Labarai




 Shinfida:


Dakin Ka’abah shi ne gini na farko a doron wannan kasa, malaman tarihi sun


karawa juna sani akan waye farkon wanda ya gina Ka’abah, shin Annabi Adam 


ne ko Mala’iku? Ko kuma ma Annabi Ibrahim  ne. Falalar wannan daki tana da


matukar yawa har ma ta shafi falalar birnin na Makkah ya zama birni mai albarka


mai daraja, wanda duk ya yi nufin aikata barna to za’a dandana masa azaba mai


radadi.


Wannan daki ya taba rushewa ya zamana Annabi Ibrahim ne da kuma dansa


Annabi Isma’il عليهما السلام suka daga shi kamar yadda Allah yake cewa:





Allah madaukakin sarki ya sanya wannan daki na Ka’abah ya zama shi ne


mafuskantar dukkan musulmi (Alkiblah) a dukkanin lokutan sa, kamar sallah ko


yanka ko addu’a da dai sauransu.


Yin sallah a wannan wuri ya fi yin sallah da sauran ibadu a ko’ina na duniya. To da


zarar maniyyata sun isa birnin Makkah mota ta sauke su a masauki to kada su


manta suna cikin harami ne kodai da hajji – ga wanda ya yi niyyar ifradi, ko ya yi


niyyar hajji da umarah a hade wato kirani kenan - ko kuma da umarah ga wanda ya


yi niyyar tamattu’i, ammadai kowa na cikin harami, to daga nan sai a nufi wannan


daki mai alfarma, to da an shiga masallacin Ka’abah kada a manta da kafar dama


ake shiga masallaci dawafi kuma za’a fara, saidai idan ana bin mutum salloli ko


kuma ya tarar ana sallah sai ya gabatar da wannan sallar, daga nan kuma ya sha


ruwan zamzam sai dawafi.


DAWAFI


3


 Shar’antuwarsa da kuma inda ake yin sa.


(a) Shar’antuwarsa: Yin Dawafi a Ka’abah ya tabbata ne daga littafin Allah mai


girma da kuma Sunnar Ma’aikin Allah , Allah madaukakin sarki yana cewa:





Ma’ana: Kuma su yi dawafi a dadaddan dakin nan”. Suratul Hajji, aya ta:29.


Kenan maniyyaci da Hajji ko da Umarah ya tabbatarwa zuciyar shi wannan aiki da


yake gabatarwa ibada ce ba wasa ba ne.


(b) Inda ake yinsa. Ana yin dawafi ne a Ka’abah kadai a fadin wannan duniya,


wannan ibada ta dawafi tana daga cikin ibadu kalilan da wannan wuri shi kadai ya


kebanta da su, Allah madaukakin sarki yana cewa:





Ma’ana: Kuma su yi dawafi a dadaddan dakin nan”. Suratul Hajji, aya ta:29. Kenan


ba ya halatta a yi dawafi a ko’ina a fadin duniya inba’a Ka’aba ba.


 Nau’ukansa.


(1). Dawafin Umarah.


(2). Dawafin Isowa (Dawaful Kudum).


(3). Dawaful Ifadha/Ziyarah.


(4). Dawafin Nafila.


(5). Dawafin Bankwana (Dawaful Wada’i).


Wadannan su ne nau’ukan dawafi da ake da su, kuma yanzu za’a kawo bayanan


kowanne da kuma matsayinsa.


DAWAFI


4


(1). Dawafin Umarah: Wannan dawafi ne ga wanda ya dauko Umarah yake gabatar da shi ko kirani, kuma rukuni yake a cikin aikin Umarah, idan mutum bai yi shi ba to ba shi da umarah. Da zarar ka shiga birnin Makkah, an sauke ku a masauki kun isa Ka’abah to idan ana gabatar da sallar farilla ko ana bin ku sallar farilla ita za ku fara gabatar wa daga nan kuma sai ku yi dawafi, idan kuwa ba sallah ake yi ba kuma ba’a binku sallah to kai tsaye Ka’abah za ka dosa domin gabatar da dawafi. Shi wannan dawafin a farkon shigarka Ka’abah shi ne matsayin raka’a biyu da ake yi inda wani masallaci mutum ya shiga.


