wadannan bayanai da suka gabata zasu haskaka mana yadda


alwala take, amma hanya mafi sauki shi ne a yi maka ita a aikace


ka gani domin haka sahabban ma'aikin Allah suka yi, an tambayi


Usman dan Affan dan gane da alwala sai yasa aka kawo mishi


butar alawala ya yi musu ita a aikace, yace kuma irinta ma'aikin


Allah ce.


Anan nake kira ga dukkanin limamai na juma'a dana sauran


masallatai da kuma malamai a jami'oi da kwalejin ilimi da kuma


malamai a sakandare da firamare da malaman islamiyyu da


malamai masu karantarwa a masallatai da masu wa'azi da sauran


wadanda abin ya shafa da su karantar da mutane ita wannan


alwalar a aikace kowa ya gani ya kuma yi tambaya, kada ka ga


kamar kowa ya gane da zarar ka yi ta a aikace zaka ga abin


mamaki, ni na taba gwada hakan, ita ibada sai an koyawa mutum


ba wai daka kawai shikenan ya iyaba, ko kuma ai shi iyaye da


kakanni duk musulmai ne sabo da haka ba sai ya koyaba, duk


wannan maganace ta wanda yake nesa da makaranta, kai da ganin


alwalar wani kasan bai je makaranta ba, Allah ya karba mana


ibadummu.


Kammalawa: Lalle wadannan bayanai sun kara tabbatar


mana ashe alwa abace da sai an tashi tuku domin a koyeta tana da


falala da kuma sharudda sannan ga farillai da sunnoni da kuma


mustahabbai, lalle ka nana bukatar malamai daga kowanne


bangare su tashi tsaye su karantar da al'umma wannan ibada a


aikace, domin a gudu tare a tsira tare.


Rbutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA