Labarai




ABUBUWAN DA SUKE KAWO


BA’ADIYYAH A CIKIN


SALLAH


Gabatarwa: Ayanzu za’a kawo bayanaine akan


abubuwan da suke sanya ba’adiyyah kadai, da fatan


Allah ya an fanar da mu.


Manyan abubuwan da suke haifar da ba’adiyyah,


abubuwane kamar haka:


1. Kari (Da mantuwa)


2. Kokwanto


Wadannan sune manyan abubuwan da suke kawo


sujjadar ba’adiyyah, kuma akan su za muyi bayani a


wannan karon da izinin Allah.


Idan mutum ya yi kari a sallah da rafkannuwa ba wai


daganganba to ba’adiyyah zai yi, kamar mutumin da ya


kara raka’a a asuba ta zama uku, ko a magariba ta zama


hudu, ko kuma a azahar ko la’asar ko kuma lisha ta


zama biyar to hukuncinshi anan ya yi sujjadar


ba’adiyyah domin ya yi kari.


Haka mutumin da ya kara sujjada a raka’a ta zama


uku ko ya kara ruku’i ya zama biyu, amma da mantuwa


shi ma ba’adiyyah zai yi.


Wanda ya yi Magana a cikin sallah da mantuwa shima


ba’adiyyah zai yi, ko ya sallame daga raka’a biyu da


4


mantuwa, saida ya sallame ya tuna to anan sai ya ciko


ragowar raka’o’in sannan ya yi ba’adiyyah.


Wanda ya karanta surori biyu ko sama da biyu a


raka’a guda, ko ya fita daga surar da yake karantawa


zuwa wata surar ko kuma ya yi ruku’i kafi ya kammala


karatun surar duk anan ba komai akan shi, wato ba


kabaliyyah kuma ba ba’adiyyah, haka kuma wanda ya


yi nuni da hannusa ko da kansa kuma yana cikin sallah,


saidai yana rage lada.


Wanda ya maimaita karatun fatiha a raka’a duga da


rafkannuwa to shima zai yi ba’adiyyah.


Amma wanda ya tuna cewar bai karanta suraba bayan


kuma ya sunkuya zuwa ruku’u to anan bazai koma


tsaye domin ya karantaba, saidai bayan sallama ya yi


kabaliyyah, saidai idan ya tuna asurtawane ko


bayyanawa kafin ya yi ruku’i to anan zai sake karatun,


idan karatun surane zai sake karatunne ba wata


kabaliyyah ko ba’adiyyah, amma idan karatun fatihane


zai sake din amma kuma zai yi ba’adiyyah.


Wanda kuma ya mike bayan ya yi raka’a biyu amma


kuma bai zauna ba sai ya tuna kafin hannayansa da


gwiwowinsa su bar kasa shikenan sai ya koma ya zauna


ba komai akansa, in ko ha ya rabu da kasane to sai ya ci


gaba ba zai dawo ya zaunaba saidai zai yi kabaliyyah


domin ya rage wani abu a sallarshi, idan kuma bayan ya


mikedin ya dawo ya zauna bayan kuma ance da shi ya


wuce to anan sallarshi ta yi sai dai zai yi ba’adiyyah ne


saboda ya yi kari na wannan mikewar.


Wanda ya yi atishawa a cikin sallah baya


cewa ‘’Alhamdu Lillah’’ idan kuma har ya fadadin


sallah shi nanan kuma ba komai akanshi, sannan kuma


5


baya maida gaisuwa ga wanda ya gaida shi saboda yana cikin sallah.


Wanda kuma ya yi hamma yana cikin sallah sai ya rufe bakinsa shikenan.


Wanda kuma ya sa wata kalma alokacin da ya karatu wacce ba ta Kur’ani ba zai yi ba’adiyyah ne, amma idan ta Kur’anice babu komai akanshi, saidai idan ya canza lafazi ko ya bata ma’ana to anan sai ya yi ba’adiyyah. Lalle wadannan bayanai za su sa mutsaya mu gyara karatummu na sallah da kuma limamammu, domin ana tafka kurakurai a karatuttukan sallah.


Amma kuma wanda ya manta da ruku’i saida yana sujjadah ya tuna to sai ya koma tsaye, sannan an so ya sake wani abu na karatun sallah, sannan sai ya yi ruku’in ya kuma ci gaba da sallar, bayan ya kammala sai ya yi ba’adiyyah.


Sannan wanda ya manta sujjada guda bai yi ta biyun ba, saida ya mike sannan ya tuna to kawai zai dawo ya zaunane sannan ya yi wannan sujjadar, saidai idan ya yi wannan zaman kafin ya mike to kawai sai ya wuce zuwa gabatar da wannan sujjadar kai-tsaye, bayan ya kammala saii ya yi ba’adiyyah.


Wanda kuma ya manta da sujjadu biyu sai bayan ya mike sannan ya tuna to kawai zai tafi zuwa gabatar da wadannan sujjadunne ba tare da ya zauna ba, sannan ya yi ba’adiyyah.


Abu na biyu daga cikin abubuwan da suke janyo ba’adiyyah a cikin sallah shine :-


Kokwanto:


Idan mutum ya yi kokwanton sallarshi ta cika ko bata cika ba sai ya kawo abinda ya yi kokwanton sannan ba’adiyyah, misali; Idan ya yi kokwanton shin ya yi


6


sujjadar ta cika ko bata cika ba, sai ka cika sannan ka yi ba’adiyyah.


Idan mutum ya yi kokwanton wannan raka’ar itace ta hudu ko itace ta uku sai ya barta itace tau kun sai ya kawo cikon ta hudun sannan ya yi ba’adiyyah.


Mutum mai yawan wasuwasi to abinda da ake so daga gareshi shine yabar wasuwasin ya kakkabeshi daga zuciyarsa ba zai kawo abinda ya yi kokwanton akanshi ba, sai bayan ya sallame sai ya yi ba’adiyyah, shin kokwanton akan karine ko akan ragi. Wannan yana nuna mana mafita daga mutanan da suke da yawan kokwanto da wasuwasi, Allah ya yaye musu mu kuma ya tsaremu, amin.


Idan mutum ya yi shakkun yana da hadasi ko bai da shi? Sannan sai ya dan yi tunani kadan sai kuma ya samu tabbas akan yana da tsarki to ba komai akanshi, dudda ya yi hakan ne a cikin sallah.


Yin rafkannuwa a sallolin da ake ramakwansu daidaine da wadanda ake yin su cikin lokaci ba banbanci, kenan suma kabaliyyah da ba’adiyyah tana shiga cikinsu.


Idan mamu ya yi lafkannuwa alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, misali; da aka yi zaman tahiya na farko kawai sai ka yi sallama ka dauka an gama sallar, ko kuma kuna sujjada sai ka ji wani ya yi kabbara sai ka taso daga sujjadar ka dauka liman sai ka ga ba haka bane sai ka koma sujjadar duk bakomai akanka, saboda kana bayan liman.


Idan masabuki (wanda yake ciko sallarsa bayan sallamar liman) ya yi rafkannuwa a lokacin da yake kawo raka’o’in da suka wuce masa bayan sallamar liman to fa anan hukuncinsa hukuncin mai sallah ne shi


7


kadai saboda haka ba’abinda liman ya dauke masa domin tuni liman ya sallame shi, saboda haka idan kabaliyyah ta kamashi a wannan lokacin sai ya yi ta hakama idan ba’adiyyah ce.


Idan kabaliyyah ko ba’adiyyah ta kama liman to ta shafi mamu ko tare dashi abin ya faru ko ba tare da shi bane.


Idan kabaliyyah ta kamaliman to mamu zai yi tare da liman, sannan idan liman ya sallame sai ya mike ya kawo ragowar raka’o’insa. Amma idan ba’adiyyah ce to bazaka yi tare da liman ba har sai ka ciko ragowar abinda ake binka ka yi sallama sannan ka yi ta, kasan dalilin da liman ya yi ta ko baka saniba.


Idan mutum ba’adiyyah ta kamashi ta bangaran liman, sannan da ya tashi yana kawo abinda ya saura akansa sai kuma kabalillah ta same shi to anan idan ya yi kabaliyyar ta wadatar, ba sai ya yi ba’adiyyar ba.


Wanda ya yi kokwanton ‘‘shin yanzu yana wuturine ko yana raka’a ta biyun shafa’ine’’? to sai ya barta itace raka’a ta biyun shafa’in, sannan bayan ya sallame sai ya yi ba’adiyyah sai kuma ya mike ya kawo wuturin.


Idan kuna sallah tare da liman sai shi limamin ya yi rafkannuwa ta yadda ya yi kari ko ya rage to mamu tasbihi zai yi, sai kace ‘’Subhanallahi’’, idan liman ya kara sujjada ta zama uku to abinda zaka yi shine tasbihi ba zaka yi sujjadar ta uku tare da shi ba.


Idan liman ya tashi zuwa raka’a ta biyar to duk wanda ya tabbatar itace ta hudun sai ya bishi, haka kuma duk wanda yake kokwanto; shin ta biyarce ko ta hudu, to shima zai mike ya bishi. Amma duk wanda ya tabbatar wannan raka’ar itace ta biyar to ba zai bi shi ba sai ya yi zamanshi.


8


Idan liman ya sallame kafin sallah ta cika, to wadanda ke bayansa sai su yi masa tasbihi wato su ce ‘’Subhanallah’’, idan liman ya gasgata wanda ya yi tasbihin sai ya mike ya ciko sallar, sai kuma a yi ba’adiyyah, idan kuwa liman yana kokwanto akan hakan, sai ya tambayi mutane biyu adilai, kuma ya halatta su yi Magana anan, idan kuwa shi liman yanada yakini akan sallar ta cika to sai ya yi aiki da yakinin na sa, ya ajiye tanbayar, saidai idan mutanen dake bayansa sun ta tasbihi sai ya bar yakinin na sa, ya koma zuwa ga abinda suke a kai, kamar yadda mai Akhdari ya zayyano.


Kammalawa: Wannan shine gwargwadon abinda ya samu na bayani akan rafkannuwa a cikin salloli na farilla, ko na ramuwa ko wadanda ake yin su a lokacinsu, da fatan zamu kara kusantar inda malamai suke. Akaro na gaba da izinin Allah madaukakin Sarki zamu kawo bayanaine dangane da rafkannuwa a cikin salloli na nafilfili. Ga dukkan mai tambaya kofa a bude take, fatammu shine Allah ya karbi ayyukammu ya kuma sanya mu cikin wadanda ya yiwa rahama.


Kammalawa: Adaidainan zamu dakata kan abinda ya shafi yin ba’adiyyah ta sanadiyyar kari da mantuwa, a karo na gaba bayanai za su zo akan ba’adiyyah ta sanadiyyar kokwanto, da fatan mun anfana.


Rubutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu





ABUBUWAN DA SUKE


KAWO KABALIYYAH


Gabatarwa: Ayanzu za’a kawo bayanaine akan


abubuwan da suke sanya kabaliyyah kadai, sannan bayan


haka a kawo bayanai akan abubuwan da suke sanya


ba’adiyyah suma su kadai, fatammu a tsaya a karanta


bayanan a natse kuma a fahimcesu, idan akwai abninda ya


shigewa mutum yana da dama ya yi tambaya, da fatan Allah


ya ganar da mu.


Abubuwan Da Suke Kawo Kabaliyyah: Manyan


abubuwan da ke sawa a yi sujjadar Kabaliyyah su ne;


1. Ragi.


2. Ragi Da Kari.(Alokaci guda)


Dukkan mutumin da ya yi ragi a sallar sa to kabaliyyah ta


kamashi, kamar:


1. Karatun Sura: Idan mutum ya manta a raka’ar farko ko


a ta biyu bai karanta suraba kawai shi da ya karanta fatiha


sai ya yi sujjada, to wannan kabaliyyah ta kamashi.


2. Asurtawa A Inda Ake Bayyanawa: Duk wanda ya yi


karatun sallah sirrance a inda ake bayyanawa, to wannan


shima kabaliyyah ta kamashi.


3. Fadin ‘’Sami’allu Liman Hamidah’’ haka wanda ya


manta da fadin wannan kalma kabaliyyah zai yi domin rage.


4


4. Tahiyar Farko: Duk wanda ya barta to ya yi ragi a


sallarsa kabaliyyah zai yi.


5. Zama Domin Tahiyyar Farko: Haka duk wanda ya


manta da zaman tsakiya shima kabaliyyah zai domin ai shi


ya rage manyan sunnonine ma guda biyu. Zama domin


tahiyyar da kuma ita kanta tahiyyar.


6. Tahiyyar Karshe: Itama dukkan wanda ya manta bai yi


ta ba to kabaliyyah ta kamashi.


7. Zama Domin Wannan Tahiyyar Ta Karshe: Shima


zaman duk wanda ya manta ya barshi to kabaliyyah zai yi.


Kada ku sha’afa zaman da ya karu akan gwargwadon


sallama shine ake Magana, amma shi zama gwargwadon


sallama wannan wajibine, idan mutum ya barshi kabaliyyah


ko ba’adiyyah bata daukeshi.


Sannan dukkanin wadannan abubuwa da aka bari, ana


maganane idan akabarsu da mantuwa ba wai daganganba.


Ragi Da Kari. (Alokaci guda)


Hakanan dukkan mutumin da ya yi ragi a cikin sallah


kuma ya yi kari a cikin sallar to shima kabaliyyah zai yi,


misali mutumin da ya manta bai yi zaman farkoba wato da


ya kammala raka’a biyu maimakon ya zauna ya yi tahiyyah


sai ya manta ya mike zuwa raka’a ta uku, sannan kuma da ya


raka’oin mai makon ya zauna sai ya ci gaba ya kara wata


raka’ar ta zama hudu idan a magaribane ko ta zama biyar


idan a azaharne ko la’asar ko lisha. To ka ga wannan a sallah


guda ya yi ragi domin bai yi zaman farkoba kuma ya yi


Karin raka’a to shima kabaliyyah zai yi shikenan ya gyara


sallar shi.


5


Wanda sujjadar kabaliyyah ta kamashi amma sa ya manta bai tuna ba sai bayan da ya yi sallama, shikenan sai ya yi ta a wannan lokacin ta zama ba’adiyyah kenan kuma sallar ta yi, to amma idan bai tuna da hakanba sai bayan wani lokaci ko ma har ya fita daga masallaci to anan sujjadar ta baci, haka itama sallar zata iya baci idan ya rage sunnonin da suka kai uku ko sama da haka.


Rafkannuwar da mamu ya yi alokacin yana bayan liman to liman ya dauke masa, saidai idan mamun ya rage farillane kama ya bar sujjada, ko sallama..’’.


Idan mamu ya yi rafkannuwa ko ya yi gyangyadi ko ma aka matse shi bai sami damar yin ruku’i ba sannan kuma ba’a raka’ar farko bace to anan idan ya tabbatar zai iya samin liman kafin ya dago daga sujjada ta biyu ta wannan raka’ar sai ya yi ruku’in ya riski limamin, amma idan ya tabbata ba zai same shi ba, sai ya bar ruku’un, wannan raka’ar kuma sai ya ajiyeta gefe guda sai ya rama wata raka’ar a matsayin wannan din bayan sallamar limamin nasa, babu kabaliyyah ko ba’adiyyah.


Idan kuma ya yi rafkannuwane ya bar sujjada ko aka matseshi ko ya yi gyangyadi har liman ya tashi zuwa wata sabuwar raka’ar to anan idan ya tabbatar zai riski liman kafin ya yi ruku’i sai ya yi sujjadar, amma idan ya tabbata ba zai iya riskar liman ba sai kawai ya hakura ya ci gaba da bin limamin sai ya rama raka’ar da bai yi mata sujjada ba, bayan liman ya sallame.


Kada mutum ya yi mamaki ya ji an ce ‘an matse shi’ ka dauki al’amarin da fadi bawai iya garin ku ba, domin idan Allah ya kaika kasa mai tsarki zaka ga irin cunkoson da ake


6


yi alokutan sallah, musamman idan ya yi daidai alokacin Hajji ka je ko Umarah.


Kammalawa: Wadannan kadan kenan daga cikin abubuwan da suke sabba sujjadar Kabaliyyah, da mun anfana kuma zamu kara kusantar malamai, a karo na gaba za’a kawo bayanaine akan abinda ya shafi sabuban sujjadar ba’adiyyah, da fatan Allah ya kai mu lokacin ta re da imani, amin.


Rbutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA