Labarai




TSARKI DA YADDA AKE YINSA


Shinfida: Mu sani ya 'yan-uwa masu albarka,


wannan addini na musulunci addinine da yake


cikakken addini ta kowanne bangare, bai takaitu ga


alwala da sallaba kadai, ya shafi kowanne bangare


na rayuwa, kamar tsafta kiwon lafiya zamantakewa,


kasuwanci taimakon juna, tsare-tsaren gudanarwa


dadai sauransu.


A yanzu zamu kawo bayanaine da suka shafi


tsarki, dame-dame ake yiwa tsarki? Me rashin


tsarkin yake jawowa? Ya ladubban yin tsarkin suke?


Ya ake shiga makewayi? Dadai sauran wadansu


batutuwa da suke da alaka da wannan maudu'i, da


fatan Allah ya yi mana jagora ya kuma fahimtar da


mu.


Abubuwan Da Akewa Tsarki: ana yin tsarki ne


daga dukkan abinda ya fito ta daya daga mafitar


guda biyu ko ma ta duka inbanda hutu (tusa). Kenan


ana yiwa fitsari, bayangida maniyyi maziyyi jinin


al'ada….tsarki, kawai dai idan mutum yana da alwala


sai ya yi tusa to alwalar kawai zai sake ba sai ya


dauki butu ya yi tsarki ba.


Hukuncin Tsarki: Tsarki wajibine, saboda haka


dukkan wanda dayan wadancan abubuwa da


makamantansu suka same shi to dole ya tabbata ya


gabatar da ya yi tsarki.


Abinda Ake Tsarki Da Shi: Abinda ake tsarki da


ashar'ance shine ruwa mai tsarki mai tsarkakewa,


4


wannan shi ake kira Istinja'u. Saidai idan mutum bai


sami ruwanba sai ya yi da duwatsu a kalla guda uku,


idan ya ga na ukun ya fito a bushe ba wata laima


shikenen, idan kuma akwai laima to sai ya kara su


kai biyar wuturi ake bukata (3,5,7,9…) wannan


kuma ana yinshi a fitsari ko bayan gida, sannan idan


ka sami ruwa ba sai ka sake ba, wannan hukunci shi


ake kira Istijmari, ka samu ka hada duka a lokaci


guda, misali idan ka yi bayan gida sai kasa tsinke ko


takarda mara rubutu sai ka share sannan sai ka biyo


shi da ruwa. Kenan ba'a tsarki da yawu (miyau).


Kada asha'afa, idan aka yi la'akari da abinda ya


fita da kuma abinda ya fantsamo maka, za'a raba


tsarki zuwa gida biyu:


(1) Tsarkin Hadasi: Shine tsarkin abinda ya fita


daga dayan mafita guda biyu, kamar fitsari,


maziyyi…'.


(2) Tsarkin Kabasi: Shine tsarkake abinda ya taba


jiki ko tufafi ko kuma wuri, kuma ko wannensu baya


yiwuwa said a ruwa mai tsarki mai tsarkakewa.


Amma idan aka yi la'akari da girma ko rashin


girma za'a kasa tsarki zuwa gida biyu shima:


(1) Babba wanda ake kira Hadasul Akbar: Ankira


shi babbane domin ba'a tsarkaka daga gareshi sai an


yi wanka, kamar fitar maniyyi, ko saduwa, ko


daukewar jinin al'ada ko na biki.


5


(2) Karami wanda ake kira Hadasul Asghar:


wanda yake tsarki ko alwala ta wadatar, kamar


fitsari ko maziyyi.


Yadda ake yi: Da farko mutum ya wanke


hannunsa na hagu kafin ya sa a wurin da zai wanke,


domin hannun sa ya koshi da ruwa, sannan sai ya


wanke wurin fitsari. Daga nan kuma sai ya fara


wanke wurin bayan gida musamman idan ya kaatse,


ana bukatar mutum ya wanke al'aurar sa baki


dayanta musamman idan maziyyi ne ya fita.


Ladubban Zagawa (Fitsari Ko Bayangida): Akwai


tsari na ladubba da musulunci yake da su a lokacin


da mutum ya ke niyyar kewayawa, wannan zai nuna


maka cewa musulunci ya karade komai:


(1) Anbaton Allah: Ana bukatar kafin ka shiga ka


ambaci Allah domin ba'a anbaton Allah a makewayi,


kuma ka nemi Allah ya tsareka da sharrin aljanu,


domin irin wadannan wurare matattarace ta su,


yace:





Ma'ana: Da sunan Allah, Ya Allah lalle ni ina


neman tsarinka (Ka tsareni) daga aljanu maza da


kuma aljanu mata.


Idan kuma zaka fito sai kace:





Ma'ana: (Ina neman) gafarar Ka, Dukkan godiya


ta tabbata ga Allah wanda ya rabani da wannan


kazantar kuma ya bani lafiya.


6


Ka sani ba'a shiga bayi da dukkan wani da yake dauke da sunan Allah, kamar zobe, ko carbi…'. Hakanan kuma ba'a katse bayangida da dukkan wani abu da yake da sunan Allah. (2) Fara Gabatar Da Kafar Hagu Lokacin Shiga, kafar dama kuma lokacin fita. (3) Ayi A Tsugunne: kada mutum ya yi fitsari ko bayan gida a tsaye, sai dai idan wurin kangone ko yana tsoron fitarin ya fallatso masa, sannan ba wanda zai ganshi ya samu ya yi a tsaye. (4) Tabbatuwa A Cikin Sutura: ana bukatar kada mutum ya yaye al'aurar sa tun yana tsaye, sai ya tsugunna ya yi dab da kasa sai ya daga suturarsa, domin ba'a yarda wani ya ga al'aurar wani ba in ba miji da mataba, amma halin ko unkula da wasu suke nunawa na bayyanar da al'aurarsu ga kowa muddin jinsi gudane wannan baidaceba, sai ka ji wana yace 'Ai duka mazane, abinda kake da shi ina dashi', wannan ba koyarwar musulunci bace, haka namma mata, wannan zai kaika ka ga maza sun tube suna wanka lokaci guda a dakin wanka guda, haka namma mata, wai sun dauka abinda yake haram shine namiji ya ga al'aurar mace ko mace ta ga al'aurar namiji, kai wani lokaci kana tafiya a cikin mota sai kai arba da wani gabjejen kato yana wanka a rafi, wani kuma a gefan titi ya kafe mashin ko ya je kayan tallansa, duk wadannan bakewawan halaye bane, mutum musulmi ya nisance su. (5) Yafi Bada Karfi A Kafarsa Ta Hagu: Kenan abinda akafi so shine mutum ya fi bayar da karfinsa a kan kafarsa ta hagu.


7


(6) Ya Bude Tsakanin Cinyoyinsa: kenan kada ya matse, ballantana ya sa matsattsiyar tufa wacce idan yana fitsari na gaban ne kawai zai fita, sannan idan ya mayar cikin wando sauran ya gangaro, Allah ya sawwake. (7) Ya Nisanci Inda Ruwa Yake: musulunci bai yadda mutun ya yi fitsari ko bayan gida a inda ruwa yakeba ko kusa dashi, dan wannan zai haifar da cututtuka. (8) Ya Rufe Kansa: Ana son wanda yake bayangida ya rufe kansa a daidai lokacin da yake yi, domin koda wani ya yi kuskuren ganinsa to shi bai ganshiba, abin zai zo da sauki, amma ba zaka ji dadiba kana bayan gida ka hada ido da wani, wanda zai iya zama dalibinka ne ko suruki ko da..,'. (8) Kada Ayi Magana: anhana mutum yana bayan gida yana Magana, sai dai idan akwai dalili mai kwari, kamar ka ga makaho ya nufi rijiya ko karamin yaro…'. (9) Kada A Tari Iska: an hana idan mutum zai yi bayan gida a dawa (daji) an hana ya tari iska, domin zai bsowa jama'a warin bayan gidansa, kenan sai ya yi nesa, ya kuma duba ina iska take kadawa. (10) Kaucewa Rami: Ba'a yarda idan za ka yi fitsari ko bayangida ka yi aramiba saidai idan kai ka haka, domin bakasan mekecikin ramin ba, takan yiwu akwai mugun abu.


(11) Kaucewa Wuraran Tsinuwa: Wadannan wurare sune wuraran da mutane suke yawan


8


tsinema dukkan wanda ya yi musu bayangida a wurin, wadannan wurare sune: (a) Inda mutane suke zama su huta, jikin bangone ko karkashin bishi komadai inane. (b) Kan hanya: Akwai rashin mutunci mutum ya zo kan hanya ya gicciya bayangida, wannan dabi'a musulunci bai yarda da ita ba. ( c ) Mashayarruwa: Hakanan baya cikin karantarwar musulunci mutum ya zo inda al'umma suke diban ruwa rafine ko wani gulbi ko gindin fanfo komadai inane ya aikata wannan ta'asa. Wadannan wurare uku musulunci ya hana a aikata wannan danyan aiki a wurin, domin mutum yana jawa kansa tsinuwa, Allah ya tsaremu. (12) Nesa Da Jama'a: ana bukatar dukkan wanda zai yi bayan gida ya yi nesa da jama'a ta yadda ba za su ganshiba kuma ba za su ji nishin shiba, ba zai yi kyauba ace kana bayan gida mutane suna ganinka ko suna jin nshinka, ko da a bayan bishiya ko ganyan kargo sai ka boye, amma sau da yawa mutane suna tafiya a mota da motar ta tsaya sai ka ga kowa ya tsaya dab da motar, sannan ba za'a tafi a barshiba. (13) Kada Ya Fuskanci Alkibla: wato inda mutum yake kallo lokacin sallah, kuma kada ya juya mata baya, wannan idan a dajine, amma idan a gidane to da sauki.


Abubuwan Da Rashin Tsarki Yake Hanawa: kamar yadda bayani ya gabata cewar tsarki wajibine, to mu


9


sani idan mutum bashi da tsarki bai halatta a gareshi wadannan abubuwanba: (1) Sallah: Bai halatta ga wanda bashi da tsarki ba ya yi sallah nafila ko farillah. (2) Dawafi: Kewayan Ka'aba kenan a birnin makkah, saboda haka idan mutum yana dawafi sai ya yi tusa to dawafisa ya warware sai ya sake alwala domin ita tusa ba'a yi mata tsarki. (3) Sujjadar Tilawa: Wato sujjadar da mutum zai yi ida yana karatun Alkur'ani mai girma sai ya kai wadansu gurare, domin ba shi da tsarki, dudda malamai sun kawa juna sani akai. (4) Kabli Ko Ba'adi: Bai halatta ga wanda bashi da tsarki ba ya yi kabli ko ba'adiba har sai ya yi tsarki, idan akce kabli ana nufin sujjadar da mutum zai yi kafin ya yi sallama, amma idan ake ba'adi to wacce zai yi bayan sallama. Idan jiya ba'adi ta kamaka sai kuma ka manta baka yi to ya halatta ka yi ta a yanzu idan kana da tsarki. (5) Daukar Alkur'ani Mai Tsarki: idan mutum bashi da tsarki to sai yi tsarki kafin ya taba wannan littafi mai tsarki.


Kammalawa: ina fatan wadannan takaitattun bayanai sun warkar da abinda ake bukata, kuma sun nuna lallai addinin musulunci gamamman addinine da ya shafi komai ya kuma yi bayani akan komai, domin idan yakai bayan gida sai an nunawa mutum yadda ya kamata ya yi to ashe wannan ba karamin gata musulunci ya yi mana, muna godiya ga Allah.


10


Rbutawa :


Malan Aliyu Muhammad Sadisu



Posts na kwanan nan

TAMBAYOYI DA AMSOSHI ...

TAMBAYOYI DA AMSOSHI A CIKIN MAS’ALOLIN AKIDAH DA KAFIRCI

BIDI’A MA’ANARTA – NA ...

BIDI’A MA’ANARTA – NAU’IKANTA – HUKUNCE-HUKUNCENTA

MUSULUNCI ADDININ MAN ...

MUSULUNCI ADDININ MANZANNIN ALLAH

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA