da sunan allah mai rahama mai jin kai
Kafin mu shiga cikin bayani game da rayuwar shugaban mu
Annabi Isah amincin Allah ya tabbata a gare shi a cikin
alkur’ani ya kamata ne mu dan yi shinfida ga wannan maudu’in
da wata iyar gabatarwa wacce zamu bayyana farkon halitta a
cikinta da kuma tushen dan adam da kuma hikimar halittar su
da kuma matsananciyar bukatuwar su ga abincin ruhi wanda
yake tabbatar musu da natsuwa da kuma kwanciyar hankali,
wanda yake rikiduwa cikin aqidar tsara al’amuran su da kuma
na al’ummar su da kuma inda tunanin su ke fuskanta da
ababaen da suka fatan su samu na ingantaccen inda suka
fuskanta, hakan kuwa na cikin ababen da aka shar’anta wanda
ke tabbatar musu kiyaye hakkoki da tsare rayuka da kuma kare
mutunci da dukiya, kuma wadannan shari’u basa zuwa sai ta
hanyar wasu mutane wanda suke isar da sako daga Allah sune
Annabawa da Manzanni tsira da amincin Allah ya tabbata a
gare su.
Dukda cewa Alkur’ani mai girma shima daya ne daga cikin
littattafan da suka sauko daga sama, hakika Allah ya saukar da
shi ga Annabi Muhammad (S.A.W) cikamakin manzanni dan
ya zama shi ne littafi na karshe wanda ya sauko daga sama,
saboda haka ne ya zama littafi na duk duniya baki daya wanda
ya dace da kowane zamani da kuma lokaci kuma ya tattaro
4
dukkan dukkan abunda murtane ke bukata dan tabbatar da jin
dadin su a nan duniya da kuma lahira.
Daga cikin abunda Alkur’ani yayi bayanin sa a kwai jerin
labarin faruwar halitta da kuma samuwar wannan duniyar da
kuma ci gaban da aka samu a cikin ta, ta hanyar uslubi na gaske
wanda hankali lafiyayye ke karba da kuma fidira tatacciya da
mandiki ingantacce wanda aka tace shi daga kwaikwayo,
hakika Alkur’ani mai girma ya maida halittan wannan duniyar
da abunda ke cikin ta zuwa ga Allah shi kadai bashi da abokin
taraiyya.
Kuma hakika manzan musulunci Muhammad (S.A.W) me isar
da sako daga Allah yayi bayanin yadda aka fara halitta a cikin
hadisin Imran binil Husain inda yace: “ wasu mutane daga cikin
mutanen yaman sun zo wurin manzan Allah (S.A.W) sai suka
ce: ya manzan Allah munzo wurinka ne dan ka fahimtar da mu
addini kuma mu tambaye ka game da farkon wannan al-amari
(farkon halitta)? Sai Annabi (S.A.W) yace:” Allah ya kasance
tun farko babu komai a tare da shi kuma al’arshin sa ya kasance
akan ruwa sai ya rubuta komai a cikin lauhil mahfuzi sa’nnan
sai ya halicci sammai da kasa” “sahihu ibn Hibban”.
Sai Annabi (S.A.W) ya baiyana musu abunda yafi
mahimmancin abunda suka tambaya shi ne tabbatar da cewa
Allah na nan tuntuni shi kadai, sai yace: “Allah ya kasance
yana nan tun tuni kuma babu komai sai shi” wato ma’na Allah
ya kasance tun farkon lamari yana nan kuma babu kowa tare da
shi, sai ya fa’idantar da su cewa dadantaka ta kai tsaya ta Allah
ce shi kadai, kuma lallai wanda babu farkon samuwar sa shi ne
Allah tsarkakakke madaukaki kawai, babu wanda ke taraiyya
5
da shi cikin wannan siffan tashi cikin halittu, domin Allahn
taka bata inganta tare da tabbatar da wani abu tare da Allah
cikin samuwar sa tun farko, kuma hakika Allah ya tabbatar a
cikin Alkur’ani mai girma cewa shi samamme ne tuntuni shi
kadai da ma’ana ta bai daya wacce ta tattaro dukkan ma’anoni
dan ya baiyana ma halittun sa cewa wannan duniyar dukkanta
halitta ce, an halicce ta daga babu zuwa samuwa, sai Allah
madaukaki yace: “ abunda ke cikin sammmai da kasa suna
tasbihi ga Allah kuma shi ne mabuwayi mai hikima (1)
mulkin abunda ke cikin sammai da kasa nashi ne yana
rayawa kuma yana kashewa kuma shi mai iko ne akan
dukkan komai (2) shi ne na farko da karshe kuma na
baiyane da boye kuma shi masani ne akan dukkan komai
(3)” suratul Hadeed, aya ta: 1-3.
Allah shi ne na farko tun tuni wanda babu farkon samuwar shi,
ya kasance shi kadai ne tun farko kuma babu wata halitta tare
da shi cikin halittu, yana da dukkan siffofi na kamala da kuma
kyau wanda babu wani wanda ke kama da shi a cikin su kuma
babu wanda yake daidai da shi a cikin su cikin halittu kamar
yadda Allah ya baiyana haka cikin fadar sa madaukaki: “
mahaliccin sammai da kasa ya sanya muku mata daga gare
ku kuma ya sanya dabbobi jinsi biyu dan ya yawaita ku ta
hanyar su babu wani abu wanda yayi kama da shi kuma shi
mai ji ne mai gani (11) mabudan sammai da kasa nashi ne
yana shimfida arziki ga wanda yaga dama kuma ya
kaddara lallai shi masani ne ga dukkan komai (12)”
suratush shurah, aya ta: 11-12.
Kamar yadda Allah ya baiyana rashin yiwuwar iya siffanta shi
dari bisa dri da kuma kewawa wurin sanin sa da girman
6
wannan abun bautan ya baiyyana ga bawa wanda yake bauta
masa sai tsoransa da firgicin sa su auko a cikin zuciyar sa sai ya
kankan da kai a gare shi kuma sai ya tabbatar da rububiyyar sa
da Allahn takakar sa, Allah madaukaki ya fada yana mai bayani
akan gaskiyar wannan lamarin: “ yana sanin abunda ke gaban
sau da bayan su kuma su baza su iya kewaye shi ba da
sanin su (110) kuma fuskoki sun kaskanta ga rayaiyye
madawwami kuma duk wanda ya dauko zalunci to hakika
ya tabe (111) kuma duk wanda ya aikata aiki na kwarai
alhali shi mumini ne to baya tsoran zalunci ko kuma
tawaya (112)” suratu Daha, aya ta: 110-112.