(2). Dawafin Isowa (Dawaful Kudum): Wannan dawafi shi ne dawafin isowa Ka’abah ga wanda bai shigo da umarah ba sai dai shi nau’in hajjin da ya dakko shi ne: Ifradi, domin shi wanda ya yi Tamattu’i, ba shi da Dawaful Kudum, domin ya riga ya gabatar da Dawafin Umarah, haka ma wanda ya yi niyyar Kirani.


Mazauna birnin Makkah ba su da dawafil kudum, kuma shi dawafil kudum lokacin sa yana wucewane da yin tsayuwar Arafat, kenan an so a gabatar da shi farkon shigarka Makkah domin Ma’aikin Allah  idan ya shiga Makkah farkon abinda yake farawa da shi shi ne dawafi.


Shi dawaful kudum wajibine ga dukkan mai ifradi, ta yadda idan ya barshi to sai ya yi fidiya, wannan amazahabin Malikiyya kenan, amma a Hanafiyya da Shafi’iyya da kuma Hanabila su suna ganin wannan dawafi na Kudum sunnah ne ba wajibiba, saboda haka kenan a mazahabarsu ba zai yi fidiya ba.


Amma mace mai al’ada ko biki to babu komai akanta ko wanda yake tsoron wucewar tsayuwar Arafat.


(3). Dawaful Ifadha/Ziyarah: Shi ne dawafin da maniyyaci da aikin hajji yake yi, kuma shi rukuni ne daga cikin rukunan aikin hajji, kenan idan babu shi to babu aikin hajji.


DAWAFI


5


Lokacinsa: Bayan rana ta fito a ranar sallah, wato ranar 10 ga zul hajji kenan. A wannan rana maniyyaci yana da ayyuka kamar haka:


(1) Jifan jamratul Akabah.


(2) Yanka.


(3) Aski.


(4) Dawafi.


(5) Sa’ayi.


To abinnda aka fi so ya gabatar da su kamar yadda suka zo a jere. Idan maniyyaci ya jinkirta yin dawafi har saida ya dawo Makkah bayan kammala zaman muna babu wani abu, saidai bai yi ‘Tahalluli babba’ ba. Domin idan ya aikata biyu daga cikin wadancan abubuwa hudu (akan lissafa dawafi da sa’ayi kamar abu guda, domin ba’a yi sa’ayi sai an yi dawafi) to ya yi ‘Tahalluli karami’ zai iya shafa turare ya sa kayan gida idan namiji ne ko ta sanya nikabi idan mace ce, amma saduwar aure ba ta halatta har sai an yi wannan dawafi, shi yasa ake cewa da shi Tahalluli babba, idan aka yi dawafi.


Lokacin karewarsa: Dawafin Ifadha wanda yake rukuni ne a aikin hajji, ba shi da takamaiman lokacin karewa, saidai maniyyaci yasan cewa sai ya yi shi ne sannan ya kammala aikin hajji, idan bai yi shi ba kodako bayan sallah da kwana arba’in ne ko abinda ya fi haka to ya sani bai kammala aikin hajji ba, kuma alfarmar hajji tana tare da shi, wannan yana kasancewa ne musamman ga marasa lafiya ko ya manta.


An tambayi Imamu Malik –Allah ya yi masa rahama- Dan gane da mutumin da ya manta bai yi Dawaful Ifadha ba, har ya fita daga Makkah ya koma garin su?. Sai ya ce: Ni ina ganin idan bai sadu da iyali ba to ya dawo ya yi dawafin ifadha, idan kuma ya kasance ya sadu da iyali to ya dawo ya yi dawaful Ifadha din, sannan kuma ya yi umarah sai ya yi hadaya, kuma ba zai sayi dabbar hadayar a Makkah kuma ya yankata a Makkan ba, saidai idan bai taho da hadayar daga inda ya dakko umarah ba (mikati kenan ba) to sai ya sayeta a Makkah sannan ya fitar da ita zuwa


DAWAFI


6


wajan harami, sai ya taho da ita daga nan zuwa Makkah sannan sai ya yanka. (Muwatta’u Malik, Kitabul Hajji, Babi Na: 50).


(4). Dawafin Nafila: Shi ne dawafin da mutum yake yi a lokacin zaman shi a Makkah, cikin kayan gida, saidai amma fi so ga wanda yake bako ya yawaita yin dawafin nafila, domin kada ka manta babu inda ake yin wannan dawafi a fadin duniya sai a Ka’abah, a dawafin nafila ba’a sassarfa kuma zagaye bakwai ake yi sai a yi sallah raka’a biyu, sannan idan mutum zai kara sai ya sake yin bakwai sai ya yi sallar dawafin, kamar yadda bayanai za su zo da izinin Allah.


(5). Dawafin Bankwana (Dawaful Wada’i): Wannan shi ne dawafin da duk mutumin da yake bako wato ba mazaunin Makkah ba zai gabatar a lokacin da ya kammala aikinsa zai koma garinsu/kasarsu, sai ya zama karshen rabuwarsa dawafi ne Ka’abah, domin ba zai yi wannan dawafin ba sai ya tabbatar da lokacin tafiyarsu ya yi.


Malamai sun kara wa juna sani akan wannan dawafi, wadansu suka ce wajibine, kenan duk wanda bai yi shi ba sai ya yi fidiya in banda mai al’ada, wadansu kuma suka ce Sunnah ne ba wajibi bane.


Lalle maniyyaci ya yi iya kokarinsa wurin aikata wannan aiki cikin natsuwa da kulawa da kuma sanin hukunce-hukunce.


Wadannan su ne nau’ukan dawafi da ake da su, da fatan an fahimce su.


 Wajibansa da kuma sunnoninsa:


Shi dawafi yana da wajibai da dole a same su, sannan kuma yana da sunnoni da suke bin wajibai a karfi, kana kuma yana da mustahabbai.


- Wajibabbun Dawafi:


(1) Tsarki: Dole ne mai dawafi ya tabbata ya tsarkaka daga Hadasi da kuma Khabasi, domin idan ba shi da tsarki to dawafinsa bai yi ba, idan mace tana


DAWAFI


7


al’ada zata yi duk abin da mai hajji yake yi saidai ba zata yi dawafi ba har sai ta sami tsarki kuma ta yi wanka, kenan aduk lokacin da take da tsarki kada ta yi wasa sai ta gabatar da dawafinta. Hakanan mutumin da yake dawafi sai alwalarsa ta karye to zai fita ne ya sake ta ko da yana kan zagaye na bakwai ne, sannan idan ya dawo sai ya faro dawafin daga farko.


Imamu Malik yake cewa: Dukkan wanda wani abu da yake karya alwala ya same shi a lokacin yana dawafi a Ka’abah ko yana Safa da Marwa ko tsakanin haka, to fa duk wanda hakan ya same shi kuma a lokacin ya yi wani sashi na dawafin ko ma ya gama shi duka amma bai yi raka’o’i biyu da ake yi bayan dawafi ba to wannan zai yi alwalane ya kuma sake dawafin da kuma wadannan raka’oin biyu. Amma ita Safa-da-Marwa to abinda ya same shi na warwarewar alwala ba zai warware masa shi ba, saidai ba zai fara Sa’ayi ba sai yana da alwala. (Muwatta’u Malik, Kitabul Hajji, Babi Na:37).


(2) Suturce Al’aura: Domin ba ya halatta a yi dawafi tsirara.


(3) Sanya Ka’abah a Hagu: Domin ba’a sanya Ka’aba a dama lokacin dawafi.


(4) Yin Dawafin Zagaye Bakwai: Kenan duk wanda ya yi kasa da haka bai yi ba, ko kuma ya yi sama da haka dagangan shi ma bai yi ba.


Imamu Malik yake cewa: Dangane da mutumin da ya yi rafkannuwa har ya yi zagaye takwas ko tara, sai ya ce: Zai yanke ne (nan take) idan ya tabbatar da hakika ya kara, sannan ya sallaci raka’a biyu, ba zai lissafa wannan da ya kara ba, kuma ba zai taba yiwuwa ba ya yi dori akan wadannan taran da ya yi ba ya ce zai karo wata bakwai din, in ya gama (wato bakwai biyu a hade) sai ya yi sallah raka’a biyu-biyu ba. Domin Sunnah a dawafi ita ce; Kowacce bakwai a yi mata raka’a biyu.


