HUKUN-HUKUNCEN RUWA
(RUWA ABOKIN AIKI)
Kada ka manta sallah itace shisshike na biyu daga cikin
shikashikan musulunci guda biyar, itace kuma ginshikin addinin
musulunci duk wanda ya tsaida ita to ya tsayar da addini, haka kuma
duk wanda yabar sallah to yabar addini. Ita kuma sallah bata zama
sallah sai idan an yi alwala, an tsarkaka daga dukkanin najasa an
gusar da hadasi da kuma kabasi, wato dukkanin najasar da ta fito
daga jiki ita ake kira Hadasi, kamar mutum ya yi: fitsari, bayangida,
maziyyi…'' shikuma kabasi shine dukkanin najasar da ta shafi jikinka,
ko tufafinka, ko kuma wurin sallah. Gusar da wadannan abubuwa na
hadasi da kuma kabasi da aiwatar da alwala, basa tabbata sai da ruwa
mai tsarki kuma mai tsarkakewa, wato kenan rowan sai ya cika
sharudda biyu, na farko ya zama mai tsarki, na biyu kuma ya zama zai
iya tsarkake wani.
Allah madaukakin sarki yana cewa ''Kuma mun saukar da ruwa
daga sama wanda za'a yi tsarki da shi'' Suratl Furkan, aya ta:48.
Wannan ayar tana kunshe da hukunce hukunce da dama, daga ciki
akwa: Allah ya sanya ruwa shine abinda za'ayi tsarki da shi, ba'ayi da
yawu/miyau, abunmamaki sai mutum ya gama fitsa sai lakato
yawunsa ya goga abansa, lalle wannan ya yi nesa da makaranta. Abu
na biyu kuma shine ruwan sama ruwane da za'a yi tsarki da shi kai
tsaye, abu na uku dukkan ruwan da yake a cikakkiyar siffarsa ta ruwa
babu abinda ya canza shi to za'a yi tsarki da shi.
Abubuwan Da Suke Canza Ruwa. Abubuwan da suke canza ruwa
har ya zama wannan ba za'a yi ibada da shi ba (kamar alwala, tsarki..)
abubuwane guda uku, da zarar ruwa ya canza da daya daga cikinsu to
wannan rowan ba za'a yi ibada dashiba, wadannan abubuwa sune:
(1) Launi: Kazarar kalar ruwa ta canza ba yadda aka san ruwaba, ko
dai ya yi canza ya yi ja, ko baki, ko kore…' to wannan rowan ba za'a yi
ibada dashiba.
(2) Dandano: Idan dandanon ruwa ya canza to wannan ruwan ba
za'a yi ibada dashi ba.
(3) Shinshina: Hakana duk abinda ya jirta kanshin ruwa zuwa wani
abu daban to wannan ruwan ba za'a yi ibada da shi ba.
3
Idan ruwa ya canza da yada daga cikin wadancan abubuwa uku
kenan wadannan abubuwa sun jirkita shi ta yadda ba zai iya amsa
sunan ruwaba, domin ya zama Sobo (Zobo) ko kunu ko ruwannan
datti, to wannan ruwan ba za'a yi ibada da shiba. Amma idan daya
daga cikinsu ya fada cikin ruwa amma bai canza ruwanba ta dayan
wadancan fuskoki uku to babu abinda ya sami ruwan za'a yi aiki da
shi, kuma za'a ibada da shi. Wannan zai nuna kuskren da ake yi na
idan ansa hannu a ruwa ko mutum ya tara fanfo sai kasa hannu ko
kasa kwano ko buta sai ace za'a malalar da ruwan wai bashi da tsarki,
ko wata dabba da ake ci (wacce ba ta cin najasa) ta sha, ko kuma
dabba ta fada rijiya ko ma mutum sai ace wai za'a kwashe ruwan
rijiyar azubar (ko guga kaza) wannan duk bai halattaba a musulunci,
duk abinda ka ga ya cikin ruwa kuma ka cire shi ka ga babu abinda ya
canza rowan kwatakwata cikin wadancan abubuwa uku ka yi shiru da
bakinka aci gaba da aiki da ruwa.
Nau'ukan Abinda Ruwa Yake Canzawa Da Su: Canzawar ruwa da
muke Magana akanshi yana da kyau musan abinda ruwa yake da
canzawa da shi lura da hukunce-hukuncen kowanne, kamar haka:
- Da Makwancinsa: Idan ruwa ya canza kala ko dandano ko
shinshina, saboda inda yake, kamar Jarkasa, Farar kasa, Kanwa,
Kainuwa, Gansakuka… duk wadannan idan ruwa ya canza ya yi fari
saboda wurin farar kasace ko ya yi Jaa saboda wurin jarkasace ko
dandanonshi ya yi gafi saboda wurin kanwace ko tekuce ko wuraran
da ake hakar mai, duk wannan canza wad a ruwa ya yi babu abinda ya
shafeka zaka yi ibadarka da shi salin-alin alattacciyar ibada.
Kenan waccar Magana da aka yi sai idan ruwan ya canza da wani
abu na daban da ba makwancinsaba ta yadda zai iya yuwuwa a rabasu
amma a inda yake makwancinsane babu yadda za'a yi ka rabasu.
- Abu Mai Tsarki: Idan wani abu mai tsarki kamar gishiri ko yaji ko
miya ko sabulu ya zuba cikin ruwa amma kwatakwata bai canza
ruwanba to wannan ruwan za'a yi ibada dashi kamar yadda bayanai
suka gabata, amma idan sun canza ruwane to wannan rowan ba za'a
yi ibada da shi ba, amma za'a yi ayyukan gida da shi, kamar girki
wanki kunun-zaki d.s.
- Najasa: Idan najasa ta jirkita ruwa ta daya daga cikin abubuwannan
uku, to bai halatta a yi anfani da wannan rowan kwatakwata ba za'a yi
ibada da shi ba, kuma ba za'a yi wasu ayyuka nadaban da shiba kenan
kwararar da shi kawai za'a yi.
4
Lalle wannan ya nuna mana muhimmacin ruwa da kuma yadda
addinin musulunci ruwa shine abinda ba yi za su ibada da shi bai sa
musu feturba ko gas domin rahamar Allah ga bayinsa sai ya sanya
musu ruwa kuma ya sanya shi ya zama sinadarin rayuwa. Saidai
kawai idan mutum bai sami ruwaba a lokacinda zai yi tsarki sai ya yi
Istijmari, ko zai yi alwala kuma gashi babu ruwa sai ya yi taimama,
kamar yadda bayanansu zasu zo nan gaba.
Kammalawa: Daga wadannan bayanai da suka gabata zai nuna baka
yadda addinin musulunci ya baima ruwa kulawa ya kuma sawwake shi,
kuma wannan yana nuna mana yadda ya zama wajibi mu tashi musan
hukunce-hukuncen ruwa domin idan mutum bai sani ba sai ya debi
ruwan wanki ko kuma ruwan da ya gama wanka da shi bayan ya zama
sabulu ya ce zai yi tsarki da shi, domin wasu sun dauka ruwan alwala
shi ake bashi wannan hukunce-hukunce amma shi tsarki mutum zai
iya yi da ko wanne, alhali abin ba haka bane, Allah ya sawwake amin.
Allah Shi ne masani.
Rbutawa :
Malan Aliyu Muhammad Sadisu