Duk wanda ba Allah ba to fararre ne kuma halitta ne Allah ya
halicce shi da ikon sa sai ya fito da shi daga rashi zuwa
samuwa, kamar yadda Allah ya baiyyana haka cikin fadar sa: “
wannan shi ne Allah ubangijin ku mahaliccin dukkan
komai babu abun bauta da gaskiya sai shi to ta yaya ake
juyadda ku daga bin gaskiya (62) haka nan ake juyad da
wadanda suka kasance da ayoyin Allah suke karyatawa
(63) shi ne wanda ya sanya muku kasa tabbatatta da sama
ginanna kuma ya suranta ku sai ya kyautata suran
halittarku kuma ya azurta ku daga kayan marmari wannan
shi ne Allah ubangijin ku Allah yayi albarka ubangijin
talikai (64) shi ne rayaiyye babu abun bauta da gaskiya sai
shi to ku bauta masa kuna masu tsarkakae addini a gare shi
godiya ta tabbata ga Allah ubangijin talikai (65) kace lallai
ni am hane ni daga bautar abunda kuke bauta ma koma
bayan Allah lokacin da hujjoji suka zo mini daga ubangiji
na kuma an umarce ni da in mika wuya ga ubangijin talikai
(66)” suratu Gafir, aya ta: 62-66.
7
Kuma daga cikin tabbatacciyar aqidar musulmai akwai cewa
lallai Allah yana halittan abunda yaga dama kuma yana aikata
abunda yake so babu mai mayadda hukuncin sa kuma babu mai
gyara ga lamarin sa abunda ya so mai aukuwa ne kuma
umarnin sa mai kasancewa ne, kamar yadda Allah ya baiyana
haka da fadar sa: “ kuma ubangijinka yana halitta abunda
yaga dama kuma ya zabazabi ba a wurin su yake ba tsarki
ya tabbata a gare shi kuma ya daukaka daga abunda suke
shirka da shi (68) kuma ubangijin ka yana sanin abunda
zukatan su ke boyewa da kuma abunda suke baiyanawa
(69) kuma shi ne Allah babu abun bauta da gaskiya sai shi
godiya a gare shi take farko da karshe kuma hukunci nashi
ne kuma zuwa gare shi zaku koma (70)” suratul Kasas, aya
ta: 68-70.
Allah baya halitta dan wasa kuma baya barin halittun sa kara
zube, ba’a halicci wata halitta ba a wannan duniyar sai dan
wata hikima kuma ba’a halicce su ba sai dan suyi wani aiki,
kuma wannan hikimar zata iya zama mun santa kuma zata iya
zama bamu santa ba, hakika ilimin zamani ya baiyanar a
wannan zamanin irin shakuwar da halittu masu rai sukeyi da
junan su cikin abunda ake kira jerin gwanan hanyar abinc1 da
kuma shakuwar halittu da wasu wanda ba suba cikin sauran
halittu daskararu, kamar tasirin haske da duhu da kuma rana da
wata da kuma dare da yini a gare su, wannan shi ne abunda aka
sanar da mu kuma nan gaba za’a zo da sababben bincike, Allah
yayi albarka mafi kyautata halitta wanda yace: “ lallai mu mun
1
- hanyar abinci.
8
halicci kowane abu da kaddara (49)” suratul Kamar, aya ta:
49
www.islamland.com
info@islamland.com
9
Alkur’ani wanda yake maganar Allah ne yayi bayani cewa
lallai farkon duniya an halicce ta ne ba daga wani abu ba kawai
da kaddarawar Allah da kuma ikonsa ya halicce ta da kuma
umarnin sa kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa:
“wanda ya kirkiro halittan sammai da kasa kuma idan ya
hukunta faruwar wani abu to kawai yana ce masa ne
kasance sai ya kasance (117)” suratul bakara, aya ta: 117.
Kuma Annabi Muhammad (S.A.W) yayi bayani cewa lallai
ruwa shi ne farkon abunda aka halittun da Allah ya samar kuma
shi ne tushen komai cikin halittu, Allah ya halicce shi da ikon
sa ba tare da wani tushe ba kuma ya sanya shi tushe na halittar
duniya baki daya, sai yace: “ an halicci komai daga ruwa”
sahihu ibn Hibban.
Allah ya bada labari a cikin Alkur’ani cewa ya halicci sammai
guda bakwai da kassai guda bakwai a cikin kwanaki shida ba
tare da gajiya ba, sai yace: “kuma hakika mun halicci
sammai da kassai da abunda ke tsakanin su a cikin
kwanaki shida kuma babu abunda ya same mu na gajiya
(38)” suratu Qaaf, aya ta: 38.
Duk dacewa yana da iko madaukaki akan halittar su cikin
kiftawar ido ko kuma abunda yafi kusa da haka, kamar yadda
ya baiyana haka cikin fadar sa: “kuma umarnin mu bai
10
kasance ba face sai daya kamar kiftawar ido (50)” suratul
Kamar, aya ta: 50.
In aka ce: to dan me bai halicce su ba cikin sakan daya matukar
yana da iko yace musu kasane sai su kasance?
Ibn jauzy ya fada game da baiyana wasu daga cikin hikimar
hakan:
Na farko: lallai Shi yayi nufin samar da wani abu a kowace
rana wanda mala’iku zasu dinga girmama hakan da kuma
dukkan wanda yake kallon sa.
Na biyu: lallai hakan tabbaci ne na shimfida ga abunda za’a
halitta ga Annabi Adam da zuriyar sa tun kafin a halicce shi,
hakan zai fi girma wurjen girmama shi a wurin mala’iku.
Na uku: lallai gaggawa yafi karfi ta bangaren iko, shi kuma
tabbata yafi tasiri ta bangaren hikima, sai yayi nufin baiyana
hikimar sa a cikin haka, kamar yadda yake baiyana ikon sa
cikin fadar sa: “kasance sai ya kasance”.
Na hudu: lallai shi ya koyarda bayin sa tabbatatuwa, duk
abunda ya tabbata bazai gushe ba, abunda yake gushewa shi ne
yafi kamata da tabbatuwa.
Na biyar: lallai wannan jinkirin wurin halittar wani abu bayan
wani abu, yafi nisantuwa wurin tunanin cewa hakan ya auku ne
da dabi’a ko kuma da yarjejeniya.
Da kuma wata hikimar wacce Kurdaby Allah yayi masa rahama
ya ambata- a cikin tafsirin sa “ Aljam”i li Ahkamil Kur’an” sai
yace: Allah ya halicce su ne cikin kwanaki shida, saboda komai
nada lokaci a wurin sa, da wannan sai ya baiyana rashin
11
gaggawa wajan yin ukuba ga masu sabo, saboda komai yana da
lokaci n sa.
Kuma bayani filla-filla ya zo a cikin Alkur’ani game da halittar
sammai da kasa cikin fadar Allah madaukaki: kace shin yanzu
ku za ku dinga kafurce ma wanda ya halicci kasa a cikin
kwana biyu kuma ku dinga sanya masa kishiyoyi wannan
shi ne ubangijin talikai (9) kuma sai dora mata duwatsu a
samanta kuma ya sanya albarka a cikin ta kuma ya kadda
abincin ta a cikin ta a cikin kwanaki hudu dai dai ne ga
masu tambaya (10) sa’nnan sai ya daidaita a sama alhali
lokacin ita hayaki ce sai yace mata da kasa ku taho kuna
masu biyaiya ko kuma rashi biyaiya sai suka ce mun zo
muna masu biyaiya (11) sai ya kaddara su sammai bakwai
a cikin kwana biyu kuma yayi ahayi a ckin kowace sama da
al’amuranta kuma muka kawata saman duniya da fitilu da
kuma tsaro wannan kaddarawa ne na mabuwaye masani
(12)” suratu Fussilat, aya ta: 9-12.
Sayyid qutub yana cewa a cikin littafin sa “ Fi zilalil kur’an”
.....wadannan kwanaki biyu wanda Allah ya halicci kasa a cikin
su, da kuma kwanaki biyu wanda ya halicci duwatsu a cikin su
kuma ya kaddara abinci kuma ya saukar da albarka a cikin su
sai suka cika daidai cikin kwanaki hudu.....lallai su babu
kokwantu kwanaki ne cikin kwanukan Allah wanda shi ne
yasan irin su, su ba irin kwanukan mu bane na duniya.....kuma
kwanakin da aka halicci kasa a cikin su da farko, sa’annan sai
aka samar da duwatsu a cikin su, kuma aka kaddara abinci a
cikin su, su wasu kwanuka ne na daban wanda ake kiyasta su
da wani ma’auni na daban wanda basu san hi ba, sai dai mu
mun san cewa sunfi kwanakin duniya da muka sani tsawo sosai
12
kuma mafi kusan abunda zamu sawwara da shi daidai da abun
da ilimin mu ya kai na iyan adam cewa lallai su wasu lokuta ne
wamda suka gabata a ban kasa zamani bayan zamani, har ta
tabbata kuma bayan ta yayi kauri, kuma ta zama dai dai da
hadda za’a iya rayuwa a cikin ta wadda muka sani.
13
A nan ne tambaya ta hankali ke zuwa cewa: me dalilin halittar
mutane wanda Allah ya yi musu irin wannan karramawar ta
hanyar hore musu dukkan abun da ke cikin wannan duniyar?
Kuma miye dalilin halittar su?
Hakika Alkur’ani mai girma ya baiyana hikimar halittan
mutane a fili ta yadda kar ya bar fage dan lalube da hange na
kwakwale da tunane-tunane, sai Alkur’ani yayi bayani cewa
lallai su an halicce su ne dan wani abu mai girma kuma babba
saboda shi ne Allah ya halicci sammai da kasa kuma saboda shi
ne aka halicci aljannah da wuta, wannan kuwa ba komai bane
face bautar Allah shi kadai bashi da abokin taraiyya kamar
yadda Allah ya baiyana hak da fadar sa: “ kuma ban halicci
aljanu da mutane ba sai dan su bauta mini (56) bana nufin
wani arziki daga wurin su kuma bana nufin su ciyar da ni
(57) lallai Allah shi ne mai azurtawa ma’abocin karfi mai
tsanani (58)” suratuz Zariyat, aya ta: 56-58.
Rayuwar ba kamar yadda i’yan gurguzu da mulhidai suke
tunani bace cewa babu tashi bayan mutuwa kuma babu hisabi
kuma babu ukuba kawai rayuwa ce da karewa, kamar yadda
Allah ya bada labarin su da fadar sa: ´kuma suka cea ba wani
abu bane face rayuwar mu ata duniya muna mutuwa kuma
muna rayuwa kuma babu abunda ke halaka mu face
zamani kuma su basu da wani ilimi akan haka kawai su
suna zato ne (24)” suratul Jasiya, aya ta: 24.
Babu abunda yafi wahala irin ace mutum ya rayu da wannan t
tunanin kuma babu ran da tai tozarta feye da ran da ta kudurce
wannan , saboda mutum kamar yada yake da bukatuwa ta
14
kosarda burin sa na jiki a cikin a bunda yake bukata haka nan
ma bukatun sa na ruhi, kuma wannan bai yiwuwa sai ta hanyar
sanin Allah shi kuma wannan bai yuwuwa sai ta hanyar bin
abunda manzanni suka zo da shi, kuma ita kadiyyar ilhadi da
kuma inkarin tada mutane bayan mutuwa zance ne wanda ba
wannan zamanin aka fara shi ba, a a zance ne da yake ta yawo
tsakanin mutane tun da wanda suke mulhidai ne suna koyar da
ita daga wasu a’umma zuwa wasu wadanda ke bayan su dan
wanda Allah ya tayshe basirar sa daga gaskiya ya rungume ta
saboda kauda kai da yayi daga manhajin Allah da kuma
hukuntar da hankali da yayi a inda ba’a hukuntar da hankali a
cikin sa, Allah madaukaki yana cewa: “ sai muka aika da
manzo daga cikin su zuwa gare su cewa ku bauta wa Allah
baku da wani abun bauta koma bayan sa shin baza ku ji
tsoran Allah ba (32) sai manya suka ce daga cikin mutanen
sa cikin wadanda suka kafurta kuma suka karyata da
haduwar lahira kuma muka jiyar da su dadi a rayuwar
duniya wannan ba komawai bane face wani mutum daga
cikin ku yana cin irin abunda kuke ci na abinci kuma yana
shan irin abunda kuke sha (33) kuma idan har kuka yi
biyayya ga wani mutum irin ku to lallai ku hasararru ne
(34) yanzu zai dinga muku alkawari cewa lallai ku in kun
mutu kuma kuka kasance turbaya da kasusuwa wai lallai
za’a fitar da ku (35) har abada abunda yake muku alkawari
bazai faru ba (36) kawai ba wane abu bane face rauwar mu
ta duniya muna mutuwa kuma muna rayuwa kuma mu
baza’a tashe mu ba (37)” suratul muminuun, aya ta: 32-37.
Hakika mutane sun kasance a farkon halitta al’umma ne guda
daya kansu a hade ba a rarrabe ba saboda suna zaune ne a wuri
15
daya iyakantacce kuma basu da yawa sai dai bayan da yaran
Adam sukayi yawa kuma inda suke zaune yayi musu kadan sai
hakan ya tilasta ma wasun su tashi daga inda suke zuwa wasu
bangarori na ban kasa da kuma yaduwa cikin ta dan bincike da
neman arziki, kuma hakika Alkur’ani ya baiyyana wannan
hakikar zancen inda Allah madaukaki ya fada: “ kuma mutane
basu kasance ba a da face al’umma guda daya sai suka
rarrabu badan wata kalma wadda ta gabata daga ubangijin
ka ba da anyi hukunci tsakanin su cikin abunda suka
kasance suna sabani a cikin sa (19)” suratu Yunus, aya ta: 19.
Sai wannan warwatsuwar a bayan kasa ta haifar da sabanin ta
bangaren yaruka da al’au haka nan ma da kuma nisanta daga
tushen addini na farko, yana daga cikin adalcin na Allah wanda
baya zalunci da mugunta shi ne cewa baya yin azaba sai bayan
yayi gargadi ta hanyar wanda yake aikowa cikin Manzannin sa
dan suyi wa mutane bayanin ingantacciyar hanya ta gaskiya
wacce take kaiwa zuwa gare shi, sai rahamar Allah ga mutane
ta hukunta cewa bazai yi musu ukuba ba har sai ya aiko musu
da manzanni wadan da suke nuna musu hanyar shiriya, kuma
suna tsawatar da su daga bin hanyar bata, kamar yadda mukayi
bayani a baya, saboda haka ne ma babu wata al’umma da ba’a
aika mata da manzo ba da kuma sako cikin koane amani, kamar
yadda Allah madaukaki ya baiyyana haka cikin fadar sa: “
lallai mu mun aiko ka da gaskiya kana mai bushara da
kuma gargadi kuma babu wata al’umma face sai mai
gargadi ya je mata (24)” suratu Fadir, aya ta: 24.
Allah madaukaki ya kasance yana aikawa da manzanni da
Annabawa tsakanin wani lokaci zuwa wani lokaci dan su maida
mutane zuwa ga kadaita ubangijin su da kuma bauta masa
16
bayan sun kauce wa a kidar su kuma manhajin su ya samu
matsala, dukkan su tsira da amincin Allah ya tabbata a gare su
tun daga na farkon su har zuwa na karshen su da’awar su iri
daya ce wacce ta hadu akan tauhidi wanda shi ne kadaita Allah
da bauta wurin kudurcewa da zantuttuka da kuma aiyyuka da
kuma kafurce ma dukkan abunda ake bauta mawa koma bayan
sa saboda fadar Allah madaukaki: “ kuma hakika mun aika
da manzao a cikin kowace al’umma cewa ku bauta ma
Allah kuma ku nisanci dagutu daga cikin su akwai
wadanda Allah ya shiryar kuma daga cikin su akwai
wadanda bata ta tabbata a kan su kuyi tafiya a ban kasa sai
kuyi dubi kuga yaya karshen masu karyatawa take
kasancewa (36)” suratun Nahl, aya ta: 36.
Kuma wadannan manzanni Allah madaukaki yana aiko su ne
saboda kada ya zamo an samu wata hujja akan Allah ga mutane
bayan manzanni, kamar yadda Allah madaukaki ya bada labari
da fadar sa: “ manzanni ne masu bushara da kuma gargadi
saboda kada a samu wata hujja akan Allah bayan aiko da
manzanni kuma Allah mabuwayi ne mai hikima (165)”
suratun Nisa’i, aya ta: 165.
Dukda sanin cewa dukkan manzanni da annabawa sun kasance
mutane ne su kuma basuda wani abu na siffan Allahn taka,babu
wani bambanci tsakanin su da wasun su cikin mutane sai da
abunda Allah ya kebance su da shi kawai na ma’asumanci cikin
abunda suke isarwa daga gare shi da kuma abunda ya kebance
su da shi na mu’ujiza wacce take gudana ta hannayen su dan ta
zama aya ga mutanen su dan suyi imani kuma su tabbatar da
gaskiyar manzancin su da Annabtakan su, Allah madaukaki
yana cewa: “ kuma bamu aiko ba gabanin ka cikin
17
manzanni face su suna cin abunci kuma suna zuwa kasuwa
kuma muka sanya sashinku fitina ne ga sashi ko zaku iya
hakuri kuma ubangijin ka ya kasance mai hakuri (20)”
suratul Furkan, aya ta: 20.
Kuma Allah ya baiyyana mutuntakan su da kuma irin abunda
suke da shi na fidira hakika sun kasance suna da mata da kuma
zurriyya saboda kada wani yayi tunanin cewa su da ban ne da
mutane, Allah madaukaki yana cewa: “ kuma hakika mun
aika da manzanni tun gabanin ka kuma muka sanya musu
mata da kuma zuriyya kuma baya kamata ga wani manzo
yazo da wata aya sai da izinin Allah kowane abu yana da
lokaci rubutacce (38)” suratul Ra’ad, aya ta: 38.
Kuma Allah madaukaki yana cewa: “ hakika wadanda sukace
lallai Allah shi ne masihu dan Maryam sun kafurta kuma
masihu yace yaku bani isra’ila ku bautawa Allah ubamgiji
na kuma ubangijin ku lallai duk wanda yayi shirka da
Allah to hakika Allah ya haramta masa shiga aljannah
kuma makomar sa wuta kuma azzalumai basuda
mataimaka (72) hakika sun kafurta wadanda sukace lallai
Allah dayan uku ne kuma babu wani abun bauta sai dai
abun bauta guda daya kuma idan basu hanu ba daga
abunda suke cewa to lallai azaba mai radadi zata shafi
wadanda suka kafurta daga cikin su (73) shin baza su tuba
ba zuwa ga Allah kuma su nemi gafarar sa kuma Allah mai
yawan gafara ne mai jin kai (74) masihu dan Maryama ba
kowa bane face manzo wanda manzannin sun shude
gabanin sa kuma mahaifiyarsa ta kasance mai gaskiya
dukkan su biyun sun kasance suna cin abinci ka duba
yadda muke musu bayanin ayaoyi sa’annan kuma ka duba
18
yadda ake juya su (75) kace shin yanzu zaku dinga bauta
ma wani abu daban koma bayan Allah wanda baya
mallakar cutarwa ko amfanarwa gare ku kuma Allah shi ne
mai ji masani (76) kace ya ku ma’abota littafi kada ku wuce
gona da iri cikin addinin ku da abunda ba gaskiya ba kuma
kada ku dinga bin san ran wasu mutane wadanda sun bace
tun gabanin haka kuma sun batarda mutane da yawa kuma
sun bata daga hanya madaidaiciya (77)” suratul Ma’idah,
aya ta: 72-77.
Kuma basu da wani abu da ya shafi al’amuran ubangiji da
bauta, basuda ikon yin tasarrufi cikin duniya kuma basa
mallakawa kansu ko wanin su cutarwa ko amfanarwa kuma
basa mallakar mutuwa ko rayuwa ko kuma tashi daga kabari,
Allah madaukaki yana cewa yana bada labari gameda manzan
sa Annabi Muhammad (S.A.W) wanda shi ne mafi falalar
mutane kuma mafi tsarkin su: “ kace bana mallakar
amfanarwa ko cutarwa ga kaina sai abunda Allah ya so
kuma da ace nasan gaibu da na yawaita aikin alheri kuma
da ba wani abu da zai same ni na cutarwa ni ba kowa bane
face mai gargadi da bushara ga mutanen da sukayi imani
(188)” suratul A’araf, aya ta: 188.
19
Hikimar Allah da nufin sa sun zartu akan cewa zai sanya halifa
a ban kasa wanda zai raya ta kuma za’a samu yaduwa cikin
zurriyyar sa wadanda hakan da izinin Allah zai tabbatar da
abunda hikimar sa ta hukunta na raya kasa, kuma dan ta zama
gidan jarabawa da fitina a gare su, dan mai biyaiyya a cikin su
gare shi ya baiyyana cikin bayin sa kuma waye mai sabawa
kuma waye mumini sannan kuma waye zai kafurta, Allah
madaukaki yana cewa: “ kuma lokacin da ubangijin ka yace
wa mala’iku lallai ni zan sanya halifa a ban kasa sai suka ce
yanzu zaka saka a cikinta wadanda zasu yi barna a cikin ta
kuma su zubarda jini kuma alhali mu muna tasbihi a gare
ka kuma muna tsarkake ka sai yace lallai ni na san abun da
baku sani ba (30)” suratul Bakara, aya ta: 30.
Sai wannan halifan ya zama shi ne Annabi Adam amincin
Allah ya tabbata a gare shi uban mutane na karshe cikin
nau’o’in abunda Allah madaukaki ya halitta, kuma an halicce
shi ne ranar juma’a kamar yadda manzan Allah (S.A.W) ya
baiyana haka cikin fadar sa: “ mafi alherin yini da rana ta
bullo a cikin sa shi ne ranar juma’a, a cikinta ne aka halicci
Adam, kuma a cikin ta ne aka shigar da shi aljannah, kuma
a ciki ta ne aka fitar da shi daga cikin ta, kuma alkiyama
baza ta tsayu ba sai ranar juma’a” sahi hu muslim.
Saboda haka ne Allah madaukaki ya zabe ta dan ta zama ranar
idi ga musulmai a duk sati, kuma saboda darajar Adam da
matsayin sa a wurin Allah sai ya umarci mala’ikun sa da suyi
masa sujada dan matsayin sa da darajta shi da kuma karamci a
wurin halittar sa kuma ya yi busa a cikin sa daga ruhin sa sai
20
dukkan mala’iku suka yi biyaiyya ga umarnin Allah sai dai
Iblis wanda ya saba wa Allah kuma yaki yin sujada dan hassada
da kuma girman kai daga kansa ga wannan abun halittan wanda
Allah ya fifita shi a kan sa, kamar yadda Allah ya bada labarin
haka da fadar sa:” lokacin da ubangijin ka yace wa mala’iku
lallai ni zan halicci wani mutum daga turbaya (71) idan na
daidaita shi kuma na busa masa daga rai na to ku fadi a
gare shi kuna masu sujada (72) sai mala’iku dukkan su
sukayi sujada (73) sai dai ibilis ne yayi girman kai kuma ya
kasance cikin kafirai (74) sai yace ya kai ibiis meye ya
hanaka yin sujada ga abunda na halitta da hannaye na biyu
shin kayi girman kai ne ko kuma ka kasance ne cikin
madaukaka (75) sai yaceni na fi shi alhri ka halicce ni daga
wuta shi kuma ka halicce shi daga turbaya (76) sai yace to
ka fita daga cikin ta domin lallai kai tsinanne ne (77) kuma
lallai akwai la’anta ta akan ka har zuwa ranar sakamako
(78) sai yace ya ubangiji to ka jinkir ta mun har zuwaranar
da za’a tada su (79) sai yace lallai kai kana cikin wadanda
za’a yi musu jinkiri (80) har zuwa ranar da aka sa lokaci
sananne (81) sai yace to saboda buwayarka lallai ni sai na
batar da su baki dayan su (82) sai dai bayin ka a cikin su
wadan da aka tsiratar (83) sai yace magana ta gaskiya
kuma wallahi gaskiya nake fada (84) wallahi lallai sai na
cika wutar jahannama da kai da kuma wadanda suka bi ka
cikin su baki daya (85)” suratu Saad, aya ta: 71-85.
Sai halittan sammai da kasa ya zama shinfida ne na halittar
Adsam amincin Allah ya tabbata a gare shi wanda hikimar
Allah ta hukunta yaduwar mutane zata fara ne daga gare shi da
kuma matar sa Hauwa’u, sai Allah madaukaki yayi bayani
21
cewa wannan duniyar da dukkan abbunda ke cikin ta an yi su
ne dan dan Adaman halicce su ne dan ya amfana da abunda
Allah ya sanya a cikin ta na alheri kuma dan ya zama fili e mai
fadi a gare shi wanda ta hanyar sa ne zai iya gano abunda zai
tabbatar masa da rayuwa ta karamci, inda Allah madaukaki
yace: “ ashe baku gani ba cewa lallai Allah ya hore muku
abunda ke cikin sammai da kasa kuma ya cika muku
ni’imar sa a gare ku ta baiyyane da boye kuma daga cikin
mutane akwai wadanda suke jayaiyya game da Allah ba
tare da wani ililimi ba ko kuma shiriya ko kuma wani littafi
mai haskakawa (20)” suratul Luqman, aya ta: 20.
Kuma dan ya zama wuri mai fadi dan tunani da kuma lura
wadanda suke kaiwa zuwa ga sanin wannan mahaliccin mai
girma wanda ya cancanta da bauta kamar yadda Allah ya
baiyyana haka da fadar sa: “ lallai a cikin halittar sammai da
kasa da kuma sabawar dare da rana akwai ayoyi ga masu
hankali (190) wadanda suke ambatan Allah a tsaye da
zaune da kuma kan gefen jikin su kuma suna tunani cikin
halittar sammai da kasa suna cewa ya ubangijin mu baka
halicci wannan dan wasa ba tsarki ya tabbata a gare kato
ka kare mu daga azabar wuta (191) ya ubangijin mu lallai
kai duk wanda ka shigar da shi wuta to hakika ka tabar da
shi kuma azzalumai basu da mataimaka (192) ya
ubangijinmu lallai u munji wani mai kira yana kira zuwa
ga imani cewa kuyi imani da ubangijin ku sai mukayi imani
ya ubangijinmu to ka gafarta mana zunuban mukuma ka
kankare mana kurakuran mu kuma ka kashe mu tare da
masu biyiaiyya (193) ya ubangijinmu kuma ka bamu
abunda kayi mana alkawari da shi ta hanyar manzannnin
22
ka kuma kada ka tozarta mu ranar alkiyama lallai kai baka
saba alkawari (194)” suratu Ali imran, aya ta:190-194.
23
Bayan shaidan ya sabawa ubangijin sa yaki yin sujada ga Adam
sai Allah ya rubuta masa tabewa da kuma fitarwa daga
aljannah, sai shaidan yayi alkawarin batar da iyan adam da
kuma kautar da su daga hanya ingantacciya saboda hassadar da
ke ransa kamar yadda yayi hassada ga babansu Annabi Adam
kamafin haka, kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar
sa: “ lokacin da ubangijin ka yace wa mala’iku lallai ni zan
halicci wani mutum daga busashshen tabo mai canzawa
(28) to idan na daidaita shi kuma na busa masa daga ruhi
na to ku fadi a gare shi kuna masu sujada (29) sai mala’iku
dukkan su sukayi sujada baki daya (30) sai dai iblis shi yaki
ya zama tare da masu sujada (31) sai yace ya kai iblis me ya
same ka baka tare da masu sujada (32) sai yace ban zama
mai sujada ba ga wani mutum wanda ka halicce shi daga
tabo baki busashshe mai caccanzawa (33) sai yace to ka fita
daga cikinta domin lallai kai korarre ne (34) kuma kai lallai
akwai tsinuwa akan ka har zuwa ranar sakamako (35) sai
ya ce ya ubangiji to ka mun jinkiri har zuwa ranar da za’a
tada su (36) sai yace lallai kai kana cikin wadanda za’ayi
wa jinkiri (37) har zuwa ranar da aka sa lokai sananne (38)
sai yace ya ubangiji saboda batar dani da kayi sai na
kawata musu duniya kuma wallahi lallai sai na batar dasu
baki daya (39) sai dai bayinka a cikin su wadan da ka
kubutar (40) sai yace wannan itace hanya ta madaidaiciya
(41) lallai bayina baka da wani iko akan su sai dai wadanda
suka bika cikin batattu (42) kuma lallai wutar jahannama
24
itace inda akayi musu alkawari dukkan su (43)” suratul Hijr,
aya ta: 28-43.
Kuma hakika farkon gabar da iblis yake yiwa Adam ta fara ne
cikin a gidan aljannah tun farkon fara halittar shi, sai ya fara
dakun sa yana kulla masa makirci kuma yana rudar shi da yaci
daga wannan bishiyar da Allah ya hane shi ci daga gare ta dan
ya samu ya fitar da shi da matar sa daga cikin ta da kuma irin
ni’imar da suke cikin ta, sai shaidan ya samu damar batar da
Adam amincin Allah ya tabbata a gareshi har sai da Adam yaci
wannan bishiyar sai daga baya yayi nadama akan wannan
sabon da yayi kuma ya tabbatar da kuskuran sa sai ya tuba
kuma ya nemi gafarar Allah sai Allah ya karbi tubar sa, to
sakamakon wannan laifin sai aka fitar da shi daga aljannah da
matar shi kuma aka saukar da su zuwa kasa kamar yadda Allah
ya baiyyana haka da fadar sa: “ kuma lokacin da mukace wa
mala’iku kuyi sujada ga Adam sai sukayi sujada sai dai
Iblis ne yaki yin sujada (116) sai mukace ya Adam lallai
wannan makiyin ka ne da matar ka to kada ku yadda ya
fitar da ku daga aljannah sai ku tabe (117) lallai kai baza
ka ji yunwa ba a cikinta kuma baza kayi tsiraici ba (118)
kuma lallai kai baza ka ji kishi ba a cikinta kuma baza ka
yi walha ba (119) sai shaidan ya samai wasiwasi sai yace ya
kai Adam shin bazan nuna maka wata bishiya ba ta
dawwama da kuma wani irin mulki da baya yanke wa (120)
sai suka ci daga gare ta sai al’aurar su ta baiyana a gare su
sai suka fara boye ta da ganye na aljannah kuma sai Adam
ya saba wa ubangijin sa sai ya bace (121) sa’annan sai
ubangijin sa ya zabe shi sai ya karbi tubarsa kuma ya
shirya shi (122) sai yace ku fita daga cikin ta dukkan ku
25
sashinku yana makiyi ga sahi to idan shiriya tazo muku
daga gare ni to duk wanda yabi shiriya ta to bazai bata ba
kuma bazai tabe ba (123) kuma duk wanda ya kauda kai
daga ambato na to lallai shi yana da wata irin rayuwa ta
kunci kuma zamu tada shi ranar alkiyama makaho (124)
sai yace ya ubangiji dan me ka tada ni makaho alhali da na
kasance ina gani (125) sai yace hakannan ayoyin mu suka
zo maka sai ka manta da su to haka nan kaima yau za’a
manta da kai (126) kuma haka nan muke sakawa duk
wanda ya ketare iyaka kuma bai yi imani da ayoyin
ubangijin sa ba kuma lallai azabar lahira tafi tsanani kuma
tafi dauwama (127)” suratu Daha, aya ta: 116-127.
Bayan karni goma daga sauko da Iblis daga aljannah zuwa ban
kasa saboda sabawa umarnin Allah madaukaki da yayi na kin
yin sujada ga Adam kuma shima Adam aka sauko da shi daga
aljannah saboda sabawa umarnin Allah da yayi na cin bishiyar
da aka hana shi ci daga gare ta, sai sabani da shirka da kuma
ninsanta daga manhajin Allah da ya tsara wa Adam da zuriyyar
sa suka auku, wanda ke tabbatar musu da jin dadi a gidaje biyu
na duniya da lahira, saboda farkon manzanni bayan Adam shi
ne Nuhu amincin Allah ya tabbata a garesu wanda a cikin
mutanen sa ne shirka ta fara baiyana sai aka aike shi zuwa gare
su dan ya maida su zuwa manhajin Allah, Allah madaukaki
yana cewa yana mai hikaito da’awar Annabi Nuhu ga mutanen
sa: “ sai Nuhu yace ya ubangiji lallai su sun saba mini kuma
sun bi wanda bazai kara musu komai ba a cikin dukiyar su
da yaran su sai dai hasara (21) kuma sunyi makirci makirci
mai girma (22) kuma suka ce kada ku bar ababen bautar
ku kuma kada ku bar Wuddu da Suwa’a da Yagusa da
26
Ya’uka da Nasra (23) kuma hakika sun batar da mutane da
yawa kuma kada ka karawa azzalumai sai dai bata (24)
saboda sabun da sukeyi ne aka nutsar da su a cikin ruwa
sannan za’a sa su a cikin wuta kuma baza su samu wasu
masu taimaka musu ba koma bayan Allah (25) kuma
Annabi Nuhu yace ya ubangiji kada ka bar wani gida na
kafiri a ban kasa (26) domin lallai kai in ka kyale su to zasu
batar da bayin ka kuma baza su dinga haihuwa ba sai
fajirai kafurai (27) ya ubangiji ka gafarta mini da iyayena
da duk wanda ya shiga gidana yana mumini da muminai
maza da mata kuma kada ka kara wa kafurai sai dai
halaka (28)” suratun Nuh, aya ta: 21-28.
27
Mutane suna da bukatar manzanni da kuma karantar war su irin
yadda suke da bukata ga abinci da abin sha, su suna da
bukatuwar su dan su san mahaliccin su ta hanyar su kuma dan
karantarwar su ta zama hanya ta gyaran rayuwar su da kuma
haskaka zukatan su da kuma shiryar da kwakwalen su, kuma
dan su san inda zasu dosa a cikin rayuwa ta sanadiyyar su da
kuma alakar su da rayuwa da abunda ke cikin ta, ta yadda baza
su kauce ba su auka cikin alfasha da zunubai kuma dan su san
hakkin su da kuma abunda ya wajaba a kan su ta fuskar
mahaliccin su da kawunan su da kuma mutanen da ke kewaye
da su.
Ibn alkayyim yana cewa yana mai baiyyana wannan lamari:
kuma daga nan ne zaka san irin matsananciyar bukatar bawa
zuwa ga sanin manzannin cewa ta wuce kowace bukata, da
kuma abunda yazo da shi, da gaskata shi cikin abunda ya bada
labarin shi, da yi masa biyayya cikin abunda ya bada umarni,
domin kuwa lallai babu wata hanya ta jin dadi da rabauta a
duniya da kuma lahira sai ta hanyar manzanni, kuma babu wata
hanya ta sanin kyawawa daga munana filla-filla sai ta bangaren
su, kuma ba’a samun yaddar Allah ko kadan sai ta hannun su,
abu mai kyau na aiyuka da zantuttuka da halaye ba komai bane
face shiryarwar su da kuma abny da suka zo da shi, su ne
ma’auni mai rinjaye, wanda da aiyukan su da zantuttakan su da
halayen su ne ake auna halaye da aiyuka, kuma da bin su ne
shiryaiyyu suke banbanta da batattu, bukata zuwa gare su tafi
bukatuwar gangan jiki zuwa ga ruhin sa, da bukatauwar ido
28
zuwa ga hasken sa, da bukatuwar ruhi zuwa ga rayuwar sa, duk
wata irin bukatuwa da matsantuwa da za’a kwatanta to
bukatuwar bawa zuwa ga manzanni tafi tsanani sosai, meye
tunanin ka da wanda idan shiriyar sa ta kubce maka da kuma
abunda ya zo da shi ko da da kiftawar ido ne zuciyar ka zata
baci, kuma ta zama kamar kifi idan ya bar cikin ruwa aka jefa
shi cikin kaskon suya, to halin da bawa zai samu kansa idan
zuciyar sa ta rabu da abunda manzanni suka zo da shi kamar
irin wannan halin ne kai yama fi haka tsanani sai dai babu mai
jin hakan sai dai zuciya rayaiyya.
29
Lallai manzanci da Annabci kyauta ce ta ubangiji da kuma zabi
na Allah kuma tagomashi ne daga ubangiji Allah yana yin
kyautar sa ga wanda yaga dama cikin bayin sa bata da alaka da
dangantaka ko alfarma ko daraja, Allah masani ne mai hikima a
inda yake sanya manzancin sa, inda Allah madaukaki yake
cewa: “ ya ku mutane an buga wani misali sai ku saurare
shi lallai wadanda kuke kira kuna bauta musu koma bayan
Allah baza su iya halittan kuda ba koda sun tarun masa ne
kuwa kuma idan kuda ya fisgi wani abu a wurin su baza su
iya kwato shi daga wurin shi ba me nema da wanda ake
nema duk masu rauni ne (73) basu girmama Allah ba
yadda ya kamata su girmama shi ba lallai Allah mai karfi
ne mabuwayi (74) Allah yana zaban manzanni daga cikin
mutane da mala’iku lallai Allah mai ji ne mai gani (75)”
suratul hajj, aya ta: 73-75.
Shi yasa bai kamata ba ayi wa Annabi Muhammad (S.A.W)
hassada ba kamar yadda akayi wa Annabi Isah hassada kafun
haka ta bangaren bani isra’ila, domin ita kamar yadda mukayi
bayani ne kyauta ce daga Allah yana yin ta ga wanda ya ga
dama, Allah madaukaki yana cewa: “ shin ko suna yi wa
mutane hassada ne akan abunda Allah ya basu na falalar sa
to hakika mun baiwa mutanen gidan Annabi Ibrahim littafi
da hikima kuma mun basu mulki mai girma (54)” suratun
Nisa’i, aya ta: 54.
Kuma manzannin Allah amincin Allah ya tabbata a gare su
matsayin su da darajarsu sun banbanta su ba daidai suke ba ta
30
wurin falala kuma hakan falala ne daga Allah yana bada shi ga
wanda ya so cikin bayin sa, Allah madaukaki yana cewa: “
wadannan manzanni ne mun fifita sashin su akan sashe
daga cikin su akwai wanda Allah yayi wa magana kuma ya
daga darajar wasun su kuma mun baiwa Isa dan Maryama
ayoyi baiyanannu kuma mun karfafa shi da ruhi mai tsarki
inda Allah ya ga dama da wadanda suke bayan su basuyi
kashe-kashe ba bayan hujjoji sun zo musu sai dai su sunyi
sabani daga cikin su akwai wadanda sukayi imani kuma
daga cikin su akwai wadanda suka kafurce kuma da Allah
ya ga dama da basyi yake-yake ba sai dai Allah yana aikata
abunda yake so ne (253)” suratul bakara, aya ta “ 253.
31
Shi ne na farkon manzanni, Allah ya aiko shi bayan mutanen
shi sunyi shirka kuma halin su ya baci, kuma suka manta da
tushen shari’ar Allah wacce ya saukar wa Annabi Adam, sai
suka koma bautan gumaka, kamar yadda Allah ya baiyana
hakan da fadar sa: “lallai mu mun aika da Nuhu zuwa ga
mutanen sa cewa ka yi gargadi ga mutanen ka tun kafin
wata azaba mai radadi ta zo musu (1) sai yace ya ku
mutane na lallai ni mai gargadi ne a gare ku mabiyyani (2)
ku bauta wa Allah kuma kuji tsoran sa kuma kuyi mun
biyaiya (3) zai gafarta muku zunuban ku kuma zai muku
jinkiri har zuwa wani lokaci na musamman da aka aje lallai
lokacin da Allah yasa in yazo to ba’a jinkirta shi da kun
kasance kuna da sani (4)” suratu Nuh, aya ta: 1-4.
Sun riki gumaka guda biyar na su, sun kasance suna nufin su da
bauta kuma suna bauta musu koma bayan Allah: (Wudu –
Suwa’u – Yagusu – Ya’uqu – Nasra), Allah yayi bayanin su a
cikin Alkur’ani da fadar sa: “kuma suka ce kada kubar
ababen bautar ku kuma kada ku sake ku bar Wuddu da
Suwa’u da Yagusu da Ya’uqu da Nasra (23)” suratun Nuh,
aya ta:23.
Kuma shi Annabi Nuhu amincin Allah ya tabbata a gare shi ya
kasance mai tsoran Allah ne mai gaskiya, ya kira mutanen sa da
da hakuri da kuma tabbatuwa, kuma yabi hanyoyi daban daban
wurin kiran mutanen sa wadanda sukayi masa isgili kuma suka
karyata shi,kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “
32
sai yace ya ubangiji lallai ni na kira mutane na dare da
rana (5) amma kiran da nake musu bai kara musu komai
ba sai dai guduwa (6) kuma lallai ni a duk lokacin da nake
kiran su dan ka gafarta musu sai su sanya yatsun su a cikin
kunnuwan su kuma su nannada tufafin su kuma su kangare
kuma suyi girman kai girman kai (7) sa’annan lallai ni na
kira su a baiyane (8) sannan lalli ni na baiyana musu kuma
na musu a sirrance sirrantawa (9) sai nace musu ku nemi
gafarar ubangijin ku domin lallai shi ya kasance mai yawan
gafara ne (10)” suratu Nuh, aya ta: 5-10.
Ammma duk da haka ya ci gaba da kiran su tsira da amincin
Allah ya tabbata a gare shi kuma duk lokacin da ya kara
dagewa wajan kiran su da tunasar da su sai su kara kaimi wajen
kauda kai da dogewa akan barna, sai ya cigaba da yin hakuri a
kan su kuma ya ci gaba da kiran su zuwa ga addinin Allah sai a
ka samu mutane kadan suka bi shi, su kuma kafurai sai suka ci
gaba cikin kangarewar su sai Allah ya hana musu ruwan sama
sai Annabi Nuhu ya kira su zuwa ga yin imani dan Allah ya
dauke musu wannan azabar sai sukayi imani sai Allah ya dage
musu wannan azabar sai dai su daga baya sun koma cikin
kafurcin su, kuma yaci gaba da kiran su har tsawan shekaru dari
tara da hamsin sai daga baya Annabi Nuhu ya kai koke zuwa ga
ubangijin sa cewa mutanen sa sun saba masa kuma sun bi
batattu daga cikin su, sai ya roki ubangijin sa kuma yace:
“kuma Annabi Nuhu yace ya ubangiji kada ka bar wani
gida na kafiri a ban kasa (26) domin lallai kai in ka kyale su
to zasu batar da bayin ka kuma baza su dinga haihuwa ba
sai fajirai kafurai (27) ya ubangiji ka gafarta mini da
iyayena da duk wanda ya shiga gidana yana mumini da
33
muminai maza da mata kuma kada ka kara wa kafurai sai
dai halaka (28)” suratun Nuh, aya ta: 26-28.
Sai Allah ya karba addu’ar sa sai Allah ya umarce shi da gina
jirgin ruwa- kuma dama shi kwararre ne a bangaran kafintanciwannan farkon shiri ne na tsiratar da shi shi da wadanda suke
tare da shi cikin mutanen sa daga ruwan dufana wanda zai
wanke kasa daga kafurci, kuma aka ce ya dauki jinsi biyu na
kowane nau’in abu, sai ruwan dufana ya zo hakan kuwa ya
auku ne ta yadda Allah yayi umarni ga sama da tayi ruwa ita
kuma kasa ta fitar da idanun ruwa sai Allah ya nitsar da su baki
dayan su, kamar yadda Allah ya baiyana haka da fadar sa: “
mutanen Nuhu sun karyata gabanin su sai suka karyata
bawan mu kuma sukace mahaukaci ne kuma suka yi mai
tsawa (9) sai ya roki ubangijin sa yace lallai ni an rinjaye ni
to ka kawo mun agaji (10) sai muka bude kofofin sama da
wani rirn ruwa mai bubbugowa mai yawa (11) kuma muka
bude kasa da idanu ruwa sai ruwan ya hadu akan wani
lamari wanda an riga an kaddara shi (12) kuma muka
dauke shi akan jirgin ruwa ma’abociya katakai da kusoshi
(13) tana gudana kan kulawar mu wannan sakamako ne ga
wanda suka kasance sun kafurce (14) kuma hakika mun
barta aya ce shin ko akwai mai tunani (15)” suratul Kamar,
aya ta: 9-15.
Kuma Annabi anuhu tsira da amincin Allah ya tabbata a gare
shi ya kasance daga gare shi ne da yaran sa guda uku wadanda
suke tare da shi sauran mutane suka yadu, su ne: Saam (baban
larabawa da farisawa da rumawa), Haam: (baban bakake da
ifranjawa da kibtawa da indiyawa da sindawa), Yafis: (baban
turkawa da chinisawa da sakalibawa da ya’juju da ma’juju).
34
Maji dadin Allah baban Annabawa an haifa masa Isma’il da
Ishaq bayan ya tsofa amincin Allah ya tabbata a gare su, su ne
wadanda aka samu mafi yawancin Annabawa daga cikin
zurriyar su, kamar yadda Allah ya baiyyana haka da fadar sa: “
godiya ta tabbata ga Allah wanda ya bani Isma’il da Ishaq
bayan na manyanta lallai ubangiji na mai karbar addu’a ne
(39) ya ubangiji ka sanya ni mai tsaida sallah da kuma
zurriya ta ya ubangiji ka karbi addu’a ta (40)” suratu
Ibrahim, aya ta: 39-40.
Allah ya zabe shi da manzancin sa kuma ya fifita shi akan da
yawa daga cikin halittun sa, kuma Annabi Ibrahim amincin
Allah ya tabbata a gare shi ya kasance yana rayuwa a tsakanin
wasu mutane da ke shirka da Allah kuma suke bauta wa taurari,
kamar yadda Allah ya bada labarin haka da fadar sa: “ kuma
lokacin da Ibrahim yace wa mahaifin sa Azara shin yanzu
zaka riki gumaka a matsin ababen bauta lallai ni ina ganin
ka da mutanen ka kuna cikin wata irin bata baiyananna
(74) kuma haka nan muka nuna wa Ibrahim mulkin
sammai da kasa dan ya zama cikin masu yakini da tabbaci
(75) lokacin da dare ya shigo masa sai yaga wani tauraro
sai yace wannan shi ne ubangiji na lokacin da ya gushe sai
yace ni bana san masu gushewa (76) lokacin da yaga wata
ya fito a fili sai yace wannan shi ne ubangiji na lokacin da
ya gushe sai yace in dai har ubangiji na bai shiryar da ni ba
to lallai ni zan kasance cikin mutane batattu (77) lokacin da
yaga rana ta fita a fili sai yace wannan shi ne ubangiji na