Labarai

GINSHIQAI GUDA SHIDA DON KOMAWA ZUWA GA ALLAH A LOKACIN TSANANI


(MAGANA KAN CUTAR CORONA)


TA BABBAN MALAMI KUMA DR


SALEH BN ABDULAH BN HAMAD AL-USAIMY


WAKILI A QUNGIYAR MANYAN MALAMAI, KUMA MALAMI A HARAMAI GUDA BIYU


ALLAH YAI MASA GAFARA SHI DA IYAYENSA DA MALAMANSA DA MUSULMAI BAKI XAYA





3


Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin kai.


Godiya ta tabbata ga Allah, yana aikata abin da yaso, kuma yana hukunta abun da ya so,kuma na shaida babu wani abun bauta da gaskiya sais hi kaxai wanda bashi da abokin tarayya. Irin shadawar kaxaitawa, kuma na shaiada Annabi Muhamad bawansa ne kuma Manzonsa, Alah kayi Salati a gare shi da Alayansa da Sahabansa, Salati wanzajje kuma dawwamamme har zuwa ranar Al-qiyama


Bayan haka


Yaku ‘Yan Uwana Muminai, lallai buqatar Bawa zuwa ga Allah maigirma da Xaukaka lalura ce da kuma ta lazimce shi, Allah Maxaukakin Sarki ya ce:





”.YÃ KŨ MUTÃNE! KŨ NE MÃSU BUKÃTA ZUWA GA ALLAH, KUMA ALLAH, SHĨ NE MAWADÃCI, GÕDADDE ”. (Faxir:15)


Kuma wanan lalurar tana daxa qarfafa lokacin Lalura, da halin tsanani a wajen baki xayan Mutane; saboda Mutane idan aka tava su da cuta ko kuma tsanani sukan buqatu zuwa Ubangijinsu Maigirma da Xaukaka, buqatuwa Mai Girma.


Kuma wanan Buqatuwa tana daxa futowa fili a cikin Shari’a, cikin ginshiqai guda shida masu girma:


4


GINSHIQI NA FARKO: IMANI DA QADARAR ALLAH MAXAUKAKIN SARKI:


Allah Madaukakin Sarki ya ce





“KUMA YA HALICCI KOWANE ABU, SABODA HAKA YA QADDARA SHI QADARTAWA” (Al-furqan: 2) kuma Allah Madaukaki ya ce Lalle Mũ,





“KÕWANE IRIN ABU MUN HALITTA SHI A KAN TSÃRI“. (Al-qamar: 49) saboda haka ya dace ga Bawa yayi imani da qaddarar Allah Maxaukakin Sarki, Kuma ya karveshi da haquri. Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: ’’Lamarin mumini da ban mamaki yake, dukkannin al’amurransa alheri ne ,idan abin farinciki ne ya same shi sai ya godewa Allah sai ya zamar masa Alheri ,idan kuma na sharri ne ya same shi sai ya yi hakuri, shi ma sai ya zamar masa Alheri, sai dai hakan baya kasancewa ga kowa sai ga Mumini’’.


Saboda haka ya dace ga Mumini ya raya Zuciyarsa da imani da qaddarar Allah mai girma da xaukaka,kuma dukan Al-amari nasa ne haka Hukunci ma hukuncinsa ne, kuma duk abunda ya so shi zai wakana, kuma duk abunda bai so ba ba zai wakana ba


5


GINSHIQI NA BIYU:CIKAR TAWAKALI GA ALLAH DA KUMA MIQA DUKAN AL-AMARI ZUWA GARE SHI:


Allah Madaukakin Sarki ya ce





‘’WANDA DUK YA DOGARA GA ALLAH SHI KUMA ZAI ISAR MASA ‘’ [Al-Xalaq: 3] ai shi ne mai isar masa kuma Allah Madaukaki ya ce Ka ce:





"BÃBU ABIN DA YAKE SÃMUN MU FÃCE ABIN DA ALLAH YA RUBŨTA SAHÕDA MU. SHĨ NE MAJIƁINCINMU. KUMA GA ALLAH, SAI MŨMINAI SU DÕGARA." [Al-tauba:51]. Saboda haka ya dace ga Bawa ya dogara da Allah Mai girma da Xaukaka, kuma maida Al-amuransa gareshi, kuma kada ya dogara da wasu abubuwa na rayawar zuciya Vatattu; saboda kada ya zamanto Mutum rarrauna, wanda kowane irin Mumunan tunani da zai shigar masa, saboda Annabi –Tsira da Amincin Allah su tabbata a gareshi- “Qarqarfan Mumini yafi Al-kairi da Soyuwa a wajen Allah sama da Mumini Rarrauna, kowanne yana da Al-khairi” .


6


GINSHIQI NA UKU: Shi ne komawa zuwa ga Allah SWT da kuma tuba zuwa gare shi


Allah Madaukaki ya ce





“¥ARNÃ TÃ BAYYANA A CIKIN ƘASA DA TẼKU, SABÕDA ABIN DA HANNÃYEN MUTÃNE SUKA AIKATA. DÕMIN ALLAH YA ƊANƊANA MUSU SÃSHIN ABIN DA SUKA AIKATA, ƊAMMÃNINSU ZÃ SU KÕMO “. [Al-Rum: 41] ai cewa varna ta yaxu acin halayyar a tsandauri da kuma cikin kogi, cikin abincinsu, da abun shansu, da lafiyar su, da Qarfinsu, kuma da baki xayan Al-amuransu.


Kuma dalilin haka: abun a Hannu Mutane suka aikata; saboda Allah ya xanxana musu Uquba don su koma ga Allah.


Ibn Abbas ya ce cikin abunda Ibn Munzir ya rawaito: “KO SA TUBA”


Haka kuma dai a cikin daga gare shi: “KO SA DAWO KAN HANYA” [ Al-rum: 41]. Ai ga barin Savo1


Saboda haka lallai ya kamata Mutum yayi qoqari wajen komawa ga Allah Maigirma da xaukaka, da kuma tuba zuwa gare shi, kuma ya sani cewa Allah ya yalwata masa a cikin Ajalinsa, da kuma futar masa da Alamomin Qarfinsa; don bawa ya wa'azantu kuma ya koma zuwa ga Allah


Allah Madaukakin Sarki ya


1 Littafin da ya gabata


7





CE KUMA LALLE MUN AIKA ZUWA GA AL'UMMAI DAGA GABÃNINKA, SAI MUKA KÃMÃ SU DA TSANANI DA CŨTA, TSAMMÃNINSU ZÃ SU ƘANƘAN DA KAI, TO, DON ME, A LÕKACIN DA TSANANINMU YA JẼ MUSU BA SU YI TAWÃLU'I BA? KUMA AMMA ZUKATANSU SUN ƘẼƘASHE KUMA SHAIƊAN YÃ ƘAWÃTA MUSU ABIN DA SUKA KASANCE SUNÃ AIKATÃWA. SA'AN NAN KUMA ALÕKACIN DA SUKA MANTA DA ABIN DA AKA TUNÃTAR DA SU DA SHI, SAI MUKA BŨƊE, A KANSU, ƘÕFÕFIN DUKKAN KÕME, HAR A LÕKACIN DA SUKA YI FARIN CIKI DA ABIN DA AKA BA SU, MUKA KÃMÃ SU, KWATSAM, SAI GÃ SU SUN YI TSURU TSURU. [Surat Al-an'am: 42-44 ] Ai Azaba ta zo Musu da Azabar Allah Maigirma da Xaukaka basu shirya ba; saboda su wannan lokacin suna masu yankewar haso daga kowane irin Al-khari


Saboda idan Allah ya bayyanawa halittarsa wani abu na Qarfinsa, abunda ya kamata su koma zuwa gare shi, to ya wajaba suyi gaggawar Tuba zuwa ga Allah SWT in ba haka ba to suka juya baya ga barin hakan, kuma zukatansu suka qeqashe, kuma Shaixan ya Qawata Musu abuda suke aikatawa; to Allah SWT zai buxe musu qofofin Yalwa, har sai same su kuma suna ta farin ciki da su, sai allah ya kama su kamu mai tsanani wanda ba zasu tsira ba daga shi.


8


ASALI NA HUXU: YA KAMAT GA BAWA LALLAI YAYI RIQO DA SABABI


Saboda Allah Maxaukaki ya ce:





"KUMA KADA KU JEFA HANNAYENKU XUWA HALLAKA" [Al-baqara: 195] Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Kada a haxa Mara lafiya da Mai Lafiya" 5


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Ku guji mai kuturta kamar yadda kuke gujewa Zaki" 6


Annabi tsira da amincin Allah su qara tabbata a gare shi ya ce: "Idan kuka ji faruwar Annoba a wani gari, to kada ku shige shi, kuma idan ta faru a gari kuna cikinsa, to kada ku futa daga cikinsa"


Saboda haka ya kamata ga Bawa lallai ya riqi Sababai da zasu kare shi daga abun da yake tsoro ga Kansa na Illa ko rashin lafiya


9


ASALI NA BIYAR: YA KAMATA LALLAI MUTUM YAYI QOQARIN RIQO DA HANYOYIN ILIMI WAXANDA SUKA DAME SHI DAGA BANGARORIN DA SUKA QWARE, KUMA YA NISANCI JITA JITA:


Allah Madaukakin Sarki ya ce:





"KUMA IDAN WANI AL'AMARI DAGA AMINCI KO TSÕRO YA JE MUSU, SAI SU WÃTSA SHI. DÃ SUN MAYAR DA SHI ZUWA GA MANZO DA MA'ABŨTA AL'AMARI DAGA GARE SU, LALLE NE, WAƊANDA SUKE YIN BINCIKENSA, DAGA GARE SU, ZÃ SU SAN SHI. KUMA BÃ DÕMIN FALALAR ALLAH BÃ A KANKU DA RAHAMARSA, HAƘĨƘA, DÃ KUN BI SHAIƊAN FÃCE KAƊAN". [Al-Nisa'a: 83]


Saboda haka ya kamata ga Mutum ya Mayar da Al-amura zuwa ma'abotansu, kuma kada ya xauki wani ilimi da zai haskaka da shi sai daga Vangarorin da suka qware banda Wasun su, kuma kada ya zamanto Qaho da za'a riqa busa jita jita daga cikinsa, kuma yana yaxa ta ga Mutane, cikin abunda zai cutar da su a Addinin su da Duniyar su


10


ASALI NA SHIDA: Ya kamata ga bawa yayi Qoqari wajen roqon Allah SWT; saboda "Addu'a ita ce Ibada" Kamar yada Annabi ya ce SAW ya ce: {7}


Kuma wannan Addu'ar ta kasu gida biyu:


NA FARKON SU: Gamammiyar Addu'a; saboda yayi Addu'ar yaye Bala'i, ko kautar da shi ko wanin haka daga nau'o'in Addu'a waxanda yake Addu'a da su; kamar ya ce: "Ya Ubangiji ka karemu daga wannan Bala'i, ya Ubangiji ka ije mana wannan Annoba"; Saboda wannan shi ne abunda aka Shar'anta


Kuma haqiqa Al-bukhari ya fassara hakan cikin <Sahihinsa> a (Babin Addu'a don xaukewar Annoba da kuma Ciwo)


Kuma Nasa'i a cikin <Al-Sunan Al-Kubra> (Babin Addu'a don yaye Annoba)


Kuma haka sun faxa a cikin Hadisin lallai cewa Manzon Allah SAW yayi Addu'a don yaye Zazzavin Madina zuwa Al-Juhfa (8)


Sai Mutum ya roqi Ubangijinsa Maxaukakin Sarki da ya kawar masa da Annoba da kuma Bala'i daga Musulmai baki xaya, da kuma garuruwan waxan nan a kexance


AMMA NAU'I NA BIYU: SHI NE NAU'I NA MUSAMMAN DA YAKE DA ALAQA DA NEMAN TSARI DA KUMA KARIYA DAGA WAXAN NAN ILLOLIN DA KUMA CUTUTTUKA; KUMA SHI KASHI UKU NE:


NA FARKO: KARANTA SURAT AL-FALAQ DA NASI : Saboda Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wani abu abu da mai neman tsari da zai nemi tsari da su kamar su" Ai lallai cewa Mutum idan yaji tsoron


11


wani abu to ya kamata ya karanta waxan nan Surori biyu, yana mai rokon Allah SWT da ya kiyaye shi daga abun da yake tsoronsa, kuma daga cikin hakan: wannan Annobar.


ADDU'A TA BIYU: ita abunda aka rawaito daga Abu Daud da waninsa, kuma Ibn Hibban ya inganta shi cewa Annabi SAW ya kasance yana cewa: "Ya Ubangiji ina ina neman tsarinka daga Al-baras da kuma Hauka da Kuturta, da Munanen Cututtuka"2Annabi -tsira da amincin Allah- ya kasance yana Addu'a da da wannan kuma yana neman tsari da ita


kuma daga cikin abunda ya ke qarqashin faxinsa SAW: "da kuma Munanan Ciwuka" Cutukan da Mutane suke tsoronsu; saboda haka Mutum yake wan nan Addu'ar


NA UKU: ZIKIRIN SAFIYA DA MARAICE: Kuma shi ma an rawito daga Abu daud da waninsa Cewa Manzon Allah SAW ya ce: "Babu wani bawa da zai ce a kowace Safiya ko Maraice: "Da sunan Allah wanda babu abunda yake cutarwa idan aka ambaci sunansa a Qasa ne ko a Sama kuma shi Mai ji ne kuma Masani" Sau Uku wani abun ya same shi" 11


Kuma cikin wata Riwayar daga Abu Daud: "Bala'i ba zai same shi ba Fuj'a"


Kuma daga cikin Addu'o'in da da Mutum zai kiqe maganin Annoba wannan Addu'ar wacce Annabi SAW ya ke faxa safe da Maraice sau Uku:


2 Abu Daud ya rawaito shi (1554) daga Hadisin Anas -Allah ya yarda da shi-


12


Saboda waxan nan Ginshiqai shida, ya kamata Mutum ya kula wajen kwatanta su da aiki da su; saboda suna daga cikin Manyan alamomin buqatuwarmu zuwa ga Allah SWT a irin wannan lokaci da aka jefowa Mutane wannan Annoba mai tsoratarwa da hallakawa, kuma Kariya daga waxan nan baki xaya shi ne zabura zuwa ga Allah SWT da kuma buqatuwa zuwa gare shi da wasu al-amura: Mafi girmansu waxan nan ginshiqai guda Shida


Ina Roqon Allah SWT da ya kawar mana da wannan Annoba ga barin Musulmai baki xaya, da garinmu, kuma ya tsare mana Musuluncin mu muna masu riqo da shi, kuma ya tsare mana Musualuncin mu muna masu kare shi, kuma ya tsare Mana Musuluncinmu muna cikin bacci, kuma ya kare mana lafiyar jikin mu, kuma ya yalwata Arzikinmu, da kuma cikar Imaninmu, kuma ya jivancemu da jivantarsa, kuma ya karemu da kariyarsa


Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.


Anyi wannan Huxubar ce bayan Sallar la'asar Ranar litinin Sha biyar ga watan Rajab a shekarar 1441 Hijira a Masallacin Mus'ab Bn Umair a Unguwar Al-Jazira da ke birnin Raiyadh


13


ABUBUWAN DA KE CIKI


GINSHIQAI GUDA SHIDA DON KOMAWA ZUWA GA ALLAH A LOKACIN TSANANI ..................................................................................... 1


GINSHIQI NA FARKO: IMANI DA QADARAR ALLAH MAXAUKAKIN SARKI: .... 4


GINSHIQI NA BIYU:CIKAR TAWAKALI GA ALLAH DA KUMA MIQA DUKAN AL-AMARI ZUWA GARE SHI: ......................................................................... 5


GINSHIQI NA UKU: Shi ne komawa zuwa ga Allah SWT da kuma tuba zuwa gare shi ......................................................................................................... 6


ASALI NA HUXU: YA KAMAT GA BAWA LALLAI YAYI RIQO DA SABABI ......... 8


ASALI NA BIYAR: YA KAMATA LALLAI MUTUM YAYI QOQARIN RIQO DA HANYOYIN ILIMI WAXANDA SUKA DAME SHI DAGA BANGARORIN DA SUKA QWARE, KUMA YA NISANCI JITA JITA: .......................................................... 9


ASALI NA SHIDA: Ya kamata ga bawa yayi Qoqari wajen roqon Allah SWT; saboda "Addu'a ita ce Ibada" Kamar yada Annabi ya ce SAW ya ce: {7} .... 10


NA FARKON SU: ...................................................................................... 10


AMMA NAU'I NA BIYU: ........................................................................... 10


NA FARKO: .......................................................................................... 10


ADDU'A TA BIYU: ................................................................................ 11


NA UKU: .................................................................................................. 11


Abubuwan da ke ciki ................................................................... 13



Posts na kwanan nan

SAKO DAGA MUSULMI MAI ...

SAKO DAGA MUSULMI MAI WA'AZI ZUWA GA MUTUM KIRISTOCI

FALALAR AZUMIN KWANA ...

FALALAR AZUMIN KWANA SHIDA SHAWAL

TAKAITACCEN BAYANI MA ...

TAKAITACCEN BAYANI MAI ANFANI GA SABON SHIGA MUSULUNC

ZIKIRAI WADANDA AKE Y ...

ZIKIRAI WADANDA AKE YIN SU DA SAFE DA KUMA YAMMA