Kuma dai Malik din yace: Duk wanda ya yi shakka a dawafinsa, bayan ya kammala raka’o’in dawafi to fa zai koma ne har sai ya cika dawafinsa akan


DAWAFI


8


yakini sannan ya sake wadannan raka’o’i biyun, domin babu wata sallah da ake yi wa dawafi sai bayan an kammala bakwai. (Muwatta’u Malik, Kitabul Hajji, Babi Na:37).


(6) Fitar da dukkanin jiki daga Ka’abah: Kenan ba’a yin dawafi a cikin Ka’abah, ko mutum ya tsallaka ta Hijr, domin idan mutum ya yi haka bashi da dawafi.


(7) Yin sallah raka’a biyu: Bayan da mutum ya kammala dawafinsa zagaye bakwai to sai ya yi sallah raka’a biyu, zai yi su ne a bayan ‘Makamu Ibrahim’, idan kuma akwai cunkoso sai ya yi a duk inda ya sawwaka a gareshi a masallacin. Wadannan raka’o’i biyu zai yi su ne akowanne dawafi ya yi.


- Sunnonin Dawafi:


(1) Tafiya: Wato ba’a gudu kuma ba’a sauri, wannan idan dawafin ba na Umarah ba ne ba kuma dawafin Kudum ba ne, idan kuwa sune to sassarfa ake yi a ukun farko.


(2) Sunbantar Bakin Dutse: Wannan kuwa zai yi shi ne da bakinsa muddin zai iya kaiwa kuma ba zai cutar da wasu ba a zagayen farko, idan kuwa ba zai iyaba sai ya shafe shi da hannunsa ko wani abu, sai ya sunbanci wannan hannun ko wannan abun, idan shi ma hakan ya tsananta sai ya nuna shi, to amma a wannan lokacin ba zai sunbanci abinda ya yi nuni da shi ba. A lokacin da zai yi sumbantar sai ya ce;


بِسْمِ اَللهِ، وَاللهُ أَكْبَرُ.


Amma a lokacin da zai yi nuni sai ya ce: اَللهُ أَكْبَرُ.


(3) Shafar Rukunul Yamani: Ana kiran wannan kusurwar da wannan sunan ne domin ita ce kusurwar dake bangaren kasar Yaman, kuma daga wannan kusurwar sai Hajarul Aswad, ita wannan kusurwar shafarta ake yi ba’a sumbantarta kuma ba’a sumbantar abinda aka shafeta da shi. A Ka’aba ba’a shafar ko’ina sai Hajarul


DAWAFI


9


Aswad da kuma wannan kusurwar, haka kuma ba’a sumbartar ko’ina sai Hajarul Aswad.


(4) Addu’a: Domin kowa yasan wannan wurin wurin addu’a ne a shar’ance. Sannan babu wata addu’a da aka warewa kowanne zagaye na dawafi, ballantana a ce zagayan farko ga addu’arsa haka na biyu ….’. ka roki Allah bukatunka na duniya da lahira.


(5) Yin Salati ga Ma’aikin Allah .


(6) Yin Sassarfa: Wannan ga maza kadai yake banda mata, kuma ana yin shi ne a zagayen ukun farko, a dawafin umarah ko na Kudumi kadai. To amma idan mutum ya manta bai yi a ukun farkon ba babu komai akansa, kuma ba zai ce zai yi a na hudu ba.


 Inda ake fara Dawafi da kuma inda ake gamashi.


Ana fara dawafine daga inda bakin dutse yake wato Hajarul Aswad, saboda haka dukkan wanda bai fara daga nan ba to ba zai lissafa wannan zagayan ba, saboda haka wanda ya yi na biyu shi ne na farko a shar’ance. Haka kuma kammalawa dole sai mutum ya kai ga daidai wannan Hajarul Aswad din a zagayan shi na bakwai sannan ya kammala sai ya nufi inda zai yi sallah.


Gangancin da wasu maniyyata suke yi shi ne; da zarar sun zo dab da wurin kammalawa din sai su kama hanyar sa’ayi.


Shi wannan hajarul aswad da ake fara dawafi ta inda yake kuma ake kammalawa a nan, kuma shi kadaine inda ake sunbanta a Ka’abah yana da falala da daraja ta musamman. A shekara ta: 317 (bayan hijira) ne Abu Tahir Aljuba’i ya jagoranci ‘yan shi’a Karamidawa ( ةطمارقلا ) a ranar tarwiya (8, ga Zul Hajj) suka shigo haramin Makkah suka yi wa mahajjata mummunan kisa, suka kuma dauke dutsan suka gudu da shi, sai bayan shekaru ashirin da biyu (22) al’ummar musulmi suka dawo da shi.


DAWAFI


10


(A duba الكامل في التاريخ Juzu’i na: 8, shafi na:207. Da kuma سير أعلام النبلاء , Juzu’i na: 15, shafi na: 320, da المغني Tahkikin: Abdullahi bin Abdulmuhsin Atturki, Juzu’i na: 5, Shafi na:214).


Shi hajarul aswad yana dab da komar Ka’aba ne.


 Siffar yadda ake Dawafi.


Da zarar Allah madaukakin sarki ya kai mu wannan wuri mai albarka, ka isa masallacin Ka’abah ka sha ruwan zamzam ka yi sallolin da suke kanka to zaka wuce inda Ka’abah take ne kaitsaye, ka natsu ka gano ta inda Hajarul Aswad yake, kuma ka bude kafadarka ta dama, domin a wannan dawafin kadai ne ake bude kafada aduk aikin hajji baki daya.


Da ka je inda yake ka sunbance shi – idan da sarari ka yi kuma wannan addu’ar: بسم الله والله أكبر ko kuma ka yi nuni to sai ka fara kewayawa kana mai yin sassarfa, tunda wannan shi ne dawafinka na umarah (idan Tamattu’i ko Kirani) ko kuma na Kudum (Idan Ifradi ka yi), sai ka zagayo amma ka fi kusantar Ka’abah muddin akwai damar hakan, za ka zagayo har ka zo daidai inda kusurwar dake kusa da hajarul aswad wato kusurwar rukunul yamani sai ka shafe shi amma ba zaka sunbanta ba, sai daga nan ka karanta addur’ar:


چ ۈ ٷ ۋ ۋ ۅ ۅ ۉ ۉ ې ې ې چ


Ma’ana: “Ya Allah Ubangijin mu! Ka ba mu anan duniya abu maikyau, a lahira ma abu maikyau, kuma ka tsare mu daga azabar wuta”. Ita zaka dinga karantawa har ka kai hajarul asawad.


Daga nan sai ka karasa hajarul aswad, to yanzu ka gama guda daya kenan, haka zaka ci gaba da yi har ka kammala bakwai ciccif, sannan sai ka koma inda makamu Ibrahim yake –inda sarari- ka yi sallah raka’a biyu.


DAWAFI


11


To idan kana cikin wannan dawafi sai aka tada sallah ta farilla to zaka tsaya ne a nan inda kake ka sallaci wannan sallar sannan bayan ka kammala sallar sai ka ci gaba da dawafinka.


 Wasu daga cikin hukunce-hukuncen Dawafi.


1. Mutum ya tabbata ya kawo aikinsa na dawafi kamar yadda aka zayyana a shar’ance.


2. Mace mai al’ada ko mai biki zata yi dukkan abinda mai hajji yake yi saidai ba zata yi tawafi ba.


3. Idan mutum bai yi dawafi ba to alfarmar dawafin tana kansa, saboda haka ko ya koma garins u ko kasarsu sannan ya tuna to zai dawone ya yi dawafin, wannan idan bai sadu da iyali ba, amma idan ya sadu da iyali to zai dawo ne da umarah, saboda haka sai ya taho da hadaya daga mikati kamar yadda bayanai suka gabata, irin wannan yana faruwa ga maralafiya ko mantuwa.


4. Idan mutum ya tara da iyali bayan ya yi aski ya yi yanka kafin ya yi dawafi aikin hajjinsa ya rushe.


5. Idan mutum yana cikin dawafi sai alwalarsa ta karye to lissafin dawafinsa ya rushe, zai fita ne ya yi alwala sannan ya koma ya fara daga farko.


6. Idan mutum bai yi dawafin Ifadha ba har saida ya zo tafiya gida sannan ya yi to ya wadatar masa da dawafin bankwana.


7. Idan mutum yana dawafi sai aka tayar da sallah to zai bi sallar ne, sannan bayan ya idar da sallar sai ya dora a inda ya tsaya kafin fara sallar.


8. Idan mutum bai fara dawafi daga hajarul aswad ba to ba zai fara lissafa wannan zagayan ba.


9. Idan mutum ya zo zagaye na bakwai sai bai karasa hajarul aswad ba to dawafinsa bai yi ba.


10. Idan mutum yana dawafi sai lissafi ya rikice masa to sai ya yi gini a binda yake da yakini akansa, kamar yana kokwanto maikarfi akan wannan zagayan


DAWAFI


12


shi ne na shida ko shi ne na biyar, to anan sai ya bari akan shi ne na biyar, sai ya kawo na shida da na bakwai.


11. Idan mai dawafi ya tsallaka hijir to bai kewaya Ka’abah bakidayanta ba saboda haka ba shi da dawafi.


12. Idan mutum yana dawafi sai ya yi Magana babu abinda ya taba dawafinsa, saidai ya sani ba’a dawafi ana fira, ko da kuwa na nafila ne.


13. Idan mai dawafi ya kammala to ya tabbata ya kawo sallah raka’a biyu kodako wannan dawafin na nafila ne.


14. Shi dawafi bakwai ake yi sai a yi sallah ra’aka biyu kodako sau nawa kake so ka yi.


15. Idan mace mai al’ada bata samu ta yi dawafin bankwana ba to babu komai akanta.


16. Idan ankwantar da mutum a asibiti bai yi dawafi ba to ya sani yana cikin alfarmar hajji ko yaushe ya sami sauki.


17. Fitar da maniyyi ta hanyar mafarki kafin dawafi ba ya bata hajji, saidai ayi wankan janaba.


 Ladubban Dawafi.


- Rage surutu.


- Sanin hukunce hukuncensa.


- Natsuwa.


- Ba’ayin talbiya a dawafi.


- Yawaita yin dawafin ga wanda yake ba dan Makkah ba.


- Yawaita addu’a.


- Kada ka cutar da wani.


 Kammalawa:


DAWAFI


13


Zuwa nan muka zo karshen wannan tsokaci da fatan Allah ya kai mu lafiya ya kuma dawo da mu lafiya, ya saka da alheri ga dukkanin wadanda suka shirya wannan haduwa. Kuma daga karshe ina jan hankalin maniyyata akan:


1. Yin kowacce ibada domin Allah.


2. Lizimtar tsoronsa.


3. Rikon abinda ya kaika.


4. Riko da abinda aka karantar da kai.


5. Kada ka dauki wannan tafiya a matsayin yawon bude ido.


6. Lizimtar ibada a wadannan masallatai. (Makkah da Madina).


7. Sanya lokacin ziyara ya kasance da safe, domin kada ka rasa sallah a masallacin Ma'aiki .


8. Kimanta lokaci.


9. Abokantaka da wanda yake da himma.


10. Daraja wannan wuri domin Allah ya daraja shi


11. Ba'a dawafi a Madina ko ma a wani wuri domin a Ka'abah kadai ake dawafi, Allah madaukakin Sarki yana cewa: چ ڭ ڭ ۓ چ .


وصلى الله وسلم على نبينا محمد وعلى آله وصحبه وسلم


DAWAFI


14


Abubuwan Dake Ciki:


 Gabatarwa. ………………………………………………………………………….. 2


 Shinfida. ………………………………………………………………………………. 3


 Shar’antuwarsa da kuma inda ake yin sa. ………………………….…. 4


 Nau’ukansa. ………………………………………………….……………………… 4


 Wajibansa da kuma sunnoninsa. …………………….……………………. 7


 Inda ake farashi da kuma inda ake gamashi. ………………………. 10


 Siffar yadda ake Dawafi. …………………………………………….………. 11


 Wasu daga cikin hukunce-hukuncen Dawafi. ………….………….. 12


 Ladubban Dawafi. ……………………………………………………..………… 13


 Kammalawa. ………………………………………………………….…………… 14


 Abubuwan dake ciki. ……………………………………………………….….. 15


DAWAFI


15



Posts na kwanan nan

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA