35
dan wannan yafi girma lokacin da ta fadi sa yace ya ku
mutane na lallai ni na barranta dag abunda kuke shirka da
shi (78) lallai ni na fuskantar da fuska ta ga wanda ya kagi
halittar sammai da kasa ina mai karkata zuwa gare shi
kuma ni bana cikin masu shirka (79)” suratul An’am, aya ta:
74-79.
Hakan bai burge shi kuma da fiirar shi yaji a jikin sa cewa
akwai abun bauta da yafi wadannan halittun girma wadan da
basa cutarwa ko amfanarwa, har Allah ya shiryar da shi zuwa
ga sanin sa kuma ya zabe shi da manzancin sa, kuma shi tsira
da amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana yawan
jayaiyya da mutanen sa musamman ma da dalilai na hankali
wadanda basa barin wani wuri na kokwanto wajen bata abun da
suke kudurcewa da kuma abunda suke bautawa komabayan
Allah, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “
kuma ka karanta musu labarin annabi Ibrahim (69) lokacin
da yace wa mahaifin sa da mutanen sa me kuke bauta ma
(70) sai sukace muna bauta wa wasu gumaka ne sai mu
doge muna masu gurfana a gare su (71) sai yace shin suna
jin ku in kuna kiran su (72) kuma suna amfanar da ku ne
ko cutarwa (73) sai suka ce a’a mu mun samu iyayen mu ne
haka suke aikatawa (74) sai yace kun ga ababen nan da
kuke bautawa (75) ku da iyayen ku na da (76) to lallai su
makiya ne a gare ni sai dai ubangijin talikai (77) wanda ya
halicce ni to shi ne zai shiryar da ni (78) kuma wand yake
ciyar da ni da shayar da ni (79) kuma in nayi rashin lafiya
to shi ne yake warkar da ni (80) kuma shi ne wanda yake
kashe ni sannan ya rayar dani (81) kuma shi ne wanda nake
kwadayin ya gafarta mun zunubai na ranar sakamako (82)
36
ya ubangiji ka bani wani hukunci kuma ka riskar da ni da
salihai (83) kuma ka sanya mun harshe na gaskiya a cikin
masu zuwa (84)” suratush Shu’ara’i, aya ta: 69-84.
Ya ci gaba da kirn mutanen sa tsira da amincin Allah ya tabbata
a gare shi zuwa ga kadaita Allah da bauta masa da kuma jifa da
dukkan abunda suke bautawa koma bayan Allah sai dai su sun
karyata shi kuma suka musa manzancin sa kuma sukayi
yunkirin kona shi da wuta sai Allah ya tsiratar da shi daga gare
su, kamar yadda Allah ya bada labarin sa da fadar sa: “ kuma
hakika mun baiwa Ibrahim shiriyar sa tun gabanin haka
kuma mu game da shi masana ne (51) lokacin da yace wa
mahaifinsa da mutanen sa wadannan wasu irin gumaka ne
da kuke bautama wa (52) sai sukace mun samu iyayen mu
ne muma suna bauta musu (53) sai yace hakika ku da
iyayen ku kun kasance cikin bata baiyananna (54) sai suka
e shin kazo mana da gaskiya ne ko kuwa kai kana cikin
masu wasa ne (55) sai yace ai ubangijin ku shi ne ubangijin
sammai da kasa wanda ya halicce su kuma ni mai shaida ne
akan haka (56) kuma wallahi sai na rusa gumakan ku
bayan kun juya baya kun tafi (57) sai ya sanya su a farfashe
sai dai babban su dan wata kila zasu komo zuwa gare shi
(58) sai sukace waye ya aikata haka ga allolin mu lalli shi
yana cikin azzalumai (59) sai sukace munji wani saurayi
yana ambaton su da batanci ana kiran shi Ibrahim (60) sai
sukace to kuzo da shi a gaban idan mutane ko zasu bada
shaida (61) sai sukace shin kai ne ka aikata haka ga allolin
mu ya kai Ibrahim (62) sai yace a’a wannan babban na
cikin su ne ya aikatato ku tambaye su mana in suna
magana (63) sai suka koma zuwa ga kawonan su sai sukace
37
lallai kune azzalumai (64) sa’annan sai suka sunkuyar da
kawunan su suka ce hakika ka san cewa wadancan basa
magana (65) sai yace to yanzu zaku dinga bautawa wani
abu koma bayan Allah wanda bazai amfane ku da komai ba
ko kuma ya cutar da ku (66) tur da ku da kuma abunda
kuke bautawa koma bayan Allah shin baza ku hankalta ba
(67) sai sukace ku kona shi kuma ku taimaki allolin ku in
har zaku aikata (68) sai mukace yake wuta ki kasance sanyi
da aminci ga Ibrahim (69) kuma sunyi nufin makirci a gare
shi sai muka sanya su sune masu hasara tababbu (70)”
suratul Anbiya’i, aya ta: 51-70.
Bayan mutanen shi sun karyata shi sai Allah ya umarci shi da
barin garin shi da matar shi Hajara da yaran sa Isma’il zuwa
makkah a inda Allah ya nuna wa Annabi Ibrahim wurin da
dakin ka’abah yake sai ya ginashi kuma yaran sa Ismail ya
taimake shi wanda ta tsatson shi ne na karshen Annabawa ya
fito wato Annabi Muhammad (S.A.W) wanda aka aiko shi
zuwa ga mutane baki daya har zuwa ranar alkiyama, dan
wannan gidan ya zama alkiblar musulmai dukkan su a gabas da
yamma, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “
kuma lokacin da Ibrahim yace ya ubangiji ka sanya
wannan gari ya zama amintacce kuma ka azurta mutanen
cikin sa da kayan marmari wanda sukayi imani daga cikin
su da Allah da rana ta karshi sai yace kuma duk wanda ya
kafurce to zan jiyar da shi ddi dan kadan sannan zan jefa
shi cikin azabar wuta kuma makoma tayi muni (126) kuma
lokacin da Ibrahim yake daga tushe na ginin ka’abah da
kuma Isma’il sai suka ce ya ubangiji ka amsa mana lallai
kai mai ji ne masani (127) ya ubangiji kuma ka sanya mu
38
mu zama masu mika wuya a gare ka da kuma zurriyyar mu
su zama al’umma masu mika wuya a gare ka kuma ka
nuna mana wuraraen bautan mu kuma ka yafe mana lallai
kai mai yawan karbar tuba ne mai jin kai (128) ya
ubangijin mu kuma ka aika da wani manzo daga cikin su
zuwa gare su wanda zai dinga karanta musu ayoyin ka
kuma ya sanar da su littafi da hikima kuma ya tsarkake su
lallai kai mabuwayi ne mai hikima (129) kuma babu mai
kauda kai daga tafarkin Ibrahim sai dai fa wanda ya
wawantar da kansa kuma hakika mun zabe shi a nan
duniya kuma lallai shi a lahira yana cikin salihai (130)
lokacin da ubangijin sa yace masa ka mika wuya sai yace
na mika wuya ga ubangijin talikai (131) kuma sai Ibrahim
yayi wasiyya da ita ga yaran sa da Yaqub cewa ya ku
yarana lallai Allah ya zabar muku addini kada ku sake ku
mutu sai dai kuna musulmai masu mika wuya (132)” suratul
bakara, aya ta: 126-132.
39
Shi ne wanda yayi magana da Allah, Allah ya mai magana ba
tare da wani shamaki ba, kamar yadda Allah ya baiyana haka
da fadar sa: “ lokacin da Musa yazo mikatin mu kuma
ubangijin sa yayi masa magana sai yace ya ubangiji ka
nuna mun kai in ganka sai yace baza ka iya gani na ba sai
dai kayi dubi zuwa ga wancan dutsen idan har ya tabbata a
inda yake to da sannu zaka ganni lokacin da ubangijin sa
yayi tajalli zuwa ga dutsen sai ya mai da shi a farfashe a
warwatse sai Musa ya fadi yana sumamme lokacin da ya
farfado sai yace tsarki ya tabbata a gare ka na tuba a
gareka kuma ni ne farkon muminai (143)” suratul A’raf, aya
ta: 143.
Kuma shi ne wanda aka fi ambato cikin manzanni bani isra’ila
a cikin Alkur’ani mai girma, an ambace shi a wurare dari
daashirin da tara wannan yana nuni akan matsayin wannan
Annabin da darajar sa mai girma, Allah ya karfafa shi da
mu’jizozi guda biyu, ta farkon su itace sanda wacce ta koma
kamar katon macijiya, amma dayar mu’jizar ita ce hannun sa
wanda yake shigar da shi cikin hammatan sa sai ya fito da shi
ya koma fari ba tare da mis ba, wannan na nuni akan gaskiyar
mazancin sa ga firauna da mutanen sa dan ko watakila su zama
dalili na gaskatawar su da imanin su ga Allah kamar yadda
Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “ kuma Musa yace ya kai
fir’auna lallai ni manzo ne daga ubangijin talikai (104) da
gaskene bazan fadi komai bai game da Allah sai dai gaskiya
hakika nazo muku da hujjoji daga ubangijin ku to ka saki
40
mutanen bani isra’ila su tafi tare da ni (105) sai yace in har
kazo da hujjoji to ka kawo su mu gani in har kai ka
kasance cikin masu gaskiya (106) sai ya wurga sandar shi
sai gashi ta zama katon kumurcin maciji a baiyane (107)
kuma sai ya fito da hannun sasai ga shi yana haske fari tas
ga masu kallo (108)” suratul A’araf, aya ta: 104-108.
Allah ya aike shi zuwa wurin fir’auna da mutanen sa dan ya
kirasu zuwa ga bautar Allah shi kadai da watsar da dukkan
wani abu koma bayan sa bayan sun karkace daga addinin
gaskiya kuma sukayi girmankai da dagawa da kuma zalunci, ta
yadda fir’auna ya dunga kiran mutanen sa da su bauta masa
kuma yana umurtar su da yin bauta a gare shi irin wadda basa
yi wa Allah madaukaki, kamar yadda Allah ya baiyyana haka
da fadar sa: “ kuma sai fir’auna yace ya ku mutanen gari
ban san wani abun bauta a gare ku ba sai ni to ya kai
Hamana ka dauke ni akan tabo sai ka gina mun babban
gidan sama dan wata kila ko na leko Allahn Musa kuma
lallai ni ina zatan shi yana cikin makaryata (38)” suratul
Kasas, aya ta: 38.
Sai Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare shi ya kira
shi ta hanyar hikima da sassaukan zance zuwa ga kadaita Allah
da bautar Allah shi kadai, sai Fir’auna ya yake shi kuma ya tara
mai bokaye dan su mai makirci, sai dai Annabi Musa amincin
Allah ya tabbata a gare shi ya yi rinjaye a kansu da ikon Allah,
bayan ya jefa sandar sa wacce ta hadiye sandunan bokayen da
igiyoyin su wadanda aka juyar da su suka koma suna tafiya
saboda tsafi suka zama kamar macizai kamar yadda Allah ya
baiyyana haka da fadar sa: “ sai iyan lagwada daga cikin
mutanen fir’auna sukace lallai wannan mai sirhiri ne
41
masani (109) yana so ne ya fitar da ku daga kasarku to
meye kuke umarni da shi (110) sai suka ce a kore shi da dan
uwan shi kuma ku tura gari gari dan tattaro mutane (111)
dan a zo maka da kowane mai sihiri masani (112) sai masu
sihirin fir’auna suka zo sai suka ce lallai mu munada wata
lada ne in mun kasance mu ne masu galaba (113) sai yace
eh kuma lallai ku zaku zama cikin makusanta (114) sai
suka ce ya Musa ko dai ka fara jefawa ko kuma mu ne
zamu fara jefawa (115) sai yace ku jefa lokacin da suka jefa
sai suka sihirce idanun mutane kuma suka firgitar da su
kuma sun zo da sihiri mai girma (116) sai mukayi wahayi
zuwa ga Musa cewa ka jefa sandar ka sai gashi tana hadiye
abunda suke jefawa (117) sai gaskiya ta baiyyana kuma
abunda suka kasance suna aikatawa ya blalace ya baci
(118) kuma sai aka rinjaye su a wannan wurin sai suka
komo suna kaskantattu (119) sai masu sihiri suka fadi suna
masu sujada (120)” suratul A’araf, aya ta: 109-120.
Fir’auna da mutanen sa sun karyata Annabi Musa amincin
Allah ya tabbata a gare shi sai Allah ya daura musu ukubobi iriiri saboda karayatawar da sukayi da kuma barna da suke yi
aban kasa, sai Allah ya aiko musu da ruwan dufana da fari da
kwarkwata da kwadi da jini, ayo yi filla-filla sai sukayi girman
kai kuma suka zama kafurai, sai daga baya Allah ya dage su
daga gare su saboda addu’ar Annabi Musa bayan sun nemi da
yayi addu’a ya roki ubangijin sa dan ya yaye su daga gare su
wta kila zasu gaskata kuma suyi imani, sai dai hakan bai kara
musu komai ba sai dai kangare wa da kafurci da girman kai,
kamar yadda Allah ya baiyyana haka da gadar sa:“ kuma
sukace duk abunda zaka zo mana da shi na ayoyi dan ka
42
sihirce mu da su to mu baza muyi imani da kai ba (132)sai
muka aika musu da dufaan da fari da kwarkwata da kwadi
da jini ayoyi ne a rarrabe sai sukayi girman kai kuma sun
kasance mutane mujirimai (133) lokacin da girgije ya fado
a kan su sai suka ce ya Musa ka roka mana ubangijin ka da
abunda ya saba maka da shi dan idan ka dauke mana
wannan girgijen to wallahi lallai zamuyi imani da kai kuma
lallai zamu saki bani isra’ila tare da kai (134) lokacin da
muka yaye musu girgijen zuwa wani lokaci wanda su zasu
kai shi sai gashi suna warware alkawari (135)” suratul
A’araf, aya ta:132-135.
Bayan wanna sabawar da taurin kai da kafurci baiyananne daga
Fir’auna da mutanen sa sai Allah ya umarci Annabi Musa
amincin Allah ya tabbata a gare shi da fita shi da mutanen sa
cikin dare sai ya fita daga masar shi da muminai cikin mutanen
sa daga cikin mutanen bani isra’ila dan su gudu da addinin su,
si Fir’auna da rundunar sa suka bi shi saboda kiyaiyya da
zalunci, lokacin da jama’ar biyu suka hango juna kuma ga teku
a gaban su kuma fir’auna da rundunar shi suna bayan su, sai
mutanen Annabi Musa suka ce:” lallai mu an kama mu” sai
Annabi Musa fada yana mai tabbaci da ubangijin sa cewa zai
kubutar da su da kuma irin alkawarin da yayi masa na samun
nasara akan abokan gaban sa:” a’a” sai Allah yayi masa wahayi
cewa ya bigi tekun da sandar sasai ya tsage biyu sai ya zama
kamar dutse mai girma dan Allah ya tsiratar da Annabi Musa
da wadan da suke tare da shi kuma ya nutsar da Fir’auna da
rundunar sa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka d fadar sa: “
lokacin da jama’r biyu suka ga juna sai mutanen Annabi
Musa suka ce lallai mu za’a riske mu (61) sai yace a’a lallai
43
ni akwai ubangiji na a tare da ni zai shiryar da ni (62) sai
mukayi wahayi zuwa ga musa cewa ka bigi tekun da sandar
ka sai tekun ya rabe sai kowane bangare ya zama kamar
dutse mai girma (63) kumai sai muka kusanto da wadancan
jama’ar na daban (64) kuma sai muka kubutar da Musa da
wadanda suke tare da shi baki daya (65) sa’annan sai muka
nutsarda wadancan da suka rage (66)” suratush Shu’ara’i,
aya ta: 61-66.
Allah ya karfafa Annabi Musa amincin Allah ya tabbata a gare
shi da wannan mu’ujizar wacce Fir’auna da mutanen sa basu
taba tsammanin ta ba, sai dai al’amarin Allah mai zartuwa ne
kuma abunda yayi nufi mai kasantuwa ne dan ya zama a cikin
haka akwai kubutar Annabi Musa da wadanda suke tare da shi
cikin muminai kuma dan ya zama a cikin ta akwai halakar
fir’auna da mabiyan sa dan ya zama aya ga wadanda suke
bayan sa da kuma abun izina, ta yadda tekun ya jeho shi waje
bayan ya halaka, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar
sa: “ kuma muka ketarar da bani isra’ila teku sai fir’auna da
rundunar sa suka bisu dan mugunta da kiyaiyya har zuwa
lokacin da nutsewa ta riske shi sai yace nayi imani cewa lallai
babu abun bauta sai wannan wanda bani isra’ila sukayi imani
da shi kuma nima ina cikin musulmai masu mika wuya (90)
shin a yanzu kuma alhali a baya ka bijire kuma ka sance cikin
masu barna (91) a yau zamu tsiratar da kai da gangan jikin ka
dan ka zama aya ga wadanda zasu zo a bayan ka kuma lallai da
yawa daga cikin mutane gafalallu ne game da ayoyin mu (92)”
suratu Yunus, aya ta: 90-92.
44
Shine shugaban mu Isah dan Maryam Annabi na karshe na bani
isra’ila, Allah ya aiko shi bayan Annabi Musaamincin Allah ya
tabbata a gare shi zuwa ga mutanen bani isra’ila lokacin da
suka baci kuma suka kauce daga ingantacciyar hanya, kamar
yadda Allah yabaiyana haka da fadar sa: “ kuma sai muka zo
da Isah dan Maryama a bayan su yana mai gaskata abunda
ya gabace shi na attaura kuma mun bashi injila a cikinta a
kwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda ya
gabace shi na attaura kuma shiriya ne da kuma tunatarwa
ga masu tsoran Allah (46)” suratul Ma’ida, aya ta: 46.
An haife shi ba tare da uba ba saboda wata hikima da Allah
yake nufi, hakika ya so ne ya baiyana wa halittunsa ikon sa ga
ga halittar sa, ta yadda ya halicci Adam ba uwa ba uba, kuma
ya halicci Hauwa’u daga namiji ba mace, sai kuma ya halicci
Isah ba namiji, saboda haka ne Allah ya fada a cikin suratu
maryam: “ kuma dan sanya shi ya zama aya ne ga mutane “
suratu Maryam, aya ta:21.
Misalin halittar sa kamar misalin halittar Adam ne Allah ya
halcce shi daga turbaya sannan sai ya ce masa “ kasance” sai ya
kasance, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa:”
lallai misalin Isah a wurin Allah kamar misalin Adam ne
Allah ya halicce shi daga turbaya sa’annan sai yace masa
kasance sai ya kasance (59)” suratu Ali imaran, aya ta: 59.
An aike shi zuwa ga bani isra’ila sai sukakaryata shi kuma suka
yake shi kuma suka cutar da shi, sai yayi hakuri kuma yaci
gaba da isar da sakon manzancin sa, kuma saboda yasan cewa
45
ba shi ne na karshen manzannin Allah ba sai yayi bushara da
wani manzo da zai zo a bayan sa sunan sa Ahmad2
(S.A.W),
Allah ya sanar da shi littafi da hikima da attaura da injila kuma
ya karfafa shi da mala’ika Jibrilu kuma ya kasance mai daraja a
nan duniya da kuma lahira kuma ya kasance cikin makusanta,
Allah ya bashi wasu mu’ujizozi wadanda suka ruda mtanen
lokacin sa, hakika shi yayi wa mutane magana alhali yana cikin
tsumman goyo, kuma ya kasanceyana hada tsuntsu na tabo sai
yayi busa a ci sai ya tashi sama ya zama tsuntsu da izinin Allah,
kuma yana warkar da mai kyasfi da kuturu kuma yana raya
matattu dukkkan wannan na faruwa ne da izinin Allah, kuma
yana baiwa mutane labarin abunda suka ci da abun da suka
taskace, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “
lokacin da mala’iku suka ce ya ke Maryam lallai Allah yana
miki bushara da wata kalma daga gare shi sunan sa
almasihu Isah dan Maryama mai daraja ne a duniya da
lahira kuma yana cikin makusanta (45) kuma yana magana
da mutane a cikin tsumman goyo da kuma bayan ya
manyanta kuma yana cikin salihai (46) sai tace ya ubangiji
ta yaya zan samu yaro kuma alhali babu wani mutum da ya
taba taba ni sai yace haka nan Allah yake halitta abunda
yaga dama idan ya kaddara wani lamari to kawai yana ce
masa ne kasance sai ya kasance (47) kuma zai sanar da shi
littafi da hikima da Attaura da Injila (48) kuma manzo ne
zuwa ga bani isra’ila cewa lallai ni nazo muku da hujjoji
daga ubangijin ku lallai ni ina halitta muku daga daga tabo
wani abu mai kama da tsutsu sai in yi busa a cikin sa sai ya
zama tsuntsu da izinin Allah kuma ina warkar da mai
2
- Ahmad daya ne daga cikin sunayen Annabi Muhammad S.A.W.
46
kyasfi da kuturu kuma ina raya matattu da izinin Allah
kuma ina baku labarin abunda kuka ci da abunda kuke
taskacewa a cikin gidajen ku lallai a cikin haka akwai ayoyi
a gare ku in kun kasance muminai (49)” suratu Ali imran,
aya ta: 45-49.
Da’awarsa ta kasance irin da’awar sauran iyan uwansa
manzanni kafin sa, sai ya kira mutanen sa zuwa ga bautar Allah
madaukaki, sai dai shi ya hadu da abun da ya hadu dashi daga
gare su na karyatawa da girmankai, kuma ba wanda yayi imani
da shi sai dai masu rauni cikin mutanen sa, yahudawa sun yi
yunkurin halaka shi da da’awar sa sai Allah ya tsiratar da shi
daga gare su ta yadda ya dauke shi zuwa sama, sai yahudawa
suka kashe mutumin da Allah ya sanya mai kama irin ta Annabi
Isah, sai yahudawa da wadanda suka rako su cikin kiristawa
sukayi zatan cewa an kashe shi, kuma shi zai sauko a karshen
zamani zuwa kasa kma zaiyi hukunci da shari’ar Annabi
Muhammad (S.A.W) daga baya sai Allah ya dau ran sa dan
tabbatar da fadar Allah madaukaki:” dukkan wanda ke kanta
mai karewa ne (26) kuma fuskar ubangijin ka ce zata rage
ta wanzo ma’abocin girma da karamci (27)” suratur
Rahman, aya ta: 26-27.
47
Manzan Allah Muhammad (S.A.W) Annabin da bai san karatu
ba ko rubutu balarabe daga tstson Annabi Isma’ila dan
Ibrahima baban Annabawa, shi ne karshen manzanni kuma
mafificin su baki daya, an aiko shi zuwa ga mutane baki daya,
an haife shi a makkah bayan rasuwar mahaifin shi da watanni
kadan, sannan sai daga baya mahaifiyar shi ta rasu alhali yana
jariri, sai kakan sa Abdul mutallib ya raine shi, sai dan uwan
baban sa Abu dalib, kuma yayi kiwon dabbobi na wani lokaci
ga mutanen makkah, Allah ya aiko shi zuwa ga mutane baki
daya ba wai larabawa ba kawai, ya aiko shi dan jin dadin
mutane baki daya kuma dan ya baiyana musu hanyar gaskiya
da alheri kuma ya tsawatar da su daga hanyar barna da sharri,
rayuwar sa dukkanta ta kasance gaskiya ce da amana, ba’a
sanshi da yaudara da karya ba, ko cin amana da zamba,an
sanshi tsakanin mutane da amintacce sun kasance suna aje
amanaonin su a wurin sa, kuma suna aje kayan su a wurin sa in
zasuyi tafiya, kuma sun sanshi da gaskiya, saboda irin abunda
aka san shi da shi na gaskiya cikin abunda yake fada da kuma
bada labarin sa, wahayi ya sauka a gare shi yana da shekaru
arba’in, ya zauna a garin makkah shekaru goma sha uku yana
kiran mutane zuwa ga kadaita Allah da kuma barin bautar
gumaka sannan sai yayi hijira zuwa madinah mai haske ku a ya
kira mutanen ta zuwa musulunci sai suka musulunta sai Allah
ya saukar masa da sauran aiyuka na shari’o’in addini, kuma ya
ci makkah da yaki bayan shekaru takwas da yin hijiran sa kuma
ya rasu shekariun sa sittin da uku bayan an saukar masa da
Alkur’ani cikakke kuma shari’a ta cika dukkan ta kuma
48
larabawa suka shiga cikin musulunci kuma mabiyan sa suka
fara yada musuluni a bayan sa a cikin lunguna na doran kasa
wacce aka raya kai har zuwa wannan ranar tamu mutane suna
shiga cikin wannan addinin mai girma dan yarda da sukayi da
shi da kansu cew hi ne addini na gaskiya wnnan kuwa bayan
sun san hanyoyin ushen sa ingantattu.
49
Aiko da manzanni da kuma annabawa ya ci gaba har zuwa
wani lokaci mai tsawo bayan Annabi Nuhu amincin Allah ya
tabbata a gare shi har zuwa Annabi Isah amincin Allah ya
tabbata a gare shi wanda da shi ne aka cike Ammabawan bani
isra’ila dan al’amarin manzanci da annabci ya koma ga Annabi
Muhammad (S.A.W) dan ya zama na karshen Annabawa baki
daya, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “
Muhammadu bai zamo mahaifin daya daga cikin mazajen
ku ba sai dai shi manzan Allah ne kuma cikamakin
Annabawa kuma Allah ya kasance masani ne ga dukkan
komai (40)” suratul Ahzab, aya ta: 40.
Lallai Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi yana da
wta irin daraja ta musamman a cikin zukatan musulmai saboda
shi zamanin sa yafi kusa da su kuma yana cikin wadanda
sukayi bushara a fili da zuwan Annabin su Muhammad
(S.A.W), kuma hakika mamakin kiristoci zai karu in suka san
cewa sunan Annabi Isah ya maimaitu a cikin Alkur’ani har sau
ashirin da biyar a lokacin da shi kuma Annabi Muhammad
(S.A.W) manzan musulunci wanda shi ne aka saukar wa
Alkur’ani cewa ba/a ambaci sunan ba sai sau biyar kawai!!
Wannan yana cikin ababen da ke nuni karara akan cewa lallai
Annabi Muhammad (S.A.W) shi Annabi ne da aka aiko kuma
lallai abun da ake saukar masa da shi wahayi ne ake yi masa ba
daga zancen shi bane, da ace kur’ani maganar shi ne to da
sunan shi zai fi maimaituwa fiye da kowane mutum na daban.
Saboda matsayin wannan Annabi mai girma wato Isah amincin
Allah ya tabbata a gare shi alkur’ani ya kunshi ayoyi masu
50
yawa wadanda sukayi magana game da shi da kuma dangin sa
na gari masu albarka.
Haka nan ma Maryam mai tasrki mahaifiyar Annabin Allah
Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi da danginta suna da
matsayi na musamman a cikin zukatan musulmai, hakika
Alkur’ani yayi yabo a gare ta kuma ya siffanta mahaifiyarta da
cewa ita mai bauta ce mai tsarki wadda take da tushe mai
albarka da kuma matsira mai kyau da kuma dangi na gari, kuma
ya daure sunan dangi ta –iyalan Imran- iyalai masu karamci da
kuma zurriyya masu albarka tsatsaon Annabawa da manzanni
wadda Annabi Isah yake dangantuwa zuwa gare ta da sura ta
uku a cikin Alkur’ani ita ce suratu Ali imaran, dan girmamawa
da kuma karramawa a gare su kuma dan wannan iyalan su
zama sunan zaune cikin kwakwalen musulmai suna mau
karamci da daraja a wurin su, Allah madaukakai yace: “ lallai
Allah ya zabi Adam da Nuhu da iyalan Ibrahim da iyalan
Imrana ya fifita su akan talikai (33) zurriyya ne sashin su
daga sashi kuma Allah mai ji ne masani (34)” suratu Ali
imaran, aya ta: 33-34.
51
Alkur’ani mi girma yayi yabo ga Maryam iyar Imran
mahaifiyar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi,
mai gaskiya mai daraja mai tsarke wacce ta taso a gidan
kamewa da tsarki, a cikin wurare da dama a Alkur’ani an
siffanta ta da salihanci da tsarki da kuma tsoran Allah, Allah
madaukaki yace: “ da kuma Maryam yarinyar Imrana
wacce ta tsare farkinta sai muka yi busa a cikin sa daga
ruhin mu kuma ta gaskata da kalmomin ubangijin ta da
littattafan sa kuma ta kasance cikin masu kankantar da kai
(12)” suratut Tahrim, aya ta: 12.
Kuma Alkur’ani ya baiyana cewa lallai Maryam amincin Allah
ya tabbata a gare ta ta samu ne ta sanadiyyar addu’a mai
albarka da ta fito daga uwa mai albarka, Allah madaukaki yana
cewa: “ lokacin da matar Imrana tace ya ubangiji lallai ni
nayi alwashi a gare ka na abunda ke ciki na cewa zaiyi
bauta ne a gre ka to ka amsa daga gare ni lalli kai mai ji ne
masani (35)” suratu Ali imran, aya ta: 35.
Kuma lallai wannan addu’ar mai albarka itace ta zama sababi
na tsare ta da yaranta Isa amincin Allah ya tabbata a gareshi kar
shaidan ya samu galaba a kan su, ta yadda ubangijin ta ya
amshe ta kuma ya karfafa ta da wasu karamomi wadanda suke
nuni akan kyawon inda ta taso, ta yadda arzikinta ke zuwa mata
alhali tana zaune awurin ta kuma abunda ke zuwa mata na
arziki yana zuwa ne a lokacin da ba nashi ba na kayan marmari
da sauran su, kuma lura da ita ya zama karkashin Annabi
Zakariyya amincin Allah ya tabbat a gare shi mutumin kirki
52
dan ya kula da ita da kuma damuwa da lamuran ta kamar yadda
Allah ya baiyyana haka a cikin Alkur’ani da fadar sa: “ lokacin
da ta haife ta sai tace ya ubangiji lallai ni haifeta mace
kuma Allah yafi ni sanin abunda na haifa kuma amma
mace ba kamar namiji ba kuma lallai ni na sa mata suna
Maryama kuma lallai ni ina nema mata tsarin ka da
zuriyyarta daga shaidan jifaffe (36) sai ubangijin ta ya
karbe ta karba mai kyau kuma ya raya ta rayuwa mai kyau
kuma Annabi Zakariyya ya jibinci lamuran ta lokacinda
Zakariyya ya shiga wurin ta a wurin bauta sai ya samu
arziki a wajen ta sai yace ya Maryam a ina kika samu
wannan sai tace shi daga wurin Allah yake lallai Allah yana
azurta wanda yaga dama ba tare da lissafi ba (37)” suratu
Ali imaran, aya ta: 36-37.
Ita ta kasance cikin masu bauta tsira da amincin Allah ya
tabbata a gare ta cikin wadanda babu kamar su a wajen bauta a
lokan su, Allah yayi mata baiwa da zabinta da yayi a cikin
matan lokacin ta, sai mala’iku sukayi mata bushara da hakan,
kamar yadda Allah ya bada lagarin haka a cikin Alkur’ani da
fadar sa: “ kuma lokacin da mala’iku suka ce ya ke maryam
lallai Allah ya zabe ki kuma ya tsarkake ki kuma ya zabe ki
ya fifita ki akan matan talikai (42) ya ke Maryam ki
kankan da kai ga ubangijin ki kuma kiyi sujada kuma kiyi
ruku’i tare da masu ruku’i (43)” suratu Ali imaran, aya ta:
42-43.
Kuma ma kari akan karamcin ta da bayanin falalar ta amincin
Allah ya tabbata a gare ta ya karu ta yadda Allah ya saukar da
sura kacukan da sunan ta (suratu Maryam) kuma itace sura ta
goma sha tara a cikin Alkur’ani, kuma it ce sura daya tilo
53
wacce take dauke da sunan mace a cikin Alkur’ani, kuma a
cikin wannan surar akwai yabo da girmamawa ga Maryam
wanda babu irin shi a cikin littattafan kiritoci ko bible- bible
din su, duk da cewa babu wata sura ko daya a cikin Alkur’ani
mai dauke da sunan daya daga cikin matan Annabi (S.A.W),
kamar Khadijah ko Aisha ko kuma yaran sa mata kamar
Fadima ko kuma iyan uwan sa Allah ya kara yadda a gre su,
haka nan kuma babu sura mai dauke da sunan dangin sa, sai dai
ma an samu sura ne mai dauke da alkawari na narkon azaba ga
daya daga cikin dangin sa shi ne baffan sa Abu Lahab wanda
Alkur’ani yayi hukunci cewa shi dan wuta ne, kuma wannan
babu kokwanto a cikin sa wanda haka ke nuni akan gaskiyar
manzancin sa, saboda da ace daga abunda ya rubuta ne da
kansa kamar yadda suke cewa da sun samu kwarzanta kansa a
cikin sa da kuma iyalan sa.
Kuma hakika Manzan musulunci Muhammad (S.A.W) yayi
yabo akan Maryama amincin Allah ya tabbata a gare ta kuma
ya lissafa ta cikin mafiya alherin matan duniya, a inda yace: “
mafi alherin matan duniya su ne: Maryam iyar Imran da
Khadija iyar Khuwailid, da fatima iyar Muhammad
(S.A.W) , da Asiya matar Fir’auna” sahihu ibn hibban.
Kuma Manzan musulunci Muhammad (S.A.W) yayi mata
shaida da cewa tana cikin mafiya falalan matan aljannah, sai
yace: “ mafiya falalan matan aljannah: Khadijah iyar
Khuwailid, da Fatima iyar Muhammad, da Maryam iyar
Imran, da Aiya iyar muzahim matar Fir’auna”. Sahihu ibn
hibban.
54
Alkur’ani mai girma yayi yabo ga Annabi Isah dan Maryam
amincin Allah ya tabbata a gare shi kuma ya siffanta shi da
wasu irin siffofi da suke nuni akan daukakar darajarsa a wurin
Allah madukaki, ta yadda ya sanya shi ya zama bushara ne ga
mahaifiyar sa Maryam amincin Allah ya tabbat aa gare ta, ta
yadda zai bata kayutan yaro zai halicce shi wata irin halitta da
ta sabawa hanyar halittan sauran mutane, zai halicce shi da
kudurarr shi da kuma ikon shi da kalmar “kun” kuma zai zama
mai daraja a duniya da lahira kuma yana cikin makusanta kuma
Annabi mai karamci mai tsarki wanda za’a karrama shi kum a
karfafe shi da wau irin mu’ujizozi, kuma manzo ne zuwa ga
bani isra’ila, kamar yadda Allah madaukaki ya ce: kuma yana
magana da mutane a cikin tsumman goyo da kuma bayan
ya manyanta kuma yana cikin salihai (46) sai tace ya
ubangiji ta yaya zan samu yaro kuma alhali babu wani
mutum da ya taba taba ni sai yace haka nan Allah yake
halitta abunda yaga dama idan ya kaddara wani lamari to
kawai yana ce masa ne kasance sai ya kasance (47) kuma
zai sanar da shi littafi da hikima da Attaura da Injila(48)”
suratu Ali imran, aya ta: 45-48.
55
Allah yayi bayani a cikin Alkur’ani mai girma hakikanin
Annabi Isah dan Maryam amincin Allah ya tabbata a gare shi
da kuma irin abunda Allah madaukaki ya kebance shi da shi na
mu’ujizozi, sai ya baiyyana yadda aka haife shi bayani mai
warkarwa isasshe lafiyaiyyen hankali na karbar sa da kuma
ingantaccen mandiki, ta yadda ya ajiye shi a inda ya dace da shi
a matsayin sa na Annabi sai ya sanya shi mutum bawa ga Allah
wanda aka tsarkake daga alfasha da kuma abunda yahudawa
suka jefe shi da shi cewa wai shi dan zina ne- Allah ya tsare shi
daga hakan- da kuma irin abunda wasu suka jefe shi da shi na
cewa shi dan Allah ne ko kuma shi Allah ne- Allah ya daukaka
daga haka daukaka mai girma-, Alkur’ani baya ganin cewa
haihuwar Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi ba da
uba ba abu ne da zai sa a bauta masa ko kuma ya maida shi dan
Allah- - Allah ya daukaka daga haka daukaka mai girma- a’a ai
a cikin haka akwai dalili da ke nuni akan cikan ikon Allah akan
nau’o’in halitta, domin Allah ya halicci Adam ba tare da namiji
da macce ba, kuma ya halicci Hauwa’u daga namiji ba macce,
kuma ya halicci Annabi Isah daga macce ba namiji, kuma sai
ya halicci sauran halittu daga namiji da macce, Allah
madaukaki yana cewa: “ lallai misalin Isah a wurin Allah
kamar misalin Adam ne ya halicce shi daga turbaya sannan
sai yace masa kasance sai ya kasance (59) gaskiya ce daga
ubangijin ka kada ka kasance cikin masu jayaiyya (60) duk
wanda yayi jayaiyya da kai game da shi bayan abunda yazo
maka na ilimi to kace ku taho mu kira yaran mu da yaran
ku da matan mu da matan ku da mu kan mu da ku kan ku
sannan sai muyi mubahala sai mu sanya tsinuwar Allah ta
56
tabbbata akan makaryata (61) lallai wannnan shi ne
labarin gaskiya kuma babu wani abun bauta da gaskiya sai
dai Allah kuma lalllai Allah shi ne mabuwayi mai hikima
(62) kuma idan suka juya baya to lallai Allah masani ne ga
mabarnata (63) kace yaku ma’abota littafi ku taho zuwa ga
wata kalma wacce take daidaita tsakanin mu da ku cewa
kada mu bautawa kowa sai Allah kuma kada muyi shirka
da shi da komai kuma kada shashin mu su riki sashi
ababen bauta koma bayan Allah to in sun juya baya to kuce
musu ku shaida lallai mu musulmai ne (64) ya ku ma’abota
littafi dan me kuke jayaiyya game da Ibrahim alhalin ba’a
saukar da Attaura da Injila basai a bayan sa shin baza kuyi
hankali ba (65) ku dunnan yanzu kunyi jayaiyya a cikin
abunda kuke da ilimi to dan me kuke jayaiyya a cikin
abunda baku da ilimi akan sa kuma Allah ya san komai
kuma ku baku sani ba (66) Ibrahim bai zama bayahude ba
ko kuma banasare sai dai shi ya kasance ne mai mika wuya
ga Allah musulmi kuma bai kasance cikin mushirikai ba
(67)” suratu Ali imaran, aya ta: 59-63.
Haihuwar Annabi Isah haihuwa ce irin ta mutane, Allah ya
halicce shi a cikin mahaifa kamar yadda ya halicci sauran
halittu, ikon mahalicce ya baiyyana a cikin haihuwar sa ta
yadda ya halicce shi ba uba kamar yadda ta baiyyana ga sauran
halittu da yawa, sai Allah madaukaki ya baiyyana hakikanin
Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi kafin halittar
sa da kuma bayan halittar sa da fadar sa madaukaki: “ kuma ka
ambata a cikin littafin Maryama lokacin da ta fita tabar
mutanen ta ta tafi wuri mai nisa (16) sai ta riki wurin buya
daga gare su sai muka aika mata da mala’ikan mu sai yazo
57
mata a siffar mutum madaidaici (17) sai tace lallai ni ina
neman tsarin mai rahama daga gare ka in kai me tsoran
Allah ne (18) sai yace lallai ni dan sako ne na ubangijin ki
dan in baki kyautar yaro mai tsarki (19) sai tace ta yaya zai
zamu inada yaro alhali babu wani mutum da ya taba ni
kuma ni ba karuwa ba (20) sai yace haka ubangijin ki ya ce
kuma hakan mai sauki ne a gare ni kuma dan mu sanya shi
ya zama aya ga mutane da kuma rahama daga gare mu
kuma hakan al’amari ne da aka riga a hukunta (21) sai ta
dauki cikin sa sai ta tafi da shi wani wuri mai nisa (22) sai
nakuda ta zo mata a gefen wani tushen bishiyar dabino sai
tace kaice na dama na mutu kafin wannan lokacin kuma in
zama abr mantawa (23) sai ya kirata daga kasanta cewa
kada kiyi bakinciki hakika ubangijin ki ya sanya idn ruwa
a kasanki (24) kuma ki girgiza tushen dabinonnan dabinai
danyu masu dadi zasu fado akan ki (25) to ki ci kuma ki sha
kuam ki ji sanyin ido idan har kin ga wani daga cikin
mutane to ki ce lallai ni nayi alwashin azumi ga mai
rahama bazan yi magana da wani mutum ba a yau (26) sai
ta zo da shi wurin mutanen ta tana dauke da shi sai sukace
ya ke Maryam hakika kinzo da wani babban al’amari (27)
ya ke iyar uwar Annabi Haruna mahaifin ki ba mutumin
banza bane kuma mahaifiyarki ba karuwa bace (28) sai tayi
nuni zuwa gare shi sai sukace ta yaya zamuyi magana da
wanda ke cikin tsumman goyo jariri (29) sai yace lallai ni
bawan Allah ne ya bani littafi kuma ya sanya ni a matsayin
Annabi (30) kuma ya sanya ne mai albarka a duk inda nake
kuma yayi mun wasiyya da sallah da kuma zakkah
matukar ina raye (31) kuma ni mai biyaiyyane ga
58
mahaifiyata kuma bai sanya ni na zama mai girman kai ba
tababbe (32) kuma aminci ya tabbata a gare ni ranar da
aka haife ni da kuma ranar da zan mutu da kuma ranar da
za’a tashe ni rayaiyye (33) wannan shi ne Isah dan Maryam
zance na gaskiya da suke kokwantu a kan sa (34) bai
kamata ba ga Allah ya riki wani a matsayin yaro tsarki ya
tabbata a gare shi idan yayi nufi aukuwar wani abu to
kawai yana ce masa ne kasance sai ya kasance (35)” suratu
Maryam, aya ta: 16-35.
Kuma Alkur’ani mai girma ya baiyyana cewa lallai daukar
cikin da Maryam tayi na Annabi Isah ya faru ne da busa daga
mala’ika Jibrilu amincin Allah ya tabbata a gare shi ta yadda ya
zo mata a siffa ta mutum kuma Allah ya umarce shi ya hura
gefen hannun rigar ta, sai iskar ta sauka zuwa farjin ta, sai ta
dau ciki nan take, Allah ya tsare ta ta zama kamar yadda
yahudawa suke tuhumarta cewa ita mazinaciya ce kuma yaran
ta dan zina ne, shi tsarkakakke ne daga haka da mahaifiyar sa
Maryam amincin Allah ya tabbata a gare ta tsarkakakkace daga
datti kuma tsarkakakka ce daga alfasha, Alkur’ani ya barrantar
da ita daga dukkan haka, kamar yadda Allah ya baiyyana haka
a cikin Alkur’ani da fadar sa: “ da kuma wcce ta tsre farjin ta
sai muka yi busa a cikin sa daga ruhin mu kuma muka
sanya ta ita da yaran ta suka zama aya ga talikai (91)”
suratul Anbiya’i, aya ta:91.
59
Alkur’ani ya yi bayanin hakikanin Isah dan Maryam amincin
Allah ya tabbata a gare shi kuma ya bada labari cewa shi bawan
Allah ne Allah yayi ni’ima a gare shi kuma ya zabe shi dan isar
da sakon sa zuwa ga bani isra’ila bayan Annabi Musa, kuma ya
baiyyana cewa mahaifiyar sa ta kasance mai gaskiya ce mai
tsarki duk irin abunda ke samun mutane to itama yana samunta
da yaran ta, su suna ci kuma suna sha kuma suna bacci su tashi
kuma suna ji zafin ciwo kuma suna kuka, to duk wanda haka
shi ne siffar sa to taya zai zama abun bauta? Kuma shi Allah
abun bauta ya tsarkaka daga dukkan wannan, kamar yadda
Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ Msihu dan Maryam
ba kowa bane face Manzo wanda hakika manzanni sun
gabata kafin sa kuma mahaifiyar sa mai gaskiya ce sun
kasance suna cin abinci ka duba kaga yadda muke
baiyyana musu ayoyi sannan ka duba kaga yadda ake
kirkira musu karya (75)” suratul Ma’ida, aya ta: 75.
Allah bai cancanta da mata ba ko yaro domin shi tsarki ya
tabbata a gare shi shi ne ubangijin halittu baki daya babu abun
bautawa da gaskiya sai shi kuma babu abun bauta koma bayan
sa, dan haka jingina wa Allah da yana daga cikin karya mafi
girma a gare shi, duk wani abu da ba Allah ba to halitta ne
bawan sa ne kuma yana karkashin klawar sa yana mai jayuwa a
gare shi makaskanci a gare shi yana mai tabbatar da haka kodai
da harshen sa ko kuma fidirar sa kamar yadda Allah ya
baiyyana hak da fadar sa: “ kuma sukace Allah mai rahama
yana da da (88) hakika kunzo da wani abu mai girma (89)
60
sama ta kusa ruguzowa saboda shi kuma kasa ta tsasttsage
kuma duwatsu su fadi a farfashe (90) saboda sunce Allah
yana da yaro (91) kuma baya kamata ga mai rahama ya
riki wani a matsayin yaro (92) babu wani abu a cikin
sammai da kasa face sai duk sun je wurin mai rahama suna
bayi (93)” suratu Maryam, aya ta: 88-93.
To ta yaya zai zama yanada yaro kuma yaro ba’a samun shi sai
da sakamakon abubuwa biyu daidai da juna kankankan ko
kuma kusa da juna, alhali shi Allah babu irin shi kuma babu
kama da shi, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa:
“ kace shi ne Allah makadaici (1) Allah wanda ake nufin sa
dan biyan bukatu (2) bai haifa ba kuma ba’a haife shi ba
(3) kuma babu wanda ya kasance daidai da shi (4)” suratul
Ikhlas, aya ta: 1-4.
Kuma kirkirawa Allah yaro maganace ba sabuwa ba ta dade
sosai kamar yadda mutum ya dade, ta fara bayana ne bayan fara
baiyanar shirka a cikin mutane, mushirikan larabawa sun yi
karyan cewa wai Allah yayi surukuntakata da aljanu sai ya haifi
mala’iku wanda suke cewa su yaran Allah ne mata- Allah ya
daukaka daga abunda suke fada daukaka mai girma- sai Allah
madaukaki yace: “ ka tambaye su shin ubangijinka nada
yara mata su kuma suna da maza (149) kuma shin mun
halicci mala’iku mata ne alhali su suna gani (150) ku saura
lallai su suna fadan haka ne daga abunda suka kirkira na
karya (151) cewa Allah ya haihu kuma lallai su makaryata
ne (152) ya zabi mata fiye da maza (153) me yasame ku ne
yaya kuke yin hukunci (154) shin baza kuyi tunani ba (155)
ko kuma kunada wata hujja ne baiyyananna (156) to kuzo
da littafin ku in har kun kasance kunada gaskiya (157)
61
kuma suka sanya dangantaka tsakaninsa da aljanu kuma
su aljanu sun san cewa lallai su za’a gurfanar da su (158)
tsarke ya tabbata ga Allah daga abunda suke siffantashi da
shi (159) sai dai bayin Allah wanda aka kubutar (160)”
suratus Saffat, aya ta:149-160.
Kuma da yawa daga cikin yahudawa da kiristoci sun jinginawa
Allah yaro saboda zalunci da kuma karya, dan koyi da wadanda
suka gabace su a fadan wannan maganar wacce lafiyaiyyen
hankali bai yadda da ita kamar yadda Allah ya baiyyana haka a
cikin Alkur’ani da fadar sa: “ kuma yahudawa sunce Uzairu
dan Allah ne su kuma kiristoci suka ce Almasihu dan Allah
ne wannan shi zantuttukan su da bakunan su suna
kwaikwayon zantuttukan wadanda suka kafurta gabanin
su, Allah ya tsine musu ta yaya suke kirkirawa Allah karya
(30) sun riki manyan malaman su da kuma masu bautan su
ababen bauta koma bayan Allah da kuma almasihu dan
Maryam kuma ba’a umarce su ba sai dai su bautawa Allah
shi kadai babu wanin abun bauta da gaskiya sai shi tsarki
ya tabbata a gareshi daga abunda suke shirka da shi (31)”
suratut Taubah, aya ta: 30-31.
Kuma hakika Alkur’ani yayi hukunci dakafurta duk wanda ya
kudurta cewa Annabi Isah dan Maryam shi Allah ne ko kuma
shi yaran Allah ne ko kuma shi ne Allah daya cikin uku, kuma
ya baiyyana cewa da’awar almasihu tsira da amincin Allah ya
tabbata a gare shi ta kasance ne dan tabbatar da tauhidi da kuma
kira zuwa gare shi da kuma rashin yin shirka da Allah dan koyi
da wadanda suka gabace shi cikin Annabawa da manzanni
kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ hakika
wadanda sukace lallai Allah shi ne Almasihu dan Maryam
62
sun kafurta kuma Almasihu yace ya ku mutanen bani
isra’ila ku bautawa Allah ubangiji na kuma ubangijin ku
lallai duk wanda yayi shirka da Allah to hakika Allah ya
haramta masa aljannah kuma makomarsa wuta kuma
azzalumai basuda wasu mataimaka (72) hakika wadanda
suka ce lallai Allah daya ne cikin uku sun kafurta kuma
babu wani abun bauta sai dai abun bauta guda daya kuma
idan basu hanu ba daga abunda suke fada to lallai azaba
mai radadi za ta shafi wadanda suka kafurta daga cikin su
(73) shin baza su tuba zuwa ga Allah ba kuma su nemi
gafarar sa kuma Allah mai yawan gafartawa ne mai jin kai
(74)” suratul Ma’idah, aya ta: 72-74.
Kuma hakika dalilai na hankali wadanda Alkur’ani ke korowa
sun kasance suna nuni akan cewa lallai Allah shi ne mahalicci
mai iko mai jujjuya al’amura ubangijin komai kuma
mamallakin sawanda yake halitta abunda yaga dama kuma yake
aikata abunda yake so, kuma ababen da suke aukuwa ta hannun
Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi na mu’ujizozi
suna faruwa ne da umarnin Allah da ikon saba wai daga wani
umarni bane ta bangare Annabi Isah, kuma suna baiyyana cewa
lalai Annabi Isah da mahaifiyar sa basa mallakan cutarwa ko
amfanarwa ga kawunan su ko ga wanin su cikin mutane kuma
basa mallakar rayuwa ko tashi daga kabari, kuma Allah
madaukaki baya da bukatuwa a gare su ko kuma wata halitta
daga cikin halittun sa, sai dai su halittu ne suke da bukata a gare
shi dukkan su suna tsananin bukatar rahamar sa, inda Allah
madaukaki ya fada: “ hakika wadanda sukace lalai Allah shi
ne almasihu dan Maryama sun kafurta kace musu to waye
ke mallakar wani abu a wurin Allah in ya so ya halakarda
63
Almasihu dan Maryama da mahaifiyar sa da wadanda suke
ban kasa baki daya kuma abunda ke cikin sammai da kasa
da abun da ke tsakanin su na Allah ne yana halitta abunda
ya so kuma Allah mai iko ne akan dukkan komai (17)”
suratul ma’idah, aya ta: 17.
Kuma hakika Allah ya saukar da ayoyin Alkur’ani suna
tsawatar da bani isra’ila suna hana daga wuce iyaka a cikin
addinin su duka fadan wani abu game da Allah ba tare
dagaskiya ba, kuma suna baiyya cewa lallai Annabi Isah
amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda kiristoci ke raya
cewa shi Allah ne ko kuma dan Allah ne ko kuma shi daya ne
cikin uku cewa shi mutum ne kamar sauran mutane, yana kira
zuwa ga Allah kuma yana bautan Allah kuma baya girman kai
ya zama bawa mai kaskantar da kai ga Allah da umarnin sa,
kuma duk wanda toge kuma yayi girman kai ga bautar Allah to
lalo makomar sa itace azaba da kuma dauwwama a cikin wutar
jahannama, kamar yadda Alkur’ani mai karamci ya baiyyana
haka da fadar Allah madaukaki: “ ya ku ma’abota littafi kada
ku wuce gona da iri a cikin addinin ku kuma kada ku fadi
komai game da Allah sai dai gaskiya lallai shi Almasihu
Isah dan Maryaam Manzan Allah ne kuma kalmarsa ce da
ya jefata ga Maryama kuma ruhi ne daga gare shi to kuyi
imani da Allah da manzannin sa kuma kada kuce Allah uku
ne ku hanu daga haka shi yafi alheri a gare ku lallai Allah
abun bauta ne guda daya tsarki ya tabbata a gare shi a ce
yanada yaro dukkan abunda ke cikin sammai da kasa nashi
ne kuma Allah ya isa ya zama wakili (171) Almasihu bazai
yi girman kai ba dan ya zama bawa ga Allah hakanan ma
mala’iku makusanta kuma duk wanda ya doge ya ki bauta
64
masa kuma yayi girman kai to zai tada su zuwa gare shi
baki daya (172) to amma wadanda sukayi imani kuma suka
aikata aiyuka na kwarai to zai cika musu ladan su kuma ya
kara musu daga falalar shi amma kuma wadanda suka
bijire sukayi girman kai to zai azabtar da su azaba mai
radadi kuma baza su samu wani masoyi ko mataimaki ba
koma bayan Allah (173) ya ku mutane hakika gaskiya ta zo
muku daga ubangijin ku kuma mun saukar da wani haske
zuwa gare ku mabaiyyani (174) to duk wadanda sukayi
imani da Allah kuma sukayi ruko da shi to da sannu zai
shigar da su cikin wata rahamadaga gare shi da wata irin
falala kuma zai shiryar da su wata hanya mukakkiya zuwa
gare shi (175)” suratun Nisa’i, aya ta: 171-175.
Kuma a bangare guda na masu cewa shi Allah ne kokuma
yaran Allah ne ko kuma shi Allah daya ne cikin uku hakika su
kuma yahudawa sun kasance suna zargin Annabi Isah ne
amincin Allah ya tabbata a gare shi da cewa shi rai ne na
shaidan mai sharri kuma shi mayaudari ne makaryaci, sai
Alkur’ani ya baiyyana lalacewar zancen su kuma ya baiyyana
cewa Annabi Isah Annabi ne da aka aiko me gaskiya ne cikin
abun da yake isarwa daga ubangijin sa, kamar yaddad Allah
madaukaki ya fada: “ lallai Almasihu Isah dan Maryama
manzan Allah ne kuma kalmar sa ce da ya jefa ta zuwa ga
maryam kuam ruhi ne daga gare shi to kuyi imani da Allah
da kuma manzannin sa....” suratun Nisa’i, aya ta: 171.
Sai dai wannan ruhin irin sauran ruhi ne da aka halitta an
jingina ta ne zuwa ga Allah ta fuskar darajtawa da kuma
karramawa a gare shi, kuma ita kalmar ruhi bawai wani
kebantaccen abu bane da aka kebance Annabi Isah da shi ba shi
65
kadai Annabi Adam amincin Allah ya tabbata a gare shi an
jingina ransa zuwa ga Allah dan girmamawa da karramawa a
gare shi, kamar yadda Allah ya bada labarin haka a cikin littafin
sa da fadar sa: “ lokacin da ubangijin ka ya ce wa mala’iku
lallai ni zan halicci wani mutum daga tabo (71) to idan na
daidaita shi kuma na busa masa daga rai na to ku fadi a
gareshi kuna masu sujada (72)” suratu Saad, aya ta: 71-72.
Kuma kamar yadda ya gabata wurin haihuwar Annabi Isah
amincin Allah ya tabbata a gare shi, inda Allah ya kira mala’ika
Jibril amincin Allah ya tabbat a gare shi ruhi daga Allah
madaukaki lokacin da ya aike shi zuwa wurin maryam amincin
Allah ya tabbata a gare shi dan ya bata kyautar Annabi Isah: “
kuma ka ambata a cikin littafin Maryam lokacin da ta bar
mutanen ta ta tafi wuri mai nisa (16) sai ta riki wurin buya
daga gare su sai muka aika mata da ruhin mu sai ya zo
mata a matsayin mutum madaidaici (17)” suratu Maryam,
aya ta: 16-17.
Hakanan ma Allah ya kira Alkur’ani da suna ruhi saboda
zukata na rayuwa da shi saboda irin abunda ya ke kwararo mata
na kwanciyar hankali da natsuwar zuciya haka nan kuma
al’umma na rayuwa da shi da abunda ke tabbatar msusu da
maslahohin duniya wanda ke ba kowane me hakki hakkin sa sai
rayuka tsaru da mutunci da dukiyoyi, kamar yadda Allah ya
baiyyana haka da fadar sa: “haka nan kuma mukayi maka
wahayin ruhi daga gare mu kai baka kasance kasan meye
rubutu ba ko kuma imani sai dai munsanya shi ya zama
haske muna shiryadda wanda muka gada da shi cikin bayin
mu kuma lallai kai kana shiryarwa zuwa ga hanya
madaidaiciya (52)” suratush Shura, aya ta: 52.
66
Alkur’ani mai girma ya baiyana cewa dukkan Annabawa su
daga zurriyyar Annabi Nuhu suka fito da Annabi Ibrahim
amincin Allah ya tabbata a gare su, kuma dukkan littafan da
suka sauka daga sama an saukar da su ne akan manzanni ne
daga zurriyyar wadannan Annabawan ne biyu masu karamci,
kuam yana daga cikin abunda ba kokwanto a cikin sa cewa
lallai Annabin mu Muhammad (S.A.W) yana daga cikin
zuriyyar Annabi Isma’ila dan Ibrahim amincin Allah ya tabbata
a gare su, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “
kuma hakika mun aiki Nuhu da Ibrahim kuma muka sanya
Annabci da littafi a cikin zurriyyar su su biyu daga cikin su
akwai shiryaiyyu kuma da yawa daga cikn su fasikai ne
(26)” suratul Hadeed, aya ta: 26.
Kuma yana daga cikin tushe na imani a wurin musulmai imani
da manzannin Allah madaukaki dukkan su, hakika umarni ya
zo a cikin Alkur’ani na cewa a girmama su da kuma sansu da
kwarzanta su da kuma kariya a gare su da kuma yada soyaiyyar
su a cikin mutane da kuma imani da abunda aka saukar musu
daga Allah madaukaki, kuma daga cikin wadannan manzannin
akwai Annabi Isah dan Maryam amincin Allah ya tabbata a
gare shi wanda yake da daraja mai girma da matsayi madaukaki
a wurin musulmai, Allah madaukaki yana cewa: “ kuce munyi
imani da Allah da abunda aka saukar mana da abunda aka
saukar wa Ibrahim da Isma’il da Ishaq da Ya’aqubu da
Asbad da abunda aka baiwa musa da Isah da abunda aka
baiwa Annabawa daga ubangijin su bama rarrabe wa
67
tsakanin daya daga cikin su kuma mu masu mika wuya ne
a gare shi (136) idan sunyi imani da irin abunda kukayi
imani da shi to hakika sun shiryu in kuma suka juya baya
to lallai su suna cikin tabewa da sabani kuma da sannu
Allah zai kareka daga gare su kuma shi mai ji ne masani
(137)” suratul Bakara, aya ta: 136-137.
Hakika bani sra’ila kafin aiko da Annabi musa sun kasance
masu rauni kaskantattu kuma ana bautar da su a ban kasa kamar
yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ kuma lokacin
da muka tsiratar da ku daga mutanen Fir’auna suna gana
muku muguwar azaba suna kashe yaran ku maza kuma
suna raya yaran ku mata kuma a cikin haka akwai
jarabawa mai girma daga ubangijin ku (141)” suratul
A’araf, aya ta: 141.
Sai Allah ya yi musu baiwa na aiko da Annabi Musa amincin
Allah ya tabbata a gare shi sai Allah ya daukaka su da wannan
aikowan mai daraja sai halin da suke ciki ya canza daga
kaskanci zuwa daukaka kuma daga talauci zuwa wadata kuma
daga tozarci zuwa daraja sai suka zama sunyi nasara.
Sai zamani yayi tsawo akan mutanen bani isra’ila sai da yawan
su suka kauce daga tsarin Allah wanda Annabi Musa ya zo da
shi sai sukayi zalunci kuma sukayi barna a ban kasa sai suka
karyata kuma suka kashe Annabawa da salihai daga cikin su sai
wasu daga cikin su suka karyata tasi alkiyama da hisabi da
azaba kuma suka nutse a cikin bin san rai da ababen more
rayuwa kuma suka ci ukiyoyin mutane da barna, sai Allah ya
aiko musu da Annabi Isah dan Maryam a matsayin manzo
kuma ya sanar da shi Attaura da Injila dan ya maida su zuwa
68
tsarin ubangiji da kuma mabubbuga tatacciya ingantacciya
wanda zai kubutar da su daga abunda suke ciki na bata kamar
yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ kuma sai biyo
da Annabi Isah dan Maryam a bayan su yana mai gaskata
abunda ya gabace shi na Attaura kuma mun bashi Injila a
cikin ta akwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda
ya gabace shi na Attaura kuam shiriya ne da tunatarwa ga
masu takawa (46)” suratul Ma’idah, aya ta: 46.
Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi ya tsayu da
kiran mutanen bani isra’ila zuwa ga bautar Allah da kuma isar
musu da sakon sa da kuma yin aiki da abun da ya zo a cikin
Injila na hukunce-hukunce mafi alherin tsayuwa, Allah ya bada
labarin haka da fadar sa: “ lokacin da Isah ya zo da hujjoji
baiyyanannu sai yace hakika nazo muku da hikima kuma
zan baiyyana muku sashin abunda kuke sabani a cikin sa to
kuji tsoran Allah kuma kuyi ini biyaiyya (63) lallai Allah
shi ne ubangiji na kuma ubangijin ku to ku bauta masa
wannan itace hanya madaidaiciya (64)” suratuz Zukruf, aya
ta: 63-64.
Lokacin da Annabi Isah ya ga irin yadda suke karyata shi da
kuma kafurcewar su ga da’awar sa sai yayi kira a cikin
mutanen sa yana cewa waye zai taimake ni kuma yayi hakuri
akan abunda zai same shi saboda yada addinin Allah? sai
hawariyawa sukayi imani da shi kuma adadin su mutum goma
sha biyu ne suka kulla alkawi da shi akan zasu yda addinin
Allah da kuma kira zuwa gare shi a cikin mutanen su da kuma
hakuri akan abunda zai same su akan wannan hanyar kamar
yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ lokacin da
Isah ya ga kafurci daga garesu sai yace waye zai taimake ne
69
saboda Allah sai hawariyawa suka ce mu ne mataimaka
Allah munyi imani da Allah kuma ka shaida cewa lallai mu
musulmai ne (52)” suratu Ali imran, aya ta: 52-53.
70
Hakika Alkur’ani ya siffata Annabi Isah amincin Allah ya
tabbata a gare shi da wasu irin siffofi da suke nuni akan darajar
wannan manzan mai karamci a wurin Allah madaukaki kuma
hakika shi ya tattaru siffa ta kamala ta dan dam wanda ke nuni
akan wannan darajar mai girma, kamar yadda Alllah ya
baiyyana haka da fadar sa: “ kuma sai biyo da Annabi Isah
dan Maryam a bayan su yana mai gaskata abunda ya
gabace shi na Attaura kuma mun bashi Injila a cikin ta
akwai shiriya da haske kuma yana gaskata abunda ya
gabace shi na Attaura kuam shiriya ne da tunatarwa ga
masu takawa (46)” suratul Ma’idah, aya ta: 46.
Kuma Alkur’ani mai karamci ya bada labari cewa lallai wannan
manzan abun karfafawa ne daga Allah madaukaki kuma abun
tsarewa ne da tsaran sa, Allah madaukaki yace: “ kuma hakika
mun baiya Musa littafi kuma muka biyo da Annabawa a
bayan sa kuma muka baiya Isah dan Maryam hujjoji
baiyyanannu kuma muka karfafa shi da mala’ika Jibrilu to
yanzu duk lokacin da wani manzo yazo muku da abunda
ranku basa so sai kuyi girman kai wasun su ku kashe su
wasun su kuma ku karyata (87)” suratul Bakara, aya ta: 87.
Kuma manzan Allah (S.A.W) ya siffanta shi da cewa shi abun
koyi ne mai kyau kuam misali ne lafiyayye wurin imani da
ibada da iklasi ga Allah madaukaki, kuma lallai saukar sa a
karshen zamani alama ne me girma cikin alamun tashin
alkiyama kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “