Labarai

Takaice


sakon littan "Hakkoki wadanda drah


-tsarin halittar rai- take kira gare su,


,"kuma shari'a ta tabbatar da su


wallafar Shehun malami Ibnu


Usaimin, Allah Ta'alah ya


masa rahama


01 / 30


Wanda ya takaita shi : Dr. Haisam Sarhan


Tsohon Malami a sakandaren masallacin


Annabi SAW, kuma Mai sanya ido akan


ayyukan Ma'ahadus Sunnah


Hausa -  -


Ka haska barikod - sarhaan.com


Shine ka bauta masa Shi kadai; baShi da abokin tarayya, sai


ka kasance bawa a gare Shi, mai kan-kan-da kai, mai tawali'u,


kana aiki da umurninSa, kana hanuwa da haninSa, kana mai


gaskata labarinSa, akan akida madaukakiya, da yin imani da


gaskiya, da aiki na kwarai mai amfani, akidar da kashin


bayanta shine, son Allah da girmama Shi, alfanonta kuma


.tsarkake bauta ga Allah da juriya akan haka


1- Hakkin Allah Ta'alah


Shine darajanta shi da jin alfarmarsa da girmama shi, irin


girmamawar da ta dace da shi, ba tare da wuce iyaka ko


takaitawa ba, da gaskata shi cikin abinda ya bada labarinsu


na al'amuran da suka shude, da wadanda ake fuskanta, da


yin aiki da abinda ya yi umurni da shi, da nisantar dukkan


abinda ya yi hani akansa, ya tsawatar, da imani da cewar lallai


shiriyarsa itace mafi kammaluwar shiriya, da aiki don bayar da


.kariya ga shari'arsa da shiriyarsa


2- Hakkin Manzon Allah :


shine ka musu biyayya, ta hanyar kyautata musu a zance da


aiki, da dukiya da kuma jiki, ka rika aiki da umurninsu matukar


.babu sabon Allah a cikin haka, matukar babu cutuwa a ciki


3- Hakkokin iyaye biyu :





1- Shine tarbiyya; ta hanyar habaka riko da addini da kuma


kyawawan dabi'u a cikin zukatansu, har su kasance akan


yanayi yardajje.


2- Sai ciyar da su, da kyautatawa, ba tare da ballagazar da


dukiya ko gazawa ba.


3- Kada ya fifita wani akan wani a yayin da yayi nufin basu


kyauta.


4- Hakkin 'ya'ya :


Shine ya sada zumuntan makusancinsa da kyautatawa, ta


hanyar ka amfanar da su da matsayinka, da kuma amfani na


jiki, da amfanarwar dukiya, gwargwadon yadda karfin


dangantakar ta hukunta, da kuma gwargwadon bukata


(talauci).


5- Hakkokin dangi makusanta :


Shine kowanne ya yi zamantakewa da dayan da kyautatawa,


kuma ya bayar da hakkin da ya wajaba akansa, cikin sauki da


dadin rai, ba tare da jin an tursasa masa ba, kuma ba tare da


kwauro ba.


Daga cikin hakkin mace, akan mijinta: Ya tsayu da abinda ya


wajaba akansa na ciyar da ita, shayar da ita, tufatar da ita,


bata wurin zama, da abinda yake biye da haka. Kuma ya rika


adalci a tsakanin matansa biyu ko fiye.


6- Hakkin ma'aurata biyu :





Daga cikin hakkokin miji akan matarsa: ta masa biyayya ba a


cikin sabon Allah ba, ta rika kiyaye sirrinsa da dukiyarsa, kada


ta yi wani aikatau wanda zai sanya mijin ya kasa samun


cikakken jin dadinsa da ita.


Hakkokin mabiya akan shugabanninsu shine; Su tsayu wurin


sauke amanar da Allah Ya dora musu ita, kana Ya lazimta


musu tsayuwa da ita, na tausayin mabiya, da jagorantarsu


wurin tafiya akan mikakkiyar turba wacce zata lamunce musu


samun maslahohin Duniya da lahira, wanda hakan kawai zai


tabbata ne ta hanyar bin tafarkin muminan farko (sahabbai).


Hakkokin shugabanni kuma akan mabiyansu na farko shine:


Kaiwa makura wajen rike musu amanar abinda mutum ya


jibinta na lamuransu, da fadakar da su idan suka gafala, da


yin addu'a a gare su idan suka kauce ma gaskiya, da bin


umurninsu, matukar ba cikin sabon Allah ba, da taimakonsu.


7- Hakkokin shugabanni da talakawa :


shine wanda gidansa yake kusa da kai, za a kyautata masa


da abinda aka samu iko, na dukiya, matsayi, da amfani,


sannan a nisantar da nau'ukan cutarwar zance ko aiki a gare


shi.


8- Hakkokin Makwabci :





1- Idan makwabcinka, danginka ne a nasaba, kuma musulmi,


to yana da hakkoki iri uku akanka; Hakkin makwabtaka, da


hakkin 'yan'uwantaka, da hakkin musulunci.


2- In kuma musulmi ne, amma babu wata dangantaka ta jini a


tsakaninku, to yana da hakkoki biyu: Hakkin makwabtaka, da


hakkin musulunci.


3- Haka, idan akwai 'yan'uwantaka a tsakaninku, saidai ba


musulmi ba ne, nan ma yana da hakkoki biyu, hakkin


makwabtaka, da hakkin 'yan'uwantaka.


4- Idan kuma ba makusanci ba ne, kuma ba musulmi ba ne,


to yana da hakki daya rak; wato hakkin makwabtaka. right: the


right of the neighbor.


Daga ciki: akwai yin sallama da amsata, na biyu kuma idan ya


gayyace ka ko ya kira ka, to ka amsa masa, idan ya nemi


nasiharka ka masa nasiha, Idan ya yi atishawa ya ce, Alhamdu


lilLahi, to ka masa addu'ar neman rahama «YarhamukalLahu»,


idan ya yi jinya ka ziyarce shi, idan ya rasu ka raka gawarsa. Ka


nisanci cutar da shi. Hakkokin musulmi akan musulmi suna


dayawa, saidai ma'anar da zata hade wannan lamari itace fadin


Annabi  : "Musulmi dan'uwan musulmi ne", domin duk lokacin


da mutum ya tsayu wurin bayar da hakkin wannan


'yan'uwantakar, to zai yi wa musulmi kokarin samar masa


kowane alheri, ya kuma nisanci dukkan abinda zai cutar da shi.


9-Hakkin sauran musulmai gabadaya :





Wajibi ne ga shugaban musulmai ya yi hukunci ga wadanda


ba musulmai ba da hukuncin musulunci a lamarin rai, dukiya,


da mutunci, ya tsayar musu da haddi cikin abinda suka


kudurta haramcinsa, kuma wajibi ne akansa ya basu tsaro da


kariya, kuma ya kiyaye musu duk wata cutarwar da zata fado


musu.


Kuma wajibi ne, a samu banbanci tsakaninsu da musulmai ga


lamarin tufafi, kuma dole ne akansu kada su bayyanar da


abin kyama a musulunci, ko kuma wani abu wanda yake


alamta addininsu, kamar sharewa da giciye.


10- Hakkokin wadanda ba musulmai ba :


Ma'ahadus Sunnah


0504250337 mahadsunnah


mahadsunnah.com Shafin Shehi na yanar gizo-gizo


alsarhaan.com



Posts na kwanan nan

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA